𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamualaikum warahmatullah wabarakatu malam barka da dare fatan an yi Sallah lafiya ameen. Mlm nayi Aure kafin fara Azumin ramadan to mun kasance ni da mijina da Rana sai ya rika nema na da Jima'i ni kuma bana hana mun haka har sau 3 ba mu san cewa ba a yin Jima'i da Mace da rana a cikin watan Azumi ba sai yanzu muke ji shi ne muke tambaya ya hukuncin Azumin mu yake? kuma mun tambayi wasu sun ce tunda ba mu sani ba ai shike nan babu komai a kan mu. Ndg a huta gajiya.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salaam wa
rahmatullahi wa Barkatuhu
Inna lillahi Wa inna
Ilaihi Rajee'un, babu wani hujja a cikin maganar ki ko madafa, wannan wacce
irin rayuwa ce kina Musulma iyayen ki Musulmai ne, wadda zai ya Aure ki Shima
Musulmi iyayen sa Musulmai ne, sa'annan kun girma a cikin Anguwa da gari na Musulunci,
shekarun ku har suka kai Balaga, har ma aka Kai ga son yin Aure yanzu Kun yi
Auren, wai ku zo da maganar cewa ai ba ku san cewa Allah ya haramta yin Jima'i
da Rana a cikin watan Azumi ba, ke nan ba ku san hukuncin mutum ya Sha Ruwa ko
ya ci Abinci da Rana alhalin yana Azumin watan Ramadan ba, ke nan halal ne
shima a ci a Sha da Rana a cikin Azumin, indai ba ku san hukuncin yin Jima'i da
Rana Haramun ba ne, haka idan mutum ya sha Ruwa ko ya ci Abinci ma ke nan ba ku
san cewa Haramun ba ne.
Wannan son zuciya ce
bawai ba ku sani ba dukkan ku kun sani, babu wadda za su kai munzalin yin Aure
ace ba su san wannan hukuncin ba, idan ma Kun ce ba ku sani ba, toh kamata yayi
ayi gaggawar Raba Auren ku yanzun nan wallahi domin ba ku cancanci zama Ma'aurata
ba.
Sabida haka babu wani
cewa babu komai a kanku, dole ne kuyi Kaffara Azumi 61 da sau 3, ko Kuma ku
ciyar da Mabukata 60 Sau 3, ko kuma ku tufatar da Mabukata 60 Sau 3, sa'annan
ku Rama Azumi 3 wadda kuka yi Jima'in ku da Rana gurin Saɓawa Allah, duniya ina za ki kaimu Jima'i da Rana a cikin
watan Azumi? Ba ki son wani ya Saɓa miki amma kina
Saɓawa Allah kuma ko a jikin ki haba Jama'a.
Sa'annan ki sani cewa
duk wadda ya Karya Azumin sa da ganganci yana sane da hukuncin Allah da Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya take sanin sa ya aikata abun da yake so,
toh ga abun da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce, Annabi Muhammad Mai
Tsira Da Amincin Allah Su Tabbata Agare Shi, (( Duk Wanda Ya Karya Azumin Rana ɗaya daga Cikin Ramadan, Ba a AKan Wani Rangwame da Allah
Yayi Masa ba, toh ko Azumin Zamani gaba ɗaya, ba Zai iya
Rama Masa Wannan Azumin nasa guda Ɗayan Nan ba. Duba Cikin Dawud))
Mutum Yayi Asara Babba
Wallahi, lokacin da ba ku da Auren Zina kuke yi ne? Wata 1 tak nan ma a Yini ne
aka ce kada kuyi, da dare ko kwana zai yi a kanki yayi mana amma a rufe ido
dole sai an Saɓawa Allah tukuna, Azabar
Allah Ya Tabbata ga Wanda Ya Karya Azumin sa da Gangan, Azaba mai Girma. An Karɓo Hadisi Daga Abu Umaimata Al-Bahili Allah Ya Kara Yarda
Gare Shi, Ya ce Na Ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasalam Yana Cewa, Ina
Cikin Barci, Sai Wasu Mutane Ɓiyu 2 Suka Zo Min, Sannan Suka Tafi da Ni, Sai Kawai Na ga Wasu Mutane An
Rataye Su ta Agarar Su, Muqamuqansu a Tsatsassage, Jini Yana ta Ƙwarara. Sai Ya ce, na ce
Shin Su Wanene Waɗannan? Sai Ya ce,
Waɗannan Waɗanda Suke Karya
Azumin Su ne Tun Gabanin Lokacin Shan Ruwa Yayi)) Duba Cikin (Ibn Hibban). Kin
je kina bayar da Jikin ki ga Mijin ki yana Jima'i da ke akwai abun da yake
Jiran ku.
Dole ne akwai Kaffara a
kanku tare da rama Azumin nan, ko da jahilci ne ya karya azumin, toh sai ya
rama saboda hadisin Annabi sallallahu alaihi wa sallama da ya ce, sun kashe
shi, sai ya ce me ya hana su tambaya tunda da ba su sani ba.
4362 - 1515 -
"قتلوه قتلهم الله ألا سألوا إذا لم يعلموا فإنما شفاء العي السؤال؟
إنما كان يكفيه أن يتيمم.... ... ".
(صحيح) [د] عن جابر. الإرواء 105، صحيح أبي داود 363.
Allahu Subhanahu
Wata'ala yana cewa;
أُحِلَّ لَكُمْ لَيْلَةَ الصِّيَامِ الرَّفَثُ إِلَىٰ نِسَائِكُمْ
ۚ هُنَّ لِبَاسٌ لَكُمْ وَأَنْتُمْ لِبَاسٌ لَهُنَّ ۗ
An halatta a gare ku, a
daren azumi, yin jima´i zuwa ga matan ku, sũ tufa ne a gare ku, kuma kũ tufa ne
a gare su, Allah Yã sani lalle ne ku kun kasance kuna yaudarar kanku.
Idan Kun ce wai ba ku
sani ba shin meyasa ba kuyi tambaya ga tun kafin kuyi Auren ku? Allah ya san
abun da yake cikin zuciyar ku tun kafin ku aikata don haka ku Dena Yaudarar
kanku, da fakewa akan cewa wai ba ku sani ba shi ne wani Karin laifi ne.
Ina Kara Jan Hankalin
Matasa da Yan Mata waɗanda suke yin
Aure kafin Azumi, suna ɗaukar Azumi a
cikin Ramadan da rana su je suna ta yin jima'in su ko a jikin su, sun biyewa
son zuciyar su da more rayuwar su suna ta Saɓawa Allah suna Jima'i da Rana a cikin watan Azumin da
Allah da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam suka ce Haramun ne Namiji ya
sadu da Matar sa da Rana alhalin suna Azumi.
Hakanan kafin ayi Sallar
Layya wallahi akwai Mata ta ce min wai wata ne ta zo gidan tana tambayar ta,
wai sun yi Aure kafin Ramadan ɗin nan da ya
wuce, toh Mijin ta kullum da Rana sai ya neme ta sun yi Jima'i da Rana a cikin
Ramadan ɗin nan, Yarinyar ta ce sun yi ta yin Jima'i da Rana
wallahi ba zata iya tuna Yawan kwanakin ba ma, wai take cewa Mijin bai san cewa
Haramun ne ayi Jima'i da Mace a cikin Azumi da Rana ba, itama Yarinyar wai bata
San wannan hukuncin sa ba sai a kwanan nan ne ta sani, ta ce ai yanzu Hankalin
su ya tashi. Shi ne matar ta ke ce mata ita ma ba ta sani ba amma zatayi musu
tambaya. Sa'annan wai ai sun yi tambaya an gaya musu cewa ai tunda sun yi sa
abisa Kuskure ne sai dai su kiyaye gaba ai Allah Bai kama Bawan sa da laifin da
Bai sani ba Fatawar da aka ba su kenen. Ban sani ba ma kene?
Farko abun da na ce ma
wannan Matar, na ce mata karya suke yi sun san wannan hukuncin, kawai dai sun
biyewa son zuciyar su ne suna Saɓawa da yake yin
ibada bai dame su ba, na ce babu Namiji ko Macen da suka kai munzalin yin Aure
ace wai ba su san cewa yin Jima'i da Rana Haramun ba ne, karya suke yi, na ce idan
kuma da gaske ba su sani ba, toh kin ga ke nan ba su cancanci zama Ma'aurata ba
dole ne a raba Auren su.
Nace mata amma bari zan
yi tambaya nima akai, na tambayi Malaman mu guda 2, na farkon abun da ya ce
min, ya ce Arna ne suka Musulunta? na ce wlh Musulmai ne dukkan su, ya ce min
toh karya suke yi sun sani, kawai su yi lissafin kwanakin da suka yi suna yin
Jima'i da Rana a cikin Ramadan su yi kaffarar Azumin su, ko Kuma su ciyar da
Miskanai 60 sau adadin kwanakin da suka suna yi Jima'in da Rana, ko kuma su Ɗinkawa Mabukata 60 sau
adadin kwanakin Jima'in da suka yi da Rana a cikin ramadan, sa'annan su rama
wannan Azumin da suka yi Jima'in da Rana a cikin Ramadan din. Na sake yin
magana da Malami na biyu shi ma abun da ya ce ke nan, sai na ce ma wannan matar
ta haɗa ni da ita Yarinyar domin nayi mata Nasiha na fahimtar
da ita, Matar ta haɗa ni da ita
Yarinyar, na ce ta bani numbern Mijin ta muyi magana, budan Bakin ta wai idan
Mijin ta ya sani ai zai yi mata Faɗa, zai yi Surutu
za a su samu matsala, Yarinyar Nan kamar wasa, ta ce sai dai a bar maganar
indai sai ta bayar da numbern Mijin ta ne, Nasihar da ban yi ba ke nan na bar
ta, tayi shiru ma ta ki ta ce komai don an ce ta bayar da numbern Mijin ta ayi
musu Nasiha a tunatar da shi a gaya masa gaskiya.
Matasa da Yan Mata wadda
suka yi Sabon Aure, suna yin wannan Kuskuren sosai wallahi a cikin Azumi kuma
sun sani, suna kafewa da karya, alhalin wallahi duk karyar ka, Allah ya riga da
ya san menene a Zuciyar ka, tun kafin kayi Jima'i da ita, Allah ya San komai a
cikin zuciyar ka, idan kayi karyar cewa ai ba ka sani ba, toh Allah ya riga da
ya San komai tun kafin ka aikata abun da kake so.
Sa'annan wai Mace ban da
Jahilci da rashin tunani, da yake ita Yarinyar ma ibada ko Addini bai dame ta
ba, wai akan kiyiwa Mijin ki magana ku gyara Kuskuren ku, a San me za a yi a ba
ku shawara a gaya muku abun da yakamata kuyi, akan kiyi hakan Mijin ya gyara
wai gara an yi shiru an bar sa domin kada ya miki Faɗa da surutu kada ki samu matsala da shi, abu ne fa da ya
Kai ma a raba Auren ku da shi dalilin Saɓawa Allah da
yayi da ke a cikin Azumin Ramadan, amma wai gara a bar maganar a je da Zunuban
a haka wani Ramadan ɗin ma ya sake
zuwa a ci gaba da yin Jima'in da rana, ai Allah baya kama Bawan sa akan abun da
bai sani ba. Wallahi kin yi asara kin yi Kuskure sosai mafi girman Kuskure,
shiyasa fa idan Allah ya tashi kama Ma'aurata ake samun matsaloli sosai, wadda
ke ba ki taɓa tsammanin haka zai
faru da ke da mijin ki ba sai ga shi yanzu komai ma suna faruwa babu Jin daɗi kwanciyar hankali tsakanin ki da mijin ki.
Dalilin shi ne irin
yadda kuke sabawa ke kin yarda gara kada a gayawa Mijin ki gaskiya, don idan an
gaya masa kanki zai koma, gara ayi shiru a bar sa ya ci gaba da sabawa, kema
yayi ta je fa ki Cikin Sabon Allah gara hakan akan wai ayi masa magana, toh Yau
ko SAKIN ki zai yi idan an gaya masa gaskiya, ai yakamata ace kin gaya masa, ko
kuma ki sa a gaya masa, idan an gaya masa in ya so ya SAKE ki mana, da ki zauna
zaman Aure da irin wannan Namijin wallahi gara Auren ya mutu. Allah ya San kin
fita kin yi kokari gurin gaya masa gaskiya, amma wai gara ya Sabawa Allah din
akan ya miki Faɗa ko yayi fushi
da ke.
Yan Mata da wasu mãtan
Aure da Mazãjen da suke aikatawa irin wannan, wallahi ku ji tsoron Allah, Shi
Allah ya san komai a cikin zuciyar sa Bayin sa tun kafin kiyi niyyar aikata
wannan abun babu abun da yake Ɓoye masa, don haka idan ma Kun yi karya cewa Kuskure ne ai ba ku sani ba,
toh shi Allah babu abun da yake Ɓoye masa, wallahi kuyi gaggawar yin Kaffarar Azumin ku tun kafin lokaci ya
kure muku, ko a ciyar da mutane 60 Sau adadin kwanakin da kuka dauka kuna yin
Jima'in ku da rana a cikin Ramadan, ko kuma ayi Kaffarar Azumi 61 Sau adadin
kwanakin Jima'in da kuka yi a cikin Ramadan din, ko ciyar da mabukata 60 sau
adadin kwanakin Jima'in da kuka yi da Rana a cikin ramadan, sa'annan a biya
wannan Azumin da aka yi Jima'in da Rana. Kuma a nema Gafarar Allah sosai babu
dare babu Rana idan an ce a'a toh Allah na Jiran kowa wallahi.
Son zuciya ido da ido a
fake da karya, ko zamani guda zakuyi kina rama Azumi 1 tak da kika karya da
ganganci bai isa ya biya guda ɗayan Nan ba, Toh
Ina ga kuma ace kullum sai Kun yi Jima'i da Rana a cikin Ramadan kuna sane da
cewa Haramun ne amma kuka take sanin ku, laifin yayi muni wallahi abun bakin
ciki abun takaici ne, ai kamata yayi a raba wannan Auren wallahi indai kin San
me kike yi a rayuwar ki da Addinin ki. Allah ya shirya. ku ji tsoron Allah Yan
Uwana masu Saɓawa Allah kowa zai mutu.
Wallahu A'alamu.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.