GANIN ANNABI A FARKE: HAƘIƘA KO RUƊU?
Lallai ya tabbata cikin Hadisi Mutawatiri cewa; duk wanda ya ga Annabi (saw) a cikin mafarki, yana bacci to lallai shi ɗin ya gani a bisa haƙiƙa, ba wani sheɗani ne ya rikeɗe ya zo a kamanninsa ba.
Babu saɓani a kan
wannan. Saboda abu ne da aka sani bisa dole a Addinin Muslunci.
To amma daga baya an samu wasu Sufaye suna iƙirarin ganin Annabi
(saw) a farke - ba a mafarki ba -, -wai- har suke iƙirarin haɗuwa da shi ido
da ido, har ya ba su wani abu na ilimi ko ibada, na zikirori da wuridai da
salatai.
Ta wannar hanya aka samu Ɗariƙun Sufaye, kamar Ɗariƙar Tijjaniyya, wacce
Shehu Tijjani ya yi iƙirarin ya haɗu da Annabi
(saw) a zahiri, ya gan shi a farke, har ya ba shi Ɗariƙa. Ta haka suka samo "Salatul Fatih".
To Sufaye suna raya cewa; suna da madogara a kan
wannar da'awa tasu, inda suke cewa; hujja a kan haka ita ce Hadisin da Imamul
Bukhari ya ruwaito a cikin Sahihi nasa kamar haka
«من رآني في المنام فسيراني في اليقظة، ولا يتمثل الشيطان بي»
صحيح البخاري (9/ 33)
"Duk wanda ya ganni a cikin mafarki to zai
ganni a farke, saboda Shaiɗan ba ya
kamantuwa da ni".
To da wannan Hadisi Sufaye suka ce lallai ana
ganin Annabi a farke a nan Duniya. Amma sai dai sauran Malaman al'umma gaba ɗaya sun yi watsi da wannar fahimta, saboda dalilai guda
biyu
1- Lafazin Hadisin yana da rikitarwa, saboda
dalilai masu yawa.
2- Kuma ko da ya tabbata Annabi ya faɗi haka, to lallai Hadisin bai Nassanta GANIN ANNABI A
FARKE A DUNIYA BA.
Saboda haka, idan muka ɗauki dalili na farko, wato kasancewar Hadisin yana da
rikitarwa, Malamai sun faɗi haka ne saboda
wasu dalilai
(1) Wannan lafazi (فسيراني في اليقظة) ya saɓa ma sauran lafuzan da suka zo cikin sauran Hadisan.
(2) Abin da Sufaye suke zato daga Hadisin, na
cewa; Hadisin yana nuna za a IYA GANIN ANNABI A NAN DUNIYA, ya saɓa ma wasu dalilai na Shari'a da Hankali da Waƙi'i, da Ƙiyasi da Lura.
To in mun ɗauki dalili na
farko, wato cewa; lafazin (فسيراني في اليقظة) ya saɓa ma sauran lafuzan da suka zo cikin sauran Hadisan, za
mu ga cewa; da ma Malaman sanin illa da kuskuren da ke cikin Hadisi ingantacce
suna da wata ƙa'ida kamar haka
الباب إذا لم تجمع طرقه لم يتبين خطؤه
"Hadisin da ya zo a wata mas'ala, idan ba a
tattara dukkan hanyoyinsa da riwayoyinsa an yi nazarinsu ba to kuskuren da ke
cikinsa ba zai bayyana ba".
Manyan Malaman Hadisi ne suka gindaya wannar ƙa'ida, kamar su Imam
Aliyu bn al-Madeeniy inda ya ce
«الباب إذا لم تجمع طرقه لم يتبين خطؤه»
الجامع لأخلاق الراوي للخطيب البغدادي (2/
212)
Imam Ibnu al-Mubarak ya ce
«إذا أردت أن يصح لك الحديث فاضرب بعضه ببعض»
الجامع لأخلاق الراوي للخطيب البغدادي (2/
295)
Imam Ahmad ya ce
«الحديث إذا لم تجمع طرقه لم تفهمه والحديث يفسر بعضه بعضا»
الجامع لأخلاق الراوي للخطيب البغدادي (2/
212)
Imam Ibnu Ma'een ya ce
«لو لم نكتب الحديث من ثلاثين وجها ما عقلناه»
الجامع لأخلاق الراوي للخطيب البغدادي (2/ 212) المجروحين لابن
حبان ت حمدي (1/ 35)
Saboda haka wannar ƙa'ida ce a wajen Malaman Hadisi, dole a tattara
dukkan hanyoyi da lafuzan Hadisi don a tantance dadai daga kuskurensa.
Dan haka ya kamata mu yi nazarin hanyoyin Hadisan
da lafuzansu, don gano inda kuskure da matsalar da aka samu a wannan Hadisi
suke.
To, shi dai wannan Hadisi na ganin Annabi (saw) a
mafarki Sahabbai goma sha biyu (12) ne suka ruwaito shi ko fiye da haka. Su ne
Abu Huraira, Abu Ƙatada, Anas, Jabir, Ibnu Mas'ud, Abu Sa'eed al-Khudriy, Abu Juhaifa, Ibnu
Abbas, Ɗariƙ, Aliyu bn Abi Ɗalib, Abu Bakrah, da Abdullahi bn Amr (ra). Amma
duk cikinsu babu wanda aka ruwaito ganin Annabi (saw) a farke (wato lafazin
"فسيراني في اليقظة") daga gare shi sai Abu
Hurarah shi kaɗai. Ma'ana; wannar
riwayar da aka yi daga gare shi ta saɓa ma ta sauran
Sahabbai (11).
To shi Hadisin Abu Huraira, Bukhari ya ruwaito shi
a wurare guda uku (3), Muslim a wuri ɗaya, haka Abu
Dawud, Tirmiziy, Ibnu Majah da Imamu Ahmad a wurare 10 ko fiye da haka.
To duk da cewa; inda aka ruwaito waɗannan Hadisan a cikin littatafan Hadisi ya kai wuri (44)
ko fiye, amma duk da haka a wuri ɗaya ne kaɗai daga wurare uku (3) Bukhari ya ruwaito Hadisin daga
Abu Huraira da lafazin "فسيراني في اليقظة" a
yanke ba shakka.
Amma ga yadda sauran suka zo kamar haka
(فقد رآني)، (فقد رآى الحق)، (فكأنما رآني في اليقظة)، (فسيراني في
اليقظة أو فكأنما رآني في اليقظة).
To a nan sai mu lura da abubuwa kamar haka
(1) Bukhari ya ruwaito Hadisin mafarkin a wurare
shida (6), daga ciki ya ruwaito Hadisin Abu Huraira (ra) a wurare uku (3), amma
daga ciki wuri ɗaya ne tak ya zo
da lafazin (فسيراني في اليقظة).
(2) Muslim, Abu Dawud da Ahmad sun ruwaito Hadisin
Abu Hurairan (ra), da irin Isnadin Bukhari, amma da lafazin shakka, kamar haka
(فسيراني في اليقظة أو لكأنما رآني في اليقظة).
(3) Ibnu Hajar ya ambaci cewa; a wajen Isma'iliy -
(المستخرج على صحيح البخاري للإسماعيلي) -
yadda lafazin yake shi ne: (فقد رآني في اليقظة) a
maimakon faɗinsa (فسيراني). Inda ya ce
"ووقع عند الإسماعيلي في الطريق المذكورة "فقد رآني في اليقظة"
بدل قوله: "فسيراني".
فتح الباري لابن حجر (12/ 383)
TO WANNAN SHI YA NUNA CEWA; WANNAN LAFAZI KUSKURE
NE, BA SHI NE LAFAZI NA DADAI A HADISIN BA, HAR MA MALAMAI SUKA YI ISHARA GA
CEWA; LAFAZI NE "SHAZZI" BA "MAHFUZI" BA.
Ibnu Hajar ya naƙalto daga al-Maziriy ya ce
وقال المازري: إن كان المحفوظ فكأنما رآني في اليقظة فمعناه
ظاهر
فتح الباري لابن حجر (12/ 385)
In ka ji ana maganar "Mahfuz" to
kishiyarsa shi ne "Shazzi", wanda ya saɓa ma sauran riwayoyi na Hadisin.
Kuma shi ne abin da Ibnu Hajar ɗin ya ambata cewa
"وشذ بعض الصالحين فزعم أنها تقع بعيني الرأس حقيقة"
فتح الباري لابن حجر (12/ 384)
Saboda haka a bisa haƙika wannan lafazi da ya zo a Hadisin Abu Huraira
(ra) ya saɓa ma sauran lafuza na
riwayoyin Hadisin nasa, kuma ya saɓa ma Hadisan
sauran Sahabbai. Saboda haka riwaya ce ta kuskure. Ba za a kafa hujja da ita
ba.
2- Dalili na biyu; ko da a ce wannan lafazi na (فسيراني في اليقظة) ba kuskure ba ne, to a bisa haƙiƙa ba NASSI ba ne a kan GANIN ANNABI A NAN DUNIYA.
A cikin Hadisin babu inda aka bayyana cewa; ganin nasa a nan Duniya zai
kasance. Don haka "ihtimali" zai shiga cikinsa. Wannan ya sa wasu
Malaman suka fassara lafazin da cewa a Lahira ake nufi.
Imamu Nawawiy ya ce
"وإن كان "سيراني في اليقظة" ففيه أقوال
أحدها المراد به أهل عصره ومعناه أن من رآه في النوم ولم يكن
هاجر يوفقه الله تعالى للهجرة ورؤيته صلى الله عليه وسلم في اليقظة عيانا
والثاني معناه أنه يرى تصديق تلك الرؤيا في اليقظة في الدار
الآخرة لأنه يراه في الآخرة جميع أمته من رآه في الدنيا ومن لم يره
والثالث يراه في الآخرة رؤية خاصته في القرب منه وحصول شفاعته".
شرح النووي على مسلم (15/ 26)
Saboda haka ko da an sallama cewa; lafazin (فسيراني في اليقظة) "Mahfuzi" ne ba
"Shazzi" ba, ma'ana; ya tabbata daga Annabi (saw), TO BA NASSI BA NE
A KAN HAƊUWA DA ANNABI DA GANINSA
A NAN DUNIYA, shi ya sa Malamai suka yi tawilinsa, saboda an samu dalilai masu
yawa da suka tabbatar da cewa; Annabi (saw) ba zai dawo wannar Duniya a irin
wannar rayuwa ba, balle har a ce ya haɗu da wani mutum,
har a yi ƙaryar an karɓi wani abu na Addini daga gare shi.
3- Daga cikin abubuwa da suke bayyana cewa; wannar
ma'ana da Sufaye suka riƙe kuskure ce, ai ya tabbata mutane da yawa sun yi mafarkin Annabi (saw),
amma kuma daga baya ba su zo sun ce sun gan shi a farke ba. Alhali - a bisa
fahimtar Sufayen - in dai mutum ya yi mafarkin Annabi (saw) to dole sai ya gan
shi a farke ido da ido, saboda Annabi (saw) in ya faɗi abu dole sai ya faru. Ibnu Hajar ya ce
"إن جمعا جما رأوه في المنام
ثم لم يذكر واحد منهم أنه رآه في اليقظة وخبر الصادق لا يتخلف".
فتح الباري لابن حجر (12/ 385)
4- Kuma hatta cikin Sahabbai sun yi mafarkin
Annabi (saw), amma ba a ruwaito da Isnadi ingantacce, cewa; wani cikin Sahabban
ya gan shi a farke ko ya haɗu da shi ba. Duk
da tsananin buƙata zuwa ga haɗuwa da shi ɗin, don warware
matsaloli da saɓani da suka yi
ta afkuwa a zamaninsu, amma ba a taɓa jin wani
Sahabi ya ce: ya ga Annabi a farke har ya ba da mafita ko ya warware wani saɓani da suka yi ba, wanda har yaƙe - yaƙe sun yi a tsakaninsu.
Saboda haka a bisa haƙiƙa LAFAZIN (فسيراني في اليقظة) KUSKURE NE, YA SAƁA MA SAURAN HADISAN. Da
ma kuma ƙa'idar Malaman Hadisi -
kamar yadda ya gabata daga Ibnul Madeeniy - ita ce
«الباب إذا لم تجمع طرقه لم يتبين خطؤه»
الجامع لأخلاق الراوي للخطيب البغدادي (2/
212)
Sai ka tara riwayoyin Hadisin, sannan sashe ya
fassara sashensa, kamar yadda ya gabata daga Imamu Ahmad
«الحديث إذا لم تجمع طرقه لم تفهمه، والحديث يفسر بعضه بعضا»
الجامع لأخلاق الراوي للخطيب البغدادي (2/
212)
Saboda haka, a ƙarshe, kar ku yi mamaki don Ƴan Ɗariƙu sun yi jayayya, sun ja
sun kafe a kan wannan lamari, saboda idan suka sallama ba a ganin Annabi a
farke, to dole su yarda cewa; Shehu Tijjaniy maƙaryaci ne, ya musu ƙarya ya ce: -wai- ya haɗu da Annabi (saw), har ya ba shi Ɗariƙa, wani kuma aka ba shi "Salatul Fatih". Ka ga girma ya faɗi kenan, ka ga daga nan duka Ɗariƙar ta rushe A to Z, gayya ta watse.
Dr.
Aliyu Muh'd Sani (H)
19
June, 2020
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.