Ticker

6/recent/ticker-posts

Wane Laifi Wahabiyanci/Salafiyya Ya Yi Musu Ne?!

Yau a ko'ina a fadin Duniya an tsangwami Wahabiyanci, abokan husumarsa sun bata masa suna, ta hanyar yada propaganda a kansa, da kirkiran Kungiyoyin Ta'addanci da alakanta su da Wahabiyanci. Alhali da zaran an samu wasu mutane ko wata kungiya sun halasta jinanen al'umma (Musulmai da Kafiran amana), suka dauki makami a kansu to sun fita daga Wahabiyanci. Saboda kowa ya san cewa; babu ta'addanci a cikin Akidar Wahabiyanci.

Don haka babu yadda za a yi a alakanta Kungiyoyin ta'addanci - irinsu al-Qa'ida, ISIS da Boko Haram - ga Wahabiyanci, saboda sun saba jigo da ginshikai na Akidar Wahabiyanci.

Dukkan abokan husumar Wahabiyawa sun san haka, amma da yake Wahabiyancin ne ba sa bukata - saboda ya tsole musu ido - to sai aka rike wannan propaganda, a kullum ake bata ma Wahabiyawa suna.

Shi ya sa wani kalu-bale mai daukar hankali da aka taba jefa ma irin wadannan abokan husuma, aka ce musu: da a ce Wahabiyawa 'yan ta'adda ne, da yanzu duk Duniya ta hargitse, babu sauran zaman lafiya ko na kiftawar ido, a kowane lungu a fadin Duniya.

To, wannan ya sa a kullum ake mamakin irin wannar adawa, ake tambaya a kan sababinta.

To amsa a kan wannar tambaya ita ce

Babu dalilin da ya sa Wahabiyawa suke fiskantar wannar bakar adawa mai tsanani daga sassa daban - daban; Mulhidai, Mabiya Addinai, Shi'a, Sufaye, Boko Akida da sauran karkatattu, kuma suka daura damarar ganin bayansu sai saboda abu daya tak. Wannan abu dayan kuwa shi ne: UMURNI DA KYAKKYAWA, DA HANI GA MUMMUNA.

Wannan shi ne laifin da Wahabiyawa suka yi wa bangarorin da suke adawa da su, saboda a kullum Wahabiyawa suna cewa: A yi Addinin Muslunci kamar yadda yake a cikin Alkur'ani da Hadisi, kamar yadda Musulman farko (Sahabbai da Tabi'ai) suka yi.

Kuma a kullum suna cewa; abu kaza Kafirci ne, wajibi ne a nisance shi. Abu kaza Shirka ne, wajibi ne a guje shi. Abu kaza Bidi'a ne, wajibi ne a kawar da shi. Abu kaza fasikanci ne, wajibi ne a dena. Abu kaza Haramun ne, wajibi ne a tuba, abu kaza Sabo ne, wajibi ne a bar shi.

Kuma a kullum suna cewa; wajibi ne a bi Allah da Manzonsa, a yi aiki da Alkur'ani da Sunna a cikin harkokin rayuwa, a kiyaye Shari'a a cikin dukkan mu'amaloli. Gomnatoci su yi hukunci da Shari'ar Allah, su zartas da horo da ukubobin Shari'a; wanda ya yi ridda a kashe shi, wanda ya yi zina a zane shi ko a jefe shi, wanda ya yi sata a yanke masa hanu, da sauransu. Mata kuma su saka hijabi, su nisanci cakuduwa da maza, kuma su zauna a gidajen mazajensu su yi zaman aure.

Kuma a dena dukkan aiyukan assha da aiyukan sabo da sauran aiyukan badala.

To wannan shi ne laifin da Wahabiyawa suka yi musu. Su Mulhidai me ya sa za a ce musu; su yi Addini? Su kuma Kafirai kar a nuna musu kyama. Su kuma Shi'a da Sufaye kar a ce: su bar Shirka da bidi'o'i da wasu munanan Aqidunsu na kafirci.

Su kuma Boko Akida, kar a ce a yi aiki da Shari'a, kar a ce; a zartas da haddodin Shari'a, kar a ce; a hana rayuwar holewa da masha'a, kar a ce: mata su saka hijabi, kar a ce; su zauna su yi zaman aure.

Shi ya sa a kullum za ka ji suna cewa: a bar kowa ya yi Addininsa yadda ya fahimta, a bar kowa ya yi rayuwarsa yadda yake so, a bar kowa ya aikata abin da ya ga dama.

Alhali Allah Madaukaki ya nuna cewa; al'ummar Annabi (saw) ta samu daukaka ne a kan sauran al'umomi saboda abubuwa guda uku

1- Imani da Allah.

2- Umurni da kyakkyawa.

3- Hani ga mummuna.

Allah ya ce

{كُنْتُمْ خَيْرَ أُمَّةٍ أُخْرِجَتْ لِلنَّاسِ تَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَتَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنْكَرِ وَتُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ} [آل عمران: 110]

Don haka wannan shi ne laifin Wahabiyawa, suna zarginsu da tsattsauran ra'ayi.

To Menene tsattsauran ra'ayin?

Shi ne sun ce; a yi imani da Allah da Manzonsa, a bi Alkur'ani da Sunna. Kuma suna hani a kan gurbatattun Akidu da munanan aiyuka.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
21 June, 2021

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments