Article Citation: Suleiman, M. (2025). Sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano [Master’s dissertation]. Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
SAUYE-SAUYEN ZAMANI A WASU SARAUTUN SANA’O’IN GARGAJIYA DA AYYUKANSU A GARIN KANO
Na
SULEIMAN Musa
Email: musasuleiman424@gmail.com
Phone: 08061256096
BABI NA HUƊU
SAUYE-SAUYE A WASU SARAUTUN SANA’O’IN GARGAJIYA DA AYYUKANSU
4.0 Shimfiɗa
A wannan babin, an yi bayani ne a kan sauye-sauye a wasu sarautun sana’o’in gargajiya. Kamar
yadda farfajiyar wannan bincike ta nuna, aikin an taƙaita shi a kan sarautar Sarkin ɗori da Sarkin fawa da Sarkin gini da
Sarkin ƙira. Babin ya kawo bayani a kan asalin
sarautun sana’o’in gargajiya da yadda sarautun suke a da, da kuma sauye-sauyen da aka samu
a yanzu. Haka kuma, babin ya yi bayanin taƙaitaccen tarihin sarakunan da ke riƙe da waɗannan sarautu na
sana’o’in gargajiya a garin Kano. Babin ya yi bayani a kan hakiman sarautun
sana’o’i da ayyukansu da kuma ƙananan muƙamai na waɗannan sana’o’i. Sannan, an kawo bayanin
ayyukan sarakunan sarautun da sauye-sauyen da ke tattare da al’adun sarautun
sana’o’in Hausawa na gargajiya. Bugu da ƙari, babin ya yi bayanin
matsayin sarautun da dangantakarsu da kuma naɗewa.
4.1 Sarautun Sana’o’i
Magabata sun yi abin a zo a gani wajen
bayyana ma’anar sarautun sana’o’i daidai gwargwado. Ga abin da wasu daga ciki
suke cewa:
Sallaman Kano Alhaji Dauda, ya bayyana
sarautun sana’o’i da cewa:
“Sarautu ne da ake bayarwa ga wani
jajirtacce da ya keɓanta da wata sana’a ta gargajiya.
Galibi ba a ba wani irin wannan sarauta sai wanda ya gaji irin wannan sana’a
yake yin ta, kuma ya ƙware a cikinta.”[1]
Shi kuwa Alhaji Wada Muhammad (Shamakin
Kano), yana ganin sarautun a matsayin “Sarautu ne da ake naɗa wa wani daga
cikin rukunin wasu al’umma da suke gudanar da wata sana’a ta gargajiya. Akan ba
da wannan sarauta ga wani babba a cikin masu wannan sana’a domin ya jagorance
su da yi musu sulhu a tsakaninsu tare da inganta harkokin da suka shafi
rayuwarsu.”[2]
Ta la’akari da waɗannan ma’anoni da
magabata suka bayar, za a iya cewa: Sarautun sana’o’i sarautu ne na ‘yan gado
ba taka haye ba, akan ba da irin waɗanan sarautu ne ga wani jarumi a cikin
masu sana’a, wanda yake iya faɗa a ji ya kuma ba da umarni a aiwatar.
4.2 Asalin Sarautun Sana’o’in Gargajiya a Garin Kano
Idan aka ce asalin abu, ana magana a
kan salsala da tushe na wani abu da aka jima ana gudanar da shi shekara da
shekaru. Ita kuwa kalmar gargajiya ana ambatar ta, abu na farko da yake fara
zuwa a zuciyar Bahaushe shi ne, wannan abin daɗaɗɗe ne, wanda aka daɗe ana yi iyaye da
kakanni. Bisa ga haka, idan ana magana ta asalin sarautar Hausawa ya zama
wajibi a dubi yanayin zaman Hausawa tun farkon lokaci, wato tun kafin u cuɗanya da wasu ƙabilu ko al’ummomi.
Al’ummar Hausawa, kamar sauran
al’ummomin duniya ta samu ne tun daga zama irin na Gandu, wanda kuma ana zaune
ne a cikin gonaki. Da al’umma suka yawaita sai aka samu kafa ta buƙatuwar abubuwan more rayuwa da kula da lafiya da
makamantansu. Wannan dalilin ne ya sa aka ƙirƙiro dabarar noma da gini da saƙa da ƙira. An ɓullo da wannan
dabara ne domin a samu abinci da wurin zama (gidaje) da kuma gonaki. Hausawa
suka saba da irin wannan rayuwa da samuwar sana’o’i, shi ne ya sa aka samu
wanzuwar rukunin al’umma waɗanda suke gudanar da nau’ikan sana’o’i
daban-daban. Wannan dalilin ne ya haifar da samuwar sarautun sana’o’i irin su
sarautar sarkin noma da sarkin maƙera da sarkin ruwa
da sarkin aska da dai sauransu da dama. Argungu (2017:8-9).
Idan aka waiwayi tarihin sarautun
sana’o’in gargajiya a garin Kano, za a ga cewa mahadi ne mai dogon zamani.
Kasancewar tun farkon samuwar al’umma a garin Kano da sana’o’insu na gargajiya
suka tashi kuma da su aka san su. Tarihi ya nuna cewa, lokacin da Bayajidda ya
zo Kano, ya sauka a bakin dutsen Dala a wajen Kana maƙeri. Kana maƙeri ne ya ƙera masa takobin da ya yi amfani da shi wajen kashe macijiyar a garin Daura
da ake kira Sarki. Adamu (1997). Kenan, tun daga wannan, za a ga cewa an daɗe ana gudanar da
irin waɗannan sana’o’i a birnin Kano. Haka abin ya ci gaba a sassan rayuwar
al’umma, wanda wasu buƙatu na musamman suka haifar da samuwar
wasu sana’o’i a birni Kano. A kan samu rukunin al’umma da suke gudanar da wata sana’a
tasu ta gado, kamar dukanci da ƙira da jima da
rini da ɗori da sauransu.[3]
A wancan lokacin, idan za su naɗa shugaba ko
mai’ungwa, akan samu dattijo wanda ya fi kowa yawan shekaru, sai a naɗa shi a matsayin
shugaba. Akasari akan zaɓi wanda ya ƙware a kan sana’a da mutanen suka
gada kuma suke gudanarwa. Saleh (2006:33). A dalilin gudanar da waɗannan sana’o’i,
wasu unguwanni da ake gudanar da waɗannan sana’o’i suka samo sunayensu a
sakamakon masu gudanar da sana’o’in da suke zaune a unguwannin. A birnin Kano
akwai unguwar Dukawa wanda tarihi ya nuna cewa, mutanen wannan unguwa asali
sana’arsu ce dukanci. Haka abin yake a unguwar gini da Rimin ƙira da Lungun Maƙera da ke unguwar
Galadanci a cikin birnin Kano.
4.3 Sarautun Sana’o’in Gargajiya a Jiya
“Jiya” a wannan aikin tana nufin daga zamanin
mulkin sarkin Kano Abdullahi Bayero (1927) zuwa shekarar 1963.[4]
Sarautun sana’o’i a ƙasar Hausa, kusan su ne sarautun da aka
fara assasawa a ƙasar Hausa. Hakan ya biyo tsarin zaman
gidan Hausawa, wato mai gida da iyalansa. A wancan lokacin, kowane gidan
Bahaushe akan samu wata sana’a da suke gudanarwa a wannan gida. Kamar ƙira ko fawa da dai sauransu. Wannan dalilin ne ya sa Hausawa suka ɗauki waɗannan nau’ukan
sarautu da mutuƙar muhimmanci, kuma aka ci gaba da
gudanar da su har zuwa yau. Duk da cewa sarautun, na sana’o’i ne, ba kai tsaye
ake naɗa su ba. Ana yin la’akari da waɗansu mizanai da sai mutum ya cika su,
sannan ake iya naɗa shi a irin waɗannan sarautu na sana’o’in gargajiya.
Daga cikin mizanan, akwai:
4.3.1 Gado
Gado na nufin dukiyar mamaci, kamar
yadda ƙamusun Hausa (2006:149) ya bayyana cewa
gado dukiyar da mamaci ya bari, ko kuma muƙami ko hali ko sifa ko kaya da mutum ya gada. A al’adar waɗannan sarautu na sana’o’in gargajiya,
ba a naɗa kowa, dole sai ɗan gado. Wato dai ya kasance ga
maihaifinsa ko kakansa ya gaji wannan sana’a da sarauta, kuma yana yin sana’ar
a aikace. Galibi a al’ada, ko da mutum ya gaji sarauta idan ba ya aiwatar da
sana’ar, ba a cika naɗa shi a wannan sarauta ba. Saboda ana
ganin bai fahimci sana’ar ba, balle kuma ya san halin da take ciki. Wannan ne
ya sa a tsarin bayar da sarauta a ƙasar Hausa, gado
yana da mutuƙar tasiri sosai. Gaskiyar malamin waƙa Ibrahim Narambaɗa da yake cewa:
Jagora: Ko dauri ƙoƙarin ɗan Sarki,
: Ya kai ga gadon tsoho nai,
Yara: Iro ya kai ga gadon Magaji,
Dango ɗan Garba,
Ga ya gun hannunai,
Gindi: Ginjimin Haliru Uban Zagi
Na Malam Isa.
A nan Narambaɗa ya kawo hoton
gado a cikin tsarin sarautun Hausawa na gargajiya, inda ya nuna cewa duk ɗan Sarki burin sa
ya zama Sarki. Wato dai ya gaji mahaifinsa a wannan sarauta.
Haka abin yake, Idan aka waiwayi Alhaji
Musa Ɗankwairo a cikin waƙar ‘Yandoton Tsahe ya tabbatar da wannan iƙirari, inda yake cewa:
Jagora: Kyawon ɗan Sarki talatin,
: Ɗan Sarki sai yay yi sittin,
‘Yan amshi: Bai gaji gidansu ba ta ɓace mai,
: Sai biɗar jalli, ai dugun
jakkai,
: A samu na shan dawo kar a lalace.
Gusau, (2009:102).
A nan za a ga cewa Ɗankwairo ya nuna gado a cikin wannan ɗiyan waƙa, inda yake cewa, kyawun duk ɗan Sarki yana so
ya gaji gidansu. Idan har ya kai shekara talatin bai gaji gidansu ba, kuma
shekarunsa ya kai sittin, to sai dai ya nemi sana’a a samu na cin abinci ka da
a shiga gararin rayuwa.
4.3.2 SƘwarewa
Kwarewa ita ce iya yin abu sosai.[5] Ga al’ada bayan mutum ya kasance ɗan gado ga wata sarauta, musamman ma ta sana’a, yana da mutuƙar tasiri ya kasance ƙwararre ne shi kuma gwani a wajen gudanar da wannan sana’a. Ƙwarewa na ɗaya daga cikin mizanai na al’ada da ake dubawa idan za a yi wa mutum sarauta. Wannan shi ne zai sa idan aka yi wa mutum sarauta, masu gudanar da sana’ar za su riƙa ganin ƙimarsa da darajarsa saɓanin wanda ba ya yin wannan sana’a.
4.3.3 Jaruntaka
A dauri akan ba jarumi irin wannan
sarauta, musamman ma a ce ya gaji wannan sarauta. Hausawa sun yi imani da cewa,
duk inda jarumi yake zai iya jagorantar wani rukuni na masu sana’a a duk
lokacin da wani abu ya taso, kamar hari ko kuma yaƙi da makamantansu. Waɗannan jarumai su ne haziƙan da suke ba da gagarumar gudummawa a lokacin gudanar da
yaƙi. Yaƙin yakan iya kasancewa tsakanin wata masarauta da wata, ko kuma tsakanin
wata ƙabila da wata. A ƙasar Hausa kowane gari ko ƙasa tana da ƙa’doji da take bi
wajen naɗa wannan sarauta, wasu akan gwada jarumtarsu ta hanyar kokowa ko harbi da
dai makamatansu. Misali: A ƙasar Kano a dauri suna
amfani da ƙarfi a matsayin mizani na samun
sarauta. Su kuwa ƙasar Katsina, suna da abin da suke kira
da “gagara kaye”. Wato za a yi kokawa duk wanda ya yi nasara shi zai zama
sarki.[6]
4.3.4 Sanin Asirai
Shaharar mutum wajen sanin asirai da
tsafi da surƙulle na wannan sana’a na taimakawa wajen
ba wa mutum sarauta. Ba irin waɗannan mutane sarauta yana taimakawa
wajen kare martaba da daraja da ƙima na masu sana’ar da kuma al’ummar da yake jagoranta.
4.4 Sarautun Sana’o’in Gargajiya a Yau
“Yau” a wannan aikin tana nufin daga
zamanin mulkin sarkin Kano Ado Bayero (1964) zuwa shekara 2024. A wannan
zamanin da aka ambata, sarautun sana’o’in gargajiya sun ɗauki wani sabon
salo baya ga tsohon tsari na al’ada da ake bi wajen samar da waɗannan sarautu. Duk
da cewa ba za a rasa rina a kaba ba, amma zamani ya yi mutuƙar tasiri wajen naɗa waɗannan sarautu.
Wannan tasiri ya wanzu a sakamakon cuɗanya da baƙin al’adu na wasu al’ummomi da shigowar kayan ƙere-ƙere da na kalle-kalle na Bature da
sauransu. A wannan lokaci akan yi la’akari da wasu abubuwa a kaikaice gabanin a
yi wannan sarautu. Daga cikinsu, akwai:
4.4.1 Gado
Gado a sarautar gargajiya har yanzu
yana taka muhimmiyar rawa. Duk da ana kauce masa ga naɗa wasu sarautun
gargajiya. A wannan lokaci da ake ciki, akan yi la’akari da gado kafin a yi wa
mutum waɗannan sarautu na sana’o’in gargajiya. Babu yadda za a yi a ɗauko wani wanda
bai gaji waɗannan sana’o’i ba a ba shi wannan sarauta saɓanin wasu sarautu
da ake naɗawa irin sarautun karramawa ko na alfarma da dai sauransu.
4.4.2 Siyasa
Ƙamusun Hausa (2006:397) ya bayyana siyasa da cewa tafiyar da al’amuran
jama’a hanyar neman ra’ayinsu da shawarwari da su. Ko kuma dabara ko wayo na
iya hulɗa da jama’a. Yanayin siyasar Nijeriya ta yi mutuƙar tasiri wajen naɗa wasu sarautun sana’o’in gargajiya.[7]
Wannan ya faru ne kasancewar sauyawar zamani. An samu kai a lokacin da ƙarfin iko da zartarwa ya koma hannun ‘yan siyasa. Wannan ne ya sanya idan irin waɗannan sarautu suka
faɗi, an fi naɗa wanda yake da ra’ayin siyasa na gwamnatin da ludayinta yake a kan dawo.
Hakan na faruwa ne sakamakon ɗaurin gindi da suke da shi a wajen masu
riƙe da madafun iko a wannan gwamnati. Ko
wanda yake da dangantaka da su a mu’amula, ko ya yi komun ƙafa da su don cimma wannan buƙata ta samun
sarauta.
4.4.3 Abin Hannu (Kuɗi)
Abin hannu a nan yana nufin samun arziƙi na kuɗi, kamar yadda ƙamusun Hausa (2006:251) ya bayyana kuɗi da cewa, ƙarfe ko takarda ko wani abu da hukuma
ta amince a yi amfani da shi don saye da sayarwa. A wannan lokaci, ƙarfin arziƙi da jari yana yin
mutuƙar tasiri wajen samuwar sarautu irin na
sana’o’in gargajiya a garin Kano. Musamman a wannan lokaci da aka riska da wasu
masu riƙe da madafun iko na al’ada suke fuskantar ƙamfar tattalin
arziki. Ana ganin bai wa mai abin hannu irin waɗannan sarautu zai
taimaka wajen cigaba da bunƙasa tattalin arziƙin waɗannan sana’o’i. Haka kuma, zai samu sauƙin gudanar da al’amuran sarautar cikin kwanciyar hankali tare da bunƙasa ayyukan sana’ar da masu sana’ar.
4.5 Sarautar Sarkin Ɗori
Ɗori a wannan bincike na nufin ƙarin wani abu a
kan wani, ko gyaran karaya ta ƙashin mutum ko
dabba Ƙamusun Hausa (2006:126). Sarautar
sarkin ɗori kuwa, sarauta ce babba ga masu gudanar da sana’ar ɗori a birnin Kano
da ma wasu sassan ƙasar Hausa. Sarkin ɗori shugaba ne na
masu wannan sana’a, shi ne mai jagorantar masu sana’ar, ta fuskar mulki tare da
samar da dokoki wajen tafiyar da wannan sana’a. Babu wata al’umma da ba ta
mu’amula da harkar ɗori, kasancewar sana’a ce da ta shafi ɓangaren lafiyar
al’umma. Wannan ne ya sa al’umma a birnin Kano da ƙasar Hausa suka ɗauke ta da muhimmanci ƙwarai da gaske.
4.5.1 Asalin Sarautar Sarkin Ɗori a Birnin Kano
Sana’ar ɗori tsohuwar
sana’a ce da ta ɗauki tsawon lokaci a na gudanar da ita a duniya. Ana gani cewa, tun zamanin
Annabi Muhammadu (S.A.W), ake aiwatar da wannan sana’ar ta ɗori.[8]
A birnin Kano kuwa, masu gudanar da wannan sana’a wata zuri’a ce daga cikin
Wangarawa da suka zo birnin Kano daga ƙasar Mali suka
zauna, a zamanin Sarkin Kano Tukur (1892).[9]
Ganin yadda wannan sana’a ta karɓu kuma zuri’arsu ta yalwata sosai a
cikin garin Kano. Wannan ne ya sa Sarkin Kano Tukur ya naɗa babbansu mai
suna Suleimanu a matsayin Sarkin ɗorin Sarkin Kano. Haka aka ci gaba da
tafiya, har aka kai ga yaƙin basasa, da aka
gudanar da shi a wani gari da ake kira Tafashiya tsakani Sarkin Kano Tukur da
Galadima Yusuf. A lokacin wannan yaƙi na basasa ne,
idan an sami wasu masu rauni da ya shafi karaya, sai Sarki Tukur ya nemi Sarkin
ɗori da ya zo ya ɗora waɗanda suka samu
karaya. Bayan rasuwar Sarkin ɗori Suleimanu da Madakin ɗori, ba a ƙara naɗa wannan sarauta ba ta sarkin ɗori a Kano
sakamakon rashin kulawa da waɗannan sarautu suke fuskanta a wannan
lokacin, har sai a zamani sarkin Kano Aminu Ado Bayero.[10]
Haka abin ya ci gaba da tafiya zamani
mai tsawo, har ta kai duk wasu daga cikin zuri’ar maɗoran Kano suna
kiran kansu da Sarakunan ɗori.[11]
Duk wani wanda yake gudanar da sana’ar ɗori a birnin Kano, yana kiran kansa da
Sarkin ɗori. Hakan ya biyo bayan tasirin da Sarautar Sarkin ɗori take da shi a
idon al’umma a birnin Kano. A wannan lokacin an samu ɗaya daga cikin
‘ya’yan Sarkin Kano da ya samu karaya, aka kawo shi wajen Sarkin ɗori.
A zamanin sarkin Kano Abdullahi Bayero
(1927) miladiyya, aka kawo ɗan Sarki mai suna Barde ya karye, sai a
kai rashin sa’a Sarkin ɗori ba ya nan. Sai Madakin ɗori suka tarar. A
nan ne Madakin ɗori ya yi ƙoƙarin ya ɗora shi, sai suka
hana shi suka ce su dole sai Sarkin ɗori shi ne zai ɗora shi. Madakin ɗori ransa ya yi
mutuƙar ɓaci. A lokacin da
Sarkin ɗori ya dawo, sai ya samu ɗan’uwansa cikin ɓacin rai. Wannan
ne ya sa ya tambaye shi abin da ya faru, madaki ya faɗa masa abin da ya
faru da aka kawo ɗan Sarki. Ko da jin haka, shi ma ya ce ba zai ɗora shi ba. A sakamakon haka, Sarki ɗori ya ƙi komawa gidan Sarki. Don haka, bai kuma koma ba ya dawo
gidansu, ya zauna ya ci gaba da sana’arsa ta ɗori. [12]
A zamanin Sarkin Kano marigayi Alhaji
Ado Bayero aka farfaɗo da wannan sarauta. Wannan ya faru a
sakamakon rauni da Sarkin Kano Ado Bayero ya samu a ƙafarsa wato (Ankle). Ya sa aka nemo masa mai ɗori, domin ya
gyara masa ƙafarsa. A nan ne aka kira Sarkin ɗori na yanzu
Alhaji Uba Muhammad ya ɗora shi. Da ya gama aikinsa, sai Sarki
ya ce, “dama har yanzu akwai irin ku a cikin al’umma”? Ya ce “sosai kuwa”. Daga
nan Sarkin Kano ya umarce shi da ya je ya samu Madakin Kano. Da ya je ya samu
Madakin Kano ya faɗa masa abin da Sarki ya turo shi.
Madakin Kano, ya ce “Sarki ya ce a naɗa ka Sarkin ɗorin Kano gaba ɗaya”. Kasancewar
sarautarku sarautar sana’a ce, kuma tana da muhimmaci sosai a cikin al’umma.
Sai ka je ka shirya. Cikin ikon Allah, shirin nan bai kammala ba, har Allah ya
yi wa Sarkin Kano Ado rasuwa, kuma ba a yi naɗin ba.[13]
Da Sarki Kano Muhammad Sunusi na II ya
zo, sai maganar naɗin sarautar sarkin ɗorin Kano ta ƙara tasowa. Wanda ake so a naɗa a Sarkin ɗori mai suna
Nafi’u, ya ɗora wani ɗan uwan Sarkin Kano Muhammadu Sunusi mai suna Aminu Tijjani Sunusi Bayero.
Daga nan Sarki Sunusi na II ya ce ya kamata a farfaɗo da wannan
sarauta ta Sarkin ɗori. A nan Sarki ya ƙara ba da umarnin a naɗa Alhaji Uba
Muhammad a matsayin Sarkin ɗorin Kano. A wannan lokaci shi ma
shirin naɗin Sarkin ɗori bai kammala ba, sai a zamanin Sarkin Kano Aminu Ado Bayero. Madakin
Kano ya tuna masa cewa da alƙawarin mahaifinka
na naɗa Sarkin ɗori. Shi ne ya ba da umarni aka naɗa sabon Sarkin ɗorin Kano. Wato
Alhaji Uba Yusuf Muhammad.[14]
An naɗa Sarkin ɗorin Kano a ranar 18/10/2020, bisa umarnin mai martaba Sarkin Kano Alhaji
Aminu Ado Bayero.
4.5.2 Taƙaitaccen Tarihin Sarkin Ɗorin Kano Alhaji Uba Muhammad
An haifi Alhaji Uba Muhammad Sarkin Ɗorin Kano a Unguwar Lokon Maƙera a ƙaramar Hukumar Gwale da ke Jihar Kano,
a ranar 17/11/1943. Ya yi karatun addini a wajen Alaramma Malam Aminu Liman da
ke Ƙofar Na’isa. Sannan ya yi karatun zamani makarantar firamare ta
Shahuci. Alhaji Uba ya yi aiki a hukumar tsafta ta jihar Kano. Daga bisani ya
koma harkar kasuwanci da harkar sufuri da sana’ar sayar da fatu da ƙiraga. Ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin mai biyan kuɗi wato (Cashier) a
kamfanin Alhaji Babbale Ila and Son
Limited, na marigayi Alhaji Baballe Ila. Ya kuma yi sana’ar ɗori, wadde ya gada
tun iyaye da kakanni.
Salsalar Alhaji Uba ta fara ne tun daga
kan mahaifinsa, wato Malam Muhammad Inuwa (Madakin Ɗori). An yi sarakunan ɗori guda biyar daga cikinsu akwai:
1.
Sarkin ɗori Yusufu
2.
Sarkin ɗori Suleiman
Shuada’u
3.
Sarkin ɗori Umaru
4.
Sarkin ɗori Yusufu na II
5.
Sarkin ɗori Uba Muhammad
Daga cikin mashahuran mutanen da ya yi
wa ɗori akwai marigayi Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero a ranar
2/4/1996. Allah ya jaddada rahama a gare shi da sauran al’ummar Musulmi baki ɗaya. Allah ya
albarkaci Sarkin ɗori Alhaji Uba Muhammad da ‘ya’ya maza 14 da mata 13 da jikoki da dama.
4.5.3 Ayyukan Sarkin Ɗori
A al’adar wannan sarauta, Sarkin ɗori shi ne shugaba
na zuri’ar maɗora na ƙasar Kano baki ɗaya. Dangane da
ayyukan Sarkin ɗori kuwa, akwai:
4.5.3.1 Aikin Ɗori
Sarkin ɗori Kano shi ne
mai gudanar da aikin sana’ar ɗori a birnin Kano.Yakan iya gyara ko ɗora karaya ko
gocewa ko ƙashi na ciwo ko riƙewar jijiya kuma tsagewar ƙashi da kuma
dangoginsu. A can dauri masu wannan sana’a daga tsatso ɗaya suka fito. Sai
dai a yanzu da aka samu sauyawar zamani, an samu wasu taka haye, da suke
gudanar da sana’ar ɗori, ba tare da sun gaji wannan sarauta
ba.
4.5.3.2 Kula da Gudanar da Aikin Ɗori
Sarkin ɗorin shi ne yake
kula da yadda masu wannan sana’a suke gudanar da ayyukansu bisa tsari ba kara
zube ba. Haka kuma, ya tabbatar da duk aikin da aka kawo musu wanda za a iya yi
ne, idan wanda ba za a iya yi ba ne, zai ba da shawara a tafi zuwa asibiti.[15]
4.5.3.3 Sulhu da Sasanci
A wajen gudanar da wannan sana’a ta ɗori, Sarkin ɗori shi ne jagora
kuma shi ne yake shari’a a tsakanin masu gudanar da wannan sana’a ta ɗori. Yin hakan shi
ne yake ƙara tabbatar da fahimtar juna a
tsakanin musu gudanar da wannan sana’a ta ɗori a birnin Kano.
4.5.3.4 Bayar da Magunguna
Sarkin ɗori shi ne yake
bayar da magunguna da suka shafi ƙashi a wannan sana’a ta ɗori. Magungunan suna iya kasancewa wasu
a sha wasu kuma a shafawa a wajen da aka sami rauni. Irin waɗannan magunguna
suna akwai manshanu da man kaɗe da sauransu. Sannan suna da sharuɗɗa d suke gindaya
wa wanda aka ɗora. Daga cikin su akwai:
1.
Kada a riƙa motsa ƙafar ko hannu inda aka samu karaya.
2.
Kada a yawaita cin abu mai maiko.
3.
A riƙa shafa ɓargon raƙumi daga lokaci zuwa lokaci.
4.5.3.5 Karɓar Haraji
Sarkin ɗori shi ne yake tattara harajin rukunin
al’ummar da yake jagoranta. Daga nan shi kuma sarkin ɗori ya kai wa mai
martaba Sarkin Kano. Wannan ba wani baƙon abu ba ne a ƙasar Hausa. Tun can dauri, shugabannin masu sana’o’in gargajiya su ne
suke karɓar haraji da jangali a wajen al’ummar da suke jagoranta domin kai wa gaba
inda ya dace.
4.5.4 Hakiman Sarkin Ɗori da Ayyukansu
Kamar kowace sarauta, sarautar Sarkin ɗorin Kano tana da
hakimai da ƙananan Sarakuna waɗanda suke taimaka
wa Sarkin ɗori wajen gudanar da wasu ayyukansa. Naɗa waɗannan hakimai da ƙananan Sarakunan ɗori na taimakawa wajen rage wa Sarkin ɗori nauyin da
Sarkin Kano ya ɗora masa a kansa. An yi haka ne kasancewar garin Kano gari ne ce Allah ya
albarka shi da yawan al’umma da kuma faɗin ƙasa. Wannan ne ya sa aka naɗa su domin Sarkin ɗori ya riƙa samun rahotannin al’ummar daga ɓangarori daban-daban a cikin garin
Kano. Daga cikin waɗannan hakimai da ƙananan sarakuna akwai:
4.5.4.1 Madakin Ɗori
Sarautar Madakin Ɗori sarauta ce babba a fadar Sarkin ɗorin Kano, shi ne na biyu a fadar, a
tsarin sarautar Sarkin ɗorin Kano. Madakin ɗori shi ne yake
wakiltar Sarkin ɗori a fadar Sarkin Kano, idan ya kasance Sarkin ɗori ya tafi wani
uzuri ko kuma ba ya nan.
4.5.4.2 Ciroman Ɗori
Sarautar Ciroman sarautar ta ɗanmajalisar Sarkin
ɗori ce wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suke zartarwa
da shi a majalisar Sarkin ɗorin Kano. Sannan yakan wakilci Sarki a
wajen wasu tarurruka da suka shafi masu gudanar da sana’ar ɗori ko kuma
sana’o’in gargajiya a Kano.
4.5.4.3 Galadiman Ɗori
Sarautar Galadiman ɗori a fadar Sarkin
ɗorin Kano, shi ne mai kula da duk wasu ayyuka da za a gudanar a fadar
Sarkin ɗorin Kano. Sannan shi ne mai karɓar baƙi, musamman ma waɗanda za a ɗora su, da ba su
kulawa a fadar Sarkin ɗorin Kano.
4.5.4.4 Garkuwan Ɗori
Garkuwan Sarkin ɗorin Kano shi ne
yake tare da Sarkin ɗori a yayin da yake zaune a fadarsa ko
kuma zai yi wata tafiya. Shi ne yake zame wa Sarkin ɗori kamar Sarkin
zagi a tsarin sarautar ƙasar Hausa.
4.5.4.5 Ma’ajin Ɗori
Kamar yadda sunan sarautar tasa ta
bayyana, shi ne mai kula da harkokin kuɗi na fadar Sarkin ɗorin Kano. Shi
yake bayar da duk wata kyauta ko gudummawar, da Sarki zai bayar wajen wata
hidima ko kuma taimakon mabuƙata da suka
ziyarci fadar Sarkin ɗori.
4.5.4.6 Mata A
Farfajiyar Ɗori
A al’adance, maɗora suna da hikima
na barin mata su yi wa mata aikin ɗori. Akan samu wasu mata da suka gaji
wannan sana’a a wajen iyaye da kakanni, suna gudanar da irin waɗannan ayyuka na
sana’ar ɗori a cikin gidajensu. Wannan ya biyo bayan samuwar ilimin addini Musulunci
a ƙasar Hausa, da haramta wa maza taɓa matan da ba nasu
ba, sai dai in da lalura. Wannan ne ya sa wasu mata magada wannan sana’a ta ɗori suka himmatu
wajen ganin sun cike wannan giɓi da aka samu. A yanzu haka, akwai mata
da dama da suke gudanar da wannan sana’a ta ɗori domin su
tallafi mata ‘yan’uwansu.
4.5.5 Ƙananan Sarakunan Ɗori
A tsarin sarautar Sarkin ɗorin Kano, akwai ƙananan sarakunan ɗori waɗanda suke wakiltar
Sarkin ɗori a ƙananan hukumominsu, musamman ma waɗanda ba a cikin
garin Kano suke ba. Haka kuma, wasu daga cikinsu sukan kawo masa ziyara fadarsa
lokaci zuwa lokaci tare da sanar da shi halin da al’ummarsu suke ciki, wasu
daga cikin irin waɗannan ƙananan sarakunan ɗori shi ne ya naɗa su. Wasu kuma ya
tarar da su ne a kan wannan sarauta tasu. Daga cikin irin waɗannan ƙananan sarakunan akwai:
1.
Sarkin Ɗori na Kwanar ‘yandaddawa da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo.
2.
Sarkin Ɗori na Ƙofar Na’isa da ke a Ƙaramar Hukumar
Gwale
3.
Sarkin Ɗori na Ƙaramar hukumar Wudil.
4.
Sarkin Ɗori na Warawa
4.5.6 Al’adan Sarautar Ɗori a Jiya
Babu wata sarauta a ƙasar Hausa da ba ta da wata al’ada da take gudanarwa, musamman a lokutan bukukuwansu, ko
bikin naɗin sarautar ko kuma bikin aure ko haihuwa. Daga cikin al’adun sarautar ɗori a cikin birnin
Kano akwai:
4.5.6.1 Bikin Naɗin Sarkin Ɗori
Wannan biki ne da ake gudanar da shi a
ranar da aka naɗa Sarkin ɗori. Za a fara wannan shagalin biki tun daga fadar Sarkin Kano bayan an naɗa Sarkin ɗori. Sarkin ɗori zai hau kan
doki ya taho gidansa inda za a taho ana ta kaɗe-kaɗe da bushe-bushe
irin na sarautar ɗori. A yayin wannan biki ne kowane daga cikin zuri’ar Sarkin ɗori zai fito filin
ƙofar gidan Sarkin ɗori ya nuna wata
buwaya da Allah ya hore masa a sana’ar ɗori.[16]
Haka kuma, irin waɗannan al’adu su ake gudanar a wajen
bikin aure da makamantansu.
4.5.6.2 Nuna Buwaya
A wancan lokacin, akan samu wasu da
suke iya fitowa fili su nuna buwayar da Allah ya hore musu a wannan sana’a tasu
ta ɗori. Misali, akan samu wasu ko wani ya riƙa karya ɗanyen karan gero ko dawa kuma ya ɗora shi a gaban mutane, kuma ya tashi
ya ci gaba da girmansa har sai ya fitar da kai. Wasu kuma su gitta kara a kan
hanya duk wanda ya zo tsallaka karan ya karye. Wasu kuma kan iya ɗora wanda ya yi
karaya daga gida ba tare da sun gan shi ba ko sun taɓa shi ba. Sai
kawai su ba da umarni su ce a daidai lokaci kaza a riƙe shi. A wannan lokacin za su ɗora shi kuma ya ɗoru. Haka kuma,
Bunza (2006:47) ya rawaito cewa “An ce wasu shahararrun masu ɗori, mutum zai
kare sai su ɗora shi ba tare da sun gan shi ba. A wasu lokuta kuwa, nan take za su ɗora wani wanda
yake a wani gari ko wata unguwa da ba tare da suna a wuri ɗaya ba. Wannan duk
tsafe-tsafe ne da aka tabbatar da samuwarsu a ƙasar Hausa.”
4.5.6.3 Kai Gaisuwa
A al’adance Sarkin ɗori ya kan je ya
kai gaisuwa fadar Sarkin Kano lokaci zuwa lokaci. Amma dai ga al’adar sarautar
ana kai wannan gaisuwa ne ranar juma’a. Sannan akan kai irin wannan gaisuwa a
lokutan bukukuwan sallah domin yi wa Sarkin Kano barka da sallah.
4.5.7 Sauye-Sauye a Sarautar Ɗori da Al’adunta
Sauye-sauye a nan yana nufin kutsen da wasu abubuwa na zamani suka yi a cikin sarautar ɗori, wanda hakan, ka iya jawo salancewar al’adar ko kuma ta yi rauni ko kuma ta ma ɓace gaba ɗaya. Tabbas zamani ya yi mutuƙar tasiri a sarautar sana’ar ɗori. Wannan ya faru a sakamakon karatun zamani da addini da ya yawaita a cuɗanyar wasu al’ummomi da ke gudanar da wannan sana’a a birnin Kano. Bisa ga manufar ra’in wannan bincike ta duba sauyin al’adun da ci gaban al’umma, an samu sauye-sauye da dama a sarautar Sarkin ɗori a garin Kano. Daga cikin sauye-sauyen akwai:
4.5.7.1 Samuwar Ofishin Sarkin Ɗori
A al’adance, duk inda wata masarauta
take a ƙasar Hausa, Sarkin ne yake jagorantar
wannan masarauta. Haka kuma, ba shi da wani waje da ya wuce fadarsa, domin a
nan ne yake zaman fadanci da kuma gudanar da shari’a da sauran ayyukan sarauta. A sakamakon sauyawar zamani,
an samu ofis wanda mafi yawan sarakuna suke amfani da shi maimakon fadarsa. Shi
ma Sarkin ɗorin Kano yana da ofis inda yake gudanar da ayyukansa na sarauta, tare da
aiwatar da sana’a ta ɗori. Wannan ofis ya zama kamar shi ne
cibiyar da suke gudanar da ayyukansu na sana’ar ɗori da mulki.
Dalili kuwa shi ne, ana shiga ofishin, za a ga tebur da kujeru da babban tebur
da shimfiɗu a kansa, wato inda ake kwantar da marar lafiya domin a yi masa aiki.
Sannan za a ga kayayyakin gudanar da wannan sana’ar an rataye su a jikin bango
a wannan ofis.
4.5.7.2 Rijistar Adana Bayanai
A dauri ba a damu da yin rijistar adana
bayanai ba, kasancewar ba a samu karatun da rubutu kamar yanzu ba, amma
sakamakon sauye-sauyen da zamani ya zo da su, musamman samuwar karatu da kuma
rubutu. An yi tsari mai kyau na ajiye ƙaton littafi mai
suna Rijista. Duk lokacin da aka kawo wa Sarkin ɗorin Kano aiki,
yakan sa a rubuta sunan mai wannan karaya da na mahaifinsa da adireshinsa da
kuma lambar wayarsu da kuma irin karayar da ya samu. Ana yin haka saboda
dalilai kamar haka:
1.
Idan wata matsala ta ƙara samuwa a nan gaba, za su ɗauko wannan bayani
da suka taɓa yi wa wannan aiki su duba, domin su san inda aka tsaya da kuma inda ya
dace a dosa.
2.
Buƙatar sanin adadin aikin da aka yi a cikin shekara. Misali, mutum nawa aka
yi wa aiki.
3.
Haka kuma, ana samun bayanai na waɗanda aka yi wa
aikin guiwa ko hannu ko ƙashin baya da
sauransu.
4.5.7.3 Naɗin Sarautun Mataimaka Sarkin Ɗori
Al’adar sarautar Sarkin ɗori a can baya,
sarautun duka guda biyu ne wato daga Sarkin ɗori sai Madakin ɗori a duk birnin
Kano. Yanzu zamani ya zo da sauyi, kuma birnin ya ƙara girma sosai, an samu sarautun yanki a ƙarƙashin Sarkin ɗori, waɗanda suke kula da
wani ɓangare na sarautar Sarkin ɗori a birnin Kano. Daga cikin akwai:
1.
Sarkin Ɗori na Kwanar ‘Yandaddawa
2.
Sarkin Ɗori na Ƙofar Na’isa.
4.5.7.4 Saukar Karatun Alƙur’ani
Saukar karatun Al’ƙur’ani ya zama kamar ruwan dare ga zuri’ar masu ɗori a birnin Kano. Wannan ya faru ne
saboda kasancewar su ma’abota ilimi na addinin Musulunci. Suna yin wannan sauka
ne yayin bukukuwansu da duk wani muhimmin abu da ya taso a cikin zuri’arsu da
nufin neman kariya da neman biyan buƙata ga Ubangiji.
4.5.7.5 Ziyarar Abokan Aiki
Sarkin ɗorin Kano kan ware
wasu lokuta na musamman domin ziyarar ‘yan ‘uwa da abokan sana’arsu ta ɗori da kuma
hakimansa da sarautun yanki da ke sauran ƙananan hukumomin
Kano da kewaye. Yana yin haka ne domin sada zumunci da kuma gane wa idonsa
yadda sauran wakilansa ke gudanar da ayyukansu a wuraren da suke wakiltarsa. A
al’dar wannan ziyara ana yin ta ne a
lokacin kaka. Sarkin ɗorin Kano kan sanar wa sarautun yanki
ranar da zai kawo musu ziyara, su kuma a wannan rana sukan shirya masa tarba ta
musamman da suka haɗa da makaɗa da mawaƙa, inda suke zuwa bakin gari su tare shi. Mai riƙe da wannan sarauta ta wannan yanki zai saka alƙyabba ya yi rawani, ya samu kujera ya zauna shi da
mutanensa. Idan sarkin ɗorin Kano ya ƙaraso, sai ya faɗi ya yi gaisuwa shi da mutanensa. Daga
nan sai su shigo cikin gari baki ɗaya domin yin ziyara ga ‘yan uwa da
abokan arziƙi, musamman masu gudanar da wannan sana’a ta ɗori.
4.5.7.6 Yanayin Naɗin Sarautar Sarkin Ɗori
Ana yin naɗin sarautu da ke ƙarƙashin Sarkin ɗorin Kano a ƙofar gidan Sarkin ɗori bisa sahalewar Sarkin Kano. Ana yin
naɗin ne inda ake saka rumfa canopy
da kujerun roba a zagaye wajen taron. Sannan a kan buƙaci wanda za a naɗa a wannan sarauta da ya kawo rawani da
kwagiri da Alkyabba da takarda mai ɗauke da nasabarsa da taƙaitaccen tarihin rayuwarsa. A tsarin naɗi a wannan
sarauta, madaki da galadiman ɗori su ne suke yi wa wanda aka naɗa rawani a wannan
wuri. Bayan an yi naɗi sai a raka wanda aka naɗa ya kai gaisuwa
ga Sarkin ɗori. Bayan ya kai gaisuwa Sarkin ɗori zai yi masa bayani akan irin nauyin
da aka ɗora a kan wannan sarauta da aka ba shi. A wannan wuri za a samu makaɗa da maroƙa da masu Dj da suke yi wa wanda aka naɗa waƙoƙi iri daban daban na sarauta. Daga nan
sai a ɗora shi a kan doki a raka shi zuwa gidansa. A wannan lokaci makaɗan za su bi shi
har zuwa gidansa, inda za su cigaba da yin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe
na al’ada.
4.5.8 Sauye-Sauye A Ayyukan Ɗori
Masu iya magana kan ce “Zaman riga
ne.....”, wannan batu haka yake, kasancewar zamani ya zo sabon salo na yanayin
yadda ake gudanar da ayyukan ɗori da suka yi daidai da zamani. Wannan
shi ya haifar da samuwar sauye-sauye a ayyukan ɗori. Daga cikin
sauyin da aka samu akwai:
4.5.8.1 Amfani da Auduga da Bandeji
A al’ada, ana yin amfani da kara da
yanki ko tsumma mai ƙwari wajen ɗaure karaya. A
yanzu kuwa, zamani ya zo da sababbin abubuwa masu tsafta. A dauri ba a damu ba,
idan an yi amfani da irin waɗannan kayayyaki a wajen aikinsu ba.
Saboda a wannan lokaci babu yawan cututtuka na zamani da ake tunani za a iya ɗauka. A yanzu
zamani ya zo, cututtuka sun yawaita. Wannan ne ya sa aikin sana’ar ɗori ya ɗauki wani sabon
salo. A yanzu suke yin amfani da kayan aiki na zamani wajen ɗori. Daga cikin
kayan aikin akwai: Auduga da Filasta da Bandeji da safar hannu. Haka kuma, a
dauri ana yin amfani da kara wajen ɗaure karaya, amma yanzu suna amfani da
wasu ƙanana kataƙwaye masu ƙyau ƙanana da ake amfani da su wajen yin sili, tare da bandeji wajen ɗora karaya. Idan
suka yi wannan ɗori a yanzu sai a ga aikin ma kamar a asibiti aka yi shi.
4.5.8.2 Amfani da Magungunan Zamani
A gargajiyance, ana amfani da manshanu
ko man kaɗe wajen aikin ɗori, amma a sakamakon sauye-sauyen
zamani da aka samu a wannan sana’a ɗori. Yanzu an samu wasu daga cikin
‘ya’yan maɗoran da suka yi karatun zamani (boko), wannan ya sa wasu daga cikinsu suke
rubuta wa wanda ya samu rauni wasu daga cikin magungunan zamani (tablets) da za su taimaka masa wajen
saurin haɗewar ƙashin da ya karye. Wasu daga cikin
magungunan da suke rubutawa sun haɗa da: Painkiller (analgesics), wanda ya ƙunshi paracetamol da codeine da occasionally morphine. Haka kuma, sukan
rubuta Non-steroidal anti-inflammatory
drug da ya haɗa da Iburofen ko naproxen. Duk waɗannan magunguna da
ake rubutawa, ana amfani da su ne domin su rage wa mai karaya zafi da raɗaɗin ciwon da yake
ji. Wasu kuma suna taimakawa wajen saurin haɗewar ƙashin.
4.5.8.3 Hoton Ƙashi (X-Ray)
A can dauri ba a san wani a je a yi
hoto ba, sai dai su maɗora su yi amfani da ilhama wadda Allah
ya ba su wajen ɗora karaya. A yanzu sauyin zamani ya zo da yin hoto (X-Ray), da mafi yawancin maɗora sukan sa a je a yi kafin su ɗora karaya. Sannan
bayan an ɗora karaya an samu sauƙi, sukan sa a je a
sake wani hoton. Yin hoton shi ne zai ba su damar duba ƙashin, ko ya ɗoru, ya haɗe ko sai an sake wani aiki.
4.5.8.4 Shugowar Hukuma
A baya sarakunan ɗori ba su damu da
saka hukuma a cikin aikinsu ba. Su ne suke yin shari’a, idan wani abu ya faru
da ya shafi wannan sana’a ta su ta ɗori, amma yanzu hukuma ta shigo ciki,
domin da wuya a kawo musu aikin karaya ba tare da hukuma ba. A wasu lokuta akan
zo da ɗansanda ko Civil Defence musamman
idan an yi haɗari, bugewar mota, faɗa daba da sauransu. Domin ya gane wa idonsa abin da yake faruwa a yayin aikin ɗori, sannan ya
kula da abin da aka kashe a yayin aikin ɗora karayar. Daga bisani su koma ofis ɗinsu don yin sulhu
da sasanci ko kuma yanke hukunci. Sauyin zamani na ƙarfin da hukuma take da shi a yanzu, shi ne ya rage ƙarfin ikon da Sarkin ɗori yake da shi na sulhu da sasanci a
yayin gudanar da aikinsa.
4.5.8.5 Zuwa Koyon Ɗori a Makarantun Boko
A baya aikin ɗori gado ne ga
masu sana’ar bisa bin tafarkin al’adar aikin. Sukan gudanar da aikin bisa yadda
iyaye da kakanni suka ɗora su a kai. A yanzu sauyin da zamani
ya zo da shi, sai abin ya sauya salo. Masu iya magana suna cewa; “idan kiɗa ya sauya, dole
ma rawa ta sauya”. Wannan dalilin ne ya sa mafi yawan masu sana’ar ɗori suke tura
‘ya’yansu makarantun zamani domin su yi karatun harkar lafiya, musamman ma abin
da ya shafi ƙashi da ɗori, domin su
inganta wannan sana’ar tasu, ta tafi daidai da zamani. Daga cikin ‘ya’yansu waɗanda suka yi
wannan karatu na lafiya da ya shafi ƙashi, akwai ɗaya daga cikin ɗan sarkin ɗorin Kano mai suna
Nafi’u Uba Muhammad. Ya yi karatun kuma yana aiwatar da wannan aikin na
karatunsa a fagen ɗori na al’ada. Ga hotonsa nan a
ofishinsa inda yake gudanar da wannan aiki na ɗori.
4.6 Sarautar Sarkin Fawa
Sarautar Sarkin Fawa sarauta ce da ake
samun ta ta hanyar gado da ƙwarewa a wannan
sana’a ta fawa. Mai riƙe da wannan sarauta shi ake kira “Sarkin Fawa”. Sarkin fawa shi ne yake shugabantar
masu gudanar da sana’ar fawa, shi yake
shimfiɗa dokokinta ta hanyar mulki tare da hukunci da kare lafiya da dukiyar
mahauta. Ita ma wannan sarauta Sarki ne yake naɗa ta ga rukunin
wannan al’umma. Haka shi ma Sarkin fawa yana da hakimai da suke tallafa masa
wajen gudanar da wannan jagoranci.
4.6.1 Asalin Sarautar Fawa a Birnin Kano
Sarautar Fawa sarauta ce mai daɗaɗɗen tarihi a birnin
Kano. A halin da ake ciki yanzu babu wanda zai iya bugun gaba ya ce ga lokacin
da aka fara gudanar da wannan sarauta a birnin Kano. Ana ganin cewa, sarautar
fawa ta faro tun daga lokacin da ɗan’adam ya ƙara wayewa da sana’o’in gargajiya da yawa, a sakamakon samun gindin zama da
sana’ar kiwo ta samu a birnin Kano, sai wasu suke ganin tsayawa yanka dabbobi
da gyara naman kamar ɓata lokaci. Daga nan ne waɗansu rukunin
al’umma daga cikin mutanen Kano suka ɗauki sana’ar sayar da nama wato fawa.
Shu’aibu (2002:27). Da sana’ar fawa ta samu cigaba, kuma garin Kano ya ƙara bunƙasa, sai aka samu
yawaitar masu gudanar da wannan sana’a a birnin Kano.
Ganin haka ya sa wannan rukunin al’umma
suka zaɓi dattijon da ya fi kowa shekaru a cikinsu ya zama shigabansu, domin kare
mutunci da martabar wannan sana’a. Wannan dalilin ne ya haifar da samuwar
sarautar fawa a birnin Kano.[17]
An samar da sarautar fawa ne a birnin Kano, domin a riƙa kula da yadda suke tafiyar da sana’ar da kuma tsafta ce ta.
4.6.2 Taƙaitaccen Tarihin Sarkin
Fawan Kano Alhaji Isiyaku Alin Muli
An haifi Sarkin fawan Kano Alhaji
Isiyaku Alin Muli a unguwar Juma da ke ƙaramar hukumar
Dala da ke cikin birnin Kano, a shekarar 1965. Kimanin shekara 58 a yanzu.
Sarkin Fawan Kano ya yi karatun addini daidai gwargwado a lokacin tasowarsa. Ya
yi karatun Allo a wajen malamansa irin su malam Maigari da malam Inusa Shaɗare da malam Sani,
duk a nan tsallaken Unguwar Jujin ‘Yallabu. Daga baya, ya yi wata makarantar
Islamiyya a Unguwar Dambazau.[18]
Sarkin fawan Kano ya yi karantun boko daidai gwargwado, inda ya yi makarantar
firamare ta Gwammaja da ke Ƙofar wakili. Wato
(Gwammaja Special Primary School) a yanzu. Haka ya ci gaba da karantunsa na
sakandare a makaranta Gwammaja II wato (Government Secondary School Gwammaja) a
yanzu. Duk da kasancewarsa ɗalibi a wannan lokacin, karatunsa bai
hana shi fita kasuwa wajen neman ɗari da kwabo ba. Yakan tafi kasuwa a
yayin da aka yi hutu, ya ɗauki tallar nama a faranti, ya zagaya
da shi cikin kasuwar Kurmi da ke cikin birnin Kano. Bayan ya kammala karatunsa
na sakandare, bai samu damar ci gaba ba. Wannan ne ya ba shi damar fara mayar
da hankalinsa a kan sana’ar fawa. Sarkin fawan Kano ya yi sana’ar fawa tun daga
matakin tallan nama a faranti, da sayar da ƙashi da sayar da kai da ƙafafu na awaki da
shanu da sauransu.
Da tafiya ta yi tafiya a shekarar 1985,
ya fara bin yayan mahaifinsa zuwa fataucin dabbobi. A wannan lokacin suna zuwa
kasuwanni, domin su sayo dabbobi su kawo Abbatuwa ta cikin birnin Kano su sayar
a tsaye, wasu kuma su yanka su sayar. A wannan lokaci suna zuwa kasuwar dabbobi
ta Gaidan da Malamdori da dai sauransu. Da wannan sana’a tashi ta kan kama
sosai, ya fara sayen shanu yana yankawa da kansa. Haka abin ya ci gaba har ya
fara sayen shanu yana kai wa Legas yana sayarwa.
Himma ba ta ga rago, wata rana ya kai
shanu 4 Legas sai ya yi shawara kada ya sayar da su a tsaye. A wannan lokaci ne
ya yanka shanu huɗu a Legas da ya je da su. Cikin ikon Allah ya samu riba mai yawa har sai da
ya sayi shanu 7. A nan ne ya yanke shawarar ya yi zamansa a wannan gari na
Legas, domin ya ci gaba da kasuwanci bisa amincewar magabatansa. Haka ya ci
gaba da zama a Legas har zuwa shekarar 2015 ya dawo birnin Kano da zama.[19]
An sanar da ba wa Alhaji Alhaji Isiyaku
Sarautar Sarkin Fawan Kano a ranar 16/3/2018. Sai dai ba a yi naɗi ba sai a
12/12/2018. Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II ne ya naɗa shi a wannan
sarauta ta Sarki Fawan Kano. Allah ya albarkaci Sarkin Fawa da ‘ya’ya maza 6 da
mata 5.
4.6.3 Ayyukan Sarkin Fawa
Sarautar Sarkin Fawa tana da ayyuka na
musamman da aka ɗora masa a kansa waɗanda yake gudanarwa a ƙarƙashin rukunin al’ummar da yake jagoranta masu gudanar da sana’ar Fawa a birnin Kano. Daga cikin ayyukansa akwai:
4.6.3.1 Aikin Sana’ar Fawa
Sarkin fawan Kano mutum ne da ya ƙware a wajen sana’ar fawa. Wannan dalilin ne ya sa aka ba shi wannan sarauta saboda ganin
yadda ya bunƙasa wajen sana’ar Fawa a ciki da wajen Kano. Sai dai shi a yanzu ba ya
yanka dabba ya sayar, sai dai ya sayar da su a tsaye ko kuma ya tura su jahohin
kudancin Nijeriya.
4.6.3.2 Samar da Tsaro A Kwata da Kara
Sarkin Fawan Kano yana ƙoƙari wajen tabbatar da samar da tsaro,
zaman lafiya a Abbatuwa da ke cikin birnin Kano. Wannan ya biyo bayan,
kasancewa abbatuwa mattara ce ta mabambantan mutane daga ɓangarori
daban-daban a cikin birnin Kano. Hakan shi ya haifar da samuwar gurɓatattun mutane a
wannan wuri da ake gudanar da wannan sana’a.[20]
4.6.3.3 Sulhu da Sasanci
Sarkin Fawan Kano shi ne mai gudanar da
sulhu da sasanci tsakanin mahauta a Abbatuwa da ke birnin Kano. Duk wani wanda
aka zalunta ko aka ci bashinsa na nama ba a biya shi ba, yakan kawo ƙara ga Sarkin Fawa. Shi kuma zai tabbatar da an karɓar masa haƙƙinsa. Idan kuma abin ya fi ƙarfinsa, sai ya tura abin zuwa mataki na gaba domin tabbatar da mai
gaskiya.
4.6.4 Hakiman Sarkin Fawa da Ayyukansu
A birnin Kano, kowace sana’a ta
garagajiya tana da tsarin shugabanci a cikinta. Wannan ya sa sarautar Sarkin
Fawan Kano take da tsarin hakimai da suke taimaka masa wajen gudanar da
ayyukansa. Waɗannan hakimai Sarkin fawan Kano yake naɗa su fadarsa, bisa
sahalewar Sarkin Kano. Daga cikin hakiman Sarkin Fawan Kano akwai:
4.6.4.1 Galadiman Fawa
Galadiman Fawa shi ne mai wakiltar
Sarkin Fawa a harkokin da suka shafi sulhu da sasanci. Haka kuma, shi ne yake
da alhakin kula da ƙahunna da kofatai na dabbobin da aka
yanka a Abbatuwa.
4.6.4.2 Ciroman Fawa
Ciroman Fawa shi ma hakimin Sarkin Fawa
ne, shi ne yake da alhakin karɓar rasit da tattara kuɗaɗen shiga na
abbatuwa. A tsarin Abbatuwa ta Kano, akan biya kuɗi idan za a shiga
da dabbobin da za a yanka a wannan wajen. Hakan ya sa Ciroman Fawa yake
wakiltar Sarkin Fawa a wannan ɓangare.
4.6.4.3 Majidaɗin Fawa
Sarautar majidaɗi a fadar Sarkin
Fawan Kano hakimi ne wanda yake kula da shige da ficen dabbobi a cikin Abbatuwa
da kara. Yana taimakawa wajen kawar da ɓata gari a cikin harkar sana’ar fawa a
fadar Sarkin Fawan Kano.
4.6.4.4 Turakin Fawa
Sarautar Turakin Fawar Sarkin fawan
Kano ne shi yake wakiltar Sarkin Fawa a wajen wasu tarurruka da aka gayyaci
Sarkin Fawa. Yakan wakilci Sarkin Fawa a lokacin da ya yi wata tafiya ko kuma
yake da wani uzuri da ya hana shi halartar wannan taro.
4.6.4.5 Shamakin Fawa
Shamaki shi ne ƙasaitacen bawan Sarkin Fawa, shi ne shugaban bayin Sarkin Fawan Kano.[21]
Babban aikin Shamakin Fawa shi ne kula da dawaki da kuma haɗa wa Sarkin Fawa
sirdi.
4.6.4.6 Sarkin Fada
Sarkin Fada shi ma hakimin Sarkin Fawa
ne da yake kula da al’amuran da suka shafi fadar Sarkin Fawan Kano. Duk wani
abu da ya shiga fada da cikin gidan Sarkin Fawa shi ne yake kula da shi. Saboda
shi ne amintaccen Sarkin Fawa, wannan dalilin ne ya sa ba shi da shamaki da
matan Sarkin Fawa.
4.6.4.7 Babban Zagi
Babban zagi shi ma bawan Sarkin Fawa
ne, shi ne yake kula da tsaron Sarki da kuma zuwa gayyato masu laifi a Abbatuwa
da kara ta Kano.
4.6.4.8 Mata a Farfajiyar Fawa
A farfajiyar sana’ar fawa ba a bar
matan mahauta a baya ba. Matan mahauta suna gudanar da wannan sana’a kamar
yadda mazajensu suke gudanarwa. A wannan bagire matar Sarkin fawa ita ce take
shugabantar sauran matan, kuma ta wajenta ne suke samun irin ɗan yaɗin nama wanda suke
sarrafa shi su sayar. Sani, (1995). Baya ga wannan, wasu matan har sukan dinga
yanka nama su kasa na sayarwa inda suke zuwa manyan kasuwanni su sayo dabba su
kawo Abbatuwa a nan Kano a yanka su sayar.[22]
Akan samu wasu da suke zuwa suna sayan fince da yaɗi da fata suna
sayarwa ɗanye, wanda ya rage ba su sayar ba, su tafi da shi gida su yi ragadada su
sayar,[23]
wasu kuma su ba ‘ya’yansu talla zuwa gida-gida su sayar musu.
4.6.5 Ƙananan Sarakunan Fawa a
Birnin Kano
Birnin Kano ƙasaitaccen gari ne mai girma da yawan al’umma. Wannan ne ya sanya birnin Kano yake da wasu ƙananan mayanka da kara, inda ake sayar da dabbobi da kuma
yanka su. A sakamakon haka, Sarkin Fawan Kano ya naɗa ƙananan sarakuna da suke wakiltarsa a wajen gudanar da
ayyuka a waɗannan ƙananan mayanka a cikin birnin Kano.[24]
Daga cikin waɗannan ƙananan sarakunan Fawa akwai:
4.6.5.1 Sarkin Fawan Birget
Sarkin Fawan Birget shi ne mai kula da
ayyukan Sarkin Fawan Kano a wannan mayanka da kara. Sannan shi yake kai wa
Sarkin fawar Kano rahotanin duk wani abu da yake faruwa a wannan wuri.[25]
4.6.5.2 Sarkin Fawan Ungogo
Sarkin Fawan Ƙwanar Ungogo shi ne mai kula da ayyukan Sarkin Fawan Kano a wannan mayanka
da kara. Haka kuma, shi yake wakiltar Sarki a duk wasu ayyuka da suka shafi
sana’ar Fawa a yankin Ungogo da kewaye.
4.6.5.3 Sarkin Fawan Tudun Fulani
Sarkin Fawan Tudun fulani shi ne mai
kula da ayyukan Sarkin Fawan Kano a wannan yanki na unguwar tudun fulani.
Sannan shi ne mai wakiltar Sarkin Fawa a duk wasu al’amura da suka shafi
sana’ar Fawa a wannan yanki.[26]
4.6.5.4 Sarkin Fawan Unguwa Uku
Sarkin Fawan Unguwa uku shi ne mai kula da ayyukan Sarkin
Fawan Kano a wannan unguwa. Haka kuma, shi ne yake kai masa rahoton duk wani
abu da ya shafi wannan sana’a ta Fawa a wannan yanki.[27]
4.6.6 Al’adun Sarautar Fawa A Jiya
Sarautar Fawa kamar sauran sarautu tana
da al’adu nata na musamman da ake gudanarwa. Waɗannan al’adun sun
taimaka wajen keɓance wannan sana’a daga sauran taƙwarorinta. Daga
cikin al’adun akwai:
4.6.6.1 Bayar da Magunguna
Sarkin Fawa ba a iya sana’ar fawa kawai ya tsaya ba, yakan bayar da gudummawa ta musamman a fannin kiwon lafiya a kan cututtuka da suka danganci wannan sana’a tasu ta fawa. Yana bayar da magunguna ga al’umma idan wata lalura ta samu ta rashin lafiya, kamar tsayawar ƙashi a maƙogaro, ko tsinken tsire ya yi wa mutum rauni, ko kashi ya yi wa mutum rauni, ko ƙaho ya soke mutum ya yi masa rauni da laƙanin wuƙa. Haka kuma, su kansu mahautan sukan yi magani domin kare kansu da kuma sana’arsu, kamar maganin kaifi (Wuƙa) da tsini (Ƙaho) da dai sauransu. Wannan ne ya sa a da idan ana buƙatar ‘yan tauri, ana samun su a cikin mahauta. Sani (1995:26).
4.6.6.2 Hawan Ƙaho
Wannan wasa na hawan ƙaho bisa ga tarihi, ya samo asali ne daga mahauta masu
yin sana’ar fawa. Wannan rukunin al’ummma su ne aka sani da yin wannan wasa na
hawan ƙaho a ƙasar Hausa. Mahauta suna gudanar da wannan wasa na hawan ƙaho a duk lokacin da wani bikin farin ciki ya same su ko
ya samu jama’ar gari, kamar lokacin shagalin sallah ƙarama ko kuma babba.
A al’adance, mahauta na yin wannan wasa
ne idan sallah ta rage saura kwana ɗaya ko biyu, wato ranar jajibirin
sallah. Wani lokaci suna yin wasan ne idan an zo yanka shanu, sai aka lura cewa
akwai wani sa mai faɗan gaske. To kafin a yanka shi, sai
wani daga cikin mahauta mai ji da kansa ya ce sai ya yi wasa da shi kafin a
yanka shi. Wannan abin alfahari ne ga dukkan mahaucin da ya yi wasa da sa mai
faɗa, domin wasan kasada ne ƙwarai da gaske.
Salisu (1984:39).
A duk lokacin da za a gudanar da wannan
wasa, akan gayyato makada da suke yi wa mahauta kiɗa su zo mayanka da
sassafe. A nan ne za su fara kiɗa dan sanar da al’umma cewa za a yi
wasan hawan ƙaho. Su kuma masu hawan, da jin kiɗan duk jikin su
zai ɗauki tsuma har ma su ƙagara a zo a fara
wasan.
Masu wannan wasa na hawan ƙaho, sukan yi shiri na magani domin kare kansu daga bacin
rana, da kuma sukar ƙahon sa tun kafin ranar yin wasan.
Magungunan da sukan yi amfani da su don yin wannan wasa sun haɗa da: Maganin ƙaho da kau-da-bara da baduhu da kuma iya bauɗiya da dabara na
mai yin wannan wasa.
A yanzu an ci gaba da gudanar da wannan
al’ada a fadar Sarkin Fawan Kano, sai dai kawai ya sauya salo saɓanin yadda ake yin
sa a dauri. A yanzu ana gudanar da shi a lokutan wasu bukukuwa da fadar Sarkin
Fawan Kano take gudanarwa. Yana sa a gudanar da wannan wasa ne domin a saka
nishaɗi da jindaɗi a zukatan waɗanda suka halarci wannan taron biki a
fadar. A yayin aiwatar da wannan wasa na hawan ƙaho, akan samu masu kiɗa na zamani (DJ) da kujerun zama na baƙi da Rumfuna canopy
da ake sauke baƙi da aka gayyato a wannan waje.
4.6.6.3 Dambe
Wasan dambe yana ɗaya daga cikin
wasannin gargajiya na Hausawa da aka daɗe ana gudanar na shi har ya zuwa yau.
Wannan wasa na dambe ya samo asali ne daga masu sana’ar fawa (mahauta). Mahauta
suna yin wannan wasa a lokacin kaka idan an kau da amfanin gona. Ana yin sa duk
lokacin da wani abin farin ciki ya samu al’umma ko mahauta. A da can ana yin
wasan danbe a dandali don jama’a su yi kallo kyauta. Yanzu da zamani ya zo sai
ake kewye fili ko gida don mutane su riƙa shig kallo suna
biya ana samun kuɗin shiga. Wannan ne yasa dambe wannan zamani ya zama abin neman kuɗi. Haka zalika,
wasan dambe maza ne kaɗai suke yin sa wanda galibin su duk
samari ne ‘ya’yan mahauta. Galibi idan kaka ta yi suna shiryawa su tafi neman
wurin dambe don samun abin masarufi. Kafin ranar da za a fara dambe sukan
shirya don kare kan su. Wasu su tafi wajen malamansu na tsubbu don neman
taimakon yin galaba akan abokin damben su. Idan lokaci ya yi ‘yandambe za su
fara shigowa gidan dambe ƙungiya-ƙungiya. A gefe guda kuma makaɗa ne d suke yi
musu kiɗa d kirari. Idan jama’a sun taru, ‘yan dambe za su fara shiryawa suna saka
guraye da naɗi na hannu da sanya gajeru wanduna da kambuna da dai sauran kayan tsubbun
su. Bayan an gama shiri makaɗa za su fara kiɗa suna sako take,
duk wanda aka saka taken sa sai ya shigo fili yana kirari ko da akwai mai
tarbarsa, har ya je kusa da abokan dambe yana kirari. Idan akwai wanda zai iya
sai ya fito a fafata. Da abokin yi ya shigo fili sai a raba rana. Yadda ake
raba rana shi ne; kow zai taho sai a gama hannuwansu da juna wato su gogi juna,
wannan raba rana da suka yi kamar gaisuwa yake a wajen ‘yan dambe. Suna komawa
gefe sai kowa ya dawo a fara dambe. Idan an yi kisa shikenan idan kuma ba a yi
ba, har aka yi turmi uku saia hakura sai wani lokaci.
4.6.6.4 Tsatsube-Tsatsuben Fawa
Masana fannin sana’ar fawa da masu
gudanar da ita da al’umma baki ɗaya sun bayyana yadda tsatsube-tsatsube
yake, da yadda ake wanzar da shi a cikin sana’ar fawa. Kowace sana’a ta
gargajiya tana da hanyoyin da ake bi ko taimaka mata wajen gudanar da ita.
Sallau (2013:205). Wannan dalili ne ya sanya ba a bar mahauta a baya ba, wajen
bunƙasa al’adunsu da tattalin arziki a ƙasar Hausa. Mahauta suna yin amfani da hikima da dabara da laƙani da tambaya da surƙulle wajen kare martabar wannan sana’a ta fawa. (Yakubu da Gafai 2018:262).
Daga cikin wannan tsatsube-tsatsube a sana’ar fawa akwai:
4.6.6.4.1 Ba-duhu
Ba-duhu wata hanya ce ko hikima ko
dabara da ake yi idan buƙatar ta taso. Ana ɓacewa daga sarari
ta yadda mutane ba su ganin mutum ko dabba, musamman a wajen bukukuwa, kamar
hawan ƙaho. Bunza (2006:41-42) ya rawaito cewa,
ba-duhu wani magani ne da ake yi na tsafi ta fuskar amfani da tayin dabbobi, da
kyanwar da ta buɗe ido ba, da suturar makaho ko makauniya. Mai ba-duhu yakan ɓace ga ganin
mutane gaba ɗaya, ko da ga shi ga su, yana magana suna jin sa. Waɗanda suka ƙware da wannan tsafi akwai, Fatake da Mayaƙa da Mafarauta da manyan masu milki da sarkawa da kuma
Rundawa. Yayin gudanar da wannan laƙani na ba-duhu,
dole sai an yi wasu tsatsube-tsatsube da surkulle na al’ada domin tabbatuwar wannan laƙani na ba-duhu.[28]
Wannan surƙulle ana gudanar da shi kamar haka:
Yakubu da Gafai (2018) sun rawaito
cewa: Mahauci zai sami kwatarniya ko tukunya a zuba ruwa a cikinta, sannan a
sami ciyawar goga-masu da itacen shiriya da ɓawon itacen
tsamiya da kaucin gawo wanda bai wuce shekara ɗaya da fitowa ba, sai
a haɗe su wuri guda a shanya ya bushe, adake shi a turmi. Daga nan sai a sami ƙashin nan da ake kira da gagara-kure a haɗe a zuba cikin
kwatarniya a zuba ruwa. Bayan ya yi sati uku ko wata ɗaya, a lokacin
ruwan ya fara wari, sai a dunga ɗiba ana kuskure baki da shi sau uku,
kuma a yi wanka da shi asubar fari. Sannan ba a barin wurin da aka yi wankan
sai ruwan ya tsane a jikin mutum. Bayan ya gama sai ya ɗaga hunnusa na
hagu ya ce:
“ Duhunduhuma uwar duhu,
Baƙin bajimi bi gamba,
Ina muka yi?
Ko da cikin ƙafan tambasawa,
Sai wata rana.”[29]
Haka za a ci gaba da yi har tsawon wata
uku.
4.6.6.4.2 Ɓata Kasuwa
Mahauta suna yin amfani da hikimomi na
sihiri ko surkulle domin su ɓata kasuwar wani wanda ake jin
haushinsa a fagen sana’ar fawa. Ana ɓata naman mutum ya ƙi sayuwa ko gasuwa ko ya yi baƙi, mutane su ƙi saye. (Yakubu da Gafai 2018:263). Shi
ma wannan sihiri sai dole an yi amfani da tsatsube-tsatsube wajen haɗa wannan laƙani. Ana amfani da hikimomi na sihiri da surƙulle domin a ɓata kasuwar wani wanda ake ji wa haushi
a fagen sana’ar fawa. Ana ɓata naman mutum ya ƙi soyuwa ko gasuwa ko ya yi baƙi mutune su ƙi saye.
Yadda ake gudanar da wannan surƙullen shi ne, ana samun kaucin tsamiya da goga-masu da
kaucin kalgo da ganyen tumfafiya, a shanya su bushe. Sai a haɗe wannan maganin a
ƙulla shi wuri bakwai, sannan a sami
fitsarin kare wanda bai wuce shekara ɗaya ba, sai a saka maganin a ciki ya yi
kwana bakwai. Daga nan sai a fitar da shi da daddare a nufi maƙabarta, a sami kabarurruka da ba su wuce kwana bakwai da
ba a daɗe da rufe mamaci ba, sai a sanya ƙulli daya a cikin
kowane kabari ana faɗin sunan mutum har sau bakwai. Daga nan
sai a dawo gida, bayan kwana bakwai sai a koma maƙabarta a ɗauko magungunan da aka binne a dawo gida a dinga shan maganin ɗaya bayan ɗaya har kwana
bakwai ana ambaton sunan wanda za a ɓata wa kasuwar. (Yakubu da Gafai 2018).
4.6.7 Sauye-Sauye a Sarautar Fawa da Al’adunta
An samu sauye-sauyen zamani da dama a
cikin sarautar Fawa a cikin birnin Kano. Daga cikin sauye-sauyen da aka samu
sun haɗa da:
4.6.7.1 Samar da Ofishin Sarkin Fawa
Sarkin Fawan Kano yana da ofishinsa a
cikin Abbatuwa ta Kano. A nan ne yake zama da shi da muƙarrabansa domin gudanar da ayyukansa. Sannan, a nan ne yake karɓar shari’a da
sulhu da sasanci a tsakanin mahauta masu gudanar da sana’ar Fawa.
4.6.7.2 Mataimaka na Musamman
Sarkin fawan Kano ya samar da
mataimakansa, waɗanda suke taimaka masa wajen gudanar da wasu ayyuka a ofishinsa. Yana da
magatakarda (Secretary) da mai taimaka masa na musamman (Personal Asistant). Waɗannan su ne suke
taimaka masa wajen gudanar a ayyukansa a ofis.
4.6.7.3 Samar da Masu Raba Rasiɗi
Sarkin Fawan Kano ya samar da wasu
jami’ai da suke tsayawa a bakin mashigar Abbatuwa domin raba rasit ga masu
shigowa da dabbobin da za a yanka a Abbatuwa. Wannan ya taimaka wajen kula da ɓata-gari masu
shigowa da dabbobin sata da makamantasu.
4.6.7.4 Samar da Ofishin Likitocin Dabbobi
Sarkin fawan Kano ya yi ƙoƙarin samar da ofishin likitocin dabbobi
tare da haɗin guiwa da hukumomin gwamnati. Waɗannan likitoci su ne suke kula da
lafiya da inganci dabbobin da ake yankawa a cikin Abbatuwa. An yi haka ne
sakamakon yawaitar samun dabbobi masu ɗauke da wasu cututtuka da ka iya cutar
da al’umma.[30] Sannan, su ne suke kula
da lafiyar ragowar dabbobin da suke a tsaye da ba a yanka a wannan lokacin ba.
Sakamakon ana samu dabbabi masu ɗauke da wasu cututtuka kamar ciwon
hanta da makamantansu. Hakan ya taimaka wajen tsaftace sana’ar, tare da samar
da ingataccen nama mai ƙyau da ake sayar wa da al’umma a cikin birnin Kano. Ga hoton ofishin likitocin
dabbabin a ƙasa.
4.6.7.5 Samar da Gidan Sanyi Domin Ajiyar Nama
Sarkin Fawan Kano ya yi ƙoƙarin samar da gidan sanyi a Abbatuwa da
ke cikin birnin Kano. Dalilin samar da wannan wuri shi ne; akan samu wasu da
yawa daga cikin mahautan da namansu ba ya ƙarewa a rana sai ya kwana. Hakan ya sa aka samar da wannan wuri domin ajiye
ɗanyen nama a cikin manyan firjuna don gudun kada ya lalace. Akwai inji na
musamman da aka samar domin samar da wadatacciyar wuta a wannan gidan sanyi. Ga
hoton gidan sanyin nan a ƙasa.
4.6.7.6 Hanyoyin Samun Kuɗin Shiga
Sarkin Fawan Kano ya samar da hanyoyin
da ake samun kuɗin shiga da ake amfani da su wajen gudanar da ayyukan wannan Abbatuwa. Ana
samun wannan kuɗaɗe ne ta hanyar sayar da jini da izga da ƙaho da ƙashi da kuma taki, waɗanda ake samu
bayan an yi yanka a wannan wuri.[31]
4.6.7.7 Ɗaukar Ma’aikata
Sarkin Fawan Kano yana da ma’aikata waɗanda suke kula da
tsaftar wannan Abbatuwa. Wasu daga cikinsu suna wanke mayanka, wasu suna
tattara taki, wasu suna yin gadi, da dai ayyuka makamantansu.
4.6.7.8 Samar da Makaranta
Sarkin Fawan Kano ya samar da makaranta
a wannan wuri domin samar da ilimi ga masu gudanar da wannan sana’a ta Fawa.
Sukan yi sana’arsu da safe, da yamma su koma su yi wanka su dawo makaranta
domin ɗaukar karatu. Wannan dalilin ne ya sa ake yi wa mahauta kirari da “Ƙazaman safe Larabawan yamma”.[32]
4.6.7.9 Kai Gaisuwar Juma’a
Sarautar fawa na gudanar da wata al’ada
kamar yadda sauran hakiman Sarkin Kano suke gudanarwa, wato al’adar gaisuwar
juma’a. Sarkin fawan Kano kan shirya da shi da hakimansa a duk ranar juma’a su
je fadar Sarkin Kano domin kai masa gaiwar juma’a. Wannan ya zama al’ada ga duk
wani mai riƙe da wata sarauta ta gargajiya da take
a ƙarƙashin kulawar masarautar Kano. A yayin wannan gaisuwa, sukan tafi ne tare
da hakimansu. Idan an je fadar Sarkin Kano, dukkansu hakimai za su jera gabanin
Sarki ya fito daga cikin gidansa. Idan Sarki ya fito daga cikin gidan duka
hakiman za su jinjina wa Sarki tare da ɗaga kwagirin da ke hannuwansu. Bayan
Sarki ya shiga fada ya zauna, kowane hakimi zai cire Alƙyabbarsa ya ba wa yaransa tare da kwagirinsa su riƙe masa; sannan ya shiga fada ya yi gaisuwa. Idan mai hakimin mai wajen ne a
gaban Sarki, bayan ya yi gaisuwa ya samu wurinsa da yake zama ya zauna. Idan
kuma ba shi da wajen zama, sai ya fito ya samu yaransa su tafi zuwa gida, sai kuma
wani sati.
4.6.7.10 Hawan Sallah
Bisa al’ada Sarkin fawa Kano ba ya yin
hawan sallah. sai dai kawai ya tsaya ya kula da al’ummarsa da kuma sana’arsu ta
fawa. A yanzu kuwa, Sarkin fawan Kano yana halartar hawan sallah ƙarama da babba. Haka kuma, yana halartar hawan daba da
masarautar Kano kan gudanar a sakamakon faruwar wani abu na musamman, kamar naɗin sarauta ko kuma
ziyarar wani babban baƙo zuwa wannan masarauta. Sarkin fawan
Kano yana da waje na musamman a cikin tawagar Sarkin Kano a yayin hawa, wadda
aka fi sani da rumfar masu.[33]
4.6.7.11 Shirya Gasa
Gasa a wannan bincike na nufin shirya
wani wasa tare da saka wani abu a matsayin lada ga duk wanda ya yi nasara ko ya
lashe wannan gasa. A yanzu sarkin fawan Kano yana shirya gasa a tsakanin
mahauta, domin ƙara musu ƙaimi da saka musu nishaɗi da ƙara fahimtar juna tsakaninsu. Daga cikin wannan gasa da sarkin fawa yake
shiryawa ta haɗa da:
4.6.7.11.1 Gasar Kwallon Kafa
Sarkin fawan Kano yana shirya wannan
gasa ga matasan mahauta, inda ya ke saka musu kofi da wasu kyaututtuka a
tsakaninsu. Ana gudanar da wannan gasa a tsakanin wasu ɓangarori na masu
gudanar da sana’ar fawa. Daga cikin ɓangarorin akwai: Kara da ‘yan fiɗa da ‘yan babbaka
da ‘yan fata da ‘yan ƙirgi da kuma ‘yan dakon nama. Ana gudanar da wannan gasa a lokacin
rani, a filin kwallo na dalar gyaɗa (Filin Polo) da ke unguwar Ƙofar Mazugal a cikin birnin Kano.[34]
4.6.7.11.2 Gasar Dambe
Wasan dambe, ya samo asali ne daga masu
gudanar da sa na’ar fawa (mahauta). Suna gudanar da wannan wasa da kaka, idan
sun kau da amfanin gona. A al’adance, mahauta na ganin duk matashin da ya gaji
fawa, kuma ba ya yin dambe a matsayin rago. A yanzu sarkin fawar Kano yana
shirya wa matasan fawa gasa ta dambe, inda yake saka musu kofi da wasu ƙyaututtuka da za su ƙayatar da gasar. Yana yin haka ne domin ya ƙara musu ƙaimi wajen riƙo da al’adunsu na mahauta.
4.7 Sarautar Sarkin Gini
Sarautar Sarkin gini sarauta ce da ake
naɗa ta ga ma’abota sana’ar gini a garin Kano.[35]
Wanda yake riƙe da wannan sarauta shi ake kira da “Sarkin Gini”. Sarkin gini shi ne shugaban masu gudanar da sana’ar gini a garin Kano. Shi ne yake shimfiɗa dokokin wannan
sana’a ta hanyar mulki tare da hukunci da kare lafiyarsu. Ita ma wannan sarauta
Sarkin Kano ne yake naɗa ta ga rukunin wannan al’umma. Haka
shi ma Sarkin gini yana da hakimai da suke tallafa masa wajen gudanar da wannan
jagoranci na magina a garin Kano.
4.7.1 Asalin Sarautar Gini a Birnin Kano
Babu wani lokaci takamaimai da za a iya
cewa ga lokacin da aka fara sarautar gini a birnin Kano. A dauri ba a san
tsarin-ginin muhalli a birnin Kano ba. A sakamakon rashin muhalli ya sa mutanen
wannaan birni suke rayuwa a kan duwatsu da gindin bishiyoyi da kogunan duwatsu.[36]
Suna zama a waɗannan wurare ne saboda gudun iska da ruwan sama da kuma miyagun dabbobi.
Na’iya (1983:2).
Da tafiya ta yi tafiya, mutane suna ƙara samun wayewa da kuma basira da Allah ya hore musu,
sai suka fara ƙoƙarin samar da
rumfuna na itace da na kara, daga nan suka fara zagaye rumfunan da karare. Wannan
ya haifar da samun bukka a cikin wannan al’umma. Haka aka ci gaba da yi har
wasu suka fara yayyaɓe bukkokinsu da rumfunansu da ganyayen
bishiyoyi. Suna yin haka ne domin gudun miyagun ƙwari da namun daji.
Sannu a hankali, aka ƙara samun cigaba, sai aka fara kafa bukkoki da ɗakin ciyawa da na
kara, wanda akan yaɓe shi da ɗanyar ƙasa. Daga wannan dabara ta yayyaɓe ɗakunansu da ɗanyar ƙasa, mutane suka fara tayar da ginin muhalli a sigar
kantanga. Haka dai aka ci gaba kullun basira na daɗa ƙaruwa, har aka gane amfanin ginin muhalli da tsaron kai
da kuma fa’idar sirranta iyali. Wannan dalili shi
ya haifar da gine-gine iri-iri a birnin Kano da wasu sassa na ƙasar Hausa. Na’iya (1983).
Haka abin ya ci gaba har aka samu ɗaiɗaikun mutane da
suka ƙware wajen aikin gini a birnin Kano. waɗannan mutane suna
ji suna gani suka haƙura da farauta a lokacin rani suke tsayawa
suna yin sana’ar gini. Sannu a hankali har ta kai wannan magina sun samu zuri’a
mai tarin yawa da suke gudanar da wannan sana’a. Haka abin ya ci gaba, har aka
zo gina ganuwar Kano. A nan ne magina suka nuna basirarsu da ƙwarewarsu a kan wannan sana’a. Sannan daga wannan aiki na ginin ganuwar Kano, aka
samu sarautar gini a masarautar Kano ta taso. Wannan ne ya sa rukunin maginan
suka zaɓi dattijo jarumi kuma ƙwarare a matsayin
shugaba, kuma wanda zai riƙa sulhu da sasanci
a tsakanin masu wannan sana’a ta gini. Wannan shi ne asalin samuwar sarautar gini a birnin Kano.[37]
4.7.2 Taƙaitaccen Tarihin Sarkin
Ginin Kano Abdulƙadir Muhammad
An haifi Sarkin ginin Sarkin Kano Abdulƙadir Muhammad a unguwar Yakasai da ke cikin birnin Kano a
shekarar 1940.[38] Kimanin shekara 83 a
yanzu. A lokacin da ya tashi yana yaro, babu abin da ya fi mai da hankali a
kansa da ya wuce karatun addini. Sarkin ginin Kano ya yi karatu a hannun
malamansa da suka haɗa da; Liman Malam Bashiri da Malam Ali.[39]
Haka kuma, ya yi karatu na ilimi a hannun malam Bukhari da ke unguwar Yakasai.
Daga baya ya koma wajen malam Abdulrazaƙi da ke nan cikin Loko
a unguwar Yakasai. Daga baya ya dawo gida domin koyon wannan sana’a ta gini. A
wannan lokacin Sarkin ginin Kano yana bin yayyansa zuwa wannan aiki. Har sannu
a hankali ya iya wannan sana’a ta gini. Duk mafi yawan wannan gine-gine da suke
gudanarwa na ƙasa ne, domin a lokacin ginin siminti
sai wane da wane.
Malam Abdulƙadir Sarkin gini ya yi aikin gandiroba a gidan yarin gidan Sarkin Kano a
matsayin magini. Daga baya ya juye zuwa cikakkun ma’aikaci, ya riƙe muƙamai da dama har ya kai matsayin A.S.P., wanda a nan ne ya ajiye aiki. Bayan ya ajiye aiki ya dawo,
ya tarar da mahaifinsa yana yin wannan aikin gini na gidan Sarkin Kano. Da
maihaifinsu ya rasu aka mai da sarautar ga babban yayansu Alhaji Ibrahim,
sannan yayansa Gwande ya yi wannan sarauta. Daga nan ne aka naɗa shi wannan
sarauta ta Sarkin ginin Kano, a shekarar 2014 a zamanin Sarkin Kano Muhammadu
Sunusi na II.[40]
Sarkin ginin Kano
ya yi aure a shekara 1967. Yana da mata biyu yanzu. Allah ya albarkace shi da
‘ya’ya maza 6 da mata 9.
4.7.3 Ayyukan Sarkin Gini
Sarautar Sarkin gini kamar dangoginta,
tana da wasu ayyuka na musamman da aka ware mata domin ta riƙa gudanarwa a tsakanin masu wannan sana’a da kuma masarautar Kano. Daga cikin waɗannan ayyuka na
Sarkin gini akwai:
4.7.3.1 Aikin Gini
Aikin gini shi ne babban aikin da mai
wannan sarauta yake gudanarwa a garin Kano. A al’adance Sarkin ginin Kano shi
ne ke jagorantar ginin Badala ko Ganuwar Kano da kuma kula da ita a ƙarƙashin kulawar
masarautar Kano. Ke nan, aikin gini shi ne maƙasudin samuwar wannan sarauta ta gini a garin Kano.
4.7.3.2 Gine-Ginen Gidan Sarki
Sarkin ginin Kano shi yake da alhakin
yin gine-gine a gidan Sarkin Kano, tun daga kan abin da ya shafi fadoji da
zauruka da katangu. Sannan duk wani gyara da za a yi wanda ya shafi gini a
cikin gidan Sarki, shi ne yake kula da wannan ɓangaren a tsarin
masarautar Kano.
4.7.3.3 Kula da Gine-Ginen Sarki
Sarkin ginin Kano shi ne yake kula da
sauran gine-gine na masarautar Kano. A tsarin masarautar Kano, bayan fada akwai
wasu gine-gine na masarauta masu tarihi da muhimmanci a wannan masarauta. Daga
ciki akwai gidan Sarki na Nasarawa da Fanisau da kuma na Ɗorayi. Duk shekara Sarkin ginin Kano kan zagaya ya duba halin da waɗannan gidaje suke
ciki. Yana yin haka ne, domin a gyara su gabanin Sarkin Kano ya kawo ziyarar
sallah a waɗannan gidaje kamar yadda al’adar wannan masarauta ta tanada.
4.7.3.4 Sulhu da Sasanci
Sarkin ginin Sarkin Kano shi ne yake
yin sulhu da sansanci a tsakanin masu gudanar da sana’ar gini. Akan samu wasu
magina su sami saɓani da waɗanda suke yi wa aiki. Sarkin gini shi ne yake shiga tsakani ya samar da
masalaha ko mafita a tsakaninsu, sai dai idan abin ya fi ƙarfinsa sai ya tura shi zuwa gaban Sarki.
4.7.3.5 Bayar da Shawarwari a Lamuran Gine-Ginen Fada
Duk da cewa an samu sauye-sauyen zamini
ta fuskar gine-gine a masarautar Kano, har zuwa yanzu Sarkin gini Kano yana da
muhimmiyar rawar da yake takawa a wajen aiwatar da gine-ginen masarautar Kano.
Duk wani gini da za a yi a masarautar Kano, shi ne yake ba da shawarar yadda za
a yi wannan gini, domin ya yi daidai da na al’ada.[41]
Idan za a yi sabon gini akan kira ɗan ƙwangila ya zo su zauna da Sarkin gini a zana taswirar yadda ya dace a yi
wannan gini daidai da al’adar wannan masarauta.
4.7.4 Hakiman Sarkin Gini da Ayyukansu
Masu iya magana kan ce: “Hannu da yawa
maganin ƙazamar miya”. Sarkin gini shi yake naɗa hakimansa da
sauran sarautu da suka shafi gini Liman (1985). Sarkin ginin Sarkin Kano yana
da hakimai da suke taimaka masa wajen gudanar da ayyukansa na gini, musamman a
masarautar Kano. Daga cikin hakiman Sarkin akwai:
4.7.4.1 Galadiman Gini
Galadiman gini shi ne yake wakiltar Sarki wajen gudanar da ayyukan da suka
shafi wannan sarauta. Haka kuma, ta fannin gini kuma, ya ƙware a wajen shirya guga[42] musamman a fadoji da zaurukan gidan Sarkin Kano.
4.7.4.2 Madakin Gini
Madakin gini shi ne shugaban dukkanin
hakiman Sarkin gini. Yana taimaka wa Sarkin gini a wajen gudanar da aiki a
gidan Sarkin Kano, musamman abin da ya shafi ado da ƙawata gini kamar zane-zanen dagi[43]
da sauransu.
4.7.4.3 Turakin Gini
Turakin gini shi ma hakimi ne wanda
yake kula da kayan aikin gini da ake ajiye su a ɗakin ajiye kaya
(Store). Haka kuma, duk wani gyare-gyare na gini da za a yi cikin gidan Sarkin
Kano shi ne yake gudanar da wannan aiki.
4.7.4.4 Shamakin Gini
Shamaki shi ne mai kula da dawakin
Sarkin gini da kuma haɗa wa Sarkin gini sirdi. Haka kuma, duk
wani aiki na gini da ya taso a gidan Sarkin Kano, da shi ake gudanar da wannan
aiki.[44]
4.7.5 Al’adun Magina a Jiya
Sarautar gini na da wasu al’adu na
musamman da take gudanarwa a ƙarƙshin sana’ar. Wasu al’adun suna gudanarwa a kan kansu, wasu
kuma ga masarautar Kano. Daga cikin irin waɗannan al’adu
akwai:
4.7.5.1 Kai Gaisuwa
Wannan tsohuwar al’ada ce ta sarautar
gini. Sarkin gini kan je fada gaisuwa ga Sarki tare da hakimansa da dogarawa.
Wannan gaisuwa akan yi ta ne ranar juma’a a duk ƙarshen mako. Haka kuma, akwai gaisuwar sallah ƙarama da babba. Duk ana yin su ne domin a yi wa Sarki barka da sallah.
4.7.5.2 Fasa Sabuwar Ƙofa
Fasa ƙofa al’ada ce da aka daɗe ana gudanarwa a
masarautar Kano. Sarkin ginin Kano da muƙarrabansa su ne
suke yin wannan aiki na fasa ƙofa. Ana fasa ƙofa ne idan an yi sabon Sarkin Kano. Ta wannan ƙofa ne sabon Sarki yake shiga gidan Rumfa. Sarkin gini
yana fasa ƙofar a jikin katangar gidan Rumfa ta
biyu. Gidan yana da tsarin katanga guda biyu. Bayan ta farko, akwai wata a
ciki, to ta cikin ita ake fasa wa sabon Sarkin Kano ya shigo cikin gidan. Bayan
Sarki ya shiga cikin gida, sai Sarkin gini da muƙarrabansa su liƙe ƙofar.[45] Binciken ya tabbatar da
cewa ana fasa wa sabon Sarki ƙofa ne don gudun
taka sawun tsahon Sarki. Wannan na nuni da cewa an samu sabon Sarki wannan
masarauta ta Kano.[46]
4.7.5.3 Tukuici
Tukuici wata al’ada da ake ba wa Sarkin
gini da shi da muƙarrabansa, bayan ya gama aikin fasa ƙofa da liƙe ta. Sabon Sarkin
Kano kan aiko wa Sarkin gini da manyan riguna na alfarma da rago da kayan abinci,
wani lokacin ma har da kuɗin kayan miya. Wannan ya zama tilas duk
lokacin da aka yi wannan aiki, akan ba da wannan kayayyaki a matsayin tukuicin
aiki.
4.7.5.4 Tsatsube-Tsatsuben Magina
Magina suna da wasu tsatsube-tsatsube
da suke gudanarwa daidai da wannan sana’a tasu. Suna yin waɗannan
tsatsube-tsatsuben domin kare mutuncin wannan sana’a da kuma lafiyarsu. Daga
cikin wannan tsatsube-tsatsube na magina akwai:
4.7.5.4.1 Jifa
Jifa na nufin na wurga wani abu, Ƙamusun Hausa (2006:216). A al’adance, magina kan jefi
abokan gudanar da wannan sana’a tasu. Musamman waɗanda suka ga sun
yi fice ko sun samu wata ɗaukaka a cikin wannan sana’a. Wasu
sukan jefi wani ko dai ya susuce ko ya haukace ko kuma ya yi ta rashin lafiya.
Duk mahaɗan irin waɗannan tsatsebe-tsatsube sai an yi amfani da iskoki ko surƙulle da dai makamansu a yayin gudanar da su.[47]
4.7.5.4.2 Lalata Aiki
Magina suna lalata wa abokan sana’arsu
aiki, musamman idan suka ga tauraruwar wani a cikinsu tana haskawa. Duk lokacin
da ya yi aiki wanda ya ɗauki hankalin al’umma kuma ya birge mutane,
wani yana kallon aikin ya yi ƙwafa[48]
aikin zai lalace.[49]
Ko dai ya tsattsage ko kuma ya karkace. Shi ma irin wannan laƙani a yayin haɗa shi, dole sai an yi wasu
tsatsube-tsatsube.[50]
4.7.6 Sauye-Sauye A Sarautar Gini da Al’adunta
Duk da cewa zamani ya yi mutuƙar haifar da sauye-sauye a wajen gudanar da wannan
sarauta ta sana’ar gini. Wannan ne ya sa yanzu duk wani
abu da za a gudanar, wanda ya shafi wannan sarauta ta sana’ar gini ana yin sa ne
a zamanance. Daga cikin sauye-sauyen zamani da aka samu a wannan sarauta ta
gini akwai:
4.7.6.1 Samuwar Ofishin Sarkin Gini
Saboda muhimmanci da wannan sarauta
take da shi a wannan masarauta ta Kano. Sarkin Kano ya samar da ofis na Sarkin
gini a cikin gidan Sarki, wanda a nan ne yake zama shi da muƙarrabansa da suke gudanar da ayyukansu na gini a
masarautar Kano, saɓanin takwarorinsa da su suke samar da
na su ofis da kansu. A wannan ofis ne ake rubuta duk wani aiki da za a gudanar
da kuma wanda ake so a gudanar tare da tattare bayanan duk ayyukan da aka
gudanar da suka shafi gini a wannan masarauta.
4.7.6.2 Samuwar Ɗakin Ajiya
An samar wa Sarkin ginin Kano da ɗakin da yake ajiye
kayan aikinsu na gini, wato (store) a turance. A dauri sai dai su ajiye su a
filin Allah. Amma yanzu kasancewar an samu wasu kayan aikin gini da ba a buƙatar su samu matsala ko su jiƙe da dai sauransu. Wannan dalilin ne ya sa aka samar da wannan ɗaki domin a ba su
kulawa ta musamman.
4.7.6.3 Rakiyar Sarki Soron Shekara
Soron shekara ɗaya ne daga cikin
tsofaffin sorayen gidan Sarki da ake zaman fadanci a dauri. Wannan soro Sarkin
Kano Ibrahim Dabo ya samar da shi a shekarar 1819. Rakiyar Sarki soron shekara
wata al’ada ce da wannan sarauta take gudanarwa. Inda Sarkin ginin Kano yake raka
sabon Sarkin Kano zuwa wannan soro bayan fasa ƙofa. A nan ne Sarkin Kano zai zauna ya yi sallah raka’a biyu ya yi godiya ga Allah bisa wannan ni’ima da ya yi masa. Wani lokaci ma har kwana yake a wannan
soro gabanin ya fita ya shiga zuwa garkar Sarki.
4.7.6.4 Naɗin Hakiman Sarkin Gini
Sarkin gini yana naɗa hakimansa waɗanda suke taimaka
masa wajen gudanar da wasu ayyuka da suka shafi wannan sarauta ta gini. Ana
wannan naɗi ne a ƙofar gidan Sarkin gini. A wajen wannan
naɗi, akan zagaye wajen da kujerun roba da rumfuna canopy. Haka kuma, kafin wannan naɗi, akan buƙaci wanda za a naɗa da ya kawo taƙaitaccen tarihin rayuwarsa da nasabarsa da rawani da kuma kwagiri. Madakin
gini da Galadiman gini su ne suke naɗi a wannan wajen. Bayan an gama naɗi, wanda aka yi wa
wannan sarauta ta gini, zai tashi ya je ya kai gaisuwa ga Sarkin gini. Sarkin
gini zai yi masa bayani a kan irin nauyin da aka ɗor masa a wannan
sarauta. Daga nan sai ya wuce zuwa gidansa tare da makaɗa da za su raka
shi a kan doki.
4.7.6.5 Kai Gaisuwa
Gaisuwa na nufin gai da shugaba ko
aboki, ko aikawa da saƙo na musamman ga shiugaba. Ƙamusan Hausa (2006:150). Kamar yadda aka bayyana a sama,
Sarkin gini yana zuwa kai gaisuwar juma’a da ƙaramar salla da babbar sallah ga Sarkin
Kano. Wannan al’ada an ci gaba da gudanar da ita har
zuwa yau. Sai dai kawai an ɗan samu sauye-sauye na yadda ake zuwa
gaisuwar saɓanin dauri. A yanzu Sarkin gini yana zuwa gaisuwa daga shi sai shamakinsa
da wani daga cikin hakimansa. Saɓanin dauri da ake zuwa da muƙarrabai baki ɗaya.
4.7.6.6 Fasa Ƙofa
Fasa ƙofa na nufin fasa katangar gidan Sarki ta cikin gida wadda daga ita sai
cikin gidan Sarki, ta wannan wajen da aka fasa a jikin katangar, nan ne ake
shiga da sabon Sarki da aka naɗa. Haka kuma, wannan ƙofa a masarautar Kano ana fasa daga jikin katangar gabas
ta gidan Sarki.[51] Al’adar fasa ƙofa har yanzu an ci gaba da gudanar da ita kamar yadda
ake yi a dauri, sai dai a yanzu sarkin gini da shi ake raka sabon sarki har
cikin gida, saɓanin dauri. Haka kuma, Sarkin gini shi ne yake jagorantar wannan aiki na
fasa ƙofa bayan an naɗa sabon Sarkin
Kano.
4.7.7 Samuwar Kayan Aikin Gini da Ado na Zamani
A al’adance duk kayan aikin gini na
gargajiya ne ake amfani da shi a tsarin wannan sana’a ta gini. Ana amfani da
magirbi da kwando da tulu da azara da igiya da ƙashin dabbobi da sakaina da ƙasa da burji da
yumɓu da ɓaɓarkiya da itace da kuma garin ɗorawa. Na’iya (1983:6). Amma yanzu
zamani ya zo, duk an sauya waɗannan kayan aiki. Ana yin aikin gini da
kayan aiki na zamani da suka haɗa da:
4.7.7.1 Shebur
Shebur wani ƙarfe ne mai faɗi da yake haɗe da ɗan dogon itace da ake amfani da shi wajen ɗibar yashi ko ƙasa ko kuma siminti. A dauri ba a yin amfani da shi a wajen gini, sai a yi amfani da sassan duwatsu masu faɗi don ɗibar kasa a yi gini.
4.7.7.2 Wuƙa
Wuƙa a wannan bincike na nufin wani ɗan ƙarfe ne mai faɗi kaɗan da yake haɗe da mariƙi na katako, ƙasan ƙarfen yana da silɓi. Ana amafani da wannan wuƙa wajen yin shafen siminti da kuma jera bulo a lokacin da
ake gini. A dauri ba a yin amfani da wuƙa sai dai a yi
amfani da hannu wajen yin yaɓe a lokacin gini.
4.7.7.3 Katako
Katako itace ne na timba da ake gogewa
a yi amfani da shi wajen aikin gini, musamman a yayin da ake jera bulo, sannan ana
amfani da shi wajen yin rufi bayan an kammala gini. A dauri magina ba sa yin
amfani da katako a wajen aikin gini. Galibi suna yin amfani da azaru da kwangi
wajen rufe gininsu.
4.7.7.4 Siminti
Siminti a wannan bincike wani sinadari
ne na gari da ake zuba shi a cikin yashi domin ya ƙara wa yashi danƙo a yayin gudanar da gini. A dauri
magani ba su yin amfani da siminti sai su yi amfani da laka da ɓaɓarkiya da ciyawa
da kashin dabbobi domin su ƙara wa ƙasa danƙo da ƙwari a lokacin gini.
4.7.7.5 Yashi
Yashi ƙasa ce da ake samo ta a ƙorama ko gulbi ko
kuma wata magudanar ruwa, da ake amfani da shi wajen gudanar da gini a
zamanance. Yashi yakan iya kasancewa mai laushi ne ko kuma mai tsakuwa. Ana
mafani da mai laushi wajen shafe yayin da ake amfani da mai tsakuwa wajen yin
gini ko kuma yin bulo.
4.7.7.6 Duwatsu
Magina a wannan zamani suna yin amfani
da duwatsu wajen shimfiɗa gini da kuma yin ginshiƙai. Ana amfani da duwatsu da rodi a yi wannan ginshiƙai domin su ƙara wa gini kwari
da ƙarko. Saɓanin a dauri ana
yin amfani ne da ƙasa da tubali da itace wajen yin ginshiƙi a gini.
4.7.7.7 Bulo
Bulo shi ne ake amfani da shi a madadin
tubali a zamanance. Ana cura shi ne da moli na hannu ko na inji, inda ake samun
ya shi mai tsakuwa a haɗa da siminti a cura shi. Shi ne ake
jerawa a tayar da katanga. Dauri magana ba su san shi ba, sai dai su yi amfani
da tubali a wajen gininsu.
4.7.7.8 Samuwar Kayan Rufin Gida
A al’adance Hausawa suna rufe gine-ginensu
da laka da itace da karare da jinka da boto da bunu. Da sauyin zamani ya zo duk
wannan tsohon salo ya sauya. A yanzu ana amfani da kwano ko dakin ko alminiyon
da ake amfani da shi wajen aikin rufin gini salon Abuja (Abuja Style).[52]
4.7.7.9 Goyon
Ginin Zamani
A wancan lokacin mafi yawancin
gine-ginen da suke a masarautar Kano na ƙasa ne, sai dai
yanzu zamani ya zo, duk an sauya su ta hanyar goya musu ginin zamani a jikinsu.
Idan an zo yin aikin akan saka ginin na gargajiya ko na ƙasa a tsakiya, a zamantar da shi. Amma a tsari na
gargajiya ba na zamani ba. An yi haka ne sakamakon rushewa da suke yi da kuma ƙoƙarin adana al’adar ginin masarauta domin kada ya salwance.
4.8 Sarautar Sarkin Ƙira
Sarautar Sarkin ƙira ta samu ne daga sana’ar ƙira. Sarkin ƙira shi ne mai shugabantar masu wannan sana’ar. Shi ne yake da alhakin tsara hanyoyin kiyaye lafiya
da dukiyar masu wannan sana’ar, tare da shimfiɗa dokoki da zartar da hukunci a garesu.
Galibi akan samu wannan sarauta ne ta hanyar gado da nuna jarumta da ƙwarewa a wannan sana’a. Sarkin Kano ne yake naɗa wannan sarauta
ta Sarkin ƙira. Haka kuma, shi ma Sarkin ƙira yana da muƙarrabansa waɗanda suke tallafa
masa wajen gudanar da ayyukan wannan sarauta
4.8.1 Asalin Sarautar Ƙira A Birnin Kano
Sarautar Sarkin ƙira a birnin Kano ta kai a ƙalla kimanin
shekara ɗari biyu zuwa ɗari uku.[53]
Dalili kuwa shi ne tun lokaci da aka kafa birnin Kano ake da wannan sana’a ta ƙira. Maƙera suna daga
cikin zuri’ar farko da suka fara zama a birnin Kano.[54]
Maƙera zuri’a ce mai yawan al’umma, wannan ne ya sa tun a wannan lokaci suke da shugabanci a fadar Sarkin
Kano.
Ana ganin cewa maƙera su ne suka kafa birnin Kano, idan aka waiwayi tarihin Kana Maƙeri. Wato maƙerin nan da yake
zaune a baƙin dutsen Dala. Wannan dalilin ne ya sa
ake ganin sana’ar ƙira ita ce sana’ar farko ta
gargajiya da aka fara gudanarwa a birnin Kano. Tun daga wannan lokaci zuri’ar
ta cigaba da bunƙasa zuwa unguwanni daban-daban a cikin
birnin Kano. Irin waɗannan unguwanni kuwa duk sun samo
sunansu ne daga wannan sana’a. Misali: Akwai unguwar Rimin ƙira da ta samo asali daga wasu fatake da suke zuwa daga
jamhuriyar Nijer a jakuna suna yin sana’ar ƙere-ƙere a gindin wani itacen Rimi. To shi ne daga baya ake kiran unguwar da
suna “Rimin ƙira” Gwangwazo (2001:76). Haka abin yake a unguwar Tudun maƙera, ita ma unguwa ce da maƙera suka yi kaka-gida a cikinta. Wannan dalilin ne ya sa ake kiran unguwar
da suna “Tudun maƙera” Bahago (1998:44). Idan aka dubi lokon maƙera da ke unguwar Galadanci a cikin birnin Kano, asali sunan
wannan unguwa Manani, sai kuma wasu maƙera fatake suka riƙa zuwa suna sauka a wannan loko, har jama’a suka yi musu rumfa wadda suke yin ƙira a ciki, Bahago (1998:129). A wannan unguwa ta lokon maƙera, a nan Sarkin Maƙeran Kano yake kuma a nan aka haife shi.
4.8.2 Taƙaitaccen Tarihin Sarkin
Maƙeran Kano Alhaji Usman
Muhammad
An haifi Sarkin Maƙera Alhaji Usman Muhammad a unguwar Galadanci da ke cikin birnin Kano a
shekarar 1941, kimanin shekara 82 ke nan a yanzu. A lokacin da ya tashi a
gidansu abin da ya fara buɗe ido da shi, shi ne neman ilimin
addini. Ya yi karantun allo a wajen malamansa da suka haɗa da: malam Audu
da ke unguwar Ɗiso da kuma Malam Almajir Shehu
Maihula, da ke a unguwar Ɗiso a cikin birnin
Kano, inda ya samu ilimin littattafan addini.
Haka kuma, Alhaji Usman ya yi karatu a
makarantar Ɗandago Firamare, inda ya ƙare a shekara 1963. Sarkin maƙera ya yi aikin gwamnati, inda ya yi aiki da hukumar ruwan sha ta karkara
wato (Rural Water Supply). Sannan, ya yi aikin Soja inda ya yi shekara goma sha
ɗaya da kwana ashirin da bakwai.[55]
A wannan aiki na gidan Soja ya ƙware ne a fannin
sadarwa, wato (Communication). Bayan da ya dawo daga aikin soja, ya cigaba da
aiki a gidan talabijin na C.T.V, wato (A.R.T.V.) a yanzu.[56]
A nan gidan Talabijin, ya shekara takwas yana aiki sannan ya bari.[57]
A wannan lokaci ne ya dawo gida ya ci gaba da sana’ar ƙira kamar yadda aka saba tun iyaye da kakanni.
Sarkin Kano marigayi Alhaji Ado Bayero
ne ya naɗa shi sarautar Sarkin Maƙeran Kano. An yi
wannan naɗi ne a shekarar 1979. A wannan lokaci an gudanar da gagarumin bikin naɗin wannan sarautar
tare da wasanni na al’adar maƙera. Sarkin maƙeran Kano a yanzu, ya kai kimanin shekara 40 yana gudanar
da wannan sarauta ta Sarkin maƙera. Allah ya
albarkace shi da ‘ya’ya goma (10) maza 3 da mata 7 da jikoki da dama.
4.8.3 Ayyukan Sarkin Maƙera
Sarautar Sarkin maƙeran Kano tana da ayyuka na musamman da take gudanarwa domin ci gaban al’umma da kuma wannan sana’a tasu. Daga cikin ayyukan wannan sarauta akwai:
4.8.3.1 Aikin ƙira
Aikin ƙira shi ne babban aikin sarkin ƙira, ƙwarewarsa da jajircewa a wannan sana’a ta ƙira ita ce ta yi
sanadiyar zamansa sarkin maƙera baya ga gadon
wannan sarauta da ya yi. Har inda ake yanzu sarkin maƙeran Kano kan shiga maƙera ya yi aiki
kamar yadda ya saɓa. Ya kan ƙera masu da linzami da kayan aikin gona
da na faɗa da na kare kai da dai sauransu da dama.
4.8.3.2 Bayar da Magani
Magani na nufin harhaɗawa ko yin wasu
abubuwa na musamman don shawo kan wani, ko samun galaba a kan wani abu. Haka
kuma, magani yana iya kasacewa abin da ake sha ko shafawa a jiki ko ɗurawa a jini ta
hanyar yin allura.[58]
Sarkin maƙeran Kano yana bayar da maganin wuta,
musamman idan an kone abin ya yi muni. Yakan taimaka wa da magani kuma cikin
ikon Allah a samu lafiya ta warke.
4.8.3.3 Samar da Makaman Yaƙi
Makaman yaƙi na nufin kayan
da ake amfani da su wajen kare kai da lafiya a lokacin yaƙi. Kamar yadda Ƙamusun Hausa (2006:322), ya bayyana
makami da cewa abin faɗa ko yaƙi kamar bindiga ko takobi ko mashi ko sanda da makamantansu.
Tun a dauri, Sarkin maƙeran Kano shi ne yake da alhakin ƙera wa masarautar Kano makamai na yaƙi domin kare kansu
da lafiyarsu. Wannan ya biyo bayan hare-hare da sarakunan ƙasar Hausa suke kai wa junansu. Ga wasu daga cikin makaman a hoto a ƙasa.
4.8.4 4 Ƙera Ƙofofin Shiga Garin Kano
Ƙofofin Kano su ne mashigai da suke a jikin ganuwa da ta zagaye garin Kano.
Kamar yadda ƙamusun Hausa (2006:282), ya bayyana ƙofa da cewa kafa ko ƙofa da aka yi don shiga rufaffen abu kamar ɗaki ko mota da
sauransu. Sarkin Maƙeran Kano shi ne yake ƙera kofofin Kano, ana ƙera su ne don a rufe gari saboda gudun kada a kawo hari a shigo gari. Yin
hakan, shi ya taimaka wajen samar da cikakken tsaro a ƙwaryar birnin Kano.[59]
Ga wasu daga cikin tsofaffin ƙofofin Kano.
4.8.3.5 Kula da Tsaron Maƙera da Lafiyar Maƙera
Tsaro shi ne bayar da kariya da kulawa
ga wasu mutane ko dukiya da take keɓance a wani waje na musamman. Sarkin maƙeran Kano shi yake kula da tsaron rukunin al’umma masu wannan sana’a ta ƙira. Kowace sana’a suna da rukunin gidajensu da iya masu gudanar da wannan
sana’ar suke rayuwa domin gudanar a
ayyukansu na yau da kullum. Wannan ya sa ya zama dole ya kula da tsaron lafiyar
su saboda tsoron masu kawo musu hari da makamantansu. Yana wannan aiki ne ta
hanyar ƙera ƙofofin gari da za a kulle ko’ina da kuma ƙera kayan yaƙi da na faɗa waɗanda ake amfani da su domin ba kai da dukiya kariya.
4.8.3.6 Sulhu da Sasanci
Sarkin maƙera a farfajiya kira a birnin Kano, shi ne yake kula da abubuwan da suka
shafi shari’a a tsakanin masu gudanar da sana’ar ƙira a birnin Kano.
Idan shari’a ta fi karfinsa a cikin rukunin wannan
masu sana’a, sai dai a tafi gaban Sarkin Kano.
4.8.3.7 Karɓar Haraji
Ga al’ada Sarkin maƙeran Kano shi yake
da alhakin karɓar haraji na wannan rukunin al’umma masu gudanar da wannan sana’a ta ƙira. Idan ya karɓa zai kai kuɗin wajen dagaci ko
mai gari. Su kuma su kai wa hakimi. Haka dai abin yake tafiya har zuwa wajen
Sarki.
4.8.4 Hakiman Sarkin Ƙira da Ayyukansu
Dukkan wata sarauta a ƙasar Hausa ba ta rasa ƙananan sarautu a ƙarƙashinta da suke taimaka mata wajen gudanar da wasu ayyukanta. Masu iya
magana kan ce “Hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka”. Daga
cikin waɗannan sarautu da suke taimaka wa Sarkin maƙera wajen aiwatar da ayyukansa sun haɗa da:
4.8.4.1 Ciroman Ƙira
A al’adar masarautar Kano, sarautar
Ciroma sarauta ce ta babban ɗan Sarki. Wannan dalilin ne ya sa
Sarkin maƙeran Kano ya ƙwaiƙwayi wannan tsari ya naɗa babban ɗansa a wannan
sarauta ta Ciroman ƙira. Haka kuma shi ne mai gudanar da
duk wani abu a madadin Sarkin ƙira.[60]
4.8.4 2 Galadiman Ƙira
Sarautar galadiman ƙira sarauta ce da ake ba wa ɗan Sarkin ƙira domin ya kula da yadda ayyukan ƙira suke gudana a masarautar Sarkin maƙeran Kano. Sannan shi ne mai sayar da duk wani kaya da aka ƙera a wannan maƙera da take a
gidan Sarkin maƙeran Kano.
4.8.4.3 Ɗanmasanin Ƙira
Sarautar Ɗanmasani sarauta ce ta malanta a masarautar Kano. Galibi an fi naɗa wannan sarauta
ga wanda yake ƙwararre kuma masani a wani fanni na
ilimin addini ko na zamani.[61]
Wannan dalilin ne ya sanya ya naɗa ɗansa Auwalu Usman
a wannan sarauta. Wannan ya biyo bayan ƙwarewarsa a fagen
aikin ƙira. Babban aikin wannan sarauta a
fadar Sarkin maƙeran Kano shi ne: Duk wani aiki da za a
yi na bajinta da fita kunya shi ake ba wa wannan aikin saboda ƙwarewarsa a aikin ƙira.[62]
4.8.4.4 Wamban Ƙira
Wamban ƙira sarauta ce da Sarkin maƙeran Kano yake naɗa ta ga ɗansa. Aikin wannan
sarauta shi ne kula da lafiyar kayan aiki a cikin maƙera. Duk wani abu da za a yi aiki da shi a maƙera, shi ne ya ke gyara shi kafin a fara aiki. Daga cikin kayan da yake
kula da su akwai, kula da lafiyar zuga-zugi da kafin kulafe da zartuna da zaman
uwar maƙera.
4.8.5 Al’adun Maƙera A Jiya
Sarautar Sarkin ƙira kamar sauran sarautun sana’o’in gargajiya, tana da al’adu da take
gudanarwa a wajen bukukuwansu da wajen gudanar da wannan sana’a tasu. Daga
cikin waɗannan al’adu na sarautar ƙira akwai:
4.8.5.1 Wasan Wuta
Wasan wuta wasa ne da maƙera suke yi a lokacin bukukuwansu na al’ada. Sukan yi
wannan wasa ne ta hanyar shafa wa jikinsu wuta da kananzir, ba tare da wutar ta
kama su ba. Kafin su fara wannan wasannin nasu sukan shafa magungunan na al’ada
kafin a fara gudanar da wasan. Yin hakan shi zai hana wuta ta ƙona mai yin wasa da ita. Amma bayan an tashi wasan da
kwana ɗaya, idan ya taɓa wutar za ta ƙona shi.
Maƙera suna haɗa maganin wuta ta hanyar amfani da sassaƙen ƙirya da sassaƙen marke da sassaƙen bagaruwa. Idan waɗannan saƙe-saƙi sun samu, sai a
tashi tsakiyar dare a je a ɗebo sassaƙen tumfafiya. Daga nan sai a haɗe su wuri guda a shanya su su bushe
sosai, a dake su gaba ɗaya har su zama gari. Idan buƙatar wasan wuta ta taso, sai a ɗauko wannan garin
magani a jiƙa shi a shafe duk jiki a lokacin da za
a gudanar da wannan wasan wuta. Idan aka yi haka har a gama wasan wutar ba za
ta ci mutum ba. Amma idan aka gama wasan da kwana ɗaya, idan mutum ya
yi wasa da wutar za ta ƙona shi.[63]
4.8.5.2 Bikin Cin Tama
Wannan tsohuwar al’adar maƙera ce da suka daɗe suna gudanarwa. Suna yin wannan
al’ada ne domin su nemo wa kansu ƙarafan da za su yi
amfani da su wajen ƙira. Sukan yi tafiya mai nisa wajen
neman sinadarin ƙarfe wanda ake kira tama, a ƙarƙashin jagoranci
Sarkin ƙira. Idan suka samu inda wannan
sinadari yake, sukan yi rami su zuba a cikin a hura wuta har sai duwatsun da
sinadarin tamar yake ciki sun ƙone, sun
rugurguje. A nan ne ruwan ƙarfen zai ware a ƙasa, garin dutsen tamar a sama. Wannan ita ce hanyar da
maƙera suke amfani da ita a dauri wajen
samar wa kansu ƙarfen da suke sarrafawa domin gudanar
da ayyukansu na ƙira. Akan share kwanaki da yawa ko
watanni ko shekara a dawa, ana aiwatar da cin tama. Sannan babu makawa ga cin
tama sai an yi tsafi. Don haka makaɗa Ɗan’anace ke cewa:
“Maƙera ba su cin tama
Sai sun tsahwa.”
(Gindin Waƙa: “Maza na tsoron karo da Ado.........”) Bunza (2006:40).
4.8.5.3 Nuna Buwaya
Maƙera da dama kan nuna buwayarsu a wajen wasanninsu ko bukukuwansu na al’ada.
Akan samu wasu su bayyana tsatsube-tsatsubensu ta hanyar wasa da wuta. A wannan
yanayi ne wani zai yi wani zanensa wuta ta yi bartsi ta kama hakukuwan da ke
wurin. Wani ya yi kaki ya zubar da majina nan take ta koma garwashin wuta. Wani
ya saka ƙarfe a wuta ya yi ja ya yi tozali da
shi ko a saka a baki ko hammata, sai ya yi sanyi a fitar da shi. Bunza
(2006:46). Duk wannan buwaya da suka nuna wutar ba zata cutar da su ba. Wajen
samun magungunan waɗannan asirai ake samun
tsatsube-tsatsuben da maƙera suke yi domin
kare martabar gado.
4.8.6 Sauye-Sauye a Sarautar Ƙira da Al’adunsu
Masu iya magana kan ce: “Zamani riga ce....”.
Wannan ya biyo bayan sauye-sauyen zamani da aka samu a cikin sarautar Sarkin ƙira. Wannan ne ya sa aka samu wasu ƙarin abubuwa a cikinta saɓanin waɗanda ake da su a
gargajiyance. Daga cikin waɗannan sauye-sauye da aka samu akwai:
4.8.6.1 Samar da Ofishin Sarkin Maƙera
A sakamakon sauyawar zamani ya sa wasu
daga cikin maƙera sun koma ƙirar zamani. Hakan ne ya ba wa Sarkin maƙeran Kano damar samar da ofishinsa, domin kula da wannan sana’a ta maƙera a garin Kano.
Duk da cewa ‘ya’yansa ne suka samar da wannan ofis, amma dai an samar da
shi domin shi. Kuma ‘ya’yansa ne suke gudanar da ayyukansa a wannan ofis. A
wannan waje akwai inda ake siyar da kayan da ake ƙera akwai kuma ɓangare da aka ware na daban inda ake
kira, wato maƙera. Sannan a nan ne ake sauke duk wani
baƙo da ya kawo ziyara ko sayan kaya a
wannan wuri.
4.8.6.2 Kai Gaisuwa
Wannan al’ada ta gaisuwa al’ada ce da
har yanzu ake gudanar da ita, domin yi wa Sarkin Kano barka da juma’an ko
sallah. Sarkin maƙeran Kano yakan kai wa mai martaba
Sarkin Kano gaisuwar domin girmamawa a lokacin da ake zaman fadaci.
4.8.6.3 Tukuicin Sallah
Tukuici na nufin lada da akan ba wanda
ya kai wata ƙyauta don nuna yabawa da ƙyautar da aka yi Ƙamusun Hausa
(2006:442). Al’adance wata ƙyauta ce da mai martaba Sarkin Kano ke yi wa Sarkin maƙeran Kano. A kan yi masa wannan tuƙuici da ragon
layya da babbar riga. Wani lokacin ma a kan haɗo masa da buhun
shinkafa da har da abin cefane.[64]
Ana yi masa haka ne sakamakon ƙera wa Sarki kayan
kawa da suka haɗa da masu da linzamai na dawaki da dai sauransu.
4.8.6.4 Bikin Naɗin Sarauta
Har yanzu ana gudanar da wannan bikin
naɗin sarauta a al’adan maƙera a garin Kano.
Sarkin maƙeran Kano kan naɗa hakimansa bisa
sahalewar mai martaba Sarkin Kano. Ana yin wannan naɗin ne a ƙofar gidan Sarki maƙera, inda ake kawo
kujerun roba da rumfuna (conopy) a
zagaye wajen. A nan ake naɗe hakiman Sarkin maƙeran Kano. Daga nan ne bayan an yi naɗin wanda aka naɗa zai kai gaisuwar
ban girma ga Sarkin maƙera. Bayan ya yi gaisuwa, sarkin maƙera zai yi masa bayani akan nauyin da aka ɗora masa. Daga
nan, sai ya hau doki zuwa gidansa tare da makaɗe da masu
bushe-bushe. Yana zuwa ƙofar gidansa zai tarar da matasan maƙera sun taru suna jiran sa, domin gudanar da wasanninsu
na al’ada da dai sauransu.
4.8.7 Samuwar Kayan Aikin Ƙira Na Zamani
Zamani ya yi mutuƙar tasiri a sana’ar ƙira, wannan dalilin ne yasa aka samu yawaitar sabbin
kayan aikin ƙira na zamani. Daga cikinsu akwai:
4.8.7.1 Injin Hura Wuta
A can baya, maƙera suna amfani da zuga-zugi wajen hura wuta a cikin maƙera, amma yanzu zamani ya sauya, inda aka samu wani inji
da ya kawo sauƙi wajen hura wuta. Wannan injin yana
amfani da batur ko sola da fanka mai farfela da take hura wutar da ake gasa ƙarfe a cikin maƙera.[65]
Wannan ya kawo wa maƙeran zamani sauƙi sosai wajen gudanar da ayyukansu na ƙira. Ga hoton injin nan a ƙasa.
4.8.7.2 Wadatattun Ƙarafa
A al’adance maƙera kan sha mutuƙar wahala wajen cin tamar da za su yi
amfani da ita a wajen aikin ƙira. Wannan
dalilin ne ya sa har sai sun je cin tama a waje mai nisa, sannan su samar wa da
kansu ƙarafan da za su yi amfani da su. Yanzu
zamani ya sa an samu wadatattun ƙarafa a sakamakon
wadatar ƙarafa da ake samu daga tsofaffun motoci
da babura da injina da dai makamantasu. Sannan suna samun ƙarafan cikin sauƙi ba tare da sun sha wahalar zuwa haƙo tama ba, sai dai su sayo su daga masu sana’ar ƙarafa ko wurin waɗanda ake kira Bola-jari.
4.8.7.3 Injinan Zamani
Maƙera kan sha mutuƙar wahala a wancan lokacin wajen karya ƙarafa ko sarrafa su, tare da ɓata lokaci a yayin
gudanar da wannan aiki. Zamani ya samar da inji mai suna (Carbide), wanda yake karya karfe ya daddatsa ya kuma lauya shi
cikin sauƙi ba tare da ɓata lokaci ba. Ga
hotonsa nan a ƙasa.
4.8.7.4 Samuwar Ma’aunai
A dauri maƙera ba su yi wa sana’ar tanadi na wani abin awo na musamman, wanda ya shafi tsawo ko kuma faɗi. A wancan lokaci
idan za su yi wani abu, sai dai kawai su kintata su yi. Amma a sakamakon
sauye-sauyen zamani da aka samu a cikin wannan sana’a, an samu ruler da tape da ake amfani da su waje
awon tsawo da kuma faɗin abin da ake so a ƙera a zamanance.
4.8.7.5 Nau’ikan Ƙarafa
Gabanin zamani ya yi tasiri a wannan
sana’a ta ƙira, maƙera suna amfani da baƙin ƙarfe kawai wajen aikin ƙira. Yanzu an samu sauyi na zamani da ya zo da nau’ikan ƙarafa daban-daban waɗanda ake yin
amfani da su wajen ƙere ƙeren abubuwa da dama. An samu ƙarafa irin su
tagulla (bronze) da alminium da ake amfani da su wajen yin
kwalliya a ƙarafan da aka sarrafa a maƙera.
4.8.7.6 Injin Walda
Maƙera a ƙasar Hausa ba sa yin walda domin ba su da kayan aikin da
za su yi ta, amma yanzu zamani ya zo da ita, kuma ta ba maƙera gagarumar gudummawa wajen sauƙaƙa musu aiki. Wannan ne ya sa a yanzu ake ƙira galmar shanu da cakarkara da injin casar gyaɗa da na masara da na
shinkafa da sauransu.
4.9 Matsayin Sarautun Sana’o’in Gargajiya a Masarautar Kano
A tsarin masarautar Kano, sarautun sana’o’in
gargajiya duk hakiman Sarki ne, kuma hakimi shi ne mutum na biyu mafi girman
sarauta da iko a tsarin wannan masarauta.[66]
Wannan ne ya sanya yake shugabantar rukunin al’umma masu gudanar da irin waɗannan sana’o’i, ko
kuma su wakilci Sarki a wani muhimmin taro a wani wuri na musamman da ake buƙatar masu wannan sana’o’i.[67]
A masarautar Kano Sarki shi yake naɗa hakimi a
matsayin wakilinsa. Su ne suke zama a matsayin idon Sarki a wajen wannan
al’umma, domin su sa idanu a kan duk abin da yake faruwa a ƙarkashin ikon sa. Sannan, ko da kuwa wata matsala ce ta
taso a ƙarƙashin ikon wannan mai sarauta, ba za ta wuce kai tsaye zuwa gaban Sarki ba
. A nan za su yi duk abin da ya dace domin kawo ƙarshen wannan matsalar da ta taso, domin kuwa su ne wakilan Sarki. A duk wani
abu da waɗannan sarautuna sana’o’i suka aiwatar sun aiwatar ne da sunnan Sarki. Duk
lokacin da waɗannan sarakunan na sana’o’in gargajiya suka zo gaisuwar juma’a wajen Sarki,
sukan isar wa da Sarki rahoton abin da ya faru da kuma matakin da suka ɗauka a kan wannan
matsala da ta kunno kai a tsakanin masu gudanar da wannan sana’o’i. Sarki zai
yi musu godiya da sanya albnarka a kan wannan aikin da suka gudanar a madadin
Sarki. Idan kuma, lokacin da suka zartar da hukunci sun yi wani abu wanda ba
daidai ba, a nan ne Sarki zai yi musu gyare-gyare saboda su kiyaye gaba.
4.9.1 Matsayin Sarautar Sarkin Ɗori
A gargajiyance, idan aka dubi matsayin
sarautar ɗori dangane da sana’arsu, za a ga cewa sarauta ce ta masu sana’a wadda ta
danganci lafiyar al’umma a ƙasar Hausa. Suna kusa
da al’umma dai dai gwargwado. Idan aka duba za a ga cewa maɗora suna yawan
hulda da al’umma mabambanta, kasancewar sana’arsu, sana’a ce da ta jiɓinci kiwon lafiya.
Wannan dalilin ya sa suke yin hulɗa da kowane irin rukuni na al’umma, kama
daga kan sarakuna da talakawa, da maza da kuma mata. Maɗora suna yin
wannan hulɗa dangane da sana’ar ɗori.
Al’ummar Hausawa suna mutuƙar ganin daraja da ƙimar sarautar
Sarkin ɗori, domin suna gani cewa yana ba su gagarumar gudummawa wajen kula da
lafiyar al’umma, musamman abin da ya shafi ƙashi kamar targaɗe ko gocewa ko tsagewar ƙashi ko kuma karaya. Maɗora a ƙasar Kano su ne suke yin duk yadda za su yi don ganin an
samar wa mutum lafiya dangane da abin da ya shafi matsalar ƙashi.
Haka abin yake a ɓangaren sarakuna a
ƙasar Kano, matsayin sarautar ɗori ba shi
misaltuwa. Idan aka waiwayi tarihin sarautar, za a ga cewa an yi sarautar ne a
sakamakon kula da lafiyar al’umma waɗanda suka samu rauni a fagen yaƙi tun a dauri. Irin wannan shahara da suka yi wajen kula
da lafiya, shi ya sa Sarkin Kano Tukur ya naɗa musu Sarki wanda
yake jagorantar wannan rukunin al’umma masu ɗori. Ke nan
sarautar Sarkin ɗori tana da cikakken matsayi a wajen sarakuna da al’ummar ƙasar Hausa baki ɗaya.
4.9.2 Matsayin Sarautar Sarkin Gini
Sarautar gini sarauta ce ta rukunin
al’umma da suke gudanar da wannan sana’a ta gini. Sannan magina sun ba da
gagarumar gudummawa wajen ganin al’ummar ƙasar Kano da
sauran sassan ƙasar Hausa sun samu muhalli. Sakamakon
a can dauri suna zama a kogunan itace da saman duwatsu da kogunan duwatsu da
dai makamansu. A sakamakon haka ne wannan rukuni na al’umma suka ɓullo da dabarar gini domin killace kai
da suturta zuri’a. Abin da wannan al’umma suka yi, ya sa al’ummar Hausawa suke
ganin darajar magina a ƙasar Hausa.
A fagen sarauta kuwa, sarakunan Kano na
ganin daraja da martabar wannan sarauta a ƙasar Kano. Dalili kuwa shi ne, waɗannan rukuni na magina sun ba da
gudummawa wajen kare garin Kano daga harin abokan gaba a dauri. Waɗannan rukunin su
ne suka gina katangar da ta zagaye garin Kano wadda ake kira da ganuwa ko
badala. Haka kuma, su ne suka gina gidan Muhammadu Rumfa, wato (Masarautar
Kano). Sakamakon wannan aiki da suka yi, ya sa aka samar da wannan sarauta a
wannan rukunin al’umma. Har wa yau, wannan sarauta tana gudanar da irin waɗannan ayyuka a
cikin masarautar Kano, a duk lokacin da aka sami sabon sarki, inda suke fasa
masa ƙofa. Sannan duk lokacin da wani aiki ya
taso da ya shafi gine-ginen wannan masarauta masu wannan sarauta su suke kula
da su.
4.9.3 Matsayin Sarautar Sarkin Fawa
A al’adance, idan aka dubi matsayin sarautar
Sarkin fawa a garin Kano, za a ga cewa sarauta ce da take kula da wani rukunin
al’umma waɗanda sana’arsu take da alaƙa da jini da ƙazanta da wari, wato Rundawa.[68]
Don haka, wasu a cikin al’umma suke yi musu kallon ƙazamai, wanda hakan bai dace ba. To amma ina, abin ya gagari kundila. Al’umma a garin Kano sun ɗauki masu wannan
sana’a ta fawa a matsayin ƙazamai, har wasu
ma suka tsane su dangane da sana’ar da suke gudanarwa. Wannan dalilin ne ya sa idan yaransu suka shigo cikin
yara tsaransu suke zolayarsu da cewa “Ga ‘ya’yan Sarkin fawa shugaban karnukan lahira”. Harris (1934:315) da Adamu (1978:6), sun alaƙanta mahauta da bauta, ma’ana su bayi ne na sauran al’umma da ba su da alaƙa da sarauta. Wannan ne dalilin ƙyamar da ake yi
musu, har ta kai ba kowa yake auren ‘ya’yansu ba. Sannan a dauri idan dokin
sarki ko wani ƙasƙantaccen mutum ya mutu, su ake ba wa su binne shi.
Wani matsayi da Sarkin fawa yake da
shi, shi ne mutane suna masa kallon mutune mai ƙwazo, jarumi da kuma juriya. Musamman ta fuskar sana’arsa da yadda yake da juriya a wajen sayo dabbar da za a
yanka domin sayar wa al’umma. Ta fuskar ɗabi’a kuwa Sarkin fawa mutum ne mai son
wasa da mutane da suke sayen nama a wajensa.
Haka kuma, idan aka kalli matsayin
Sarkin fawa ta fuskar addinin Musulunci, za a ga yana da babban matsayi dangane
da irin gudummawar da yake bayarwa wajen yanka dabbar da addinin Musulunci ya
halatta cin namanta. Haka kuma, ba a yarda a yanka dabbar da Musulunci ya
haramta cin namanta. Sarkin fawa kan ajiye malamin da yake da alaƙa da wannan sana’a ta fawa,[69] da zai riƙa yanka dabbobi ta hanyar da addinin Musulunci ya aminta
da ita. Ana yin haka ne sakamakon ƙyama da sauran al’umma uke yi wa masu gudanar da sana’ar fawa. Wannan shi ne dalilin samar da malamin yanka.[70]
4.9.4 Matsayin Sarautar Sarkin Ƙira
Matsayin sarautar Sarkin ƙira a nan shi ne, daraja ko girma da yake da shi a idan
al’ummar Hausawa dangane da sana’ar rukunin al’ummar da yake jagoranta. Sarkin ƙira shi ne yake kula da al’ummar da suke ƙera kayan aikin
noman abinci a gonakin al’umma. Irin waɗannan abubuwa da suke ƙerawa sun haɗa da: garma da
fartanya da magirbi da gatari da sauransu. Ba don sun ƙera waɗannan abubauwa ba da ba yi noma cikin sauƙi ba.
Sarkin ƙira na da wani matsayi na musamma a cikin al’umma, kasancewar sana’ar
al’ummar da yake jagoranta take taimakawa wajen haifar da ci gaban wasu
sana’o’in Hausawa na gargajiya. Idan aka dubi kayan aikin da suke samarwa domin
yin wasu sana’o’i a ƙasar Hausa, kamar sana’ar fawa da noma da jima da wanzanci da dai sauransu.
Dangane da matsayin sana’ar ƙira, Rimmer da Wasu (1948:116) sun rawaito cewa: Baba Maƙeri ya yi wani kirari da ya ƙoɗa kansa da nuna matsayin sana’ar ƙira. Ga abin da ya
ce:
“Sai ni baƙi, dodon ƙarfe, mai amana da maharba!
Da ba domin taya ba, da na yi mota!
Ba don ni ba, da ƙasa ta yi saura!
Kai, ba don ni ba, da maza sun yi gizo!
Sai ni na Ali, gatan kaka, mai abin mamaki!
Ƙarya kuke,
magauta,
Sai na gaji na bari don kaina!”
A nan Baba Maƙeri ya nana matsayin wannan sana’a ta ƙira, inda yake cewa: Sai shi baƙi dodon ƙarfe amanar maharba. Ke nan ya nuna yadda sana’ar ƙira suke da amana da fahimtar juna su da maharba. Su ne
suke ƙera musu makaman da suke yin amfani da
su a wajen harbi. Haka kuma, ya ƙara kambama kansa
ta hanyar nuna cewa shi gwani ne a wannan sana’a tasa. Sannan ya nuna cewa ba dan taya ba da ya yi mota.
A ganin sa, taya ce kawai ake yi ba da ƙarfe ba. Ya nuna
cewa, da ita ma da ƙarfe ake sarrafawa a yi, to da tuni ya
yi mota. Har ila yau, yana ganin ba don sana’ar ƙira ba, da duk gonaki sun zama saura, wato da ba su ƙera kayan aikin gona ba, da noman ma ba zai samu ba. Duk ya yi wannan
kirari ne domin ya fito da matsayin sana’ar ƙira a fili kowa ya gan ta, ya ga irin ababen da take samarwa domin aiwatar
da wasu sana’o’i ko samar d wasu kayayyakin aiki.
Wannan sarauta ta ƙira tana da mutuƙar matsayi a idon mata, musamman ma
Sarkin Fari.[71] Su ne suke ƙera musu ɗankunne da sarƙa da dai makamatansu. Wannan ne dalilin da ya sa mata suke mutuƙar gannin darajarsu. Haka kuma, sauran maƙera suna da babban matsayi a wajen al’umma, kasancewar su ne suke ƙera musu abubuwan da suke kare lafiyar kansu daga abokan gaba, kamar kibiya
da bindiga da masu. Suna gani da ba don su ba, da ba za su samu abin da za su
kare kansu ba.
A gargajiyance, an san Sarkin maƙera na da wata al’ada ta kyawun mu’amula da kusan
dukkan masu gudanar da wasu sana’o’i na gargajiya. Don haka ne masu iya magana kan ce masa “Komai da
ruwanka” a cikin sana’o’in Hausawa na gargajiya. Haka kuma, ana ganin Sarkin ƙira a matsayin mutum mai juriya, idan aka yi la’akari da wahalar aikin ƙira da cin tama da zafin wutar da suke yin aiki da ita. Amma a haka za a
gan su suna nishaɗi a lokacin da suke gudanar da wannan aiki nasu na ƙira.
Sarkin ƙira na da mutuƙar matsayi da daraja a idanun sarakunan
ƙasar Hausa. Shi ne yake sa a ƙera musu linzamin doki da kayan adon da ƙawa da kayan yaƙi da ƙofofin gari. Wannan ya isa ya nuna cewa, sarautar ƙira da maƙera na taka
muhimmiyar rawar gani a ci gaba da haɓaka tattalin arzikin al’ummar Hausawa.
Har ila yau, wasu na ganin cewa da ba maƙera, da wasu
sana’o’in gargajiya da dama ba a samu damar aiwatar da su ba.
4.10 Dangantakar Sana’o’in Gargjiya da Junansu
Idan aka waiwayi yanayin rayuwar ɗan’adam, za a ga
cewa babu yadda za a yi ya rayu shi kaɗai. Ana ganin ba yadda za ai ya ji daɗin rayuwar tashi
har ta kai shi ga cin nasarar bukatarsa, ba tare da cuɗanya da jama’a ba.
Wannan dalili na cuɗanya ya sa wani kan ci albarkacin wani.
Kamar yadda masu iya magana kan ce “Albarkacin kaza ƙadangare kan sha ruwan kasko”. Domin dangantakar da ke tsakanin sana’o’in gargajiya na nuna yadda
al’umma suke zama ɗaya wajen tafiyar da rayuwa. Kowace
sana’a na cike wani gurbi da wata san a’a ta bari, wanda hakan yake ƙarfafa haɗin kai da wanzar da tsarin tattalin
arziƙi ga al’adun Hausawa. Wannan haɗin kai ne yake
tabbatar da ɗorewar waɗannan sana’o’i na gargajiya.
Tun asali Hausawa sun fara musayar
kayan sana’a ne ta hanyar ba-ni-gishiri-in-ba-ka-manda. Wannan ya nuna cewa,
tun asali tsarin sana’o’in Hausawa na gargajiya an gina shi ne a kan tsarin cuɗe-ni-in-cuɗe-ka. Misali: a
can dauri ba a amfani da kuɗi, saboda haka mutane suke yin sana’o’i
daban-daban kasancewar sana’a ɗaya da mutum yake yi ba ta isa ta biya
masa dukkan buƙatunsa ba. Wannan dalilin ya sanya dole
sai ya nemi wani abu daga hannun wani mai yin wata irin sana’a daban da tashi.
Wannan al’amari shi ya haifar da musaya ko tsarin ba-ni-gishiri-in-ba-ka-manda.
Shu’aibu (2002).
Wannan tsari ya haifar da kyakkyawar
dangantaka tsakanin Sana’o’in Hausawa na gargajiya. Misali: dubi tsakanin fawa
da ƙira, inda mahauci zai bayar da nama ga
maƙeri, shi kuma maƙeri ya ba shi kayan aikin fawa kamar wuƙa da gatari da jan taɗi. Haka abin yake tsakanin maƙeri da magini, maƙeri kan bayar da
kayan aiki ga magini kamar wuƙar gini, shi kuma
ya yi masa aikin gini. Haka abin yake ga sana’ar dori, inda maɗora kan buƙaci kara daga manoma, su kuma su yi musu aikin ɗori idan buƙatar hakan ta taso. Haka zalika, idan aka danganta
sana’ar wanzanci da ƙira, za a ga cewa maƙeri yakan bayar da kayan aiki kamar aska ko zabira domin
a yi masa tsagar gado ko aski.
Kusan dukkan sana’o’in Hausawa na
gargajiya akwai irin wannan dangantaka a tsakaninsu sanadiyar bambance-bambancen
buƙatu na ɗan’adam wanda ya
haifar da wannan musaya. Wannan musaya kuma ta zama tushen bunƙasa sana’o’in Hausawa na gargajiya.
4.11 Dangantakar Sarautun Sana’o’in Gargajiya da Junansu
Sarautun sana’o’in gargajiya a al’adun
Hausawa su ne a matsayin shugabanni da ake bai wa kwararru a wasu sana’o’i
domin kare martabar sana’ar, da tabbatar da bin ƙa’idojin wannan sana’a. Irin waɗannan sarautu suna da dangantaka da
juna ta fuskar zamantakewa, tattalin arziƙi, da gudanar da
sana’o’in cikin haɗin kai. Misali:
4.11.1 Haɗin Guiwar Sarakuna a Harkokin Sana’o’i
Sarakunan sana’o’in gargajiya sukan haɗu a wasu lokutan
bukukuwa, domin su shawo kan wasu matsaloli da suke faruwa a cikin waɗannan sana’o’i na
su tare da zartar da hukunci. Wannan dangantaka tana ƙarfafa zaman lafiya da ingantacciyar mu’amula tsakanin masu gudanar da
sana’o’in gargajiya daban-daban.
4.11.2 Cuɗe-ni-in-cuɗe-ka
Sarautun sana’o’in Hausawa na gargajiya
suna gudanar da irin wannan cuɗanya a tsakanin masu gudanar da wasu
sana’o’in gargajiya. Wannan hulɗa ta kasuwanci ta sanya dole sai an yi
cuɗanya da juna ta fuskar kasuwanci. Tun a dauri, Hausawa ba su da wata hanyar
kasuwanci da ta wuce ba-ni-gishiri in-baka-manda. Sakamakon haka ne ya sa cuɗanya ta wanzu a
tsakanin sarakunan sana’o’i, musamman ta hanyar musayar abubuwan buƙata na rayuwar al’umma.
4.11.3 Asali
Idan aka duba asalin sarautun sana’o’in
gargajiya tun daga tushe, za a ga cewa duk asalinsu ɗaya. Bisa ga
tarihi, za a ga cewa sana’o’in Hausawa tun asali wata ce ke haifar da wata, tun
gabanin samuwar sarautun Sana’o’i a ƙasar Hausa.
Misali: A hasashen Garba (1991) da Rimmer da Wasu (1948) suna ganin cewa,
sana’ar noma ita ce sana’a ta farko da aka fara a ƙasar Hausa. Kamar yadda Hausawa suke cewa, “Noma na duƙe tsohon ciniki,
kowa ya zo duniya kai ya tarar”. Hasashen na ganin cewa, buƙatar abinci ga ɗan’adam ne ya
haifar da sana’ar noma. Sannan buƙatar kayan aikin
gona ta haifar da samuwar sana’ar ƙira da sassaƙa. Sannan buƙatar sutura da sana’ar saƙa, buƙatar muhalli da sana’ar gini. Haka wannan sana’a’o’i suka ci gaba da wanzuwa har aka kawo lokacin da aka
samu tsarin shugabanci a cikinsu, wanda haka shi ya haifar da samuwar sarautun
sana’o’in Hausawa na gargajiya.
4.11.4 Bunƙasa Tattalin Arziƙi
Waɗannan sarautu,
sarautu ne da suke da dangantaka ta fuskar bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar Hausa. Wannan ya biyo bayan kasancewar sarautu ne da suke jagorantar
rukunin al’umma da suke gudanar da wasu keɓantattun sana’o’in
gargajiya. Duka waɗannan sana’o’i babbar manufarsu ta bai ɗaya ce. Wato dai,
ana yin su ne domin samar da abin masarufi da kuma bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar Hausa.
4.11.5 Tsarin Shugabanci
Tsarin shugabanci abu ne mai mutuƙar muhimmanci a rayuwar Hausawa gaba ɗaya, kuma shugaba
yana mutuƙar taka rawar gani wajen wanzar da
zaman lafiya da daidaita duk waɗanda suka samu saɓani cikin
mabiyansa. Shu’aibu (2002). Sarautun sana’o’i suna da tsari na shugabanci.
Sanin kowa ne a rukunin masu gudanar da wata sana’a ta gargajiya, shugaba yana
da rawar da yake takawa wajen samar da zaman lafiya da daidaito a tsakanin masu
wannan sana’a. Idan aka duba kusan dukkan sana’o’in Hausawa na gargajiya, akwai
irin wannan tsarin na shugabanci. Misali, kamar yadda sana’ar fawa suke da
Sarkin fawa manona suke da Sarkin noma, wanzamai suke da Sarkin Aska. Haka
kuma, waɗannan sarakuna na taka rawa iri ɗaya, wato kare martabar sana’arsu da
wanzar da adalci da kuma bunƙasar da sana’o’insu. Waɗannan kawai sun
isa su nuna ƙyaƙƙyawar dangantakar dake tsakanin waɗannan sarautu na
sana’o’in Hausawa.
4.12 Dangantakar Sana’o’in Gargajiya da Cigaban Al’umma
Sana’o’in Hausawa na gargajiya sun kawo
ci gaba tsakanin al’ummar Hausawa, wanda a dalilin haka sana’o’in suke ta haɓaka ta fuskoki
daban-daban. Daga cikin irin cigaban da aka samu akwai:
4.12.1 Samar da Kayan Aiki
A wannan bagire za a ga yadda samar da
kayan aiki suke taimakawa wajen cigaban al’umma ta fuskar sana’o’in gargajiya.
Kamar yadda aka sani, sana’o’in Hausawa na gargajiya suke samar wa da kansu
kayan aiki. Misali, kamar yadda aka yi bayani a baya cewa maƙeri shi yake samar wa da magina kayan aiki irin su wuƙa da shabur. Haka kuma, shi yake samarwa da mahauta kayan
aikin irin wuƙa da gatari da jantaɗi. Sannan shi yake
samarwa da wanzami kayan aiki kamar askar da yake aski. Bugu da ƙari shi yake samar wa da manomi kayan aiki irinsu fatanya
da garma da sungumi. Yayin da manomi yake noma audugar da masaƙi yaƙe saƙa da ita, kamar yadda mahauci yake samar da fata ga
majemi.
4.12.2 Magani
Babu wani abu da za a yi ba tare da
lafiya ba, wannan yasa Hausswa suke cewa “lafiya uwar jiki”. Sana’o’in Hausawa
na gargajiya na ba da gagarumar gudummawa wajen kiwon lafiyar al’umma. Domin
akan samu wani ciwo ko rashin lafiya da yake da alaƙa da wata sana’a ta gargajiya. A
irin wannan hali masu gudanar da irin waɗannan sana’o’i suna ba da magani da
irin wannan lalura da take da alaƙa da sana’arsu. Misali, akan samu wani ya haɗiyi ƙayar kifi ta tsaya masa a maƙogoro, a irin wannan hali surkawa ko Sarkin ruwa na taimakawa da magani
kuma cikin ikon Allah a samu lafiya. Haka abin yake ga wanda ya ƙone, shi ma maƙera ko sarkin ƙira kan taimaka da maganin wuta. Sarkin fawa ma ba a bar
shi a baya ba wajen ba da irin wannan taimakon musamman ga wanda ya haɗiyi ƙashi ko sa ya soke shi da ƙaho ko tsinke tsire ya tsire shi. Haka yake ga wanzamai da Sarkin aska su
ma suna bayar da maganin warkar da kaciya da sauran cututtuka da suka shafe su.
Wannan ya nuna cewa sarautun suna taimakawa wajen kiwon lafiya a tsakanin
junansu.
4.12.3 Hanyar Samar da Abinci
Sana’o’in Hausawa na gargajiya na ba da
gadummawa wajen samar da abinci ga al’umma, musamman manoma da suke noma kayan
abinci da suka haɗa da dawa da masara da gero da alkama da maiwa da dauro da shinkafa da
dankali da makani da doya da rogo da sauransu. Waɗannan duk kayan
abinci da al’ummar Hausawa suka dogara da su a matsayin abincinsu na yau da
kullum. Haka kuma, mahauta suka samar da nama da ake ciki yau da kulluma, kamar
yadda surkawa suke samar da kifi da yadda mafarauta suke farauto nama domin
samun abinci.
4.12.4 Hanyar Samun Kuɗi
Mafi yawancin sana’o’in Hausawa na
gargajiya sukan zamo wa al’ummar Hausawa hanyar samun kuɗi. Domin dukkanin
sana’o’in Hausawa na gargajiya dodo ɗaya suke yi wa tsafi, don ana yin su ne
domin samun kuɗi da abin masarufi. Kamar yadda sana’ar noma take taimakawa wajen samar da
kuɗi idan an sayar da amfanin gona. Haka suna sauran sana’o’in Hausawa irin
Fawa da Gini da Ƙira da Ɗori da Sassaƙa da Wanzanci da dai sauransu, su ma
suke taimakawa wajen samar da kuɗin shiga ga al’ummar Hausawa. A taƙaice dai duk sana’o’in Hausawa na gargajiya sun yi tarayya
wajen cimma wannan manufa ta samun kuɗi.
4.12.5 Adana Al’adu da Tarihi
Sana’o’in Hausawa na gargajiya su ne
manyan hanyoyi na adana al’adun al’ummar Hausawa. Domin gudanar da su da ake yi
yau da kullum zai taimaka wajen adana al’adun Hausawa da tarihin wannan sana’a
da kuma kare martabar gado musamman ga masu sana’ar. Daina yin irin waɗannan sana’o’i na
gargajiya yakan sa wasu al’adun su salance ko ma su salwance ko su fuskanci
barazanar zamani.
4.13 Dangantakar Sarautun Sana’o’in Gargajiya da Cigaban Al’umma
Sarautun sana’o’in gargajiya su ne a
matsayin shugabanci da ake bai wa kwararru a fannoni daban-daban da sana’o’in
gargajiya kamar Sarkin Fawa da Sarkin Ƙira da Sarkin Ɗori da Sarkin Gini da Sarkin Aska da sauransu. Waɗannan sarakuna su
ne suke da alhkin shugabantar rukunin masu waɗannan sana’o’i,
tare da kare muradun mabiyan su. Dangantakar sarautun sana’o’in da ci gaban
al’umma na bayyana a fannoni da dama. Daga ciki akwai:
4.13.1 Shugabanci Da Tsari A Fannin Sana’a
Sarakunan sana’o’i na tsara dokoki da
horar da masu yin ta, wanda hakan kan taimaka wajen inganta ƙwarewa da hana aikata laifuka kamar sata da yaudara a
wannan sana’a. Wannan tsari yana taimakawa wajen
tabbatar da bin doka da oda a tsakanin masu wannan sana’a.
4.13.2`Ƙarfafa Tattalin Arziƙi
Ta hanyar inganta sana’ar da suke
jagoranta, sarautun sana’o’i na taimakawa masu yin ta wajen bunƙasa har su zama masu dogaro da kai. Misali, sarakuna
sukan shirya wa ‘ya’yansu wani zama da gwamnati don su samu horo mai kyau a
kan wannan sana’a da kuma tallafi.
4.13.3 Horar Da Matasa Da Samar Da Ayyukan Yi
Sarakunan sana’o’in sun taka rawar gani
wajen koya wa matasa sana’a, wanda suke rage zaman banza da laifuka. Wannan
yana taimakawa matasa su zama ‘yan kasuwa ko masana, su kuma daina dogaro da
gwamnti.
4.13.4 Haɗin Guiwa Da Gwamnati Da
Cibiyoyi
Sarakunan sana’o’i na iya wakiltar
rukunin al’ummar da suke jagoranta wajen shiga shirye-shiryen ci gaba da horo
daga gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu da kamfanoni.wannan haɗin kai na ƙara ba masu sana’o’i damar ci gaba da haɓaka sana’ar su.
4.14 Dangantakar Sana’o’in Gargajiya da Cigaban Zamani
Sana’o’in gargajiya su ne ayyukan hannu
da aka gada tun kaka da kakanni kamar su da saƙa d gini da ƙira da fawa da ɗori da dai
makamantansu. Waɗannan sana’o’i sun taka rawar gani wajen raya al’ummar Hausawa a dauri. A
zamanance kuwa, akwai sauye-sauye da fasahar zamani da ke shafar yadda ake
gudanar da waɗannan sana’o’i. Wannan ne ya haifar da wata muhimmiyar dangantaka tsakanin
sana’o’in gargajiya da ci gaban zamani. Daga cikin wannan dangantaka akwai:
4.14.1 Sabunta Fasaha Da Tsarin Aiki
Fasahar zamani ta sauya hanyoyin
gudanar da sana’o’in Hausawa na gargajiya. Misali, ana iya amfani da naurorin
zamani wajen gudanar da wasu sana’o’in gargajiya kamar saƙa da dinki da gini da makamantansu. Wannan sabuntawa na ƙara haɓaka sana’o’i da dacewa da buƙatun kasuwar yau saɓanin dauri da ake amfani da tsohon
tsari na gargajiya.
4.14.2 Tallace-Tallace Ta Hanyar Intanet
Masu sana’o’in gargajiya na amfani da
shafukan sada zumunta kamar Facebook
da Instagram da Tiktok domin tallata hajarsu. Wannan ya ba su damar isa ga
kasuwannin duniya, ya kuma sauƙaƙa samun sabbin abokan ciniki fiye da na dauri.
4.14.3 Ƙirƙirar Sabbin Kayayyaki Cikin Tsarin Gargajiya
A yau, ana haɗa fashar zamani da
fasahar gargajiya wajen ƙirƙirar sabbin abubuwa. Misali, tufafin gargajiya kamar saƙi da rini da suna da sabbin salo da yake jituwa da
zamani. Haka kuma, sana’ar gini da ƙira da fawa da ɗori suna suna da salo mai jituwa da ƙa’idojin zamani.
4.14.4 Koyarwa da ba da Horo A Zamanance
A wannan lokacin an samu makarantu da
kwasa-kwasai da ke koyar da sana’o’in gargajiya cikin sabon salo na zamani.
Wannan na taimakawa matasa su koyi sana’a cikin sauƙi ta hanyar amfani da bidiyo da manhajoji kamar YouTube ko Coursera.
4.14.5 Shiga Kasuwannin Duniya
A yau, zamani ya kawo sauƙi wajen sufuri da sadarwa, wannan ya ba da damar bazuwar
kayyayyakin sana’o’in gargajiya zuwa manyan kasuwannin duniya. Misali, hajoji irin su tukwane
da saƙa da kayan ado na mata, ana tura su
cikin sauƙi ba tare da an sha wahala ba kamar
dauri. Wannan ci gaba yana buɗe ƙofofi ga masu sana’o’in gargajiya su shahara da kuma samun kuɗaɗen shiga.
4.15 Dangantakar Sarautun Sana’o’in Gargajiya da Cigaban Zamani
Kamar yadda aka bayyana a baya,
sarautun sana’o’i su ne jagororin masu gudanar da sana’o’in gargajiya. A da waɗannan sarakuna su
suke kula da tsari da tarbiyya da bunƙasa sana’o’insu. A zamanance,
ci gaban fasaha da sauyin rayuwa ya kawo canji a yadda ake gudanar da sana’o’i da kuma rawar da
sarakunan sana’o’i suke takawa. Wannan ya haifar da muhimmiyar huldar zamani da sarautun
sana’o’in gargajiya. Daga cikin dangantakar da aka samu tsakanin sarautun
sana’o’in gargajiya da ci gaban zamani akwai:
4.15.1 Rikiɗewar Sarautun Sana’o’in Gargajiya Zuwa Shugabancin Zamani
A zamanance, sarakunan sana’o’in
gargajiya suna taka rawa fiye gargajiya kaɗai, suna zama masu
wakilci a hukumomi da ƙungiyoyi da kwamitocin gwamnati. Wannan
ya ba su damar samun goyon baya gwamnati da NGO don bunƙasa sana’ar su da masu yin sana’ar.
4.15.2 Haɗin Guiwa da Cibiyoyi Na Fasaha Da Horo
Sarakunan sana’o’i na iya shiga hulɗa da makarantu da
cibiyoyin koyon sana’o’i da ƙungiyoyin
kasuwanci domin sabunta kwarewar masu sana’o’in gargajiya.
Misali, Sarkin gini na iya shirya horaswa a kan sabbin dabarun gini ko amfani
da wasu injina na zamani a wajen gini.
4.15.3 Tallafawa Masu Sana’o’in Gargajiya da Bayar da Shawarwari
Sarakuna sana’o’in gargajiya na taka
rawar gani wajen ganin masu gudanar da sana’o’in sun rungumi ci gaban zamani
don bunƙasa sana’o’insu. Suna yin
haka ne domin su karɓi sabbin dabaru kamar sayar da
kayyayaki ta intanet da samar da samfura masu jituwa da buƙatun zamani.
4.15.4 Zama Jakadu A Kasuwannin Zamani
Sarakunan sana’o’in gargajiya na iya
amfani da matsayin su wajen tallata sana’ar su a manyan kasuwanin baje-koli na
duniya. Misali, a yayin expo ko fair sarakunan sana’o’i na iya wakiltar
sana’ar su da kayan gargajiya cikin tsarin zamani.[72]
4.16 Naɗewa
Daga ƙarshe, an yi bayani a kan sarautun sana’o’in Hausawa na
gargajiya. Inda aka dubi sarautar Sarkin ɗori, da Sarkin fawa, da Sarkin gini, da
kuma Sarkin ƙira. Sannan an yi bayani a kan asalin
sarautun sana’o’in gargajiya da sarautun a jiya da kuma a yau. Haka kuma, an yi bayani a
kan taƙaitaccen tarihin sarakunan da ke riƙe da waɗannan sarautu na sana’o’in gargajiya a
garin Kano. An yi bayanin a kan hakiman sarautun da ayyukansu da ƙananan sarakunan waɗannan sana’o’i. Sannan, an yi bayani a
kan ayyukan sarakunan sarautun da sauye-sauyen da ke tattare da al’adun
sarautun sana’o’in Hausawa na gargajiya. Bugu da ƙari, an yi bayanin matsayi da dangantakar sarautun sana’o’in Hausawa na
gargajiya musamman a garin Kano.
[1] Tattaunawa da Sallaman Kano Alhaji Dauda a gidansa dake Ƙofar Ƙwaru cikin gidan Mai martaba
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero. Ranar Laraba 06/4/2022 da ƙarfe 8:00 na
dare.
[2]
Tattaunawa da Alhaji Wada Muhammad (Shamakin Kano) a gidansa da ke ƙofar Ƙwaru cikin gidan Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado
Bayero. Ranar Laraba 06/4/2022 da ƙarfe 8:00 na dare.
[3]
Tattaunawa da Ɗanrimin Kano Alhaji Sarki Waziri a ofishinsa da ke Majalisar
masarautar Kano (Kano Emerate Council), ranar Talata 5/4/2022 da misalin ƙarfe
3:20 na yamma.
[4] Wato zamanin
Sarkin Kano Muhammadu Inuwa.
[5] CSNL (2006). Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero. Wallafar Cibiyar Nazarin
Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
[6] Irin wannan tsari shi ne ya ba Korau da ya fito daga
Tsahe nasara a gasar kokawa a ƙasar Katsina, inda ya kayar da Sannau ya zama Sarkin
Katsina.
[7] Yanayin tsarin siyasar mulkin Nijeriya yana taka rawar gani ga tsarin
shugabanci gargajiya a yanzu. ‘Yan siyasa sun tsunduma sarakunan gargajiya
cikin harkokin siyasarsu. Wannan dalilin ya sa sarautun gargajiya a wannan
lokaci suke fuskantar barazana daga wasu ‘yan siyasar Nijeriya.
[8] Dan garin bayyani a dubi hadisan Abu Dauda mai lamba 2043 da Tirmizi
mai lamba 2082 da Ibn Maja mai lamba 3525. An karɓo
daga Abdullahi ɗan Abbas, Allah ya ƙara masa yadda ya ce “ Wani mutumi ya karya
ƙafarsa, ya zo ga Annabi (S.A.W), Annabi Muhammadu ya riƙe ƙafar ya haɗe ta, ya
kuma roƙi Allah ya sa ta haɗe, cikin Ikon Allah ƙafar ta haɗe. Ya kuma samu
sauƙi. Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Maja suka rawaito. (Fassarar mai bincike).
[9]
Tattaunawa da Nafi’u Uba Muhammada (Ɗaya daga cikin ‘ya’yan Sarkin Ɗorin Kano)
a gidan Sarkin Ɗorin Kano da ke unguwar Ƙofar Na’isa a cikin birnin Kano. Ranar
Juma’a 18/08/2023 da misalin ƙarfe 3:30 na yamma.
[10] Tattaunawa da
Sarkin Ɗorin Kano Alhaji Uba Yusuf Muhammad ranar Asabar 05/07/2023 da misalin
ƙarfe 3:30 na yamma a gidansa da ke unguwar Ƙofar Na’isa a cikin birnin Kano.
[11] Amma Sarkin ɗorin
a baki (wato shigege), ba Sarkin Kano ne ya naɗa shi ba, galibi suna yin haka
ne domin su ɗaukaka sana’arsu ta ɗori a idon al’umma.
[12] Tattaunawa da Nafi’u Uba Muhammad (Ɗaya daga cikin
‘ya’yan Sarkin ɗorin Kano) a gidan Sarkin ɗori Kano da ke unguwar Ƙofar Na’isa a cikin birnin Kano. Ranar Juma’a 18/08/2023,
da misalin ƙarfe 3:30 na yamma.
[13] Daidai da ɗure na 20
[14] Tattaunawa da
Nafi’u Uba Muhammada (ɗaya daga cikin ‘ya’yan Sarkin Ɗorin Kano) a gidan Sarkin
Ɗorin Kano da ke unguwar Ƙofar Na’isa a cikin birnin Kano.
Ranar Juma’a 18/08/2023, da misalin ƙarfe 3:30 na yamma.
[15] Musamman idan
aka samu karaya wadda ta fasa ƙashi ta fito, ko kuma kashin ya ragargaje. Duk
yana yin haka ne domin kare martabar sana’arsu.
[16] Tattauwanawa
da Sarkin Ɗorin Kano Alhaji Uba Yusuf Muhammad ranar Asabar 05/07/ 2023. da
misalin karfe 3:30 na yamma a gidansa da ke Ƙofar
Na’isa a cikin Birnin Kano.
[17] Tattaunawa da
Shamakin Fawan Kano Malam Abubakar Hamisu a gidansu da ke Unguwar Arzai a cikin
birnin Kano, ranar juma’a 11/08/2023 da misalin ƙarfe 3:30 na rana.
[18] Ita wannan
makaranta ba Islamiyya ba ce ba kawai, ana haɗawa da karatun boko ne da kuma na
addini.
[19] Tattaunawa da
Sarkin Fawan Kano Alhaji Isyaku Alin Muli a ofishinsa da ke Abbatuwa a Unguwar
Ƙofar Mazugal a cikin birnin Kano, ranar Laraba 6/9/2023 da misalin ƙarfe 11:00
na safe.
[20] Akan samu ɓarayi
dabbobi da mashaya da makamansu duk a wannnan wuri.
[21] Amma a yanzu
saboda tasiri na addini Musulunci da zamananci, babu bawa kamar dauri. Sai dai
akan samu bawa ne na sa kai a tsarin sarauta a ƙasar Hausa.
[22] Daga cikin
irin waɗannan mata masu wannan sana’a ta fawa a garin Kano, akwai Hajiya Taɓalla
wadda aka samu wannan bayani daga gare ta a wata tattaunawa da mai bincike ya
yi da ita a gidanta da ke unguwar Koƙi a cikin birnin Kano ranar Laraba
11/6/2024 da misalin ƙarfe 10:00 na safe.
[23] Tattaunawa da Hajiya Ruƙayya Haruna, ɗaya daga cikin mata masu sana’ar
fawa a garin Kano Wadda take zaune a Shago Tara a unguwar Kurna a Ƙaramar Hukumar Dala da ke jihar Kano ranar Alhamis
12/6/2024 da misalin ƙarfe 11:00na safe.
[24] Daidai
da ɗure na 32
[25] Birget
(Bridgate) unguwa ce mai ɗauke da tarin al’umma da ke a yankin arewa maso
gabashin birnin Kano.
[26] Unguwar Tudun
Falani unguwa ce da take a yamma maso arewacin birnin Kano.
[27] Unguwa uku
unguwa ce mai tarin al’umma da ke a kudu da birnin Kano.
[28] Wasu sukan yi surƙullen ta hanyar haɗawa da idanun
jaririyar Mage da ba ta buɗe ido ba da dai makamantasu.
[29] Dubi Bunza, A. M. (2006:233). Gadon Feɗe Al’ada. Jerin Littattafan
Cibiyar Nazarin Al’adun Hausawa. Lagos: Tiwal Nigerian Limited.
[30] A tattaunawa
da Dr. Datti Sani likitan dabbobi a ranar Laraba 6/9/2023 a ofishi likitan
dabbobi na Abbatuwa da ke cikin birnin Kano, ya bayyana cewa, a lokacin da aka
yanka dabbobin, likitocin kan zagaya su duba su musamman wasu sassan na jikin
dabbobi da kan iya kamuwa da wasu cututtuka kamar hanta da ake iya samun
cututtuka irin su Fascioliasis da Multiple Absecess da
Liver Cirrhosis. Haka kuma, akan iya samun cuta a huhun dabbobin irinsu
Bovine
Tuberculosis da Knocadiosis da Contafious Bovine Pleuro
plreumonia. Sannan a Ƙoda ma a kan samu irin wannan
cututtuka inda suke kamuwa da cuta irin su Intestitial Nephritis da
Culumerular Nephritis, sai kuma zuciya da ake samun cututtuka irinsu Cysticercosis
da Traumatic
Pericarditis da dai sauransu.
[31] Tattaunawa da
Shamakin fawan Kano Malam Abubakar Hamisu a gidansu da ke Unguwar Arzai, a
cikin birnin Kano, a ranar juma’a 11/08/2023 da misalin ƙarfe 3:30 na rana.
[32] Tattaunawa da
Sarkin fawan Kano Alhaji Isiyaku Alin Muli a ofishinsa da ke Abbatuwa a Unguwar
Ƙofar Mazugal da ke cikin birnin Kano, ranar Laraba
6/9/2023 da misalin ƙarfe 11:00 na safe.
[33] Rumfar masu
ita ce tawagar mai martaba Sarkin Kano, duk wanda aka gan shi a cikin wannan
tawaga mutum ne mai mutuƙar muhimmanci a masarautar Kano.
[34] Daidai d ɗure na 42
[35] Wato waɗanda
suka gaji wannan sarauta daga iyaye da kakanni.
[36] A wanann
lokacin mutane Kano suna rayuwa a kan dutsen Dala da magwan da kuma dutsen
fanisau da dai sauransu.
[37] Tattaunawa da
Sarkin Ginin Kano Abdulƙadir Muhammad a gidansa da ke unguwar Yakasai a cikin
birnin Kano, Ranar Talata 5/9/2023 da misalin ƙarfe goma na safe.
[38] Ba iya gane
rana da watan da aka haife shi ba, sai dai ya bayyana cewa ana hasashen cewa a
watan 2 ko watan 3 aka haife shi a shekara 1940.
[39] A hannun
wannan malami ya sauke Al’ƙur’ani har ma ya fara rubuta shi.
[40] Daidai da ɗure na 48
[41] Tattaunawa da
mai bincike ya yi da Sarkin ginin Kano. Ya bayyana cewa ko sabuwar fadar Sarkin
Kano (Soron Ingila) da aka gyara, wadda Sarkin Kano Sunusi ya rushe ta. Shi aka
kira ya fasalta yadda waccan tsohuwar fadar take kuma aka sake gina wata sabuwa
da aka zamanantar da ita.
[42] Guga rufi ne
da ake yi da itace da zana ko karare a fada ko zaure na gidajen sarakuna ko
kuma gidajen manyan attajirai a dauri. Kamusun Hausa (2006:172) ya bayyana guga
da cewa: Ɗaurin rufin soro mai ƙafa huɗu wanda ba a yi wa ginshiƙi.
[43] Dagi zanannen tambari ne na hukuma (Kamusun Hausa
2006:86). Galibi an fi samun sa a fadojin sarakunan ƙasar Hausa. A wani ƙaulin,
yakan iya kasancewa tambari ne da ake ɗinkawa a riga musamman kufta.
[44] Tattaunawa da
Lawan Gwadabe Sarkin Gini a gidan Sarkin gini Kano dake unguwar Yakasai a cikin
birnin Kano, Ranar Talata 5/9/2023 da misalin ƙarfe goma na safe.
[45] A tattaunawar da mai bincike ya yi da Sarkin ginin Kano ya tabbatar da
wannan zance, inda ya ce, shi da kansa da muƙarrabansa su ne suke fasa ƙofar da
Sarkin Kano na yanzu da wanda ya gabace shi suka shiga cikin wannan gidan na
Sarkin Kano Muhammadu Rumfa. Musamman a wannan lokaci da masarautar take
fuskantar barazanar siyasa, inda ake ta sa-toka sa-katsi tsakanin Sarakunan
masarautar guda biyu. Wannan ya biyo bayan sauke Sarki Muhammadu sunusi II da
tsahon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi a shekarar 2019. Sannan aka naɗa
Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano. Da sabuwar gwammati ta zo
wadda ludayinta yake akan dawo, wato lokacin gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, da
take da ra’ayin Muhmmadu Sunusi II, ta Sake sauke Alhaji Aminu Ado Bayero a
shekarar 2024. Wannan sa-toka sa-katsi ya sauya salon sarauta a garin Kano,
inda tsarin sarautar ya ɗauki wani sabon salo. Wato garin Kano ya kasance yana
da sarakuna guda biyu, Muhammadu Sunusi II da yake zaune a gidan Muhammadu
Rumfa. Sai kuma Alhaji Aminu Ado Bayero da yake zaune a gidan sarki na
Nasarawa. A haka dai ake ta gudanar da shari’a a tsakanin su. Sai dai ita
gwamnatin Kano a hukumance tana ganin Sarkin Muhammadu Sunusi shi ne halattacen
Sarki da yake zaune a gidan Muhammadu Rumfa. Yayin da magoya bayan Alhaji Aminu
Ado Bayero suke ganin shi ne halattacen Sarkin Kano. A yanzu dai suna gaban
shari’a, inda kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da Alhaji Aminu Ado a matsayin
halattacen Sarkin Kano. Sai dai su kuma ɓangaren gwamntin Kano da suke goyon bayan
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II sun ƙara ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli. A yanzu
dai a wannan mataki ake, shari’a dai mace ce da ciki ba a san me zata haifa ba.
[46] A Tattaunawa da Ibrahim Hussaini Dawaki ta wayar tarho
ranar Juma’a 14/06/2024 da misalin ƙarfe 11:00 na safe.
[47] Tattaunawa da
malam Balarabe Hassan Ka iya Gini. Ɗaya daga cikin magina da ke zaune a unguwar
Kofar Mazugal a cikin birnin Kano. Ranar laraba 20/09/2023 da misalin ƙarfe
3:00 na rana.
[48] Ƙwafa tana nufi ƙullata, a taƙaice dai wani ya ƙullaci
abokin sana’arsa da nufin zai yi masa wani abu da bai sani ba na sharri ko
mugunta.
[49] A tattaunawar
da mai bincike ya yi da Lawan Gwadabe Sarkin gini a ranar Talata 6/6/2024. a
gidansa da ke Yakasai, a cikin birnin Kano, ya nuna cewa, a dauri wasu da suke
irin wannan asirai suna samun tsohuwar hawainiya da ba ta iya motsi sosai, da
baƙin tufafin makaho, da ruwan sama da aka yi tsawa sosai a yayin saukarsa. Sai
a saka hawainiyar a cikin yankin tufar makahon da aka samu. Daga nan a riƙa
yayyafa wa hawainiyar nan ruwan ana ambatar sunan wanda za a lalata wa aiki.
Bayan an yi haka, sai a ɗauki hawainiyar nan a saka ta a cikin tufafin nan a ɗanke
da baƙin zare, ana ɗinkin ana ambatar sunan wanda ake yi wa asirin. Daga nan
sai a ɗauke ta a tafi ciki daji a samu tsohon itacen gawo ko tsamiya. Ana hawa
kan itacen ana ambatar sunan wanda za a yi wa asirin har a kai inda ake so.
Wato can saman itacen. Sanan a rataye a nan a sakko ƙasa. Daga wannan lokaci
wanda aka yi wa wannan asiri, ba zai ƙara lafiya ba. ko gini ya yi zai
tsattsage har sai ya rushe.
[50] Daidai da ɗure na 60
[51] Tattaunawa da Lawan Gwadabe Sarkin Gini a gidan Sarkin ginin Kano da ke
Unguwar Yakasai a cikin birnin Kano. Ranar Talata 5/9/2023 da misalin ƙarfe
goma na safe.
[52] Daidai da ɗure n 60.
[53] Tattaunawa da
Sarkin Maƙeran Kano Alhaji Usman Muhammad a gidansa dake unguwar Galadanci a
cikin birnin Kano. Ranar 16/08/2023 da misalin ƙarfe 3:30 na yamma.
[54] Daidai
da ɗure na 8.
[55] Sarkin maƙeran
Kano ya halarci yaƙin Biafara, locakin da tsohon shugaban ƙasar Nijeriya
Muhammadu Buhari shi ne Kwamanda mai ba su umarni.
[56] Ya gudanar da
wannan aikin a lokacin da Malam Hassan Suleiman yake managing Director.
[57] A zamanin Kabo
Idris shi ne Managing Director.
[58] Ƙamusun Hausa (2006:316). Ƙamusun
Hausa. Wallafar Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
[59] A wata
tattaunawa da Sarkin Maƙeran Kano ya tabbatar wa da mai bincike wannan, inda ya
ce shi a kan kansa bai san iya ƙoƙofin Kano da ya gyara da hannunsa ba. Ya ƙara
da cewa irin waɗannan ƙofofi yanzu haka suna nan a gidan adana kayan tarihi na
ƙasa dake gidan makama a kusa da fadar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado
Bayero.
[60] Daidai da ɗure
na 8.
[61] Wannan
dalilin ya sanya masarauta Kano ta naɗa Yusuf Maitama Sule a sarautar
Ɗanmasanin Kano.
[62] Kamar ƙera wa
Sarkin Kano linzamin doki da masu da makamantansu. An samu wannan bayani a
tattaunawa da Yusuf Usman, ɗaya daga cikin ‘ya’yan Sarkin Maƙeran Kano a ranar
16/08/2023. A lokon maƙera da ke unguwar Galdanci a cikin birnin Kano, da
misalin ƙarfe 4:00 na yamma.
[63] Tattaunawa da Sarkin maƙeran Kano Alhaji Usman Muhammad a
gidansa dake unguwar Diso a
cikin birnin Kano ranar Alhamis 20/06/2024. Da misalin ƙarfe 12:00 na rana.
[64] Tattaunawa da
Sarkin Maƙeran Kano Alhaji Usman Muhammad a gidansa da ke unguwar Galadanci a
cikin birnin Kano. Ranar 16/08/2023 da misalin 3:30 na yamma.
[65] Yanzu ma an samu cigaba domin an samu wani inji mai amfani da hasken
rana (solar).
[66] A tsarin masarautar Kano, waɗannan sarakuna ba hakimai ba ne masu
gunduma ko gari, su hakimai ne masu Alƙyabba. Ba su da garin da suke jagoranta,
sai dai wani rukunin al’umma musamman masu gudanar da wata keɓantacciyar sana’a
ta gargajiya.
[67] Kamar a irin
taron baje kolin sana’o’in gargajiya da taron ranar Hausa ta duniya da ake
gudanarwa a wasu Jami’o’i da Kwalejin ilimi, musamman a Arewacin Nijeriya.
[68] Harris
(1934:315), ya rawaito cewa kalmar Bangaro ana amfani da ita ne domin
bambancewa tsakani bayin sarki da kuma bayin sauran al’umma waɗanda ba su da
alaƙa da sarauta. Waɗanda ba su da alaƙa da sarauta su ake kira “Runji” ko ”Rundawa”.
[69] A wasu wuraren, ba lallai sai mutumin da yake da alaƙa da
mahauta ba, ana son ya kasance masanin ilimin addini ne.
[70] Tattaunawa da
Sarkin Fawan Kano Alhaji Isiyaku Alin Muli ofishinsa da ke Abbatuwa a cikin
birnin Kano, ranar Laraba 6/9/2023 da misalin ƙarfe 11:30 na safe.
[71] Wato shugaban
maƙeran da suke ƙera kayan ado na mata da sauransu.
[72] Tattaunawa da Malam Abubakar Yunusa
Shugaban cibiyar koyar da sana’o’i ta Aliko Ɗangote da ke da matsuguni a kan
titin Zariya, ranar Litinin 7/04/2025. Da misalin ƙarfe 12:00 na rana.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.