Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarihin Hajiya Aishatu Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, Matar Marigayi Alhaji Ahmadu Danbaba Marafan Sakkwato

30 ga watan Oktoba na shekarar 1945 aka haife ta a wata unguwa da ake kira Takardawa dake cikin Birnin Sakkwato, Arewa Maso yammacin Nijeriya.

Tayi karatun Addinin Musulunci a hannun Malamai daban - daban a cikin Sakkwato ciki kuwa har da Malam Maigandi dake Gidadawa. A Kaduna kuwa tayi karatu a hannun Malam Bagudu.

Ta halarci Makarantar Elimentare ta Magajin Rafi dake  Sakkwato domin samun ilimin zamani kafin daga bisani tayi aure.

Allah ya albarkaci auren nata da 'ya'ya /diya 8, 3 Maza, 5 Mata.

Abdulkadir da  Hassan da Husaini sune 'ya'yanta /diyanta maza, Asma'u da Hadiza da Maryam da Safiya da Aisha kuma sune 'ya'yanta /diyanta mata.

Su 3 Mahaifiyarsu ta haifa dukansu kuwa Mata ne, ita ce ta biyu duk da yake akwai namiji tsakanin ta da wadda take bima wanda tun a matakin jarinta ne ya rasu.

Gaba da baya yar sarauta ce ( ta wurin mahaifi da mahaifiya)  ta  auri Basarake, ta kuma haifi Basarake. 

Ya'yanta /diyanta mata daya ta auri Sarki, 3 suka auri 'ya'yan Sarakuna d'aya kuma ta auri d'an wani shahararren Malamin Addinin Musulunci /Babban Alkali.

Marigayiya Hajiya Aishatu Marafa Ahmadu Danbaba (1945-2021).

Marigayiya Hajiya Aishatu Marafa Ahmadu Danbaba (1945-2021).

Wannan baiwar Allah ita ce Marigayiya Hajiya Aisha/Aishatu yar Sir Ahmadu Bello GCON KBE Sardaunan Sakkwato Firimiyan Jihar Arewa na farko kuma na karshe dan Sarkin Rabah Malam Ibrahimu dan Sarkin Musulmi Abubakar II /Mai Rabah dan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello dan Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo Tagammadahullah Birahamatihi.

Ita ce 'ya /d'iya ta biyu daga cikin 'ya'ya /d'iya uku wadanda Marigayiya Hajiya Amina/Gwaggon Kano yar Sarkin Bichi Abubakar dan Sarkin Bichi Mustapha ta haifawa Sardaunan Sakkwato Sir Ahmadu Bello, sauran sune Marigayiya Hajiya Fatima /Inno da Hajiya Lubabatu/Luba wadda ke raye a halin yanzu.

Makada Musa Dankwairo Maradun a faifansa mai amshi "Ya wuce reni ba ayi mai shi, Amadu jikan Garba sadauki" da ya yiwa Mahaifinsu (Sardaunan Sakkwato Sir Ahmadu Bello) ya na ambatarta a ciki ya na cewa "Mai girma d'an Mai girma Uban Luba baban A'i da Inno".

Mijinta shine Marigayi Mai girma Sanata Alh. Ahmadu Danbaba Marafan Sakkwato dan Magajin Garin Sakkwato Usman dan Magajin Garin Sakkwato Abdu wanda kuma jika ne ga Magajin Garin Sakkwato na farko Malam Abubakar Haruna Dan Jada Ba'allibe.

D'anta Marigayi Alhaji Hassan Ahmadu Danbaba yana rike da sarautar Magajin Garin Sakkwato ne Allah SWT ya yi masa wafati.

'Yarta/D'iyarta Hajiya Asma'u (Ammi) ita ce matar Marigayi Mai girma Sarkin Sudan na Wurno Alhaji Shehu Malami, Hajiya Hadiza ce matar Alh. Umaru Shehu Goronyo Tsohon Shugaban Majalisar Dokoki a Tsohuwar Jihar Sakkwato (Sokoto da Zamfara a yau) kuma tsatso daga zuriyar Sarkin Musulmi Aliyu Babba dan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello dan Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo, Hajiya Maryam tana auren  Alhaji Bashir Huseini Adamu jikan Malam Ibrahim Dan Tunku wadda Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo ya baiwa Tutar Jihadin Jaddada Addinin Musulunci a Kazaure ta Jihar Jigawa ta yau.

Yarta/D'iyarta Marigayiya Hajiya Safiya ta auri Alhaji Alhassan dan Malam/Alkali Mutasibbi Sakkwato yayinda Hajiya Aisha ke auren Farfesa Isah Muhammad Maishanu, Kwamishinan ilimi mai zurfi na Jihar Sakkwato daga tsatson zuriyar Sarkin Kabin Yabo Muhammadu Moyijo daya daga cikin manyan mataimakan Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo dake da Tutar yakin jaddada Addinin Musulunci a Daular Usmaniyyah.

Hajiya Aishatu Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, Matar Marigayi Alhaji Ahmadu Danbaba Marafan Sakkwato, Mahaifiyar Magajin Garin Sakkwato Alhaji Hassan Danbaba ta rasu a shekarar 2021, Allah SWT ya jaddada mata rahama ita da dukan Magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani, amin.

Ibrahim Muhammad Danmadamin Birnin Magaji, Jihar Zamfara, Nijeriya.

Jumu'a, 10/07 /2025.

Post a Comment

0 Comments