"Bakura mun biya,
Muka wa Tudu murna
Bakura an naɗa sabon Sarki".
☝☝Haka Makada Alh. Muhammadu Bawa Dan Anace Yar Tsakkuwa, Gandi Sakkwato ya ce a faifansa na Dan Dambe Marigayi Mika'ilu dake ƙauyen Bandawa a Karamar Hukumar Mulkin Roni ta Jihar Jigawa da aka fi sani da Miko Dogo wanda ya rasu a shekarar 1974 sanadiyar cin gubar da ake zargin an saka masa a abinci.
A cikin faifan mai amshi
"Kai maza suka sauna hili, taho maƙi gudu Miko dogo" Makada Dan Anace
yana nufin da suka fito daga garinsu na Yar Tsakkuwa (garin yana makwabtaka da
Bakura daga Arewa maso yamma) akan hanyarsu ta zuwa Kano wajen Dan Dambe Miko
Dogo sai suka ratse a garin Bakura domin su taya Dagacin Birnin Tudu dake
Gundumar Bakura, wato Tudun Birnin Tudu Muhammadu Tukur murnar naɗa
yayansa/wansa wanda kuma shi ne ya gada a matsayin Tudu a Birnin Tudu, Alh.
Muhammadu Mai lafiya a matsayin sabon Uban Ƙasar/Hakimin Gundumar/Sarkin Ɓurmin
Bakura a shekarar 1970 bayan wafatin Sarkin Ɓurmi Yusuf II.
Da Sarkin Ɓurmin Bakura
Alhaji Muhammadu Mailafiya da Tudun Birnin Tudu Alh. Muhammadu Tukur ɓiyan
Sarkin Ɓurmin Bakura Ibrahim Ima ne wanda ya yi sarauta daga 1919-1937 shi kuma
ɓan Sarkin Ɓurmin Bakura Yusuf Ɗan Ƙwai ne wanda ya yi sarauta daga 1856 -
1885. Allah SWT ya jaddada masu rahama, amin.
A shekarar 1970 da aka
dauko Alh. Muhammadu Mailafiya daga garin Birnin Tudu inda yake matsayin Dagaci
da laƙabin Tudu aka naɓa shi Sarkin Ɓurmin Bakura shi kuma ƙanensa ya na rike
da sarautar Bunun Bakura sai shi yayan nasa/wan nasa da ya baro Birnin Tudu
zuwa Bakura a matsayin sabon Sarkin Ɓurmi/Uban Ƙasar/Hakimin Gundumar Bakura ya Ɗauki wannan ƙane nasa dake rike da sarautar Bunun Bakura ya kai shi Birnin
Tudu a matsayin Dagaci wato "Tudun Birnin Tudu" wanda shi ne su
Makada Dan Anace suka biya Bakura su yi masa murnar yayansa/wansa Alh.
Muhammadu Mailafiya ya zama sabon Sarkin Bakura /Sarkin Ɓurmin Bakura.
Kenan dai ita wannan
wakar ana hasashen anyi ta ne a farko farkon 1970s. Da Sarkin Ɓurmin Bakura
Alhaji Muhammadu Mai lafiya Ibrahim da ƙanensa Tudun Birnin Tudu Alh. Muhammadu
Tukur Ibrahim an cire su daga sarautun su a shekarar 1981, daga bisani Allah
SWT ya yi masu wafati.
Masu Sarautar Bakura
asalinsu daga Tsohuwar Daular Borno ne wato Barebari ne/Kanuri ne da ake
kirdadon sun fito ne daga Borno tun a farkon ƙarni na 14, suka dinga yada zango
har lokacin da Allah SWT ya yi zamansu a inda suke a halin yanzu wato Bakura a
cikin ƙarni na 17.
Muna rokon Allah SWT ya
jaddada rahamarsa zuwa ga dukan magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da
kyau da imani, amin.
Hon. Ibrahim Muhammad
Danmadamin Birnin Magaji,
Jihar Zamfara, Nijeriya.
13/07 /2025.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.