Ticker

6/recent/ticker-posts

Zamani Zo Mu Tafi: Al’adun Hausawa a Duniyar Intanet (Babi Na Farko)

Citation: Sani, A-U. (2021). Zamani zo mu tafi: Al’adun Hausawa a duniyar intanet. [Kundin digiri na biyu da ba a wallafa ba]. Jami'ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Nijeriya.

ZAMANI ZO MU TAFI: AL’ADUN HAUSAWA A DUNIYAR INTANET

NA

ABU-UBAIDA SANI
Email: abuubaidasani5@gmail.com ko official@amsoshi.com
Site: www.abu-ubaida.com
WhatsApp: +2348133529736

Zamani Zo Mu Tafi: Al’adun Hausawa a Duniyar Intanet

BABI NA ƊAYA

GABATARWA

1.0 Shimfiɗa

Wannan bincike ya ɗauki intanet a matsayin “duniya” mai zaman kanta. A ciki (duniyar) akan tarar da duk waɗansu al’amura na yau da kullum suna gudana tamkar yadda suka kasance a sananniyar duniyar mutane.[1] Wani lokaci kuwa, al’amuran na kasancewa cikin siga da salo makamanciyar yadda suke a duniyar zahiri. Akan kuma samu cuɗanya tsakanin al’amuran da ke wanzuwa a duniyoyin guda biyu.[2] Babban al’amari kuma shi ne, akan rayu kuma a mutu a duniyar intanet.

A rahoton da BBC ta fitar bayan bincike kan Fesbuk a shekarar 2016, ta bayyana kafar Fesbuk a matsayin wata babbar maƙabarta. Rahoton na da taken: “Yadda Facebook ya zama makekiyar maƙabarta.”  An tabbatar da cewa, shekaru takwas (8) kacal bayan buɗe Fesbuk, an samu masu amfani da kafar da suka mutu kimanin miliyan talatin (30,000,000). Tun a shekarar 2012, adadin masu amfani da Fesbuk da ke mutuwa a kowace rana ya kai dubu takwas (8,000) (BBC, 2016: 1). Ke nan adadin zai ci gaba da hauhawa yayin da ake samun ƙaruwar masu amfani da kafar.

Haƙiƙa akwai buƙatar a samu jakadu da wakilan Hausa da Hausawa a duniyar intanet, tamkar yadda ake da su a duniyar zahiri. Wannan bincike sharar fage ne da zai buɗe hanyar samar da wakilcin al’adun Hausa a duniyar ta intanet. An karkasa aikin zuwa babuka biyar kamar haka: Babi na farko ya kasance gabatarwa ga binciken. A ciki ne aka kawo dalilin bincike da manufar bincike da maƙasudi da tambayoyin bincike. Bayan nan babin ya zayyana farfajiyar binciken tare da dabarun da aka yi amfani da su wajen kai wa ga nasarar kammaluwarsa.

Babi na biyu kuwa ya kasance bitar ayyukan da suka gabata. Da farko an yi bitar muhimman batutuwan binciken. Daga nan sai aka gangaro kan bitar ra’i. Daga ƙarshe kuma an yi bitar ayyukan da suke da dangantaka na kai tsaye da wannan bincike. Babi na uku ya mai da hankali ne kan duba ya zuwa bunƙasar aladun Hausawa a duniyar intanet. A nan ne aka dubi ci gaba da aladun suka samu a intanet ya zuwa yau. A babi na huɗu kuwa, an kawo bunƙasa da ƙalubalen kafafen intanet na Hausa. A ciki ne aka nazarci ci gaban da kakafen intanet na Hausa suka samu. Bayan nan sai aka dubi ire-iren ci baya da kafafen ke da shi. Babi na biyar shi ne na ƙarshe. Ya kasance kammalawar aikin. Ya ƙunshi taƙaitawa da sakamakon bincike da kuma shawarwari.

1.1 Dalilin Bincike

Intanet ya zo da gagarumin sauyi a ɓangarorin rayuwa daban-daban a faɗin duniya. Da wuya a samu wani al’amari da ya yi tasiri kan rayuwar al’umma tamkar intanet. Babu wani ɓangare na rayuwar ɗan’adam wanda intanet bai taɓa ba.[3]

Bayan samuwar intanet, rayuwa gaba ɗaya ta karkata alƙiblarta zuwa gare shi (intanet). Clement, (2020: 1) ya bayyana cewa: “By now, a world without the internet is unimaginable.” Ma’ana: “A yanzu, ba za a iya kwatanta yadda duniya za ta kasance ba idan aka ce babu intanet.” Domin tabbatar da maganar Clement, a yau an wayi gari:

i. Kasuwanci ba zai haɓaka ya yi gawurtar a-zo-a-gani ba, sai an haɗa da intanet.

ii. Makaranta ko cibiyar ilimi ba za ta kai ƙololuwa a fice ba, sai ta gwane wajen sarrafa intanet.[4]

iii. Ƙasa ba za ta samu bunƙasa da ƙarfin ikon faɗa-a-ji ba, har sai ta nuna wa duniya ita ba kanwar lasa ba ce a sha’anin intanet.

iv. Muryar malamin addini ba za ta karaɗe duniya ba, har sai an haɗa da intanet.

v. Al’adu da tadojin wata al’umma ba za su yaɗu a haƙiƙanin siffofi da sigoginsu ba sai idan masu su sun auri intanet.[5]

La’akari da waɗannan bayanai, abu ne mai muhimmanci a yi hoɓɓasa wajen samar da kyakkyawan wakilcin al’adun Hausawa a duniyar intanet. Kamar yadda Bahaushe ke cewa: “Sai bango ya tsage kadangare ke samun mafaka.” Yayin da aka nuna halin ko-in-kula game da bayyana wa duniya haƙiƙanin al’adun Hausawa, an ba da ƙofa ga mutane na daban domin aikata yadda suka ga dama.

A ɓangare guda kuwa, an samu ƙaruwar kafafen intanet na Hausa musamman daga wajajen shekarun 2015 zuwa yau (2020). Babban ƙalubalen shi ne, da dama daga cikin waɗannan kafafen intanet ba Hausawa ne ke jagorantar su ba. Hausawan ma da suke jagorancin kafafen sun kasance ba masu ilimin harshe da al’adar Hausawa ba. Dangane da yawaitar rubuce-rubucen Hausa a kafar intanet musamman na labarai, wata manazarciyar ƙagaggun labarai ta ce:

Mu ne ya kamata mu yi wani ƙoƙari na bincike tun da wuri domin mu gano tare da tantance inganci da rashin ingancin labaran Hausa da ake ɗorawa a kafafen intanet. Idan ba mu yi haka ba, kafin mu farga an yi musu gagarumar illa. (Adamu, 2019)[6]

Wannan na nuna cewa, tabbas akwai buƙatar gudanar da bincike a wannan ɓangaren. Dole ne binciken ya bibiyi inda aka kwana dangane da al’adun Hausawa a duniyar intanet. Hakan zai ba da haske kan irin ƙoƙari da masana da kuma cibiyoyi da sassan nazarin Hausa ya dace su yi. Ko da ma dai “Waƙa a bakin mai ita ta fi daɗi.”

Wani dalilin gudanar da wannan bincike shi ne sha’awar mai binciken kan al’amuran da suka shafi kwamfuta da intanet. A taƙaice idan aka yi amfani da wannan sha’awa yadda ya kamata, sai sakamakon ya kasance wata dirka da za ta tallafi wani gefe na shigifar al’adun Hausawa. Wannan ɓangare kuwa ya shafi kare ingancin wakilcin Hausawa a duniyar intanet tare da isar da al’adun nasu wuraren da ba su kai ba.

1.2 Manufar Bincike

Manufar wannan bincike ita ce nazartar al’adun Hausawa a cikin duniyar intanet domin tantance inda aka fito, da inda aka kwana, tare da ƙoƙarin samar da matakan inganta makoma (makomar al’adun Hausawa a intanet).

1.3 Maƙasudi

Domin cimma manufar wannan bincike, akwai manyan maƙasudai guda uku da aka zayyana. Su ne:

i. Nazartar yanaye-yanayen al’adun Hausawa cikin duniyar intanet,

ii. Nazartar ci gaba da ƙalubalen da ke dabaibaiye da kafafen intanet na Hausa, da

iii. Nazartar hanyoyi da matakan amfani da intanet wajen bunƙasawa da yayata al’adun Hausawa.

1.4 Tambayoyin Bincike

Akwai manyan tambayoyi guda uku da wannan bincike ya duƙufa wajen samar da amsoshinsu. Samuwar amsoshin nasu shi zai kai ga cin nasarar maƙasudan da aka zayyana a sama (ƙarƙashin 1.3). Hakan kuwa shi ke tabbatar da cimma manufar wannan bincike. Tambayoyin su ne:

i. Yaya yanaye-yanayen al’adun Hausawa suke a duniyar intanet?

ii. Waɗanne nau’ukan ƙalubale kafafen intanet na Hausa ke fuskanta?

iii. Waɗanne hanyoyi da matakan amfani da intanet ne za su iya taimakawa wajen ingantawa da yayata al’adun Hausawa?

1.5 Muhimmancin Bincike

Daga cikin muhimmancin wannan bincike akwai:

1. Zai zama sharar fage ga manazarta domin nazarin harshe da al’ada da adabin Hausawa a duniyar intanet. Hakan zai ba da damar samar da ingantaccen wakilci a kowane ɓangare. Ana sa ran ya kasance wani abin nazari ga ɗalibai da malamai da manazarta domin neman bayanai da suka shafi al’adun Hausawa a intanet.

2. Ana sa ran aikin ya samar da nagartattun shawarwari kan ingantattun hanyoyin da za a bi domin yayata al’adun Hausawa. Hakan zai taimaka wajen samar da tabbatattun bayanai game da al’adun Bahaushe tare da rage yaɗuwar gurɓatattun bayanai.[7]

3. Zai taimaka wa ɗalibai da malamai a darrusan da suka shafi ilimin intanet da harshe (Language and ICT).

4. Ana sa ran ya kasance wani mataki na samar da ƙarin litattatafai da mujallu da maƙalu (da makamantansu) na Hausa a kan intanet. Hakan zai taimaka wajen bunƙasawa da yayata aladu har ma da harshe da adabin Hausa.

5. Zai taimaka a matsayin wani hoɓɓasa na sanya Hausa cikin jerin Harsunan duniya da ke gudun-ya-da-ƙanin-wani a duniyar intanet. Wannan kuwa ci gaba ne da zai iya ƙara wa harshen ɗaukaka tare da yawaitar makaranta da manazartansa a matakin duniya.

6. Ana hasashen cewa, aikin na iya taimakawa ga muhawarar da aka daɗe ana gudanarwa dangane da Harshen Ƙasa (Harshen Hukuma) a Nijeriya.[8] Duk wani mataki na bunƙasa al’adu da harshen Hausa ƙarin daraja ne ga harshen (kamar yadda aka yi tsokaci a ƙarƙashin lamba ta 5 da ke 1.5). Bayan haka, yana mazaunin ƙarin ta-cewa ga muhawarar gabatar da Hausa a matsayin Harshen Ƙasa.

1.6  Farfajiyar Bincike

Wannan bincike ya taƙaita ne a kan al’adun Hausawa da intanet. Kadadar binciken ba ta wuce duniyar intanet ba. Ko a duniyar intanet ɗin ba ko’ina aka duba ba. Binciken ya taƙaita a kafafen intanet na Hausa kawai. Dangane da sauran kafafen intanet, an yi ƙoƙarin duba aladun Hausawa ne kawai daga cikinsu tare da nazartar irin tasirin da suka yi a kan aladun Bahaushe. Ma’ana, an bibiyi kafafen domin ganin abin da suke faɗa ko suke nunawa dangane da al’adun Hausawa. An cimma nasarar hakan ta hanyar:

i. nazartar nau’ukan rubuce-rubucen da ke kan kafafen dangane da al’adun Hausa;

ii. nazartar hotuna da ke kan kafafen dangane da al’adun Hausawa;

iii. nazartar bidiyoyi da ke kan kafafen dangane da al’adun Hausawa; da

iv. nazartar alamomi da ke kan kafafen dangane da al’adun Hausawa.[9]

Ba a iyakance adadin kafafen intanet da za a dubo waɗannan ba. Dalili kuwa shi ne, ya zuwa yau (2020), akwai kafafen intanet a duniya da adadinsu ya kai biliyan ɗaya da miliyan ɗari bakwai da hamsin da ɗaya da dubu talatin da ɗaya da ɗari huɗu da arba’in da bakwai (1,751,031,447) (Internet Live Stats, 2020: 1). Zaɓen wasu tsiraru daga cikin kafafen intanet ɗin na iya sa a tsallake wasu muhimman abubuwa da suka dace a yi magana a kansu. Hakan zai faru idan fitilar binciken ba ta haska kafafen intanet da ke ɗauke da waɗannan bayanai ba. A ɓangaren tasiri kuwa, za a yi ƙoƙarin binciken irin gurbin kafafen na intanet ga rayuwar Bahaushe, musamman aladunsa.

Domin nazartar hanyoyin inganta wakilcin al’adun Hausawa a duniyar intanet kuwa, za a mayar da hankali ne kan kafafen intanet na Hausa kawai. Har zuwa lokacin da aka shimfiɗa tabarmar ƙudurin wannan bincike, fitattun kafafen intanet na Hausa ba su wuce arba’in da huɗu (44) ba. Su ne:

  1. Abincin Hausawa: https://abinci.com/
  2. Al’ummar Hausa: https://www.alummarhausa.com.ng/
  3. Amsoshi:[10] https://www.amsoshi.com/
  4. Arewa Fresh: https://www.arewafresh.com.ng/
  5. Arewa Nishaɗi: https://www.arewanishadi.com/
  6. Arewa Swag: https://www.arewaswag.com.ng/
  7. Arewarmu: https://www.arewarmu.com.ng/
  8. Azare Online: http://azareonline.com/
  9. Baban Sadik: https://www.babansadik.com/
  10. Bakandamiya:[11] https://www.bakandamiya.com/
  11. Batsa Post: https://www.batsapost.com/
  12. Dandali: http://www.dandali.com/
  13. Duniyarso: http://duniyarso.blogspot.com/
  14. Gidan Karatu:[12] https://www.gidankaratu.com
  15. Gidan Novels: https://gidannovels.guidetricks.com/
  16. Gobir Mob: https://gobirmob.com/ha/
  17. Gumel: http://www.gumel.com/
  18. Haiman: http://www.haiman.com.ng/
  19. Hausa Dictionary: http://hausadictionary.com/
  20. Hausa Gett: https://www.hausagett.com.ng/
  21. Hausa Loaded: https://www.hausaloaded.com/
  22. Hausa Ng: http://www.hausang.com/
  23. Hausa Online:[13] https://hausaonline.wordpress.com/
  24. Hausa Top: http://www.hausatop.com/
  25. Hausa Trust: https://www.hausatrust.com/
  26. Hausa Weddings: https://hausaweddings.com/
  27. Hausawa Site: https://www.hausawasite.com.ng/
  28. Hutu Dole:[14] https://hutudole.com/
  29. Isyaku: https://www.isyaku.com/
  30. Jakadan Fasaha: https://www.jakadanfasaha.com/
  31. Jaridar Hausa: https://jaridarhausa.com/
  32. Ƙalubale: https://qalubale.news.blog/
  33. Kano Online: http://kanoonline.com/
  34. Katsina Post Hausa: http://katsinaposthausa.com/
  35. Madubiya: https://www.madubiya.com/
  36. Makarantar Hausa:[15] https://makarantarhausa.com/
  37. Managarciya: https://managarciya.com/
  38. Muryar ‘Yanci: https://www.muryaryanci.com/
  39. Muryar Hausa 24: https://www.muryarhausa24.com.ng/
  40. Rumbun Ilimi:[16] https://www.rumbunilimi.com.ng/ 
  41. Teach Yourself Hausa: http://www.teachyourselfhausa.com/
  42. Tsangayar Adabi: http://tsangayaradabi.blogspot.com/
  43. WikiHausa: https://www.wikihausa.com.ng/
  44. Zahra Muhammad Mahmud: http://zahramuhammadmahmud.blogspot.com/

Yana da kyau a fahimci cewa, akan samu wasu kafafen intanet da ke ɗauke da bayanai cikin harshen Hausa bayan waɗannan. Wasu daga cikinsu ba a gina su don Hausa kai tsaye ba. A bisa wannan dalili, ba a sanya ire-iren waɗannan kafafe cikin jerin waɗanda za a nazarta ba. Wasu kafafen kuwa, mallaki ne na gidajen rediyo ko talabijin ko jaridu. Waɗannan kafafe suna da manufofi takamaimai. Yawanci sukan mayar da hankali ne kan labarai cikin rubutu da hotuna da bidiyo da odiyo.[17] Wasu daga cikin waɗannan kafafe su ne:

1. Arewa24 News: https://www.arewa24news.com/

2. Dala FM: https://dalafmkano.com/

3. Freedom Radio Kano: https://freedomradionig.com/

4. Gidan Rediyon Amurka: https://www.voahausa.com/

5. Gidan Rediyon Bejin: http://hausa.cri.cn/

6. Gidan Rediyon Faransa: http://ha.rfi.fr/

7. Jaridar Aminiya: https://aminiya.dailytrust.com.ng/

8. Jaridar Leadership Hausa: https://hausa.leadership.ng/

Dangane da waɗannan kafafen intanet na Hausa, za a mayar da hankali ne kan abin da ya shafi al’adu kawai. Hakan na nuna cewa, harshe da adabin Hausa ba sa cikin kadadar binciken. A cikin kafafen, za a yi ƙoƙarin zaƙulo aladun Hausawa. Wannan kuwa ya shafi:

i. nazarin inda aka fito dangane da adanawa da yayata al’adun Hausawa a duniyar intanet;

ii. nazarin matsayin da al’adun Hausawa suka tsinci kansu a yau cikin waɗannan kafafen intanet na Hausa;

iii. nazarin matsaloli ko barazanar da al’adun Hausa ke fuskanta a duniyar intanet; da

iv. nazarin hanyoyi ko matakai da za a iya inganta kafafen.

Daga cikin kafafen arba’in da huɗu (44), an zaɓi guda talatin da tara (39) a matsayin waɗanda za a gudanar da binciken a kansu. Wannan ya yi daidai da ƙa’idar ɗaukar samfuri na Krejcie & Morgan, (1970). A taƙaice, huɗu daga cikin kafafen ne kawai ba a ɗauke su a matsayin samfuri ba. An yi amfani da tsarin zaɓe na kan-mai-uwa-da-wabi (random sampling).

Kafafen da aka zaɓa su ne:

1. Abincin Hausawa

2. Al’ummar Hausa

3. Amsoshi

4. Arewa Fresh

5. Arewa Nishaɗi

6. Arewa Swag

7. Arewarmu

8. Baban Sadik

9. Bakandamiya

10. Batsa Post

11. Dandali

12. Duniyarso

13. Gidan Novels

14. Gobir Mob

15. Gumel

16. Haiman

17. Hausa Gett

18. Hausa Loaded

19. Hausa Ng

20. Hausa Online

21. Hausa Top

22. Hausa Trust

23. Hausa Weddings

24. Hausawa Site

25. Hutu Dole 

26. Jakadan Fasaha

27. Jaridar Hausa

28. Ƙalubale

29. Kano Online

30. Katsina Post Hausa

31. Madubiya

32. Makarantar Hausa

33. Managarciya

34. Muryar ‘Yanci

35. Rumbun Ilimi 

36. Teach Yourself Hausa

37. Tsangayar Adabi

38. WikiHausa

39. Zahra Muhammad Mahmu

1.7 Hanyoyin Gudanar da Bincike

Domin samun ingantattun bayanai tare da cimma manufar binciken, an bi wasu tsararrun hanyoyin gudanar da bincike. Hanya ta farko ita ce “hira.” Wannan ya kasance ta fuskoki daban-daban. Za a iya karkasa su kamar haka:

i. An yi hira da masana al’ada da adabi da harshen Hausa domin samun bayanai da suka haskaka wa binciken hanya. Har ila yau, daga bakin masanan ne aka samu tabbacin ingancin wasu ra’ayoyi da aka kalato yayin gudanar da binciken.

ii. An yi hira da masana ilimin intanet a matakai daban-daban. Hakan ya taimaka wajen samun haske game da duniyar intanet tare da samun ilimi kan hanyoyin tattara bayanai mafiya inganci.

iii. An yi hira da masu gudanar da kafafen intanet na Hausa daban-daban. Wannan ya taimaka kai tsaye wajen samun ƙarin haske kan inda aka fito da matsayinsu a yau tare da hasashen gobensu. Har ila yau, ya taimaka wajen fahimtar ƙalubale da kafafen intanet na Hausa ke fuskanta. Daga nan ne kuma aka samu damar nazartar hanyoyin magance matsalolin tare da matakan inganta aladun Hausa a duniyar ta intanet.

Hanya ta biyu da aka bi ita ce karance-karancen kundayen digiri da ƙamusoshi da littattafai da mujallu da maƙalu da jaridu. Bai tsaya a nan ba, ya shafi nazartar duk wani maadanin ilimi a rubuce ko cikin bidiyo ko sauti (odiyo). An cimma hakan ta hanyar ziyartar ɗakunan karatu da cibiyoyin nazari (musamman na nazarin Hausa). Wannan duka ya taimaka wajen samun ƙarin haske kan batun da ake magana a kansa. Bugu da ƙari ya taimaka wajen haskaka wasu kalmomi da batutuwa da suka shafi binciken.

Hanya ta uku kuwa ita ce bibiya da nazartar duniyar intanet ta fuskoki daban-daban. Wannan ya haɗa da nazarin sigar duniyar da hada-hada da kai-komo da sauran al’amura da ke gudana cikinta. A ɓangare guda kuwa ya shafi bincike kan ƙididdigaggun alaƙaluman shaanoninta na yau da kullum. Hakan ya ba da haske a yunƙurin da ake yi na nazartar aladun Hausawa a duniyar intanet. Ya kuma ba da damar nazartar tasirin intanet ɗin a kan al’adun Hausawa. Kai tsaye an mayar da hankali wajen:

i. Yin amfani da injunan nema domin zaƙulo bayanai da suka shafi aladun Hausawa a duniyar ta intanet. Waɗannan injuna sun haɗa da:

a. AOL

b. Ask

c. Baidu

d. Bing

e. DuckDuckGo

f. Google (Gogul)

g. Internet Archive

h. WolframAlpha

i. Yandex (Yandes)

j. Yahoo (Yahu)

A cikinsu an fi mayar da hankali kan Gogul kasancewar ya fi tattara bayanai sama da sauran injunan. Binciken Pandey,  Shukla, &  Pradhan, (2015: 138-143) ya tabbatar da cewa Gogul ne ke fara zuwa koyaushe kafin sauran injunan.

ii. An bibiyi manya kuma amintattun kafafen da suka shahara wajen samar da ƙididdigar alƙaluma dangane da duniyar intanet (misali Live Internet Stats[18] da Statista[19]). Hakan ya taimaka wa yunƙurin wannan bincike na gano tasirin intanet kan rayuwar alummar duniya a jimlace. Daga nan kuma an kalli wannan tasiri a kan rayuwar Hausawa wanda shi ne ya shafi maƙasudin binciken kai tsaye. Abubuwan da aka bincika a nan sun haɗa da:

a. Adadin kafafen intanet[20]

b. Adadin mutanen da ke amfani da intanet

c. Adadin kafafen intanet na Hausa da alƙalumman ƙididdigar da ke nuna adadin Hausawa da ke amfani da su a kullum

d. Bayanai da ke nuna tasirin intanet kan rayuwar al’umma gaba ɗaya, da kuma Hausawa a keɓance

Yayin gudanar da binciken, waɗannan hanyoyi uku sun kasance cikin sigar zamantakewa ta cuɗe-ni-in-cuɗe-ka. Ana sa ran idan aka yi amfani da su gaba ɗaya cikin sigar da ta ɗace, za a kai ga nasarar cimma manufar wannan bincike. A yayin gudanar da binciken:

1. Karance-karance da hirarraki da aka gudanar, su suka tabbatar da ingancin bayanai da aka samo daga kafafen intanet dangane da al’adun Hausawa. Ta haka ne aka iya ware ingantattun bayanai da kuma gurɓatattu kai tsaye.

2. Wasu daga cikin littattafai da mujallu da maƙalu da jaridu a kan intanet aka same su. Da ma dai a ƙarƙashin 1.0, an bayyana cewa akan samu ɗakunan karatu a duniyar intanet kwatankwacin yadda abin yake a duniyar zahiri.

3. Hirarraki kuwa a ɗaya ɓangaren, sun ba da haske kan hanyoyin da suka fi dacewa da a bi wajen samun ingantattun bayanan da za su kai ga cimma manufar binciken. Wasu daga cikin hirarrakin kuwa an yi su ne da taimakon kafafen intanet kamar TeamViewer da Zoom.[21]

1.8 Kalmomin Fannu

Fassarori

Akwai kalmomin fannu da babu fassarorinsu na gama-gari. Ma’ana, ba a riga da an yi musu takamaimai fassarori da suka sanu a tsakanin ɗalibai da manazarta da masana Hausa ba. A bisa wannan dalili, binciken ya zayyano ire-iren waɗannan kalmomi ko batutuwa tare da bayyana fassarar da aka ba wa kowanne. An yi hakan domin mai karatu ko nazari ya fahimci abin da ake nufi da kowace kalma ko batu.

Bottom-up: Daga ƙasa zuwa sama

Graph: Giraf

Incorporealism: Ra’in Ɓoyayyiyar Gaskiya

Incorporeality: Ɓoyayyiyar Gaskiya

Natural: Al’adar Rayuwa

Pulatonism: Pulatoriyya

Realism: Zahiriyya

Service: Sabis

Sprituality: Baɗiniyya

Top-down: Daga sama zuwa ƙasa

Taƙaitattun Kalmomi

BBC: British Braodcasting Company

DW: Deutsche Welle

ND: No date (Ba shekara)

RFI: Radio France Internationale

VOA: Voice of America

1.9 Naɗewa

Za a iya kallon intanet a matsayin duniya mai zaman kanta. Da ma dai ra’in Pulatoriyya na da tunanin cewa gaskiya iri biyu ce (wadda ake gani da wadda ba a iya gani). Da a ce intanet zai bayyana a gan shi ciki da waje, tabbas da za a tarar yana ƙunshe da duk wani abin da ake da shi a duniyar zahiri. Akwai ƙarancin ingantancen wakilci na aladun Hausawa a wannan duniya ta intanet. Hakan kuwa ba ƙaramin ƙalubale ba ne ga Hausa da Hausawa a idon duniya. A bisa haka, akwai buƙatar gudanar da bincike da zai nazarci lamarin tare da gabatar da ingantattun hanyoyi da matakan tunkarar ƙalubalen. Hakan kuwa shi ne manufar wannan bincike.

Domin cimma manufar, an gina binciken kan maƙasudai guda uku. Sun shafi nazarin aladun Hausawa a duniyar intanet da tasirin intanet ɗin kan al’adun Hausawa da kuma hanyoyin ingantawa da yayata al’adun a kafafen intanet. Kadadar binciken ba ta fita daga cikin da’irar al’adun Hausawa da duniyar intanet ba. Ninƙaya cikin intanet da karance-karance da hirarraki su ne dabarun da suka taimaki binciken domin haƙa ta cimma ruwa.



[1] A duniyar intanet akan samu ɗaiɗaikun mutane (akawun-akawun da kafafen intanet na ɗaiɗaikun mutane). Akan kuma samu unguwanni (zauruka da kafafen intanet na tarayya). Ana kuma samun garuruwa da ƙasashe. Alamuran da ke gudana a kowane daga cikin ɓangarorin sun kasance tamkar a duniya ta daban wadda ta kai ta dogara da kanta. A duniyar intanet:

i. Akan samu kasuwanci na gudana tamkar yadda ake yi a duniyar zahiri ta mutane (kasuwanni da shaguna da dillalai da makamantansu).

ii. Ana samun zamantakewa da rayuwa mai kama da mafarki. Misali, ana iya samun tarayya tsakanin al’ummomi daga ɓangarorin duniya waɗanda ba su taɓa kallon juna a zahiri ba.

iii. Akan samu makarantu da azuzuwa har da ɗakunan karatu.

iv. Akan samu gine-gine da wurare da sauran abubuwan amfani masu matsayi kwatankwacin na abubuwan amfanin ‘yan’adam a rayuwar zahiri.

[2] Daga duniyar zahiri ne ake samun damar cuɗanya da duniyar intanet ta hanyar na’urori. Wasu lokutan akan kai ga dawo da gudanarwar cuɗanyar zuwa duniyar zahiri. Misali, soyayyar duniyar intanet ta Isa Suleiman Fanshekara (ɗan Kano a Nijeriya) da Ba’amurkiya Janine Sanchez ta zama gaskiya. Don ƙarin bayani a duba BBC, (2020: 1)2 ko Abubakar, (2020: 1).

[3] Duk wani ɓangare na rayuwa da al’amuran zamantakewa da aka duba, sai an samu tasirin intanet ko dai kai tsaye, ko a kaikaice. Bayan taron watan Maris na shekarar 2010 da BBC ta shirya kan Tasirin Fasahar Intanet, ta wallafa a shafinta cewa: “Fasahar intanet fasaha ce da wasu masana ke cewa ta sauya fasalin yadda ake gudanar al'amuran rayuwa a duk faɗin duniya.”

[4][4] Yayin da makaranta ko cibiyar ilimi ke son ta yi fice a duniya, dole ta kasance ta yi amfani da intanet yadda ya kamata. A ciki za ta baje hajarta. Hakan zai sa mutane daga ko’ina a faɗin duniya su ci karo da ayyukan da makarantar ko cibiyar ke gudanarwa.

[5] Yayin da aka yi rashin sa’a al’umma ba ta da wakilai a kan intanet, za a samu wasu mutane na daban waɗanda za su riƙa ɗora bayanai dangane da al’adunta. Ba dole ne su ɗora gaskiya ba kasancewar ba su da ilimi na haƙiƙa game da al’adun. Abdullahi, (2017) ya yi tir da bayanan da ya ci karo da su a wata kafar intanet mai suna Maguzawa, kasancewarsa masani a wannan ɓangare (An tattauna da shi a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato a wajajen watan Satumba, shekarar 2017).

[6] Dr. Aliya Adamu wanda a lokacin take Shugabar Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya na Jami’ar Jahar Sakkwato, ta furta wannan batu ga Dr. Umar Bunza. Shi ya kasance dakta a ɓangaren adabi a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

[7] Har yau ana kai-komo a kan tarihin Bahaushe. “Maimakon a yi canjaras ga abu ɗaya, sai a ga kowane bakin wuta da irin nasa hayaƙi.” (Bunza, 2014: 1). Hakan ya biyo bayan kasancewar rubutattun bayanan farko kan tarihin ba Hausawa ne suka samar da su ba. Idan har aka yi sakacin barin duniyar intanet ba tare da wakilan ƙwarai ba, babu makawa tarihi na iya maimaita kansa. Kafin a farga, gurɓatattun bayanai kan Hausa da Hausawa na iya mamaye duniyar intanet.

[8] An daɗe ana gudanar da muhawara a kan wannan batu. Don ƙarin bayani ana iya duba Bamgbose, (1991) da Akindele & Adegbite, (1999) da Danladi, (2013) da Ogbonna, (2013) da Morakinyo, (2015) Argungu, (2016) da Ashafa, (2016) da Olatuja, (2016) da Tsaure & Sani, (2016).

[9] Alamomi da ke kan intanet wasu zane-zane ne waɗanda ba hotuna ba. Ana amfani da su domin yin ishara ko sauƙaƙa bayani.

[10] Mallakin Abu-Ubaida Sani da Shehu Auwal

[11] Mallakin Malam Lawan Ɗalha

[12] Mallakin Mohammed Atabo

[13] Mallakin Mr. Uwe Seibert

[14] Mallakin Bashir Ahmed

[15] Mallakin Bello Muhammad

[16] Mallakin Abubakar Muhammad Tsangarwa

[17] Akan samu wasu shirye-shiryen na daban da suka shafi faɗakarwa da ilmantarwa da nishaɗantarwa. Misali, Gane Mana Hanyar (BBC), Ra’ayi Riga (BBC), Afirka a Mako (DW), Ra’ayin Malamai (DW), Amsoshin Tambayoyinku (DW), Ciki da Gaskiya (VOA), Lafiya Uwar Jiki (VOA), Al’adunmu (FRI) (An samu waɗannan bayanai daga hira da aka yi da Malam Aliyu Hamma, ranar 5 ga watan Maris, shekarar 2020).

[18] Internet Live Stats kafa ce ta intanet da ta shahara wajen kawo ƙididdigar alƙaluma da suka shafi duniyar intanet. American Library Association (ALA) sun bayyana su a matsayin mafiya amincin ingancin bayanai daga cikin kafafen intanet da ke samar da ƙididdigar alƙaluman duniyar intanet. Domin ƙarin bayani sai a bincika https://www.internetlivestats.com/about/.

[19] Statista kafar intanet ce ta binciken alƙaluma wanda ke da babban ofishinta a Hamburg da ke Jamani. Tana karɓar bayanai daga hukumomi da gwamnatoci da cibiyoyin bincike daban-daban da ke faɗin duniya. Tana samar da bayanai cikin harsunan Ingilishi da Faransanci da Jamusanci da Sifaniyanci. Manyan kamfanonin duniya sama da dubu goma sha huɗu (14,000) sun aminta da ingancin bayanan da take samarwa. Daga ciki har da Google da Paypal da Adobe. Domin ƙarin bayani ana iya duba https://www.statista.com/

[20] Adadin kafafen intanet da ke duniya na nuna yadda al’umma suka damu da harkar intanet.

[21] TeamViewer da Zoom duk suna ba da damar wani da ke zaune a wuri na daban ya iya gudanar da al’amuran kwamfutar wanda suke magana da shi (a wani wuri na daban). Misali, wanda yake Indiya na iya gudanar da al’amuran kwamfutar wani da ke zaune a Nijeriya. Ta haka zai iya shiga cikin lunguna da saƙunan kwamfutar abokin hirar tasa domin nuna masa abubuwa daban-daban. Akan yi haka domin fayyace al’amuran kwamfuta da intanet masu wuyar ganewa a bayanin baki. Ma’ana, bayanan baki ba su kai a samu ilimin shiga wuraren ba tare da jagora ba.

Post a Comment

0 Comments