Ticker

6/recent/ticker-posts

Wa Ya Fara Haramta Azumin Nafila a Ranar Asabat?

Wasu cikin Manazarta suka ce: ba su san wanda ya fara haramta Azumin Nafila a ranar Asabat ba kafin Shaikh Muhammad Nasiruddeen al-Albaniy. Shi Shaikh Albaniy ya dogara ne a kan Hadisin Abdullahi bn Busr (ra), daga ‘yar’uwarsa al-Samma’u (ra). Alhali Hadisi ne da manyan Malaman Hadisi suka illata shi.

- Imamu Zuhriy yana sukarsa.

- Imamu Malik ya ce: Hadisin karya ne.

- Yahya al-Qattan yana kaffa-kaffa da shi.

- Abu Dawud ya ce: an soke Hadisin (Mansukhi).

- Imamu al-Nasa’iy ya ce: Hadisi ne birkitacce.

- Ibnu Taimiyya ya ce: Hadisi ne “Shazzi”.

- Haka Ibnul Qayyim ma ya fada.

- Ibnu Hajar ma ya ce: Hadisi ne birkitacce.

To ka ga idan aka dauki maganar Malaman da suka raunana Hadisin, to dole a jefar da shi. In kuma aka lura da maganar wadanda suka kyautata Isnadinsa, to Hadisi ne “Shazzi”, ya saba wa Hadisai Mutawatirai.

Almajirin Imam Ahmad, Abubakar al-Athram ya ambaci Hadisin sai ya ce

"فجاء هذا الحديث بما خالف الأحاديث كلها".

ناسخ الحديث ومنسوخه للأثرم (ص: 201)

Sai wannan Hadisin ya zo da abin da ya saba wa dukkan Hadisai”.

Sai kuma ya ambaci Hadisan da ya saba musu, daga ciki

- Hadisin Azumin watan al-Muharram gaba dayansa. Alhali akwai ranakun Asabat fiye da daya a cikin watan.

- Haka Hadisin Azumtar watan Sha’aban.

- Hadisin Sittu Shawwal.

- Hadisin Ashura.

- Hadisin Arafah.

- Hadisin Azumi na tsakiyan kowane wata.

Duka wadannan Azumi dole ana samu suna dacewa da ranar Asabat.

A takaice, Haramta Azumin Nafila a ranar Asabat ya saba wa Ijma’i, kamar yadda Shaikhul Islam ya ce

"إن ظاهر الحديث خلاف الإجماع".

شرح العمدة لابن تيمية (2/ 653)

Saboda haka asali ra’ayoyi biyu ake da shi a mas’alar; ra’ayin Jumhur na karhanta ware ranar Asabat ita kadai da yin Azumin Nafila, in ba ranakun falala ba.

Da kuma ra’ayin su Imamu Malik da Ibnu Taimiyya na halasci a sake ba kaidi.

Alhali a ka’ida; idan aka yi sabani zuwa ra’ayoyi biyu a kan mas’ala, to bai kamata daga baya a kirkiri ra’ayi na uku ba.

Don haka babu abin da ya hana azumtar ranar Arafa a ranar Asabat, ita kadai ba tare da an hada ta da wata rana ba.

Saboda haka kar ka yarda wani ya hana ka yin Azumin ranar Arafah, idan ta zo a ranar Asabat, ra’ayin haramtawan ya saba Ijma’i.

~ Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

 11 June, 2024

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments