Ticker

6/recent/ticker-posts

Siffofin Mumini Na Gaskiya Wanda Ya Yi Imani Na Hakika

SIFFOFIN MUMINI NA GASKIYA WANDA YA YI IMANI NA HAƘIƘA

Wanda ya yi imani da Allah imani na gaskiya, hakika yana jin dadi da ni'ima a bautar da yake yi ma Allah, in yana cikin aikata bautar Allah ji yake yi yana cikin babbar ni'ima ce, yana yi yana mai fatan samun alheri a wajen Ubangijinsa, kuma yana samun ni'ima da rabon da Allah ya ba shi na abin duniya, saboda yana amfani da shi ne a matsayin abin da yake taimaka masa a kan bautar Allah, don ya samu ikon aikata wajiban da Allah ya wajabta masa.

Shi mumini siffarsa ita ce; tawali'u da kaskantar da kai ma Allah da kuma bayinsa, kuma yana bin gaskiya a duk inda take, kuma yana yin Addini ne ta hanyar nasiha wa bayin Allah a bisa banbancin matsayinsu.

Amma shi kuma mai musun gaskiya, siffarsa ita ce; girman kai wa gaskiyar, da kuma girman kai wa bayin Allah da ruduwa da kai, ba ya yin Addini ta hanyar yin nasiha ma kowa a cikin bayin Allah.

Shi mumini zuciyarsa a wanke take daga gisshi (ha'inci) da jin haushin bayin Allah da kullesu a zuciya, shi mai gaskiya ne a maganarsa, mai kyakkyawar mu'amala ne, siffarsa ita ce; hakuri da kwanciyar hankali da nitsuwa, da juriya da tausayin mutane da cika alkawari da tabbatuwa a kan gaskiya. Ba ya kaskantuwa ma kowa sai ma Allah.

Yana hada tsakanin kokarin aikata sabuba masu amfani wajen neman abu, da kuma dogaro ga Allah da neman taimako a wajensa a kan dukkan lamura.

Shi mumini idan abin duniya ya zo masa yana karbansa ne da godiya ma Allah da yin amfani da shi cikin abin da zai amfane shi, ya janyo masa alheri, haka idan abin bakin ciki ya same shi sai ya karbe shi da hakuri da neman sakamako da lada a wajen Allah, da kuma neman Allah ya yaye masa, sai ya kasance abin da aka canza masa na alheri da imani da nitsuwa ya fi girma fiye da abin da ya rasa na abin da yake so, ko abin da ya same shi na bakin cikin.

Madalla da muminai zababbun Allah, masu gaskiya a cikin imaninsu masu da'a ma Allah, wadanda suka raya zukatansu da sanin Allah da soyayya gare shi, haka bakunansu suka cika da furta ambaton Allah da yabo gare shi, kuma suka raya lokutansu da yin da'a ma Allah da yi masa ibada, sa'annan kuma da wannan imanin nasu na gaskiya suka mu'amalanci bayin Allah da kyawawan dabi'u da halaye, na rangwame da tausayawa da nasiha wa bayin Allah. Kuma wannan imanin nasu ya hanasu dukkan mummunan hali makaskanci, kamar yadda ya kwadaitar da su ga dukkan kyakkyawan hali.

Shi imani ba abin ado ba ne ko abin buri a baki kawai, a'a, imani kawai shi ne abin da ya tabbata a zuciya sa'annan aiyuka suka gaskata shi a bisa hakika. Da tantancewa da jarabawa ne makaryaci yake bayyana daga mai imani na gaskiya.

Daga littafin Sheikh Ibnu Sa'adiy (r): Al- Riyadhun Nadhirah.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
3 July, 2014

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments