Abu ne sananne babu abin da ya raba 'Yan Bidi'a da Ahlus Sunna sai neman ilimin Hadisan Manzon Allah (saw) da gaskata su da aiki da su da binsu sau da kafa. Wannan ya sa 'Yan Bidi'a tun zamanin da, har zuwa yau, hadi da makiya Addinin Muslunci cikin "Mustashriqoun" (Orientalists) da yaransu 'Yan Boko Aqida a kullum suke yakar Hadisan Annabi (saw), musamman littafin da ya fi kowanne inganci a cikinsu, wato Littafin "Sahihul Bukhari", na Imam Abu Abdillah, Muhammad bn Isma'il Al-Bukhariy.
Imamul Bukhariy babban Malamin Hadisi ne, har ya
kai kololuwar daraja a ilimin Hadisi, inda ya cancanci lakabin "Amirul
Muminina fil Hadeeth".
To kasancewar Sunna ita ce ruhin Muslunci da
bayanin Alkur'ani, shi ya sa 'Yan Boko Aqida a kullum sara da sassakansu ya
kare a kan "Sahihul Bukhariy", saboda in sun yi nasara sun cire
kwarjininsa a zukatan Musulmai to shi kenan sun ci nasarar yakar Muslunci a
zukatar Musulmai, wannan ya sa a kullum ba sa gajiya da sukar wannan babban
littafin da har yau babu kamarsa cikin littatafan da bil'adama suka wallafa.
Imamul Bukhari ba karamar tafiya ya yi wajen neman
ilimin Hadisin Annabi (saw) ba. Ya shafe tsawon 13900 KL a tafiya irin ta
wancan lokaci, zamanin tafiya a kan doki da jaki da rakuma.
Duk garin da ya je sai ya zauna a garin, ya hadu
da Malaman Hadisi da suke garin, ya dauki Hadisi a wajensu, ya rubuta ya
haddace, kuma ya yi "Muzakara" (bita) tare da daliban Hadisi a garin,
har ya yi wallafe-wallafe a wasu garuruwan, kamar yadda ya wallafa
"Al-Tarikhul Kabeer" a birnin Madina.
Da farko ya taso daga garinsu Bukhara (birni da ke
kasar Uzbekistan a yanzu) ya tafi garin Balkh (garin da ke cikin kasar
Afghanistan a yanzu) tafiyar tsawon 599 KL.
Daga Balkh kuma ya wuce Merv (birni da ke kasar
Turkmenistan a yanzu) tafiyar tsawon 792 KL.
Daga Merv kuma ya wuce Nishapur (birni da ke kasar
Iran a yanzu) tafiyar tsawon 136 KL.
Daga Nishapur kuma ya wuce Rey (birni da ke kasar
Iran a yanzu) tafiyar tsawon 757 KL.
Daga Rey kuma ya wuce Wasit (gari da ke kasar Iraq
a yanzu) tafiyar tsawon 984 KL.
Daga Wasit kuma ya wuce Basra (birni da ke kasar
Iraq a yanzu) tafiyar tsawon 364 KL.
Daga Basra kuma ya wuce Kufa (gari da ke kasar
Iraq a yanzu) tafiyar tsawon 396 KL.
Daga Kufa kuma ya wuce Baghdad (babban birnin
kasar Iraq a yanzu) tafiyar tsawon 164 KL.
Daga birnin Baghdad kuma ya wuce Medina (birnin
Manzon Allah (saw) da yake kasar Saudi Arabia a yanzu) tafiyar tsawon 1524 KL.
Daga birnin Medina kuma ya wuce Mecca (birni mai
alfarma da yake kasar Saudi Arabia a yanzu) tafiyar tsawon 432 KL.
Daga birnin Mecca kuma ya wuce Jeddah (birni da
yake kasar Saudi Arabia a yanzu) tafiyar tsawon 70 KL.
Daga Jeddah kuma ya wuce ‘Aydhab (ruwa ya mamaye
garin, yana tsakanin mallakar Egypt da Sudan) tafiyar tsawon kusan 130 KL.
Daga ‘Aydhab kuma ya wuce Fustat (gari da yake
kasar Egypt a yanzu) tafiyar tsawon 1073 KL.
Daga Fustat kuma ya wuce Ashkelon (gari da yake
kasar Israel a yanzu) tafiyar tsawon kusan 500 KL.
Daga Ashkelon kuma ya wuce Caesarea (gari da yake
kasar Israel a yanzu) tafiyar tsawon 118 KL.
Daga Caesarea kuma ya wuce Damascus (babban birnin
kasar Syria a yanzu) tafiyar tsawon kusan 400 KL.
Daga garin Damascus kuma ya koma Baghdad tafiyar
tsawon 913 KL.
Daga Baghdad kuma sai ya kama hanyar da ya tafo
har ya koma gida Bukhara.
Saboda haka wannan shi ne tafiye - tafiye da
wannan bawon Allah ya yi don neman ilimin Hadisin Annabi (saw), ta hanyar
rubutawa da haddacewa, da kuma tace ingantattu daga wadanda ba su inganta ba,
har ya tara mana ingantattun ya wallafa mana "Al-Sahihul Jami'u",
littafin da ya zama bakin ciki ga 'Yan Bidi'a da makiya Addinin Muslunci, cikin
"Mustashriqoun" (Orientalists) da yaransu 'Yan Boko Aqida.
Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
24 May, 2019

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.