Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Masu Haramta Azumin Ashura A Ranar Asabat Suna Da Hujja?

A bara mun tattauna sosai a kan ra'ayin haramta yin Azumin Nafila a ranar Asabat, tare da dalilai mun tabbatar da cewa; ƙauli ne ƙirƙirarre, bayan magabata sun yi saɓani zuwa ƙauli biyu, wato karhanci da halasci. Sai ya zama Ijma'i a kan haka.

Hujjar masu ra'ayin haramta Azumin wani Hadisi ne "shazzi". Kai, har wasu Malaman ma sun ƙaryata shi.

Bayan nan suna da wata shubuha, cewa; an hakaito daga wasu Tabi'ai, cewa: sun karhanta.

Don haka -wai- karhantawa a yaren magabata shi ne haramtawa.

To amma sai dai, shi Imam al-Ɗahawiy da ya hakaito karhancin daga gare su, bai naƙalto mana ainihin lafuzansu ba, shi dai kawai cewa ya yi: "فكرهوا".

Don haka wannan lafazi daga gare shi ne, ibararsa ce ba tasu ba.

To abin da za a yi a nan shi ne, sai a koma a ga: idan Imam al-Ɗahawiy ya ambaci "karhanci" me yake nufi?

Shin karhanci ne na haramci, ko karhanci ne na makruhi, wanda bai kai haramci ba?

Ni dai da na bibiyi wuraren da al-Ɗahawiy ya yi amfani da lafazin "karhanci", sai na samu cewa: idan ya ce: "Makruhi, ko an karhanta", ba karhanci na haramtawa yake nufi ba. Makruhi ƙanin haramun, kishiyar mustahabbi yake nufi. Wato "كراهة تنزيه".

Saboda haka maganar haramta Azumin Nafila a ranar Asabat ra'ayi ne ƙirƙirarre, ya zo ne bayan Salaf sun yi saɓani zuwa ƙauli biyu. A bisa ƙa'ida ya zama sun yi Ijma'i a kan waɗannan ƙauli biyun, ƙirƙiran ƙauli na uku keta Ijma'i ne, bai halasta ba.

Saboda haka gobe Asabat kowa ya yi Azuminsa na ranar Ashura, masu haramtawa ba su da hujja. Shubuhar tasu ma mai matuƙar rauni ce.

✍️ Dr. Aliyu Muhd Sani Misau (Hafizahullah)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments