Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Jinin Dake Fita Bayan Bari (Miscarriage)

HUKUNCIN JININ DAKE FITA BAYAN ƁARI (MISCARRIAGE)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Allah ya karawa malam lafiya. Tambaya: Idan mace tana zubar ciki za ta iya yin ibadarta kamar sallah Azumi Jima'i da sauransu ko kuwa sai bayan adadin wasu kwanaki?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Ya danganta ne da yanayin abinda ta ɓarar ɗin. Misali idan abinda ta ɓarar ɗin ya fito da cikakkiyar siffar ɗan Adam, to wannan jinin da ya biyo bayan ɓarin nan za a ɗaukeshi ne amatsayin jinin haihuwa. Ba zatayi sallah ko azumi ba sai bayan Ɗaukewarsa. Mutukar dai bai haura kwanaki arba'in ko sittin ba (awani kaulin).

Amma idan abinda ta ɓarar ya fito ne kaɗai bisa siffar gudaji-gudajin jini, ko tsokoki ne kawai, ko kuma zallar jini, ko wata tsoka guda amma ba bisa siffar ɗan Adam ba, to wannan jinin za ta ɗaukeshi ne amatsayin jini rashin lafiya (istihadha). Kuma ba zai hanata yin sallah ko azumi ko zuwa shimfidar mijinta ba.

Sai dai za ta rika sabunta tsarkin jini da tufafi da sake yin alwala kafin kowacce sallar farilla. Kuma za ta iya haɗa sallar azahar da laasar tayisu lokaci guda. Hakanan magriba da isha'i.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments