ADDININ MUSLUNCI YA DAWO BAƘO KAMAR YADDA YA FARO A BAƘO
Idan ka ce: Ba a cewa: Ku ba ni sadaka don Allah, don Annabi, sai dai a ce: Don Allah shi kadai, saboda Allah ya ce
{وَاتَّقُوا اللَّهَ الَّذِي تَسَاءَلُونَ بِهِ} [النساء: 1]
{Ku ji tsoron Allah wanda kuke tambayan juna da
shi}.
Sai Sufaye su ce ka zagi Annabi (saw).
Idan ka ce: Ba a neman taimakon Annabi (saw) sai
dai a nemi taimakon Allah shi kadai, saboda Allah ya ce
{إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ} [الفاتحة: 5]
{Kai kadai muke bautawa, kuma kai kadai muke neman
taimakonka}.
Sai su ce ka zagi Annabi. Kamar yadda Ibnu
Jamaa'ah ya fada wa Ibnu Taimiyya, don ya fadi haka, ya ce ya munana ladabi ga
Annabi (saw).
Idan ka ce Annabi ya mutu, saboda Allah ya ce
{إِنَّكَ مَيِّتٌ وَإِنَّهُمْ مَيِّتُونَ} [الزمر: 30]
{Lallai kai (Annabi) mai mutuwa ne, kuma lallai su
ma masu mutuwa ne}.
Sai su ce ka zagi Annabi (saw).
Idan ka ce ba a tawassuli da Annabi (saw) saboda
Allah ya ce
{قُلِ ادْعُوا الَّذِينَ زَعَمْتُمْ مِنْ دُونِهِ فَلَا يَمْلِكُونَ
كَشْفَ الضُّرِّ عَنْكُمْ وَلَا تَحْوِيلًا (56) أُولَئِكَ الَّذِينَ يَدْعُونَ يَبْتَغُونَ
إِلَى رَبِّهِمُ الْوَسِيلَةَ أَيُّهُمْ أَقْرَبُ وَيَرْجُونَ رَحْمَتَهُ وَيَخَافُونَ
عَذَابَهُ } [الإسراء: 56، 57]
Ma'ana; su ma wadanda ake roka koma bayan Allah,
cikin bayin Allah (Annabawa da sauran Salihan bayi) su ma a wajen Allah suke
neman kusaci da WASILA, suke fatan rahamarsa, suke tsoron azabarsa.
Sai su ce ka zagi Annabi (saw), kamar yadda suka
yi ma wani mabiyin Ibnu Taimiyya, aka kai masa farmaki, da kyar ya tsira. Allah
ya kiyaye shi.
Idan ka ce kar a nemi ceto a wajen Annabi (saw),
sai a wajen Allah kadai, saboda Allah ya ce
{قُلْ لِلَّهِ الشَّفَاعَةُ جَمِيعًا} [الزمر: 44]
{Ka ce: ceto gaba daya na Allah ne}.
Sai su ce ka zagi Annabi (saw).
Da makamantan haka, cikin hakkokin Allah wadanda
ake kore su daga Annabi (saw) ko waninsa cikin halittu.
A kan haka Sufaye suke hukunta Wahabiyawa Ahlus
Sunna da cewa; su makiya Annabi (saw) ne. Har aka kai ga matakin daure su a
kurkuku, har yanzu aka zo ga daukar matakin kisa, kamar yadda ya faru yau a
Sokoto. An kashe Bawahabiye don ya ce: Ba a cewa: don Annabi a ba ni sadaka.
Abu mai muhimmanci shi ne fadakar da hukuma, dole
ne Hukuma ta dauki mataki a kan wannan, don samun zaman lafiya a cikin al'umma.
Dr.
Aliyu Muh'd Sani (H)
25
June, 2023
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.