Ticker

6/recent/ticker-posts

Fa'idojin Salla Guda Biyar

FA'IDOJIN SALLAH GUDA BIYAR

Sallah tana da wasu fa'idoji guda biyar, kowanne daga cikinsu ya fi duniya da abin da yake cikinta:

1- Tsayuwar Addinin bawa, saboda duk wanda ba ya Sallah ba zai zama musulmi ba, saboda ita ce rukuni na biyu mafi girma a cikin rukunnan Muslunci.

2- Kankare zunubai, da karuwan samun lada.

3- Samun daukakar daraja a wajen Allah.

4- Karuwan samun kusaci zuwa ga Allah Ubangijin sammai.

5- Karuwar imani a cikin zuciyarsa.

Kuma daga cikin fa'idojin Sallah, Allah ya shar'anta mana Sallolin farilla da ta Juma'a da ta Idi a cikin jam'i da yinsu tare da jama'a, saboda haduwa da taruwa don yin Sallar yana samar da soyayya da sadar da zumunci a tsakanin musulmai, kuma ga karin lada da za a samu saboda yinta cikin jama'a, ga kuma yawan taku zuwa masallaci, kowane taku ana samun lada.

Lallai abin da ke cikin Sallah na tafiya zuwa masallaci da dawowa, da tsayuwa a cikin Sallar da zama, da ruku'u da sujada da ake maimaitasu, ga maimaita tsarki da alola, duka wadannan kazar – kazar da motsa jiki aiyuka ne masu matukar amfani a gangar jikin dan'adam.

Daga cikin amfaninta mafi girma, kasancewar asalin ruhin Sallah da manufarta mafi girma shi ne halarto zuciya a gaban Allah (T) da kuma ganawa da shi, ta hanyar karanta maganarsa da ambatonsa da yi masa yabo, da rokonsa bukata da kaskantar da kai gare shi, da neman kusaci da shi da fatan samun lada da sakamako a wajensa.

Lallai ko shakka babu, wannan abu ne da yake haskaka zuciya, kuma yake faranta rai, yake bude kirji. Alhali abu ne sananne, aikata abin da yake faranta rai da sa mata jin dadi, da kawar mata da bakin ciki da damuwa yana daga cikin manyan hanyoyin samun cikakkiyar lafiya da take tunkude cutuka da kuma saukaka zafin ciwo da radadi.

Kai, fa'idojin Sallah na Addini da na duniya da na zamantakewa da na gangar jiki suna da yawan da ba za a iya iyakancesu ba.

Daga littafin Sheikh Ibnu Sa'adiy (r): Al- Riyadhun Nadhirah.

A sha ruwa lafiya.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
08 July, 2014

Fa'idojin Salla Guda Biyar

Post a Comment

0 Comments