Ticker

6/recent/ticker-posts

Sauye-Sauyen Zamani a Wasu Sarautun Sana’o’in Gargajiya Da Ayyukansu a Garin Kano (Kashi Na Farko)

Article Citation: Suleiman, M. (2025). Sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano [Master’s dissertation]. Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

SAUYE-SAUYEN ZAMANI A WASU SARAUTUN SANA’O’IN GARGAJIYA DA AYYUKANSU A GARIN KANO

Na

SULEIMAN Musa
Email: musasuleiman424@gmail.com  
Phone: 08061256096

Sauye-Sauyen Zamani a Wasu Sarautun Sana’o’in Gargajiya Da Ayyukansu a Garin Kano

GODIYA

Dukkan yabo da godiya su tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W) da alayensa da sahabbansa da mabiyansa har ya zuwa ranar tashin alƙiyama.

Godiya ta musamman ga Farfesa Yakubu Aliyu Gobir, wanda ya ɗauki ɗawainiyar duba wannan aiki, ba don shi ba da wannan binciken ba zai kammalu ba. Haƙiƙa Malam ya nuna juriya da haƙuri wajen ganin wannan binciken ya kammalu. Haka kuma, Malam ya yi ƙoƙari wajen gyara da ba da shawarwari da gudummawa domin kyautatuwar wannan bincike. Allah ya saka masa da mafificin alherinSa ya kuma albarkaci zuriarsa.

Haka kuma, ina miƙa godiya mai ɗumbin yawa ga mai dubawa na biyu Dakta Musa Fadama Gummi. Sai kuma mai dubawa na uku Dakta Abubakar Musa Mijinyawa (wanda yake jagorancin Sashen Koyar da Ayyukan Jarida, na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato). Waɗannan haziƙan malamai sun ƙara mini ƙwarin guiwa da ba ni shawarwari da suka ƙara ƙawata wannan bincike. Allah ya saka musu da mafifinci alkhairinSa, amin

Sannan, ina miƙa godiya ta musamman ga sauran malamaina na Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, waɗanda da bazarsu ce nake rawa a halin yanzu.

Ina godiya wadda ba ta da iyaka ga Kawu na Dakta Sani Ahmad Sufi wanda shi ne yake ɗaukar ɗawainiyar karatuna, tun daga farko har zuwa wannan mataki. Allah Ya saka masa da mafificin alhreinSa, Ya ƙara masa lafiya da zama lafiya da nisan kwana Ya shirya masa zuriarsa Ya jikan magabatansa baki ɗaya.

Ina godiya da jinjina ga dukkan dangina, musamman iyayena da suka tarbiyantar da ni a kan tafarkin ilimi, da kuma addu’o’in da suke yi a gare ni kodayaushe, don ganin na samu nasara ga duk abin da na sa gaba a rayuwa. Allah Ya saka musu da mafificin alkairisa, amin.

Ina miƙa godiya mara adadi ga masu riƙe da waɗannan sarautu na sana’o’in gargajiya a garin Kano. Musamman Sarkin fawan Kano Alhaji Isyaku Alin Muli, da Sarkin Ginin Kano Alhaji Abdulƙadir Muhammad, da Sarkin ɗorin Kano Alhaji Uba Muhammad, da kuma Sarkin Ƙiran Kano Alhaji Usman Muhammad. Haƙiƙa waɗannan mutane sun ba ni gagarumar gudummawa wajen samun wasu muhimman bayanai yayin gudanar da wannan bincike. Allah ya saka musu da alkhairi.

Godiya mai tari yawa ga Shamakin Kano ba Alhaji Wada Muhammad da Sallaman Kano Alhaji Dauda da Ɗanrimin Kano Alhaji Sarki Waziri. Haƙiƙa waɗannan bayin Allah sun taka muhimmiyar rawar gani wajen ba ni wasu bayanai akan abin da ya shafi wannan bincike. Allah ya ƙara musu lafiya da zaman lafiya ya ɗaukaka zuri’arsu.

Daga ƙarshe, ina ƙara miƙa godiya ta ga dukkan abokan karatuna waɗanda da su ne muka yi ta faɗi-ta-shi don ganin mun kai ga gaci. Allah Ya saka wa kowa da alheri Ya ba mu nasara a duk abin da muka sa gaba. Amin ya Allah.

ABUBUWAN DA KE CIKI

TAKEN KUNDIN BINCIKE i

SADAUKARWA ii

CERTIFICATION iii

GODIYA iv

ABUBUWAN DA KE CIKI vi

ABSTRACT xvi

TSAKURE xvii

BABI NA ƊAYA 1

GABATARWA 1

1.0 Shimfiɗa 1

1.1 Dalilan Bincike 2

1.2 Manufofin Bincike 3

1.3 Tambayoyin Bincike 3

1.4 Farfajiyar Bincike 4

1.5 Muhimmancin Bincike 4

1.6 Waiwayen Tubalan Kalmomin Matashiya 5

1.6.1 Sauyi 5

1.6.2 Sarauta 6

1.6.2.1 Sarauta A Ƙasar Hausa 7

1.6.3 Sana’a 9

1.6.3.1 Asalin Sana’o’in Hausawa na Gargajiya 10

1.6.4 Gargajiya 11

1.6.5 Waiwayen Tarihin Birnin Kano a Taƙaice 12

1.7 Naɗewa 15

BABI NA BIYU 17

BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA 17

2. 0 Shimfiɗa 17

2.1 Rukunin Kundayen Bincike 17

2.1.1 Kundayen Digiri na Uku. 17

2.1.2 Kundayen Digiri Na Biyu 19

2.1.3 Kundayen Digirin Farko 24

2.2 Maƙalu a Cikin Mujallu 27

2.3 Maƙalu A Tarukan Ƙara wa Juna Ilimi 30

2.4 Bugaggun Littattafai 31

2.5 Hujjar Cigaba da Bincike 37

2.6 Naɗewa 38

BABI NA UKU 39

HANYOYIN GUDANAR DA BINCIKE 39

3.0 Shimfiɗa 39

3.1 Ziyara 39

3.1.1 Tattaunawa da Masana 40

3.1.2 Tuntuɓar Manazarta 41

3.2 Nazarin Rubuce-Rubuce 41

3.3 Tuntuɓar Kafafen Yaɗa Labarai da Jaridu 41

3.4 Kafar Sadarwa ta Intanet 42

3.5 Hanyoyin Tantance Bayanan Bincike 43

3.6 Ra’in Bincike 43

3.7 Naɗewa 45

BABI NA HUƊU 46

SAUYE-SAUYE A WASU SARAUTUN SANA’O’IN GARGAJIYA DA AYYUKANSU 46

4.0 Shimfiɗa 46

4.1 Sarautun Sana’o’i 46

4.2 Asalin Sarautun Sana’o’in Gargajiya a Garin Kano 47

4.3 Sarautun Sana’o’in Gargajiya a Jiya 49

4.3.1 Gado 50

4.3.2 SƘwarewa 51

4.3.3 Jaruntaka 52

4.3.4 Sanin Asirai 52

4.4 Sarautun Sana’o’in Gargajiya a Yau 52

4.4.1 Gado 53

4.4.2 Siyasa 53

4.4.3 Abin Hannu (Kuɗi) 54

4.5 Sarautar Sarkin Ɗori 54

4.5.1 Asalin Sarautar Sarkin Ɗori a Birnin Kano 55

4.5.2 Taƙaitaccen Tarihin Sarkin Ɗorin Kano Alhaji Uba Muhammad 57

4.5.3 Ayyukan Sarkin Ɗori 58

4.5.3.1 Aikin Ɗori 59

4.5.3.2 Kula da Gudanar da Aikin Ɗori 59

4.5.3.3 Sulhu da Sasanci 59

4.5.3.4 Bayar da Magunguna 59

4.5.3.5 Karɓar Haraji 60

4.5.4 Hakiman Sarkin Ɗori da Ayyukansu 60

4.5.4.1 Madakin Ɗori 61

4.5.4.3 Galadiman Ɗori 61

4.5.4.4 Garkuwan Ɗori 61

4.5.4.5 Ma’ajin Ɗori 62

4.5.5 Ƙananan Sarakunan Ɗori 62

4.5.6 Al’adan Sarautar Ɗori a Jiya 63

4.5.6.1 Bikin Naɗin Sarkin Ɗori 63

4.5.6.2 Nuna Buwaya 63

4.5.6.3 Kai Gaisuwa 64

4.5.7 Sauye-Sauye a Sarautar Ɗori da Aladunta 64

4.5.7.1 Samuwar Ofishin Sarkin Ɗori 65

4.5.7.2 Rijistar Adana Bayanai 65

4.5.7.3 Naɗin Sarautun Mataimaka Sarkin Ɗori 66

4.5.7.4 Saukar Karatun Alƙurani 66

4.5.7.5 Ziyarar Abokan Aiki 66

4.5.7.6 Yanayin Naɗin Sarautar Sarkin Ɗori 67

4.5.8 Sauye-Sauye A Ayyukan Ɗori 68

4.5.8.1 Amfani da Auduga da Bandeji 68

4.5.8.2 Amfani da Magungunan Zamani 69

4.5.8.3 Hoton Ƙashi (X-Ray) 69

4.5.8.4 Shugowar Hukuma 70

4.5.8.5 Zuwa Koyon Ɗori a Makarantun Boko 70

4.6 Sarautar Sarkin Fawa 71

4.6.1 Asalin Sarautar Fawa a Birnin Kano 72

4.6.2 Taƙaitaccen Tarihin Sarkin Fawan Kano Alhaji Isiyaku Alin Muli 72

4.6.3 Ayyukan Sarkin Fawa 74

4.6.3.1 Aikin Sana’ar Fawa 74

4.6.3.2 Samar da Tsaro A Kwata da Kara 74

4.6.3.3 Sulhu da Sasanci 75

4.6.4 Hakiman Sarkin Fawa da Ayyukansu 75

4.6.4.1 Galadiman Fawa 75

4.6.4.2 Ciroman Fawa 75

4.6.4.3 Majidaɗin Fawa 76

4.6.4.4 Turakin Fawa 76

4.6.4.5 Shamakin Fawa 76

4.6.4.6 Sarkin Fada 76

4.6.4.7 Babban Zagi 77

4.6.4.8 Mata a Farfajiyar Fawa 77

4.6.5 Ƙananan Sarakunan Fawa a Birnin Kano 77

4.6.5.1 Sarkin Fawan Birget 78

4.6.5.2 Sarkin Fawan Ungogo 78

4.6.5.3 Sarkin Fawan Tudun Fulani 78

4.6.5.4 Sarkin Fawan Unguwa Uku 79

4.6.6 Al’adun Sarautar Fawa A Jiya 79

4.6.6.1 Bayar da Magunguna 79

4.6.6.2 Hawan Ƙaho 80

4.6.6.3 Dambe 81

4.6.6.4 Tsatsube-Tsatsuben Fawa 82

4.6.6.4.1 Ba-duhu 82

4.6.6.4.2 Ɓata Kasuwa 84

4.6.7 Sauye-Sauye a Sarautar Fawa da Al’adunta 84

4.6.7.1 Samar da Ofishin Sarkin Fawa 85

4.6.7.2 Mataimaka na Musamman 85

4.6.7.3 Samar da Masu Raba Rasiɗi 85

4.6.7.4 Samar da Ofishin Likitocin Dabbobi 85

4.6.7.5 Samar da Gidan Sanyi Domin Ajiyar Nama 86

4.6.7.6 Hanyoyin Samun Kuɗin Shiga 87

4.6.7.7 Ɗaukar Maaikata 87

4.6.7.8 Samar da Makaranta 87

4.6.7.9 Kai Gaisuwar Juma’a 88

4.6.7.10 Hawan Sallah 88

4.6.7.11 Shirya Gasa 89

4.6.7.11.1 Gasar Kwallon Kafa 89

4.6.7.11.2 Gasar Dambe 89

4.7 Sarautar Sarkin Gini 90

4.7.1 Asalin Sarautar Gini a Birnin Kano 90

4.7.2 Taƙaitaccen Tarihin Sarkin Ginin Kano Abdulƙadir Muhammad 92

4.7.3 Ayyukan Sarkin Gini 93

4.7.3.1 Aikin Gini 93

4.7.3.2 Gine-Ginen Gidan Sarki 93

4.7.3.3 Kula da Gine-Ginen Sarki 94

4.7.3.4 Sulhu da Sasanci 94

4.7.3.5 Bayar da Shawarwari a Lamuran Gine-Ginen Fada 94

4.7.4 Hakiman Sarkin Gini da Ayyukansu 95

4.7.4.1 Galadiman Gini 95

4.7.4.2 Madakin Gini 96

4.7.4.3 Turakin Gini 96

4.7.4.4 Shamakin Gini 96

4.7.5 Al’adun Magina a Jiya 96

4.7.5.1 Kai Gaisuwa 97

4.7.5.2 Fasa Sabuwar Ƙofa 97

4.7.5.3 Tukuici 98

4.7.5.4 Tsatsube-Tsatsuben Magina 98

4.7.5.4.1 Jifa 98

4.7.5.4.2 Lalata Aiki 99

4.7.6 Sauye-Sauye A Sarautar Gini da Al’adunta 99

4.7.6.1 Samuwar Ofishin Sarkin Gini 99

4.7.6.2 Samuwar Ɗakin Ajiya 100

4.7.6.3 Rakiyar Sarki Soron Shekara 100

4.7.6.4 Naɗin Hakiman Sarkin Gini 100

4.7.6.5 Kai Gaisuwa 101

4.7.6.6 Fasa Ƙofa 101

4.7.7 Samuwar Kayan Aikin Gini da Ado na Zamani 102

4.7.7.1 Shebur 102

4.7.7.2 Wuƙa 103

4.7.7.3 Katako 103

4.7.7.4 Siminti 104

4.7.7.5 Yashi 104

4.7.7.6 Duwatsu 105

4.7.7.7 Bulo 105

4.7.7.8 Samuwar Kayan Rufin Gida 106

4.8 Sarautar Sarkin Ƙira 107

4.8.1 Asalin Sarautar Ƙira A Birnin Kano 108

4.8.2 Taƙaitaccen Tarihin Sarkin Maƙeran Kano Alhaji Usman Muhammad 109

4.8.3 Ayyukan Sarkin Maƙera 110

4.8.3.1 Aikin ƙira 110

4.8.3.2 Bayar da Magani 110

4.8.3.3 Samar da Makaman Yaƙi 111

4.8.4 4 Ƙera Ƙofofin Shiga Garin Kano 111

4.8.3.5 Kula da Tsaron Maƙera da Lafiyar Maƙera 112

4.8.3.6 Sulhu da Sasanci 113

4.8.3.7 Karɓar Haraji 113

4.8.4 Hakiman Sarkin Ƙira da Ayyukansu 113

4.8.4.1 Ciroman Ƙira 113

4.8.4 2 Galadiman Ƙira 114

4.8.4.3 Ɗanmasanin Ƙira 114

4.8.4.4 Wamban Ƙira 114

4.8.5 Al’adun Maƙera A Jiya 115

4.8.5.1 Wasan Wuta 115

4.8.5.2 Bikin Cin Tama 116

4.8.5.3 Nuna Buwaya 116

4.8.6 Sauye-Sauye a Sarautar Ƙira da Aladunsu 117

4.8.6.1 Samar da Ofishin Sarkin Maƙera 117

4.8.6.2 Kai Gaisuwa 117

4.8.6.3 Tukuicin Sallah 117

4.8.6.4 Bikin Naɗin Sarauta 118

4.8.7 Samuwar Kayan Aikin Ƙira Na Zamani 118

4.8.7.1 Injin Hura Wuta 118

4.8.7.2 Wadatattun Ƙarafa 119

4.8.7.3 Injinan Zamani 119

4.8.7.4 Samuwar Ma’aunai 120

4.8.7.5 Nau’ikan Ƙarafa 121

4.8.7.6 Injin Walda 121

4.9 Matsayin Sarautun Sana’o’in Gargajiya a Masarautar Kano 122

4.9.1 Matsayin Sarautar Sarkin Ɗori 123

4.9.2 Matsayin Sarautar Sarkin Gini 124

4.9.3 Matsayin Sarautar Sarkin Fawa 125

4.9.4 Matsayin Sarautar Sarkin Ƙira 126

4.10 Dangantakar Sana’o’in Gargjiya da Junansu 129

4.11 Dangantakar Sarautun Sana’o’in Gargajiya da Junansu 130

4.11.1 Haɗin Guiwar Sarakuna a Harkokin Sana’o’i 130

4.11.2 Cuɗe-ni-in-cuɗe-ka 130

4.11.3 Asali 131

4.11.4 Bunƙasa Tattalin Arziƙi 131

4.11.5 Tsarin Shugabanci 132

4.12 Dangantakar Sana’o’in Gargajiya da Cigaban Al’umma 132

4.12.1 Samar da Kayan Aiki 132

4.12.2 Magani 133

4.12.3 Hanyar Samar da Abinci 133

4.12.4 Hanyar Samun Kuɗi 134

4.12.5 Adana Al’adu da Tarihi 134

4.13 Dangantakar Sarautun Sana’o’in Gargajiya da Cigaban Al’umma 134

4.13.1 Shugabanci Da Tsari A Fannin Sana’a 135

4.13.2`Ƙarfafa Tattalin Arziƙi 135

4.13.3 Horar Da Matasa Da Samar Da Ayyukan Yi 135

4.13.4 Haɗin Guiwa Da Gwamnati Da Cibiyoyi 135

4.14 Dangantakar Sana’o’in Gargajiya da Cigaban Zamani 136

4.14.1 Sabunta Fasaha Da Tsarin Aiki 136

4.14.2 Tallace-Tallace Ta Hanyar Intanet 136

4.14.3 Ƙirƙirar Sabbin Kayayyaki Cikin Tsarin Gargajiya 136

4.14.4 Koyarwa da ba da Horo A Zamanance 137

4.14.5 Shiga Kasuwannin Duniya 137

4.15 Dangantakar Sarautun Sana’o’in Gargajiya da Cigaban Zamani 137

4.15.1 Rikiɗewar Sarautun Sana’o’in Gargajiya Zuwa Shugabancin Zamani 137

4.15.2 Haɗin Guiwa da Cibiyoyi Na Fasaha Da Horo 138

4.15.3 Tallafawa Masu Sana’o’in Gargajiya da Bayar da Shawarwari 138

4.15.4 Zama Jakadu A Kasuwannin Zamani 138

4.16 Naɗewa 139

BABI NA BIYAR 140

KAMMALAWA 140

5.0 Shimfiɗa 140

5.1 Taƙaitawa 140

5.2 Shawarwari 142

5.3 Sakamakon Bincike 143

MANAZARTA 144

RATAYE 151

ABSTRACT

This research explores the contemporary transformations among traditional occupational title holders and their duties in Kano metropolis. The study aims to examine the chieftaincy, hegemonic position, norms, customs, and practices associated with these title. The research is guided by theories of Social Change, Cultural Evolution, and Human Development. To achieve its objectives, the study consulted various libraries, reviewed relevant books, journals, projects, dissertations and theses. Additionally, the research sought insight from renowned experts with in-depth knowledge of the professions. The study is anchored on the following research questions: What is the contemporary status of traditional occupational titles? What are the obligations and duties of traditional occupational title holders in modern times? What transformations have the occupational title brought to the environment? What positions and traditions are attached to the occupational title? The research findings reveal the current state and conditions of traditional occupational titles in the 21st century, including their duties, roles, and transformations. The study also identifies the traditional position and customs associated with these titles. Furthermore, the research explores the status and dynamics of traditional occupational title holders.

TSAKURE

Wannan bincike mai taken “Sauye-Sauyen Zamani a Wasu Sarautun Sana’o’in Gargajiya da Ayyukansu a Garin Kano”. An gudanar da shi ne da manufar duba wasu sarautun sana’o’in gargajiya da tsarin bayar da su, da al’adun da suke tattare da su. An ɗora wannan bincike a kan ra’in “Sauyin Al’adu da Cigaban Al’uumma” (Theory of Social Change, Cultural Evolution, And Human Development). An bibiyi ɗakunan adana bayanan ilimi domin bitar littattafai da kundaye da maƙalu, musamman masu alaƙa da wannan bincike. An tattauna da mutane da suke da masaniya a kan sarautun. An shimfiɗa tambayoyin bincike da suka haɗa da: Wane yanayi sarautun sana’o’in gargajiya suke ciki a yanzu? Waɗanne ayyuka sarautu sana’o’i suke yi? kuma waɗanne sauye-sauye aka samu a yanzu? Waɗanne muƙamai ne da aladu suke tattare da sarautun sanaoin gargajiya? A ƙarshe bincike ya samu damar fito da sakamako guda huɗu (4) kamar haka: Fito da yanayin da sarautun sana’o’in gargajiya suke ciki a yanzu. Kundin ya zaƙulo ayyuka da sauye-sauyen da aka samu a waɗannan sarautu. Binciken ya gano muƙamai da aladun da suke tattare da waɗannan sarautu. A ƙarshe aikin ya fito da matsayi da dangantakar wasu sarautun sana’o’in gargajiya.

Post a Comment

0 Comments