Yusuf, J. (2025). Tarihin Ganuwar Wasu Al'amuran Siyasar Jam'iyyu a Cikin Rubutun Zuben Hausa Daga 1950-2023 (Ph.D. Thesis) Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo, Sokoto.
TARIHIN GINUWAR WASU AL’AMURAN SIYASAR JAM’IYYU A CIKIN RUBUTUN ZUBEN HAUSA DAGA 1950-2023
Na
Jibril Yusuf
Email: yusuf.jibril@kasu.edu.ng
Phone: +2347030399995
*** ***
BABI NA BIYAR
SIYASAR
JAm’iyya DA CIGABAN AL’UMMA DAGA CIKIN RUBUTACCEN ADABIN HAUSA
5.0 Shimfiɗa
A cikin wannan babin an kawo bayanai
kan abin da ya shafi manufar siyasar jam’iyyu, inda aka
kawo bayanai kan irin abubuwan da jam’iyyu
kan dogara da su a matsayin manufar siyasarsu. Waɗannan abubuwan su ne jam’iyyun
sukan riƙa yaɗa su ta hanyar tallata siyasarsu domin jama’a su karɓe su. A cikin
babin an kawo bayanai kan abubuwan da ake gwagwarmaya a kansu domin ɗorewar siyasa,
daga bisani kuma sai a kawo bayanai kan abubuwan da suke zama tarnaƙi ga ci gaban
siyasa, inda ka bi tsawon tarihi tun daga samuwar siyasar jam’iyyu zuwa yau, aka
ga inda suka riƙa fitowa a cikin ayyukan rubutaccen zube. A ƙarshen babin an kawo
bayanai ne kan irin kallon da ‘yan siyasa suke yi wa talakawa da kuma yadda su kansu
talakawa suke kallon ‘yan siyasa. Duk waɗannan bayanan an
kawo su ne ta hanyar kafa hujjoji daga rubutaccen zube.
5.1 Manufar Siyasar Jam’iyyu
Dukkan wani abu da ɗan’Adam zai gudanar a rayuwarsa yakan yi
shi ne bisa wata manufa wadda zai aiwatar da fatar kaiwa gare ta ko kuma samun ta.
A cikin siyasa akan riƙa ayyana waɗansu muhimman abubuwa waɗanda kan zama su ne
manufar ita kanta wannan siyasar, wato su ne za su zama abubuwan da wannan tsarin
siyasar ya sanya a gaba domin tabbatar da su. Irin wannan ne ya sanya kowace jam’iyyar
siyasa takan kasance tana da wasu manufofi da tsare-tsare waɗanda akan kafa ta a
kansu domin su zama wata gada da za a taka zuwa ga samun nasarar jam’iyyar a siyasance.
Manufofin bisa kansu ne za a kafa jam’iyya, da su ne za a tallata ta, kuma ta hanyar
amfani da su ne idan an samu nasarar ɗarewa kan madafun iko za a gudanar da shugabancin
al’umma, domin a yi nasara.
A cikin tarihin siyasar Arewacin Nijeriya, akwai manufofin da
tun da aka ƙirƙiri siyasar ake amfani da su wajen tallata siyasa da kuma gudanar
da ita, wannan ba zai rasa nasaba da irin muhimmancin da irin waɗannan manufofin
suke da shi a cikin rayuwar al’umma ta yau da kullum ba. Abubuwa ne waɗanda rayuwar
ma kacokam a kansu ta ginu, kuma su ne abubuwan da kan samar da sauƙi wajen tafiyar
da harkokin yau da kullum na al’umma.
Bayan kafa jam’iyya bisa manufofi, sai a fitar da jam’iyyar a
fara tallar ta ga al’umma ta hanyar manufofin, inda akan yi amfani da wasu hanyoyi
fitattu wajen fito da ire-iren waɗannan manufofi. Alal misali, fitacciyar hanyar
da ake tallar manufar siyasa ita ce, ta hanyar yaƙin neman zaɓe, inda akan tara
jama’a na garuruwa da yankuna domin yi masu bayani kan abin ya sa wannan jam’iyyar
take neman a zaɓe ta a wani mataki. Za a ta bayyana manufofinta ga al’umma ta hanyar
ƙoƙarin gamsar da su, wanda in suka amince to sai ta samu goyon baya daga wurinsu.
A jamhuriya ta farko, jamiyyar NPC ta kafu ne bisa manufar yaƙi
da lalaci da talauci da kuma zalunci. Wannan ya sa da farko ‘yan ƙasa suka shige
ta, kuma suka goya mata baya tare da tallata manufofin ga sauran jama’a domin su
ma su karɓa. An hasko irin wannan manufar a cikin jawabin wakilin NPC na lardin
Kano, Malam Sabo Bakin Zuwo, wanda aka tura yaƙin neman zaɓe a Sakkwato a kakar
zaɓe ta shekarar 1959. Dubi abin da ya ce a cikin jawabinsa:
“Jama’a ku gane mu mutanen
Arewa, akwai arziƙi mai yawa a ƙasarmu to mun yi sa’a ƙwarai da yake mun sami jam’iyya
wadda take da manufa ta kiyaye mutuncin Arewa da kiyaye arziƙinta da ƙoƙarin sama
wa jama’a zaman jin daɗi sosai. Wannan jam’iyya kuwa ita ce NPC.”
(“Sabo Bakin Zuwo Ya Yi Nasarar Yaƙin Zaɓe”, 1959).
A nan ya haska wa al’umma irin manufofin jam’iyyar NPC ne, inda
ya nuna cewa irin ɗimbin arziƙin da yankin Arewa yake da shi ne ya sa jam’iyyar
ta tsara cikin manufofinta cewa za ta kiyaye mutuncin yankin na Arewa da arziƙin
da ke cikin yankinj ba tare da yin sakaci wasu su riƙa kwashe arziƙin suna tafiya
da shi ƙasashensu ba. Ta hanyar yin amfani da arziƙin yankin ne za a samar wa al’umma
zaman jin daɗi.
Daga bisani da wasu daga ciki suka lura cewa jam’iyyar
ta sauka daga manufofin da aka kafa ta a kansu, sai suka dawo daga rakiyarta, suka
kafa jam’iyyar hamayya ta NEPU bisa manufar ciyar da tattalin arziƙi gaba da kuma
faɗa da danniya da ake wa talakawa da mulkin mallakar Turawa. Akan wannan manufar
jam’iyyar NEPU ta kafu kuma ta gudanar da siyasarta har zuwa lokacin da sojoji suka
kawo ƙarshenta a 1966. Bayan dawowa mulkin demokuraɗiyya a jamhuriya ta biyu ma
jam’iyyu irin su PRP sun tallata manufofinsu ga al’umma. An samo wani bayani daga
jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo wanda ya hasko
wasu daga cikin manufofin jam’iyyar kamar haka:
“A cikin jawabinsa Alhaji
Sabo Bakin Zuwa, ya tabbatar wa da jama’ar da suka hallara a wajen taron cewa jam’iyyar
PRP ita ce kaɗai jam’iyyar da za ta iya ceto jama’ar ƙasar nan daga danniya, zalunci,
fatara, jahilci da kuma handame kayan jama’a.”
(“Jam’iyyar PRP Za Ta Ceto Jama’a”, 1979).
Shugaban Jam’iyyar PRP na Ƙaramar Hukumar Birnin Kano da kewaye
ne yake yi wa ‘ya’yan jam’iyyar bayani dangane da manufofin jam’iyyar PRP kamar
yadda aka kafa ta. An sani cewa jam’iyyar PRP gyauron jam’iyyar NEPU ce, wannan
ya sa ko a manufofin jam’iyyar ma ba su saɓa wa juna ba, domin an ɗora ne daga inda
NEPU ta asali ta tsaya. Daga cikin manufofin kamar yadda ya yi bayani, ya nuna cewa
jam’iyyar PRP ce kaɗai za ta ita ceto al’umma daga halin ƙuncin da suke ciki na
danniya da zaluncin masu mulki. Haka kuma za ta tsamo talaka daga cikin ƙangin fatara
da talaucin da yake ciki ta hanyar samar masa da hanyoyin samuj abubuwan buƙatun
rayuwa. Ya kuma bayyana cewa, daga cikin manufofin jam’iyyarsu akwai yaƙi da jahilci
ta hanyar wadata hanyoyin samun ilimi tare da magance matsalar cin dukiyar talakawa
ta hanyar sace dukiyar ƙasa. Idan aka duba za a ga cewa manufofin jam’iyyar ne ya
kawo su a dunƙule domin faɗa wa talakawa irin tanadin da jam’iyyar ta yi masu.
Tun farkon siyasar Jam’iyyu a Arewacin Nijeriya, kowace jam’iyyar
siyasa takan samar wa da kanta tutar da take amfani da ita. Wannan tutar takan kasance
mai ɗauke da launuka da wasu alamomi da akan bai wa wasu ma’anoni da sukan wakilci
manufofin jam’iyya. A cikin wani jawabi na Malam Aminu Kano a jamhuriya ta biyu,
ya kawo bayani a kan launukan tutar jam’iyyar PRP kamar haka:
“Jam’iyyar tana da tuta
mai launuka uku, an shirya su a tsaye, launin ja a sama, fari a tsakiya da baƙi
a ƙasa. Launi ja yana nufin babban aikin da yake gabanmu, fari kuwa yana nufin nasara
bayan jajircewa, baƙin kuma yana nufin ‘yanci bayan mulkin mallaka na jari-hujja
da ƙasashe masu bin tsarin jari-hujja da kuma mulkin gargajiya a Nijeriya. Da akwai
mabuɗin gwal a ɓangaren farin a jikin tutar, wanda yake nufina mabuɗin nasara na
sabuwar Nijeriya, a inda babu wani ƙuduri na rashin gaskiya a kan talaka ”
(Jega da wasu, 2002:18).
Idan aka dubi jawabin za a fahimci cewa, manufofin jam’iyyar
PRP ne aka bayyana, inda ake yi wa jam’iyyar taken “mutunci da jajircewa”. A cikin
bayanin launukan tutar jam’iyyar ya yi bayanin manufofin da jam’iyyar take kai ne,
inda ya nuna cewa, launin ja yana nufin jan aiki na tsayuwa tsayin daka da jajircewa
ba tare da tsoro ko shakka ba wajen ganin an kai ga nasarar abin da aka sanya a
gaba. Launin fari kuwa yana nufin nasara bayan dagewa da juriya har a kai ga cimma
buri. Shi kuwa launin baƙi yana nufin samun ‘yanci daga mulkin mallaka na ‘yan jari-hujja
da danniya da babakere na sarakunan gargajiya. Wannan ya nuna manufofin siyasar
jam’iyyar PRP ne a taƙaice kamar yadda kowacce jam’iyya takan fito da nata.
Irin wannan misalin ya fito a cikin littafin Tura Ta Kai Bango, inda shugaban jam’iyyar
Riƙau ya bayyana ma’anar launukan da suke jikin tutar jam’iyyarsu kamar haka:
“ taken jam’iyyarmu shi ne ‘zumunci’ kana ga tutar
jam’iyyarmu fari da rawaya. Farin na nufin zaman lafiya da kwanciyar hankali. Rawayar
kuwa, yana nufin wadata jin daɗi da sakewa.”
(Katsina, 1983:8).
A nan idan aka duba yana bayani ne a kan manufofin jam’iyyarsu
ta Riƙau, inda ya danganta su da launukan da suke jikin tutar jam’iyyarsu, wato
manufarsu samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma da kuma wadata
‘yan ƙasa su samu sakewa da jin daɗin rayuwa.
Irin waɗannan manufofin na siyasar jam’iyyu sun bayyana a cikin
tarihin siyasar jam’iyyu kamar yadda suka fito a cikin ayyukan rubutaccen zube na
Hausa, waɗanda su ne ‘yan siyasa suke amfani da su a matsayin manufofinsu ga al’umma,
kamar yadda ya fito a cikin wannan misalin:
“Bayan da ya sauka, sai
mai gabatarwa ya gabatar da wani wanda zai yi bayani a kan manufa da sauran abubuwan
da jam’iyyar ta ƙunsa. Yana faɗa musu cewa, ita jam’iyyarsu ta yi alƙawarin ba da
isasshen ruwan sha in an zaɓe ta. Za ta ba da ilimi mai inganci. Za ta wadatar da
gidaje, da inganta noma da kuma girmama sarakunan gargajiya.”
(Katsina, 1983:7).
A wannan misalin an ga yadda ‘yan siyasa suke yin bayanin manufofin
jam’iyyunsu ga al’umma, inda a nan aka nuna cewa an yi wa jama’ar da suka halarci
taron gangamin yaƙin neman zaɓe ne bayanin irin abin da jam’iyyar ta ƙudurta za
ta yi wa al’umma domin jin daɗin rayuwarsu. Sun nuna cewa za samar da ingantaccen
ruwan sha mai tsafta, da ilimi mai inganci wanda za su kore duhun jahilci da kuma
samun cigaban rayuwa. Haka kuma jam’iyyar za ta samar da muhalli ta hanyar gina
gidaje ga al’umma, da kuma inganta hanyoyin samar da abinci na noma, sannan kuma
za ta tabbatar da kiyaye ƙima da darajar masarautu da sarakanunan gargajiya. Idan
aka duba za a ga cewa, jam’iyyar Riƙau ce take bayyana manufofinta, abubuwa ne na
jin daɗi da kyautata rayuwar al’umma jam’iyyar take bayyanawa domin neman shugabancin
jama’a. Wannan kuwa al’adar siyasar jam’iyya ce, ta yadda kowacce jam’iyya za ta
faɗi nata manufofin domin jama’a su yi alƙalanci.
A nasu ɓangaren ‘yan jam’iyyar Sauyi suna ganin cewa, ai bai
ce komai ba tun da bai yi batun talaka ba, ya kamata jam’iyyar ta bayyana irin tanadin
da ta yi wa talakawa, tun da dai ta ambaci girmama masu riƙe da sarautar gargajiya,
shi kuwa talaka fa? Dubi abin da Hassan Wurjanjan yake ce wa abokinsa Sabo Garba
wanda suka halarci wurin taron tare:
“Ni ban ji ya yi maganar
‘yancin talaka ba, wanda kuma kusan kansa ne komai ke ginuwa!”
(Katsina, 1983:8).
A ganin ‘yan jam’iyyar hamayya Sauyi ai talaka shi ne ake mulka,
kuma dole a yi masa gurbi a cikin manufofin kowacce jam’iyya, domin duk wani abu
na ci gaba da za a samar domin amfaninsa ne. Don haka dole in ana so siyasar kowacce
jam’iyya ta karɓu kuma a yi adalci, to a sanya batun kyautata rayuwar talakawa a
kan gaba.
Wannan ya nuna cewa, akwai manufofi da dama da suke ƙunshe a
cikin siyasar jam’iyyu, waɗanda suka fito a cikin ayyukan zube na Hausa, waɗanda
‘ya’yan jam’iyyu kan riƙa bayyana wa al’umma domin samun amincewa da goyon bayansu.
Ga wasu daga cikin iri-iren waɗannan manufofin kamar haka:
5.1.1 Samar Da Walwala Ga ‘Yan Ƙasa
Samar da walwala ga ‘yan ƙasa muhimmin al’amari
ne a cikin manufofin siyasa, kasancewar walwalar al’umma shi ne ƙashin bayan rayuwa.
Walwala na nufin fara’a ko sakin fuska (Bargery, 1934: 1078 da CNHN, 2006: 467).
A wata ma’anar kuma an bayyana walwala da cewa, samun hutu da kasancewa cikin jin
daɗi da kwanciyar hankali (Paul da Roxana, 2020: 255). Shi kuwa Bunza (2023: 8)
ya bayyana walwala da cewa, samun sukunin gudanar
da rayuwa ne cikin jin daɗi da sakewa. Wannan ya ƙunshi samun zaman lafiya da kariyar
mutunci da tattalin arziki da sauran abubuwan da rayuwa take buƙata. Ta la’akari da waɗannan ma’anonin za a
iya cewa, walwala ta shafi sakewa da wadatar da al’umma da kayayyakin more rayuwa
da harkokin kasuwanci da zama cikin aminci da neman na kai da dai sauransu.
A cikin tarihin siyasar jam’iyyu tun daga farko, ‘yan siyasa
sukan bayyana wa al’ummarsu cewa suna da manufar samar masu da walwala a cikin rayuwarsu,
sai dai akan samu yanayin da masu riƙe da madafu iko kan takura wa al’ummarsu da
saninsu ko ba da saninsu, ta yadda dukkan wasu abubuwa da kan samar da walwalar
kan kasance babu su, ko kuma al’umma ba su samun kaiwa gare su.
Muhimmancin walwala ga jama’a yana daga cikin dalilan samun ‘yancin
kan ƙasa, domin zai bai wa ‘yan ƙasa damar sarrafa arziƙin ƙasarsu wanda zai samar
masu da abubuwan yi domin gudanar da rayuwarsu cikin sauƙi. Rashin ‘yanci yakan
tauye dukkan waɗannan abubuwa sai ‘yan ƙasa su rasa samun walwala da jin daɗin rayuwa
su kasance cikin ƙunci da damuwa. Hakan yana faruwa ne saboda kasancewar sha’anin
mulkin ƙasa yana hannun wasu mutane na daban waɗanda ma ba ‘yan ƙasar ba, waɗanda
suke tatsar arziƙin ƙasar suna tafiya da shi suna inganta ƙasashensu.
Tun a jamhuriya ta farko, wani da ya fahimci manufar siyasar
jam’iyyu
ya bayyana haka a ciki wata wasiƙa da ya aika wa jaridar Daily comet, inda a ciki ya ce:
“ domin idan kuka duba
za ku ga cewa mulkin kai ana son sa ne saboda jin dadi da zaman lafiya na jama’a,
da samun arzikin kasa da kuma walwala.”
(Gasakas,1961).
A wannan gaɓar an nuna manufar jama’a su zama masu mulkin kansu
da kansu. Mulkin kansu da kansu shi yake bayar da damar shimfiɗa wa kowane ɗan ƙasa
walwala domin ya ji daɗin ni’imar arziƙin ƙasarsa. Shi yake ba da dama a samu zaman
lafiya a cikin jama’a domin masu mulki da talakawa dukkansu ‘yan ƙasa ne, uwa ɗaya
uba ɗaya. Shi ne mulki na babu cuta babu cutarwa ga ƙasa da alummar cikinta. Shimfiɗa
irin wannan tsari shi ne yake haifar da jin ɗaɗi ga ‘yan ƙasa, ya kuma sanya su
ji cewa a ƙasarsu suke rayuwa ba a wata ƙasa ta daban ba.
Tun farkon siyasar jam’iyyu an riƙa samun irin wannan yanayi
da kan kasance al’umma sun tsinci kansu a cikin ƙunci wanda a wasu lokuta kan haifar
da ƙorafe-ƙorafe daga talakawa. Irin wannan ƙorafe-ƙorafen sun riƙa bayyana a cikin
ayyukan rubutaccen zuben Hausa. Alal misali, a cikin jaridar Daily Comet da ta buga wata wasiƙa wanda
aka yin ƙorafi kan wani wakilin gwamnati kamar haka:
“Ina rokon Edita ya ba
ni fili domin na baiyana wani bakin mulki da shishigi da tsorata talakawa da yaudara
da wani wakilin NPC mai wakiltar wani bangare a kasar Gumel yake yi wa talakawan
kasar. Wannan mutum ko kuma mutumin da yake da irin wannan hali bai kamata a ba
shi amanar riƙon jama’a ba. amma da ya ke Gwamnatin NPC taro ne na masu son kansu
wato namu naku naku naku, sai aka danka wa Wazirin Gumel NA sukutum shine mai ja
mata gora. Mun sani kawace NA ta jihar Arewa haka abin yake, amma ba a samu wata
NA wanda shugabanta yake gwada wa Talakwa azaba da nuna bambanci irin na Gumel ba.”
(Ɗanjani, 1961).
A cikin wannan wasiƙar an yi ƙorafi ne kan takura da rashin walwalar
da al’ummar wani yanki na ƙasar Hausa suke ciki, inda suka ɗora alhakin wannan rashin
walwalar da suke ciki a kan gwamnati domin haƙƙinta ta samar masu da walwala da
jin daɗi. A cikin wasiƙar an nuna yadda talakawa suke cikin tsoro da rashin tabbas,
wanda wakilin gwamnati na ƙasar Gumel ya jefa su a ciki. An nuna cewa duk mutum
mai hali irin nasa na ƙuntata wa talaka bai kamata a ba shi wakilcin jama’a ba.
sun nuna cewa yana ƙuntata wa talakawa tare da gana masu azaba, wanda wannan ya
tauye masu hakkin walwala da jin daɗi, wadda kuma babbar manufa ce ta mulkin siyasar
da ake ciki.
Samar da walwala abu ne mai muhimmanci a cikin manufofin siyasar
jam’iyyu,
domin kowace jam’iyya manufofinta ba su cika ba tare da sanya wannan manufar a cikin
manyan manufofinta ba. Domin kuwa ya ƙunshi wasu manufofin da dama a cikinsa, kamar
su ‘yanci da tsaron rayuka da wadata da sauransu.
Malam Aminu Kano ya tabbatar da wannan a cikin wani jawabinsa,
inda ya nuna cewa inganta rayuwar jama’a da samar masu da zaman lafiya shi ne abin
da tsarin guguzu wato gwamnatin son gina jama’a take da manufar yi. Tsari ne wanda
ba zai tauye ‘yancin ‘yan ƙasa ba. Ga abin da ya ce:
“A Nijeriya a tsarin gwamnatin
son-gina-jama’a (gurguzu) da ake da buƙata shi ne wanda ba zai sarayar da ‘yancin
ƙasa ba; wanda ba zai kasance kwatankwacin na waɗansu ƙasashen ba. Inganta rayuwar
jama’a da samar wa jama’a da zaman lafiya su zama su ne ginshiƙin wannan aƙida da
Nijeriya ke son ɗabbaƙawa.”
(Jega da wasu, 2002:155-156)
A nan yana magana ne a kan inganta rayuwa da walwalar al’umma,
inda a ganinsa zaman lafiya shi ne tushen walwalar al’umma, sannan kuma yalwar arziƙi
shi ne ke haifar da zaman lafiya wanda ke haifar da walwalar da ake son samarwa
a Nijeriya. Idan ya kasance an samar wa da ‘yan ƙasa ingantaccen yanayi na zaman
lafiya da kwanciyar hankali, sukan samu damar gudanar da harkokinsu ba tare da matsala
ba. Idan kuwa aka samu irin wannan yanayin to tattalin arziƙin al’umma yakan bunƙasa
wanda shi ne yake buƙasa tattalin arziƙin gwamnati. Bunƙasar tattalin arziƙin al’umma
kuma yakan haifar da zaman lafiya a tsakaninsu domin babu wanda yake cikin ƙuncin
da zai sanya shi duban abin hannun wani. Ke nan samar wa da al’umma walwala yakan
taimaka wajen samar da zaman lafiyar al’umma.
Malam Aminu Kano ya ci gaba da bayyana cewa, walwalwar da ake
fafutukar samar wa ‘yan ƙasa bai tsaya a kan maza kaɗai ba, har da mata da yara
ƙanana, inda ya nuna cewa jam’iyyarsu za ta bayar da kyakkyawar kulawa gare su,
ta hanyar bunƙasa manya da ƙananan sana’o’i kamar su noma da jima da rini da saƙa
da sauranasu, domin bunƙasa tattalin arziƙi da kuma samun walwala da sauƙin rayuwa.
Ga abin da aka tsakuro daga jawabin nasa:
“Game da ‘yanci da walwalar
yara da matasa da mata ma, wannan jam’iyya za ta bayar da kyakkyawar kulawa ga manoma
da sauran masana’antu, kamar masu sana’ar hannu,wanda wani ɓangare ne da muka dogara
da shi wajen bunƙasar tattalain arzikinmu. Za mu tabbatar da an sauƙaƙa wa kowane
ɗan kasuwa da mai sana’ar hannu irin su: rini da jima da saƙa da saƙar dinkin tabarma
da sauransu ”
(Jega da wasu, 2002:18).
Ke nan, idan aka duba misalin da suke sama, za a fahimci cewa
samar da walwala ga ‘yan ƙasa ya shafi inganta hanyoyin samun abin hannunsu na more
rayuwa, wanda da shi ne suke gudanar harkokinsu na yau da kullum ba tare da matsaloli
ba. Irin waɗannan ingantattun hanyoyin da akan samar wa al’umma don su yi amfani
domin inganta walwalalrsu sun shafi inganta ayyukan noma, wanda ya kasance babbar
hanyar rayuwa ce da al’ummar ƙasar Hausa suka yi riƙo da ita tun fil azal, kuma
inganta wannan sana’ar zai samar da hanyoyin samun kuɗin shiga ga al’umma da kuma
gwamnati. Haka kuma, samarwa da inganta sana’o’in hannu domin dogaro da kai, shi
ma zai ƙara bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa da na al’umma. Idan aka buƙasa sana’o’in
hannu za su taimaka wa al’umma wajen samun abin biyan buƙatun yau da kullum domin
guje wa faɗa wa cikin ƙuncin da damuwa. Irin wannan ƙorafi na rashin samar da walwala
ga ‘yan ƙasa ya fito a cikin littafin Tura
Ta Kai Bango inda marubucin ya nuna cewa, waɗanda al’amarin jagorancin ƙasa
yake hannunsu suna amfani da damar da suke da ita wajen ƙara tsauwala wa rayuwar
talaka, maimakon su yi amfanin da wannan damar wajen samar da walwala da jin daɗin
jama’a tare da inganta rayuwarsu, kamar yadda ya ce:
“Wannan ma haka take game
da wahalolin da ni da kai muke sha wajen tsauwalar da muke fama da ita daga hannun
waɗanda aka bai wa jagorancinmu. Ana mayar da hanyoyi da ya kamata a yi amfani da
su don inganta rayuwarmu suna zama hanyoyi na ƙara bautar da mu. Kuma sun dage don
ganin cewa mun dauwama a bayinsu su kuma iyayen gijinmu.”
(Katsina, 1983: 28).
Idan ana batun walwalar al’umma dole ne a samu mafita ga wasu
matsaloli da suke zama tarnaki ga samun walwalar, waɗannan abubuwa kuwa shugabanni
ne ya kamata su gano su don su yi ƙoƙarin magance su. Kada ya zama hanyoyin da za
su inganta rayuwar al’umma don samun walwala sun salwanta don sakacin mahukunta.
Da zarar an samu magance irin waɗannan matsaloli rayuwa za ta inganta, matsaloli
za su kau, sai kuma walwalar da ake nufi ta samu tare da ingantacciyar rayuwar ‘yan
ƙasa.
A jamhuriya ta huɗu ma irin wannan manufa ta samar da walwala
ga ‘yan ƙasa ta fito a cikin Jaridar Gaskiya
Ta Fi Kwabo, inda ta kawo jawabin ɗan takarar shugabancin Nijeriya na Jam’iyyar
APP a Shekara 1999, Alhaji Lema Jibrilu, a wajen taron ayyana takararsa a Katsina.
Ga abin da ya ce:
Guguwar sauyin da take
kaɗawa a duniya tana nufin a yanzu babu sauran danne wa jama’a haƙƙinsu da sunan
shugabanci. Dole ne a mayar da hankali wajen inganta rayuwar jama’a da tattalin
arziƙinsu. Saboda haka Nijeriya tana buƙatar shugabancin ƙwarai shugabancin da zai
fitar da ita daga cikin ƙangin zalunci da danniya.
(“Shirin Gina Ƙasaitacciyar Ƙasa”, 1999).
Kasancewar ana shirin dawo da mulki hannun farar hula ne wanda
zai samar da jamhuriya ta huɗu a shekarar 1999, a lokacin da aka buga kugen siyasa
sai ‘yan takara suka riƙa fito da manufofin jam’iyyunsu da suke son tsayawa takara
ƙarƙashinsu. Kamar yadda misalin da yake sama ya nuna walwalar al’umma shi ne abu
mafi muhimmanci a cikin manufofin siyasa, domin kusan dukkan waɗansu abubuwa sukan
zo ne a bayansa ko ma a ƙarƙashinsa. A nan jawabin ɗan takarar ya nuna cewa dole
ne a kula da wajen inganta rayuwar al’umma. Idan kuwa aka yi batun inganta rayuwar
al’umma to ya zama tilas a sanya walwalarsu a ciki domin kuwa babu yadda za a yi
rayuwa ta inganta ba tare da ingantacciyar walwala ba. A cikin jawabin nasa ya kuma
nuna cewa inganta tattalin arziƙin al’umma ita ma tana cikin manufar jam’iyyarsu
da kuma takararsa. Shi kuwa ingantaccen tattalain arziƙi kamar yadda aka yi bayani
a sama yana samar da ingantacciyar rayuwa mai cike da walwala.
5.1.2 Wadata ‘Yan Ƙasa
Kalmar wadata tana nufin gamsuwa da abin da ake da shi na dukiya
ko wani abin da aka mallaka (Paul da Roxana, 2020: 253). Shi ƙuwa Ƙamusun Hausa
ya ce kalmar tana nufin yalwanta (CNHN, 2006: 464). Bargery (1934: 1072) Ya bayyana
kalmar wadata da cewa, samun yalwar arziki. Idan aka dubi ma’anonin biyu za a iya
cewa wadata tana nufin samar da abin biyan buƙatar rayuwa cikin sauƙi domin sauƙaƙa
rayuwa.
Ke nan, wadata ‘yan ƙasa yana nufin sama wa ‘yan ƙasa hanyoyin
samun yalwa ta fuskar arziƙi da samun abin da za su riƙa gudanar da rayuwarsu cikin
sauƙi. Wannan ya shafi buɗa masu hanyoyin samun arziƙi ko ƙaruwarsa ko kuma a kawo
masu wasu abubuwa na jin daɗin rayuwa waɗanda ba su da shi kuma ba su da wadatacce.
Daga cikin manufofin siyasar jam’iyyu akwai wadata ‘yan ƙasa wanda shi ma abu ne
mai muhimmanci wanda ‘yan siyasa kullum suke kumfar baki a kansa. Talauci a cikin
al’umma babbar illa ce da kan haifar da munanan abubuwa kamar manyan laifuka da
suka shafi fashi da makami da kashe-kashe da tashe-tashen hankula da dai sauran
nau’o’in matsalolin waɗanda sukan haifar wa da ƙasa ci baya.
A kodayaushe ‘yan siyasa sukan riƙa bayyana hanyoyin da za su
bi wajen samar wa da a’umma abubuwan da za su fitar da su daga ƙangin talauci, su
samu wadata da yalwar arziƙi. Siyasa tana tafe ne da wannan manufar, kuma a kullum
yana cikin abubuwan da ake bayyana wa mutane domin neman goyon bayansu.
A cikin ayyukan rubutaccen zuben Hausa an samu wani abu na tarihin
ginuwar siyasa Nijeriya, inda irin wannan manufa ta riƙa fitowa. Alal misali, Malam
Aminu Kano ya fito da wannan batun wadata ‘yan ƙasa a cikin wani jawabi nasa. Dubi
abin da aka tsakuro daga cikin jawabin:
“ bai wa ‘yan Nijeriya
da kamfanoni masu zaman kansu ƙwarin gwiwa da ma kawar da rashin daidai wajen raba
dukiyar ƙasa; sai kuma ƙirƙiro wani yunƙuri da zai kawo wa kowane ɗan ƙasa hanyar
samun kuɗin shiga ko dogaro da kai.”
(Jega da wasu, 2002:143).
A nan yana bayani ne a kan manufofin jam’iyyar PRP inda yake
nuna cewa, za a ƙarfafa wa ‘yan Nijeriya da kamfanoni masu zaman kansu guiwa wajen
raba dukiyar ƙasa wanda zai amfani kamfanoni wajen bunƙasa ayyukansu da kuma samar
wa da ƙasa kuɗaɗen shiga wanda zai bunƙasa tattalin arziƙi, sannan kuma su kansu
ɗaiɗaikun mutane a samar da wani shiri da zai kawo masu hanyoyin shigar kuɗi a aljihunsu.
Wannan kuwa idan aka duba manufa ce ta wadata ‘yan ƙasa, kamfanonin da za a bunƙasa
masu zaman kansu ne, wanda kuma akwai mutane da dama da suke aiki ƙarƙashinsu waɗanda
za su riƙa samun kuɗin shiga.
A jamhuriya ta huɗu ma
ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a shekarar 1999, Cif Olushegun Obasanjo
ya bayyana manufofin jam’iyyarsa dangane da wadata ‘yan ƙasa, inda ya nuna hanyoyin
da za su bi wajen tabbatar da ganin ‘yan ƙasa sun wadata. Ga abin da jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ruwaito:
“ ya ce zai ba su wasu
gurabe a cikin gwamnatinsa don taimaka musu da aikin yi a matsayin muƙamin tarayya
da kuma wadata matan da abubuwan more rayuwa na yau da kullum kamar yadda ya taɓa
yi a can baya a lokacin da ya shugabanci ƙasar.”
(Ahmed, 1999)
Idan aka duba za a ga cewa, ɗan takarar da jam’iyyar PDP ɗin
ta tsayar ya bayyana wa mata manufarsa ta wadata su da abubuwan more rayuwa ne,
inda ya bayyana masu cewa, a ciki zai sama masu ayyukan yi a matakin tarayya. Ayyukan
da za a samar masu za ta zama wata hanya ce ta buƙasa tattalin arziƙinsu, wanda
zai sauƙaƙe masu wahalhalu na rayuwa. Haka kuma wada su da abubuwan more rayuwa
zai kasance samar masu da abubuwan jindaɗi ne waanda zai sa rayuwa ta yi sauƙi a
gare su. Irin wannan manufar ba mata kaɗai ba, har da maza ma ya shafa domin dukkansu
‘yan ƙasa ne kuma ba za a yi wa wani a bar wani ba.
5.1.3 Sama wa Ƙasa da
‘Yan Ƙasa ‘Yanci
Ayyukan adabi da dama musamman na zube sun fito da yadda manufofin
siyasar jam’iyyu suka ƙunshi samar da ‘yanci ga ‘yan ƙasa. Bargery (1934: 1103-1104)
ya bayyana ‘yanci da cewa, yananyi ne da mutum yakan kasance a sake ba tare da kasancewa
ƙarƙashin bauta ba. A cikin Paul da Roxana (2020: 267) an bayyana ‘yanci ta fuskoki
daban-daban kamar haka:
i- Na Farko, ‘yancin kan ƙasa
ii- Na biyu, ‘yancin ɗan’adam
iii- Na uku, nuna halayya da ɗabi’u a matsayin ɗa, tare da
kare mutuncin da ƙima da darajar mutum (musamman mata). Dukkan ma’anonin da ya
kawo suna da alaƙa da wannan batun, kasancewar ana magana ne a kan samar wa da
ƙasa da ‘yan ƙasar ‘yancin gudanar da al’amura ba tare da tsangwama ko takurawa
ba.
Ƙamusun Hausa na CNHN, (2006:484) ya bayar da ma’anoni uku dangane
da kalmar ‘yanci kamar haka:
i- Kasancewar mutum ɗa ba bawa ba.
ii- Samun damar aiwatar da wani abu ba tare an nemi izini ba
a wajen wani.
iii- Samun mulkin kai na ƙasa daga hannun ‘yan mulkin
mallaka.
Idan aka dubi waɗannan ma’anonin guda uku za a ga cewa dukkansu
suna da alaƙa da wannan aiki, domin kuwa a wannan gaɓar ana maganar samar wa da
ƙasa da ‘yan ƙasa ‘yanci ne. Idan aka dubi ma’ana ta farko za a iya danganta ta
da ‘yanƙasa waɗanda suke rayuwa a cikinta, waɗanda za su so su yi rayuwa a sake
ba tare da takura ko muzgunawa ba daga wano ko wasu. Kasancewarsu ‘yan ƙasa za su
so su kasance suna da iko a ƙasarsu tun da ba su da wata ƙasar da ta wuce ta. Don
haka a ba su dama su mori yanayi mai daɗi na ƙasarsu maimakon a takura masu a mayar
da su tamkar bayi a ƙasarsu ta haihuwa.
Haka ma a ma’ana ta biyu, ‘yan ƙasa suna da buƙatar samun damar
aiwatar da abubuwan da suke so don jin daɗinsu, ba tare da sun nemi sahalewar wani
ba. Kamar dai mai gida ne da gidansa, ba shi da buƙatar neman izinin wani idan yana
si ya yi amfani da wani ɓangare na gidan ko wani abu makamancin haka.
Ma’ana ta uku kuwa tana nufin samun ‘yancin kai daga ‘yan mulkin
mallaka, waɗanda a farkon siyasar jam’iyyu su ne suke juya akalar shugabancin ƙasar
ƙarƙashin jagorancin Ingila,wanda daga bisani bayan fafutukar ‘yan ƙasa aka samu
mulkin kai. Ke nan, akwai buƙatar ‘yancin ta kowa ne fuska, wato ‘yancin ƙasa da
kuma ‘yancin ‘yan ƙasa. Saboda haka samar wa da ƙasa da ‘yan ƙasa ‘yanci yana nufin
a bai wa ƙasar damar gudanar da mulkin kanta ta hanyar sarrafa albarkatun ƙasarta
da kuma juya su ta yadda ‘yan ƙasar za su ci amfaninta ba tare da katsalandan ɗin
wani ko wasu daga ƙetare ba.
A jamhuriya ta farko, ‘yan siyasa da jam’iyyunsu
sun riƙa bayyana manufofinsu na neman ‘yanci kan ƙasa ne baki ɗaya, daga baya kuma
bayan an samu ‘yanci daga Turawan mulkin mallaka, sai ‘yan ƙasa suka ci gaba da
bayyana manufar samar wa da ‘yan ƙasa ‘yancin rayuwa da na gudanar da al’amuran
da suka shafi cigaban ƙasa da na harkokin yau da kullum. Ala misali, har a yau wasu
suna ganin cewa suna ne kawai an samu ‘yancin kai, amma a zahiri ba ‘yancin kai
aka samu ba, mulkin kai ne aka samu, amma ikon sarrafa albarkatun ƙasar da kuma
juya akalar al’amuran ƙasar har yanzu dai ba a rabu da bukar ba. Haka batun ‘yancin
‘yan ƙasa wajen gudanar da al’amuran rayuwa, da sauran abubuwan da rayuwar take
buƙata kamar tsaro da sauran abubuwan jin ɗaɗin rayuwa, shi ma ba a san daɗin ‘yanci
ba, a suna ne kawai ake cewa an samu ‘yanci.
Jam’iyyun siyasa musamman masu hamayya da gwamnati suna ganin
cewa gwamnati mai mulki a jamhuriya ta farko bakinsu ɗaya ne da Turawa, wannan ya
sa suke ganin cewa an yi ta jan ƙafa dangane da batun samun ‘yancin kan ƙasa daga
Turawa. Wannan ya sa suka miƙe, suka yi ta sukar jam’iyya mai mulki tare da nuna
cewa zama ƙarƙashin mulkin Turawa ba abu ne da zai haifar wa da ‘yan ƙasa cigaba
mai ma’ana ba. Haka kuma ko bayan samun ‘yancin kai daga Turawa, ‘yan hamayya sun
riƙa bayyana cewa, suna ne kawai an samu ‘yanci, amma har yanzu talaka yana cikin
ƙangin bauta da talauci. Irin wannan ya fito a cikin ayyukan adabi na zube da dama.
Ga misalin wata wasiƙa da aka tsakuro daga jaridar Daily Comet:
“ na yi mamaki da ache
ƙasa muhimmiya a idon duniya kamar Nigeria a che ta samu mulkin kan ta amma a che
wani bangare daga chikin Nigeria ba su ji kanshin ‘yanchi ma dadin danne su da aka
yi. Wato babu shakka a nan Arewa ba mu san an samu ‘yanchi ba, dalili kuwa shi ne,
Nigeria ta samu ‘yanchin kanta maimakon mu ga danne mun da ake ta yi shekara da
shekaru mun samu kuɓuta, sai gwamnatin Arewa ta ƙalƙalo wata doka wai ita penal
code wadda ta ƙara nuna danne mu mu talakawan ƙasa Gwamnatin Arewa wadda NPC ke
rike da ita ba ta ma nuna bambancin dadin mulkin kai ba da rashin dadin saba ”
(Kano, 1961).
Kamar yadda aka gani cikin wannan misali, ‘yan hamayya na Jam’iyyar
NEPU ne suke ƙorafin cewa, sun kasa bambance tsakanin zamanin mulkin mallaka da
kuma bayan samun ‘yancin kai, domin kuwa al’ummar ƙasar Hausa sun yi tsammanin cewa,
bayan Turawan mulki sun bar Nijeriya ‘yan ƙasa za su samu cikakken ‘yancin rayuwa
ba tare da matsi daga shugabanni ba. Duk da a cikin wasiƙar an nuna cewa wasu yankunan
na Nijeriya sun fara ɗanɗana daɗin ‘yancin, amma sai aka nuna cewa, Arewa ba a ma
ji ƙamshinsa ba, domin irin salon mulkin danniyar da ake fama da shi lokacin Turawa
wanda sarakuna suke yi bai sauya ba. A ciki an nuna cewa gwamnatin NPC ta ƙirƙiro
wasu dokoki waɗanda talakawa suka yi ƙorafin cewa don su aka yi dokokin don a ƙara
danne su. Wannan ya sa suka koka cewa ba su ɗanɗani daɗin ‘yancin da aka ce an samu
ba.
A jamhuriya ta biyu ma ba ta sake zane ba, domin idan aka duba
za a ga cewa, a kodayaushe ‘yan ƙasa suna fafutukar samun ‘yancin gudanar da rayuwa
cikin sauƙi ba tare da takurawa ko tasananta wa daga shugabanni ba. Wannan ‘yancin
shi ne zai sa al’umma su samu walwala da jin daɗi, kuma su fahimci cewa su ma ‘yaya
ne ba bayi ba. Haka kuma samun cikakken ‘yancin ƙasa yana bai wa ‘yan ƙasa damar
aiki tuƙuru wanda hakan zai haifar da haɓakar tattalin arziƙin ƙasa wanda zai amfani
al’umma baki ɗaya. A tarihin siyasar jamhuriya ta biyu an samu wani bayani mai ɗauke
da irin wannan fasalin, wanda ya fito a cikin wani jawabi na Malam Aminu Kano, inda
yake bayyana manufofin jam’iyyar PRP cewa:
“Samun cikakken ‘yancin
ƙasa domin a sake ƙarfafar shugabanci da cikakken ‘yancin kai, jam’iyyar PRP ta
ƙuduri aniyar gina tattalin arziƙin ƙasa daidaitacce da zai dogara da kansa kuma
mai ɗorewa, kana zai kasance tattalin arzikin da ya shafi cigaban al’umma. Tabbatar
da wannan tsari ya haɗar da kawar da zalunci da samun cikakken ikon bunƙasa tattalin
arziki ƙasa ba tare da nuna son kai ba ”
(Jega da wasu, 2002:143).
Al’ummar ƙasa ba za su taɓa zama masu cikakken ‘yanci ba har
sai ƙasar ta samu cikakken ‘yanci daga wasu ƙasashe domin samun cin gashin kai.
Wannan shi ne zai tabbatar da ginuwar tattalin arziƙin ƙasa da kuma ɗorewarsa, wanda
zai bai wa al’umma damar gina kansu da kuma samun ingantacciyar rayuwa. Duk wannan
ba zai samu ba har sai an kawar da zalunci da danniya da babakere, domin samun cikakken
ikon bunƙasa ƙasa ba tare da nuna son kai ko bambanci ba.
Batun ‘yancin ƙasa da na al’ummar ƙasa ya ci gaba da bayyana
cikin ayyukan adabin Hausa na zube,wanda hakan ya nuna kasancewar waɗannan batutuwa
wani ɓangare na tarihin siyasar jam’iyyu a Arewacin Nijeriya, Duk inda batun ya
fito akan nuna irin muhimmancin da ‘yancin ƙasa da na ‘yan ƙasa yake da shi a cikin
rayuwa, wanda ‘yancin ne zai ba su damar gudanar da rayuwa a ƙasar haihuwar su batare
da tsangwama ko takura ba kamar yadda wannan misali da yake ƙasa ya bayyana manufofin
siyasar jam’iyyu. Ga misalin:
“Mene ne manufar jam’iyyar?
Sun kuwa sha bamban ƙwarai da waɗanda suka riga su zuwa nan?
Ai ko ma hanya ba su haɗa
ba. Domin ban da ruwan sha da isasshen abinci da hanyar mota da ita ma sauran ɗaya
jam’iyar ta yi, ta ma yi alƙawarin kawar da dukkan wani abu da yake mayar da mutane
su zama kamar bayi a garuruwan da aka haife su, aka kuma haifi iyayensu. A taƙaice
ta yi niyyar kare talaka daga dukkan wata wahalarwa da handama. Za a sakar wa mai
rauni wuya ya numfasa.”
(Katsina, 1983: 17).
Kowace jam’iyya takan yi ƙoƙarin bayyana irin manufofinta ga
jama’a domin neman goyon bayansu. A cikin wannan misali an gani cewa jam’iyyar Riƙau
ce ta fara bayyana manufofinta ga al’ummar garin Kabobi, inda suka bayyana cewa,
za su samar wa da al’umma kayayyakin more rayuwa, kuma za su tabbatar sun samar
masu da isasshen ruwan sha da abinci da hanyar mota da dai sauran kayan kyautata
zaman jin daɗin rayuwa. Ita kuwa jam’iyyar hamayya wato Sauyi da ta zo bayyana nata
manufofin bayan ta bayyana waɗannan manufofin na samar abubuwan sauƙaƙa jin daɗin
rayuwa da jam’iyyar riƙau ta bayyana, sai kuma ta ƙara da ‘yancin rayuwa ta yadda
za su yi rayuwa a matsayinsu na ‘yan ƙasa masu ‘yanci. Samar da wannan ‘yancin shi
ne zai bambanta su da bayi waɗanda suke kullum cikin hidimar ubangidansu ba tare
da samun damar yin rayuwa yadda suke buƙata ba. Hakan zai ba su damar sarrafa dukiyar
ƙasarsu domin samun biyan buƙatun rayuwarsu da kuma yin rayuwa cikin sauƙi da walwala.
A wani misalin da yake nuna manufofin siyasar jam’iyyu kuma an
nuna cewa, ‘yancin talaka ya shafi tabbatar da warware masa dukkan wani dabaibayi
da tarnaƙi da aka sanya masa, wanda ya hana shi motsi. Dubi abin da marubucin ya
ce:
“Ita jam’iyyar Neman Sauyi
ba wai ta yi niyyar kawo wa dukkan talakawan ƙasar nan abubuwan masarufi kawai ba
ne, a’a ta ma yi ƙudurin ganin cewa lallai duk wani tarnaƙi da aka dabaibaye talaka
da shi a ga cewa an tsittsinka shi domin mu ma mu san Allah ya halicce mu daidai
da sauran mutane.”
(Katsina, 1983: 28-29).
Jam’iyyar Neman Sauyi ita ce ita ce jam’iyyar talakawa a wadda
take fafutukar ƙwatar ‘yancin talaka daga danniya da babakeren masu mulki. A nan
marubucin ya nuna cewa, daga cikin manufar siyasar jam’iyyar Sauyi shi ne, kwance
duk wani sasari da aka sanya wa talaka, da ba shi cikakkiyar damar rayuwa da morar
arziƙin ƙasa kamar kowa, yadda shi ma zai fahimci cewa shi ma ɗan ƙasa ne mai ‘yanci.
Baya ga bayyana manufofin jam’iyyar hamayya ta sauyi da marubucin ya nuna, sai kuma
ya bayyana irin manufofin da jam’iyyar hamayya ta Riƙau take ɗauke da su kamar haka:
“ Domin ita ‘Riƙau’ ga
manufofinta ba ta da wani tanadin ƙwarai da ta yi wa talaka. Sai dai maganar kare
sarakai da masu kuɗi kawai take yi, shi kuwa talaka an bar shi bauɗe.”
(Katsina, 1983: 36-37).
A nan idan aka duba za
a ga cewa ‘yan jam’iyyar sauyi su ne suke da manufar samar da ‘yancin talaka ta
hanyar kawar da danniyar shugabanni. Ita kuwa jam’iyyar Riƙau kamar yadda aka nuna
ta a matsayin jam’iyya mai mulki ba ta da wani tanadi na ‘yanta talaka, sai dai
masu kuɗi da sarakuna da attajirai, kasancewarta jam’iyya ce ta ‘yan jari-hujja.
Irin wannan manufa ta yancin ƙasa da ta
‘yan ƙasa ita ce jam’iyyun siyasa suka riƙa bayyanawa a tsawon tarihin siyasar jam’iyyu,
wanda idan aka duba kusan duk abu guda ne suke magana a kai, domin sukan yi ƙoƙarin
danganta ‘yancin da ‘yan ƙasa suke da shi na gudanar da rayuwa da ci gaban tattalin
arziƙin ƙasa da sauran abubuwan ci gaba.
Baya ga ‘yancin ƙasa, su kansu al’umma suna buƙatar cikakken
‘yancin gudanar da rayuwa mai inganci, hakan kuwa ba zai samu ba sai shugabanni
sun tabbatar da ‘yancin da talaka yake da shi da ya shafi morar tattalin arziƙin
ƙasarsa, ba wai masu mulki ko wasu tsiraru su riƙa mayar da shi nasu su kaɗai ba.
Za a iya ganin wannan a cikin misalin da yake ƙasa:
“Kaico! A faɗa wa ‘yan
siyasa masu aƙidar gabtare da zabtare cewa yanzu fa talaka ya harzuƙa, saboda haka
babu sauran milkin mallaka ”
(Surajo, 2006: 71).
A ganin wannan marubucin yana ganin cewa wasu ‘yan siyasar ba
su son bai wa talaka ‘yanci don sun saba da babakere da rub-da-ciki kan dukiyar
ƙasa, amma yanzu talaka ya riga ya farga da cewa lokacin mulkin mallaka ya wuce,
batun ‘yanci ake yi. Don haka ya kamata shi ma talaka ya shaƙi iskar ‘yanci don
ya amfana da arziƙin ƙasarsa.
5.1.4 Samar da Tsaro
Samar da tsaro ga al’umma shi ne yake tabbatar da zama lafiya
da kwanciyar hankali. Akan samar wa da al’umma da tsaro ne ta hanyar tabbatar da
dokokin da za su kula da rayukansu da dukiyoyinsu. Waɗannan dokokin su ne suka samar
da nau’ukan jami’an tsaro daban-daban da gwamnati kan samar domin kare lafiya da
dukiyoyin al’umma. Tattabatuwar wannan tsaron shi ne yake samar da zaman lafiya
a cikin al’umma. Duk al’ummar da ta rasa ingantaccen tsaro a cikinta wannan al’ummar
ta rasa wani ɓangare mai girma da ya shafi ci gabanta. Tsaro da zaman lafiya, da
sune ake iya samun ci gaban dukkan wasu harkokin yau da kullum na al’umma.
Tarihi ya nuna tun a jamhuriya ta ɗaya an sha samun rikice-rikice
da suka shafi addini da ƙabilanci da ɓangaranci da ta’addanci da sauransu. Irin
waɗannan matsalolin tsaro sukan haifar da koma-baya ga tattalin arziƙi da yanayin
zaman jama’a. Wannan ya sa a cikin manufofin siyasar jam’iyyu a kullum sukan bai
wa matsalolin tsaro muhimmanci, sukan sanya shi a sahun gaba musamman lokacin tallata
jam’iyyu da kuma yaƙin neman ƙuri’a da ma wasu abubuwa da suka shafi siyasa. Dubi
wannan jawabin:
”Nijeriya ta kasance ƙasar
da ta fi sauƙin haɗa rikicin addini tsakanin Musulmi da Kirista domin tana da albarkatun
mai. A don haka, yayin da muke bai wa ƙungiyoyi da ɗariƙu goyon bayan kula da harkokin
ilimi, ya kamata mu lura da daɗin baki ko zaƙin harshen maƙiya addinin Musulunci
su ɗauki hankalinmu wajen haddasa mana ‘yan ta’adda da masu tsattsauran aƙidar addini
da suka yi amannar cin wa burikansu ta hanyar tarzoma da tayar da ƙayar baya da
waɗansu ke ɗaukar nauyin ayyukansu a ɓoye.”
(Jega da wasu, 2002:183-184).
Wannan jawabin ya taɓo abin da ya shafi tsaron al’umma ne da
dukiyoyinsu, inda aka nuna irin bambance-bambancen da yake tsakanin al’ummomin Nijeriya
ta fuskar addini musamman ma a Arewa. An nuna cewa, ya kamata al’ummar ƙasar Hausa
su kula da maƙiyansu waɗanda za su iya yin amfanin da bambancin addini ko na aƙida
wajen haddasa rikici a cikin al’umma. Ana amfani da zafin aƙida wajen haddasa ta’addanci
kamar dai yadda aka gani a cikin shekarun 1984 na rikicin Maitatsine, da tashe-tashen
hankula irin na ƙabilanci da na addini a tsakanin ƙabilu da kuma mabiya addinai;
da wasu rikice-rikicen ta’addanci kamar irin su Boko Haram da satar mutane da dai
sauransu, inda aka nuna cewa wasu ne suke ɗaukar nauyinsu a ɓoye. Irin waɗannan
dalilai ne sukan sa jam’iyyu bayyana tsaro a matsayin wata manufa da suke son cimma
wa idan suka samu goyon bayan al’umma.
A wani jawabi na Malam Aminu Kano wanda yake nuna muhimmancin
samar da tsaro ga al’umma, inda ya nuna cewa babu wani abu da ya kai tsaron lafiya
da dukiyoyin al’umma muhimmanci, duk da yake kowa da abin da ya fi buƙata, amma
dai tsaro shi ne kan gaba da komai, domin sai da zaman lafiya ake iya samun ci gaba.
Dubi abin da ya ce:
“A bara a hanyarmu ta
dawowa daga kamfe mun tsaya a wani gari a jihar Gongola da ake kira Nassarawa, a
garin akwai mabiya Ɗariƙar Tijjaniyya da yawa. Jagoransu ya yi mana bayanin cewa
gaba ɗayanmu masoya PRP ne, kuma labarin manufofin PRP ya ishe mu na samar da ruwan
sha, da gina asibitoci da sauransu. Mu duk ba su ne buƙatunmu ba, abin da muke so
kawai shi ne tsaro, muna zirga-zirga a cikin garuruwanmu da ƙauyuka shekaru goma
da suka wuce haka ya yi nuni da muhimmancin tsaro ga al’umma ”
(Jega da wasu, 2002:38).
A cikin wannan misalin za a ga an kawo wasu daga cikin manufofin
siyasar jam’iyyu a ciki kamar samar da ruwan sha da gina asibitoci, waɗanda abubuwa
ne muhimmai da suke da alaƙa da kula da lafiyar al’umma, sai dai an nuna cewa tsaro
shi ne kan gaba kamar yadda waɗannan mutane da Malam Aminu ya ba da labarinsu suka
bayyana masa. Sun nuna cewa babu abin da suke buƙata kamar tsaron lafiyarsu da dukiyoyinsu,
domin in waɗannan suka samu to ana sa rai sauran ma za su biyo baya. Idan kuwa ya
kasance babu tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali to duk wata manufa ta siyasa
da za a samar a wannan wuri za ta zama ba ta da amfani ga al’ummar wannan wurin.
Wannan ya nuna irin matuƙar muhimmancin da samar da tsaro yake da shi a cikin manufofin
siyasar jam’iyyu, wanda ya sa a kodayaushe suke sanya shi
a cikin manufofinsu don neman goyon bayan al’umma.
Yana daga cikin ma’anar samar da tsaro da ake bayyanawa a cikin
manufofin siyasar jam’iyyu, tabbatar da hanyoyin more rayuwa waɗanda za su tabbatar
da tsaron rayuwa da kauce wa salwantarsu. Kyautata hanyoyin mota domin tabbatar
da sufuri da tsaron rayuka a kan hanyoyi. Za a fahimci hakan idan aka dubi wannan
misalin:
“A kullum ɗaruruwan mutane
suna tawaya, wasun su na halaka a cikin hatsarin mota da bala’in fashi da makami,
saboda munin hanyoyin sufuri da kuma rashin tsaro ”
(Surajo, 2006: 71).
A wannan misalin za a ga inda aka nuna yadda rayuka suke salwanta
a dalilin hatsarin mota da fashi da makami a kan hanyoyi saboda munin hanyoyi. Irin
wannan lalacewar da hanyoyi kan yi sukan haifar da hatsarin mota wanda yakan zama
silar rasa rayuka. Masu ayyukan ta’addanci ma kamar ‘yan fashi da makami da masu
satar mutane kan tsaya a kan matattu tituna domin aiwatar da mummunar manufarsu
kasancewar hanyar da ba ta da kyau dole motoci su bi a hankali kafin su wuce, wannan
zai ba su damar tare motoci da illata wasu mutane har ma da rasa rayukan wasu. Wannan
ya sa daga cikin manufofin siyasar jam’iyyu akwai samar da tsaro wanda ya shafi
na dukiya da kuma rayuka.
Har ila yau, kamar yadda ake yawaita ƙorafi kan yadda shugabanni
suke watsi da manufofin da suka tallata siyasarsu a kansu, ita ma manufar wadata’yan
ƙasa ta kasance kamar haka, domin dai an nuna cewa Nijeriya ƙasa ce mai ɗimbin arziƙi,
sai dai maimakon ‘yan ƙasar su zama su ne suke juya arziƙinsu kuma su mori abinsu,
sai ya kasance ba su gani a ƙasa ba, kamar yadda marubucin littafin Da Bazarku ya kawo a cikin wannan misalin
da yake ƙasa:
“ A duniya duka kowa ya
san cewa ba dai a gwada wa kare iya kwanciya ba sai dai a yi masa gorin mayafi.
Saboda haka arziƙin ƙasarmu ya shahara sai dai ko a ce Allah ya haɗa mu da shugabanni
masu rariyar hannu.
(Surajo, 2006: 71)
A nan yana nuna cewa, Allah ya hore wa Nijeriya arziƙi mai tarin
yawa wanda bai kamata a ce wasu suna cikin irin talaucin da suke ciki ba, amma sai
ya kasance son ran shugabanni ya sa arzikin bai wadata ‘yan ƙasa ba, kuma sai aka
rasa ina yake zurarewa. Da a ce za su tsaya a kan manufar wadata ‘yan ƙasar lallai
za a samu wadatar.
5.2 Gwagwarmayar Samun Cigaban Al’umma A Siyasance
Siyasar jam’iyyu an ƙirƙire ta ne domin ciyar da ƙasa gaba da
kuma tabbatar da ɗorewarta. Irin wannan tunani shi ne ya haifar da gwagwarmayar
neman mafita ta hanyar samar da wasu dabaru da hanyoyin da za su taimaka wajen samar
da wannan cigaban ƙasar da aka kafa siyasar dominsa. Irin wannan faɗi-tashin da
ake yi a siyasance yakan kasance bisa wasu matakai waɗanda ake amfani da su ɗaya
bayan ɗaya domin kaiwa ga manufar cigaban da ake fata. Akwai matakai da dama da
‘yan siyasa suke amfani da su domin kai ga irin cigaban da suke gwagwarmayar samar
wa ƙasa, waɗanda suka zama ƙashin baya ko ruhin siyasar jam’iyyu, domin idan babu
su to tamkar ma babu siyasar ne. Waɗannan matakai sun haɗa da:
5.2.1 Kafuwar Jam’iyyu
Kalmar jam’iyya tana nufin ƙungiyar jama’a ta siyasa ko ta sana’a,
mai manufa guda da tsarin ƙa’idoji da zaɓaɓɓun shugabanni. (CNHN, 2006: 212). A
wasu lokuta ƙungiyoyi daban-daban ne musamman na masu sana’o’i ko na tuntuɓar juna
ko ƙungiyoyin gama kai, sukan haɗu don samar da jam’iyyar siyasa guda. Abu na farko
da ake fara bai wa muhimmanci shi ne kafa jam’iyyun da za su samar da shugabanni
ta hanyar zaɓen ‘yan takara a matakai daban-daban. A ƙasar Hausa wannan tsari aka
bi aka kakkafa jam’iyyun siyasa, domin ta hanyarsu ne za a iya yin kowace irin gwagwarmaya
a siyasance domin samar wa da al’umma cigaba mai ma’ana.
Batutuwa na tarihi musammanm na kafa jam’iyyun siyasa sun fito
a cikin ayyukan zube na Hausa a wurare da dama, inda ake nuna yadda aka riƙa gwagwarmayar
kafa jam’iyyu cikin tarihin siyasar jam’iyyu domin samar da cigaban al’umma. Alal
misali, dubi abin da aka tsakuro a cikin wannan jawabin:
“A kan waɗannan abubuwa
ne muka ga ya dace mu samar da jam’iyyar da za ta yi yaƙi da kawar da cutar da ake
wa talakawa da kuma yaƙi da rashin ɗa’a soboda waɗannan dalilai ne kwamitin wucin
gadi na gudanar da al’amura na wannan jam’iyya ke haɗuwa ba tun yanzu ba suka ƙirƙiro
da sunan wannan jam’iyyar “Peoples’ Redemption Party”. Wannan laƙabi ya ƙunshi duk
abin da jam’iyyar ta ƙudurci yi wa talakawa ‘yan Nijeriya. Jam’iyyar tana da tuta
mai launuka uku, an shirya su a tsaye, launin ja a sama, fari a tsakiya da baƙi
a ƙasa ina mai fatan sanar da ku cewa mutane suna da damar samar da rassa a wannan
jam’iyyar a mazaɓunsu da ƙauyukansu da kuma matakin jiha. Wannan ita ce jam’iyyar
da ke da ma’ana wadda ‘yan Nijeriya ke dako tun a lokaci mai tsawo.”
(Jega da wasu, 2002:18).
Idan aka duba daga bayanan da suke cikin wannan misali za a ga
cewa, irin gwagwarmayar da aka riƙa yi wajen kakkafa jam’iyyun siyasa an yi ne domin
samar wa al’umma ci gaba ta fuskokin rayuwa mabambanta. Jawabin na wani jigo a jam’iyyar
PRP ya nuna an kafa jam’iyyar ne domin kawar da zalunci da cutar da ake yi wa talakawa
sannan kuma ta kawar da rashin ɗa’a a tsakanin al’umma. Haka ma sauran jam’iyyu
sukan faɗi dalilan kafuwar nasu jam’iyyun. A cikin jawabin an nuna buƙatar samar
da rassan jam’iyyar a cikin lungu da saƙo na ƙasar baki ɗaya, tun daga mazaɓu da
ƙauyuka da ƙaramar hukuma da ma jihar baki ɗaya. Za su yi haka ne ta hanyar kakkafa
ofisoshi da tutoci da alamomin jam’iyya.
Haka kuma irin waɗannan misalan na yadda aka riƙa kakkafa jam’iyyun
siyasa a matsayin wata hanyar gwagwarmaya domin samar wa da ƙasa cigaba sun riƙa
bayyana a cikin ƙagaggun labaran Hausa, inda aka riƙa nuna cewa ko dai a karon farko
ne aka zo da jam’iyyar siyasa domin jama’a su karɓa, ko kuma rashin gamsuwa da wata
jam’iyyar da ake da ita ne ya sanya aka kafa wata sabuwa domin ta ƙalubalanci manufofin
wadda aka samar tun farko. Irin wannan ya fito a cikin littafin Tura Ta Kai Bango, inda aka nuna cewa, jam’iyyar
Riƙau jam’iyya ce mai ra’ayoyin mazan jiya wadda ta rungumi tsarin jari-hujja. A
dalilin haka wasu matasa suka yi aniyar kafa jam’iyyar da za ta ƙalubalanci jam’iyyar
ta Riƙau wanda a ganinsu hakan zai kawo ci gaba ga al’ummarsu. Dubi wannan misalin:
“ mutane cike suke da
farin ciki da murna , musamman ma irin mutanen da suka nuna sha’awarsu ga ɗaya daga
cikin sababbin jam’iyyu guda biyu da kafuwarsu ta tabbata. Yau ne ɗaya jam’iyar
ke yin taronta don buɗe reshen wannan ƙauye. Wannan kuwa
ita ce jam’iyyar masu ra’ayin mazan jiya ko kuma ‘RIƘAU’ a taƙaice.”
(Katsina, 1983: 3).
Idan aka duba za a ga cewa batun kafuwar jam’iyyu ne ake yi da
samar da rassansu a ciki lungu da saƙo na ƙasa. Marubucin ya nuna, an kafa sababbin
jam’iyyu guda biyu ne bayan waɗanda ake da su a farko. Shi kuma irin wannan kafawar
abu ne sananne cikin siyasar ƙasar nan. Wasu ‘ya’yan jam’iyyar farko su ne suke
ɓallewa , su kafa wata jam’iyyar saboda zargin jam’iyyar tasu ta saɓa manufofin
kafa ta, ko kuma ba ta biya wa al’umma buƙatocincu ba da sauransu. Wani lokaci kuma
sai ya kasance wasu mutane ne na daban za su shiga fagen siyasa a karon farko, su
ƙi aminta da jam’iyyun da ake da su, sai su kafa wata sabuwar jam’iyyar. A nan jam’iyyar
Riƙau ce take gudanar da taro na buɗe sabon ofishinta a ƙauyen Kabobi Dubi jawabin
shugaban jam’iyyar kamar yadda marubucin ya kawo:
“Jama’a salamu alaikum.
Kusan duk wanda halarci wannan wuri ya san abin da ya tara mu a nan. Wato shi ne
bikin kafa jam’iyyar ‘RIƘAU’ a wannan gari namu.”
(Katsina, 1983: 4).
Wannan jawabi ya tabbatar da maƙasudin wannan taro shi ne, bukin
kafa jam’iyyar siyasa mai suna Riƙau a garin. Haka jam’iyyun siyasa sukan yi idan
aka kafa su, shugabannin jam’iyya sukan shiga birane da ƙauyuka domin kafa ofisoshin
jam’iyyar domin ta samu wakilci a ko’ina cikin ƙasa. A wajen taron kafa jam’iyya
ne ake bayyana tutar jam’iyya da manufofinta na kawo cigaba ga al’umma.
5.2.2 Tallata Jam’iyyu
Tallata jam’iyya yana nufin neman
ra’ayin jama’a ƙarƙashin wata ƙungiya guda wadda take da ayyanannun manufofi da
ƙa’idoji, ta hanyar jan hankali da lafuzza masu daɗi, ta hanyar tausasawa da nuna
tausayi da jinƙai, domin cimma wata biyan buƙata, musamman na neman shugabanci ko
jagorancin al’umma.
Bayan an tabbatar da kafuwar jam’iyyu sai kuma a mayar da hankali
wajen tallata su ta hanyar yaɗa manufofinsu a cikin ƙasa, wannan zai sa jama’a su
karɓe su hannu bibbiyu, kuma su zaɓe su idan zaɓe ya zo. Kowace jam’iyya takan tsara
abubuwan da za ta yi amfani da su wajen tallarta, waɗannan abubuwa kan kasance muhimmai
ne ga rayuwar al’umma, kuma da su ne za a riƙa jawo hankalin al’umma tare da nuna
masu romon da za su samu idan har suka kasance sun goya wa wannan jam’iyyar baya.
‘Yan siyasa suna tallata jam’iyya ta hanyoyi masu yawa. Akwai gidajen rediyo da
talabijin da mujallu da wasiƙu da alluna da hotuna da kuma jawabai a tarukan jam’iyya.
Tun a karon farko na siyasar jam’iyyu a Arewacin Nijeriya, an
yi amfani da hanyoyi daban-daban wajen tallata jam’iyyun. Alal misali, an riƙa sanya
tallar jam’iyyu a cikin jaridu, akan sanya tallar kai tsaye, wato a ware shafi guda
a sanya sunan jam’iyya da alamar jam’iyya tare da bayanai na jan hankali da kuma
roƙo ko kira ga jama’a da su bai wa wannan jam’iyyar goyon baya. Wani lokaci kuma
sai a sanya tallar jam’iyyar a cikin wani rahoto ko bayani ta yadda manufar tallar
za ta fito. Akwai inda aka riƙa tallata jam’iyyun ga jama’a tare da jawo hankalinsu
ta hanyar bayyana wasu muhimman abubuwa waɗanda al’umma za su amfana da su idan
suka amince da su, kamar yadda aka tsakuro wannan misalin daga jaridar Sodangi:
“ saboda haka a ƙarshe
ina kira ga dukkan mutanen Najeriya a ranar da za a yi ƙuri’a su ɗunguma su jefa
wa NPC ƙuri’a don mu samu zama lafiya da jin daɗi a Nijeriya mai mulkin kanta.”
(Abdulkadir, 1959).
A wannan misalin idan
aka duba, ana yi wa jama’a tallar jam’iyyar NPC ne cewa ita ce jam’iyyar da za ta
samar da zaman lafiya ga al’umma, shi kuwa zaman lafiya shi ne yake kawo jin daɗin
rayuwa. Don haka su rungumi jam’iyyar NPC domin tabbatar da zaman lafiya da jin
daɗinsu, musamman kuma kasancewar ana gab da samun ‘yancin kai a lokacin, idan suka
zaɓi jam’iyyar za su ji daɗin rayuwa a cikin ƙasarsu mai ‘yanci. Irin waɗannan misalan
an yi ta amfani da su wajen tallata jam’iyyun siyasa a a jamhuriya ta ɗaya.
Wani misalin da ya nuna yadda aka ci gaba da tallar jam’iyyar
NPC shi ne, inda aka riƙa nuna wa jama’a abubuwa mabambanta na tagomashi domin ta
samu karɓuwa a wurin ‘yan ƙasa. Ga misali:
“ A sarari jam’iyyar NPC
ta nuna wa jama’a babu bambanci don addini, ƙabila, harshe, ko girman duniya, don
haka ashe babu mamaki idan muka zaɓe ta don ta zama gwamnatin tarayyar Najeriya,
don ita kaɗai za ta tsare mutuncin Najeriya baki ɗaya – ba wani son zuciya ko bambancin
ra’ayi.”
(Abdulkadir, 1959).
A nan ana tallata jam’iyyar NPC ne da cewa, ita ce jam’iyyar
da ta tabbata babu ruwanta da bambancin addini ko ƙabila ko kuma harshe a sha’anin
mulkin ƙasa. Haka kuma ba ta nuna bambanci tsakanin mai mulki da wanda ake mulka
ko kuma mai kuɗi da talaka. A cewarsu, duk waɗannan babu ruwan jam’iyyar NPC da
su, don haka in dai cancanta ce ake nema to wannan jam’iyya ita ya kamata a zaɓa
domin ta shugabanci tarayyar Nijeriya wadda za ta samu cikkaken mulkin kai ‘yan
watanni kaɗan masu zuwa. A cewar wannan jarida jam’iyyar ce kaɗai za ta kare mutuncin
Nijeriya ba tare da nuna son zuciya ko bambancin ra’ayi ba. An ci gaba da ganin
irin waɗannan misalan na tallar jam’iyyu har zuwa lokacin da aka fara jin ƙamshin
mulkin kai, wanda hakan ya sa aka ci gaba tallata jam’iyyun siyasa da batun ‘yancin
kan ƙasa da kuma mulkin kai.
Bayan samun ‘yancin ƙasa irin wannan salo na talata jam’iyya
ya ci gaba. Jam’iyyar NEPU a nata ɓangaren, ta riƙa tallata jam’iyyarta da cewa,
ita ce ta fi cancanta a zaɓa ba wata daban ba. Dubi wannan misalin da aka tsakuro
daga wata wasiƙa da aka buga a jaridar Daily
Comet kamar haka:
“Saboda haka nake jawo
hankalinku ‘yan’uwana talakawan Arewa, ku guji NPC a wannan zaɓe mai zuwa na Kaduna,
ku jefa ƙuri’arku a a cikin akwatu mai tauraro. Wato akwatin jam’iyyar Neman Sawaba
NEPU. Don ku ga kamun ludayinta ”
(Isa, 1961).
A cikin wannan wasiƙar an tallata jam’iyyar NEPU ga al’umma musamman
talakawa, inda aka nuna masu cewa su guji zaɓen jam’iyyar NPC mai mulki a zaɓen
da yake tafe, maimakon haka su jefa ƙuri’arsu a akwati mai alamar tauraro wato akwaitin
jam’iyyar NEPU ke nan, don ita ce jam’iyya mai alamar tauraro. Idan suyka yi hakan
za su ga kamun ludayin jam’iyyar idan ta yi nasara, wato za su ga irin abubuwan
alheran da jam’iyyar take da manufa a kansu domin amfanin al’ummar ƙasa.
A wata wasiƙar ta daban ma an nuna yadda wani tsohon ɗan jam’iyyar
NPC yake kira da kada a zaɓi tsohuwar jam’iyyar tasa wato jam’iyyar NPC mai alamar
fartanya, inda ya yi kira da a zaɓi jam’iyya mai alamar tauraro wato NEPU. Ga abin
da wasiƙar ta ce:
“Ina fata talakawan Nigeria
za su manta da jefa kuri’arsu a akwati mai fartanya, su jefa a mai tauraro.”
(Gasakas, 1961).
A nan ya yi kira ne ga jama’a da su manta da batun zaɓen jam’iyya
mai alamar fartanya wato jam’iyya NPC, maimakon haka su zaɓi jam’iyya mai alamar
tauraro wato jam’iyyar NEPU.
Marubuta sun ci gaba da haska yadda ake tallata jam’iyya ta riƙa
gudana a cikin siyasa. Alal misali a ciki littafin Tura Ta Kai Bango an fito da yadda aka riƙa gwagwarmayar tallata jam’iyyun
siyasa masu hamayya da juna kamar haka:
“ kun san wannan ita ce
jam’iyyar da duk ɗan ƙasar nan nagari ya kamata ya kasance a cikinta, ita ce ta
kishin ƙasa. Ita ce mai mutunta shugabanninmu. Ita ce mai kawo mana dukkan wasu
abubuwa da muka daɗe muna buƙata ba mu samu ba a garin nan ”
(Katsina, 1983: 3).
Idan aka dubi waɗannan bayanai za a ga cewa ana tallata jam’iyyar
ne da wasu kyawawan abubuwa waɗanda idan al’umma sun amince da ita za su samu. A
cikin bayanin an nuna cewa duk wani mai kishin ƙasa ba zai so a yi wannan jam’iyyar
ba tare da shi ba, domin jam’iyya ce ta ‘yan kishin ƙasa wadda za ta kawo wa al’umma
cigaba. Za ta kawo mafita ga wasu matsaloli da aka daɗe suna addabar al’ummar ƙasa.
Ko kafin a kai ga tara jama’a wajen tallata jam’iyyar siyasa,
akan yi amfani da hanyar tuntuɓa wajen samun manyan ‘yan jam’iyya ko kuma iyayen
jam’iyya waɗanda za su mara wa tafiyar wannan jam’iyyar baya, ta haka ne ake samun
dattijai a zauna da su a tattauna kan manufofin jam’iyya don a shawo kansu su amince
su kasance a cikin jam’iyyar. Kasancewar irin waɗannan dattijai a cikin jam’iyya
tamkar garkuwa ce gare ta, kuma zai ƙara wa jam’iyyar siyasa ƙima da daraja a idon
mutane, sannan kuma kowa zai yi iyaka iyawarsa wajen tallata wa makusantansa kafin
a kai ga sauran jama’a baki ɗaya. Irin wannan ya fito a cikin wani misali kamar
haka:
“ duk wani shiri da za
ka yi game da kafa reshen wannan jam’iyyar a nan zan yi ruwa in yi tsaki yanzu abin
da nake son mu soma shi ne, mu tunkari abokannenmu don mu ga su wane ne za su yarda
a tafi da su haka ma manyan mutane in mun haɗa abokanenmu kowa zai yi bayanin dattijon
da ya ga yana iya tunkara don ya shawo kansa mu sami dattijai a cikin jam’iyyar.”
“Ina ganin tun da kana
Arewaci ni kuma ina Yammacin garin nan, to kowannenmu ya tunkari samari goma na
sashen da yake.”
(Katsina, 1983: 18).
A wannan misali an ga yadda aka riƙa tsara yadda za a tallata
wa jama’a sabuwar jam’iyyar siyasa. A cikin misalin idan aka lura sun fara tallata
jam’iyyar ne ga abokansu na kusa, sannan suka yi tunanin samun magoya baya daga
cikin manya, iyaye ko dattijai. Haka kuma, sai suka raba aikin inda kowa zai tafi
yankinsa ko unuguwar da ya fito domin ci gaba da tallata wa mutane, inda suka ce
aƙalla kowa zai yi ƙoƙarin samun mutum goma da za su amshi jam’iyyar. Irin wannan
gwagwarmayar siyasa da fafutukar samun cigaba sun ci gaba da samuwa a cikin rubutattun
ayyukan adabi na zube har zuwa yau. ‘Yan siyasa sun ci gaba da wannan gwagwarmaya
ta hanyar tallata jam’iyyunsu a cikin shafukan jaridu musamman ma lokacin da aka
buga kugen siyasa.
5.2.3 Tallata ‘Yan Takara
Dangane da wannan aiki, takara yana nufin ƙoƙarin kaiwa ga madafun
iko ta hanyar neman goyon bayan jama’a don samun ƙuri’arsu.
Ɗan takara shi ne mai tsayawa zaɓe tare
da wani. (CNHN, 2006: 120 da Paul da Roxana, 2020: 229), jam’insa
shi ne ‘yan takara. Tallata ‘yan takara a nan yana nufin ƙoƙarin cusa
wa al’umma ra’ayin wani ɗan siyasa ta hanyar rarrashi, da roƙo da duk wata hanya
da za a iya yin amfani da kalmomin tausasawa don ya samu karɓuwa kuma a zaɓe shi.
Tallata ‘yan takara abu ne mai matuƙar muhimmanci a cikin siyasar
jam’iyyu, domin sau da dama akan yi amfani da nagartar ɗan takara ba tare da la’akari
da jam’iyyarsa ko wata nasaba tasa ba. Duk da cewa kowane zamanin siyasa yakan zo
da irin salon siyasarsa, wanda akan yi amfani da shi domin samun mafita da kuma
kai wa ga nasara, amma dai tallar ‘yan takara muhimmin abu ne a cikin tarihin siyasar
Arewacin Nijeriya. Akwai abubuwa da dama da ake la’akari da su wajen tallata ‘yan
takara; akan yi amfani da daraja ko ilimi ko matsayi ko abin duniya da dai sauransu.
Haka kuma ana amfani da hanyoyi daban-daban wajen tallata ‘yan takara, kamar su
jaridu da mujallu da sauran kafafen watsa labarai da ma tarurrukan siyasa.
Wata hanyar ta tallar ɗan takar ita ce, amfani da jaridu da mujallu.
Tun a jamhuriya ta ɗaya an yi ta amfani da jaridu wajen tallata siyasa da ‘yan siyasa,
da jam’iyyu. Kuma an ci gaba da tallata su domin samun magoya baya da kuma samun
rinjaye a kan abokan hamayya. Wani abu da wannan bincike ya lura da shi shi ne,
a jamhuriya ta farko ba a faye tallar ɗan takara kai tsaye a jaridu ba, maimakon
haka sai dai a tallata jam’iyyun da suka zaɓe a cikinsu, kuma a riƙa nuna cewa jam’iyyun
su ne suka fi cancanta a zaɓa domin kyawawan manufofinsu. Wannan ya sa da dama cikin
‘yan siyasa a jamhuriya ta ɗaya jam’iyyunsu ne ake tallatawa maimakon ɗan takarar
a karan kansa. Wannan ya sa ‘yan takarar da aka tsayar ƙarƙashin jam’iyyun sukan
ci albarkacin jam’iyyun ne, kuma idan aka samu akasin manufar jam’iyyar bayan an
zaɓi ɗan takarar, to laifin jam’iyya ce ba ɗan takara ba. An samu misalai da dama
daga jaridun jamhuriya ta farko waɗanda suke nuna cewa zaɓen jam’iyya ne abu mafi
muhimmanci ba tare da ayyana wani ɗan takara ba.
A jamhuriya ta biyu, an samu inda jaridu suka ruwaito wasu al’amura
da suka shafi tallar ɗan takara, inda aka riƙa nuna cewa jam’iyyun siyasa suna bi
gari-gari don gabatar da ‘yan takararsu ga jama’a tun gabanin a fara yaƙin neman
zaɓe. Galibi irin wannan tallar akan yi wa al’umma ne a cikin ɗan ƙwarya-ƙwaryan
taro wanda akan yi da shugabannin jam’iyya da kuma masu riƙe da al’amuran gari da
yanki musamman sarakuna da iyayen ƙasa. Alal misali, jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta kawo wani rahoto da
ya nuna tallar ɗan takara kamar haka:
“Shugaban Jam’iyyar ‘Yan
Ƙasa ta Nijeriya (NPN) reshen Jihar Kaduna, Alhaji Sulaiman Ahmed ya ce NPN ta zarce
kowace jam’iyyar siyasa da ake da ita a ƙasar nan ta fusakar samun magoya baya masu
hankali da ilimi. Ya yi wannan kalami ne a lokacin da yake jawabi a Ikara a kan
ci gaba da rangandin da yake yi na gabatar da ɗan takaran zama gwamnan jihar Kaduna
na jam’iyyar, Alhaji Lawal Kaita da mataimakinsa Malam Nuhu Adamu ga jama’a.”
(“NPN ta zarce kowace jam’iyya”, 1979).
Idan aka duba a cikin wannan misalin za a ga cewa, shugaban jam’iyyar
NPN ne yake tallata wa jama’a ɗan takararsu, inda ya nuna cewa dukkan jam’iyyun
ƙasar babu wadda take da yawan magoya baya kamar jam’iyyarsu. Ba kuma wai kawai
yawan jama’ar ba ne, sai dai dukkan magoya bayan jam’iyyar masu ilimi ne da hankali.
Ya faɗi haka ne saboda kowa zai so ya kasance cikin masu hankali da ilimi, wannan
zai ɗan takararsu ya samu goyon bayan jama’a da dama. Har ila yau, a cikin misalin
an bayyana cewa, ya yi jawabin ne a lokacin da yake gabatar da ɗan takarar zama
gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyarsu ta NPN. Wannan gabatarwar ita ce tallata ɗan
takarar, wato ya gabatar masu da shi tare da neman su zaɓe shi a ƙarƙashin jam’iyyarsu
don zama gwamnan jihar ta Kaduna.
Dangane da tallar ɗan takara, jam’iyyar PRP ita ma ta fito da
irin wannan misalin a cikin wani rahoto da jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta kawo, inda jaridar ta nuna cewa an gabatar da
ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PRP na jihar Kano kamar haka:
“Babban shugaban jam’iyyar
Ceton Al’umma (PRP) na ƙasa baki ɗaya kuma ɗan takararta wajen neman shugabancin
ƙasar nan a zaɓen da za a yi bana, Alhaji Aminu Kano, ya gabatar da wanda zai tsaya
a takarar neman zama Gwamnan Jihar Kao da sunan Jam’iyyar PRP. Wanda aka gabatar
ɗin kuwa shi ne Alhaji salihi Ilyasu, wani tsohon ma’aikacin gwamnati wanda ya yi
murabus tun shekarun baya. A cikin jawabinsa na gabatar da ɗan takarar neman gwamnan,
Alhaji Aminu Kano ya faɗi cewa Alhaji Salihi na daga cikin irin mutanen da jam’iyyar
PRP take buƙata, waɗanda za ta yi amfani da su wajen gyaran al’amura da suka dagule
a ƙasar nan.”
(“An gabatar da Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kano”, 1979)
A nan idan aka duba shi ma an tallata ɗan takara ne ta hanyar
gabatar wa al’umma da shi domin su zaɓe shi. Galibi wajen
irin wannan gabatarwar ko tallar akan samu wani mutum mai ƙima da mutunci ga jama’a,
sai ya gabatar da shi gare su, domin sun yarda da shi ba zai kawo masu wanda bai
cancanta ba. Shi ya sa Malam Aminu Kano, kasancewarsa mutumin da ya karɓu ga jama’a
kuma suka amince da shi, ya gabatar da wannan ɗan takarar gare su. A cikin byaninsa
kuma ya ƙar da cewa shi wannan ɗan takarar da aka gabatar masu irinsa ne ake buƙata
domin gyaran ƙasa.
Tallata ɗan takara ta hanyar jaridu ko mujallu ba a cikin rahoto
kaɗai ake iya ganinsa a cikin jaridu ba, akan samu wasu jaridu da mujallu da kan
fito da tallar kai tsaye a shafin talla, domin masu karatu da sauran jama’a su gani
kuma su karanta. An samu irin wannan misali a cikin wasu jaridun Hausa. Alal misali,
a kakar siyasar jamhuriya ta biyu an riƙa tallata jam’iyyu da ‘yan takara a shafukan
jaridu da mujallu domin samun karɓuwarsu ga al’umma. Kasancewar jarida tana cikin
hanyoyin watsa labarai wanda ake amfani da rubuto da kuma hoton sura, wannan ya
sa aka riƙa sanya hotunan ‘yan takara da alamar jam’iyyu domin tallata su. Haka
kuma akan ƙara da wasu bayanai na kwarzantawa ko jan hankalin masu ga wannan jam’iyyar
ko ɗan takarar da ake son tallatawa. Ga wani misali wanda ya fito a shafin jaridar
Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ranar 7 ga Afrilu,
1893, wanda aka sanya hoton ɗan takarar gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Garba Nadama
da shugaban ƙasa Alhaji Shehu Shagari, wanda ke ɗauke da bayani a rubuce kamar haka:
“Za a ƙaddamar da yekuwar
zaɓen 1983 na ƙasa baki ɗaya na jam’iyyar NPN a Sakkwato A lokacin buki, mai girma
Shugaban ƙasa Alhaji Shehu Shagari zai gabatar da ɗan takarar zama gwamnan jihar
Sakkwato, watau Alhaji Dr. Garba Nadama da ɗan takarar Mataimakin gwamna, Alhaji
Muhammadu Bachaka ga jama’ar Jihar Sakkwato.”
(“Sanarwar Ƙaddamar da Yekuwar Takarar Zaɓe”, 1983).
Kamar yadda aka gani a misalan da ke sama, ƙaddamar da ‘yan takara
daidai yake da tallata su, domin kuwa za a fito da su ne a nuna wa jama’a su gan
su, sannan su sani cewa daga wannan ranar su ne ‘yan takarar da wannan jam’iyyar
ta tsayar domin neman wata kujerar siyasa. A nan ma an nuna cewa, za a ƙaddamar
da ɗan takarar neman kujerar gwamna a jihar Sakkwato a ƙarƙashin jam’iyyar NPN.
Wannan ƙaddamarwar talla ce ga jama’ar wannan jihar na hajar siyasar da jam’iyyar
NPN ta baje don neman masu saya.
Irin wannan tallar ta sake bayyana a shafi na takwas na jaridar
Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ranar 28 ga Yuli,
1983, inda aka kawo tallar ɗan takarar Shugaban ƙasa Alhaji Shehu Shagari bayan
an sanya hotonsa[1] da bayani kamar haka:
“Shagari ya fi kowa cancanta
a shirye-shiryen ’83 Zaɓi Shehu Shagari mai kishin tafarkin demokuraɗiyya”
(“Shagari ya fi kowa”, 1983).
Wannan hoto ne na tallata ‘yan takara domin neman ƙuri’a ga jama’a
wanda aka tallata Alhaji Shehu Shagari a jamhuriya ta biyu, wanda aka sanya wannan
bayanin a rubuce a jikinsa. A nan ana nuna cewa ɗan takarar shi ne ya fi kowa cancanta
a kakar zaɓen 1983, don haka duk mai kishin tsarin demokuraɗiyya ya zaɓe shi.
An sake samun irin wannan misalin na tallar ‘yan takara ta hanyar
amfani da jarida a farkon jamhuriya ta huɗu, inda aka buga hoton ɗan takarar shugaban
ƙasa Cif Olusegun Obasanjo[2] ɗauke da bayani kamar
haka:
“Ba wanda zai iya maido
wa Nijeriya da martabarta sai Obasanjo. Shugaban da kowa ya san amintacce ne, mai
gaskiya da riƙon amana. PDP ‘Yanci.”
(“Ba wanda zai maido wa Nijeriya”, 1999).
Wannan ma tallata ɗan takarar shugaban ƙasar Nijeriya Cif Obasanjo
ake yi, inda aka nuna cewa in ba shi ba ma babu wanda zai iya maido wa Nijeriya
martabarta. Kamar yadda tallar ta nuna shi mutum ne amintacce, mai gaskiya da kuma
riƙon amana. Don haka duk wanda yake da irin waɗannan siffofi nagartattu shi ya
kamata al’umma su zaɓa.
An ci gaba da amfani da wannan alon tallar a cikin zangunan siyasar
jamhuriya ta huɗu, inda jaridu da mujallu suka ci gaba da zama wasu kafafe masu
muhimmanci na tallar ‘yan takara a matakai daban-daban a duk lokacin da aka buga
kugen siyasa.
A cikin ayyukan adabi na rubutaccen zube ma, adibai sun riƙa
haska irin waɗannan abubuwa a matsayin hanyoyin tallata ‘yan takara, inda suka riƙa
kawo hanyoyin da za su bi wajen nuna wa duniya ɗan takarar da suka suka tsayar domin
jama’a su karɓe zaɓe shi. Marubucin littafin Da Bazarku ya nuna wasu daga cikin hanyoyin tallata dan takara, inda
a ciki Lauya Uba yake yi wa Alhaji Zangina wanda ya kasance ɗan takarar shugabancin
ƙasar Gambiza ne bayanin hanyoyin da za a bi wajen tallata shi. Ga abin da yake
cewa:
“ A tsarin farko dai za
mu fara ne da kafafen watsa labarai, tun da da ma an ce dokin mai baki ya fi gudu.
A nan mun shiraya cewa daga gobe idan Allah ya kai mu, duk wani gidan radiyo da
yake ƙasar nan mun sayi fili za su sa tallarka a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa
har sau biyu a cikin kowace awa ɗaya sannan kuma a duk wata jarida ko mujalla da
ake bugawa a nan ƙasar mun riga mun sayi shafuka biyu a kowace fita da za ta yi
har zuwa lokacin da za a kammala zaɓe. Akwai hotunan liƙawa fiye da miliyan goma
da tuntuni an fara liƙa su ƙauye da birni kai har ma a kan titi a jeji.”
(Surajo, 2006: 49)
A nan marubucin ya nuna wasu hanyoyin tallar ɗan takara ne wato
ta amfani da kafar radiyo da mujallu da jaridu da kuma hotunan liƙawa. Kasancewa
amfani da radiyo abu ne mai sauƙi, kuma yana da sauƙin mallaka ga kusan kowa da
kowa, wannan zai sa dukkan wani saƙo da ake son aikawa ga al’umma idan aka yi amfani
da kafar radiyo zai yi saurin isa gare su. Wannan ya sa ‘yan siyasa sukan yi amfani
da radiyo wajen tallata ‘yan takara domin labarin ɗan takararsu zai isa har inda
ma ɗan takarar ba zai iya kaiwa da ƙafarsa ba. Saƙon tallar zai isa ga dukkanin
rukunin al’umma maza da mata, yara da manya da matasa a kowane lungu da saƙo na
mazaɓarn ɗan takarar. Haka kuma, an bayyana jaridu da mujallu a matsayin hanyoyin
da za a yi amfanin da su wajen tallar ɗan takara. Duk da cewa da radiyo da jaridu
da mujallun dukkansu kafafen watsa labarai ne, amma wasu sun fi wasu sauƙin amfani.
Kamar yadda aka bayyana radiyo ya fi sauƙin samun bayanai kasancewar sauraro ake
yi. Ita kuwa jarida akwai buƙatar mutum ya kasance mai ilimin karatu da rubutu kafin
ya iya samun saƙon da ake son isarwa a cikinta. Haka ma abin yake dangane da mujallu.
Duk da haka dai, su ma hanyoyi ne da ake amfani da su wajen tallata ‘yan takara
a siyasance.
Ke nan, amfani da kafafen watsa labarai wajen tallata ɗan takarar
siyasa wata hanya ce wadda ake amfani da ita a zamance, musamman ma a wannan jamhuriya
ta huɗu, duk da cewa an yi amfani da wannan hanya a jamhuriya ta biyu, amma a jamhuriya
ta ɗaya ba ta samu karɓuwa sosai ba, domin na’urorin zamani ba su game gidan kowa
kamar yanzu ba.
Wata hanya fitacciya da aka kawo a cikin wannan misalin wadda
ta zamo hantsi leƙa gidan kowa tun daga jamhuriya ta farko zuwa yau ita ce, tallata
ɗan takara ta amfani da hotunan liƙawa, wanda akan riƙa raba hotunan domin a lilliƙa
su a jikin bango ko wasu muhimman wurare da duk inda jama’a suke wucewa. Amfani
da hotunan ‘yan siyasa wajen tallata su yana sanya masu zaɓe su ga fuskokin ‘yan
takarar da ake tallata masu ko da kuwa ba su taɓa sanin su a zahiri ba. Wannan zai
sanya wa masu zaɓen natsuwa don ganinj fuskar ɗan takarar. A wasu lokuta hotunan
‘yan takara sukan sa mai zaɓe ya yanke hukuncin wanda ya kwanta masa a rai kuma
ya ji cewa shi ne zai zaɓa ko da kuwa ba a bayyana mana manufofin ɗan takarar ba.
Tun daga hoton ‘yan takarar kawai wasu kan tantance wanda ya kwanta masu a rai,
ko dai daga surar jikinsa, ko cika ido da kwarjininsa ko kuma sutura da iya kwalliyarsa.
Duk waɗannan suna da tasiri wajen tallar ɗan takara da hotonsa.
Bugu da ƙari, tallar ɗan takara musamman a jamhuriya ta huɗu
ita aka fi bai wa ƙarfi maimakon tallar jam’iyya. Wannan ya sanya akan yi riguna
da akan sanya wa hotunan ‘yan takara da sunayensu, da kuma wasu abubuwa na lilliƙawa,
kamar ƙananan hotuna na liƙawa a jikin ababen hawa ko kuma mariƙin makulli wanda
yakan kasance hotunan ‘yan takarar ne domin tallata su, kamar yadda marubucin Da Bazarku ya ci gaba da cewa:
“ akwai sauran abubuwa kama daga na sutura da kuma
na mannawa, waɗanda duk suna ɗauke da hotunanka.”
(Surajo, 2006: 49).
A nan idan aka duba za a ga cewa, ana yi wa ɗan takara ne bayanin
irin tanadin da aka yi wajen tallata shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, wanda
wannan tanadi ya haɗa da lungu da saƙo na ƙasar. Ke nan, waɗannan su ne fitattun
hanyoyin da ake bi wajen tallar ɗan takara a wannan zamanin.
Wata hanyar ta tallata ɗan takara ita ce kai wa sarakuna ziyarar
gaisuwa domin samun goyon bayansu da kuma sanya masu albarka a matsayinsu na sarakuna
iyayen al’umma. Da dama cikin ‘yan takara sukan kai wa sarakunan ziyara ne saboda
sun san irin tasirin da suke da shi, kasancewarsu masu ƙima da daraja a idon al’umma,
kuma suna faɗa a ji. Wannan ya sa ‘yan siyasa kan je wurinsu da sunan gaisuwar girmamawa
da kuma neman albarka a kan takarar da suka sanya a gaba.
Irin wannan misalin ya bayyana a cikin littafin Da Bazarku, an kawo wannan hanyar inda wani
tauraro mai suna Lauya Uba yake cewa:
“ Ranka ya daɗe ka san
yaro ba ya raina manya ya daɗe, saboda haka za mu yi zafin nama a cikin sauriu mu
ɗauke ka mu garzaya da kai ya zuwa fadojin sarakunan ƙasar nan don mu yi gaisuwa
da roƙon iri, mu nemi albarkarsu tun da yake mun san cewa su ba ‘yan siyasa ba ne
amma dai muna sane da cewa maganarsu kamar yankan wuƙa take.”
(Surajo, 2006: 49-50)
A cikin wannan misalin an nuna irin muhimmancin da ‘yan siyasa
suke bai wa sarakuna domin su yi amfani da girma da mutuncinsu da al’umma suke ganinsu
da shi wajen samun goyo baya. An nuna yadda aka shirya kai wa sarakuna gaisuwa da
sunan sanya albarka, inda aka nuna cewa za a ɗauki ɗan takara domin zuwa fadojinsu
da manufar gaisuwa da roƙon iri, domin irin tasirin da maganarsu take da ita a cikin
al’umma.
A wurare da dama irin waɗannan fasalce-fasalce sun riƙa bayyana
a cikin ayyukan rubutaccen zube na Hausa, wanda hakan ya nuna cewa tallata ‘yan
takara yana daga cikin irin gwagwarmayar da ‘yan siyasa sukan riƙa yi domin samar
wa da al’umma cigaba, tun daga samuwar siyarsa jam’iyyu zuwa yau, ana samun tallar
‘yan takara a cikin rubutacce adabi, musamman ma na zube.
5.2.4 Yaƙin Neman Zaɓe
Yaƙin nema zaɓe na nufin zagayen da ‘yan siyasa suke yi a manya
da ƙananan garuruwa domin neman alfarma da tallata jam’iyyu da ‘yan takararsu ga
jama’a. domin neman goyon bayan a jefa masu ƙuri’a ranar zaɓe. Haka kuma, yaƙin
neman zaɓe wani gangamin jama’a ne domin bayyana manufofin jam’iyya da tallata ‘yan
takara (Bunza, 2018: 97). Yaƙin neman zaɓe ya shafi zagayawa ciki ƙasa lungu da
saƙo domin yi wa al’umma bayanin irin abubuwan da ake ciki da kuma irin cigaban
da za a samu idan aka kai ga yin nasara a zaɓe.
Wannan al’amari na yaƙin neman zaɓe yana ɗaya daga cikin gwagwarmayar
da ‘yan siyasa kan yi domin kafa gwamnati. Shugabannin jam’iyyu kan tashi tsaye
ba dare ba rana domin zagaya dukkan yankunan mazaɓunsu domin wayar wa da al’umma
kai don gudananr da zaɓe da kuma wanda ya kamata su zaɓa. Galibi kowace jam’iyya
takan gudanar da yaƙin neman zaɓenta inda za ta riƙa bayyana wa jama’a alheran da
ke tattare da ita, da kuma irin cigaban da za ta kawo idan ta samu nasara. Idan
ya kasance jam’iyyar da take mulki ce, za ta riƙa bayyana irin ayyukan cigaba da
ta samar wa al’umma ne da kuma kira ga al’umma da su sake goya mata baya domin ɗorawa
daga inda ta tsaya. Idan kuwa jam’iyyar hamayya ce, takan riƙa yin suka ne ga jam’iyya
mai mulki ko sauran jam’iyyun hamayya domin haskaka jam’iyyarsu da kuma kiran al’umma
kan kada su sake su sake bai wa jam’iyya mai mulki dama domin ci gaba da sake ciyar
da ƙasa baya.
A cikin tarihin siyasar Arewacin Nijeriya, tundag jamhuriya ta
ɗaya, galibi idan ‘yan jam’iyyar siyasa suka fita yaƙin neman zaɓe sukan riƙa yin
jawabi na yabo ga jam’iyya da ɗan takara ta hanyar faɗin manufofin jam’iyya da kuma
alheran ɗan takara. Wani lokaci jam’iyyun sukan fara da kushe jam’iyyun hamayya.
Daga bisani kuma sai su ɗora da bayanin irin tanadin da suka yi wa al’umma idan
suka kai ga madafun iko. Irin wannan ya fito a jawabin da Malam Sabo Bakin Zuwo,
wakilin jam’iyyar NPC na lardin Kano ya yi a wurin yaƙin neman zaɓe a Sakkwato.
Dubi abin da yake cewa:
“Ga shi jam’iyyar NEPU
tana ta yaba wa da aikin Shehu Usman Ɗan Fodiyo sosai, amma kuma ga shi tana ta
zagin jikokinsa. Idan dai da jam’iyyar NEPU tana son Shehu Usman Ɗan Fodiyo sosai
da kuwa ba ta riƙa tozarta jikokinsa. Domin fa Hausawa sun ce maso uwa ya so ɗanta.
Malam Sabo Bakin Zuwo ya ce kure ne mutum ya so Annabi amma ya riƙa zagin jikokinsa
Jama’a ku gane mu mutanen Arewa, akwai arziƙi mai yawa a ƙasarmu, mutanen Kudu kuwa
suna jin haushin wannan, shi ya sa suke ta ƙoƙarin gano dabarun da za su yaudare
mu har mu yarda da su, su kuwa su riƙa kwashe arziƙinmu kafin mu farga. To, mun
yi sa’a ƙwarai da yake mun sami jam’iyya wadda take da manufa ta kiyaye mutuncin
Arewa da kiyaye arziƙinta da ƙoƙarin sama wa jama’a zaman jin daɗi sosai. Wannan
jam’iyya kuwa ita ce NPC.”
(“Sabo Bakin Zuwo Ya Yi Nasarar Yaƙin
Zaɓe”, 1959).
A nan ya nuna cewa duk da jam’iyyar hamayya ta NEPU tana yabon
ayyukan Shaihu Usmanu Ɗanfodiyo, amma kuma sun yi baya ba zane, domin kuwa masu
hikimar magana sun ce, maso uwa dole ya so ‘yarta. A nan yana magana a kan ‘yan
hamayya ne waɗanda ba su goyon bayan jam’iyyar Sardauna. Shi kuwa Sardauna jikan
Shaihu Usmanu ne wanda yake da tsatso tun daga Manzon Allah (S.A.W). don haka duk
wanda yake son Shaihu to ya kamata ya so jikokinsa, kuma cikin jikokin nasa har
da shugaban jam’iyyar NPC Ahmadu Bello Sardauna ta hanyar goya wa jam’iyyarsa baya.
Ya ci gaba da bayanin yaƙin neman zaɓe da cewa ‘yan Kudu sun lura cewa Arewa suna
da arziƙi, shi ne ya sa suke so su yi wa ‘yan Arewa dabara don su kwashe arziƙin
da suke da shi. Ya yi wannan maganar ne saboda batun ƙawanceb NEPU da NCNC, inda
ya ce suna so ne su yi amfani da wannan su kwashe arziƙin Arewa. Don haka mutanen
Arewa su sun yi sa’a tun da sun samu jam’iyyar NPC wadda take da manufar kiyaye
mutuncin Arewa da arziƙinta. Don haka jama’a su goya mata baya don ta samu nasarar
a zaɓen da ke tafe.
Irin wannan ya ginu a cikin tarihin siyasar Arewacin Nijeriya,
inda jam’iyyu suka riƙa fito da abubuwa da dama na cigaban ƙasa da suke fatan ganin
Arewacin Nijeriya ta ginu a kansu. Yawanci sukan gudanar da yaƙin neman zaɓe, inda
za a tara jama’a na wata mazaɓa a wani fili, inda jiga-jigan jam’iyya za su riƙa
miƙewa suna yi wa taron jama’a jawabi manufar jam’iyyar da kuma dalilin zuwar su
wannan garin, tare da bayanin ɗan takarar jam’iyyar da irin nagartarsa. Wannan ya
riƙa fitowa cikin ayyukan rubutaccen zube na Hausa domin bayyana yadda abubuwan
suka riƙa faruwa a cikin tarihin siyasar Arewacin Nijeriya. Ga misali:
“To da ma dai an ce mai
maɗi ne yake yin talla, amma mai zuma kuwa a gidansa ma yake sayarwa. Sannan har
ila yau ina ganin in tsaya ina wahalar yi ma talakawa bayanin wannan ɗan takara
namu, to kamar fa ina ƙoƙarin nuna ma na rigingine farin wata ne. Dalili kuwa shi
ne da ma shi Farfesa ɗanku ne, ƙaninku ne, kuma abokinku ne ”
(Surajo,2006: 72).
Idan aka lura da jawabin da ake yi a nan, za a fahimce cewa a
taron jama’a ne wurin yaƙin neman zaɓe, inda shugaban jam’iyyar JMT yake gabatar
da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar wato Farfesa Auta. A nan ya nuna cewa
ɗan takarar ba ɓoyayye ba ne wato sananne ne, kuma fitacce
a cikin al’ummarsa. Mutum ne mai farin jini tun can a cikin jama’arsa, inda ya kwatanta
shi da zuma wanda ba ya buƙatar talla, wato ba ya ma buƙatar sai an yi bayanin ko
wane ne shi. Kalmomin da ya yi amfani da su kalmomi da ‘yan siyasa suke amfani da
su a kullum domin nuna wa jama’a cewa, ɗan takarar fa ba baƙo ba ne, kuma an san
nagartarsa tun can. Don haka tsayawa bayyana ko wane ne shi ma tamkar ɓata lokaci
ne. Wannan ya sa aka gabatar da Alhaji Auta a matsayin ɗan gida, kuma ɗan’uwa na
kusa ba bare ba.
A lokuta da dama ɗan takara da kansa yakan yi bayani ga jama’a
a wurin yaƙin neman zaɓensa, ko jam’iyyarsu ga taron jama’a, galibi bayan wasu daga
jikin jiga-jigan jam’iyyarsa sun kammala jawabansu. Ga misali:
“A ƙarshe ya ku jama’ar
wannan ƙasa tamu mai albarka, ina farin cikin shaida maku cewa ni Farfesa Auta na
fito takarar shugabancin ƙasar nan a ƙarƙashin tutar jam’iyyar J.M.T. kuma na yi
hakan ne ba domin ina son tara abin duniya ko neman suna ba ”
(Surajo,2006: 71).
Farfesa Auta ne yake bayyana aniyarsa ga al’umma a wajen taron
yaƙin neman zaɓe na neman takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin tutar jam’iyyarsu,
inda yake nuna cewa ya fito takara ne don ya hidimta wa al’umma, ta hanyar warware
matsalolin da suka addabe su , ba don ya tara abin duniya ba.
Irin wannan yaƙin neman zaɓen ba rana guda ake gudanar da shi
ba.
Akan tsara yin tafiye-tafiye zuwa lungu da saƙo na mazaɓu. Kuma akan
bayar da tsari da ranar da za a fara da kuma ranar kammala yaƙin neman zaɓen. Jaridar
Leadership Hausa ta ruwaito wani batu
dangane da fara yaƙin neman zaɓe a jamhuriya ta huɗu kamar haka:
“Fara yaƙin neman zaɓe
a tsakiyar makon nan ya kasance tubalin ginin sauya ragamar mulki daga hannun gwamnatin
shugaba Muhammadu Buhari zuwa wata da ‘yan Nijeriya za su zaɓa a shekarar 2023.
Hukumar zaɓe mai zaman ta ƙasa (INEC) a cikin jhamayyalin da ta yi na zaɓen 2023,
ta keɓe ranar 28 ga watan Satumbar 2022 domin fara yaƙin neman zaɓe ga ‘yan takarar
shugaban ƙasa da ‘yan majalisun tarayya, yayin da ‘yan makwannin bayan nan su ma
masu gogoriyon neman kujerun gwamnoni za su fita fagen fama tare da ‘yan takarar
kujerun majalisun dokoki na jihohi.”
(Shuaibu, 2022).
Idan aka dubi wannan batu da jaridar ta kawo za a fahimci cewa
yaƙin neman zaɓe muhimmin al’amari ne a cikin siyasar jam’iyyu, wannan ya sanya
kowane kakar zaɓe ‘yan siyasa kan kai gwauro da mari wajen ganin sun sanya ƙafafunsu
a lungu da saƙo na mazaɓunsu don neman goyon bayan al’umma. A nan an nuna cewa yaƙin
neman zaɓe abu ne wanda hukumar zaɓe kan sanya ranar farawa da kuma ranar kammalawa.
Akan samu bambanci tsakanin ranakun fara yaƙain neman zaɓe na wasu matakai da wasu,
kamar yadda jaridar ta nuna cewa an fara na ‘yan takarar kujerar shugaban ƙasa da
na majalisun tarayya mako biyu kafin a fara na gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi.
Su ma adibai sun riƙa fito da irin waɗannan muhimman abubuwa
na tarihin ginuwar siyasa, musamman abin da ya shafi yaƙin neman zaɓe a cikin ayyukansu.
An samu inda abubuwan da suka shafi yaƙin neman zaɓe suka fito. Ala misali a cikin
littafin Da Bazarku an nuna cewa:
Manyan ‘yan siyasa na kowace jam’iyya sai taruka
suke yi ba dare ba rana. Kullum in ba su wancan gari to kuwa suna wancan ƙauyen
suna yawo kamar shanshani don jawo hankulan magoya bayansu da neman ƙuri’a.
(Surajo, 2006: 1).
A nan an nuna irin yadda ‘yan siyasa kan tashi ne su hana idonsu
bacci domin fafutukar namen goyon bayan ga jama’a. Sukan riƙa bi lungu da saƙo a
cikin mazaɓunsu domin neman ƙuri’a daga jama’a. Sukan riƙa bi gari-gari suna yi
wa jama’a jawabin manufofinsu da yadda za su ciyar da ƙasa gaba idan aka zaɓe su.
Ba su za su huta ba har sai an kammala zaɓe.
A cikin wannan zagayen yaƙin neman zaɓen sukan riƙa yin jawabi
na jan hankali wanda zai karkato hankalin al’umma su amince cewa idan aka zaɓe su
za a samu cigaban da ake buƙata. Su kuwa ‘yan hamayya sukan nemi wasu matsalolin
da suka daidaibaye gwamnati ne da kuma inda ta gaza, sai su ɗora jawaban yaƙin neman
zaɓensu a kai. Dubi wannan misalin:
“Talakawa lokaci fa ya
yi da a ƙalla ya kamata mu ga in kura ba ta kwana da yunwa ba , to kada akuya ta
kwana da ‘ya’yanta baki ɗaya. Tilas talakawa ku fito ranar zaɓe ƙwanku da ƙwarƙwata
ku nuna kun gaji da shan ruwan tabki mai kurkunu, alhali ga wasu tattaccen ruwan
famfo ma sai dai a yi ban ruwan filawoyin gidajensu da shi ”
(Surajo, 2006: 70)
Idan aka lura da bayanan da suke cikin wannan misalin za a fahimci
cewa daga bakin ‘yan hamayya ne, domin a ciki an riƙa nuna gazawar gwamnati. A cikin
jawabin an fito da irin wahalar da talakawa suke sha saboda rashin abaubuwan more
rayuwa, kamar tsaftataccen ruwan sha. An nuna shugabanni suna rayuwa ta sharholiya
da fankama; tataccen ruwan famfo ma ba su sha, sai dai a riƙa ban ruwan filawa da
shi. Irin waɗannan su ne irin jawaban da ‘yan hamayya sukan riƙa yi a wajen yaƙin
neman zaɓe domin nuna hamayyarsu da salon mulkin jam’iyya mai mulki don jawo hankalin
jama’a su ƙi jam’iyyar su zaɓi tasu.
Haka kuma, a cikin yaƙin neman zaɓe ‘yan hamayya dai su ne masu
bayyana gazawar gwamnati. A tarihin siyasar ƙasar Hausa ba a yi wani lokacin da
‘yan siyasa ba su yi yaƙin neman zaɓe da batun wutar lantaki ba. Tun daga jamhuriya
ta farko ake alƙawuran samar da wutar lantarki, amma talakawa kullum ba su gani
ba, sannan ga wasu suna facaka da kuɗin gwamnati, talakawa suna cikin wahala. Marubucin
littafin Da Bazarku ya kawo irin wannan
batu a wurin yaƙin neman zaɓe, inda aka ce:
“Sannan kuma ku nuna cewa
kun gaji da wutar a-ci-bal-bal, wutar lantarki da ko wutar kara ta fi ta jinkiri
Lallai ilalla a ƙasar nan mun gaji da tsarin wa-ka-ci-tashi wanda a ƙarƙashinsa
wasu na shan raɓa da darɓa, wasu kuwa na cin kwakwa. Tsarin da ɗaruruwan jama’a
suke mutuwa wasu kuma suna nakasa saboda rashin kuɗin magani.”
(Surajo, 2006: 70)
A cikin jawabinsa ya nuna cewa kada jama’a su zaɓi jam’iyya mai
mulki, domin sun kasa samar masu da wani cigaba mai ma’ana. Wutar lantarkin da ake
ta yi masu romon baka da ita har yanzu ba ta tsaya ba, inda ya nuna cewa ko wutar
kara ta fi ta daɗewa, wato da an kawo ta sai a ɗauke. Haka kuma a cikin wannan misalin
an ga yadda ake nuna wa jama’a gazawar gwamnati ta hanyar nuna irin wahalar da talakawa
suke ciki, su kuwa masu mulki ba su damu ba, tun da abin bai shafe su. Abin yakan
hana a tanadi abubuwan buƙata ga ƙasa har ya kai ga wasu suna mutuwa a asibitoci
saboda rashin kuɗin magani da dai sauran matsaloli na rayuwa. Ta irin wannan salon
ne ‘yan siyasa sukan riƙa gudanar da yaƙin neman zaɓensu wanda yana daga cikin irin
gwagwarmayar da ake yi a siyasance domin samun cigaban ƙasa da na al’umma.
5.2.5 Rarrashin Jama’a
Rarrashin jama’a da yi masu daɗin baki yana daga cikin shika-shikan
siyasa, domin duk wanda ake neman wani abu a wurinsa akan yi amfani da hanyar rarrashi
da balmar baka wajen ganin an samu wannan abin. Sau da dama ‘yan siyasa sukan riƙa
sanyaya harshensu, su sanya zaɓaɓɓun kalmomi na nuna tausayawa ga al’umma. Wasu lokuta har sukan zubar da hawaye da ma kuka riris! Suna nuna
sun san irin mawuyacin halin da suke ciki, kuma su ma abin yana damun su, wannan
ne ma ya sa suka dage wajen gwagwarmayar ganin sun tsamo su daga irin wannan mummunan
halin da suka tsinci kansu a ciki.
A duk lokacin da ‘yan siyasa za su tsaya a gaban talakawa su
yi masu bayani, sukan nuna cewa, talaka yana da muhimanci ƙwarai a gare su don haka
ne ma suke tausaya masa da kuma fatan samun damar da za su fitar da shi daga cikin
ƙangin da aka jefa shi. Za a iya ganin hakan a cikin wannan misalin:
“Ya ku ‘yan’uwana jama’ar
wannan ƙasa ina so in yi amfani da wannan dama domin in ƙara jaddada maku cewa dawowar
dimukoraɗiyya ƙasar nan wata dama ce wadda za ku nuna irin darasin da kuka da ɗauka
daga ciki shekaru aru-aru da aka shafe ana ta muzanta ku ba cas ba as. An yi hakan
ne kuwa ta hanyar Shimfiɗa milkin kama karya, wanda yake cike da hanyoyin rib-da-ciki
da dukiyar al’umma. Waɗannan hanyoyi da suka haɗa da coge da zabtare sun jefa talakawa
cikin tsallen tsinka tsumma.”
(Surajo, 2006: 49).
Idan aka lura da bayanan da suke cikin misalin nan da ke sama,
za a ga cewa jawabi ne a wurin taron siyasa, ta la’akari da yadda aka tsara shi
za a ga yadda aka nuna daɗin baki da rarrashi, kan yadda aka gudanar da mulkin kama-karya
a kan al’umma. Daga yadda mai jawabin ya nuna an fito ne daga mulkin soja domin
ya nuna a lokacin aka dawo ga mulkin dimokuraɗiyya daga mulkin soja , inda yake
nuna cewa wata dama ce da al’umma suka samu domin su farfaɗo daga irin mawuyacin
halin da mulkin na soja ya jefa su a ciki. Ya riƙa nuna cewa an zalunci al’ umma
ba tare da haƙƙi ba, an yi rub-da-ciki a kan dukiyar ƙasa, su kuwa aka bar su baki
buɗe suna hauma-hauma. Irin waɗannan kalmomin na nuna tausayi ta yadda za su daɗaɗa
wa talaka, ya ji kamar mai cetonsa ya zo. Yawancin ‘yan siyasa haka suke yi wa jama’a
daɗin baki don neman mulki, wanda in ba a bi a hankali ba ma wanda ya fi iya daɗin
bakin shi zai yi nasara maimakon wanda ya cancanta.
A wasu lokutan kuma, ‘yan siyasa sukan riƙa amfani da munanan
abubuwan da ake yi a siyasance waɗanda su ma ba su tsira daga aikata su ba, kamar
sayen ƙuri’a da maguɗin zaɓe da dai sauransu, domin su rarrashi jama’a da su. A
irin wannan yanayin akan yi wa talakawa daɗin baki wajen nuna masu cewa kada su
karɓi duk wani abu da zai iya zama sayar da ƙuri’a ne domin zai iya jefa su cikin
matsala daga baya. Dubi wannan misalin:
Kafin in rufe maganata
kuwa sai na jawo hankalin talakawa a kan wani muhimmin lamari na cewa kowa ya ci
ladan kuturu fa dole ne ya yi masa aski, domin haka ina tunatar da mu cewa wani
hanzari fa ba gudu ba ne, don haka kuɗin da ake ba mu don a sauya mana ra’ayinmu
a ranar zaɓe ba fa za su iya yanke mana talauci ba. saboda haka gara mu kare mutuncinmu ”
(Surajo, 2006: 71-72).
A nan ana rarrashin jama’a ne da kada su yarda su sayar da ƙuri’unsu
domin zai sake jefa su cikin matsaloli na waɗansu shekaru masu zuwa. Za a riƙa yi
masu daɗin baki da cewa duk abin da suka ba ku ba fa zai yanke maku talauci ba,
duk da cewa idan ita ma wannan jam’iyyar da take wannan daɗin bakin ta samu dama
irin abin da za ta yi ke nan. Da yawa ‘yan siyasa sukan zama kura da fatar akuya
wajen nuna cewa su ɗin na Allah ne, amma da zarar sun samu dama sun kama madafun
iko sai talakawa su koma gidan jiya.
A wani misalin kuma, an ga yadda ake lallaɓa mutane cikin daɗin
baki da tausayawa tare da nuna masu cewa an zalunce su a mulkin baya. Dubi wannan
misalin:
“Jama’a kun ga dai irin
yadda suka yi mulki, babu waɗanda suka ji daɗi sai ‘yan daudu da karuwai, tumasawa
da kawalai, mawaƙa da masu guɗa. Amma ba talakawan da suka ce suna wakilta ba jam’iyyarmu
jam’iyya ce ta cigaba jam’iyyar taku ce kuma tamu ce baki ɗaya, kuma a cikinku wanda
duk kuka ga yana hali irin na waɗancan mutane to ba shi da mazauni cikin jam’iyyarmu
Yanzu zaɓi ya rage naku ”
(Katsina, 1983: 77).
A nan ana nuna wa talakawa cewa an zalunce su, sun tura mota
ta fesa masu hayaƙi. Babu wanda ya mori mulkin sai wasu shafaffu da mai, wato daga
masu riƙe da muƙaman siyasa sai iyayen gidansu, sai kuma ‘yan korensu da ‘yan barandarsu
da abokan sharholiyarsu irin su ‘yan daudu da karuwai. Ire-iren waɗannan mutane
lalatattu ne kuma masu lalata tarbiyyar ‘ya’yan talakawa. Ba su dama a cikin gwamnati
illa ce babba da take hana samar wa talakawa abubuwan inganta rayuwa.
A wasu lokuta, irin rarrashi da ɗaɗin bakin da ‘yan siyasa sukan
riƙa yi ga jama’a domin su samu goyon bayan su, akan samu lokacin da al’umma takan
farga, ta dawo daga rakiyar jam’iyya ko ‘yan siyasar da ba su tsinana masu komai
ba. Irin wannan ya fito a cikin littafin Mizani
kamar haka:
“Duk wani daɗin baki da
kwantar da kai da Gwamna ya rinƙa yi don ganin ya ja hankulan talakawa sai lamarin
ya gagari kundila. Har takai a lokacin kamfen waɗansu wuraren idan ya je ana yi
masa korara kare a bi shi da jifa ”
(Mustapha da Sabe da Aliyu, 2023: 9).
‘Yan siyasa sukan riƙa nuna ladabi da kwantar da kai ta hanyar
amfani da maganganu masu daɗi domin al’umma su amince da su, amma idan ya kasance
hakan ya maimaitu, kuma kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba, sai jama’a su nuna
rashin amincewa. A wannan misalin an nuna cewa, Gwamna mai ci ne yake neman a sake
zaɓensa a karo na biyu. Kasancewar jama’a ba su gamsu da salon shugabancinsa a wa’adin
farko na mulkinsa ba ya sa, ko da ya dawo neman ƙarin wa’adi na biyu ba su amince
ba. Duk da cewa ya yi amfani da hanyar rarrashi da daɗin baki ga jama’arsa, amma
haƙarsa ba ta cim ma ruwa ba. Har ta kai ga duk inda ya je kamfe akan yi masu ihu
tare da jifar su don nuna alamun ba a son su.
Irin wannan ya ci gaba da mamaituwa a cikin tarihin siyasar ƙasar
Hausa, inda kusan duk gwamnatin da ta zo sai an ce gara wadda ta gabace ta. A kullum
‘yan siyasa cikin daɗin baki da rarrashin jama’a suke, suna nuna cewa abubuwa za
su sauya idan aka ba su haɗin kai, amma kullum jiya wa yau.
5.2.6 Sauya Sheƙa
Sauya sheƙa yana nufin sake wurin zama daga inda ake zuwa wani
daban da ake tunanin ya fi daɗi ko kwanciyar hankali ko kuma biyan buƙata. Sauya
sheƙa yana daga ciki irin gwagwarmayar da ‘yan siyasa suke yi domin samun cigaba
a siyasance. Ba sabon abu ne a cikin siyasar Arewacin Nijeriya ba, domin ya samo
asali tun farkon siyasar jam’iyyu. Masana tarihi sun nuna cewa an samu sauyin sheƙa
daga wasu jam’iyyun siyasa zuwa wasu tun wannan lokaci. Ba ƙasar Hausa kaɗai ba
an samu cikin tarihi cewa ‘yan siyasa na manyan yankunan Nijeriya sun riƙa sauya
sheƙa daga wasu jam’iyyu zuwa wasu bisa wasu dalilai waɗanda suke ganin su ne mafita
a gare su. Mafi yawa sukan bar jam’iyyunsu ne zuwa wasu daban domin rashin fahimta
tsakanin shugabannin jam’iyya ko matsalar shugabanci, ko rashin samun wani abu da
aka yi burin samu ko kuma gazawar jam’iyya wajen aiwatar da manufofinta ga al’umma.
An bayyana cewa sauya sheƙa na farko da aka fara samu a tarihin
siyasar jam’iyyu a Nijeriya shi ne wanda ‘yan jam’iyyar NCNC ta Azikiwe suka fice
zuwa jam’iyyar AG ta Awolowo domin su hana Azikiwe da jam’iyyarsa samun rinjaye
a majalisar wakilai ta yanki Yamma (Iliyasu, 2018:5).
An ci gaba da samun irin wannan sauyin sheƙa daga jma’iyyu daban-daban
har ma da na yankin Arewacin Nijeriya, yayin da wasu sukan bar Jam’iyyar NPC zuwa
NEPU, wasu kuma sai su fice daga NEPU su dawo Jam’iyyar NPC.
Ayyukan adabi na zube
da dama sun fito da ire-iren waɗannan abubuwa da suka shafi sauye-sauyen sheƙa na
jam’iyyun siyasa, inda masu sauya sheƙar suka riƙa bayyana dalilan da suka sa suka
bar inda suka fito zuwa inda suka koma. Dubi wannan misali:
“Malam Yusifu Nadabo Kura
ya ce Alhaji Jamilu Dantata ya ba jama’a kunya. Mallamin yana yin magana ne a bisa
wata sanarwa da Alhaji Jamilu ya yi a cikin “Northern Star” da yake cewa wai dalilin
fitarsa daga NPC ya koma AG wai don bai ga amfanin da ita NPC ta yi wa talakawa
ba, har a kansa ”
(“Jamilu Ya Ji Kunya”, 1959).
A wannan wasiƙar da ta fito a cikin jaridar Sodangi an yi wa wani ɗan jam’iyyar AG ne
martani kan sanarwar da ya bayar na barin jam’iyyar NPC zuwa jam’iyyar AG bisa dalilin
nuna rashin gamsuwa da irin yadda gwamnatin NPC ɗin take gudanar da shugabancinta,
inda ya ce babu abin da ta tsinana wa talakawa. Don haka ne ya fita ya koma wata
wadda ba ita ba.
A farkon siyasar jam’iyyu an riƙa danganta jam’iyyun da addinin
Musulunci inda wasu suke ɗauka akwai jam’iyyar da ta dace da Musulmi da wadda ba
ta dace da musulmi ba. Galibi masu irin wannan tunanin cusa masu wannan ra’ayi ake
yi ta hanyar yabon jam’iyyar da ba tasu ba tare da kushe wadda suke ciki ta hanyar
nuna masu wasu abubuwa da za a danganta su da yin takin saƙa da koyarwar Musulunci.
Wannan kan sa su amince cewa jam’iyyar da suke ciki ba ta dace da su ba domin ta
yi wa addininsu karan tsaye. Dubi wannan misali:
“Rannan muna taron jam’iyyar
NPC a Gwangwazo cikin birnin Kano sai kuwa muka ga wata takarda daga wani saurayi
mai suna Salihu Usman cewa ya fita daga NEPU ya shiga jam’iyyar NPC wadda ta fi
dacewa da addininsa na Musulunci ”
(Durumi Iya, 1959).
A nan ana nuna yadda wani saurayi ne ya sauya sheƙa daga jam’iyyarsa
ta NEPU ya koma jam’iyyar NPC, inda ya nuna dalilinsa na sauyin sheƙar da cewa,
jam’iyyar da ya bari ba ta dace da addinin Musulunci ba, wadda ya koma ita ce ta
fi dacewa da addininsa na Musulunci.
A wani misalin na daban da aka ruwaito daga jaridar Sodangi, an bayyana wani ɗan NEPU da yake
bayanin sauyin sheƙarsa daga jam’iyyar NEPU zuwa NPC kamar haka:
“ Maigari Ashura, sakataren
NEPU ya koma NPC. A cikin jawabinsa Maigari ya ce, ‘Na yi babban arziƙi da na gane
wa kaina na kuma yi tunani mai ƙarfi na bar jam’iyyar nan ta NEPU wadda a dalilinta
ne ƙasar nan ta kasa zama cikin aminci sai yawan hargitsi. Yanzu ni Maigari zan
bauta wa NPC wato, jam’iyyar mutanen Arewa ba da baki ba.”
(Kafin Hausa, 1960).
A cikin wannan rahoton da jaridar ta kawo, Maigari Ashura ya
bayyana dalilan da suka sanya ya fice daga jam’iyyar NEPU inda ya nuna cewa jam’iyya
ce mai son yawan hargitsi wanda ya sa aka kasa samun zaman lafiya a ƙasa. A cewarsa
ya yi babban arziƙi da ya fahimci hakan kuma ya bar jam’iyyar, inda ya yi alƙawarin
bauta wa sabuwar jam’iyyarsa ta NPC, inda ya ce ita ce jam’iyyar mutanen Arewa,
wato ita ce ta dace da ‘yan Arewa, kuma shi ɗan Arewa ne. Don haka zai bauta wa
sabuwar jam’iyyar da ya koma ba da baki kaɗai ba, da iyaka ƙarfinsa domin ganin
ta kai ga nasara.
A wani misalin na daban kuma, jaridar Sodangi ta kawo rahoton wani sakataren kuɗi na jam’iyyar NEPU wanda
ya fice ya koma jam’iyyar NPC, inda ya nuna cewa wai jam’iyyar ba ta dace da ‘yan
Arewa na asali ba, wato dai duk wanda aka gan shi a cikin jam’iyyar ko dai ba ɗan
Arewa ne ba, ko kuma ya shiga ne don rashin sanin dacewar hakan. Ga abin da aka
ce:
“A wannan garin ne wani
sakataren kuɗi na NEPU mai suna Usman Durum ya ce ya bar NEPU ya kuma shiga jam’iyyar
NPC ya bar ta ne saboda wai ita NEPU ba ta dace da duk mutumin Arewa na asali ba
har wa yau kuma wasu mutum takwas sun fita daga wannan jam’iyyar sun shiga jam’iyyar
NPC.”
(“Ya fita Daga NEPU”, 1960).
Cikin wannan misalin za a lura cewa, shi wannan wanda ya fice
daga NEPU ba ma wai kawai mai goyon bayan jam’iyyar ne kaɗai ba, yana ma riƙe da
muƙamin sakataren kuɗi na jam’iyyar, amma ya ajiye ya fita.
Idan aka dubi duk waɗannan misalai da aka kawo a sama za a ga
cewa, duk ‘yan hamayya ne suke ficewa suke dawowa cikin jam’iyya mai mulki bisa
dalilan da suka bayyana. Wani misali na sauya sheƙa daga wata jam’iyya, an samu
daga jaridar Daily Comet, inda aka ce:
“Jama’a zan tunantar da
ku cewa ba mamaki mutumin da yake NEPU ya koma NPC. A’a ya je bude idone ni dai
na fita daga NPC na koma jam’iyyar talakawa kuma mai kaunar zaman jin dadin talakawan
NEPU sawaba.”
(Gasakas, 1961).
A nan wani ɗan jam’iyyar
NPC ne yake bayyana fitarsa daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar NEPU, inda ya nuna cewa
da wuya ka ga wanda zai fita daga jam’iyyar NEPU ya koma NPC da zuciya ɗaya, sai
ko ya je leƙen asiri. In kuwa aka samu hakan gaskiya zai zama abin mamaki, domin
da wuya talaka ya bi NPC. A nan sai ya bayyana cewa ya fita NPC ya koma jam’iyyar
talakawa mai ƙaunar ganin talakawa cikin jin daɗi da walwala.
Irin waɗannan sauye-sauyen sheƙa sun yi ta faruwa har zuwa jamhuriya
ta biyu, inda aka samu wasu ‘yan siyasa suka riƙa barin wasu jam’iyyu zuwa wasu.
An bayyana cewa, duk da Alhaji Abubakar Rimi ya yi nasarar zama gwamnan Kano a jamhuriya
ta biyu a ƙarƙashin tutar jam’iyyar PRP ne, amma lokacin da dangantaka ta yi tsami
tsakaninsa da maigidansa a siyasance wato Malam Aminu Kano sai ya sauya sheƙa zuwa
jam’iyyar NPP[3], kuma a wannan lokacin
ma an samu sauye-sauyen sheƙa da dama zuwa wasu jam’iyyu. Alal misali, dubi abin
da jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ruwaito:
“A kwanan baya ne sama
da mutane ɗari biyar (500) magoya bayan jam’iyyar G.N.P.P ɓangaren Mahmoud Waziri,
suka fice daga cikin jam’iyyar suka koma sheƙar N.P.N a yankin mulki na Talatar
Mafara. Wannan ficewar ta biyo bayan wani namijin ƙoƙari da jam’iyyar N.P.N wanda
ta bayyana da cewa, ƙwato mutane daga durmuya cikin kogin ɓata da nutsewa wanda
tuni jirgin jam’iyyar G.N.P.P ya daɗe wargajewa kuma ‘ya’yanta na cikin halin ƙaƙa-nika-yi.”
(Sakkwato, 1983).
A nan an bayyana yadda wasu ‘yan jam’iyyar GNPP su ɗari biyar
suka sauya sheƙa daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar NPN. An nuna cewa jam’iyyar ta NPN
ce ta ɗaura ɗamarar ceto jama’a daga dulmiyewa a cikin kogin ɓata na jam’iyyar ta
GNPP. A ganin ‘yan NPN duk wanda ya shiga jam’iyyar GNPP ya ɓata, su kuma ba za
su so suna kallo ‘yan’uwansu su faɗa cikin halaka ba tare da sun ceto su ba. Hakan
ya sa suka tashi tsaye wajen ganin sun ceto su domin su shiga jam’iyya NPN su tsira.
Jamhuriya ta huɗu ma ta yi fama da irin wannan sauye-sauyen sheƙar
da ‘yan siyasa sukan yi, kusan ma za a iya cewa a wannan jamhuriyar ne abin ya fi
shahara. A sauran zamunnan siyasar da aka yi a baya wato jamhuriya ta ɗaya da ta
biyu an danganta sauya sheƙa da wasu dalilai da suka shafi aƙida a siyasa da fafutukar
ciyar da jam’iyya da al’umma da kuma ƙasa gaba, amma a wannan jamhuriyar da muke
ciki wato jamhuriya ta huɗu an fi danganta shi da son kai da neman gindin zama a
siyasa da kuma son mulki da son tara dukiya.[4] Wannan ne ya sa ‘yan
siyasa suka riƙa sauya sheƙa daga wannan jam’iyya zuwa waccan, domin samun biyan
buƙatarsu a siyasance. A yau da wuya a ji wani ɗan siyasa da ya fita daga jam’iyya
mai mulki ya koma jam’iyyar hamayya a lokacin da jam’iyyar take tsaka da mulki ba
tare da wa’adinta ya zo ƙarshe ba. Yawancin masu sauya sheƙa sukan bar jam’iyyun
hamayya ne musamman idan ba su yi nasara ba, ko alamomin faɗuwa zaɓe sun bayyana
ga jam’iyyarsu ko rashin samun damar tsayawa takara ko kuma biyayya ga ubangidansu
na siyasa. A wasu lokuta waɗanda ba su nasara a zaɓe ba sukan koma jam’iyyar da
ta yi nasara domin samun mafakar siyasa. Akwai ire-iren waɗannan misalai da dama
da suka fito a cikin rubutaccen zube wanda aka samu da suke ɗauke da wannan fasalin
na sauye-sauyen sheƙa da yan siyasa suka yi a jamhuriya ta huɗu. Ga wani misali:
“Ɗan takarar shugaban
ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar ANPP a zaɓen shekara ta 2003 da 2007, Janar Muhammadu
Buhari ya fice daga jam’iyyar ta ANPP. Wata takarda da Janar Buhari ya aike wa jam’iyyar
a ranar Litinin 1 ga Fabrairu ce ta tabbatar da ficewar janar Buhari daga jam’iyyar
Takardar ta Janar Buhari ba ta bayyana ko ya fice daga jam’iyyar ce da niyyar komawa
wata ko kafa wata sabuwa, ko kuwa zai jingine siyasa ba. ”
(Maƙera, 2010)
A cikin wannan misalin, an nuna yadda jagoran hamayya na wancan
lokacin wato Janar Muhammadu Buhari ya bar jam’iyyarsa ta ANPP ne, duk da cewa ya
yi takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar har sau biyu. Duk da cewa a lokacin
da ya bayar da sanarwar ficewan bai ayyana jam’iyyar da zai koma ba, amma dai jaridar
ta yi hasashen cewa kodai zai sauya jam’iyya, ko ya kafa wata sabuwar jam’iyyar
ko kuma ya haƙura da siyasar baki ɗaya. Kodayake a wani bayani da aka samu a jaridar
Aminiya ta 26 ga Fabrairu 2010, an yi
hasashen cewa Janar ɗin ya doshi jam’iyyar CPC ne, kuma hakan aka yi. Dubi abin
da jaridar ta ce:
Duk da babu wani furuci
da aka samu daga Janar Buhari a kan jam’iyyar da zai je ya baje kolinsa cikinta,
amma dai rahotanni na ta nunin da cewa zai doshi jam’iyyar CPC, wacce Sanata Rufa’i
Sani Hanga yake yi wa shugabancin riƙo
(Kankiya, 2010).
An nuna cewa, akwai yiwuwar bayan ayyana fitar Janar Buhari daga
jam’iyyar ANNP ba barin siyasa ko kafa wata sabuwar jam’iyyar zai yi ba, maimakon
haka zai sauya sheƙa ne zuwa jam’iyyar APC wadda su Sanata Rufa’i Hanga suka kafa
kuma kuma yake yi mata shugabancin na riƙo. Daga ƙarshe dai an ayyyana cewa Janar
Buhari ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar CPC, inda ya yi wa jam’iyyar takarar shugaban
ƙasa a zaɓen shekarar 2011.
‘Yan siyasa na jam’iyyu daban-daban sun ci gaba da sauya sheƙa
daga jam’iyyunsu zuwa wasu jam’iyyun daban-daban domin neman mafita a siyasance.
An ƙara samun wani misalin da ya nuna irin sauyin sheƙan da ‘yan siyasa da ‘yan
takara suke yi musamman a lokacin da aka buga kugen siyasa. Ga wani misalin:
“Ganin yadda ‘yan watannin
suka rage a shiga cikin ruguntsumin tallar ‘yan takara na zaɓen shekara ta 2011
ya sa tuni ‘yan siyasa suka fara canza sheƙa, tare da ɗaukar matakan da suke ganin
za su kai su ga samun nasarar cin zaɓukan muƙaman da suke neman tsayawa. Na baya-bayan
nan shi ne Sanata Sahabi Ya’u da ke wakiltar jihar Zamfara ta Arewa a Majalisar
Dattijai a ƙasa, wanda ya canza sheƙa daga jam’iyyarsa ta ANPP zuwa Jam’iyyar PDP
mai mulkin ƙasa ”
(Ɗambatta, 2010).
A cikin wannan rahoton an nuna cewa, ‘yan siyasa sukan riƙa sauya
sheƙa daga jam’iyyun da suke ciki zuwa wasu daban in an kusa fara tallar ‘yan takara
na kakar zaɓe. a cikin wannan misalin da aka kawo a sama za a fahimci cewa, daga
cikin dalilan da suke sa ‘yan siyasa sauyin sheƙa akwai rashin samun damar tsayawa
takara. Akan samu jam’iyya ta ayyana ɗan takara guda ba tare da bai wa sauran ‘yan
jam’iyya damar tsayawa don kaiwa ga zaɓen fitar da gwani ba. Wannan yakan haifar
da fushi ga wasu masu sha’awar tsayawa takarar, tare da tunanin an tauye masu haƙƙinsu
da tsarin mulki ya ba su na tsayawa. Wannan sai ya sa su fice daga jam’iyyar zuwa
wata. A cikin misalin an nuna yadda wani ɗan majalisar dattijai daga jihar Zamfara
mai suna Sanata Sahabi Ya’u ya ayyana ficewarsa daga jam’iyyar ANPP ya koma jam’iyyar
PDP mai mulki a wancan lokaci. Ya nuna cewa rikice-rikicen da ake fama da su ne
a jam’iyyar suna tilasta masa sauyin sheƙar da ya yi.
A wasu lokuta akan samu wasu tawaga na shugabannin jam’iyya ko
masu riƙe da mjuƙamai daban-daban a cikin jam’iyya su haɗu su fice daga cikin jam’iyyar
da suke wa shugabanci tare da yyana sauyin sheƙa zuwa wata jam’iyya a lokaci guda.
Irin wannan ya faru a tarihin siyasar ƙasar Hausa, inda jaridar Aminiya ta ranar 7 ga watan Mayu, 2010 ta
buga wani labari da ya nuna cewa, shugabannin jam’iyyar ANPP da magoya bayansu baki
ɗaya sun fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar CPC ta Janar Muhammadu Buhari. Ga abin
da jaridar ta ce:
“Babu sauran mutum guda
da ya ragu a cikin jam’iyyar ANPP ta jihar Kebbi. Tsohon shugaban jam’iyyar ANPP
na jihar Kebbi Alhaji musa Abubakar Argungu Ɗanmalikin Kebbi, ya bayyana haka a
lokacin da suka kira taron manema labarai domin bayyana aniyarsu ta canza sheƙa
daga jam’iyyar ANPP zuwa sabuwar jam’iyyar CPC sun yanke shawarar barin jam’iyyar
ANPP zuwa sabuwar jam’iyyar CPC domin amincewa da aƙidun da Janar Buhari yake da
su ”
(Zakka, 2010).
A cikin wannan rahoton an nuna sauyin sheƙar shugabannin jam’iyyar
ANPP ne tare da magoya bayansu baki ɗaya zuwa jam’iyyar CPC a jihar Kebbi. Dangane
da dalilin sauya sheƙar tasu sun nuna cewa, goyon baya tare da amincewa da aƙidun
janar Muhammadu ne ya sa suka bar jam’iyyar ANPP zuwa sabuwar jam’iyyar Buhari a
wancan lokaci.
Idan aka dubi misalin da yake sama, za a ga cewa, shugabannin
jam’iyya ne tare da magoya bayansu suka sauya sheƙa baki ɗaya zuwa wata jam’iyya
daban. Akan kuma samu inda ‘ya’yan jam’iyya kan haɗu ba tare da shugabanninsu ba
su bayyana sauya sheƙ daga jam’iyyar da suke zuwa wata jam’iyya daban, kamar yadda
aka samua a cikin jaridar Leadership Hausa kamar haka:
“Dimbin ‘ya’yan jam’iyyar
PDP sun sauya sheƙa zuwa APC a ƙaramar hukumar Danja da ke jihar Katsina. Gwamnan
jihar Katsina, Aminu Bello Masari shi ne ya amshi ‘ya’yan jam’iyyar PDP da suka
sauya sheƙa a gidan gwamnatin jihar Katsina. An dai bayyana cewa kimanin mambobin
jam’iyyar PDP guda 1,700 suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a gidan gwamnati.”
(Katsina, 2022)
Idan aka dubi wannan misalin, za a ga cewa, ‘ya’yan jam’iyyar
PDP su kimanin dubu ɗaya da ɗari bakwai daga ƙaramar hukumar Ɗanja ta jihar Katsina
ne suka sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC a kakar zaɓen 2023, inda aka
nuna cewa sun tafi har gidan gwamnatin jihar domin bayyana aniyar tasu. An kuma
nuna cewa, Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari ne ya karɓe su a gidan gwamnati. Irin
waɗannan misalan na sauye-sauyen sheƙa sun zama ruwan dare a cikin siyasar ƙsar
Hausa. Wannan ba zai rasa nasaba da yadda al’umma sukan riƙa lura da jam’iyyar da
ta nuna alamar samun nasara ba, sai su koma su bita don kada a yi nasara ba tare
da su ba a bar su a baya. A waɗannan misalan idan aka duba za a fahimci cewa adadin
mutanen da suke sauya sheƙa a jamhuriya ta huɗu ya zarce na sauran jamhuriyoyin
baya.
Irin wannan fasalin na sauya jam’iyyar siyasa ya riƙa fitowa
a cikin rubutattun labaran zube na Hausa, inda marubutan suka riƙa nuna sauya sheƙa
da ‘yan siyasa kan yi daga wata jam’iyya zuwa ta wata. Dubi wannan misalin:
“ Wannan irin al’amari
sauran abokan hamayya na wasu jam’iyyu suka rinka yin wankan tsarki suna komawa
cikin jam’iyyar JTT ta su Malam Nazifi Abdulkadir.”
(Jiƙamshi, 1997: 47).
Kamar yadda aka bayyana cewa dalilai da dama kan sa ‘yan siyasa
su sauya sheƙa daga jam’iyyarsu zuwa wata daban, a wannan misalin marubucin ya nuna
Malam Nazifi ne a matsayin adalin shugaba mai hangen nesa da kuma sauraron koke-koken
talakawansa. Ya duƙufa ainun wajen kyautata rayuwarsu ta hanyar samar masu da abubuwan
da za su bunƙasa tattalin arziƙinsu da walwala da jin daɗinsu. Wannan ya sa jama’a
suka ba shi haɗin kai har ma waɗanda ba ‘yan jam’iyyarsa ba suka riƙa sauya sheƙa
daga tasu jam’iyyar zuwa jam’iyya mai mulki domin gamsuwa da ayyukan cigaba da wannan
jam’iyyar ta su Malam Nazifi take aiwatarwa.
Irin wannan misali ya sake fitowa a cikin littafin Kowa Ya Bi inda aka nuna Gwamna Yaji a matsayin
mutum mai tsoron Allah da son gaskiya da kuma kiyaye haƙƙin talakawansa, wanda wannan
ya ƙara wa jam’iyyarsa ta RPP farin jini wanda har ‘yan siyasa masu ra’ayin kawo
sauyi suka riƙa sauya sheƙa zuwa jam’iyyar gwamna. Ga misali:
“ ’yan siyasa masu rajin
kawo sauyi a siyasar ƙasar suka dinga fallewa suna kafa wasu, wasu komawa suke yi
jam’iyyar RPP wato jam’iyyar gwamna Yaji wacce da ita ma me zaman kanta ce kafin
ta ci zaɓe.”
(Isa, 2007: 33).
A cikin wannan misalin, an nuna cewa ‘yan siyasa masu son kawo
sauyi da cigaba ga al’umma, sai suka riƙa sauya sheƙa daga jam’iyyunsu zuwa jam’iyyar
RPP ta Gwamna, kasancewarsa mutum mai adalci da son kawo cigaba ga al’umma.
Irin wannan gwagwarmaya da ‘yan siyasa suke yi da sunan samar
da cigaba ga al’umman da suke wakilta abu ne wanda ya wanzu cikin tarihin siyasar
jam’iyyu a ƙasar Hausa, kuma an yi amfani da shi a cikin dukkan jamhuriyoyin da
aka samu a cikin siyasar Arewacin Nijeriya. Wannan ya sa suka bayyana a cikin ayyukan
rubutaccen adabi waɗanda aka kafa misalai da su.
5.2.7 Haɗakar jam’iyyu
Haɗakar jam’iyyu a siyasar ƙasar Hausa ya samo asali tun daga
jamhuriya ta ɗaya, inda aka samu wasu jam’iyyu suka yi ƙawance domin kafa gwamnatin
haɗin kan ƙasa. Alal misali, jam’iyyar NCNC ta ƙulla ƙawance da NEPU a farko, kuma
sun haɗa kai da NPC bayan samun ‘yancin kai domin gudanar da gwamnatin haɗin kan
ƙasa. Ƙawance a siyasa yanayi ne da jam’iyyu biyu ko fiye sukan ƙulla yarjejeniyar
tafiya tare domin cimma wata manufa, musamman a kan jam’iyya mai mulki, domin a
samu nasara ka da ita a zaɓe, ko kuma don gudanar da shugabanci cikin sauƙi ta hanyar
haɗa kan jam’iyyu da gudanar da shugabanci tare. Wannan ya tabbata inda jaridu suka
fito ire-iren waɗannan bayanan kamar haka:
“ daga baya sai muka ji Malam Aminu Kano shugaban
NEPU ya ba da wani labari a Rediyo cewa shi bai ga dalilin da zai sa NCNC ƙawar
NEPU ta haɗa kai da NPC don su kafa Gwamnati ba ”
(Haɗejia, 1959).
Daga wannan abin da aka tsakuro daga wannan jaridar za a fahimci
cewa yin haɗaka ga jam’iyyun siyasa abu ne mai dogon tarihi a cikin siyasar ƙasar
Hausa, domin kuwa cikin wannan misalin an nuna ce
wa NCNC sun ƙulla ƙawance da NEPU, don haka babu dalilin da zai
sa kuma ta sake ƙulla kawance da abokiyar hamayyarta wato NPC. Abin nufi sai dai
ta tsaya wa ɗaya ko dai NEPU ko NPC kamar yadda misalin ya nuna. Wato dai irin abin
nan da masu hikimar magana suke cewa; abokin mutum biyu, munafukin mutum ɗaya ne.
Bayan an samu ‘yancin ƙasa gwamantin NPC ta nemi haɗin kan sauran
jam’iyyu domin samar da gwamnatin haɗin kan ƙasa. A cewar NPC ba za ta iya gudanar
da mulki ba tare da haɗin kan abokan hamayya ba. Wannan ya sa ta kawo shawarar kafa
gwamnati wadda za ta haɗa wakilcin kowane yanki na ƙasa domin samun haɗin kan al’ummar
ƙasar ba tare da wani yanki ya ji cewa an mayar da shi saniyar ware ba. Wannan dalilin
ne ya haifar da ƙawancen manyan jam’iyyu uku wato NPC da NCNC da kuma NEPU. Wannan
haɗin kai da aka samu wajen tafiyar da al’amuran mulki bai yi wa wasu ‘yan NEPU
daɗi ba, inda har suka zargi Malam Aminu Kano da sayar da su ga ‘yan hamayya, wannan
ya sa suka ba da sanarwar ficewa daga jam’iyyar NEPU. Dubi abin da jaridar Sodangi
ta ruwaito:
“ cikin dalilan da suka
bayar na fitarsu daga NEPU sun ce wai yardar da Malam Aminu Kano ya yi na kan haɗa
gwamnatin NPC da NCNC ba tare da shawartar masu goyon bayan NEPU ba ”
(“‘Yan NEPU 3 Sun Fita”, 1960).
A nan jaridar ta kawo labarin wasu ‘yan NEPU ne su uku da suka
fita daga jam’iyyar, inda suka bayyana dalilansu na ficewa da cewa, Malam Aminu
ya yarda ya haɗa kai da gwamnatin NPC da NCNC ba tare da ya shawarci magoya bayan
jam’iyyarsa ta NEPU ba, don haka suke ganin cewa kamar akwai wata ƙullalliya ce
a ƙasa. Idan aka duba za a ga cewa a nan ma akwai batun haɗakar jam’iyyu domin samar
da cigaban ƙasa, domin an nuna cewa jam’iyyun daga manyan yankunan siyasar Nijeriya
sun haɗa kai domin tafiyar da gwamnati guda ba tare da dunƙulewa a matsayin jam’iyya
guda ba.
A wani misalin da yake nuna haɗakar jam’iyyu an nuna cewa lokacin
da zaɓen ‘yan majalisar ƙasa ya matso wasu daga cikin ‘yan NEPU sun fara raɗa wa
junansu cewa in so samu ne jam’iyyar ta yi haɗaka da jam’iyyar AG ta Awolowo domin
su samu su kayar da jam’iyyar NPC, sai shugaban NEPU ya gargaɗe su cewa su bar wannan
zancen domin babu shi. Dubi wannan misalin da yake biye:
“ inda ya yi wa taron
gargaɗi game da wadansu yan jam’iyyar da suke ta surutai wai idan NEPU ta haɗu da
AG a wannan zabe mai zuwa za a kayar da NPC ”
(“Babban Taron NEPU Na Shekara”, 1961).
Jaridar ta kawo rahoto ne kan babban taron NEPU ne na ƙasa baki
ɗaya, wanda a cikin jawabin taron aka nuna cewa babu batun haɗakar da ake fata tsakanin
NEPU da AG, shugaban ya gargaɗe su domin su daina. A nan dai abin da ake so a nuna
shi ne batun haɗakar jam’iyyu, inda akan samu fahimtar juna tsakanin jam’iyyu biyu
ta yadda za su tunkari zaɓe ko wasu al’amuran ƙasa domin su kai ga nasara.
A jamhuriya ta biyu ma an samu haɗakar jam’iyyu, inda aka nuna
cewa jam’iyyar NPN mai mulki ta ƙulla ƙawance da jam’iyyar NPP, kamar yadda ya fito
a jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ranar
13 ga watan Fabrairu 1981. Ga shi kamar haka:
“Duk wanda ya lura da
yadda al’amura ke gudana tsakanin jam’iyyar NPN da NPP, jam’iyyoyi biyun da suka
ƙulla ƙawance don jin daɗin tafiyar da harkokin gwamnatin tarayyar ƙasar nan, ya
san lalle shirin ƙawancen ba ma cewa za a yi yana neman ya sukurkuce ba, har sai
mai lura ya ce ƙwancen ya ma sukurkuce Jam’iyyar NPN dai ta sami kanta cikin halin
da yake dole ta lura da take-taken ƙawarta, don kuwa ga alama dai tana karkata wajen
mara wa jam’iyyar UPN abokiyar hamayyar NPN baya. Hausawa kan ce abokin mutum biyu,
munafukin mutum ɗaya.”
(“Ƙawancen NPN da NPP”, 1981).
Idan aka dubi bayanan da suke cikin wannan misalin da yake sama
za a fahimci cewa jam’iyyun NPN da NPP sun ƙulla ƙawance domin jin daɗin tafiyar
da harkokin mulki ƙasa. Daga bisani sai aka samu matsala wannan ƙawance ta warware
kamar yadda misalin ya nuna. Bayanai na tarihi sun nuna cewa, gwamnatin NPN a jamhuriya
ta biyu ta naɗa wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar NPP ministoci, wasu kuma ta tura
su jakadun Nijeriya a wasu ƙasashe, amma daga baya sai aka nuna cewa alaƙar ta kwance,
inda aka ce ‘yan jam’iyyar ta NPP suna mara wa jam’iyyar UPN baya a majalisar ƙasa.
Ita kuwa jam’iyyar UPN ta kasance abokiyar hamayyar NPN ce. Wannan ya sa aka yi
zargin cewa, abokin mutum biyu, munafukin mutum ɗaya ne. Wato jam’iyyar NPP tana
yi wa NPN zagon ƙasa ke nan. Abin dai da ya kamata a lura da shi a nan shi ne, an
samu ƙawance tsakanin jam’iyyun siyasa a wannan zamanin, kamar yadda ayyuka na rubutaccen
zube ya nuna.
Tarihin siyasar jam’iyyu ba zai manta da haɗakar jam’iyyu mafi
girma da aka yi a Nijeriya ba, inda a jamhuriya ta huɗu aka samu haɗakar da ta kai
ga wasu jam’iyyu guda huɗu, wato; ANPP da ACN da CPC da wani ɓangare na jam’iyyar
APGA, suka haɗu, suka cimma matsaya, inda suka yarda suka haɗe wuri ɗaya, suka samar
da jam’iyyar hamayya mai ƙarfi ta APC, wadda ta iya karawa da jam’iyya mai mulki
a lokacin wato PDP kuma suka samu nasara. Tun lokacin da aka fara shirye-shiryen
wannan haɗakar jam’iyyu sun riƙa tuntuɓar ‘ya’yansu domin samun amincewarsu da kuma
goyon bayansu, kamar yadda jaridar Aminiya
ta ranar 25 ga Janairu, 2013 ta bayyana kamar haka:
“Shugaban kwamitin da
jam’iyyar ANPP ta ƙasa ta kafa domin farfaɗo da jam’iyyar da duba yiwuwar haɗewarta
da wasu jam’iyyun hamayya Malam Ibrahim Shekarau, ya tabbatar da cewa a watan Afrilu
mai zuwa ne ake sa ran kammala batun haɗewar ya ci gaba da cewa yanzu haka jam’iyyun
ANPP da ACN da CPC kowacce ta kafa kwamitoci masu ƙarfi da suka fara shirye shriye-shiryen
tattaunawa inda a ƙarshe za mu kafa wasu kwamitocin da za su yi aikin duba ƙa’idar
jam’iyya da sunanta da alamarta da abin da za ta sanya a gaba, domin wannan haɗewa
da muke shirin yi ba a taɓa samun irinta a tarihin siyasar Nijeriya ba. Don haka
muke so sauran jam’iyyu su zo mu tafi, kowace jam’iyya ta jingine buƙatunta mu sa
manufofi da ƙa’idoji da za a samar da alƙibla da mafita ga halin da ‘yan Nijeriya
suke ciki.”
(Ali, 2013).
Idan aka dubi wannan misalin da yake sama za fahimci cewa, batun
haɗakar jam’iyyu abu ne wanda yake buƙatar tattaunawa tsakanin shugabanni da magoya
bayan jam’iyyu daban-daban domin samun amincewarsu. Rashin samun amincewar wani
ɓangare kan haifar da matsalolin da yakan hana haɗakar ɗorewa. Kamar yadda aka gani
a cikin wannan misalin, an kafa kwamitoci domin duba yiwuwar haɗakar da kuma samun
amincewar ‘ya’yan jam’iyyu. A cikin misalin an nuna cewa bayan jam’iyyun hamayya
na ANPP da ACN da CPC sun gama tattaunawa sun amince, sai kuma aka kafa kwamitin
da zai yi aiki domin samar da ayyanannun manufofin jam’iyya da sunan da ya kamata
a raɗa ta da kuma alamar jam’iyyar. Ya nuna cewa irin wannan haɗakar shi ne irinsa
na farko a tarihin ginuwar siyasar Nijeriya. Domin kuwa idan aka dubi waɗanda aka
yi a sauran jamhuriyoyin bayan duk ƙawance ne, wanda aka yi tsakanin jam’iyya mai
mulki da sauran jam’iyyun hamayya domin samun gudanar da mulki cikin sauƙi. Wasu
kuma ƙawance ne da aka ƙulla tsakanin jam’iyyun, amma ba su kai ga narkewa sun zama
jam’iyya guda ba. Irin wannan haɗakar akan yi ta domin neman mafita ga ‘yan ƙasa,
musamman idan jam’iyyun hamayya sun yi ittifaƙin cewa jam’iyya mai mulki ta gaza
cimma manufofin da aka zaɓe ta a kansu. Don haka ne ma kamar yadda misalin ya nuna
aka yi kira ga sauran jam’iyyu da su jingine dukkan buƙatunsu da manufofin jam’iyyunsu,
su zo a dunƙule a samar da jam’iyya guda wadda za ta magance matsalolin da ‘yan
Nijeriya suke ciki.
Batun wannan haɗakar ya ci gaba da bayyana a cikin jaridun Arewacin
Nijeriya, inda aka ci gaba da bibiyar batun da kuma yaɗa shi tare
da fatan ganin tabbatarsa. Jama’a sun ci gaba da bayyana fatar samun jam’iyyar hamayya
mai ƙarfi wadda za ta tunkari jam’iyya mai mulki tare da fatan bai wa Janar Buhari
takara bayan an tabbatar da kammaluwar haɗakar. Domin sake tabbatar da batun haɗakar,
an tarsakuro wani batu da aka samu a cikin jaridar Aminiya wadda ta kawo a cikin wata hira da ta yi da Janar Buhari kamar
haka:
A wata hira da jaridar Aminiya
ta yi da Sanata Abu Ibrahim na jam’iyyar CPC daga jihar Katsina, a ciki ta taɓo
batun haɗakar jam’iyyu inda ya ce:
“Saboda haka abin da ke
gabana a yanzu shi ne, in ga an ci nasarar haɗewar jam’iyyun hamayya, wato CPC da
ACN da kuma ƙila ANPP. Abin da ‘yan Nijeriya ba su sani ba shi ne da zarar jam’iyyun
nan sun haɗe wuri ɗaya dole ne jam’iyyar PDP ta tashi tsaye.”
(Yaba, 2013).
A nan ya nuna cewa akwai batun haɗewar jam’iyyun hamayya wanda
ake tattaunawa, wanda ya nuna cewa idan har aka yi nasarar wannan haɗakar to wajibi
ne jam’iyya mai mulki ta ƙara ɗamara, domin jam’iyyar da za a samar ta hamayya za
ta kasance mai ƙarfin gaske wadda za ta iya ƙwace jagorancin ƙasar a zaɓe mai zuwa.
Duk waɗannan bayanan da jaridun suka kawo suna nuni ne da cewa akwai batun haɗakar
da ake tattauna yiwuwarsa.
Daga bisani bayan jam’iyyun sun cimma matsaya, sun samu amincewa
a tsakaninsu, sai suka ayyana batun haɗewarsu a matsayin jam’iyya guda. Dubi abin
da jaridar ta ce:
“A makonnin baya ne CPC
da jam’iyyun ACN da ANPP da APGA suka amince su narke su kafa jam’iyyar APC.”
(Maƙera da Agbese da Jimoh, 2013).
A cikin wannan misalin da ke sama an nuna
cewa jam’iyyun CPC da ACN da ANPP da wani ɓangare na APGA sun amince su haɗe wuri
guda su narke a matsayin jam’iyya guda ɗaya, inda suka sanya wa sabuwar jam’iyyar
suna APC. Wannan haɗewar da suka yi ya sanya jam’iyyar ta zama jam’iyyar hamayya
mafi girma a Nijeriya, wadda za ta ƙalubalanci jam’iyyar PDP mai mulki a wancan
lokaci.
Bayan ayyana haɗewar jam’iyyun, magoya bayan
jam’iyyun da suka yi wannan haɗakar sun riƙa gudanar da tarurruka domin nuna goyon
bayan ga wannan haɗaka, tare da gatar jam’iyyar ta yi nasarar lashe zaɓen shekarar
2015 kamar yadda jaridar Aminiya ta kawo rahoton wani taro kamar haka:
“Taron dai ya ƙunshi jigogin
jam’iyyar ANPP domin nuna goyon bayansu kan haɗewar manyan jam’iyyun hamayyar ƙasar
nan da suka haɗa da jam’iyyun ANPP da CPC da AC da kuma APGA, waɗanda suka fitar
da jam’iyyar APC don ƙalubalantar PDP a zaɓen shekarar 2015.
(Chinade, 2013)
Wannan haɗakar ita ce irinta ta farko a tarihin siyasar Nijeriya,
domin kuwa shi ne karo na farko da jam’iyyar hamayya ta yi nasarar lashe zaɓe a
matakin ƙasa da ma sauran matakai da dama na jihohi da ƙananan hukumomi, wanda aka
yi a shekar 2015, wadda kuma har zuwa shekarar 2023, jam’iyyar APC ɗin ce take jan
ragamar mulkin ƙasar. Baya ga wannan haɗakar, ba a sake samun wata haɗakar jam’iyyu
ba har zuwa ƙarshen shekarar 2023.
5.2.8 A-Kasa-A-Tsare
Tsarin siyasar jam’iyyu tsari ne wanda ya zo da zaɓe ko jefa
ƙuri’a a cikinsa, wanda akan sanar da ranar zaɓe, al’ummar ƙasa kuma za su fita
domin zaɓen jam’iyyu ko kuma ‘yan takarar da suka kwanta masu a rai. Irin wannan
hanya ta zaɓe an faro ta ne tun lokacin da aka fara siyasar jam’iyyu a ƙasar Hausa.
Galibi al’umma sukan fita ranar zaɓe su tsayu a kan layukan jefa ƙuri’a har zuwa
lokacin da za a kawo kansu su jefa nasu ƙuri’un. A tsari duk wanda ya jefa ƙuri’arsa
yakan bar filin zaɓe ne ya koma gida ya zauna, ya jira bayan an kammala a sanar
da sakamako. Daga bisani an fahimci cewa akan yi amfani da wannan dama na barin
wurin zaɓe a sauya ƙuri’u da wani abu daban wanda ba shi al’umma suka zaɓa ba, wanda
yawanci masu riƙe da madafun iko ne sukan yi amfani da ƙarfin ikon da yake hannunsu
wajen sauya ƙuri’un ta wannan hanyar domin biyan buƙatunsu da na jam’iyyarsu.
Irin wannan salon sauya ƙuri’u bayan an kammala zaɓe ne ya haifar
da wannan salon na a-kasa-a-tsare, wanda ya zama wata hanya ta gwagwarmaya domin
tabbatar da adalci da cigaban ƙasa a siyasance. Wannan tsari ya ba wa talakawa damar
jefawa da tsarewa tare da raka ƙuri’unsu har zuwa inda za a sanar da sakamako ba
tare da an sauya ƙuri’un ta hanyar maguɗi ba. Tunanin shi ne idan dandazon jama’a
suna kusa, zai yi wuya a iya sauya alƙaluman ƙuri’un da aka jefa, wanda sauyawan
yakan iya haifar da tashin hankali da hasarar rayukan jami’an hukumar zaɓe da masu
ruwa da tsaki a kan harkar zaɓen duk rayukansu na iya shiga haɗari.
Irin wannan ya faru a cikin siyasar Arewacin Nijeriya, kuma ya ci gaba da bayyana a cikin ayyukan
rubutaccen adabin Hausa na zube. Alal misali a cikin jamhuriya ta huɗu ne wannan
kalmar ta fi shahara, inda tun daga wuraren shekarar 2003 da Janar Muhammadu Buhari
ya fara fitowa takarar shugabancin ƙasa ya riƙa kira ga mutane cewa su fita su yi
zaɓe, kuma su kare ƙuri’unsu, su kuma raka su zuwa ofishin hukumar zaɓe, su jira
har sai an sanar da sakamako. Dubi wannan bayanin da jaridar Aminiya ta buga cikin wata hira da ta yi
da shugaban kwamitin tsare-tsare na jam’iyyar ANPP a jihar Katsina:
“Matuƙar jama’ar ƙasar
nan za su yi amfani da shawarar Janar Muhammadu Buhari ta tsayawa kusa da akwatunan
zaɓe har sai an gama ƙidayar ƙuri’u, zai yi wuya a yi maguɗi.”
(AbdulRahman, 2007).
Wannan misalin yana nuni ne da shawarar da ɗan takaran shugaban
ƙasa na jam’iyya ANPP a zaɓen shekarar 2007 ya bayar ga talakawa cewa su fita su
jefa ƙuri’a, kuma su tsaya su sanya ido a kan ƙuri’unsu, su tabbatar an ƙidaya ƙuri’un
kuma an sanar da sakamakon zaɓen, don gudun kada a shirya wata maƙarƙashiya. A cewarsa
idan jama’a suka bi wannan shawarar, zai yi wahala a iya yin maguɗi a cikin zaɓen
da za a yi, domin dai komai za a yi ne a gabansu ba tare da wata muna-muna ba.
A shekarar 2015 ma babbar jam’iyyar hamayya ta APC ta sake tabbatar
da wannan tsari na a-kasa-a-tsare ta bakin ɗan takaranta na shugaban ƙasa Janar
Muhammadu Buhari. A cikin wata hira da aka yi da shi, an kawo batun sharuɗɗan da
hukumar zaɓe mai zaman kanta wato INEC ta gindaya cewa, ba a yarda kafafen watsa
labarai su faɗi kowane irin sakamakon zaɓe ba sai ita kaɗai hukumar zaɓen za ta
yi haka. Jaridar ta yi wa ɗan takarar tambaya kamar haka:
“Kamar yadda kake kiran
jama’a su kasa su tsare, ko ka gamsu da wannan sharaɗi da hukumar zaɓen ta gindaya?”
(Baba-Aminu da Ahemba da Salifu da Bivan da Malumfashi, 2014).
A cikin tambayar an nuna cewa ɗan takarar ya yi kira ga masu
zaɓe da su tabbatar sun yi zaɓe, kuma su tsaya su tabbatar da cewa sun tsare ƙuri’unsu
don kada a samu ƙofar maguɗi har sai an sanar da sakamako. Amma sai ga shi hukumar
zaɓe ta ce kada a sanar da sakamako a matakin rumfar zaɓe ko mazaɓa, har sai an
kai ƙarshe, kuma an tattara sakamakon baki ɗaya. Shin ko ya gamsu da wannan sharaɗin
da hukumar ta sanya?
Ɗan takarar shugaban ƙasar ya sake jaddada wannan tsari na a-kasa-a-tsare
a cikin amsar da ya bayar, inda ya ce:
“Ban gamsu ba. Zan buƙaci
jam’iyyata ta aika da isassun wakilai kuma idan ma ta kama su buƙaci masu zaɓe su
bijire wa haka, domin kuwa akwai gyaran da aka yi wa dokokin zaɓe, wanda ya ce za
a bayyana sakamakon zaɓe a kowace rumfar zaɓe da kowace matattarar sakamako da kowace
ƙaramar hukuma da kuma kowace jiha, sannan kuma daga ƙarshe a tattara shi a bayyana
a hedikwatar Hukumar Zaɓe ta ƙasa.”
(Baba-Aminu da wasu, 2014).
A nan ya nuna rashin gamsuwarsa da wannan sharaɗin, inda ya nuna
cewa zai buƙaci jam’iyyarsa ma ta ƙara sanya wakilai da za su sanya ido, kuma idan
ta kama ma za a sanya masu zaɓe su bijire wa wannan sharaɗin. Ya nuna cewa, an yi
wa dokar zaɓe gyara, inda aka amince cewa za a bayyana sakamakon zaɓe a kowace rumfar
zaɓe da matattarar zaɓe da matakin ƙaramar hukuma da jiha da matakin ƙasa. Za a
bayyana adadin ƙuri’un da kowacce jam’iyya ta samu a kowane mataki. Wannan zai bai
wa al’umma damar sanin halin da ake ciki dangane da sakamakon zaɓen tun daga farko
har zuwa ƙarshe. Hakan zai magance matsalar cushe da aringizon ƙuri’u.
Jama’a sun amsa wannan kiran da ɗan takarar kujerar shugaban
ƙasa na wancan lokaci Janar Muhammadu Buhari ya yi, inda suka tsaya tsayin daka
wajen ganin ba a yi masu maguɗi ba, kuma suka kwana ba bacci a ofisoshin hukumar
zaɓe har sai da suka tabbatar an sanar da sakamako, inda aka sanar da ɗan takarar
APC Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaɓe.
Batun a-kasa-a-tsare wani cigaba ne mai muhimmanci a tarihin
siyasar Arewacin Nijeriya, domin idan aka dubi baya kafin jamhuriya ta huɗu babu wannna tsarin.
Kamar yadda wani rahoto da Aminiya ta
buga ya sake tabbatar da samuwar wannan tsari, inda ta nuna cewa talakawa sun fara
sanin ‘yancinsu, tun da suka tsaya suka jajirce sai an ba su abin da suka zaɓa.
Ke nan, wannan ya nuna cewa an yi aiki da tsarin na a-kasa-a-tsare kuma an ga amfanin
sa a zahiri. Ga bayanin da jaridar ta kawo kamar haka:
“Siyasar Nijeriya ta fara
canzawa, a kasa, a tsare a raka, a jira, a faɗa da talakwa suka yi yana nuna yadda
mutane suka san ‘yancinsu.”
(Mustapha, 2015).
Wannan misalin yana nuna cewa, yadda aka yi ta zargin gwamnati
da shirya maguɗin zaɓe, al’umma sun farga sun fara tsayuwa suna kare ƙuri’unsu sakamakon
kiran da ɗan takara na jam’iyyar hamayya ta wancan lokacin ya yi na a tabbatar an
kare ƙuri’un da aka jefa har zuwa lokacin da aka sanar da sakamako. Talakawa sun
fito sun kare ‘yancinsu.
Irin wannan ya ci gaba da bayyana a cikin rubutaccen zube na
Hausa inda aka riƙa nuna yadda mutane suke gwagwarmayar samun ci gaba ta hanyar
kare ƙuri’un da suka jefa., domin a yawancin lokuta talakawa sukan yi sakaci da
ƙuri’unsu tun daga tashoshin zaɓe ne, inda daga nan ne ake samun damar yi masu maguɗi
kafin a kai ga ofishin hukumar zaɓe kamar yadda wannan marubucin ya nuna:
“ a ranar zaɓe in dai
talakawa suka yi sakaci suka jefa ƙuri’a , sannan ba su yi basirar tsarewa su ga
tabbacin haƙiƙanin gaskiyar yawan ƙuri’ar da suka jefa ba, tare da rakiya zuwa ofishin
hukumar zaɓe inda kuwa muka iske talakawa sun kasa sun tsare, to sai mu duba yiwuwar
amfani da jami’ai masu kayan sarki in kuwa talakawan an yi rashin sa’a na samun
su da kafiya da kuma jajircewa to kun ga dole abin da za mu iya yi shi ne mu yi
amfani da ‘yan bangarmu na wannan jam’iyya ”
(Surajo, 2006: 109-110).
A nan ana so a fito da yadda gwagwarmayar a-kasa-a-tsare take
da tasiri wajen kawo cigaba a siyasar jam’iyyu ne, inda aka nuna irin muhimmancin
tsare ƙuri’u wanda yakan daƙile yiwuwar maguɗi. Idan talakawa suka tsare ƙuri’unsu
suka tsaya tsayin daka ba tare da tsoro ba, to sun daƙile ƙofar yi masu maguɗi na
kai tsaye. Idan sun tsaren to a nan akan yi amfanin da sa hannun jami’an tsaro ko
‘yan banga. Su jami’an tsaro su yi amfani da ƙarfin ikonsu, su watsa jama’a, su
kuma ‘yan banga aikinsu shi ne kawo tashin hankali, ‘yan jam’iyyarsu su aikata abin
da suke so.
Marubuta sun riƙa nuna
yadda akan riƙa yin kira ga jama’a don su fito su tabbatar da cewa ba a sauya masu
abin da suka zaɓa ba ta hanyar kare ƙuri’unsu har dai a kai ga sanar da wanda ya
yi nasara. Dubi wannan misali:
“Ranar zaɓe haka gwamnati
ta yi facaka da kudi, amma a banza, al’umma ni kawai suke zaɓa a kyauta. Bayan an
kammala zaɓe suka kasa, suka tsare, har sai da aka bayyana ni a matsayin wanda ya
yi nasara. Gari ya cika da murna, kusan kwana aka yi ana kaɗe-kaɗe da guje-guje
a ababen hawa domin farin ciki,”
(Aminiya-Trust, 2020: 120).
A nan an nuna hoton irin abin da ya faru ne bayan
faɗuwar jam’iyya mai mulki ta PDP a shekarar 2015, inda babbar jam’iyyar hamayya
ta APC ta wancan lokaci ta yi nasarar lashe kaso mafi tsoka na kujerun da aka tsaya
takara. A cikin misalin an nuna cewa al’umma sun tsaya sun sanya ido bayan an kammala
zaɓe, sun tsare ƙuri’unsu har aka kai ga bayyana sakamako, inda al’umma suka ɓarke
da murna don an bayyana wanda suka zaɓa a matsayin wanda ya yi nasara. Abin da aka
saba na kashe kuɗi da masu mulki suke yi ya zama a banza, jama’a suka zaɓi wanda
bai kashe ko kwabonsa ba.
A wani misalin kuma an nuna cewa, a wasu lokuta ko da mutanen
sun kasa sun tsare akan yi amfani da ƙarfi domin ƙwace mulkin, inda akan yi amfani
da jami’an tsaro kamar dai yadda misalin da yake biye ya nuna:
“Take matasan suka yi
dafifi a a ƙofar ofishin hukumar zaɓen suka fara zanga-zangar nuna rashin amincewa
da sakamakon. Har suka fara ɗauki-ba-daɗi da jami’an tsaro. Babu shakka, sun fito
ƙwansu da kwar ƙwarƙwatansu, sun dangwala wa zaɓinsu (Alhaji Abubakar Mai-Allah)
sun kasa, sun tsare, sun raka , sun jira. Amma kash An juya sakamakon!”
(Aminiya-Trust, 2020: 109).
A nan an nuna irin jajircewar da matasa ne suka yi wajen tabbatar
da ɗan takararsu ya kai ga nasara, wajen amfani da hanyar a-kasa-a-tsare suka fito
suka zaɓi ɗan takarar da suke muraɗi, kuma sun tsare ƙuri’unsu, sun raka, sun jira,
amma duk da haka an yi amfani da ƙarfin mulki an juya sakamako.
Abu mafi muhimmanci a nan shi ne, a fahimci cewa, a-kasa-a-tsare
ya ginu a cikin tarihin siyasar jam’iyyu, domin hanyar gwagwarmaya ce a siyasance
wadda aka yi aiki da ita a cikin siyasar Arewaci nijeriya, kuma ta yi aiki, domin
ta wannan hanyar an kafa tarihin da ba a taɓa samun irinsa ba a tarihin siyasar
jam’iyyu a Nijeriya, inda jam’iyyar hamayya ta yi nasarar kayar da jam’iyya mai
mulki da taimakon wannan tsari na a-kasa-tsare.
Waɗannan batutuwa da aka kawo a wannnan ɓangare batutuwa ne da
‘yan siyasa suke gwagwarmaya a siyasance ta hanyar amafani da su domin samar da
cigaba ga al’umma.
5.3 Abubuwan Da Suke Kawo
Cikas Ga Samun Cigaba
A wannan ɓangaren an kawo bayanai kan abubuwan da suka riƙa zama
tarnaƙi ne ga samun ci gaba a siyasance a cikin tarihin siyasar jam’iyyu, inda aka
kawo bayanansu ta hanyar danganta su da tarihin ginuwar siyasa a Arewacin Nijeriya.
An yi ƙoƙarin kawo misalai daga abin da aka samu cikin rubutattun ayyukan zube na
Hausa wanda shi ne ya ba da haske wajen fahimtar yadda siyasar jam’iyya ta ginu
a Arewacin Nijeriya. Abubuwan da wannan ɓangare ya tattauna a kai sun shafi abubuwa
waɗanda ‘yan siyasa ba su faye fitowa su alaƙanta kansu da su ba, sai dai an ɗauka
cewa abubuwa ne da suke da alaƙa ta ƙut-da-ƙut da siyasar jam’iyya, kuma ana alaƙanta
kowane ɗan siyasa da su. Haka kuma an yarda cewa su ne suke haifar da koma baya
ga cigaban siyasa da al’umma da ma ƙasa baki ɗaya. Irin waɗannan abubuwa sun haɗa
da:
5.3.1 Alƙawarin Ƙarya
Tarihi ya nuna cewa, tun a jamhuriya ta ɗaya an samu irin wannan
misali da ya shafi alƙawarin ƙarya, wanda ya fito a cikin jaridar Sodangi, inda aka zargi wasu jam’iyyun siyasa
da yin alƙawarin da wasu suke ganin ba abu ne mai yiwuwa ba. Dubi wannan misalin:
“ ko kadan ba daidai ba
ne kamar yadda wasu jam’iyyar siyasar ƙasar nan ke faɗi ga talakawan ƙauyukan cikin
ƙasar nan suna yi wa jama’a alƙawura waɗanda ko a mafarki mai hankali bai kamata
ya faɗa ba wannan shi ne gaya wa jama’a cewa in an ci zaɓe an kafa gwamnati za su
hana biyan haraji saboda haka nake jan hankalin dukkan ‘yan siyasa su riƙa kamanta
gaskiya ga abubuwan za su gaya wa jama’a ”
(Muhammed, 1960).
A nan ana nuna cewa, wasu ‘yan siyasa suna shiga ƙauyuka suna
yin alƙawarin ƙarya ga mutane cewa idan suka ci zaɓe za a daina biyan haraji, wanda
ake a ganin wannan ba abu ne da hankali zai ɗauka ba. Ana ganin ya kamata idan ‘yan
jam’iyya za su yi wa talakawa alƙawari to su riƙa yi masu alƙawarin abin da suka
san mai yiwuwa ne. Idan aka dubi wannan batu da kyau za a ga cewa, an samu ‘yan
siyasa da wannan ɗabi’a ta alƙawarin da su kansu ‘yan siyasar suke ganin cewa ba
zai tabbata. Ke nan, tun a jamhuriya ta farko an samu batun alƙawarin ƙarya daga
‘yan siyasa a cikin rubutaccen zube na wancan lokacin.
A jamhuriya ta biyu an samu inda Malam Aminu Kano a cikin jawabinsa
kan batun albashin malaman makaranta, yake nuna cewa, ba za su yi alƙawarin ƙarya
a kan wannan ba, kamar yadda ya ce:
“Mu PRP ba za mu yi alƙawarin
ƙara wa malamai albashi ba, saboda maganar albashi da muke niyyar yi shi ne a ƙirƙirar
da waɗansu alawus-alawus ga malamai saboda ƙara ƙarfin gwiwa a harkar ba za mu yi
alƙawarin lu’ulu’u da silba don mu jawo hankalin jama’a ba, daga baya mu kasa cika
alƙawari, muna yin alƙawarin abin da za mu iya ne.”
(Jega da wasu, 2002: 23).
A nan Malamin ya nuna cewa, jam’iyyarsu ba za ta ɗauki alƙawarin
da ba za ta iya cikawa ba, shi ya sa ma ba za su yi wa malamai alƙawarin ƙarin albashi
ba, maimakon haka za su samar masu da alawus-alawus maimakon alƙawarin da zai zama
na ƙarya ne kawai don ba za a cika ba.
Har ila yau a jamhuriya ta biyun ‘yan hamayya sun ci gaba da
kokawa kan irin yadda jam’iyya mai mulki ta riƙa yi wa al’umma alƙawura na ƙarya,
wanda aka nuna cewa ya samo asali tun daga farkon siyasar jam’iyyu kamar misalin
da aka kawo a ƙasa daga cikin littafin Tura
Ta Kai Bango ya ambata. Dubi abin da marubucin ya ce:
“ in ka duba tarihin waɗannan
mutane, za ka ga cewa, su ne suka fara yin mulki a ƙasar nan bayan tashin ‘yan mulkin
mallaka. A wannan lokaci alƙawura guda nawa ne suka cika wa jama’a? Ai kana da wayo
lokacin ”
(Katsina, 1983: 13).
Idan aka dubi wannan misalin da yake sama, marubucin ya juya
ne ya waiwayi tarihi inda ya nuna cewa, bayan Turawa sun bar ƙasar nan mulkin siyasa
ne aka ci gaba da tafiyar da ƙasar a ƙarƙashinsa, kuma ‘yan siyasa sun ɗauki alƙawura
da dama waɗanda ba a cika su ba. Wannan misalin ma ya nuna cewa da yawa cikin alƙawuran
da ‘yan siyasa kan ɗauka ba su faye cika su ba.
A wani wurin daban, marubucin ya sake bayyana yadda ‘yan siyasa
sukan yi alƙawari ba tare da la’akari da cewa akwai ranar ƙin dillanci ba, alal
misali:
“ babu irin alƙawarin da ba a yi musu ba na cewa
in an kafa gwamnati za a buɗe musu taskar kuɗi. Za a ba su kati, ganin shugaban
ƙasa ba sai an yi masu iso ba, amma ga shi ko ‘yan majalisa ma sun fi ƙarfin su
tsaya su gaisa da su ”
(Katsina, 1983: 73).
A wannan misalin za a fahimci cewa, lokacin yaƙin neman zaɓe
an yi wa jama’a alƙawarin cewa za a mori arziƙin ƙasa tare da su, kuma za a buɗe
taskokin ƙasa inda za su riƙa amfana daga ciki. Bugu da ƙari, duk lokacin da suka
ga damar ganin shugaban ƙasa za su iya ganinsa ba tare da shamaki ba, amma bayan
an ci zaɓe sai ya kasance hakan bai samu ba. Ko da ‘yan majalisa ma da suka fi kusa
da jama’a sun fi ƙarfin su tsaya a gaisa, duk kuwa da cewa sun ɗauki alƙawari ba
za su guji al’umma ba. Da yawa cikin ‘yan siyasa sun san cewa ba za su iya cika
alƙawuran da suka ɗauka ba, kuma da gangan ma suke ɗaukarsu don kawai su samu burinsu
na ɗarewa kan mulki ya tabbata. Da zaran sun cika wannan burin shi ke nan, su watsar
da alƙawuran sai kuma sun dawo sake neman wani wa’adin mulkin.
Irin waɗannan alƙawuran ƙarya sun bi tsawon tarihi, inda suka
gangaro har zuwa jamhuriya ta huɗu. Wani sauyi da aka samu wajen ɗaukar irin waɗannan
alƙawura na ƙarya shi ne, a wannan zamani ‘yan siyasa da kansu suke tambayar al’umma
abubuwan da suke buƙata don a samar masu. Bayan sun faɗi abin da suke buƙata ɗan
takara ya sa a rubuta, kamar dai da gaske aiwatarwa za a yi, amma da zarar sun yi
kai ga madafun iko shi ke nan sai su watsar da alƙawarin. A cikin littafin Dambarwar siyasa, an nuna ɗan takarar shugabancin
ƙaramar hukuma ya riƙa ɗaukar alƙawura masu nauyin da ya san ba zai iya sauke su
ba. Dubi abin da ya ce:
“Duk inda muka je idan
suka faɗi matsalarsu sai na sa an rubuta, tare da ɗaukar masu alƙawarin magance
masu ita. Alƙawuran da na ɗauka ko gwamna ne ya ɗauka bai isa ya cika musu ba, ballantana
ciyaman.”
(Aminiya-Trust, 2020: 119).
Wannan misalin shi ne misalin ‘yan siyasa musamman a wannan jamhuriyar
da muke ciki, domin kuwa sukan riƙa ɗaukar alƙawuran da suka wuce matakin da suke
nema kamar yadda wannan ɗan takarar ya bayyana cewa alƙawuran da ya riƙa ɗauka ana
rubutawa ko gwamna ne ba zai iya cika su ba.
A wannan jamhuriyar da ake ciki an yi alƙawura da dama waɗanda
an gaza cika su, kusan ma za a iya cewa sun zama tarihi. Alal misali, jaridar Leadershhip Hausa ta kawo wani sharhi wanda
wani mai suna Malam Nuruddeen Dauda ya yi kan batun fara yaƙin neman zaɓe na shekarar
2023, a ciki an nuna cewa, ‘yan siyasa suna yawaita yin alƙawura na ƙarya waɗanda
har zuwa ƙarshen wa’adin mulkinsu ba su iya cika su. Hakan ba ya hana su sake yin
irin waɗannan alƙawuran idan aka buga kugen siyasa. Dubi abin da aka samu daga jaridar:
“A nawa binciken, dukkan
yaƙin neman zaɓenmu tun daga 2014 har zuwa yau, a kowane mataki ana gudanar da shi
ne a bisa alƙawarin ƙarya, ɓatanci da kuma tashin hankali maimakon magance matsaloli.”
(Shuaibu, 2022).
Kamar yadda wannan mai sharhin ya nuna, dukkan yaƙin neman zaɓen
da aka yi tun daga shekarar 2014 zuwa shekarar 2022 duk an yi su bisa alƙawuran
ƙarya ne. Dukkan matakan tun daga matakin mazaɓa da ƙaramar hukuma da majalisun
jihohi da na tarayya da gwamna da shugaban ƙasa, duk bisa wannan tsari na alƙawarin
ƙarya suke. Idan aka duba za a ga cewa kusan duk abubuwan da ake yin alƙawari lokacin
yaƙin neman zaɓe ba a cika su har zuwa ƙarshen wa’adin mulkin. An sake samu wani
misalin mai kama da wannan a cikin jaridar Aminiya,
inda aka nuna cewa gwamnatin da take kai a daidai wannan lokacin wato ta Shugaba
Muhammadu Buhari ta yi alƙawura da dama waɗanda ba ta cika su ba har zuwa shekarar
2022. Ga misalin:
Ita wannan gwamnatin ta
yi alƙawarin za ta yi abubuwa da yawa amma ba mu ga ta yi ba. Muna jira Allah ya
sa.
(Shuaibu, 2022).
A nan an nuna cewa, gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Shugaba
Muhammadu ta yi alƙawura da dama lokacin da take neman goyon bayan al’umma lokacin
yaƙin neman zaɓe, amma har zuwa lokacin da aka buga wannan labarin ba ta cika su
ba, duk da cewa saura shekara guda wa’adinta ya ƙare.
A wani ƙarin misalin da yake nuna yadda ‘yan siyasa sukan riƙa
ɗaukar alƙawarin ƙarya, an nuna yadda ake bayyana yadda ‘yan siyasa kan nuna tausayi
da ƙaunar talakawa, har su yi masu alƙawarin samar masu da jin daɗin rayuwa ta hanyar
sama masu abubuwan more rayuwa, amma da sun ci zaɓe shi ke nan sun manta. Dubi yadda
aka kawo a cikin littafin Dambarwar Siyasa
kamar haka:
“Ummi bara za ta ɗara
baɗi daɗi ko yanzu, ki bar ganin sabon fatinki su ne masu son talakawa, da sun kai
gaci, za su manta duk wani alƙawari da kike tunanin za ku sauke ”
(Aminiya-Trust,
2020: 72).
Ummi ‘yar siyasa ce da
ta sauya sheƙa zuwa sabuwar jam’iyyar da aka kira da ta talakawa. Duk da haka sai
ake nuna mata cewa su fa ‘yan siyasa duk yadda suka kai ga ɗaukar alƙawura kafin
su samu damar ɗarewa madafun iko ne. Da zarar buƙatarsu ta biya, sukan manta da
duk wani alƙawari da suka yi.
Batutuwa na alƙawarin
ƙarya a siyasar jam’iyyu sun ci gaba da bayyana a cikin rubutaccen zube ta ko ina
domin ya zama tamkar wani abu mai muhimmanci ga ‘yan siyasa wanda sukan yaudari
talaka da shi domin kai wa ga kujerar shugabanci. A cikin littafin Mizani, an samu irin wannan misali na alƙawarin
ƙarya, inda aka nuna cewa, ‘yan siyasa sukan yi wa jama’arsu alƙawura da dama, amma
da zaran sun hau kujerar mulkin sai su manta da su. Ga misali:
“A
lokacin da ya tabbatar haƙonsa ya cimma ruwa, na fara mafarkin dangwalar romon damkwaraɗiyya
sai ya watsar da mu da buƙatunmu, ya wofantar da alƙawarirrikan da ya ɗauka na sauke
nauyin al’umma da alƙawarta mana lasar zuma farar saƙa.”
(Mustapha da wasu, 2023: 9).
A wannan misalin da yake sama, marubucin yana bayyana irin yadda
‘yan siyasa sukan yi alƙawura ne ga jama’a ta hanyar nuna masu cewa in har zaɓe
su za su sha romon dimokuraɗiyya. A cikin misalin, marubucin ya nuna matashi ne
da ya yi wa ɗan siyasa hidima domin alƙawarin da aka masa na cewa za a tafi da shi
idan an samu nasara. Daga ƙarshe bayan an yi nasara sai aka watsar da duk wata buƙatarsu
ta hanyar yin watsi da alƙawuran da aka yi masu. ‘Yan siyasa ba su ɗauki alƙawari
a bakin komai ba, domin kaso mafi tsoka na alƙawuran da suke yi ba su cika su.
Irin wannan halin na manta alƙawari ko gaza cika shi ko ma watsi
da shi, abu ne wanda an ga ɓurɓushinsa tun a farkon siyasar jam’iyyu kamar yadda
aka bayar da misali a baya, kuma wannan yana da daga cikin abubuwan da suke kawo
tarnaƙi ga samun cigaban ƙasa da kuma al’umma. Duk wanda aka yi wa alƙawari ba a
cika masa ba yakan karaya da al’amarin wanda ya yi masa alƙawarin, ta yadda ba zai
sake aminta da shi har ya fito ya zaɓe shi da burin samun sauyi ba. Da dama cikin
‘yan siyasa sun riga sun yi wa siyasar mummunar tabo, har an ɗauka ma cewa ‘yan
siyasa ba su da alƙawari.
5.3.2 Maguɗin Zaɓe
Maguɗin zaɓe yana nufin
yin amfani da duk wata hanya domin yin ha’inci yayin jefa ƙuri’a, ko bayan an kammala,
ta hanyar ƙara wa wata jam’iyya yawan ƙuri’a ko lalata ƙuri’unta domin tauye wanda
ya yi nasara da kuma tabbatar da wanda bai samu nasara ba.
Maguɗin zaɓe yana cikin abubuwan da suke haifar da tarnaƙi wajen
samun cigaban ƙasa, kasancewar akan yi amfani da haramtattun hanyoyi domin daƙile
nasarar wanda al’umma suke so, ko kuma wanda ya fi cancanta. Maguɗin zaɓe abu ne
wanda ya daɗe ana yin sa a cikin tarihin siyasar jam’iyyu, duk da cewa akwai hanyoyi
daban-daban da ake bi wajen yin maguɗin. Wannan ya danganta da irin yanayi da salon
zaɓen da za a gudanar, shi zai ba da damar sanin ko ta wace hanya ce za a bi a yi
maguɗi. Alal misali, akan yi zaɓe ta hanyar tsayuwa jere bisa layi, inda akan yi
layi daidai da adadin ‘yan takara ko jam’iyya, sai a ƙidaya masu zaɓen. Wanda mutane
suka fi yawa a layinsa shi ne zai fi samun yawan ƙuri’u. Wani salon kuma shi ne,
akan fitar da akwati da za a jefa wa ƙuria da alamar jam’iyya a jikinsa.
Adadin jam’iyyun da suka shiga zaɓen shi ne adadin akwatin da
za a kawo, kowanne da alamar jam’iyyarsa a jiki. Masu jefa ƙuri’a kuma idan sun
zo sai mutum ya duba alamar jam’iyyar da yake goyon baya ya jefa tasa ƙuri’ar a
cikinsa. Haka kuma akan yi amfani da takardun jefa ƙuri’a wanda suke ɗauke da sunan
jam’iyya da alamarta da kuma matakin da za a jefa wa ƙuri’ar, wato ko dai ya kasance
na shugaban ƙasa ko gwamna ko kuma na ‘yan majalisu ko shugabannin ƙananan hukumomi
kamar dai yadda tsarin yake a jamhuriya ta huɗu.
Ta la’akari da kowane salo na zaɓe ne akan yi amfani da hanyar
da akan yi maguɗin da ita. Daga cikin hanyoyin da ake amfani da su wajen gudanar
da maguɗin zaɓe akwai cushen ƙuri’u.
A ciki tarihin siyasar jam’iyyu an samu inda aka yi amfani da
wannan hanya ta cushen takardun ƙuri’a domin yin mguɗin zaɓe. Takardun ƙuri’u suna
daga cikin kayan aikin zaɓe waɗanda akan raba, kuma da su ne ake jefa ƙuri’a. Su
ma irin waɗannan takardu akan samar da na bogi wanda akan tanada tun kafin ranar
zaɓe, wanda za a dangwale wa jam’iyyar da ake so ta yi nasara. Bayan an dangwala
wa jam’iyyar sai a yi amfani da ƙuri’un ta hanyar dabara a kai su rumfar zaɓe tare
da zuba su cikin akwatin ɗan takarar da ake so ya samu rinjaye. Irin wannan ya fito
a cikin littafin Siyasa Waina Ce kamar
haka:
Idan kuka isaTele, kada
ku tsaya sai kun kai Tsamiya. Da kun kai Tsamiya, ku ɗau ƙunshi guda daga cikin
jakar ku zurara katunan ƙuri’u da ke ciki a akwatin YKK na ɗakin zaɓe da ke can
bayan gari. In kuka gama wannan, sai ku juyo ku zuba ƙunshin guda a akwatin YKK
da ke ƙofar gidan Sakatarenmu na can Tele. Ɗayan da ya rage ku zuba a akwatin zaɓen
YKK na ɗan ƙauyen nan Shayi da ke kan hanya. Daga nan sai ku dawo abinku.
(Zukogi, 1994: 23).
Wannan misalin da yake sama ya nuna yadda akan yi amfanin da
ƙuri’un bogi ta hanyar yin cushe a cikin akwatin zaɓe domin yin maguɗin zaɓe. A
nan an nuna magoya bayan jam’iyyar YKK ne, wato Bogi da Nako waɗanda aka ba su aikin
kai ƙuri’un bogi domin yin maguɗi da su bayan an haɗa baki da ma’aikatan zaɓe na
rumfunan. An shirya amfani da waɗannan rumfunan ne domin aiwatar da maguɗi kasancewar
ba ko’ina ne ake iya shirya irin wannan maguɗin, kuma ya yiwu ba. Yawanci akan duba
inda aka san magoya bayan jam’iyyar da za ta yi maguɗin ba su da rinjaye, sai a
haɗa baki da ma’aikatan zaɓen domin aiwartarwa ba tare da masu zaɓen sun ankara
ba.
Wata hanyar kuma da ake amfani da ita wajen yin maguɗin zaɓe
ita ce amfani da ‘yan bangar siyasa. Irin wannan salon maguɗin ya fito a cikin littafin
Siyasarmu a Yau, sai dai a ciki marubucin
bai kawo batun amfani da hikima da dabara wajen yin cushen ƙuri’un ba, maimakon
haka sai ya nuna cewa an yi amfani da ‘yan banga ne ta hanyar nuna ƙarfin makami.
Dubi abin da marubucin ya ce:
Kowace mota ƙirar Jif
ce, akwai kayan aiki a ciki, tare da akwatunan zaɓe da takardun zaɓen a ciki. Idan
kun tuna jiya, kun yini kuna cike takardun zaɓe da sunan bogi, amfanin da za ku
yi da shi ne, gobe idan kowane ya je gun da na ba shi ya kula da ɓangarensa, kuma
akwai wayar sadarwa wanda za mu dinga musayar bayanai da ku. Idan kun tabbatar da
cewa zaɓe yana tafiya daidai watau jam’iyyata tana kan gabato shi ke nan, amma idan
kun ga cewa jam’iyyar hamayya ce a kan gaba to ku tashin hankalin jama’a da harbe-harbe.
Idan jama’a sun tarwatse to sai ku yi ƙoƙarin ɗauke akwatunan zaɓen ku zuba tawa
(Kabara, 2005: 33).
Salon maguɗin da aka nuna a wannan misalin da yake sama ya bambanta
da wanda ya gabace shi. A wannan an nuna cewa ɗan takarar shugaban ƙasar Gashi,
Alhaji Naso shi ne ya tara ‘yan bangarsa yake nuna masu hanyar da suka shirya yin
maguɗin zaɓe matuƙar aka lura ba jam’iyyarsu ce za ta yi nasara ba. An nuna sun
tanadi motocin da za su yin amfani da su, waɗanda suke ɗauke da kayan zaɓe da suka
ƙunshi akwatunan zaɓe da katunan ƙuri’u waɗanda za su yi amfani da su a duk inda
suka lura cewa jam’iyyarsu ba za ta yi nasara ba. Haka kuma, ɗan takarar ya ba su
makamai da za su yi amfani da su wajen tarwatsa masu zaɓe bayan sun lura cewa ba
su suke da rinjaye a rumfar ba. Bayan sun kora jama’a sai su sauya akwatunan zaɓen
da nasu. Wannan wata hanyar maguɗi ce da aka riƙa amfani da ita a cikin tarihin
ginuwar siyasar Arewacin Nijeriya. An riƙa amfani da ‘yan banga wajen aiwatar da
irin wannan salon maguɗin zaɓen, inda sukan tayar da hankali a duk rumfar da suka
lura ba su ne suke da rinjaye ba. A wasu lokuta ma ba wani akwatin zaɓen sukan zo
da shi ba, amma tun da sun lura ba za su yi nasara a wannan rumfar zaɓen ba, sai
su tayar da yamutsi ta yadda za a fasa akwatin, a lalata ƙuri’un kowa ya rasa.
Haka kuma akan yi maguɗin zaɓe ta hanyar yin amfani da kayayyakin
zaɓe na bogi. Idan aka yi nufin yin maguɗin zaɓe, tun kafin lokacin zaɓen ya zo
akan tanadi wasu abubuwa daga cikin kayan aikin zaɓe wanda akan yi amfani da su
wajen gudanar da maguɗin. Irin waɗannan kayayyakin hukumar zaɓe ne kaɗai take da
alhakin samar da su domin gudanar da zaɓe. ‘Yan siyasa sukan tanadi irin waɗannan
kayayyakin domin su yi amfani da su hankali kwance. Sukan shirya tare da aiwatar
da maguɗin ne idan suka lura sakamakon da jama’a za su samar ba zai masu daɗi ba.
Dubi wannan misalin:
Da farko dai mun bi hanyar
da za mu bi mun samo samfurin akwatin zaɓe, kuma a yanzu haka a cikin sutona na
gidan gonata mun tara namu akwatin irin na hukumar zaɓe, waɗanda sai ranar zaɓe
za mu baza su lungu da saƙo na ƙasar nan.
(Surajo, 2006: 109).
A nan Shugaban jam’iyyar JHC ne yake bayanin irin shirin maguɗi
da suka yi. Ya nuna cewa, sun bi duk hanyar da za su bi sun samu nau’in akwatin
da za a yi amfani da shi a zaɓen, suka kuma tanade su. Ya nuna cewa sun tanadi irin
akwatunan da hukumar zaɓe za ta yi amfani da su, an ɓoye su, sai ranar zaɓe za su
raba akwatunan a ko ina cikin ƙasar. Irin wannan tanadin kayan zaɓe na bogi hanya
ce ta maguɗin zaɓe. Da kayan ne akan yi amfani domin yin maguɗi, maimakon amfani
da wanda hukumar zaɓe za ta raba ranar zaɓe. Irin waɗannan akwatunan zaɓen ba a
kai su filin zaɓe, maimakon haka akan samu wani wuri ne a ɓoye su, inda za a cika
su da ƙuri’un da aka dangwala wa jam’iyyar da ake so ta yi rinjaye. Da zarar an
kammala zaɓe za a tafi da akwatin zaɓe, sai a san hanyar da za a bi a musanya akwatin
da al’umma suka kaɗa ƙuri’unsu a ciki da wannan akwatin da aka dangwale ƙuri’un
maguɗin a cikinsu. Akan musanya idan aka samu ƙarancin masu sanya ido daga jam’iyyar
hamayya ko kuma a yi amfani da jami’an tsaro ko ‘yan banga wajen tayar da yamutsi
wanda hakan zai ba da damar a sauya akwatin zaɓen da na bogi.
Wata hanyar maguɗin da ta shahara a cikin tarihin maguɗin zaɓe
ita ce satar akwatin zaɓe. Akwatin zaɓe shi ne mazubin ƙuri’u da ake amfani da shi
domin jefa dukkan wata ƙuri’a da aka zaɓa. A cikin wannan akwatin akan sanya ƙuri’ar
da kowane ɗan takara ya samu, wanda kuma su ne za a ƙirga domin a iya gane wanda
ya yi nasara da wanda bai yi nasara ba a zaɓen. Akan yi amfani da wannan akwatin
wajen gudanar da maguɗi ta hanyar sace shi daga rumfar zaɓe ko kuma ma kafin a kai
fa kawo shi rumfar zaɓen. Akan yi haka ne domin a raunana ƙuri’un abokan hamayya.
Irin wannan batun ya fito a cikin jaridar Aminiya
kamar haka:
Haka kuma su ke shirya
mutane su sace akwatunan zaɓe, su yi dangwalen ƙarya, kamar kuma yadda suke buga
takardun zaɓe na bogi.
(Baba-Aminu da wasu, 2014).
A cikin wannan misalin an bayyana hanyar maguɗin zaɓe wadda akan
shirya wasu mutane da sukan je su sace akwatunan zaɓe. Da dama idan aka sace akwatin
akan yi amfani da shi ne a yi zuba ƙuri’un wanda aka ga dama ko kuma a lalata ƙuri’un
wanda ba a so ya kai ga nasara maimakon a bari a yi zaɓen don fitar da wanda ya
yi nasarar na gaskiya. Akan yi amfani da takardun zaɓe na jabu waɗanda aka buga
domin aiwatar da irin wannan maguɗin.
Idan aka yi duba cikin tarihi za a fahimci cewa, maguɗin zaɓe
ba ya yiwuwa in ba tare da haɗin bakin masu ruwa da tsaki a harkar zaɓen ba. Ko
dai ya kasance ma’aikatan gwamnati da suke aiki a ƙarƙashinta waɗanda akan tura
a matsayin jami’an zaɓe, ko kuma a ɗora masu wani aiki da ya shafi aikin zaɓen.
Ko waɗanda suke aiki da hukumar da take shiryawa tare da aiwatar da zaɓen, ko kuma
ma’aikatan tsaro da aka ɗora alhakin sanya ido da kula da rayukan al’umma a lokacin
zaɓe da ma bayan zaɓe. Da dama idan aka rasa haɗin kan waɗannan kason na al’umma
to maguɗin zaɓe zai samu cikas.
A cikin tsare-tsaren zaɓe an riƙa amfani da ma’aikatan gwamnati
tun daga jamhuriya ta farko domin aiwatar da maguɗin zaɓe. An samu hujjojin da suka
fito da waɗannan batutuwa a cikin rubutattun ayyukan adabin Hausa. Alal misali,a
cikin jaridar Daily Comet an samu wani
bayani a kan abin da ya shafi yunƙurin maguɗi a zaɓen ‘yan majalisar wakilai da
aka gudanar a shekarar 1961. Ga bayanin kamar haka:
Ranar Juma’a da ta wuce
majalisar Jihar Arewa ta zartar da cewa a zabe mai zuwa na majalisar wakilai, Hakimai
ne za su nada wakilan akwatunan zabe har da na abokan hamayya, mai makon shi mai
shiga zaben ya bada wakilinsa, amintaccensa. Kuma gwamnati ta ƙara da cewa wai Hakimai
su ne za a bai wa ikon takardun kuri’a Wannan ya tabbatar mana cewa gwamnatin NPC
ta tsorata da ‘yan hamayya, don haka ta shirya yadda ta ga yafi yi mata daidai in
an duba siyasar kasannan za a ga Hakimai ne suke shiga zabe da sunan NPC ashe kuwa
hauka ne a ce za a baiwa abokin gaba kayan fada. Kuma zai zama abin dariya idan
aka ce abokin gabarka shi ne wakilin ka, wajen duba akwatunan zabe.
(“Hakimai Ne Za Su Nada”,
1961).
Idan aka yi la’akari da wannan bayanin, za a fahimci cewa ba
hakimai dama cikin gudanar da ayyukan zaɓe wata dama ce da za su tafka maguɗi cikin
zaɓen da za a gudanar. Hakimai da sarakuna a wancan lokaci a ƙarƙashin gwamnati
suke, wadda jam’iyyar NPC ta kafa.
Ayyana hakimai a matsayin waɗanda za su naɗa wakilan akwatunan
zaɓe na duk jam’iyyun siyasa na wancan lokacin (1961), ya tabbatar da cewa, ana
samun sa hannun jami’an gwamnati a cikin maguɗin zaɓe. Ba yadda za a yi wani cikin
hakiman ya yarda a faɗi akwatinsa domin ya san bakin rawaninsa ke nan. Don haka
ko ta halin ƙaƙa sai ya tabbatar jam’iyyar gwamnati ta yi nasara a mazaɓarsa, domin
ya tsira da rawaninsa.
A cikin misalin da yake sama idan aka lura za a ga cewa, ‘yan
hamayya sun riga sun nuna cewa idan har ya kasance hakiman ne za a danƙa wa kula
da al’amuran zaɓen to sun tabbatar jam’iyya mai mulki ta ƙulla wani abu na rashin
gaskiya ne. Don haka take neman hanyar da za ta shirya abin da zai yi mata daɗi
kawai. Bai wa hakiman kula da al’umaran zaɓen tamkar bai wa abokin gaba ne kayan
faɗa. A cikin misalin an nuna cewa, zai iya zama abin dariya a ce abokin hamayya
kuma shi ne wakilin da za a sanya ya tsaya a madadin abokin hamayyarsa, wanda kuma
ake sa rai shi ne zai tabbatar da an yi wa wannan abokin hamayyar tasa adalci a
akwatin zaɓe.
Idan aka dubi wannan batun da aka kawo za a gane cewa, maguɗin
zaɓe ne aka shirya domin a tabbatar jam’iyya mai mulki ta wancan lokacin wato NPC
ta samu rinjaye a zaɓen ‘yan majalisar, domin in ba maguɗi ba ne, ya kamata a bai
wa kowane ɓangare damar kawo wanda zai sanya ido a kan akwatinsa domin kada a samu
matsala. Maimakon haka sai aka sanya waɗanda da su za a shirya yadda za a kayar
da jam’iyyar hamayya.
Dangane da wannan batu da aka kawo misali da shi a sama, jaridar
Daily Comet ta yi kira ga ‘yan hamayya
na jam’iyyun NEPU da Action Group da NCNC, a kan su fito su mayar da martani ta
hanyar nuna rashin jin daɗinsu a kan yunƙurin da gwamnati ta yi, wanda a ganin jaridar
wannan tsarin da gangan aka kitsa shi domin tafka maguɗin zaɓe. Dubi abin da jaridar
ta ce:
Ya zama wajibi ‘yan hamayya
musamman na NEPU, NCNC da Action Group su san sabuwar dabara. Mu baza muce ga yadda
zasu yi ba, hausawa suna cewa mai kai shi yasan makafar zanko. Amma kuma tilas ne
wannan jarida ta la’anci kuma ta tsine dukan mutanen da suke nufin zaluntar na bayansu
ko da wane irin zalunci ne. Lalle ne Talakawa da jam’iyoyin siyasa su gane wannan
kullin da ake yi masu na nufin a zambace su.
(“Hakimai Ne Za Su Nada”,
1961).
Jaridar ta bayyana cewa, wannan tsari da jam’iyya mai mulki ta
fito da shi na miƙa ikon kula da akwatunan zaɓe da takardun jefa ƙuri’a a hannun
hakimai, dole jam’iyyun hamayya su tashi tsaye wajen ganin hakan bai tabbata ba.
Jaridar ta ce, an shirya bai wa hakiman kula da akwatunan zaɓen ne domin a zambaci
sauran jam’iyyu masu hamayya. Zamba a nan yana nufin maguɗin zaɓe ne aka shirya.
Duk da cewa jaridar ta yarda cewa gwamnati tana da ikon tsara abubuwanta yadda ta
so domin ta san abin da ya kamata ta yi, amma kuma ya kamata ta yi adalci.
Ta fuskar ma’aiakatan zaɓe kuwa sukan kasance
na wucin gadi waɗanda akan ɗauka domin aikin zaɓen wannan kakar zaɓen kaɗai. Akwai
kuma waɗanda suke ma’aikatan hukumar ne na dindindin, waɗanda suke aiki da hukumar
kodayaushe. Duk waɗannan nau’o’in ma’aikatan hukumar akan yi amfani da su domin
gudanar da maguɗin zaɓe. Hanyar da ake bi domin yin irin wannan maguɗin zaɓen ita
ce, ma’aikatan hukumar zaɓe sukan miƙa wuya bayan an saye su da kuɗi da wasu manyan
kyaututtuka da sauransu. Irin wannan misali ya bayyana a cikin littafin Da Bazarku inda aka nuna wasu manyan ‘yan
siyasa wato Sanata Bolton da Lauya Uba da kuma Cif Kolade suke tattauna hanyoyin
gudanar da maguɗin zaɓe cikin ruwan sanyi. Ga abin da suka ce:
sannan kuma bugu da ƙari tuni mun riga mun saye
wasu daga cikin manyan ma’aikatan hukumar zaɓe ta ƙasa, da kuɗi da kuma kyaututtuka
na gidaje tare da yi masu alƙawarin ɗasawa da su idan mun kama ragamar mulki Murɗiyar
zaɓe ba yau muka fara ba, don haka kuwa a yau ba za mu ji kunya ba.
(Surajo, 2006: 17).
A nan Sanata Bolton ne yake bayyana tsare-tsaren da suka riga
suka yi na aiwatar da maguɗin zaɓe. Sanata Bolton ƙwararre ne kan harkar zaɓe wanda
aka ɗauko hayarsa daga ƙasar Amurka, don ya tsara hanyoyin da za a shirya maguɗin
zaɓe. A cikin bayaninsa ya nuna cewa, daga cikin hanyoyin maguɗin zaɓe akwai saye
ma’aikatan hukumar zaɓe ta yadda za su ba da ƙofar da za a yi murɗiya ba tare da
an samu wata matsala ba. Akan ba su toshiyar baki na kuɗi da gidaje da wasu manyan
kyaututtuka har ma da alƙawarin gudanar da gwamnati tare da su. A ƙarshe ma har
wani iƙirari ya yi cewa ba su suka fara murɗiyar zaɓe ba wato an saba tun a baya
ana yi, don haka za su tabbatar shirin maguɗin da suka yi ya yi nasara.
A wani misalin dangane da yadda ma’aikatan zaɓe suke gudanar
da maguɗin zaɓe, a cikin littafin Dambarwar
Siyasa an nuna yadda wata budurwa mai suna Nabila ta naɗo wa ɗan takarar jam’iyyar
hamayya hujjar bai wa jami’an zaɓe cin hanci domin su murɗe zaɓensa, a bai wa wani
daban wanda ba shi ne ya yi nasara ba. Dubi wannan misalin:
A cikin wannan Memory
card ɗin akwai bidiyoyi da dama da suke nuna lokacin da ake ba jami’an zaɓe cin
hanci domin murɗe zaɓen yau.
(Aminiya-Trust, 2020: 109).
Nabila ‘yar Alhaji Maikwabo ce, wato ɗantakara a jam’iyyar RPC
mai mulki, sai dai ta kasance tana goyon bayan ɗan takaran jam’iyyar hamayya ta
NCC, wato Abubakar Mai-Allah wanda ya kasance malaminta na darasin ‘government’
lokacin tana sakandire. Wata rana, yayin da ake tsaka da shirya maƙarƙashiyar yadda
za a yi wa jam’iyyar NCC maguɗi ta yi amfani da kyamara ta yi rikodin bidiyo na
duk maƙarƙashiyar da aka shirya wa jam’iyyar hamayya. Daga cikin maƙarƙashiyar da
aka shirya har da bai wa jami’an zabe cin hanci domin a murɗe zaɓen. A cikin misalin
da yake sama an nuna cewa daga cikin hanyar maguɗin zaɓe akan yi amfani da jami’an
zaɓe domin a murɗe zaɓe, ta hanyar ba su cin hanci domin samun sakamako na ƙarya
ga wanda bai cancanta ba.
Aikin jami’an tsaro ne tabbatar da zaman lafiyar ƙasa ta hanyar
kula da tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma. Wannan ya sa a lokacin gudanar zaɓuɓɓuka
akan tura su domin su tabbatar al’amuran zaɓe sun tafi bisa tsarin doka. An bayyana
cewa an tafka maguɗin zaɓe mai yawa jamhuriya ta biyu, inda aka nuna cewa babu jam’iyyar
da ba ta yi amfani da wata hanyar maguɗi ba sai dai wadda ba ta samu dama ba[5]. A wannan kakar zaɓen
na jamhuriya ta biyu, sojoji ba su sanya hannu wajen tabbatar da doka da oda a wajen
gudanar da zaɓuɓɓukan ba, wanda hakan ya haifar da matsaloli da dama, kuma ‘yan
siyasa suka ci karensu babu babbaka. Waɗanda ma ba su tsoma hannu cikin maguɗin
zaɓe a zaɓen 1979 ba sun shiga a zango na biyu. Hakan ne ma ya haifar da juyin mulkin
da ya kawo ƙarshen wannan jamhuriyar.[6]
An riƙa samun zarge-zarge da suke nuna cewa jami’an
tsaro suna da hannu dumu-dumu a cikin ayyukan maguɗin zaɓe. Alal misali, a jamhuriya
ta huɗu an samu irin waɗannan ƙorafe-ƙorafen na cewa, jam’iyyar PDP tana yin amfani
da jami’an tsaro wajen tafka maguɗi a zaɓuɓɓuka. Dubi abin da jaridar Aminiya ta ruwaito:
Hukumar zaɓe ta zargi
hukumomin tsaro wato ‘yan sanda da jami’an fararen kaya na S.S.S da laifin taimakawa
game da maguɗin da aka tafka a zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisu da aka gudanar
ranar Asabar ɗin da ta gabata.
(Mijinyawa, 2007).
Hukumar zaɓe hukuma ce mai zaman kanta, wadda take da alhakin
shirya zaɓuɓɓuka a dukkan matakai. Ita ce take da alhakin tura ma’aikatanta kowane
lungu da saƙo domin gudanar da zaɓuɓɓukan da aka shirya. A wannan misalin da yake
sama an nuna cewa hukumar zaɓen ce ta zargi hukumomin tsaro na ‘yan sanda da na
S.S.S. da laifin taimakawa wajen aikata maguɗi a zaɓe na shekarar 2007 da aka gudanar.
Jami’an tsaro aikinsu shi ne tabbatar da doka da oda a ƙasa. Aikinsu ne su tabbatar
lokacin gudanar zaɓuɓɓuka an yi lafiya ba tare da samun rikici ko wasu abubuwan
da suka saɓa wa doka ba, amma hukumar ta yi zargin an haɗa kai da su an yi maguɗi
a zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisu da aka gudanar a wannan lokacin. Wannan zargin
da hukumar zaɓe ta yi ya ƙara tabbatar da samuwar maguɗin zaɓe a jamhuriya ta huɗu.
Wani misalin da yake nuna yadda maguɗin zaɓe ya ginu a cikin
tarihin siyasar Nijeriya shi ne, yadda aka riƙa kama shugabannin jam’iyyar hamayya
ana kullewa ta hanyar amfani da jami’an tsaro, a matsayin wata hanya ta gudanar
da maguɗin zaɓe, kuma ba a sakinsu sai bayan an kammala zaɓe. Dubi abin da jaridar
Aminiya ta ranar 26 ga Disamba 2014 ta
wallafa:
kuma muna sane da cewa babu abin da PDP ta iya
illa maguɗin zaɓe, ta tura ma’aikatan tsaro marasa gaskiya, waɗanda suke kama shugabannin
jam’iyyun hamayya suna kullewa, su sake su bayan an kammala zaɓe.
(Baba-Aminu da wasu, 2014).
A cikin misalin an nuna cewa ana amfani da jami’an tsaro wajen
kama ‘yan hamayya da kuma tsare su har bayan kammala zaɓe, wanda hakan zai ba da
damar gudanar da dukkan wani nau’in maguɗi tun da babu masu faɗa a ji ko kuma manyan
masu sanya ido na jam’iyyun hamayya. Irin waɗannan mutanen da jami’an tsaro sukan
kama, a tsare har sai bayan zaɓe a sako su, akan lura da irin rawar da za su taka
ne a cikin zaɓuɓɓukan, kasancewar su masu faɗa a ji a cikin jam’iyyar. Wani lokaci
kuma akan kama su ne domin sun san sirrin yadda ake yin maguɗin, don haka barin
su ba tare da an kama su an tsare ba zai iya kawo wa abokan hamayya tarnaƙi.
An ci gaba da samun waɗansu batutuwa da suka shafi maguɗin zaɓe
a cikin rubutaccen zube waɗanda suka tabbatar da ginuwar maguɗin
zaɓe a cikin tarihin siyasar jam’iyyu. Duk da ba su nuna hanyar da ake bi a yi maguɗi
da kuma masu yin maguɗin ba, amma dai samun wannan batun na maguɗi ya ba da haske
cewa maguɗin zaɓe abu ne da ya ginu kuma aka riƙa amfani da shi domin samun ɗarewa
bisa madafun iko.
Sau da dama jam’iyyar
da take bisa mulki yayin da za a gudanar da zaɓe takan faɗi cewa za ta tabbatar
an yi zaɓen gaskiya, kuma za su tabbatar duk wanda ya yi nasara an tabbatar masa
da nasararsa. Kamar yadda ya faru a jamhuriya ta huɗu a shekarar 2007. Dubi wannan
misalin da aka samu daga jaridar Aminiya:
“Shugaba Olusegun Obasanjo
ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa ba za ta yi maguɗin zaɓe ba ta hanyar nuna fifiko
ga jam’iyyarsu ta PDP babban zaɓen da yake ƙaratowa Ya ce, idan mutane suka yi maganar
maguɗi a yau, jam’iyyar PDP tana da jihohi 28, to a tunaninku yana yiwuwa mu rasa
waɗannan jihohin 28?”
(“Ba za mu yi maguɗi”, 2007)
Shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ne ya yi alƙawarin gudanar
da sahihin zaɓe wanda babu maguɗi a cikinsa. Ya nuna cewa ba za su fifita jam’iyyarsu
ta PDP da take mulki a kan sauran jam’iyyu ba a zaɓen da za a yi na shekarar 2007.
Duk da haka idan aka duba a cikin misalin da yake sama, ya nuna cewa jam’iyyar fa
tana da gwamnonin jihohi har 28, kuma ya nuna cewa babu yadda za a yi su faɗi zaɓe
a waɗannan jihohin da jam’iyyar PDP take mulki. Wannan kaɗai ya isa ya nuna cewa
akwai wata a ƙasa, wato akwai shirin maguɗi in ma sun ga alamun rashin nasara. Za
su yi amfani da ƙarfin mulki su tabbatar su samu rinjaye a jihohin.
Duk da wannan alƙawarin da Shugaban ƙasa Obasanjo ya yi na gudanar
da sahihin zaɓe ba tare da maguɗi ba, bayan kammala zaɓen sai aka samu ‘yan hamayya
sun koka dangane da yadda aka tafka maguɗi a zaɓuɓɓukan da aka gudanar. Dubi wannan
misalin da aka samu daga jaridar Aminiya
kamar haka:
“Tsohon shugaban ƙasa
Janar Yakubu Gowon ya bi sahun mutanen da suke sukar zaɓen da aka gudanar kwanan
nan, inda ya yi tir da zaɓen saboda a cewarsa yana cike da maguɗi ya yi nuni da
cewa hatta masu lura da zaɓen da suka zo daga ƙasashen duniya duk sun bayar da shaidar
cewa an tafka maguɗi a zaɓen.”
(“Gowon Ya Yi Tir Da Zaɓe”,
2007).
A nan tsohon shugaban ƙasa ne a zamanin mulkin soja, Janar Yakubu
Gowon yake kokawa kan irin yadda aka gudanar da babban zaɓen shekarar 2007. Ya yi
tir da zaɓen, wanda ya ce an tafka maguɗin da hatta masu sanya ido na ƙasashen waje
sai da suka bayar da shaida kan irin maguɗin da aka yi.
Haka ma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar hamayya ta ANPP
a zaɓen shekarar ta 2007 ya bayyana cewa, zaɓen da aka gudanar yana cike da matsaloli
da suka shafi maguɗi wanda ya ce an tafka a zaɓen. Ga abin da aka samu daga jaridar
Aminiya:
“Ɗan takarar shugabancin
ƙasa na ANPP Muhammadu Buhari ya ƙara da cewa akwai matsaloli da maguɗi iri-iri
da aka tafka a lokacin zaɓen, kuma an aikata zalunci mai yawa wanda ya ce ba za
su iya haƙura da su ba.”
(“Gowon Ya Yi Tir Da Zaɓe”, 2007)
Bayan kammala zaɓen, jam’iyyar hamayya ta ANPP ta yi watsi da
sakamon zaɓen ta bakin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar Muhammadu Buhari, inda
ya bayyana cewa, zaɓen ba shi da sahihancin da za a amince da shi, domin yana cike
da maguɗi iri-iri da kuma zalunci mai yawa wanda ba za su iya zuba ido su haƙura
da su haka nan ba.
A wani wurin daban kuma, an nuna maguɗin da akan
yi zargin an tafka yawanci masu riƙe da madafun iko ne sukan yi, domin neman tabbata
a kan mulki ko da kuwa talakawa ba su so. Littafin Da Bazarku ya kawo irin wannan batun kamar haka:
“Haba ina! Maigida ka
taɓa ganin siyasa ta kafu a kan turbar da talakawa ke mutuwa don yunwa. Zaɓe kuwa
ya zama kamar kacici-kacici saboda tsabar maguɗi, yin je-ka-na-yi-ka da kuma ɗauki
ɗora a muƙaman siyasa.”
(Surajo, 2006: 6).
A nan an nuna ai siyasa ba za ta tsayu da
ƙafafunta ba matuƙar talakawa suna cikin matsananciyar yunwa, wanda kan haifar da
maguɗi cikin sauƙi, domin ko yaya aka ɗan gutsura wa talaka wani abin da bai taka
kara ya karya ba na buƙatar yau da kullum za a saye ‘yancinsu. Wannan ya sa zaɓe
ya zama cike da maguɗi da kuma ɗauki-ɗora da masu mulkin kan yi. Wato wanda suka
so kawai shi ne zai yi mulki domin duk wata hanya ta maguɗi tana hannunsu.
Idan aka dubi bayanan da aka kawo a sama za a fahimci cewa, maguɗin
zaɓe yana cikin abubuwan da suke hana samun cigaba a siyasa domin kuwa, hanya ce
da ake tauye wa al’umma haƙƙinsu da kuma hana su kai ga muradinsu. Duk wanda ya
san ba zaɓen sa aka yi ba, ko kuma al’umma ba shi suke so ba, to bai cika tsayawa
ya yi abin da al’umma suke buƙata ba. Wannan yakan sa al’ummar ƙasa su yi ƙasa a
guiwa wajen jajircewa don tabbatar da adalcin shugabanni, domin kuwa shugabannin
sun san cewa ba zaɓensu aka yi ba, kuma ko da ba su yi wa al’umma abin a-zo-a-gani
ba za su sa rai da za su iya ɗorewa a kan mulki ta hanyar da suka hau.
5.3.3 Sayen Ƙuri’a
Daga cikin abubuwan da sukan haifar da koma-baya ga cigaban ƙasa
a siyasance akwai sayen ƙuri’a a lokacin zaɓe, inda ‘yan siyasa kan riƙa bin masu
zaɓe suna ba su kuɗi ko wani abin amfani domin su jefa masu ƙuri’a. Sau da dama
jam’iyyu kan sanya wakilansu a kowacce tashar zaɓe domin kula da yadda zaɓen yake
gudana. Waɗannan wakilan kan kasance masu sanya ido ne domin ganin cewa ba a cuce
su ko an yi masu wani abin da ba daidai ba. A irin wannan yanayi akan samu wata
‘jam’iyya ta kere wata wajen samun adadin waɗanda za su jefa mata ƙuri’unsu, inda
hakan yakan sa ɗayar jam’iyyar da take ganin za a kere ta wajen samun ƙuri’u ta
yi duk mai yiwuwa, wajen ganin ba a yi nasara a kanta ba. Ita ma ɗaya jam’iyyar
sai ta shiga raba nata kayayyakin don kare kanta daga faɗuwa ko samun naƙasu a ƙuri’unta.
Irin wannan ne kan sa magoya bayan jam’iyya su fara raba wa jama’a wasu abubuwan
amfani da suka haɗa da kuɗi da abinci da turamen zannuwa da sabulun wanka da yaduka
da dai sauransu.
Sayen ƙuri’a bayyana a
cikin tarihin siyasar jam’iyyu, domin an samu batutuwa da suke nuna yadda aka riƙa
cinikin ƙuri’a ana biya da ‘yan abubuwan da ba su taka kara sun karya ba. Duk da
cewa wasu sun san sayar da ƙuri’a sayar da ‘yanci ne da yakan jefa al’umma cikin
ƙuncin rayuwa. Da dama cikin ‘yan siyasa a yau sun san cewa amfani suka yi da kuɗinsu
suka sayi kujerar da suke a kai, don haka maimakon su yi tunanin yi wa al’umma aikin
da zai kawo masu cigaba, sai su ce sai sun mayar da kuɗinsu sun ci riba, wanda a
ƙarshe al’umma sukan koma suna da-na-sani. Bugu da ƙari, sayen ƙuri’a babban laifi
ne wanda dokar ƙasa ta haramta, kamar yadda jaridar Premium Time Hausa ta ruwaito cewa:
“Magu ya ce a cikin dokar
zaɓe ta 2010 akwai sashe na 124 wanda ya ce hukuncin tara ta naira 500,000 ta hau
kan wanda aka kama yana sayen ƙuri’u da shi da mai sayarwar ya ce akwai ƙarin ɗauri
na watanni 12 ko mutum ya biya tara, ko kuma a haɗa masa biyu ɗin duka. Sannan kuma
ba zai ƙara yin zaɓe, har sai bayan ya biya tarar tukuna.”
(Murnai, 2019).
Idan ana batun abubuwan da suke kawo cikas ga samun ci gaba a
cikin siyasar jam’iyyu to sayen ƙuri’a yana ciki. Idan aka duba irin tanadin da
doka ta yi wa masu aikata wannan mummnan aiki za a yarda cewa, yana hana samun cigaba
a siyasance. Kamar yadda jaridar ta nuna akwai tara mai har na naira dubu ɗari biyar
da kuma ɗaurin shekara guda ko tara ko kuma a haɗa wa wanda ya aikata wannan laifin
duka biyu. Baya ga tarar, duk wanda aka kama da laifin sayen ƙuri’a, a doka ba zai
sake jefa ƙuri’a ba sai an tabbatar ya biya tarar kafin har ya zama ƙuri’arsa za
ta yi amfani.
A wuraren zaɓen fid da gwani kuwa akan raba maƙudan kuɗaɗe da
motoci da mashina da dai sauransu, duk don a samu ƙuri’ar mai zaɓe. Irin waɗannan
sun fito a cikin siyasar ƙasar Hausa musamman ma a wannan jamhuriyar, inda siyasar
me-zan-samu ta samu karɓuwa a zukatan al’umma, maimakon siyasar aƙida da kishin
ƙasa waɗanda aka sani a jamhuriya ta ɗaya da ta biyu. Duk da cewa hukumar zaɓe ta
tabbatar cewa laifi ne saye da sayar da ƙuri’a, kuma za ta sanya ƙafar wando ɗaya
da masu irin wannan aikin, kamar yadda ta tabbatar a cikin jaridar Leardership Hausa cewa:
“Mun san abu ne mai wahala
sosai ba mai sauƙi ba, to amma INEC za ta yi bakin ƙoƙarin ganin ta daƙile masu
bayar da kuɗi suna sayen ƙuri’u wasu ba za su ji daɗin wannan kyakkyawan aikin da
za mu yi na ƙara tsaftace zaɓe ba. Don haka su ma za su bijiro da nasu dabarun.
Sai dai kuma INEC za ta haɗa kai da ‘yan sanda, EFCC da sauran hukumomin tsaro domin
su taimaka wajen kashe kaifin masu sayen ƙuri’u a wurin zaɓe ko kafin zaɓe. Yakubu
ya yi kira ga ɗaukacin masu jefa ƙuri’a cewa su tuna ƙuri’arsu fa ‘yancinsu ce.
Don haka su yi amfani da hankali da hangen nesa, su daina sayar da ‘yancinsu a kan
wasu ‘yan kuɗi ƙalilan waɗanda za su kashe a rana ɗaya.”
(Sulaiman, 2023).
A nan shugaban hukumar zaɓe ne yake bayani kan irin matakan da
za a ɗauka kan masu sayen ƙuri’a, inda ya nuna hana saye da sayar da ƙuri’a aiki
ne mai kyau, domin zai tsaftace zaɓe. Wannan ne ma ya sa ba hukumar ce ita kaɗai
za ta yi wannan aiki ba, za ta haɗa kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da wannan
ƙuduri nata. A cikin bayaninsa kamar yadda jaridar ta ruwaito ya nuna cewa, sayar
da ƙuri’a sayar da ‘yanci ne, kuma duk wanda ya sayar da ‘yancinsa zai rayu cikin
bauta. Don haka ya yi kira ga jama’a da su daure su dai na sayar da ‘yancinsu kan
ɗan abin da ba zai kashe masu ƙishi ba. Daga cikin bayanan za a ga irin illar da
sayen ƙuri’a yake yi ga cigaban ƙasa, domin kuwa yana mayar da ‘yan ƙasa tamkar
bayi don ba su da wani cikakken ‘yanci, sai yadda aka yi da su, domin sun karɓi
kuɗi ko wani abin da bai taka kara ya karya ba a madadin su zaɓi wanda ya cancanta,
wanda zai kawo cigaba ga ƙasa da al’ummar ƙasa.
A cikin littafin ƙagaggun labaran Hausa ma an samu irin waɗannan
batutuwa na sayen ƙuri’a a lokacin zaɓe waɗanda suka tabbatar da samuwarsa a cikin
tarihin siyasar jam’iyyu a. Akan samu batun sayen ƙuri’a tun a wurin zaɓen fitar
da gwani, inda akan yi zaɓe ne ba bisa cancanta ba, akan saye masu zaɓe ne da kuɗi
masu kauri, kuma cikin ‘yan takara wanda ya fi bayar da kuɗi mai kauri shi ne wanda
zai yi nasara. Irin wannan misali na sayen ƙuri’a ya sake fitowa a cikin littafin
Tsuntsu Mai Wayo da aka samar a shekarar
1993, kamar haka:
“A gaskiya Isa, mutanen
nan miyagu ne. Shekaranjiya sun kira ni, amma jiya da na koma na tarar har sun gama
komai da komai a kan zaɓen gudun-ya-da-ƙanin-wani. Hatta rajistata ta fito sai hotunana
kawai da za a liƙa. Nan take suka ware naira miliyan biyu don sayen ‘yancin ‘yan
jam’iyya na yin zaɓe.”
(Babinlata, 1993: 28).
Zahir ne yake bai wa abokinsa Isa labarin iyayen gidansa da suka
shirya tsayar da shi takarar gwamna, inda yake nuna masa irin shirin da suka yi
na zaɓen fitar da gwani da irin kuɗin da suka tanada musamman domin sayen ƙuri’un
masu zaɓen.
A cikin littafin Kan Mage
Ya Waye an nuna inda wakilan wani ɗan takara mai suna Isyaku Nasarawa suka riƙa
bi gida-gida suna sayen ƙuri’un jama’a. Dubi wannan misalin:
Almuru na yi da misalin
karfe takwas da kwata na dare sai wakilan Isiyaku Nasarawa suka shiga aikin nasu
gari-gari, gida-gida suna tara jama’a suna yi masu bayanin abinda suke so Allah
ya kai mu safiya a wajen zabe, bayan an gama jawabi sai a kawo kuɗin su ma a ba
su kan amana su yi alƙawari su amsa a kuma tsorata mutum a ce idan bai jefa kuri’a
ba za a yi karar shi bayan zabe.
(Jiƙamshi, 1997: 41)
A nan marubucin ya nuna cewa an riƙa bin mutane gida-gida ana
ba su na goro domin su zaɓi ɗan takara, kuma ba haka nan kawai ake ba su ba sai
sun yi alƙawarin za su zaɓa da sharaɗin in ba su zaɓa ba za a kai su kotu su biya.
Yawanci irin wannan barazana ce kawai akan yi wa masu zaɓe, amma dai duk da haka
ido da kunya, a wasu lokuta wanda aka wakilta ya raba kuɗin yakan kasance a wurin
jefa ƙuri’ar, wanda yakan sanya waɗanda suka karɓi kuɗi su ji kunya wajen zaɓen
har sai sun jefa masa ƙuri’ar da suka amshi kuɗinta.
An ƙara samun irin wannan misali a cikin littafin Dambarwar Siyasa, inda aka nuna cewa, kusan
dukkan waɗanda ake sayen ƙuri’unsu talakawa ne. Dubi abin da ya ce:
“Hankula suka tashi bayan
da suka samu tabbacin cinikin kasuwa da aka yi da rayuwar talaka a mafi yawancin
rumfuna. Sai dai tana da tabbacin za a hukunta duk wani wanda aka kama da sayen
ƙuri’a, kamar yadda ta wajabta.”
(Aminiya-Trust, 2020: 75).
A nan ana nuna yadda talaka ya yi cinikin
rayuwarsa ne da hannunsa ta hanyar sayar da ƙuri’arsa wadda take da muhimmanci a
rayuwarsa, domin ita ce ‘yancinsa, a kan ‘yan kuɗin da ba su taka kara sun karya
ba a rumfunan zaɓe.
Irin wannan sayen ƙuri’ar
a ranar zaɓe ya kasance wani tarnaƙi ne da yake haifar da koma baya ga cigaban ƙasa.
Yakan kasance tamkar al’umma ta sayar da ‘yancinta ne da abubuwan da ya kamata ta
samu a cikin shekarun da waɗanda aka zaɓa za su kwashe suna jan ragamar shugabanci.
5.3.4 Angulu Da Kan Zabo
Idan aka yi batun angulu da kan zabo a cikin siyasar jam’iyyu
ana nufin wani yanayi da mutumin zai kasance cikin wata jam’iyya a zahiri, amma
a bisa gaskiya ba ita yake yi wa hidima ba. Zai riƙa yin wasu abubuwa saɓanin abin
da jam’iyyarsa take buƙata, musamman wanda zai iya jawo mata baƙin jini a wurin
al’umma ta rasa magoya baya. Angulu da kan zabo cin amana ne, domin an riga an amince
da mutum an saki jiki da shi a cikin wani rukunin mutane a matsayin ɗan jam’iyya,
kuma an damƙa masa amanar sirrin jam’iyyar da duk wasu hanyoyi na ci gabanta, amma
sai ya kasance yana bayyana sirrin jam’iyyar ga abokan hamayyarta, abin da zai iya
dakushe ta. An samu da dama a cikin tarihin siyasar jam’iyyu inda ‘yan siyasa sukan
riƙa yin angulu da kan zabo ta hanyar kushe tsarin jam’iyyar da suke ciki ko yabon
jam’iyyar da ba tasu ba, ko yi wa wata jam’iyya da ba tasu aiki a lokacin zaɓe domin
ganin ta yi nasara a kan jam’iyyarsu.
Akwai dalilai da dama da sukan sanya ‘yan siyasa ɗaukar wannan
ɗabi’a ta angulu da kan zabo, kamar su: rikicin cikin gida na jam’iyya da rashin
adalci tsakanin ‘ya’yan jam’iyya da rashin aƙida da son zuciya da son abin abin
duniya da dai sauransu. Mafi akasari masu yin angulu da kan zabo a siyasance ba
su faye kallon maslahar al’umma ba, galibi maslahar kansu ne take sa su faɗa cikin
wannan ɗabi’ar domin ganin abin da za su samu na tagomashi a siyasance.
Angulu da kan zabo yana daga cikin abubuwan sukan haifar da matsaloli
a cikin siyasar jam’iyyu domin wani abu ne wanda yawancin ‘yan siyasa suke kallon
sa a matsayin munafinci a siyasance. Ya shafi ɗaukar sirrin jam’iyya da ‘ya’yanta
suke yi su kai wa wata, ko kuma su bayar da sirrin da zai sa a yi galaba a kan jam’iyyar
da suke cikinta. Irin wannan ɗabi’a tana da tushe a tarihin siyasar jam’iyyu domin
an samu wasu bayanai a rubutaccen zube da suka nuna an fara samun irin wannan tun
a farko-farkon siyasar jam’iyyu, kafin ma a kai ga samun ‘yancin kai. Dubi wannan
misalin:
“Da me ya sa Jamilu ya fita daga AG ya koma NPC?
Dalili dai in ji M. Nadabo shi ne da ma ya shiga NPC ne don yaudara su amince masa
sannan daga baya ya riƙa kai musu sirrin NPC, sanna ya sake komawa jam’iyyar tasa
ta AG.”
(“Jamilu Ya Ji Kunya”, 1959).
Wannan wasiƙar da aka samu a cikin jaridar Sodangi ta nuna wani ɗan jam’iyyar AG mai
suna Jamilu da ya koma jam’iyyar NPC, inda ‘yan jam’iyyar suka zarge shi da yin
angulu da kan zabo ga jam’iyyar domin sun ce yana kwashe sirrin jam’iyyar yana kai
wa tsohuwar jam’iyyarsa ta AG. Wannan shi ne ake kira da angulu da kan zabo, domin
ya nuna a zahiri shi ɗan jam’iyuyar NPC ne, amma a zuciyarsa yana tare da jam’iyyar
AG domin yana kwaso sirrin NPC ya faɗa wa jam’iyyar AG ko dai don ta gano lagon
jam’iyyar ta yi nasara a kanta ko kuma don ya samu wani abu daga wajen ‘ya’yanta.
Irin wannan ne aka nuna a cikin wata wasiƙa ta Ɗanjani Haɗeja
da jaridar Daily Comet ta buga, inda ya
kawo bayani kan wasu ‘yan NEPU da suke son haifar da ruɗani a cikin jam’iyyar, inda
suke yawo da maganganu tsakanin Tanko Yakasai da Malam Lawan Dambazau domin su haddasa
rigima a tsakaninsu. Ga misalin kamar haka:
“Waɗannan mutane ba ‘yan
NEPU na halak ba ne, sayaiyu ne daga jam’iyyar hamayya musamman Action Group. Na
sami labari wai an yi tsada da su wai za a biya su fam dari da hamsin don su kawo
rudu a NEPU
”
(Haɗejia, 1961).
Ɗanjani Haɗeja ya bayyana cewa waɗanda ke yawo da waɗannan ,maganganu
na raba kan ‘yan jam’iyyar NEPU ba ‘yan NEPU ne na halak ba, sayen su aka yi daga
jam’iyyar hamayya ta AG, inda ya nuna cewa har kuɗin da aka biya su domin su kawo
rabuwar kai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar yana da masaniya a kai. Ya ce an biya kuɗi
fam ɗari da hamsin domin su haifar da matsala da rashin jituwa tsakanin ‘yan jam’iyyar
guda biyu, waɗanda kuma haifar da matsala tsakaninsu zai haifar wa da jam’iyyar
matsaloli, kasancewar suna da magoya baya.
Irin wannan ya ci gaba har zuwa jamhuriya ta biyu wuraren shekarun
1979 zuwa 1983, inda a cikin littattafan zube marubuta suka nuna wasu abubuwa da
suka shafi angulu da kan zabo a cikin ayyukansu. Alal misali, littafin Tura Ta Kai Bango ya fito da irin wannan
yanayi, inda ‘yan jam’iyyar Riƙau suka tura wani ya shiga jam’iyyar hamayya domin
ya riƙa samo masu labarin halin da jam’iyyar take ciki. Dubi abin da marubucin ya
ce:
“ Ai wannan ba wuya, domin
na sami yaron nan Mantai na liƙa cikin masu goyon bayan jam’iyyar domin ya zama
kunnenmu a can. Da shi ya gaya mini cewa sun ce ya shugabanci jam’iyyar shi kuma
ya ce jam’iyyar har guda nawa zai shiga bayan ya riga ya shiga tamu. Na ce masa
a’a je ka ka zama kunnenmu da idanunmu a can.”
(Katsina, 1983: 45).
Mantai yaron su Alhaji
Kaukai ne, wannan ya sa ya bi iyayen gidansa na siyasa zuwa jam’iyyarsu, duk da
cewa kuwa an tallata masa jam’iyyar Sauyi, amma sai ya nuna cewa ya riga ya shiga
Riƙau, amma sai maigidansa ya nemi da ya je ya nuna ya bi jam’iyyar Sauyi domin
ya riƙa ta samo bayanan sirri daga cikinsu yana kawo wa ‘yan jam’iyya Riƙau, wato
iyayen gidansa su Alhaji Kaukai. A nan idan aka duba za a ga cewa angulu da kan
zabo Mantai yake yi, wato a can ɗan jam’iyyar Sauyi, amma yana yi wa ‘yan jam’iyyar
Riƙau aiki ta kaikaice.
Shi ma marubucin littafin Kowa Ya Bi ya nuna a cikin jerin wasu abubuwa waɗanda sukan zama silar
rasa samun ci gaba a siyasa akwai angulu da kan zabo, inda ya ce:
“ baya ga haka a irin
wannan siyasa da muka tsinci kanmu a ciki ta yin amfani da kuɗi, maguɗin zaɓe, cin
amana (Anti-Party), yaudara, yarfe, ƙage yin amfani da ‘yan daba da ‘yan kalare
don biyan buƙatar kai domin ofishina yana sane da waɗanda aka ba wa alhakin wannan
binciken, duk kuwa da cewa biyu daga cikinsu ‘yan jam’iyyarmu ne amma muna sane
da irin rawar da suke takawa domin kassara wannan gwamnati ”
(Isa, 2007: 20).
A nan marubucin ya nuna wasu abubuwa ne da sukan haifar wa da
tsarin siyasa matsala domin suka haifar da koma baya a siyasance, cikinsu har da
angulu da kan zabo. Ya bayyana wasu da aka sanya cikin kwamitin bincike waɗanda
‘yan jamiyya mai mulki ne, amma kuma suna ba da gudummawa wajen cin dunun gwamanti
mai mulki a ƙarƙashin jam’iyyar da ake ganin su a cikinta.
Daga bayanan da aka kawo an fahimci cewa, angulu da kan zabo
a cikin siyasar ƙasar Hausa ba abu ne sabo ba, domin an gan shi a cikin misalai
da dama tun daga farkon siyasar jam’iyyu zuwa yau.
5.3.5 Bangar Siyasa
Dangane da wannan aikin, bangar siyasa tana nufin wasu ayyuka
da suka shafi ta’addanci da keta dokar da ta shafi cin zarafin ɗan’ Adam da lalata
dukiyar jama’a musamman abokan hamayyar siyasa domin huce haushi ko don wani dalili
da ya shafi siyasa.
Bangar siyasa ta daɗe da ginuwa cikin tarihin siyasar ƙasar Hausa,
domin kuwa abu ne wanda ya samo asali tun daga jamhuriya ta farko. Tarihi ya nuna
cewa an ga ɓullar bangar siyasa ta farko ne a Kano, ranar 29 ga Yuni, 1951 lokacin
da En’e suka shirya wani gangami na ‘yan banga waɗanda galibinsu bayin sarki ne
ƙarƙashin wani mai suna Mamman Nagindin waya, wanda suka sanar da kafa wata ƙungiya
mai suna ‘Jam’iyyar Mahaukata’, wadda ta riƙa cin zarafin ‘yan jam’iyyar NEPU har
da shugabanninsu. Sun riƙa yawo, suna zaga gari, suna waƙoƙi masu cike da zage-zage
domin su tunzura magoya bayan NEPU. Ko da aka kai ƙarar su wajen Di’o sai ya goyi
bayansu cewa su ma ‘yan NEPUn sun zagi Turawa. Wannan ya sa suka ci gaba da kai
wa ‘yan NEPU irin su Abdulƙadir Ɗanjaji da Babba Ɗan Agundi da Abba Maikwaru shugaban
jam’iyyar NEPU hare-hare har gidajensu. Sun taɓa lakaɗa wa mutane irin su Maitama
Sule da Sherif Ali duka har suka raunata Sherif ɗin. Ko da ‘yan NEPU suka lura babu
wani matakin da za a ɗauka su ma suka samar da nasu ‘yan bangar waɗanda suka riƙa
mayar da martani idan aka wulaƙanta su.[7] Wannan shi ne farkon
bangar siyasa a ƙasar Hausa wanda za a iya danganta shi da cewa shi ne ya gangaro
har zuwa jamhuriya ta huɗu.
An riƙa samun bayanai na ayyukan bangar siyasa da suka fito a
cikin rubutattun ayyukan adabi kasancewar kusan kowace jam’iyyar siyasa da aka kafa
akan samu ‘yan banga a cikinta waɗanda akan samu ayyukansu a lokacin kakar siyasa
ko zaɓe. Alal misali, irin wannan bangar siyasa ta fito a cikin jaridar Daily Comet, inda aka nuna cewa an yi wa
wani Malam Ibrahim Imam duka an farfasa motarsa. Ga misalin:
“Mun samu labarin an yi
wa Malam Ibrahim duka har an farfasa motarsa da ta Basharu a wata rana da shi M.
Ibrahim ɗin ya yi lacca a ƙarƙashin Action Group da ya zo yana lacca sai ya shiga
sukan M. Aminu da NEPU wannan ya sa aka cafke shi daga kan lacca aka fara yamutsa
shi, abin dai sai da ya shiga motarsa ya gudu. To da jama’a suka ga ya gudu zuwa
gida ne suka bi shi har can suka farfasa motar aka yi wa wani dan’iya na Action
Group duka. Daga nan fa aka tafi ofishin da suka kafa aka cire lambar aka kakkarya
kujerun ciki da teburan, sannan kuma aka zarce gidan Basharu aka yi masa duka shi
ma aka farfasa tasa motar.”
(An Yi Wa M. Ibrahim Imam
Duka, 1958)
Wannan misali ne na yadda aka fara bangar siyasa tun kafin ma
a samu ‘yancin kai, domin idan aka duba za a ga cewa tun a wuraren shekarun 1958
aka yi wa waɗannan ‘yan siyasa duka don kawai sun soki shugaban siyasar NEPU. Duk
da cewa Malam Ibrahim Imam ya gudu, amma sai da aka bi shi har gida aka farfasa
masa motarsa, kuma aka jejjefi gidansa tare da haɗawa da wani yaronsa shi ma laifin
maigidansa ya shafe shi. Duk bayan an gama yi wa wannan ɗan AG ɓarna sai aka wuce
gidan wani Basharu shi ma ɗan jam’iyyar AG aka faɗa shi da duka, shi ma aka farfasa
tasa motar.
Ba a ɗauki wani dogon lokaci ba irin wannan bangar siyasar ta
zagaya Arewacin Nijeriya, ta yadda masu iko suke samun daman gallaza wa abokan hamayya
ta hanyar amfani da ‘yan bangarsu. A wasu lokuta da gangan ake tsokanar ‘yan hamayya
don su yi magana kawai a wulaƙanta su. Alal misali, a
lardin Sakkwato an samun ɓullar bangar siyasa ne a Tsafe, inda wani Altine ya zagi
‘yan NEPU lokacin da suke gudanar da taro, ko da aka kai shi ƙara wajen ‘Yandoto
sai ya goyi bayansa. Tun daga nan al’amuran bangar siyasa suka samu gindin zama
inda akan zagi ‘yan NEPU a ci mutuncinsu ba tare da ɗaukar wani mataki ba, maimakon
haka ma ‘Yandoto yakan gode masu ne ta hanyar ba su kyaututtuka[8].
A jamhuriya ta biyu lokacin da ayyukan bangar siyasa suka yi
ƙamari, jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta
bayyana tsoronta kan irin barazanar da bangar siyasa yake yi ga tsarin siyasar jam’iyyu,
inda ta bayyana cewa tun a jamhuriya ta farko irin waɗannan ayyukan na bangar siyasa
su ne suka zama silar juyin mulki na farko a tarihin siyasar jam’iyyu a Nijeriya,
wanda sojoji suka yi a shekarar 1966. Dubi abin da jaridar ta ruwaito:
“’Yan siyasa waɗanda suka
ji daɗin mulki ko kuma suke matuƙar kwaɗayin ɗana mulkin yanzu an wayi gari sun
jefa ƙasar cikin wani irin mummunan matsayi ta hanyar yin amfani da ‘yan iska masu
shan ƙwaya da ganyen tabar wiwi da barasa, watau ‘yan banga. Waɗanda irin mummunan
ayyukansu ne suka sanya sojoji suka ƙwace mulki daga hannun farar hula a shekarar
1966.”
(“‘Yan Banga a Jam’iyyu”, 1983).
An bayyana cewa bayan sanar da zaɓen zango na biyu a jamhuriya
ta biyu wato a shekarar 1983, an zargi jam’iyyar NPN da tafka maguɗi. ‘Yan bangar
siyasa ne suka ci gaba da ta da hargitsi wanda har ya haifar da hasarar rayuka,
wanda hakan ya zama dalilin juyin mulkin da sojoji suka yi wannan ya kawo ƙarshen
jamhuriya ta biyu.[9] Dubi abin da Jaridar
Gaskiya Ta Fi Kwabo ta hasko yadda al’amuran
bangar siyasar. Dubi abin da jaridar ta ce:
“Ko kaɗan wannan jarida
ba ta ji daɗin ganin yadda salon yin amfani da ‘yan banga a cikin siyasar wannan
zamanin ba A yau an wayi gari Jihar Kano wadda aka fi san ta da daɗaɗɗen tarihi
da walawa da zaman lafiya sai ga shi ta zamo kamar TABUKA saboda yawan tashin hankalin
siyasa da zubar da jinin jama’a.”
(“‘Yan Banga a Jam’iyyu”, 1983).
A nan jaridar ce ta nuna rashin jin daɗi kan yadda al’amuran
bangar siyasa suka zama barazana ga al’umma. Ta buga misali da jihar Kano wadda
ta kasance cikin zaman lafiya, amma sakamakon al’amuran bangar siyasa duk abubuwa
sun lalace. Jaridar ta kwantanta jihar da fagen yaƙi saboda yadda ake yawan tashin
hankali da zubar da jini a dalilin ayyukan bangar siyasa.
Tun daga lokacin da aka fara samun ɓullar banbar siyasa a 1951
har zuwa 2023, galibi ‘yan bangar siyasa ba zaman kansu suke yi ba, kuma duk abubuwan
da suke aikatawa da ɗaurin gindin iyayen gidansu suke aikatawa. Wannan ne ma ya
sa iyayen gidan nasu sukan riƙa basu miyagun abubuwan da suke amfani da su na makamai
da kayan shaye-shaye kamar yadda jaridar Gaskiya
Ta Fi Kwabo ta nuna cewa:
“’Yan banga suna cin karensu
babu babbaka domin wasu la’antattu ‘yan siyasa ne iyayen gidansu waɗanda ke ba su
kuɗaɗen ɓatarwa su kuma saya masu ƙwayoyi da wiwi da makamai wai don kawai su je
su tursasa duk wani abokin hamayyarsu.”
(“‘Yan Banga a Jam’iyyu”, 1983).
A wannan misalin da yake sama, an nuna cewa ‘yan bangar siyasa
suna gudanar da ayyukansu ne tare da goyon bayan iyayen gidansu, waɗanda su ne suke
samar masu da abubuwan buƙatunsu kamar kuɗin kashewa da shaye-shayen ƙwayoyi da
tabar wiwi waɗanda sukan sha don ya gusar masu da hankali. An sani cewa duk wanda
hankalinsa ya gushe zai iya aikata komai. Daga nan kuma sai a ba su makamai wanda
yawanci sukan yi amfani da su ne a kan abokan hamayyarsu na siyasa.
Bayan an bai wa ‘yan banga ire-iren waɗannan makamai da abubuwan
gusar da hankali akan fita ko dai yaƙin neman zaɓe ko kuma ma a ranar zaɓen sukan
kasance ba su ganin kan kowa da gashi, kuma duk abin da aka sa su za su aikata shi
ba tare da wani shayi ba. Za su riƙa aikata wasu abubuwa waɗanda duk mai hankali
idan ya gan su zai fahimci ba hankali a tare da su. Ga misali:
“‘Yan banga(wato dogarai
na jam’iyya) ma ba a bar su a baya ba sai ihu suke yi suna kirarin jam’iyyarsu,
suna tsine wa wanda ba ya ƙaunarta. Kowanne daga cikinsu idanunsa jawur kamar wanda
ya sha ƙwaya. Wasu hannayensu riƙe da dorina don dukan wanda duk ya taɓa shugabanninsu,
ko ya kawo wasa.”
(Katsina, 1983: 5).
A kodayaushe idan aka fito yaƙin neman zaɓe, ‘yan bangar siyasa
su ne kan riƙa ɗaga murya suna kirarin jam’iyyarsu, suna ihu a wasu lokutan suna
zage-zagen da faɗin miyagun kalamai ga abokan hamayya kamar yadda wannan misali
ya nuna, sukan riƙa tsine wa wanda ba ya ƙaunar jam’iyyarsu. A lokacin da suke cikin
wannan hali yawanci sukan riƙe ko dai makami ko wani abu da zai iya cuta wa abokin
hamayya kamar dorina ko gora ko adda da dai sauransu. Da zaran an samu wani abokin
hamayya ya tanka masu to sai su ce da wa aka haɗa su ba da shi ba, kamar dai yadda
ya faru a cikin wannan misalin da yake ƙasa:
A wani ƙauye da ake kira
Garken Gada nan ne wani saurayin ƙauyen ya yi gigin ɗaga hannu ya nuna alamar jam’iyya
da ba ta waɗannan mutane ba ce mota guda ta ‘yan banga ta tsaya, suka sauko suka
dinga dukansa, sai dai suka bar shi kwance.”
(Katsina, 1983: 3).
Irin wannan ya sha faruwa a cikin tarihin siyasar jam’iyyu, kuma
har yanzu yana faruwa. A nan wannan matashi ya nuna alamar jam’iyyarsa ce kawai
wadda ba ta waɗannan da suka fito ba, sai suka faɗa shi da duka, suka bar shi kwance
jina-jina. A wannan zamanin da muke ciki ma irin wannan ya taɓa faruwa a kan idon
mai wannan bincike, inda jerin gwanon motocin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban
ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa a shekarar 2012 ta zo wucewa a Unguwar Rimi Kaduna.
Wani matashi ya ce masu “Ƙarya ne!” Ashe tawagar ‘yan bangar da take zuwa ɗauke
da makamai sun ji abin da ya faɗa, suna zuwa inda yake wani ya doke shi da sanda,
a take ya faɗi sumamme. A nan suka bar shi kwance.
A jamhuriya ta huɗu ma an ci gaba samun ayyukan bangar siyasa.
Galibi ‘yan bangar siyasa sun fi yin ta’addancinsu ne ranar zaɓe, kasancewar matasa
sukan yi dafifi wajen jefa ƙuri’a, kuma sukan kasance magoya bayan mabambantan jam’iyyu,
wanda hakan kan sa idan ba a kai zuciya nesa ba sai hatsaniya ta ɓarke tsakaninsu,
inda har akan kai ga ji wa juna rauni ko ma a rasa rai. Da yawa cikin masu kawo
irin wannan hatsaniyar ɗaukar nauyinsu ‘yan siyasa suke yi kamar yadda aka nuna
yadda sukan samu ɗaurin gindi a baya, ta yadda hatta makaman da sukan yi ayyukan
bangar siyasa da ta’addanci ranar zaɓe samar masu da su ‘yan siyasa suke yi. Haka
kuma sukan saya masu kayan shaye-shaye na gusar da hankali waɗanda za su iya aikata
miyagun ayyuka ba tare da sun sani ba. Dubi wannan misali:
“Sauran muhimman abubuwa
da suke buƙatar kuɗi don aiwatar da su a halin yanzu sun haɗa da yin odar tabar-wiwi
da sauran kayan caku don rabawa ga matasa da za mu yi amfani da su ranar zaɓe tare
da sawo ‘yan makamai da ba su taka kara sun karya ba don kare kai daga abokan hamayya
”
(Surajo,2006: 107-108).
Wannan misali yana nuna yadda aka shirya tsare-tsaren siyasa
har da ayyukan bangar siyasa, inda ‘yan siyasar sukan ware maƙudan kuɗaɗe domin
tabbatar da an samar da abubuwan da ‘yan banga za su yi amfani da su kamar kayan
shaye-shaye irin su tabar wiwi da ƙwayoyi da dai sauran kayan maye masu gusar da
hankali, sannan a samar da nau’o’in makamai domin kare kai daga abokan hamayya kamar
yadda misalin ya nuna.
Al’amarin bangar siyasa ya bunƙasa musamman a jamhuriya ta huɗu
lokacin da ake shirin shiga zango na uku, wato kakar zaɓen 2007, inda aka riƙa ganin
gungun ‘yan bangar siyasa na jam’iyyu daban-daban, musamman lokacin yaƙin neman
zaɓe ɗauke da makamai. ‘Yan bangar sukan riƙa wasa da makaman don tsorata abokan
hamayya. Hakan ya fito a cikin wata wasiƙa da aka aika wa jaridar Aminiya ta ranar 23 ga Maris 2007. Ga abin da aka tsakuro daga wasiƙar:
“Bayan gaisuwa don Allah
ku taimaka miƙa nasihata zuwa ga ‘yan siyasa musamman ma ‘yan jam’iyyar ANPP. Ina
kano ranar Asabar da ta wuce da yamma irin makamai da na gani ‘yan bangar jam’iyyar
ANPP suna wasa da su bayan gama taronsu a Kura ya ba ni ni tsoro.”
(“Malam Shekarau A Tsawatar”, 2007)’
A nan an nuna yadda ‘yan siyasa suke tafiya da gungun ‘yan banganrsu
ɗauke da makamai a lokacin yaƙin neman zaɓe. A wasu lokuta hakan yakan tsorata jama’a,
inda wani lokaci ma akan samu arangama tsakanin ‘yan bangar wata jam’iyya da wata,
wanda hakan kan haifar da zubar da jini ko ma a rasa rai.
Daga cikin illar bangar siyasa akwai kashe mutanen da ba su ji
ba, ba su gani ba. Galibi ana samun irin wannan hasarar rayukan ne a lokacin zaɓe,
a inda mutane suka taru domin jefa ƙuri’a, sai ‘yan bangar su zo da makamai su tarwatsa
jama’a. Jaridar Aminiya ta kawo wani labari
kamar haka:
“’Yan bangar siyasa sun
tilasta mata da ƙananan yara tserewa zuwa gonaki domin tsira da rayukansu lokacin
da aka gudanar da zaɓen cike gurbin ɗan majalisar jiha a Ƙaramar Hukumar Ringim
da ke jihar Jigawa An samu hayaniya a ƙauyen Sankara lamarin da ya sa mutane suka
ƙaurace wa gidajensu zuwa gonaki domin tsira daga harin ‘yan sara-suka da ake zargin
Sanata Ɗanladi Sankara ɗan asalin garin ne ya kawo su daga Kano domin su tarwatsa
zaɓen, saboda ya cimma burinsa na siyasa.”
(Majeri, 2013).
Wannan misalin ya fito da yadda akan yi amfani ne da ‘yan bangar
siyasa domin a cimma burin siyasa. Akan yi haka ne idan aka lura cewa jam’iyya ko
wani ɗan takara ba zai samu rinjayen ƙuri’u a wata mazaɓa ba, sai a yi amfani da
‘yan banga don su tarwatsa masu zaɓen wanda hakan zai hana su kaɗa ƙuri’unsu. Ƙuri’un
da aka riga aka kaɗa kuma sai ‘yan bangar su lalata su. A irin wannan yanayi, duk
wanda ya nemi ya yi masu gardama suna iya raunata shi ko ma su raba shi da ransa.
Irin waɗannan al’amura na bangar siyasa sun ci gaba da bayyana
a cikin rubutaccen adabin Hausa, inda wasu akan ba da labarin abubuwan da suka faru,
wasu kuma a bayyana illar bangar siyasar. Alal misali, a cikin jaridar leadrship Hausa an kawo bayani kan bangar
siyasa kamar haka:
“Idan matasanmu suka hankalta
ta hanyar ƙaurace wa bangar siyasa da rikicin zaɓe, tabbas baragurbin ‘yan siyasa
da ba su son zaman lafiya a Nijeriya ba za su kai ga cimma burinsu ba na zubar da
jinin mutane da ba su ji ba, ba su gani ba.”
(Shuaibu, 2022)
A cikin wannan misali an yi nuni ne cewa matasa su guji harkar
bangar siyasa da duk wani nau’in rikicin zaɓe, domin ba ya haifar da ɗa mai ido,
kuma dukkan waɗanda suke sa su ba masu son cigaban ƙasa ne ba, kuma ba su son zaman
lafiyar ƙasa.
A wani misalin na daban da aka samu daga jaridar Leadership Hausa ta fito da batun bangar
siyasa ne lokacin ana gab da babban zaɓen shekarar 2023, inda ta ja hankalin matasa
a kan su guji bangar siyasa. Ga abin da ta ce:
“Muna sake tunatarwa ga
dukkan matasan Nijeriya da su guji yin bangar siyasa domin rayuwarsu tana cikin
haɗari, ɓata-garin ‘yan siyasar ƙasarmu ba za su tsinana musu komai ba illa su ɗibga
masu kayan maye saboda gusar da hankulansu, domin sun san cewa idan matasan suna
cikin hayyacinsu ba za su iya saka su miyagun abubuwa ba ”
(“Matasa a Guji Bangar Siyasa”, 2022).
Daga misalin da yake sama za a fahimci cewa,
akasarin ‘yan bangar siyasa matasa, ne waɗanda ‘yan siyasa suke amfani ne da su
don cimma burinsu. Da yawansu ba za su iya aika irin miyagun ayyukan da akan sa
su su aikata ba idan suna cikin hankalinsu. Wannan dalilin ne ya sa iyayen gidansu
sukan ba su kayan shaye-shaye wanda zai gusar masu da hankali.
Don haka aka yi kira ga matasan a kan su guji bangar siyasa domin ba zai taimaki
rayuwarsu ba.
A cikin littafin Mizani
an samu inda batun bangar siyasa ya fito, inda aka nuna wani matashi ɗan bangar
siyasa da yake nadama kan irin abubuwan da suka aikata na bangar siyasa domin ganin
maigidansu ya kai ga nasara. Ga abin da yake cewa:
“ a ranar da ake gudanar
da zaɓe, irina ‘yan sara-suka ne muka yi fitar ƙwari muka tsaya kai da fata aka
tabbatar gwamna ya ɗare kan muƙamin lamba ɗaya a jihar, sakamakon fitar da makamai
da sassara duk wanda muka lura ba ya tafiyar mai gidanmu, wannan ta sa mutane suka
riƙa dangwala wa jam’iyyarmu ko ba don Allah ba. Idan kuwa mutum ya nemi ya mana
taurin kai sai mu far masa nan take ”
(Mustapha da wasu, 2023: 9).
A nan matashin yana nuna irin yadda suke gudanar da bangar siyasa
ne, inda ya nuna cewa sukan fita a ranar zaɓe domin tabbatar da cewa wanda suke
goyon baya ya kai ga samun nasara ko ta halin ƙaƙa. Ya nuna cewa, sukan fitar da
makamai tare da aikata ta’addanci ga duk wanda suka san ba zai zaɓi maigidansu ba.
Hakan yakan sanya tsoro ga jama’a masu zaɓe. Waɗansu sukan zaɓi ɗan takara ne ba
don suna son sa ba, sai don tsoron cewa rashin zaɓen sa zai iya zama barazana a
gare su. ‘Yan bangar siyasa da za su iya illata duk wanda ya zaɓi wanda ba nasu
ba, kamar yadda aka nuna a cikin misalin da yake sama cewa duk wanda ya nemi yi
‘yan bangar taurin kai, sukan far masa. Idan kuwa suka lura ba za su yi nasara ba,
kuma ba za su iya tirsasa masu zaɓe su zaɓi maigidansu ba, sai su tayar da hankali
a lalata kayan zaɓen, a fasa kowa ya rasa.
Irin waɗannan ayyuka na bangar siyasa suna da illa ga siyasar
jam’iyyu, suna haifar da ci baya ne ga al’umma da ƙasa bak i ɗaya, domin a wasu
lokuta akan samu ɓarkewar rikici wanda yakan zama sanadin hasarar rayuka da dukiyoyin
al’umma, wanda yakan shafi tattalin arziƙinsu da na ƙasa baki ɗaya.
5.3.6 Zuba Jari A Siyasa
Kalmar jari an fi saninta a cikin kasuwanci wanda aka ba ta ma’ana
da cewa, “uwar kuɗi da ake kasuwanci da ita” (CNHN, 2006:214). Duk inda mutum ya
sanya jarinsa a cikin kasuwanci to yana fatar ya ci riba ne, wato ya samu abin da ya
fi adadin abin da ya zuba bayan ya kammala kasuwancin. Irin wannan ne ‘yan siyasa
da manyan ‘yan kasuwa da ‘yan jari-hujja suka ara, suka riƙa zuba jarinsu a cikin
harkokin siyasa. Manyan ‘yan siyasa waɗanda suka riƙe muƙamai a ƙasa da wasu yankuna
na ƙasar da manyan ‘yan kasuwa sukan yi amfani da dukiyarsu wajen goya wa wani ɗan
takara baya domin ya kai ga nasara. A irin wannan yanayi sukan goya masa baya ne
ta hanyar amfani da dukiyarsu domin su yar a baya, su tsinta
a gaba. Galibi sukan kashe ɗimbin dukiya da kuma amfani da hikima da basira da ilimin
siyasar da suke da shi domin su tabbatar wanda suka goya wa baya ya kai ga nasara.
Yawanci sukan sanya wannan kuɗin ne a matsayin jarinsu, tare da tunanin za su fanshe
kuɗinsu a gaba ta wasu hanyoyi da ba wanda zai iya taka masu birki tun da jari suka
zuba.
Irin wannan ya riƙa bayyana a cikin tarihin siyasar jam’iyyu,
kamar yadda ya fito a cikin littafin Tsuntsu
Mai Wayo inda wasu manyan ‘yan kasuwa suka tsayar da wani matashi mai suna Zahir
takarar gwamna. Shi dai matashin ba komai yake da shi ba, amma dai mutum ne mai
farin jini a cikin al’umma. Sun tsayar da shi tare da alƙawarin kashe masa ko nawa
ne don ya kai ga nasara. Ga abin da marubucin ya ce:
“Za mu bayar da dukiyoyinmu
da ƙarfinmu don ganin ka yi nasara ka san shi fatauci don riba ake yin sa Dole ne
in an yi nasara ƙwaryar da ta je ta zo irin ‘yan kwangilar nan mai tsoka a ba mu
Sannan kuma a bar mu mu wataya a cikin harkokin kasuwancinmu.”
(Babinlata, 1993: 22).
Idan aka dubi bayanan da suke cikin wannan misali za a ga cewa,
ba wai kishin ƙasa ne ya sanya suke so su tsayar da matashin ba, so suke su zuba
jari ta yadda za su samu ƙazamar riba. A cikin labarin an nuna yadda suka bayyana
masa cewar za su bayar da dukiyoyinsu don ganin ya yi nasara, amma fa ya sani fatauci
don riba ake yi. Wato kasuwanci za su yi da shi, in aka yi nasara dole ya saka masu
da abubuwan da suka yi masa ta hanyar ba su manyan kwangiloli, ya kuma ƙyale su
su yi yadda suke so a cikin harkokin kasuwancinsu.
A cikin wani misalin da ya shafi zuba jari a siyasa, inda akan
tsayar ‘yan takara kuma a zuba masu maƙudan kuɗaɗe a matsayin jari. Dubi abin da
wannan marubucin ya ce:
Duk da an san Isiyaku
mutum ne mai kudi , sai aka ga cewa bai dace a zura masa ido ya yi ta wahala shi
kadai ba sai an taimaka masa. Domin ai idan aka kai ga nasara ba shi kadai zai ji
dadin ba An yi nasarar samo kuɗin nan da aka fita nema daga jama’a bayan da ya rage
saura sati daya a yi zabe, amma bisa alkawarin cewa da zarar nasara za a biya masu
bukatunsu ta wajen sama masu kwangiloli da sama ma ‘ya’yansu manya-manyan mukamai
a gwamnati.
(Jiƙamshi,
1997: 39).
A nan, an nuna ɗan takara Isiyaku Nasarawa a matsayin mai kuɗi
da ya tsaya takara a jam’iyyarsu. Hamshaƙin mai kuɗi ne, amma abokan siyasarsa na
jam’iyyarsu sai suka ga bai kamata a bar shi ya yi hidimar shi kaɗai ba. Su ma ya
kamata su zuba nasu jarin, domin idan aka yi nasara a ji daɗin tare da su. Wannan
ya sa suka tara kuɗi masu yawa bisa alƙawarin idan aka yi nasara za a biya masu
buƙatunsu ta hanyar ba su kwangiloli masu tsoka da kuma sama wa ‘ya’yansu ayyuka
a manyan ma’aikatun gwamnati.
A wani misalin kuma, an nuna wani ɗan siyasa ne wanda ba burinsa
talaka ya mori arziƙin ƙasa ba, kawai dai abin da ya sanya a gaba shi ne yadda zai
yi ya mayar da miliyoyin da ya zuba a matsayin jari lokacin kamfe, kamar yadda marubucin
ya ce:
“ Shi dai abinda kawai
yake a gabansa shi ne ta yaya zai tara miliyoyi ninkin fiye da waɗanda ya zuba jarinsu
a wajen kamfe. Sannan ya zagaya duniya a ahaha.”
(Surajo, 2006: 22).
‘Yan siyasa da dama, musamman na wannan zamanin da muke ciki,
da zarar sun hau kujerar mulki ba talaka ne a gabansu ba. Sukan yi duk yadda za
su yi ne su tara dukiya ko ta halin ƙaƙa, domin dai da ma jari suka sanya ta hanyar
zuba maƙudan kuɗaɗe domin a zaɓe su. Wannan ya sa sukan yi duk yadda za su yi domin
mayar da ninkin abin da suka zuba lokacin yaƙin neman zaɓe, ba tare da mayar da
hankali wajen yi wa al’umma wasu ayyukan cigaba ba.
Wani misalin ya sake fitowa a cikin littafin Da Bazarku inda aka nuna wani babban ɗan
siyasa yana goranta wa waɗanda ya kashe wa kuɗinsa ta hanya zuba jari a kansu kamar
haka:
“Wasun ku rigarsu da wandonsu
ɗaya tal lokacin da muka tsamo su daga talauci muka yi ruwa muka yi tsaki ba siɗi
ba saɗaɗa muka tsai da ku takara. Muka zuba jarin kuɗi muka yi maku kamfe sannan
muka maguɗa muka tsoma ku a cikin tandun ba tare da kun biya ko da sisi ba ”
(Surajo, 2006: 108)
A cikin wannan misalin marubucin ya nuna cewa, da yawa daga cikin
matasan da iyayen gidansu kan ɗauko, su kashe masu kuɗi a siyasa, ba su mallaki
komai ba, hasali ma wasu ko kayan sawa na kirki ba su da shi. Haka sukan tsaya masu
da dukiyarsu su tsayar da su takara. A nan ubangidansu ne ya fito ya bayyana masu
cewa, kuɗin da suka kashe masu a wajen kamfen fa jari suka zuba, wanda kuwa ya zuba
jari yana fatar ƙirga riba ne.
Duk da irin waɗannan abubuwa da ‘yan siyasa sukan yi na zuba
jari don su kwashe riba, akan samu waɗanda ba su ɗauki siyasa a matsayin kasuwanci
ba, sun dai ɗauka cewa wani nauyi ne da mutum kan ɗauka domin ya hidimta wa al’ummarsa.
Dubi wannan misalin:
“To ta wannan manufa na
ɗauki siyasa, saɓanin wacce ake yi a yanzu ta yadda za ka ga mutum ya ɗauki siyasa
a matsayin abin da zai yi amfani da jikinsa ko da kuɗinsa a matsayin jari da zai
sa dan juya su dan cin riba ”
(Isa, 2007: 49).
Wannan ɗan siyasar ya bayyana cewa shi bai ɗauki siyasa hanyar
zuba jari da tara abin duniya ba, kamar yadda wasu suka ɗauka cewa za su zuba jari
ne tamkar yadda ɗan kasuwa zai zuba jarinsa da nufin cin riba ba.
A wata hira da jaridar
Aminiya ta yi da wani tsohon ɗan siyasa
mai suna Alhaji Dauda Ɗangalan[10] ya bayyana damuwa a kan
yadda ake siyasar kuɗi a yanzu. Ga abin da ya ce:
“Ina bakin cikin yadda nake ganin yadda ake sa kudi a siyasar yanzu. Abin
bakin ciki shi ne yadda matasan ‘yan siyasa suke son kudi fiye da kasa da cigabanta.
Idan na tuna cewa waɗannan mutane su ne shugabannin gobe, sai abin ya dame ni. Wane
kasa muke gina wa kan mu haka?”
(Mustapha, 2018).
Wannan ɗan siyasar yana bayyana takaicinsa ne kan yadda ake zuba
kuɗi a cikin siyasa a yanzu, kasancewarsa wanda ya yi
gwagwarmayar siyasa tun daga jamhuriya ta farko, bayaninsa ya nuna, ba a kan wannan
tsarin aka gina siyasar jamhuriyoyin baya ba. Ya nuna cewa wannan ba abu ne mai
kyau ba, domin kamar ana bai wa kuɗi muhimmanci ne fiye da cigaban ƙasa da al’ummarta.
Yawancin kuɗin da ake zubawa ana zuba su ne da tunanin za a samu riba a kansu, wanda
hakan shi ne yake haifar lalacewar al’amura da kuma taɓarɓarewar harkokin ƙasa.
Akan samu inda ‘yan siyasa kan yi yarjejeniya a rubuce cewa,
za su zuba kuɗinsu a yi amfani da su, amma da alƙawari a kan irin muƙaman da za
a naɗa su ko kuma su bayar da waɗanda suke so a naɗa. Wannan ne zai sa su ci gaba
da amfana da gwamnatin ta bayan fage, su kasance su suke juya akalar gwamantin a
ɓoye. Wannan ya fito a cikin wannan misalin:
“Ɗanlami Baba ya gamsu
da bayanan Gwamna Maikaji inda suka yi a rubuce ga muƙaman da za a yi wa tsagin
gwamna Maikaji bayan an ci zaɓe. Naira biliyan ɗaya ya ba shi gudummawa tare da
ba shi tabbacin nan da kwana biyu zai turo wasu jiga-jigan jam’iyyar zuwa tafiyar
Ɗanlami Baba.”
(Aminiya-Trust, 2020: 15).
A nan gwamna ne mai ci
yake yin yarjejeniya da wanda yake so ya gaje shi a wata jam’iyya, kan irin buƙatun
da zai biya masa idan ya goya masa baya ya ci zaɓe, inda ya nuna cewa zai ba shi
gudummawar zunzurutun kuɗi har naira miliyan dubu, amma bisa alƙawarin zai ba da
waɗanda za a naɗa a kan wasu manyan muƙamai a cikin gwamnatin. Yawanci irin waɗannan
idan aka ba su to sai yadda maigidansu ya yi da su. Duk abin da yake so a ma’aikatun
da aka ba su kulawa da su ba za su ƙi yi masa ba. Shi kuma ta nan ne zai kwashe
ribarsa daga jarin da ya zuba lokacin gwagwarmayar neman mulkin.
Irin wannan yanayi na zuba jari a siyasa da nufin samun wani
tagomashi ya kasance wani ɓangare da ya ginu a tarihin siyasa, inda aka samu irin
waɗannan misalai daga cikin rubutattun ayyukan adabi na zuben Hausa.
5.3.7 Siyasar Ubangida
Siyasar ubangida abu ne da ya daɗe da samuwa a cikin siyasar
jam’iyyu. Siyasar ubangida siyasa ce wadda ake yi ƙarƙashin kulawar wani domin a
faranta masa rai ko a saka masa da wani abu da ya yi wa wani ko wasu ‘yan siyasa
ta hanyar bin umarninsa.
Irin wannan siyasar ta samu gindin zama a ƙasar Hausa, ta yadda
wasu ‘yan siyasa da dama suke ganin cewa ba a iya aiwatar da wani abu in babu su.
Su ma yaran gidansu sukan riƙa jin cewa ba za su iya aiwatar da wani abu ba tare
da yardar maigidansu na siyasa ba. Galibi siyasar ubangida takan samo asali ne daga
goyon bayan jam’iyyar wani mai mulki ko yi masa biyayya. Daga bisani bayan wannan
mai mulkin ya sauka kuma yana so ya riƙa faɗa a ji ko kuma a ci gaba da damawa da
shi a fagen siyasar, sai ya samu wani daga cikin waɗanda suka riƙa goya masa baya
a lokacin siyasarsa, ya sanya shi a gaba, ya tabbatar sai an zaɓe shi kan wani muƙami.
Tarihi ya nuna tun a jamhuriya ta farko an ga ɓurɓushin siyasar
ubangida a cikin rubutattun ayyukan adabin na zube da suka samu a wancan lokacin,
inda aka riƙa nuna yaran ‘yan siyasa suna alfahari da iyayen gidansu a siyasance
tare da nuna cewa siyasar ma kacokam domin iyayen gidan nasu suke yin ta. Dubi wannan
misalin:
“ ni karen farautar NPC
na daina sha’anin yaƙin siyasa tun da yake an yi an wanye kuma mun fita kunya tun
da mun kama wa iyayen giji namu zomo goma barewa goma. Ashe ba su kiwata mu a banza
ba. Wasukarnukan kuwa ko fara ba su kamo wa nasu iyayen gidan ba. Sai da kyar wani
tsohon karen farautar ya kama wa nasa ‘yar gafiya, ita ma ɗin sai da iyayen gidan
suka taimaka da sanda.”
(Nadabo, 1960).
Wannan misali ne na siyasar ubangida, domin kuwa mai wannan maganar
yaron gidan ‘yan siyasar NPC ne wanda ya kira kansa da ‘karen farauta’. Ya nuna
cewa, sun kama wa iyayen gidansu na siyasa zomo goma da barewa goma, ma’ana dai
sun taimaki iyayen gidansu sun yi nasara a cikin zaɓuka. Ya yi wa ‘yan hamayya shaguɓe
da cewa, wasu ma ba su iya taimakon iyayen gidan nasu da komai ba. Idan aka duba
za a ga, wannan yana nuni ne da siyasar ubangida a jamhuriya ta farko, duk da cewa
a nan yaran gidan ne suka taimaki iyayen gidansu, kuma suke alfahari da aikin da
suka yi na ƙoƙarin tabbatar da nasarar iyayen gidan nasu.
Baya ga jamhuriya ta farko, a wannan zamanin kaso
mafi tsoka na ‘yan siyasa suna da iyayen gidan da suka jingina da su, waɗanda sukan
tsaya masu kan dukkan al’amuransu, wato suna rawa namansu na jaka. Duk wani abu
da za su aiwatar a siyasance sai da amincewar iyayen gidansu, ko kuma iyayen gidan
nasu ne tun farko suka sanya su. Yawanci irin waɗannan iyayen gidan na siyasa suna
so ne su kasance kullum su ne suke faɗa a ji, kuma sai abin da suka ce za a yi. An samu irin wannan a cikin littafin Tsuntsu Mai Wayo inda aka ce:
“Wannan abu da muka yi maka gaba ɗaya ba a bakin komai yake ba a wajenmu abin da muke so
ka fahimta shi ne duk wani abu da za mu rasa a shirye muke don ganin ka haye tun
daga kan zaɓen gudun-ya-da-ƙanin-wani har ya zuwa zaɓen ƙarshe Saboda haka za mu
yi maka ƙwazo daidai ƙarfinmu, sai dai ka sanya wannan al’amari a zuciyarka ‘yan
shawarwari muhimmai a sako da mu. In mun ga wani abu wanda bai dace ba mu hana ”
(Babinlata, 1993: 22).
A nan idan aka duba, manyan ‘yan siyasa ne suka sanya wanda suke
so su tsayar takara suke faɗa masa cewa za su yi iyaka iyawarsu domin ganin ya samu
damar zama gwamna. Ba kuma wani abu suke nema daga gare shi ba illa biyayya. Duk
wasu shawarwari ya zama da su yake yi, sannan duk abin da zai aiwatar sai da amincewarsu,
domin duk abin da bai dace da ra’ayinsu ba, ba za su bari a aiwatar ba.
A wasu iyayen gida a siyasa sukan yi amfani da ƙarfin faɗa aji
da na tattalin arziƙinsu su ɗora ɗan takara ta hanyar ƙarfa-ƙarfa, wato ko ana so
ko ba a so, kasancewar su suke riƙe da akalar juya dukkan al’amuran da suka shafi
shugabanci. Wannan misalin da yake biye ya zo da irin wannan fasalin:
“ saboda haka muke so
ka bi yarima ka sha kiɗa, mu ba ma buƙatar komai daga gare ka hasali ma mu ne za
mu ba ka duk irin maƙudan kuɗin da kake so domin ka sayi wannan matsayi na shugaban
ƙasa da kake nema, tun da muna sane da cewa jama’ar wannan ƙasa galibin su dai duk
ba son ka suke yi ba.”
(Surajo, 2006: 63).
Ɗan takarar da aka tsayar ne ake nuna masa cewa ya kwantar da
hankalinsa kawai ya yi biyayya, duk abin da yake buƙata na kuɗi za a kashe masa
komai yawansu, kasancewar al’umma ba son sa suke yi ba. Don haka za a yi amfani
da kuɗin ta kowace fuska domin cika burinsu.
A wasu lokutan ‘yan siyasa sukan zama iyayen gidan wasu ne ta
hanyar kafa su, domin wata manufa tasu ta siyasa. Wani muƙami ko kujera suke burin
nema sama da na yaran gidan nasu, sai ya zama zai yi amfani da yaran da ya kafa
don su zame masa tsanin da zai taka ya haye kujerar da yake buri. Irin wannan ya
fito a cikin wannan misalin:
“Sannan ya sake juyawa
ya dubi inda zaɓaɓɓun ‘yan majalisar jiha da shugabannin ƙananan hukomomi da kansilolinsu
suke zaune ya ce, ku kua ga fa babban ƙalubale nan a gabanku, domin lokaci ya yi
da za a rama wa kura aniyarta Alhaji zangina dai kusan ince babu wanda bai ci darajarsa,
gajiyarsa da kuma taimakonsa ba har ya kai ga ga muƙamin da yake kai a yanzu Kun
ga ashe tun da dai ɗan tahalikin nan Alhaji Zangina shi ne ya yi duk wannan hidima
da kuɗin aljihunsa don ganin kun ci gaba, ashe kuwa shi masoyinku ne, ubangidanku
ne na siyasa kuma shi ba ƙashin yarwa ba ne a gare ku har abada.”
(Surajo, 2006: 108).
Alhaji Zangina babban attajiri ne ɗan kasuwa wanda ya yi amfani
da dukiyarsa wajen kakkafa ‘yan siyasa don ya tabbatar sun ci zaɓe. Ya yi amfani
da dukiyarsa ya kafa yaransa na siyasa a matakai a daban-daban na siyasa. Lokacin
da kakar zaɓe ta zagayo sai ya bayyana ƙudurinsa na yin takarar kujerar shugaban
ƙasa. A nan ana nuna wa waɗanda Alhaji zangina ya zama silar samun muƙamansu na
siyasa ne cewa, shi ne ubangidansu, kuma shi ne ya yi masu komai wanda ya zama sanadin
samun ci gabansu. Duk abin da ya yi masu da kuɗin aljihunsa ya yi masu ba tare da
sun ba da ko sisin kwabo ba. Don haka ya kamata su ma su saka masa da abin da ya
yi masu, kuma bai kamata su butulce masa ba. Don haka ya kamata a rama wa kura aniyarta.
A wasu lokuta har iyayen gidan siyasa sukan haɗa da barazanar
cire duk wanda ya bijire masu, tun da suka kafa shi to suna iya tuge shi a duk lokacin
da suka so ba tare da wata wahala ba, kamar yadda wannan misalin da yake biye ya
nuna:
“ ya kamata kowanneku
in sake tuna maku cewa kuma fa kuna son tazarce, sannan kuma ku tuna da wancan lokacin
dai da kuke sa hannuwanku a kan takardun nan na alƙawari ko rantsuwa tsakaninmu
da ku akwai takardu waɗanda ba a rubuta ko ‘A’ ba a kansu, waɗanda kuma kowanne
ɗayanku ya sa hannunsa a kansu. Don haka da ma mu muka yi yadda muka yi muka ɗora
ka a kan muƙaminka saboda haka yadda za mu yi mu wancakalar da kai kamar tuɓe hula
ne a gare mu ”
(Surajo, 2006: 109).
A cikin wannan misalin an nuna wa yaran gidan siyasa ne cewa,
matuƙar suna son tazarce to wajibi ne su goya wa ubangidansu baya. An tuna masu
cewa sun yi alƙawari a rubuce a kan hakan, kuma kowane ɗaya daga cikinsu ya sanya
hannu kan cewa zai yi yadda ake so, idan kuwa ba haka ba sai a tuɓe shi daga muƙaminsa
ko kuma ya kasa cin zaɓe tun da dama su suka ɗora shi don haka in ya bijere masu
za su cire shi cikin sauƙi kamar cire hula.
Siyasar ubangida tana daga cikin abubuwan da suke kawo matsala
a cikin siyasar jam’iyyu domin tana haifar da rashin cigaba a siyasance. Kasancewar
akan samu mutum guda ne wanda ya fi kowa ƙarfin faɗa a ji a cikin jam’iyya ko a
kan wani mai mulki. Alhaji Dauda Ɗangalan ya bayyana haka a hirarsa da jaridar Aminiya. Ga abin
da ya ce:
“Wannan yana faruwa ne idan mutum daya ya
fi karfin kowa a jam’iyya. Shi zai fadi yadda yake so da kuma waɗanda yake so a
ba matsayi da matsayin da za a ba su. Idan aka ce komai na jam’iyya na hannun mutum
daya ne, to lallai akwai matsala babba. Wannan ne ya sa muke cikin matsala a wannan
kasar.”
(Mustapha,
2018).
Alhaji Dauda Ɗangalan[11]
ya bayyana cewa, idan aka samu mutum ɗaya wanda ya fi kowa ƙarfin faɗa a ji a cikin
jam’iyya, wanda shi ne yake tsara komai sai yadda yake so za a yi, idan irin haka
ta kasance to wannan yana haifar da matsala babba ga ƙasa. Yakan yi amfani da ikonsa
ya yanke hukunci ko da kuwa a kan kuskure ne don babu wanda maganarsa take sama
da tasa. Yakan ba da damar aiwatar da wani abu na lamarin tafiyar da ƙasa ko da
kuwa zai iya zama matsala a gaba ko kuma ya hana aiwatar da wani abu don son zuciyarsa
ko da kuwa zai amfani al’umma don raɗin kansa. Irin waɗannan sukan kasance matsala
ga ƙasa da al’umma, domin ba za su bari a yi jagoranci yadda ya dace ba, sai dai
yadda suke so.
Duk wani ubangida a siyasar jam’iyyu ba shi da wani burin da
ya wuce ya faɗa a ji. Duk abin da ya kawo na buƙatarsa, da daɗi, ba daɗi, dole a
karɓe shi haka a yi masa biyayya, a kuma biya masa buƙatarsa. Shi kuwa mai riƙe
da mulkin ya zama ɗan amshin shata a gare shi. Irin wannan misali ya sake bayyana
a cikin littafin Mizani kamar haka:
“Sanin kowa ne mun sake
samun dama na kafa wata gwamantin ban da wadda ta shuɗe, a wannan karon na bayar
da sunayenku domin ci gaba da sarrafa gwamnati kamar yadda aka saba, idan gwamna
ya gama sanar da sunayenku a hukumance, to zan yi ganawar sirri da ku nan take,
domin akwai jhamayyali na ayyukan da na tsara da shi dole za a yi.”
(Mustapha da wasu, 2023: 21).
A nan Alhaji Mudi ne wani hamshaƙin attajiri yake
yin bayani ga yaransa na siyasa da ya ba da sunayensu don a ba su muƙamai bayan
jam’iyyarsu ta samu nasarar kafa gwamnati. A cikin bayaninsa ya nuna cewa ya bayar
da sunayensu ne domin ci gaba da sarrafa gwamnati yadda suka saba. A nan yana nufin
idan ya bayar da sunan yaransa na siyasa, to zai kasance akalar gwamnatin a hannunsa
take, duk kuwa da cewa kai tsaye ba shi ne shugaban ba, ba ya kuma cikin waɗanda
aka naɗa a kan muƙaman, amma dai shi ne ubangidansu baki ɗaya. Ya ƙara da cewa akwai
jhamayyalin ayyukan da ya tsara wanda bayan gwamna ya tabbatar da su, dole waɗannan
ayyukan za a yi. Irin waɗannan iyayen gidan na siyasa, galibi duk abin da suke so
shi ake aiwatarwa. A zahiri za a ga kamar mai riƙe da muƙamin siyasar ne yake aiwatarwa,
amma a gefe guda da umarnin ubangidansa yake aiki.
Irin wannan siyasar ta ubangida tana daga cikin abubuwan da suke
kawo wa siyasar jam’iyyu tarnaƙi, domin kuwa ba da ra’ayin al’umma ake amfani ba,
ana amfani ne da ra’ayin mutum guda ko wasu ‘yan tsirarun mutane, waɗanda ba lallai
ne ya kasance cigaban ƙasa da al’umma ne a gabansu ba.
5.3.8 Amfani da Kuɗi
A cikin tarihin siyasar jam’iyyu kuɗi suna taka muhimmiyar rawa
wajen gudanar da al’amura, kasancewar wasu abubuwan idan babu kuɗi ba za su yiwu
a gudanar da su cikin sauƙi ba. Wasu lokuta, amfani da kuɗi a cikin siyasa yakan
zama illa ta farko da ake yi wa siyasar tun ma kafin a kai ga gudanar da zaɓe da
kuma samar da shugabanni. Sau da dama akan kashe kuɗaɗen da sun wuce hankali ta
yadda ko da ma an zaɓi irin mutanen da suka kashe wannan maƙudan kuɗin za su yi
duk yadda za su yi su mayar da abin da suka kashe ko ta wane hali, wanda hakan yaka
jefa al’umma cikin wani hali maras daɗi.
Tun a farko-farkon siyasar jam’iyyu ne aka fara samun amfani
da kuɗi a cikin siyasa, inda a lokacin zaɓen ‘yan majalisar tarayya da aka gudanar
a 1959 aka ɓarnatar da dukiya da sunan kamfe, kamar yadda wannan misalain ya nuna:
“Kowa dai ya sani jam’iyoyin
da suka yi yaƙin neman zaɓe sun ɓatar da kuɗi masu ɗimbin yawa saboda wannan zaɓe
An yi yaƙin neman zaɓe tun daga kekuna, motoci, babura, har da jirgin sama da ake
kira ‘helicopter’.”
(Abubakar, 1960).
Yaƙin neman zaɓe abu ne wanda yake buƙatar tanadin kuɗaɗe masu
yawa domin gudanarwa, wannan ya sa akan kashe kuɗi sosai ta wannan hanyar kafin
ma a kai ga yin zaɓen. A jamhuriya ta ɗaya ne aka nuna cewa an yi kamfe da jirgin
sama, baya ga motoci da babura da kekuna, wannan ya sa aka kashe kuɗi masu ɗumbin
yawa in ji jaridar Sodangi.
Wani jawabi na Malam Aminu Kano a jamhuriya ta biyu, ya nuna
takaicinsa kan yadda ake amfani da maƙudan kuɗaɗe a cikin siyasa wanda ya nuna cewa
babbar matsala ce ga siyasar demokuraɗiyya, inda ya yi kira ga hukumar zaɓe da ta
sake tunani kan kuɗin da ‘yan siyasa suke kashewa a wajen kamfen. Dubi abin da ya
ce:
“Haka na kuma zan so na
nusasshe da hukumar zaɓe da ta yi tunani a kan kuɗaɗen da ‘yan siyasa suke kashewa
a wajen kamfen a wannan ƙasa. Ana kashe maƙudan kuɗaɗe da dama a wajen yaƙin nemna
zaɓe. Wannan ya sa ‘yan takarkaru suke zuwa yawon kamfen su riƙa kashe kuɗaɗe masu
ɗumbin yawa, wanda a ƙarshe ba komai yake jawowa ba face wanzuwar cin hanci da rashawa
mai yasa za a zuba wa ‘yan takara idanu suna kashe irin waɗannan kuɗaɗe har fam
dubu biyu zuwa dubu uku domin yaƙin neman zaɓe?”
(Jega da wasu, 2002:92).
A cikin wannan jawabin na Malam Aminu Kano ya nuna takaicinsa
ne kan yadda ‘yan siyasa suke amfani da maƙudan kuɗi wajen yaƙin neman zaɓe, inda
ya ja hankalin hukumar zaɓe ta sanya wani tsari da zai ƙayyade abin da aka amince
ɗan takara ya kashe a kowane mataki da yake nema. Ya nuna cewa amfani da kuɗi ba
tare ƙa’ida ba a cikin siyasar jam’iyyu babu abin da yake haifarwa sai ƙaruwar cin
hanci da rashawa.
A cikin littafin Tura Ta
Kai Bango an nuna irin yadda masu kuɗi suke bugun ƙirji wajen nuna ƙarfin arziƙi
a kan talaka da kuma ƙoƙarin sayen ‘yancinsa da ‘yan kuɗin da ba su taka kara ba
balle su karya. Dubi wannan misalin:
“Alhaji ya ce, ‘Tun da
shi Hassan almajiri ne bai mallaki wani abu ba, Naira za ta yi maganinsa’. Zan soma
kiransa in nuna masa wani abu ”
(Katsina, 1983: 32).
A nan an nuna cewa, ba Hassan Wurjanjan kaɗai ba, duk wani talaka
za a iya amfani da kuɗi domin a juya tunaninsa cikin sauƙi. Hakan kuwa ba haka yake
ba, duk da yadda kuɗi suke da tasiri a cikin siyasa akan samu waɗanda kan tsaya
tsayin daka wajen ganin sun kare ‘yancinsu ba tare da an saye su ba, kamar yadda
ya fito a wannan misalin:
“Ka riƙe Naira ɗarinka
na gode. In kana zaton ita za ta sayi ‘yancina da mutuncina, ka yi kuskure. A ɗa
aka haife ni, kuma a ɗa zan mutu ba bawa ba in Allah ya yarda.”
(Katsina, 1983: 34).
A nan Hassan ne yake nuna wa Alhaji Kaukai cewa kuɗinsa ba su
isa su sayi ‘yancinsa ba balle a samu damar danne masa haƙƙinsa, tamkar shi ba ɗa
ne ba. Don haka ya daina tunanin kuɗinsa za su yi amfani wajen juyar masa da ra’ayinsa
a mayar da shi bawa a ƙasar haihuwarsa.
An ci gaba da samun irin waɗannan misalai na amfani da kuɗi a
cikin siyasa a cikin ayyukan adabi na rubutaccen a wurare da dama inda marubuta
suka riƙa fito da shi. Dubi wannan misalin:
“ daga nan sai mu ware
wasu miliyoyi mu tsine musu, mu yi ƙoƙari mu samu magoya baya a cikin jam’iyya,
duk da yaron na da farin jini ”
(Babinlata, 1993: 22).
A cikin wannan misalin an nuna cewa, hanya mafi sauƙi da za a
yi amfani da ita domin samun magoya baya ita ce amfani da kuɗi, inda aka bayyana
cewa za a ware wasu miliyoyi a tsine masu, ma’ana a kashe su ta kowane hali domin
dai a samu magoya baya. Galibi a wannan zamanin siyasar ta jamhuriya ta huɗu irin
salon da ake bi ke nan, inda hatta ‘yan siyasar ba su yi wa al’umma wani aiki mai
muhimmanci da zai taimake su, sun gwammaci su tara kuɗin sai kakar siyasa ta zo
su yi ta watsi da su don su samu su koma kan kujerunsu. Kamar yadda aka gani a cikin
wannan misalin. Ga shi:
Kasancewar ana cikin matsatsi
na rashin isassun kudi da abinci ga jama’a watau talauci ya yi wa talakawa yawa,
sai ɗaya daga cikin iyayen taron ya ba da shawarar cewa a tanadi kudi masu dimbin
yawa. Kada a taba su sai kamar ana gobe zabe, watau daren zaben ke nan. Sai a je
aga masu aikin zaben da jami’an tsaro, dattawan unguwa da kuma duk wanda aka tabbatar
yana da magoya baya a ko’ina cikin fadin jihar don a yi musu alheri.
(Jiƙamshi, 1997: 38)
A nan za a ga yadda akan azabtar da mutane da talauci da gangan
domin a yi amfani da kuɗi domin a ja ra’ayinsu idan lokacin zaɓe ya zo. An nuna
cewa ana fama da talauci a ƙasa ga yunwa, maimakon a yi wani abu na sauƙaƙa wa talaka,
sai aka buƙaci a tanadi kuɗi masu yawa, kuma kada a kashe su sai ana gobe zaɓe;
al’umma sun galabaita, sannan a bi masu aikin zaɓe da jami’an tsaro don duk su ma
cikin al’ummar ƙasar, da dattawan unguwanni da kuma duk wani mai faɗa a ji a siyasance
a rarraba masu, in ya so su kuma za su ɗan guggutsura wa sauran mabiyansu ta yadda
za a iya ciyo kansu don samun ƙuri’unsu. Kusan wannan shi ne halin da ake ciki a
yau.
A yau, da yawa cikin masu mulki har ma da wasu talakawa a yau
sun yi imani cewa, duk wanda ba shi da kuɗi ba zai kai bantensa a cikin siyasa ba.
Wannan ya ƙara haifar da mummunan cin hanci da rashawa da kuma aƙidun jari-hujja
a cikin al’umma, ta yadda idan talaka ne ya samu damar samun madafun iko, zai yi
duk yadda zai yi ya mallaki dukiya ko ta halin ƙaƙa domin ganin ya ɗore a kan wannan
kujerar da ya samu, ta hanyar amfanin da kuɗin da ya tara ko da kuwa al’umma ba
son sa suke yi ba. Haka kuma idan mai kuɗi ne ya samu wannan damar, zai yi amfani
da tsarin jari-hujja domin tabbatar da arziƙinsa ya ƙara haɓaka, shi kuwa talaka
sai dai ya yi ta kukan talauci don irin halin matsin da zai ƙara tsintar kansa a
ciki. A irin wannan yanayi akan samu talakawa masu kishi su riƙa wayar da al’umma
kan illar siyasa don kuɗi, su kuwa masu kuɗin da ma a kan wannan tsarin suka ginu,
sai su riƙa ganin cewa idan kan talaka ya waye to suna cikin barazana, kamar yadda
wannan misalin da ke biye ya nuna:
“ abin kullum yana ƙara
ba ni tsoro, idan ka yi la’akari da cewa ‘yan hamayya fa a kullum sai faman wayar
da kan talakawa suke yi a kan su guji zaɓe don kuɗi. ka kuwa kwan da sanin cewa
idan wanna yekuwa tasu ta samu gindin zama a zukatan talakawa kuwa sai buzunmu ke
nan.”
(Surajo 2006: 46)
A nan an nuna yadda ‘yan hamayya kullum suke ƙara wayar da kan
talakawa ne kan su guji siyasar kuɗi domin su tsira da mutuncinsu a wurin masu mulki.
Su kuwa a ɓangaren masu mulki wannan ba shi ne abin da suke buƙata ba, domin idan
talakawa kansu ya waye a kan wannan kiran da ake masu to kashinsu ya bushe. Za su
bijire masu, kuma wannan zai kawo ƙarshen mulkin dannjiyar da suke wa talaka.
Irin wannan ya ɗore a siyasar Arewacin Nijeriya ta bunƙasa a
jamhuriya ta huɗu, inda aka ci gaba da nuna wa jama’a cewa sai an yi amfani da kuɗi
masu ɗumbin yawa kafin a ci zaɓe, duk wanda bai yi ba ko ba shi da su da wuya ya
kai labari a cikin siyasar. Da wannan aka yaudari matasa kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito a hirarta da alhaji Dauda
Ɗangalan:
“Ina tunanin cewa an yaudari matasan nan ne cewa amfani da kudi a siyasa ba
matsala ba ce, kuma shi kadai ne hanyar da za su iya samun nasara. Ya kamata waɗannan matasan su gane cewa fa su
ne shugabannnin gobe, kuma suna da nauyi mai girma da za su sauke.”
(Mustapha, 2018).
A nan babban ɗan siyasar yana nuna irin matsalar da yake tattare
da amfani da kuɗi ne da ya wuce kima a cikin harkokin siyasa, inda ya nuna cewa
matsala ce babba, domin kuwa zai lalata harkokin siyasa musamman ga matasa masu
tasowa waɗanda aka buɗe masu ido da cewa ita ce hanya ɗaya tilo da ake bi domin
samun nasara.
A wannan jamhuriya da muke cike ne abin ya fi tsanani, musamman
daga bayan mulki Shugaba Umaru Musa ‘Yar’adua, wato daga shekarar 2011 zuwa yau,
domin kuwa yadda ake nuna isa da nuna ƙarfin arziki a cikin siyasa abin ya ƙazanta.
‘Yan siyasa sun san cewa ba cancanta ake dubawa ba wajen fitar da ɗan takara. Wannan
ya sa suke fitar da kuɗi su yi ta facaka da su ga ‘yan siyasa domin samun damar
takara. Dubi abin da jaridar Leadership Hausa
ta ce:
“’Yan Nijeriya musamman
talakan da yake karkara ya ga yadda ‘yan siyasa suka riƙa kece raini da nuna isa
wajen wasa da kuɗaɗe, musamman ma ta yadda kuɗi ne ya zama manuniyar wanda zai zama
ɗan takara a matakai daban-daban a jam’iyyunmu, wato wanda ya fi bayar da kuɗi shi
ne da tabbas na tsayawa takarar da ya shiga ba wai cancanta ba.”
(“Da aka Gama Rarraba wa Deliget Kuɗi”, 2022).
A yau al’umma sun ɗauka cewa duk wanda ba shi da kuɗi ba zai
yi yiwu ya yi siyasa ba. A wannan zamanin ba a duba nagartar mutum ko ƙawarewarsa
a cikin siyasa a matsayin madubi domin auna cancantarsa. Abin da ake dubawa a yau
shi ne ƙarfin tattalin arziƙinsa ko da kuwa arziƙin nasa ba ya amfanar kowa sai
lokacin siyasa. A cikin misalin da aka kawo a sama an bayyana yadda yan siyasa na
wannan zamanin suke amfani da kuɗi ne wajen kece raini a tsakanin junansu lokacin
da suke neman damar takara a wata jam’iyya. Sukan riƙa rabon kuɗi da bushasha da
su domin samun damar tsayar da su takara a matakai daban-daban a cikin jam’iyyun
siyasar ƙasar nan. A wannan zamanin siyasar, komai nagarta da cancantar mutum, matuƙar
ba mai dukiya ne ba, ko ya fito takara da wuya ya kai labari.
Amfani da kuɗi yana haifar da ci baya ƙwarai da gaske a cikin
siyasar jam’iyyu, inda maimakon a yi wa al’umma wasu abubuwan da za su amfane su,
sai a riƙe kuɗin sai lokacin zaɓe a ɗan ba su abin da ba zai kashe masu ƙishi ba,
wanda hakan zai sa masu mulki su ci gaba da yin rub da ciki a kan dukiyar ƙasa,
a bar talakawa cikin damuwa har zuwa lokacin da wani zaɓen zai kewayo.
5.3.9 Amfani Da Malaman
Addini
Tarihi ya nuna cewa, ko da aka samu ɓullar siyasar jam’iyyu a
Arewacin Nijeriya ba a bar malamai a baya ba, inda aka nuna cewa sun shiga siyasar
wancan lokacin, kuma ko da suka tashi shiga siyasar sun shiga jam’iyyar NPC ne.
A jamhuriya ta ɗaya, ‘yan
hamayya sun riƙa zargin cewa, malamai sun haɗa kai da jam’iyyar NPC mai mulki suna
yaƙar jam’iyyun hamayya, inda suke ganin cewa malamai sun bar aikinsu na faɗar gaskiya,
sun koma faɗar abin da zai daɗaɗa wa masu mulki da jam’iyyarsu rai. Alal misali,
a cikin wata wasiƙa da aka buga cikin jaridar Sodangi wadda aka yi wa Ɗanjani Haɗeja martani kan zargin da ya yi a
kan wasu malamai waɗanda ya ce suna haɗa kai da jam’iyyar NPC, ya yi wa wasiƙarsa
suna da: “Tambayoyi ga Malaman Npcin Kano”. A ciki Ɗanjani ya zargi malaman Kano
irin su Malam Nasiru Kabara da Malam Tijjani Na ‘Yammota da kuma Malam Shehu Maihula
cewa sun kafirta ‘yan NEPU. An yi masa martani da cewa:
“Ba kafirta ‘yan NEPU
ake ba. duk wanda ya aikata aikin kafirci ya kafirta ko ɗan wane ne me ya sa ba
su yin umarni da bin na gaba a yanzu ko sai lokacin zaɓe ya matso? Umarni da bin
na gaba aya ce ta Alƙur’anin Ubangiji ba ƙirƙirar Malaman ba ne.”
(Usman, 1960).
Idan aka dubi misalin
da yake sama za a ga cewa, malaman suna amfani da ayoyin Alƙur’ani da suka yi umarni
da a bi shugabanni, kuma duk wanda ya bijire sai su ce ya saɓa umarnin Allah don
haka ya kafirta. Alal misali, sun yi amfani da ayar nan ta cikin Suratun Nisa’i
aya ta 59 domin su karkato hankalin talakawa su yi wa shugabanni biyayya kamar yadda
Allah ya faɗa. A nan an yi wa Ɗanjani Haɗeja martani cewa, su ‘yan NEPU ba su yin
umarni da bin na gaba sai zaɓe ya matso, inda sukan riƙa yin kira da a bi shugabannin
jam’iyya a lokacin zaɓe domin jam’iyyarsu ta yi nasara. Wato ba su yin umarni da
yi wa shugabanni biyayya a lokacin da suke kan shugabanci domin ba jam’iyyarsu ce
take mulki ba.
Su kuwa ‘yan hamayya na
jam’iyyar NEPU sai suke ganin cewa ai ana amfani ne da ayar ba a inda ta dace ba,
sai don kawai a danne talakawa. A cewar Ɗanjani Haɗeja ai ba irin shugabannin da
aka ce a yi wa biyayya ba ke nan. Dubi abin da ya ce a cikin wata wasiƙarsa da aka
buga a cikin jaridar Daily Comet:
“Wurin da ka ce “bin na gaba”, wannan aya ce, ba su
ne suka saukar da ita ba. Ko Malam Shehu bai san bin na gaban da Allah yake nufi
ba ne? Su waɗanda Allah ya ce a bi su, su na gaban waɗanda za su yi umarni ga kyakkyawan
aiki, su yi hani ga barin mummunan aiki, ba cewa ake yi a bi sarki, Koguna ko Sardauna
kurun ba. Sai in za su yi umarni a bi dukkan abin da Allah ya ce a yi. Ko kana nufin
mu bi malamai, su bi Sarki da Sardauna, su kuma Sarki da Sardauna, su bi Turawa?”
(Ɗanjani, 1960).
Wannan martanin da Ɗanjani
ya mayar yana nuni ne da cewa ‘bin na gaba bin Allah’ da aka cewa ayar Alƙur’ani
ce, kuma su malaman ba su ne suka saukar da ita ba. Ya ƙalubalanci ɗaya daga cikin
malaman da ya ce sun kafirta ‘yan NEPU cewa, ko bai san bin na gaban da Allah yake
nufi a cikin ayar ba ne? Ya ce ai su na gaban da Allah ya ce a bi su, su ne waɗanda
suke yin umarni da kyakkaywan aiki, kuma su yi hani da mummunan aiki. Ba cewa aka
yi a bi Sarki ko Koguna[12] ko Sardauna kawai
ba, sai dai in su ɗin za su yi umarni ne da dukkan abin da Allah ya ce a yi da kuma
hani da abin da Allah ya hana. A cikin bayanin ya ƙara da cewa, ba ana nufin a bi
malamai ne su kuma su bi Sarki, Sarki kuma ya bi Sardauna, sannan Sardauna ya bi
Turawa ba.
Kasancewar malamai a cikin fagen siyasa ne ya sanya tun a wancan
lokacin suka fara samun turjiya daga mabiyansu, inda har sukan faɗi magana talakawa
su bijire masu, domin a ganin talakawan tamkar haɗin baki ne tsakanin malamai da
masu mulki domin a ci gaba da danne talakawa. Wannan ne ya sa har a wancan lokacin
aka fara yin kiraye-kiraye a cikin jaridu kan cewa malamai su tsame hannunsu a cikin
siyasa domin zai iya taɓa mutuncinsu. Dubi wannan misalin:
“ dan allah ina son ka
jawo mana hankalin malaman sunna na kasan nan jihar Arewa su daina yarda wasu mutane
na shigar da su cikin al’amuran da babu ruwansu kamar harkokin siya sa dan kawai
a araba su da almajiransu, kan sha’anin duniya. Su malamai an so su sanya baki amma
kan abin da ya shafi addinin musulunci ”
(Isa,
1961).
Ganin yadda malamai suka
shiga siyasar ne ya sa aka fara samun bambancin ra’ayi tsakaninsu da almajiransu,
domin akan samu malami ɗan NPC, amma almajirinsa ɗan NEPU. Wannan yakan haifar da
musayar ra’ayi tsakaninsu wanda kan haifar da rabuwa, tun da ba zai yiwu su zauna
inuwa ɗaya kowa ya yi ra’ayinsa ba a wancan lokacin. Wannan ya sa aka fara samun
kiraye-kiraye da jan hankali ga malamai a cikin jaridu domin su kiyayi shiga siyasa,
su tsaya ga sha’anin karantarwa da bayani a kan al’amuran addini domin su tsira
da mutuncinsu.
Sau da dama, har yaƙin neman zaɓe akan tafi tare da malamai musamman
a jamhuriya ta huɗu da muke ciki, inda za a tara malamai suna hawa kan mumbarin
siyasa suna yi wa ‘yan siyasar addu’o’i, a wasu lokutan ma har da yi wa abokan hamayya
addu’ar rashin nasara. Irin wannan misali ya fito a cikin littafin Tura Ta Kai Bango kamar haka:
“Alhaji Kaukai ya umarci
ɗaya daga cikin malaman garinsu da ya halarci wurin da cewa ai sai ya yi addu’a.
Ya yi fatan alheri ga wannan jam’iyya da masu goyon bayanta. Ya yi fatan bala’i
ga ɗaya jam’iyyar da suke jin sunanta ta ‘yan iska da magoya bayanta ”
(Katsina, 1983: 7).
A wannan misalin an ga yadda ‘yan siyasa suke amfani da malaman
addini a wajen yaƙin neman zaɓe, inda aka nuna Alhaji Kaukai ya umarci wani malami
da ya halarci taron da ya yi masu addu’a, inda ya yi kyakkyawar addu’a da fatan
alheri ga jam’iyyar Riƙau ta su Alhaji Kaukai, sannan ya kausasa harshe da kuma
yi wa jam’iyyar hamayya mummunar fata.
Idan aka dubi wannan misalin za a ga cewa, misali ne na yadda
aka shigar da malamai cikin siyasa a jamhuriya ta biyu, yadda sukan riƙa sukar salon
wasu jam’iyyu a mimbarin huɗubobi, daga bisani a saka masu da kujerun hajjin har
ma da manyan muƙaman siyasa a cikin gwamnati.
A jamhuriya ta huɗu an samu lokacin da su malaman da kansu sukan
ɗaure wa ɗan takara gindi har su riƙa bi suna nema masa alfarmar wata kujera ko
kuma a tsayar da shi takara a wata jam’iyya. A irin wannan yanayi malaman ba su
damu da ko ta wace hanya ce ɗan takarar zai samu kujerar ba. Su dai abin da suke
buƙata kawai shi ne, a ɗora masu wanda suka kawo ko ta wace hanya ce. Irin wannan
misalin ya fito a cikin littafin Tuwon Ƙaya
kamar haka:
“Ai Musa ba godiya za
ka mini ba, ni ma da buƙatata, sai ka kwantar da hankalinka ka ji To ɗana Ali yana
son tsayawa kansila, sai kai ma ka yi mana rana wajen ciyaman ɗin mu da jama’armu,
za ka ci gaba da ganin hannuna.”
(Majid, 2004: 16).
A nan liman ne ya yi amfani da taimakon da ya yi wa Musa, ya
miƙa buƙatarsa ta neman a tsayar da ɗansa Ali a matsayin kansila na mazaɓarsu. Liman
ya ambaci cewa, Musa ya yi masu rana a wajen maigidansa ciyaman na ƙaramar hukuma
da jama’arsu. Ma’ana dai a ba wa ɗansa kujerar kansila tun da suna da manya a sama.
Musa yaron gidan ciyaman ne na siyasa. Don haka zai iya amfani da kusancinsa da
ciyaman a bai wa ɗan Liman ɗin kujerar kansila.
Idan aka duba za a ga
cewa, Liman malami ne wanda ya kamata ya duba cewa, sai ɗansa ya cancanta sannan
za a ba shi kujerar takara. Kuma ko da ya yi takarar sai al’umma sun gamsu da yanayinsa
sannan za su zaɓe shi, amma a nan ya nuna a yi amfani da ƙarfin iko da sanayya a
bai wa ɗansa kujerar.
Haka kuma irin abubuwan da ‘yan siyasa sukan shirya wa malaman
wanda yake kama da toshiyar baki domin su yi kira ga al’umma kan zaɓe ko harkokin
siyasa ko kuma a wasu lokuta ma su ayyana ɗan takarar da ya kamata a zaɓa, wannan
kan sa malaman su kasa jan hankalin gwamnati idan an yi ba daidai ba. Dubi wannan
misali:
“A halin yanzu a kowace
ƙaramar hukuma da take a ƙasar nan mun ɗauki sunan malamai biyu da kuma pasto biyu
waɗanda tuni mun biya masu kujeru don su je su sauke farali kuma su yo ziyara a
ƙasashen Saudiyya da kuma Isra’ila.”
(Surajo, 2006: 106).
A nan an nuna yadda ‘yan siyasa kan riƙa biya wa malamai kuɗin
zuwa aikin hajji da umra domin a yi masu addu’a, a wasu lokutan ma har da waɗanda
ba musulmi ba an riƙa biya masu domin su je ziyara ƙasar Isra’ila duk don a yi amfani
da su a matsayinsu na shugabannin addini su ja hankalin mabiya don su zaɓi wani
ko wata jam’iyya. Haka kuma, sukan riƙa kai taimako don gina masallatai da coci-coci
musamman a lokacin da zaɓe ya ƙarato domin samun goyon bayan mabiya, kamar yadda
wannan marubucin ya bayyana:
“Har walau kuma mun aika
da gudunmawa ta kuɗi da kuma kayan aiki da sunan ɗan takararmu ya zuwa wasu gine-gine
na masallatai da coci-coci da ake yi a faɗin ƙasar nan.
(Surajo, 2006: 107).
Idan aka duba irin waɗannan wuraren ibada da ‘yan siyasa sukan
riƙa kai taimako ko su gina, sukan kasance ƙarƙashin jagorancin malaman addini ne.
Waɗannan malaman su ne ake biyowa ta hannunsu domin bayar da taimakon, ta yadda
aƙalla za a ambaci sunan ɗan siyasa a ce a yi masa addu’a, don shi ne ya bayar da
taimako kaza don yin aiki kaza.
Wasu malamai suna ganin cewa al’umma ba su fahimci wasu abubuwa
dangane da matsayin malamai a cikin siyasa ba, amma kuma sun yarda da duk wani abu
da malamai za su faɗa dangane da abin da ya shafi al’amuran duniya da lahira, sai
shugabancin siyasa ne kawai suke ganin malamai bai dace su shiga ba. Dubi abin da
jaridar Leadership Hausa ta ruwaito bayan
tattaunawarta da wani malamin addinin Musulunci:
“Dakta Ahmad Tijjani Sani
Sa’ad wanda aka sani da al’Azhari, ya bayyana rashin gamsuwarsa da ra’ayoyin al’umma
kan cewa malamai su tsame hannunsu a cikin harkokin siyasa saboda matsalolin da
ake samu a fagen siyasar Nijeriya ya nuna cewa, duk wanda ke cewa bai kamata malami
ya shiga harkokin siyasa ba to bai san wane ne malami da kuma irin ayyukan da Allah
ya ɗora masu a kan al’umma. Ya nuna matuƙar damuwarsa na yadda al’umma sun yadda
da malamai a duk wani abu da ya shafi duniya , amma sai aka wayi gari ana nuna cewa
bai dace a saurari malamai ga al’amuran da suka shafi shugabanci da ya shafi siyasa.”
(Abdullahi, 2022).
A nan malamin yana ganin cewa irin fahimtar da al’umma suka yi
wa malamai dangane da shiga harkokin siyasa ba daidai ba ne, domin kuwa dukkan wasu
al’amura na rayuwa an yarda malamai su shiga, amma siyasa ce kawai jama’a suke nuna
cewa ya kamata malamai su tsame hannunsu daga shigar ta. A fahimtarsa malamai ne
ya kamata ma su shiga siyasa domin yana cikin ayyukan da Allah ya ɗora a kansu na
shugabancin mutane. Don haka yana ganin cewa ya kamata malamai su shiga siyasa maimakon
ƙaurace mata.
Ba wani abu ne ya sa al’umma suke ganin cewa hatsari ne shigar
malamai siyasa ba, illa ganin yadda tsarin dimokuraɗiyya yake, wanda ya yi hannun
riga da shari’ar Musulunci, kuma mafi akasarin al’ummar ƙasar Hausa Musulmai ne.
Akwai abubuwa da dama waɗanda malamai za su iya nusar da shugabanni idan ba su shiga
cikin siyasa ba, amma idan suka shiga cikinta da wuya su iya magana kan wani abu
da ake yi wanda ba daidai ne ba, ko da ma sun yi maganar za a ga cewa ai duk bakinsu
ɗaya ne domin su ma suna cikin siyasar.
Irin wannan ya ci gaba
da bayyana a cikin rubutaccen adabin Hausa inda ake nuna yadda ake amfani da malamai
a cikin siyasa domin samun tagomashi daga al’umma. Akan yi amfani da su domin samun
cin zaɓe tare da manyan alƙawura, kamar yadda ya fito a cikin littafin Dambarwar Siyasa kamar haka:
“Malam kamar yadda ka sani babu wani abu da yake
tafiya a yankin namu sai da malaman addini. To na gayyato ka cikin tafiyar nan tawa
ce saboda ka zamo malamina, duk wani abu da ya shafi addu’a nasiha da shawarwari
kan addini, kai ne. Amma malam ina so ya zamo duk wani abu da za a yi na ci zaɓen
gwamna a jihar nan a yi. Sannan idan an hau mimbarin karatu, ko a taƙaice ne a dinga
nusar da jama’a su zaɓe mu. Allah gafarta malam, idan muka ci zaɓe akwai tanadin
kujerun hajji da umra kai da almajiranka duk shekara. Sannan akwai muƙami na musamman
da za a bayar.”
(Aminiya-Trust, 2020: 125).
A cikin wannan misalin za a ga yadda ɗan takarar gwamna ya gayyaci
malami zuwa gidansa, inda suka tattauna ya kuma nuna masa muhimmancin malamai a
cikin dukkan al’amura, sannan ya buƙaci yin tafiya da malamin a matsayin malaminsa
wanda zai riƙa ba shi shawarwari da suka shafi addini da nasiha. Daga nan sai ya
fito masa da manufarsa cewa, duk abin da za a yi a matsayinsa na malami don a ci
zaɓe a yi, kuma a riƙa samun lokaci ko a taƙaice ne a riƙa tallata shi a mimbarin
wa’azi don jama’a su zaɓe shi. Shi kuma idan aka masa wannan aka kuma yi nasara
to zai saka masa da kujerun hajji shi da almajiransa, kuma za a ba shi muƙami a
gwamnatance domin a ci gaba da damawa da shi a cikin gwamnati.
Irin waɗannan abubuwa da ba daidai ba da ‘yan siyasa sukan riƙa
sanya malamai suna yi, ko kuma malaman su tsunduma da kansu, ba su iya jan hankalin
‘yan siyasar a kan su aikata abubuwa na daidai, suna daga cikin abubuwan da suke
kawo wa siyasar jam’iyyu koma baya, musamman idan aka yi batun samar da cigaban
al’umma. Wannan ya sa ‘yan siyasa sukan yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin sun haɗa kai
da malaman addini domin samun damar lashe zaɓuɓɓuka.
5.3.10 Barazana Ga Ma’aikatan
Gwamnati
Ma’aikacin gwamnati a kodayaushe yana ƙarƙashin
‘yan siyasa ne, domin kuwa su ne suke juya akalar gwamnatin da yake aiki a ƙarƙashinta.
A kowane lokaci yana cikin bin umarnin gwamnati a kan aikinsa domin kada ya saɓa
wa doka. Haka kuma, ‘yan siyasa su ne shugabannin al’umma a matakai daban-daban
waɗanda alhakin kula da jin daɗi da walwalar ma’aikata da kuma ba su haƙƙoƙinsu
yake hannunsu.
Sau da yawa ma’aikatan gwamnati sukan bi jam’iyyar gwamnati ne
ba don komai ba sai don tsoron sharri. Idan aka samu labarin wani ma’aikaci yana
hamayya da gwamnatin da yake wa aiki, to zai iya fuskantar barazana a kan aikinsa.
Tarihi ya nuna irin wannan ya riƙa faruwa tun a jamhuriya ta farko, inda da farko
aka haramta wa ma’aikatan gwamnati shiga siyasa in ba jam’iyyar gwamnati zai yi
ba. A jamhuriya ta biyu ma an ci gaba da yi wa ma’aikatan gwamnati irin wannan barazanar,
inda har aka riƙa nuna cewa, duk ma’aikacin gwamnatin da aka kama yana goyon bayan
wata jam’iyyar siyasa zai yaba wa aya zaƙinta. Dubi wannan misalin:
“ duk ma’aikacin da ya
yarda ya kutsa kansa a hakokin siyasa, kuma ya nuna a fili, wannan kurum ya isa
ya sa a kawar da shi daga muƙamin da yake kai.”
(“Zargin da NPN Ke Wa Gwamna Rimi”, 1980).
Wannan bayanin alama ce da ke nuna irin halin da ma’aikatan gwamnati
a ƙasar Hausa suka shiga dangane da al’amuran siyasa a jamhuriya ta biyu. Idan aka
duba za a ga cewa barazana ce ake masu da cewa, idan suka nuna ra’ayin da suke yi
a siyasa za su iya rasa kujerunsu. Irin wannan barazanar gwamnati ce takan riƙa
yi wa ma’aikatan da suke goyon bayan wata jam’iyyar daban ba ta gwamnatin ba.
Sau da dama, ma’aikatan gwamnati sukan shiga siyasa a dama da
su ba tare da wata barazana ba, amma sai dai ya kasance ba hamayya da gwamnati suke
yi ba. Irin wannan ya bayyana a cikin jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta shekarar 1983, inda jam’iyyar NPP ta soki jam’iyyar
NPN mai mulki da zura ido ga ma’aikatan gwamnati suna tsoma kansu a cikin lamuran
siyasa. Dubi abin da jaridar ta ce:
“A kwanan baya ne jam’iyyar
NPP ta yi kakkausar suka game da yadda ma’aikatan gwamnati ke tsunduma kansu cikin
siyasa ba tare da yin la’akari da dokar da ta hana musu yin hakan ba in da ya kasance
mutanen NPP ko UPN ko NAP ko PRP ko GNPP ne ke shiga cikin harkokin siyasa, kuma
suka kasance ma’aikatan gwamnati ne, da tuni NPN ta ɗauki mataki a game da su.”
(Gusau, 1983).
A nan jam’iyyar hamayya ta NPP ce ta zargi jam’iyya mai mulki
da NPN da zura wa ma’aikata ido suna shiga al’amuran siyasa ba tare da ta tsawatar
masu ko ta ɗauki wani mataki a kansu ba. A cikin misalin da ke sama an nuna cewa,
kasancewar ma’aikatan magoya bayan jam’iyya mai mulki ta NPN ne ya sa aka zura masu
ido. Da sun kasance ‘ya’yan wata jam’iyya ce ta hamayya da an ɗauki mataki a kansu.
Ke nan,idan aka samu ba jam’iyyar gwamnati ma’aikaci yake goyon baya ba, za a iya
kiran sa a ja masa kunne haɗe da barazana da tsoratarwa.
Irin wannan ya riƙa bayyana a cikin ayyukan adabin Hausa musamman
na rubutaccen zube, kamar yadda ya bayyana a wannan misalin:
Gaskiya ne mai martaba
ya bukaci ganinka saboda garin tone-tonenka, kana neman wukar yanka kanka… Tuba nake ranka ya daɗe” Farfesa ya faɗa
yana mai sunkuyar da kansa kasa… Ai tuni Sarki ya gafarta
maka ba don haka ba Mhm!
Abin da
muke so da kai ka sani shi ne, Baffa Madugu yaro ne mai ladabi da biyayya, wanda
ya kai mu kira shi dan gidan nan. To zagin ɗan gidan nan ko tozarta shi, zagin gidan
nan ne, kuma tozarta gidan nan ne. Wanda ya zagi gidan ko mu ya zaga. Bugu da ƙari
Senata Baffa Madugu shi ne dan takararmu na shugabancin wannan ƙasa a zabe mai zuwa.
Don haka ba za mu bari a bata masa suna ba, don kuwa hakan zai iya sawa ya yi bakin
jini a wajen jama’a. Saboda haka muna so ka aku da kanka daga kansa shi da jama’arsa.
(Marubutan Mace Mutum, 2014: 153).
A wannan misalin an nuna yadda akan yi wa ma’aikatan gwamnati
ne barazana musamman idan ba su bi abin da shugabannin gwamnatin suke so ba komai
muninsa. Akan nuna wa ma’aikata cewa za su rasa ayyukansu ko a dakatar da albashinsu
ko wani abu na ƙuntatawa. Irin wannan kan sa ko dai ma’aikaci ya yi wa bakinsa linzami
ko kuma a ɗauki irin wannan matakin a kansa. A cikin wannan misalin, marubucin ya
bayyana Farfesa Ɗalhatu a matsayin mutum mai ƙoƙarin tsare gaskiya, kuma shi ne
shugaban kwamitin binciken almundahana da kuɗaɗen rarar man fetur, inda yake bincike
kan wata almundahana da ta haɗa har da ɗan takarar shugaban ƙasa wanda gwamnati
take goya wa baya, wato Sanata Madugu. An so ya janye binciken da yake yi wa ɗan
takarar gwamnatin, amma ya dage, sai aka haɗa shi da fadar sarki, aka yi masa barazana
da cewa in ya ci gaba da binciken za su sanya ƙafar wando ɗaya da shi, kamar yadda
fada ta faɗa masa. Ke nan zai iya rasa aikinsa baki ɗaya don Sanata Madugu ya tsira
da takararsa.
Haka kuma, akan sanya ido a kan ma’aikatan gwamanti a ga wa za
su zaɓa, domin idan suka yi kuskuren zaɓen wanda ba shi gwamnati take so ba, to
aikinsa na iya shiga cikin garari, domin za su iya rasa shi, kamar yadda aka nuna
a ƙarshen wannan misalin kamar haka:
“Al’umma duk suna fatar saukan Alhaji Lado wanda
ya hau mulki ta hanyar sayen ƙuri’un talakawa da kuɗi, sai dai kuma hakan abu ne
mai wuya domin yanzu ya zama ƙadanagaren bakin tulu, domin ko ba za a zaɓe shi ba
da yiwuwar ya lashe zaɓen domin ɗan jam’iyyar da take mulki ne, kuma yana da iyayen
gida waɗanda suka ƙware wajen tafka maguɗi. Don haka dole ma’aikatan gwamnati su
zaɓe shi ko domin su tsira da ayyukansu.
(Aminiya-Trust, 2020: 85).
A wannan misalin an nuna cewa ɗan takarar yana neman wa’adi na
biyu ne, kuma da yiwuwar ya lashe zaɓen duk da cewa al’umma ba daɗinsa suke ji ba,
yana dai taƙama ne da iyayen gida da suka ƙware wajen maguɗin zaɓe. Wannan ne ya
sa ma’aikata za su zaɓe shi don dole ba don suna so ba, sai don su tsira da ayyukansu.
Ke nan, ɗan takarar barazana ce ga duk ma’aikacin da bai zaɓe shi ba in ya kasance
shi ne ya yi nasara.
A wani misalin na daban an nuna yadda aka sallami ma’aikacin
gwamnati a bakin aikinsa bayan ya gudanar da wani shiri a gidan radiyo, inda ya
ja hankalin gwamnati kan ta waiwayi talaka, ta dubi halin da yake ciki. Ga misalin:
“Bayan Zulaihat ta tafi
jami’a aka sallami Al-mustapha daga aiki a sakamakon wani shiri da ya gabatar, wanda
ya yi kira ga gwamnati ta waiwayi talakawa domin sun gaji da gafara sa ba su ga
ƙaho ba.”
(Aminiya-Trust, 2020: 83).
A cikin wannan misalin za a ga yadda aka kori wannan ɗan jaridar
da ya gabatar da shiri a gidan rediyo kan rashin cika alƙawarin gwamnati ga talakawa,
kasancewar an daɗe ana yi masu alƙawura ba a cikawa, maimakon a ɗauki matakin gyara
wannan matsalar sai aka ɗauki matakin korarsa. Idan aka dubi wannan za a ga cewa
barazana ce da tsoratarwa da kuma darasi ga sauran ma’aikatan gwamnati ‘yan’uwansa,
ta yadda ba za su iya fitowa su yi abin da ya dace ba don gudun ɓata wa gwamnati
rai da kuma matakin da za a iya ɗauka a kansu.
Irin wannan barazanar da ake wa ma’aikatan gwamnati yana haifar
da ci baya ga siyasar jam’iyyu da al’umma da ma ƙasa baki ɗaya. An sa ma’aikaci
ba shi da ‘yancin yin abin da yake ganin shi ne daidai wanda kuma doka ta tanadar,
sai abin da ‘yan siyasa da masu riƙe da madafun iko suka amince da shi ko da kuwa
ba shi ne daidai ba.
5.3.11 Fankama
A siyasance kuwa kalmar fankama tana nufin nuna isa da girman
kai da kuma almubazaranci da dukiyar ƙasa wadda ‘yan siyasa sukan riƙa yi wa dukiyar
ƙasa kisan gilla ba tare da lissafi ba. A cikin tarihin siyasar jam’iyyu an riƙa
samun ‘yan siyasa da irin wannan fankamar, ta yadda sukan bambance kansu da talakawan
da suka zaɓe su. ‘Yan siyasa masu riƙe da madafun iko su ne suke juya akalar taskar
arziƙin ƙasa, sai ya kasance suna yin yadda suka so cikin nuna isa ba tare da la’akari
da halin da talaka yake ciki ba. Masu mulki sukan riƙa amfani da dukiyar ƙasa wajen
yin rayuwa ta kece raini da tsere wa tsara, ta hanyar sayen motoci masu tsadar gaske
da gina manyan gidaje na alfarma da ware wurin zama a unguwanninsu daban da na talakawa
da dai sauransu. Irin waɗannan misalai na fankama sun fito a ciki ayyukan rubutaccen
adabi na zube tun daga jamhuriya ta ɗaya da ta biyu har zuwa wannan jamhuriya ta
huɗu da ake ciki. Alal misali, talakawa sun sha yin ƙorafi kan yadda masu mulki
sukan riƙa fankama da kuɗin asusun ƙasa, inda suka riƙa nuna cewa yin hakan ba daidai
ba ne. Ga misali:
“ Kuma wace aya ce ta ce wasu sarakuna su sayi
motoci da kuɗin talakawa?”
(“Addinin Musulunci A Mazahabar Maliki”, 1960).
A wannan misalin an nuna masu mulki suna amfani da dukiyar ƙasa domin sama wa
kansu kayayyakin jin daɗi da more rayuwa ba tare da tunawa da halin da talaka yake
ciki ba, duk da a wannan misalin an ɗora ƙorafin a kan sarakuna ne, amma idan aka
duba za a ga cewa sarakunan su ne suka riƙa riƙe muƙaman siyasa a jamhuriya ta ɗaya.
Ke nan ba abin mamaki ba ne idan aka ce sun riƙa amfani da kuɗin talakawa suna saya
wa kansu motocin na alfarma.
Talakawa ‘yan hamayya suna ganin cewa, abin da ‘yan siyasa suke yi na ɓarnata
dukiyar al’umma domin jin daɗin kansu kaɗai ba daidai ba ne, jam’iyya mai mulki
tana ganin cewa ai hamayyar siyasa ce, kamar yadda jam’iyyar NPC ta mayar wa da
‘yan NEPU martani kamar haka:
“ domin wai mutanen NPC
ba su kula da talakawa, wai suna shiga motoci da zama a gidaje masu kyau shi Awolowo
wanda ya saye ku kuka sai da mutuncinku, kuke nema ku sayar da mutuncin jama’a wai
shin ka ga irin motar da yake shiga ko ta ministocinsa?”
(Sheshe, 1960).
A kodayaushe NEPU suna
ƙorafin NPC ba ta kulawa da talaka, amma suna amfanin da dukiyar ƙasa wajen saya
wa kansu motoci na alfarma da kuma gina manyan gidaje. A ganin NEPU hakan bai dace
ba, domin talaka shi ya fi kamata a mayar da hankali a kansa domin arziƙin ƙasarsa
ne, kuma da ƙarfinsa ake gina tattalin arziƙin. Su kuwa ‘yan jam’iyyar NPC sai suka
mayar da martani cewa, ai Awolowo ma da NEPU take son yin ƙawance da jam’iyyarsa
shi ma irin wannan motar yake hawa shi da ministocinsa. Don haka wannan hassada
ce kawai da jin zafin masu arziƙi NEPU take nunawa.
A jamhuriya ta biyu, bayan jam’iyyar PRP ta yi nasarar lashe
kujerun Gwamna a jihohin Kano da Kaduna an samu raba gari tsakanin Malam Aminu Kano
da gwamnonin guda biyu, inda jam’iyyar ta rabu zuwa gida biyu: ‘Yan Santsi ɓangaren
su Gwamna Rimi da Balarabe Musa, sai kuma ‘Yan Taɓo ɓangaren su Malam Aminu Kano.
Daga cikin abin da ya kawo rabuwar da suka yi akwai batun fankama da sharholiya
da dukiyar al’umma, inda malam Aminu ya ja hankalinsu da cewa lokacin jin daɗi bai
yi ba, ya kamata su tsaya su mayar da hankali ne wajen gina talaka maimakon tunanin
jin jin daɗi.[13] Wannan misalin da aka
ciro daga cikin jawabin Malam Aminu Kano ya ɗan hasko wannan batu a kaikaice:
“ ba ɗaya daga cikin mutane
waɗanda ba masu gaskiya ba ne, waɗanda suka shiga ofis nan da nan sai suka fara
shagala suka juya wa jama’a baya suka yi watsi da su. Waɗannan mutane mayaudara
ne na haƙiƙa, kuma abin baƙin ciki ne da koma-baya a wurinmu. Allah da ikonsa ya
sa mun fahimci cewa gaggawa ɓarna ce, yanzu nan da shekara ɗaya ke nan za a sake
zaɓe. Dole mu ɓata lokaci wajen zaɓen ɗan takara, sai mun tabbatar da amanar masu
neman kujeru. Wannan yunƙurin rusa Kano sai mun dakatar da shi ta kowane hali. Duk
waɗanda aka zaɓe sai sun fi bayar da fifiko ga mutanensu sama da buƙatunsu.”
(Jega da Wasu 2002: 49).
A cikin wannan jawabin yana nuna cewa, a wannan ranar babu wani
ɗaya daga cikin ‘yan santsi a wajen wannan taro, waɗanda daga hawar su mulki suka
shagala da batun talakawa, suka kama harkar gabansu da dukiyar al’umma wanda hakan
ba zai haifar wa da al’umma cigaba ba sai dai koma-baya. Ya ci gaba da nuna wa jama’a
cewa ga shi lokacin zaɓe ya kusa, su tashi su tseratar da al’ummarsu ta hanyar zaɓen
mutanen kirki domin tseratar da jiharsu daga rushewa. Wajibi ne duk wanda aka zaɓa
ya fi mayar da hankali kan al’umma maimakon kansa da jin daɗinsa.
Irin waɗannan misalai na fankama a cikin tarihin siyasar jam’iyyu
sun ci gaba da bayyana a cikin ƙagaggun labarai musamman na jamhuriya ta huɗu. Wani
misali dangane da fankama a cikin siyasa shi ne, yadda ‘yan siyasa sukan riƙa kwasar
dukiyar ƙasa su riƙa gudanar da wasu al’amura da suka shafe su su kaɗai, ta hanyar
yin bushasha da dukiyar al’umma. Dubi wannan misalin:
“ su kuwa shugabannin
da yake sun tara abin duniya tsauni-tsauni ta wannan ƙazamar hanya sai dai su yi
bakan a cikin ramin kura wato daga ke sai ‘ya’yanki suna ta gurgurar dukiyar jama’a
a tsanake cikin sigar bushasha da ƙazamar buƙata.”
(Surajo, 2006: 1)
Sau da dama ‘yan siyasa sukan zama ramin kura ne, daga ke sai
‘ya’yanki. Sukan tara dukiya ta ƙazamar hanya, wato wawure dukiyar al’umma. Wannan
ya sa sukan riƙa yin yadda suka ga dama ta hanyar sayi banza, sayi wofi. Al’umma
suna masu kallon masu fankama da ji-da-kai, kamar yadda wannan misalin ya nuna:
“ ina jawo hankulanku
tare da tuna maku cewa dukkanin ku fa a halin yanzu kun riga kun kama tafarkin sallama da talauci, don haka dole
mu ci gaba da rungumar al’adar tururuwa wato dai ko ba za a ci ba to a dai ɗiba
a tara domin talakawan ƙasar nan sun riga sun gama yi mana mummunar fassara. Yau
a ƙasar nan ba wani mai daraja sai wanda ya mallaki gida ko kuwa mota one in town.
Sannan kuma yana da special number a jikinta ya kasance shi ne ya fi kowa ba da
gudummawa mai tsoka yayin da duk ake yin wata gidauniya ko kuwa asusu. Babu wanda
ya damu da ya ɗaga kai ya bi salsalar yadda aka yi ka tara kuɗin nan naka da kake
gararin gabanka da su.”
(Surajo, 2006: 111)
A cikin wannan misalin an ga yadda Alhaji Zangina yake jan hankalin
‘yan’uwansa ‘yan siyasa cewa, su ci gaba da yadda aka san su kawai shi ne mutuncinsu,
wato su ci gaba da wawushe dukiyar talakawa suna tarawa ko da kuwa za su ɗebi abin
da ya fi ƙarfin hidimar rayuwarsu. A ganinsa wannan dukiyar ce kawai ta rage masu
a matsayin abin da talakawa suke gani su raga masu. Don haka dole su mallaki gidaje
da motoci na alfarma waɗanda za a sanya masu lambobi na musamman, kuma in za a yi
gidauniya su je su ba da gudummawa mai tsoka. Babu wanda zai damu ya tuhumi yadda
aka yi ka tara wannan dukiyar wadda kake wadaƙa da ita. ‘Yan siyasa suna ganin cewa
matuƙar kana nuna fankama da isa ta wannan hanyar to babu wanda zai damu da wani
aikin cigaba da za ka kawo wa al’umma. Shi ya sa wani ɗan siyasar har ya shafe wa’adin
mulkinsa al’ummar mazaɓarsa ba za su iya nuna aiki ƙwara ɗaya da ya yi masu ba,
wasu sai dai su ga sauyi a jikinsa da motocinsa maimakon su samu cigaba a mazaɓarsu.
Wannan ya fito a cikin wannan misalin da yake ƙasa:
A duk tsawon zamansa a
majalisa jama’ar da yake wakilta na mazaɓarsa su dai kawai sun ga canji a rigunan
wuyansa, gidansa, motocinsa da kuma wajen kadarorinsa.
(Surajo, 2006: 22)
Wannan ɗan majalisa ne kamar yadda misalin da yake sama ya nuna,
yana wakiltar al’ummarsa a majalisar gwamnati, amma babu abin da ya tsinana masu
da a su iya nunawa. Abin da kawai suke iya gani da ya sauya shi ne irin tufafin
alfarma da yake sanyawa da gida da ya gina na alfarma, sai kuma motocin hawansa
manya-manya.
An ci gaba da nuna yadda
‘yan siyasa suke yin wadaƙa da dukiyar al’umma ta hanyar gina kansu, da kuma nuna
abubuwa na alfahari domin bambance kansu da talakawa. Alal misali, ‘yan siyasa sun
riƙa yin jerin gwanon motoci na kece raini domin nuna isa. Da wuya a ga babban ɗan
siyasa wanda zai tafi da mota ɗaya ko biyu, maimakon haka sai a ga ya jera motoci
masu yawa yana tafiya da su don dai a san cewa wani babba ne. Dubi wannan misalin:
“Cikin gaggawa ɗan sandan
da yake zaune a gefen mai zaman banza ya sadar zuwa sauran motocin da suke cikin
taragon rakiyata ”
(Aminiya-Trust, 2020: 20).
A cikin wannan misalin an bayyana jerin motocin da ke bin wannan
ɗan siyasar da tarago. Tarago dai mazaunin fasinjan jirgin ƙasa ne mai kama da ɗaki(CNHN,2006:428),
wanda yakan kasance mai tsawo, a wasu lokutan ma ba a ganin ƙarshensa daga goshin
jirgin. Wannan ne aka siffanta tsawon layin motocin da suke biye da tawagar ɗan
siyasar. Idan aka bibiya ma motoci biyu ko uku za su iya biyan buƙatar wannan tafiya,
amma saboda a nuna isa aka shirya motoci birjik don su rufa masa baya. Wani abin
mamaki duk wannan yawan motocin ba daga aljihunsa zai ɗauki nauyinsu ba, daga aljihun
gwamnati ne, domin da zarar ya sauka ba a ƙara ganin sa da irin wannan jerangiyar
motocin.
Duk da cewa masu riƙe da madafun iko ba yawa ne da su a cikin
al’umma ba idan aka kwatanta su da talakawa, amma masu mulkin su ne suke yadda suka
ga dama da dukiyar ƙasa sun bar talaka a cikin wahala. A cikin shekarar 2023 an
bayyana cewa, ‘yan majalisar ƙasa sun sayi motoci na alfarma daga cikin dukiyar
ƙasa, duk da irin tsadar rayuwa da halin matsin da ake ciki. Ga bayanin kamar yadda
jarida Premium Times Hausa ta ruwaito:
“Majalisar Nijeriya ta
bayyana shirin sayen zabga-zabgan motoci ga dukkan dattawan majalisar da mambobin
tarayya ‘yan majalisar sun ce ba su son motocin da aka fara tayin sai masu maimakon
haka sai suka ce su irin zunduma-zunduman motocin nan baƙaƙe suke so, waɗanda kuɗinsu
ya zarce ƙa’idar motocin da RMAFC ta ƙayyade a sai wa ma’aikatan gwamnati amma ‘yan
majalisar ta 10 da ke kan mulki yanzu suka rufe ido, duk da tsananin halin tsadar
rayuwar da talakawa ke ciki, suka ce su zabga-zabgan motoci masu tsada suke so ”
(Murnai, 2023).
A nan idan aka duba za a ga cewa, fankama ce da son nuna isa
da ji-da-kai, kasancewar har tayin wasu masu sauƙin kuɗi aka masu, amma suka ce
ba su so, su masu ɗan karen tsada suke so, maimakon su rage kashe kuɗin in ya so
raran da aka samu sai a yi wa talakawa wani abu da zai rage masu raɗaɗi.
Irin waɗannan misalai sun nuna yadda fankama ta ginu a cikin
siyasar jam’iyyu a ƙasar Hausa. Masu mulki sukan riƙa yin rayuwa ta kece raini a
cikin dukiyar talakawa, maimakon a fifita ayyukan cigaban ƙasa da jin daɗin ‘yan
ƙasa. Wannan kuwa ya ginu ne a cikin siyasar ƙasar Hausa tun daga farkon siyasar
jam’iyyu zuwa yau. Abubuwan sukan sauya fasali daga wata jamhuriya zuwa wata, kuma
a kullum abin sai ƙaruwa yake yi, wanda hakan yake ƙara haifar da ci baya ga harkokin
mulki da siyasa.
5.4 Dangantaka Tsakanin Masu Mulki da Waɗanda
Ake Mulka
A nan an kawo bayanai ne kan irin danagantakar da take tsakanin
‘yan siyasa waɗanda suke kan mulki ko masu neman mulkin da kuma waɗanda ake mulka
wato talakawa. An tattauna yadda talakawa suke kallon ‘yan siyasa ta fuskar yadda
suke mu’amalantarsu kafin zaɓe da kuma bayan sun ɗare madafun iko. An kawo bayanai
kan irin kallon da masu mulki suke yi wa talakawa da kuma yadda suke mu’amalantarsu
kafin zaɓe da kuma bayan sun samu mulki. Wannan ya fito da irin dangantakar da take
tsakanin ɓangarorin biyu kamar yadda yake a cikin rubutaccen zube.
5.4.1 Yadda Talakawa Suke Kallon ‘Yan Siyasa
Talakawa kamar yadda ma’anar ta nuna su ne mutanen da ba su riƙe
da wani muƙami na sarauta ko siyasa, kuma ba su mallaki wani abin duniya ba. A al’adance
talaka shi ne aka sani da yi wa shugaba biyayya, inda shi kuma mai shugaba ake sa
rai ya kula da talakawa ta hanyar tsare masu dukkan haƙƙoƙinsu daidai gwargwado
ba tare da nuna bambanci ko ɗaukar ɓangaranci ba.
Wajibi ne shugaba ya zamto tsayayye ne wajen kula da al’amuran
al’ummarsa ta yadda zai kiyaye masu dukkan wasu abubuwa waɗanda za su iya zama hatsari
ko bazarana ko kuma matsi a gare su. A kodayaushe shugaba ya kasance mai gaskiya
da riƙon amana da faɗa da cikawa a tsakanin talakawansa. A duk lokacin da shugaba
ya rasa waɗannan abubuwa, akan ce bai zama nagarataccen shugaba ba, kuma talakawa
za su riƙa yi masa wani irin kallo ta hanyar danganta shi da wasu munanan halaye
saɓanin waɗanda ya kamata ya kasance da su.
Tarihi ya nuna cewa, tun bayan samun ‘yancin kai a ƙasar Hausa,
talakawa sun riƙa yi wa shugabanni musamman na siyasa wani irin kallo na zargi.
Suna ganin cewa shugabannin ba su sauke haƙƙoƙin da Allah ya ɗora masu ba, kuma
ba su cika alƙawuran da suka ɗaukar wa talakawa ba. Marubuta ayyukan adabi na zube,
sun riƙa bayyana irin waɗannan ɗabi’u da talakawa suke kallon shugabanni da su a
cikin ayyukansu. Waɗannan ɗabi’un sun zama tamkar adireshin shugabannin siyasa a
yau. Daga cikin irin fuskokin da talakawa suke kallon shugabanni da su sun haɗa
da:
5.4.1.1 Maƙaryata
Ƙarya mummunar ɗabi’a ce ga Bahaushe, wanda takan zubar da ƙimar
mutum a duk lokacin da aka same shi da ita. A fagen siyasa ana kallon ƙarya a matsayin
wani abu da ya zama ruwan dare tsakanin ‘yan siyasa da kuma talakawa.
A wani misali an nuna yadda talakawa suke tattaunawa kan ‘yan
siyasa da yadda suke shirya ƙarya da rana tsaka bayan kuwa wasu daga cikin talakawa
sun fahimci ƙarya ce suke shiryawa domin an daɗe ana ruwa ƙasa tana shanyewa. Dubi
abin da ya ce:
“Yaya kai da ka yi yawon
duniya za ka bari waɗannan mutane su yaudare ka? Suna gina ƙarya ne su zagaye talakawa
da ita don haka in ba abin da suka nuna masu ba, ba abin da za su iya gani. Babbar
ɓarnar da za ta auku shi ne, in mu da muka fahimci munafincinsu muka bari suka yaudari
mutanen garinmu suka kai su suka baro.
“Kana nufin zancen da
suke faɗi ƙarya ne?”
“Ƙarya ce mana.”
(Katsina, 1983: 9).
A nan ana nuni da yadda ‘yan siyasa sukan riƙa cika talakawa
da ƙarya ne su zagaye su da ita, ta yadda da yawa cikin talakawa ba su iya fahimtar
cewa abin da aka faɗa masu ƙarya ce don ba za su iya ganewa ba. Babbar ɓarna ita
ce a gane ƙaryarsu, kuma a bar su su ci gaba da ita, wajibi a fahimtar da talakawa.
Talakawa sun ɗauka cewa
‘yan siyasa ba su da gaskiya, duk kuwa wanda aka samu ba shi da gaskiya to dole
a same shi akasin haka, wato maƙaryaci ne. Ƙarya a cikin sha’anin siyasar jam’iyya
ta zama tamkar jini da tsoka ce a yau, inda ‘yan siyasa sukan riƙa yi wa talakawa
ƙarairayi domin a ganinsu sha’anin siyasa ba abu ne da yake buƙatar gaskiya da gaskiya
ba, kamar yadda ya fito a cikin wannan misalin:
“ saboda sun riga sun
camfa sun ce wai sha’anin mulkin ƙasar nan ba ka iyawa ba ka gamawa, kuma ba a yaba
maka Kuma a gaskiya maigida ina son fa ka sani cewa lamarin siyasa a ƙasar nan ba
fa lamari ne na gaskiya ƙeƙe da ƙeƙe ba Haba maigida siyasar ƙasar nan cike take
da alƙawuran ƙarya da kuma zantuttukan banza kamar ‘yan matan amarya ”
(Surajo, 2006: 1).
A cikin wannan misalin an nuna cewa ma ai
siyasar ba gaskiya ce a cikinta ba, cike take da ƙarairayi, kuma ba ta ma buƙatar
gaskiyar domin cike take da alƙawura na ƙarya waɗanda akan yi wa talakawa, dukkan
zantuttukan ‘yan siyasa na banza ne kamar dai yadda akan ce zancen ‘yammatan amarya
ne wato zancen banza. Sau da dama ‘yan siyasa a lokacin kamfen sukan riƙa yin alƙawura
na ƙarya, sannan su riƙa faɗin abubuwa da ba haka suke a zahiri ba duk domin cimma
wani buri nasu.
Kamar yadda talakawa suka fahimci cewa galibin ‘yan siyasa maƙaryata
ne, su ma ‘yan siyasar sun san irin kallon da ake yi masu ko ma a ce sun amince
cewa su maƙaryatan ne domin wasu abubuwan da gangar ake faɗa wa al’umma bayan kuwa
an san ba haka ne ba ko kuma ba za a aiwatar da su ba. Alal misali, a cikin littafin
Dambarwar Siyasa an nuna inda wani ɗan
siyasa yake shirya yadda za a yi wa al’umma sanarwa ta ƙarya wadda ba za a aiwatar
ba. Dubi abin da ya ce:
“ Abin da za ka yi shi
ne, ka yi sanarwa a kafofin watsa labarai cewa gwamanati za ta bayar da tallafi
mai tsoka ga manoman alkama. Za ta bai wa kowa injin ban-ruwa, inci biyu da rabi
da iri kilo ɗari da taki buhu uku na kamfa ɗaya na yuriya da kuɗi naira dubu talatin
na aiki Cikin murmushi malam Nasiru ya dube shi; ‘Honorabul bana za a bayar da tallafin
da gaske ke nan? Dariya sakatare ya yi; Ashe har yanzu Nasiru ba ka gama sanin siyasa
ba.”
(Aminiya-Trust, 2020: 30)
A nan an nuna ƙaryar ‘yan siyasa ne a fili inda suka shirya za
a sanar cewa za a ba da tallafin kayan noma ga talakawa manoma bayan kuwa ya san
cewa ƙarya ce ba bayarwa za a yi ba. A cikin ‘yan siyasar wani ya yi mamaki cewa
shin wannan karon za a ba da tallafin ne da gaske? Ya san an saba irin wannan ƙaryar,
kuma a ƙarshe ba a bayarwa. Dariyar da Sakatare tare da faɗin cewa ashe har yanzu
Alhaji Nasiru bai san siyasa ba, shi ne ya tabbatar da cewa ‘yan siyasa da dama
sun san abin da suke faɗa ƙarya ce, kuma ba zai tabbata ba, amma a haka suke faɗa
wa al’umma. Faɗin cewa ashe har yanzu bai san siyasa ba daidai yake da ashe har
yanzu bai san siyasa cike take da ƙarairayi ba.
Galibi talakawa suna yi wa ‘yan siyasa kallon maƙaryata ne domin
maganganunsu ba su dacewa da ayyukansu, kuma sukan faɗa ba tare da cikawa ba kamar
yadda aka gani a cikin misalan da suka gabata. Kodayake akan samu wasu ‘yan kaɗan
daga cikinsu waɗanda suke da gaskiya kuma idan sun faɗa suka cika, amma dai mafi
yawa daga cikinsu masu faɗa ba cikawa ne.
5.4.1.2 Mayaudara
Yaudara ya shafi yin amfani da kalmomi ko wasu halaye domin kawar
da hankali mutane ta yadda ba za su iya fahimtar inda aka sa gaba ba sai bayan an
amince masu. Sau da dama wanda za a yaudare shi bai cika fahimta ba a karon farko
har sai abin ya faru yake iya iya ganewa.
Duk wanda yake da irin wannan halin shi
ake kira mayaudari, jam’insu kuma mayaudara. A idon talakawa galibin ‘yan siyasa
mayaudara ne, domin suna da hali na ɓoye gaskiya da niyyar cuta. Sau da dama ‘yan
siyasa sukan yi wa al’umma romon baka da nuna masu cewa nesa ta zo kusa kan irin
wahalar da talaka yake sha, amma da sun samu dama sai su manta. Shugabanni da ‘yan
siyasa kullum sukan yaudari talakawa ne ta hanyar nuna masu cewa za su fita daga
cikin ƙangin da suke ciki matuƙar suka mara masu baya, amma da sun aminta da su
sai su ga kusan ma gwamma jiya da yau.
Yaudara a nan tana nufin nuna wa talaka lagwada da hutu da jin
daɗi ta hanyar nuna masa misalai daga wasu abubuwa na jin daɗi wanda shi ma in ya
amince zai samu irin su, amma bayan ya amince ya zaɓe su, sai ya kasance akasin
abin da aka nuna masa yake gani kamar dai yadda aka nuna a cikin wannan misalin
da yake ƙasa:
Hajiya ta yi dariya ta
ce, “O ni ‘yasu, wannan kalma ta canji dai tun ina amarya nake jin ta a bakin ‘yan
siyasa, amma dai kawo yanzu na dai ga canjin a gidaje, motoci da kuma matan ‘yan
siyasar. Mu dai talakawa canji dai da muke iya ɗoraswa shi ne na wahalhalu, kama
daga kan tsadar abinci da kayan masarufi, tsadar man fetur sai kuma canji daga faɗan
ƙabilanci zuwa na addini. Saboda haka ni a wajena da taron ‘yan siyasar ƙasar nan
da taron ‘yan caca, ɗanjuma ne da ɗanjummai.”
(Surajo, 2006: 4).
An sani cewa an sha yaudarar talaka da kalmar ‘canji’ wadda kullum
ake yamaɗiɗi da ita, ana cewa za a samu sauƙi, amma har yanzu babu alamar canjin.
Wuri ɗaya da ake ganin canjin shi ne a jikin iyalan ‘yan siyasar, domin su ne ake
ganin salon rayuwarsu ta sauya. Sukan riƙa hawa motoci da gina manyan gidaje da
kuma sanya sutura masu tsada. Talakawa kuwa da aka yaudara aka yi wa romon baka
kullum suna fama da wahalar tsadar abinci da man fetur da kayan masarufi. Haka kuma
maimakon a samu canji daga tsofaffin hanyoyin rayuwa masu tsauri zuwa sababbi masu
sauƙi, sai dai a canja wa rikice-rikice salo daga na ƙabilanci su koma na addini.
Kamar yadda misalin da yake sama ya nuna, waɗannan su ne kawai canje-canjen da ake
samu a ciki siyasa, amma sauran duk yaudara ce. Wannan ya sa talakawa suke kallon
duk ‘yan siyasa a matsayin mayaudara, waɗanda suke neman dama su yi wa mutane daɗin
baki su zambace su.
A wani misalin kuma, an samu inda ‘yan siyasa suka riƙa yaudarar
al’umma da wasu manyan al’amura na addinin Musulunci kamar aiwatar da shari’ar Musulunci.
Sukan nuna cewa za su aiwatar da shari’ar Musulunci a jihohinsu kasancewar jihohin
Musulmi ne mafi yawa. Da yawansu sun ƙaddamar da shari’ar ne domin su yaudari al’umma
da kuma biyan wasu buƙatunsu, daga ƙarshe sukan fita batun shari’ar ya kasance ba
da ita ake aiki wajen gudanar da mulkin ba. Wani marubuci ya nuna irin wannan hoton
kamar haka:
“Idan ka san har ba za
ka iya aiwatar da shari’ar Musulunci ba kamar yadda take, to kuwa kada ka ƙara ambata
a cikin kamfe ɗinka. Idan ba haka ba Allah zai kama ka da laifuka masu dama. Sannan
kuma jama’ar ƙasa su ma za su riƙa tsine maka, domin kuwa ,mafi yawan ku masu ambatar
shari’ar, ɗan makullin gishiri ne ya fi gishirin zaƙi. ‘Yan siyasar zamani baki
na annabi Musa zuciya ta Fir’auna ”
(Surajo, 2006: 31).
Wannan nasiha ce aka yi wa ɗan siyasa cewa in ya san ba zai iya
aiwatar da shari’ar Musulunci yadda Allah ya shar’anta ba, to kada ya yaudari mutane
da shi lokacin yaƙin neman zaɓe. Duk kuwa wanda ya yi haka Allah zai kama shi da
laifin hakan, sannan a’ummar ƙasa za su tsine masa saboda yaudarar da ya yi masu.
An kuma nuna a cikin misalin cewa, yawancin ‘yan siyasa suna amfani da kalmomin
yaudara waɗanda za ka ji su tamkar mutanen kirki a baki, amma abin da suka ƙudurce
a zuciyarsu daban ne.
Masu mulki sun riƙa yin kalamai na yaudara da kawar da hankalin
mutane kan wasu al’amura domin su tara abin duniya. Sau da dama ‘yan siyasa sukan
yi amfani da wata matsala ƙarama sai su kambama ta domin su tara dukiya ta ƙazamar
hanya ko da kuwa talakawa za su shiga halin ƙunci. Dubi wannan misalin:
“Aikina na ƙarshe yaudara
ce. Na tuna kalamaina na ƙarshe ga talakawa: ‘Mun fitar da maƙudan kuɗi domin yaƙi
da korona ’ A haƙiƙanin gaskiya kuwa korona farin ciki muka yi da zuwanta. Dalili
shi ne ta samar mana da hanyar yin ƙafar ungulu da kuɗaɗe cikin ruwan sanyi.”
(Aminiya-Trust, 2020: 22).
A nan marubucin ya nuna yadda masu mulki suke amfani da hanyar
yaudara ne domin zaluntar talakawa. Ya nuna yadda wani ɗan siyasa yake nadama a
ranar da ya mutu cewa, aikin da ya aikata a ƙarshen rayuwarsa ita ce yaudara. Kamar
yadda yake nuna wa talakawa lokacin korona cewa, an ware maƙudan kuɗi domin yaƙi
da korona, wanda a haƙiƙanin gaskiya su shugabannin ma sun yi murna da zuwan koronar,
domin sun samu hanyar da suka yi sama da faɗi da kuɗaɗen talakawa cikin ruwan sanyi,
amma suna yaudarar mutane da cewa suna aiki ba dare ba rana wajen yaƙi da cutar.
Bugu da ƙari, su ma ‘yan siyasar sun yarda cewa suna amfani da
salon yaudarar al’umma a cikin bayanansu. Sukan yi amfani da daɗin baki su yaudari
al’umma ta yadda bayan sun jefa su rami suke komawa su riƙa tattaunawa da abokansu
na siyasa. Su riƙa cewa, abin da suka faɗa ba haka suke nufi ba, saɓanin haka suke
nufi, sun dai faɗi haka ne don su yaudari jama’a. Dubi wannan misalin:
“Ɗanƙasa ya kuma sakin bidiyon da ya girgiza gari.
Bidiyon Honorabul Baƙo ya saki a cikin ofishinsa yana tattaunawa da wani mutum,
yana cewa, ‘siyasa kasuwa ce, duk abubuwan da na ƙirgo ba wanda zan yi, ba ni da
hankali ne, sau uku fa ina nema ina faɗuwa. Daga hawa kawai sai in ɓuge da ayyuka
tun ban fanshe kuɗin da na kashe a kamfen ba.”
(Aminiya-Trust, 2020:
104).
Marubucin ya nuna yadda a wani hoton bidiyo da aka samu na shugaban
ƙaramar hukuma wanda yake bayyana wa abokin siyasarsa cewa, ya daɗe yana takara
yana faɗuwa. Don haka duk abin da ya faɗa wa al’umma cewa zai yi masu yaudara ce
kawai, domin ai da hanakalinsa. Babu abin da zai aiwatar sai ya fanshe kudinsa da
ya kashe a kamfen. Ke nan, wasu lokuta da gangan ‘yan siyasa suke yaudarar talakawa
kan wasu abubuwa da akan shafa masu zuma a baki sai sun zo lashewa a share.
Domin ƙara tabbatar da yadda talakawa suke kallon ‘yan siyasa
a matsayin mayaudara, an samu wani misali da ya fito ƙarara ya nuna hakan bayan
wani ɗan siyasa ya yi wa talakawa romon baka da cewa zai inganta rayuwarsu. Daga
baya sai ya shafa wa idonsa toka ya yi mursisi. Ga misalin:
“Babu shakka ‘yan siyasa
mayaudara ne. Ya ce a cikin ransa. Wata biyar ke nan da ɗarewar Alhaji Maikwabo
karagar mulki, amma babu abin da ya canza. Abubuwa sai ƙara taɓarɓarewa ma suke
yi.”
(Aminiya-Trust, 2020: 111).
A wannan misalin wani ɗan bangar siyasa ne da aka yi wa alƙawarin
inganta rayuwarsa, amma daga ƙarshe aka watsar da shi yake ƙorafin kan yadda yaudarar
‘yan siyasa take. Ya yi ta jaddada wa a ransa cewa lallai ‘yan siyasa mayaudara
ne, domin duk cikin alƙawuran da Alhaji Maikwaibo ya yi masu na inganta rayuwa da
cigabansu, wata biyar ke nan babu wani abin da ya sauya sai ma ƙara taɓarɓarewa
da al’amura suka yi.
Wasu ‘yan siyasa sukan yi amfani da wata hanyar yaudara domin
kawar da hankalin talakawa, ta yadda sukan lura da abin da al’umma suke buƙata amma
ba za su samar masu ba, sai ana gab da zaɓe sai su zo su fara aikin samar da wannan
abin. Da zarar an kammala zaɓe sai su yi watsi da shi domin da ma yaudara ce domin
a samu kaiwa ga madafun iko. A cikin littafin Mizani an kawo irin wannan bayanin kamar haka:
“ ba zai yiwu shugaba
ya ɗau shekara huɗu yana mulkar mu ba tare da ya amfanar da mu komai da ya danganci
ci gaban rayuwarmu ba, sai bayan ƙarewar waɗannan shekaru huɗun, ko kuma dab da
ƙarewarsu, sannan ya ce zai bijiro da wani aiko ko wani da zai iya ɗauke hankalin
mutane don samun wata ƙuri’a daga gare su, ya sake ɗarewa kan kujera a tenure ta
biyu sannan mu mara masa baya ba.”
(Mustapha da wasu, 2023: 33).
A nan Baba ne yake bayani ga jama’a domin wayar masu da kai a kan
wanda ya kamata su zaɓa. A cikin bayanin nasa ya nuna cewa, ‘yan siyasa sukan shafe
shekara huɗu suna mulki, kuma suna sane da buƙatun al’umma, amma ba za su tashi
yin wani hoɓɓasa ba sai wa’adin mulkinsu ya ƙare ko yana gab da ƙarewa. A wannan
lokaci sukan fara wasu ayyuka domin ɗauke hankalin mutane don samun wata ƙuri’ar
daga gare su. Ɗauke hankalin mutane a nan yana nufin yaudarar mutanen ne domin su
ɗauka cewa za a yi masu aikin ne domin a taimake su. Bayan kuwa yana sane da aikin,
amma bai yi ba, sai a wannan ƙurarren lokacin.
Ya sani cewa sauran lokacin da yake da shi a kan kujera ba zai ishe shi ya kammala
aikin ba, ya dai fara ne domin yaudarar al’ummar mazaɓar don su mara masa baya.
Idan aka dubi misalan da aka kawo a sama za a fahimci cewa, wasu
talakawa suna kallon ‘yan siyasa a matsayin mayaudara, masu amfani da daɗin baki
domin su samu goyon bayan al’umma kawai. A wasu lokuta akan samu waɗanda sukan ɗauka
cewa ba duk ‘yan siyasa ne mayaudara ba, wasu sukan riƙan yin abubuwa da gaske tsakaninsu
da Allah tare da ƙoƙarin ganin duk abin da suka ayyana cewa za su aiwatar na taimakon
al’umma sukan aiwatar.
5.4.1.3 Azzalumai
Azzalumi kuwa shi ne wanda yake tauye haƙƙin mutane ko cutarsu
ta hanyar fin ƙarfi. Talakawa suna kallon masu mulki a matsayin azzalumai ne domin
suna ganin cewa suna danne masu haƙƙoƙinsu waɗanda ya kamata su zo gare su don su
amfana, amma saboda zaluncin shugabanni sai abin ya kasa kai wa ga talaka.
A kodayaushe talaka yana zargin masu mulki da yi masa riƙon sakainar
kashi, ta hanyar yin biris da duk wata hanya da suka san talakan zai iya samun sauƙi,
wanda ya jefa talakan cikin mawuyacin hali. Wannan kuwa yakan faru ne a sanadiyyar
zaluncin shugabanni kamar yadda wannan misalin ya nuna:
Farfesa ya ce, “Wato kin
san an ce hannu dayawa maganin ƙazamar miya. Wato, wasu ‘yan ƙasa ne nagari waɗanda
suka damu ƙwarai da irin halin da talakawa suke ciki na ƙangin talauci da rashin
kwanciyar hankali wanda zaluncin da shuwagabanni ke yi yake haddasawa, su ne suka
kira wani muhimmin taro, kuma na halacce shi domin ba da tawa gudummawa.”
(Surajo, 2006: 1).
A cikin wannan misalin an nuna cewa ƙangin talauci da tashe-tashen
hankula ba komai yake haifar da su ba illa zaluncin shugabanni. Da a ce shugabanni
za su kasance masu adalci, da an samu sauƙin irin waɗannan abubuwa. A nan dai wannan
misalin ya tabbatar da cewa talakawa suna ganin cewa shugabanni azzalumai ne, domin
su ne suka jefa su cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yin suke ciki.
Wani misalin da za a iya gani kan abin da ya shafi yadda talakawa
suke kallon shugabanni ko masu mulki shi ne yadda wani fusataccen matashi ke nuna
cewa zaluncin shugabanni a kan talakawa ya kai matakin da za a iya tara su a tayar
masu da bom da za a samu dama. Dubi wannan misalin:
“ Hmmm wata miyar sai
a maƙwabta, da dai a wata ƙasar muke ba a Nijeriya ba. A Nijeriya kam talaka shara
ma ta fi shi daraja. Waɗannan tsinannun azzaluman shugabannin namu daga su sai ‘ya’yansu.
Wallahi na tsane su marasa imani, da zan samu damar tara su wuri ɗaya duk in tayar
da bom duk ya tarwatsa su, tsinannu!
(Aminiya-Trust, 2020:
20).
A wannan misalin ya nuna cewa talaka a wajen masu mulki shara
ma ta fi shi daraja. Azzaluman shugabanni sun yi babakere a dukiyar talakawa daga
su sai ‘ya’yansu sun bar talakawa cikin wahala. A cikin misalin an nuna cewa masu
mulki azzalumai ne kuma ba su da imani, ba su da wani amfani a cikin al’umma. Ya
nuna cewa ya tsane su saboda zaluncinsu. Ya nuna cewa duk masu irin wannan halin
zaluncin tsinannu ne, kuma da za a tara su wuri guda zai iya tayar masu da bom duk
su mutu.
Ta kowace fuska talaka ya ɗauka cewa babu wani azzalumi kamar
shugaban da bai kula da matsalar talakawansa ba, hasali ma shi ne yake yin jagora
wajen jefa su cikin ƙunci da damuwa. Kamar yadda za a gani a misalin da yake
tafe:
“Napep na shiga muna cikin
tafiya, muna sauraron gidan rediyo. Masana suna sharhi a kan dalilin ƙara kuɗin
man fetur. Direban ya girgiza kai, ya ce cikin takaici, ‘Allah ya tsine wa gwamnatin
nan! Azzalumai, mayaudara kawai!’.”
(Aminiya-Trust, 2020: 100).
Wani direban kekek napep ne ya kunna rediyonsa yana sauraro,
sai ya ji yadda masana suke fashin baƙi a kan dalilan da suka sanya aka ƙara kuɗin
man fetur. Abin da ya harzuƙa direban ya ka she rediyon cikin fushi tare da tsine
wa gwamnatin da take mulki, inda ya ce azzalumai ne mayaudara. Irin wannan ne ya
faru a kwanan nan a wannan ƙasar inda aka ƙara kuɗin mai, al’ummar ƙasa suka shiga
halin ƙunci na rayuwa, kuma suna ta ƙorafin cewa shugabanni sun zalunce su.
Akan samu inda ‘yan siyasa kan hana ma’aikata albashi har na
tsawon watanni ba tare da tunanin halin ƙuncin da za su shiga ba, amma kuma su ba
su taɓa fasa biyan kansu ko da sisin kwabo ba. Irin wannan misalin ya fito cikin
littafin Dambarwar Siyasa, kamar haka:
“Honorabul Baƙo da ya
ƙi biyan mahaifina haƙƙinsa, ya je gidan rediyo yake ƙaryar yana jinyar majinyata.
Daga ƙarshe, na bar wa Allah komai, waɗannan azzaluman mutane da kullum suke mayar
da ƙasarmu baya na haɗa su da kotun Allah ya isa!”
(Aminiya-Trust,2020: 102)
A cikin misalin an nuna cewa, ɗan siyasa ya riƙe wa wani talaka
mai aikin hannu kuɗinsa har ya kwanta rashin lafiya, ya hana kuɗin balle a samu
abin da za a yi masa magani a asibiti, daga ƙarshe rai ya yi halinsa. Duk da haka
ɗan siyasar ya je gidan rediyo yana faɗin cewa suna ɗaukar nauyin jinyar marasa
lafiya kyauta. Wannan ya sa aka kira ‘yan siyasa da azzalumai waɗanda aka nuna cewa
kullum zalunci da rashin tausayinsu ne suke mayar da al’umma baya.
Idan aka duba a nan za a ga cewa duk misalan da suke ƙarƙashin
wannan batun sun nuna irin yadda shugabanni suke zaluntar talakawa, inda suka riƙa
bayyana shugabannin a matsayin azzalumai. Abin da ya kamata a fahimta shi ne, duk
da yadda talaka yake kallon shugabanni da wannan fuskar, akwai kuma daga cikin talakawan
waɗanda suke ganin cewa ba shugabannin ne azzalumai ba. Wasu daga cikin talakawan
ne suke sawa a yi wa shugabannin wannan kallon, musamman waɗannan suke tsakanin
shugaban da talakawa. Domin dai ba a mugun sarki sai mugun bafade.
5.4.1.4 Maciya Amana
Shugabanci amana ce ta talakawa a kan masu mulki. Wannan ya sa
kodayaushe talakawa suke ganin cewa amanar jama’a aka damƙa a hannun ‘yan siyasa,
kuma an zura masu ido cike da tsammanin za su riƙe wannan amanar ba tare da wata
tangarɗa ba. Yawanci waɗanda sukan fito takara sukan nuna cewa za su iya riƙe amanar
al’umma tare da alƙawarin ba za su ci amanar ba; sai dai ba a nan gizo ke saƙar
ba. Da yawa cikin ‘yan siyasa masu mulki da aka damƙa masu irin wannan amanar ta
shugabanci sukan ci amanar, ta hanyar kasa kulawa da talakawa ko dukiyar ƙasa. Amanar
da ta fi wahalar riƙewa ga masu mulki babu kamar ta kula da dukiyar ƙasa, inda sukan
riƙa yin watanda da ita maimakon yin tattalinta da kuma gudanar da ayyukan cigaba
waɗanda za su taimaki talaka ta hanyar sauƙaƙa masa rayuwarsa.
Marubuta sun riƙa fito da yadda masu mulki da ‘yan siyasa suka
kasa riƙe irin wannan amana da akan damƙa masu, inda har suka mayar da siyasa tamkar
kasuwanci, su zuba kuɗi, su kwashi ƙazamar riba. Wasu ‘yan siyasar ba ma wai su
saci dukiyar ƙasar su yi amfani da ita a cikin ƙasar ba ne, maimakon haka sai su
kwashe ta su kai bankunan ƙasashen waje su adana. Su ba su amfana ba, kuma ba su
yi ko su bari a yi wa al’ummar ƙasa aiki da ita ba. Dubi abin da wannan misalin
ya nuna:
“Sai dai kuma kash! Gambiza
ta kasance shugaba a cikin ƙasashen da suka fi kowaɗanne cin hanci da ha’inci a
duniya. Mafi yawa daga cikin shugabanni da kuma manyan ma’aikatan wannan ƙasa sun
ƙware wajen ha’intar talakawansu ta hanyar sace kuɗin ƙasar suna sulalewa da su
zuwa bankunan ƙasashen Turai don kai ajiya.”
(Surajo, 2006: 1)
A nan ya nuna cewa, wannan ƙasar Allah ya yi mata arziƙi mai
ɗimbin yawa, sai dai ‘yan siyasar ƙasar suna daga cikin mafiya cin hanci a duniya.
Mafi yawa daga cikin shugabanninta da manyan ma’aikatan gwamnati sun yi suna wajen
wawure dukiyar al’umma su mayar da ita tasu. Dukiyar da aka damƙa a hannunsu a matsayin
amanar ƙasa, su kwashe, su mayar da ita mallakinsu. A ƙarshe, su ba su amfana da
ita ba, kuma ba su bari an yi wa al’ummar ƙasa wani aikin da zai amfane su ba. Su
kai ƙasashen Turai su ajiye, a ƙarshe ba su ci wani amfanin kirki a kan dukiyar
ba.
Wasu daga cikin ‘yan siyasa sun mayar da siyasar tamkar tudun
takawa ne domin su samu kaiwa ga dukiyar ƙasa, su yi yadda suke so da ita. Da zarar
‘yan siyasa sun samu hayewa kan mulki sai su zama ‘yan handama da babakere kamar
yadda wannan misalin ya nuna:
“Tun da dai kai ganau
ne kuma jiyau cewa siyasa fa a ƙasar nan wani dandali ne kawai wanda wasu ‘yan tsiraru
masu handama da babakere suke amfani da shi wajen wawure arziƙin ƙasar na domin
su azurta kansu. Suna ƙamuya-muya daga cikin baitulmalin jama’a bila’adadin waɗanda
da bazarsu ne ake taka rawar.”
(Surajo. 2006: 6).
A nan an nuna cewa siyasa
ta zama tamkar wani dandali da wasu mutanen ƙalilan kan shiga, inda sukan riƙa juya
dukiyar ƙasa ta hanyar handama da babakere. Sukan riƙa wawure dukiyar ƙasar su mayar
da ita mallakinsu tare da sanin cewa dukiyar ƙasa ta al’ummar ƙasa ce baki ɗaya
ba ta wani mutum guda ba. Babu wanda yake da iko ya kwashe ya mayar da ita tasa
ko kuma ya yi wani amfani da ita ba bisa ƙa’idar doka ba. Dukiyar al’ummar ƙasa
ce akan damƙa ta amana a hannun shugabanni, amma sai su ci amana ta hanyar cin dukiyar
da ɓarna ba tare da haƙƙi ba, bayan kuwa sun sani cewa da bazar al’ummar ƙasar suke
rawa don su su suka zaɓe su zuwa matakin da suke.
Sau da dama akan zaɓi shugabanni ne domin a damƙa masu amanar
dukiya da rayukan talakawa a hannunsu, kasancewar su ne abubuwa na farko da shugaba
ya kamata ya tsare wa talakawa kafin sauran abubuwa su biyo baya. Akan sami inda
talakawa kan shiga halin damuwa a zamanin wani shugaba, inda za su riƙa fatan wa’adin
mulkin ya ƙare don su zaɓi wanda zai cire masu kitse a wuta. Wani lokaci akan ci
amanarsu ko bayan sun sake zaɓen wani, inda sukan kasa samun wannan abin da suka
zaɓi shugaban dominsa. Irin wannan ya bayyana a cikin misali kamar haka:
“Shi yanzu damuwarsa ba
ta wuce yadda ya watsa wa talaka ƙasa a ido ba, talakan da ya yi ruwa ya yi tsaki
wajen ɗora shi a kan kujerarsa. Amma a yau shi ma ya san babu mai shan wahala a
jihar Dawa sai talakan, abin baƙin ciki shi ne durƙushewar tattalin arziƙi da ayyukan
ta’addanci da aka zaɓe shi domin kawar da su har yanzu suna nan , sai ma abin da
ya ci gaba.”
(Aminiya-Trust,2020: 128).
Wannan misalin ya yi daidai da halin da Arewacin Nijeriya ta
tsinci kanta a wuraren shekarun 2010 zuwa 2015, inda ‘yan Arewa suka riƙa kukan
rashin tsaro da tashe-tashen hankula da ɓarnata dukiyoyi. Suka tsaya suka dage har
aka samu sauyin gwamnati a shekarar 2015 da fatan samun sauƙin waɗannan matsaloli.
An ci gaba da samun matsalolin inda shugabanni suka kasa riƙe amanar da aka damƙa
masu, kuma har yanzu ba a fita daga cikin matsalar ba.
Idan aka dubi tarihin siyasar jam’iyyu a Arewacin Nijeriya za
a ga cewa, akwai shugabanni da dama da aka yi wa shaidar riƙon amana da adalci,
abin da kawai ba a cika fahimta ba shi ne, ba a gane matsayin riƙon amanarsu sai
bayan sun shuɗe. A wannan zamanin ma akwai shugabannin da aka shaide su da cewa
masu amana ne, kuma ba a same su da wata almundahana ba.
Talakawa da dama suna kallon cewa dukkan wani ɗan siyasa da suka
bai wa yarda suka zaɓe shi to amana ce suka damƙa masa. Idan kuwa ya kasa tsare
amanar da aka ba shi ya kasa yin abin da ya kamata domin jin daɗinsu, to ya ci amana.
Yawan cin amanar da ‘yan siyasar kan yi bayan an zaɓe su ne ya sa talakawa suke
yi masu kallo iri ɗaya ta wannan fuskar a matsayin maciya amana, duk da cewa akan
samu waɗansu daga cikin ‘yan siyasar waɗanda suke yin bakin ƙoƙarinsu wajen ganin
sun sauke haƙƙin waɗanda suke wakilta.
5.4.2 Yadda Masu Mulki
Da ‘Yan Siyasa Suke Kallon Talakawa
‘Yan siyasa da masu mulki suna da wani nauyi
da ya rataya a wuyansu na kula da al’umma musamman talakawa. Haƙƙin shugaba ne ya
tabbatar da jin daɗi da walwalar talakawa, da kuma magance masu dukkan wasu matsalolin
rayuwa daidai gwargwado ko da ta hanyar rage raɗaɗi ne. Wannan ya sa a kodayaushe
talakawa suke sa ido a kan ‘yan siyasa da masu mulki domin ganin ba su wuce gona
da iri ba.
Bibiya da sanya ido kan harkokin mulki da
talakawa suke yi wa shugabanni ya sanya wasu daga ciki sun shiga taitayinsu, ta
hanyar ƙoƙarin yin wani abu da za a gani a ce sun yi. Wasu kuwa hakan bai sa sun
sauya ba, maimakon haka sai suka ɗauka cewa talakawan ne suka gaza haƙuri ko kuma
suke so su yi kafaɗa da kafaɗa da su. Wannan ya sa suke yi wa talakawan wani irin
kallo na daban yadda su suka ɗauka.
Sau da dama masu mulki su ne kan ƙirƙiri
wata hanya da zai sa su samu sauƙin sanya ido ko bibiyar da talakawa suke yi masu
domin su kawar da hankalinsu su bi su ko ba don Allah ba. Wannan ya sanya suke yi
wa talakawan duba ta fuskoki mabambanta kamar haka:
5.4.2.1 Makwaɗaita
Yawanci masu mulki suna yi wa talakawa kallon
makwaɗaita domin kuwa duk irin abin da ɗan siyasa zai aikata na muzguna masu, da
zaran lokacin zaɓe ya zo zai fito da kuɗi ya watsa sai ka ga sun manta sun kama
rububi a kansa. A ƙarshe shi za su zaɓa ko da kuwa daga baya zai sake ƙuntata masu.
Irin wannan misalin ya fito a cikin littafin Tura Ta Kai Bango inda aka nuna yadda jam’iyyar Riƙau ta ‘yan jari-hujja
take bayyana yadda za ta shaƙe wuyan talakawa ta hanyar amfani da kuɗi. Dubi abin
da marubucin ya ce:
“Wannan mataki da kuka
yi niyyar ɗauka shi ne matakin da zai kai mu ga cimma burinmu. Domin a duniyar nan
babu abin da za ka iya yin amfani da shi ka shawo kan talaka kamar dukiya. Don shi
talaka ba shi da wuyar kamawa. In dai na Naira to ka gama da shi.
(Katsina, 1983: 11).
A cikin misalin an nuna cewa talaka ba shi da wuyar kamawa in
dai akwai abin lasawa, wato in dai akwai kuɗin da za a iya ba shi ko yaya ne to
yakan yi saurin faɗawa tarko. Akan yi amfani da kuɗi a karkato da hankalinsu ko
da kuwa an ɓata masu rai to akan yi amfani da kuɗin domin a rarrashe su a sake mai
da su gidan jiya.
Wani misali na kwaɗayin da masu mulki suke dangantawa ga talakawa
shi ne, yadda aka nuna cewa, alamar jam’iyyar Riƙau shi ne wani mutum ne riƙe da
kuɗi cike da hannunsa domin a yaudari talakawa a ga kamar raba kuɗin za su yi kamar
yadda marubucin yake cewa:
“ sun dai sa hoton kuɗin
ne domin sun raina mu talakawa. Sun san idonmu idon kuɗi, ko ba a ba mu ba an gama
da mu.”
(Katsina, 1983: 61).
A nan ana nuna yadda ‘yan siyasa suke kallon talakawa ne a matsayin
makwaɗaita, inda aka nuna masu kuɗi a hoto ba ma zahiri ba zai iya sa su zaɓi wanda
suka ga wannan alamar tattare da shi. Masu mulki sun san talaka ido a naira ne,
duk inda zai ga kuɗi nan zai bi ko da kuwa ba shi da tabbacin za a ba shi.
An
sake nuna irin wannan misalin a cikin littafin Da Bazarku, inda marubucin yake cewa:
“To yallaɓai talakawan
ƙasar nan fa har yanzu mafiya yawansu a cikin duhun kan siyasa suke, ballantana
kuma ga kwaɗayin tsiya da tsoro cushe a cikin zukatansu. Wannan shi ya ci gaba da
mayar mana da su kamar ‘yan tsaki. Wato idan ka ɗebo ‘yar tsaba sai kawai ka zo
dab da su ka ɗan watsa, ka ci gaba da kiran su kut! Kut!! Kut!!! Idan ka ga sun
sha’afa sai ka shammace su ka yi masu kamun kazar kuku.”
(Surajo, 2006: 47)
A nan ya nuna cewa talakawa ba su waye a kan siyasa ba, kuma
ma ba wannan ba, babban abin da yake damun su shi ne matsanancin kwaɗayi da tsoro
da ya mamaye zukatansu, wanda ya sa ba su iya ɗaga murya ko taɓuka wani abin da
zai sa a daidaita tsarin siyasar. Kwaɗayinsu ya sa ‘yan siyasa suka ci gaba da yi
masu kallon kaji sai da tsaba. Suna cewa, ko yaya ka ɗan ɗebo ‘yan sulalla ka watsa
nan da nan za su fara rububi zuwa inda kake, kai kuwa ka kama su. Ma’ana ka samu
su zaɓe ka ci gaba daga inda aka tsaya. Da yawa a haka ‘yan siyasa suke kallon talakawa,
kuma haka wasu talakawan suke. Ba su duba nagartar ɗan takara, wa ya ba da kuɗi
ko ya fi bayarwa kawai ake kallo. Akwai waɗanda suka fi cancanta waɗanda sukan fito
takara, amma sai a ƙyale su saboda ba su ba da kuɗi, a zaɓi wanda bai cancanta ba
saboda kwaɗayin ɗan abin da zai bayar. Wani misali da yake tabbatar da kwaɗayi ga
talakawa shi ne kamar haka:
“Ina so ka fahimta siyasar
ƙasar nan fa ta masu kuɗi ce. Ba ruwan talakawa da kirkinka da kamun kanka, in dai
ba ka ba su kuɗi ba to kuwa ba za su zaɓe ka ba. Su mutuncinsu kuɗi Domin da zarar
zaɓe ya zo to kuwa idanun talakawa rufewa suke yi kuma su manta shaf. Saboda haka
ina son ka gane cewa sun sayar mana da ‘yancinsu ne a ranar zaɓe, kai kuwa ba ka
da kuɗin da za ka iya saye.”
(Surajo, 2006: 10).
A nan ana nuna irin halin kwaɗayi ne da son abin duniya da talakawa
suke nunawa ba tare da duba yadda rayuwarsu za ta kasance bayan zaɓe ba. A cikin
misalin an nuna cewa babu ruwan talakawa da kirkin ɗan siyasa da natsuwarsa ko kamun
kansa ko dai wani abu da zai sanya ya zama mutumin kirki. Abin da suke dubawa kawai
kuɗi ne. Matuƙar ɗan takara ba shi da su, sai dai yana ji yana gani a zaɓi wanda
ba shi ba, ko da kuwa bai kai shi nagarta ba. An nuna cewa idanun talakawa rufewa
suke yi a lokacin zaɓe, tare da manta irin halin ƙunci da damuwar da gwamnati ko
masu mulkin suka jefa su a ciki, sai su karɓi ɗan abin da ba zai ma iya kashe masu
kwaɗayin ba.
A cikin littafin Ɗaukar
Jinka ma an kawo irin wannan batu da ya shafi yadda masu mulki suke kallon mabiyansu,
inda akan nuna cewa talaka ba shi da alƙibla, duk inda zai samu ɗan wani abu shi
yake ba tare da duba ina ya fi dacewa ya bi ba. Ga misalin:
“Babana ɗan a bi yarima
a sha kiɗa ne a siyasa. Shi ba shi da alƙibla ɗaya tsayayya, yau idan ka gan shi
da wancan honorabul din, gobe za ka gan shi cikin ‘yan hamayya. Shi dai duk inda
zai faɗi ya ji lema, to kuwa nan ne makwancinsa.”
(Aliyu da Mujaheed da Yusuf da Nasudan, 2023: 22).
A nan an nuna irin halin
kwaɗayin da wasu talakawa suke nunawa ne, wanda yakan hana su zama wuri guda a cikin
siyasa. A kullum ‘yan siyasa suna yi wa talaka kallon makwaɗaici domin duk inda
za a ba shi wani abu nan ne yake zuwa, ba inda ake da kyakkyawar tsari a kan al’umma
baki ɗaya ba. Ba ya duba ‘yancinsa ko haƙƙinsa a kan shugabanni. Wannan ne ya sa
aka nuna wannan ɗan siyasar da aka kawo a cikin misalin da yake sama a matsayin
maras alƙibla, yau yana wajen wannan ɗan siyasa domin samun abin lasawa, gobe yana
wajen wancan. ‘Yan siyasa suna yi wa talaka kallon mai kwaɗayi domin abin hannunsu
yake kallo, maimakon abubuwan da za su inganta rayuwarsa ba.
Waɗannan misalai da aka kawo a sama sun yi nuni ne da yadda ‘yan
siyasa suke yi wa talakawa kallon makwaɗaita, inda suke misalta su da ‘yan tsaki
waɗanda da an watsa masu tsaba za su sheƙo su zo duk inda aka buƙaci su zo, kuma
za su iya aikata duk abin da aka so in dai akwai abin hasafi ba tare da tunanin
me hakan zai haifar ba.
5.4.2.2 Matalauta
‘Yan siyasa da dama suna yi talakawa kallon matalauta wato mutanen
da ba su da wadata, abinci bai wadace su ba, domin kuwa kullum sukan ce abinci suke
nema. Kasancewar abinci yana da matuƙar muhimmanci a rayuwar ɗan’adam, wannan ya
sa ‘yan siyasa sukan yi amfani da ƙarancinsa wajen cimma burinsu, su hana abincin
ya wadace shi.
Yana daga cikin hanyoyin da ‘yan siyasa suke bi wajen tattara
ƙuri’un talaka a cikin ruwan sanyi shi ne su haifar da talauci da yunwa a cikin
al’umma, inda abinci zai riƙa gagarar talaka. A irin wannan yanayi talaka zai iya
amincewa da komai in dai abincin zai samu ko da kuwa ba zai ishe shi na tsawon shekarun
da ‘yan siyasar za su shafe suna mulki ba. Ga misali:
“Sanata mu fa a ƙasar
nan idan har kana son talaka ya saurare ka da kunnuwan basira kuma ya bi umarninka
, to kuwa sai ka gana masa azaba da talauci, ta yadda cin abinci sau uku a rana
zai kasance sai namijin duniya, kuma ko shi ma ɗin sai ya yi jiɓin goshi.”
(Surajo, 2006: 18).
A cikin wannan misalin ana nuna dabarun jawo hankalin talaka
ne a cikin siyasa, inda akan hora shi da talauci, ta yadda abinci ma zai riƙa yi
masa wahalar samu. ‘Yan siyasa sukan riƙa ƙaƙaba wa talakawa talauci ta yadda cin
abinci sau uku zai gagare su. A wannan yanayin ‘yan siyasa kan yi wa talakawa kallon
matalauta, domin sukan riƙa raba masu kayan abinci a wulaƙance wanda kuma bai wuce
ma a yi amfanin kwana ɗaya ko biyu da shi ba ya ƙare, domin su samu ƙuri’arsu. Ta
wannan hanyar sun riƙa ƙuntata wa talakawa da kuma amfani da yunwar cikinsu domin
cimma muradunsu. Ga wani misalin:
“ Su fa sun ɗauka suna
da maganin duk wani talaka. In talakan dai zai sami abin cefane na yau, bai damu
ba ya watsar da haƙƙinsa da na ‘ya’yansa, da na jikokinsa da ba su zo ba.”
(Katsina, 1983: 13).
A nan marubucin yana batun yadda ‘yan siyasa suka ɗauka cewa
su suke da hanyoyin tsara al’amura yadda suka so, kuma yadda zai tafi masu a daidai,
inda suke amfanin da talaka a matsayin bango majinginarsu. Suna ganin cewa da abin
hannunsu za su jawo talaka ya yi masu moriya ko da daga baya za su watsar da shi.
Hakan ba zai hana idan suka sake nemansa ya zo ba, domin idan ya ƙi talauci zai
tursasa shi ya zo. Matuƙar talaka zai samu ɗan abin cefane na rana ɗaya, to bai
damu ya sarayar da ‘yancin ‘ya’yansa da na jikokinsa har da waɗanda ba su ma zo
duniyar ba.
Wannan shi ne irin kallon da masu mulki suke yi wa talakawa a
wannan fuskar, suna ganin cewa ai matalauta ne, in dai aka raba masu abinci ko abin
saye ko yaya yake za su sayar da ‘yancinsu, kamar dai yadda aka shaida a zaɓen 2023
inda aka riƙa raba taliya guda ɗaya ko biyu a madadin ƙuri’ar da za a yi amfani
da ita har tsawon shekara huɗu.
5.4.2.3 Wawaye
Dangane da wannan binciken, an dubi kalmar wauta a matsayin rashin
sanin sanin ciwon kai ko rashin sanin abin da ya dace mutum ya aikata na daidai,
wanda hakan kan sa shi ya aikata abin da bai dace ba. Wanda yake da irin wannan
halin shi ake kira wawa, jam’insu kuma wawaye.
Duk da cewa talakawan ƙasar Hausa ba wawaye ne ba, amma ‘yan
siyasa suna yi masu wannan kallon. Wannan ba zai rasa nasaba da saurin mantuwa kan
irin abin da ‘yan siyasar suke yi masu ba, da kuma sake zaɓensu ko jam’iyyarsu ba
tare da wata wahala ba.
A mafi yawancin lokuta ‘yan siyasa sukan riƙa wasa da hankalin
talaka, amma sai ya yi kamar bai fahimta ba, bayan kuwa ya fahimci komai. Maimakon
ya ɗauki wani mataki da zai gyara tsarin ko kuma ya inganta rayuwarsa, sai kawai
ya yi biris ba tare da nuna damuwarsa ko kuma turjiya ba. Masu mulki sukan riƙa
cin karensu babu babbaka a tsawon shekarun da suke kan shugabanci ba tare da tunawa
da talaka da haƙƙoƙin da suka rataya a kansu nasa ba, Shi kansa talakan ya san cewa
wannan haƙƙi ne a kansu da ba su sauke ba, maimakon ya nuna rashin amincewarsa sai
ya ja baki ya yi shiru. Idan kuma aka zo zaɓe abu kaɗan za a faɗa masa sai ya manta
duk abin da ya faru a baya ta hanyar maimaita kuskuren da ya tafka a baya, in ma
ya gane kuskure ne ke nan. Irin wannan ya fito a cikin littafin Dambarwar Siyasa kamar haka:
“Wace irin zuciya ɗan
Adam ya mallaka? Ta tambayi kanta, tana jajanta yadda talaka kan yi saurin manta
duk wani mugun giɓi da aka yi wa rayuwarsa idan lokacin zaɓe ya zo.”
(Aminiya-Trust, 2020: 73).
Marubucin ya bayyana wannan ne don nuna irin wautar da take tattare
da talaka, wanda yake saurin mantuwa bisa irin cutarwar da masu mulki sukan yi masa
a tsawon shekarun da sukan kwashe suna mulki. Marubucin ya nuna mamakinsa wajen
ganin cewa wace irin zuciya ce da talaka. Wannan dalilin ne ya sa masu mulki suke
ganin talaka wawa ne, domin suna juya tunaninsa yadda suka so. A wani wurin ma don
a nuna irin kallon da masu mulki suke wa talaka, sai aka kwatanta shi da ƙwallon
ƙafa, wanda akan riƙa wasa da tunaninsa. A buga shi nan, a buga shi can. Dubi wannan
misalin:
“Mu a wurinmu fa talaka
kamar ƙwallon ƙafa ne”
“Haba ba gara na ƙwallon
ƙafa da su ba tun da su ba su da rai, ai kamata dai ya yi ka ce da su raƙumi da
akala.”
(Surajo, 2006: 19).
Marubucin ya bayyana cewa ai talaka yadda aka wawantar da hankalinsa
ya ma wuce a misalta shi da ƙwallo, tun da ƙwallon ƙafa ba shi da rai, sai da a
ce raƙumi da akala, wanda duk girmansa da ƙarfinsa, sai yaro ƙarami ya juya shi,
ya sarrafa shi yadda yake so ba tare da wata gardama ko turjiya ba.
Wani misalin na daban a kan yadda masu mulki da ‘yan siyasa suke
ganin wautar talaka shi ne, inda talaka zai zauna ƙarƙashin masu mulkin da ba su
damu da damuwarsa ba, ba su kuma nemansa sai sun buƙaci wani abu daga wurinsa, sannan
za su waiwaye shi domin biyan buƙatunsu. Duk da haka maimakon ya yi amfani da ‘yancinsa
na zaɓe domin ƙwato wa kansa ‘yanci mai ɗorewa, sai kawai ya sayar da ‘yancin nasa
kan ɗan wani abin da bai taka kara ba balle ya karya. Dubi wannan misalin:
“Babu ta yadda za a yi
talaka ya daina sayar da kansa da jin daɗinsa. Ku ɗauka cewa wannan ita ce nasara
a gare mu. Sannan ku kwantar da hankalinku, mu jira hukumar zaɓe su fitar da sakamako
sai mu san abin yi.”
(Aminiya-Trust, 2020: 77).
A wannan misalin ana kwantar da hankalin ‘yan siyasa ne kan cewa
talaka har yanzu wawa ne, bai yi hankali ba. Su kwantar da hankalinsu in ma suna
tsammanin ya sauya daga yadda suka san shi ne, domin dai ba zai fasa sayar da ‘yancinsa
da jin daɗinsa ba. Don haka a jira sanarwa kawai daga hukumar zaɓe za su ji irin
wautar da talakawa suka tafka na sake zaɓensu.
An ƙara kawo irin wannan misali na yadda masu mulki suke yi wa
talaka kallon wawa a cikin littafin Mizani,
inda aka nuna wani matashi mai suna Muhammad yayin da yake ƙoƙarin wayar wa
da abokin Ibrahim kai kan wanda ya kamata a zaɓa, inda a cikin bayanin yake nuna
masa yadda masu mulki suke kallon talakawa a matsayin wawaye. Ga abin yake cewa:
“ amma shi wancan da ya
hau faɗa min abu ɗaya da ya yi da matasa suka ƙaru da shi? Yana daga cikin ‘yan
siyasar da suka mayar da al’umma tamkar kaji, idan lokacin zaɓe ya zo ya watsa masu
tsaba, amfanin matasa ɗaya a wajensa shi ne lokacin zaɓe.”
(Mustapha da wasu, 2023: 5).
A nan matashin yana ƙoƙarin nuna wa abokinsa yadda ‘yan siyasa
suka ɗauki talaka wawa. A cikin misalin ana bayani ne a kan ɗan siyasa mai suna
Barista Jatau wanda yake takarar gwamna tare da abokin hamayyarsa mai suna Prof.
Yusuf. Ana bayyana irin halin Barista Jatau a matsayinsa na wanda ya riƙe muƙaman
siyasa da dama, amma bai tsinana wa matasa komai ba. Matasan nan dai talakawa ne,
kuma ɗan siyasar ba ya sake tunawa da su sai zaɓe ya ƙarato, wanda ya sa a cikin
misalin aka nuna ya mai da su tamkar kaji, wato idan lokacin zaɓe ya zo sai dai
ya watsa masu tsaba kawai, da an kammala kuma ya manta da su. Hakan ba zai sa idan
wa’adin mulki ya ƙare, aka zo sake zaɓe su sake maimaita wannan kuskuren ba.
Kusan duk ‘yan siyasa irin kallon wawaye suke yi wa talakawa
ke nan. Ƙangin talauci da damuwar da talaka yake ciki na rashin tsaro da na abubuwan
more rayuwa, in aka ce zai sake zaɓen waɗanda suka shugabance shi a wa’adin mulkin
da ya ƙare ko kuma ya zaɓi jam’iyyarsu, za a iya rantsuwa cewa ba zai aikata hakan
ba, domin irin masifun da ya gani. Wannan yana daga cikin dalilan da ya sa masu
mulki suke ganin wautar talakawa, kuma suke neman wasu hanyoyin daban da za su ƙara
wawantar da su don su ɗore a kan mulki.
5.4.2.4 Cima-zaune
A fagen siyasa kalmar cima-zaune tana nufin talakawa waɗanda
suka dogara da ɗan abin cefanen da suke samu daga hannun ‘yan siyasa masu mulki,
kuma ba su da aiki sai zuwa gidajen ‘yan siyasa da buƙatu domin a biya masu.
‘Yan siyasa suna yi wa talakawa kallon cima-zaune ne kasancewar
yadda talakawan sukan riƙa tururuwa zuwa inda suke domin samun na banza, ba tare
da sun yi wani aikin da za a biya su ba. Da dama daga cikin talakawa sukan ɗaukin
buƙatunsu na ƙashin kansu a matsayin wani abu da ya zama dole masu mulki su ɗauke
masu, ba tare da tunanin wani abu mai muhimmanci da za a yi wanda zai amfani dukkan
al’umma ba. Sau da dama talakawa sukan tafi da buƙata ta ƙashin kai zuwa ga masu
mulki ko ‘yan siyasa maimakon su kai kukan al’umma kan abin da ya shafe su. Wannan
yana daga cikin dalilan da suka sanya ‘yan siyasa suke yi wa talakawa irin wannan
kallon.
Irin wannan yanayi na yadda masu mulki suke yi wa talakawa kallon
‘yan son na banza ko ‘yan maula ya riƙa fitowa a cikin ayyukan rubutaccen zube na
Hausa, inda aka riƙa fito da yadda talakawan kan riƙa miƙa buƙatu na ƙashin kai
waɗanda kuma ba su taka kara ba balle su karya ga masu mulki maimakon wani abu da
za a yi masu kowa ya amfana. Ga misali:
“ saboda sabbatun talakawa
a kullum ba su wuce na ‘matata ta haihu’ ko kuwa ‘ina da buki’ ba ”
(Surajo, 2006: 22).
Wannan fitaccen misali ne na yadda masu mulki ko ‘yan siyasa
suke kallon talakawa a matsayin ‘yan son na banza. Talakawa ba su kai kukan al’umma
sai na kansu, kuma ko a buƙatun kansu ba wani abu mai girma da ya zama dole ba,
sai dai na jin daɗi. Kamar dai yadda wannan ɗan siyasar yake nuna cewa talakawa
ba su da wata buƙata a wajensu da ya wuce neman taimakon hidimar suna idan matarsu
ta haihu ko kuma idan suna wani buki.
Zubar da kai da talakawa suka yi wajen nuna rashin wayau da rashin
wayewa da kuma rashin sanin inda kansu yake ciwo ya sa masu mulki suka mayar da
su tamkar dai wasu almajirai. Bayan kuwa duk taƙamar ‘yan siyasar dai dukiyar ƙasa
ce wadda take ba ta mutum guda ce ba har da su talakawan. Wannan ya ƙara kashe wa
talaka zuciya inda yake ganin abin da yakan je ya roƙa a wajen masu mulki su ba
shi tamkar wani abin a zo a gani ne, ko kuma alfarma ce aka yi masa. Dubi wannan
misali:
“Kowa ya ga ta yadda aka ɗaure ma cin hanci da
rashawa gindi aka ci gaba da ƙumbiya-ƙumbiya ana shirya ma talakawa bi-ta-da-ƙulli
har sai da aka tabbatar an ci galabar kashe zukatan talakawa; a inda suka koyi zaman
cin bati, jiran ta faɗi gasassa da kuma tammahan min rabbika.”
(Surajo, 2006: 69)
Talaka ya kasance bai san abin da ya dace ya kai wa masu mulki
a matsayin buƙatunsa na rayuwa ba, sai ɗan abin da ba zai kashe masa ƙishi ba. Wannan
ya bai wa masu mulki damar ɗaure wa cin hanci da rashawa gindi, kuma ya taimaka
wajen yin rub-da-ciki a kan dukiyar ƙasa da masu mulki suke yi. Masu mulki sukan
sace ɗimbin dukiya daga arziƙin ƙasa, sai su riƙa raba abin da bai kai ya kawo ba
ga masu roƙo da masu kawo ƙananan buƙatu daga cikin talakawa. Ta haka suka mayar
da talakawa ‘yan maula masu zaman cin na banza, domin kullum burinsu ta faɗi gasassa.
‘Yan siyasa da masu mulki ba su kallon kansu a matsayin matsalar
al’ummar ƙasa, a matsayinsu na waɗanda suka haifar da duk matsalolin da ‘yan ƙasa
suke ciki. Suna kallon talakawa a matsayin matsala, domin su ne suke barin abin
da ya kamata su koka a kai, wanda idan aka samar zai amfani al’umma baki ɗaya. Maimakon
haka, sai su ɓige da kai kukan abin da bai zama dole a kan gwamnati da masu mulki
ba, abin da su kaɗai zai shafa kai tsaye. Wannan ne ya sa masu mulki suke wa talakawa
kallon cima-kwance, masu neman ta faɗi gasassa ko ‘yan maula da sauran kalmomi na
ƙasƙanci.
5.5 Naɗewa
Wannan babi ya tattauna a kan siyasar jam’iyyu
ne da cigaban ƙasa. Tun farko a cikin babin an fara kawo bayani kan
abin da ya shafi manufar siyasar jam’iyyu, inda aka kawo bayani kan manufofin da
akan gina siyasa a kansu kamar yadda jam’iyyun siyasa sukan riƙa bayyana wa jama’a
a lokacin tallata jam’iyyunsu da kuma lokacin yaƙin neman zaɓe. Daga nan kuma sai
aka kawo bayanai kan yadda ‘yan siyasa kan riƙa gwagwarmaya a cikin tsarin siyasar
jam’iyyu domin samar da cigaban ƙasa da na al’umma ta hanyar aiwatar da waɗansu
abubuwa a cikin siyasa waɗanda asali ana yin su ne domin ci gaban ƙasar. Daga bisani
kuma sai babin ya tattauna kan waɗansu abubuwa da sukan haifar da naƙasu ga siyasa
har ma su shafi cigaban al’umma da ƙasa baki ɗaya. A ƙarshen babin ne aka tattauna
irin dangantakar da take tsakanin ‘yan siyasa masu mulki da talakawa, inda aka yi
bayani kan yadda talakawa suke kallon masu mulki da kuma yadda masu mulkin suke
kallon talakawa.
[1] Dubi rataye
[2] Dubi rataye
[3] Bayanin yana nan a ciki takardar Waisu Iliyasu (2018) Party Defection
and Party Switching in Katsina (1999-2015) takardar da aka gabatar a sashen
Nazarin Tarihi da Harkokin Tsaro na Jam’iar Umaru Musa Yar’adua Katsina.
[4] Dubi lamba ta 12.
[5] Bayanin yana cikin takardar Awopeju, A. (2024) From Election rigging
to Vote Buying: Evolving Decay of a Dysfunctional Process in Nigeria. A cikin Innovations, Number 76 March 2024. www.
Journal-innovetions.com.
[6] Dubi takardar Micheal, O. da Ogunrotimi, O. da
Roland, U. A. (2023) Electoral Rigging and Violence in Nigeria in Historical
Perspective: A Case Study of 1959, 1964, 1965 and 1983. A cikin International Journal of Multidisciplinary
Research and Analysis, Volume 06 Issue 01 January 2023.
[7]Dubi lamba ta 4.
Dubi takardar Attahiru Ahmad Sifawa
(2017) The Genesis of Political Thuggery
in Party Politics in Modern Nigeria: A Case Study of Sakoto Province, 1950-1960 a
shafin http://www.reseacrhgate.net
[8] Bayanin yana cikin takardar Attahiru Ahmad Sifawa (2017) The Genesis of Political Thuggery in Party
Politics in Mordern Nigeria: A Case Study of Sakkwato Province, 1950-1960 a
shafin http://www.reseacrhgate.net
[9] Dubi maƙalar Ibok, A. K. da Ogar, A. O (2018) Political Violence In
Nigeria and its Implication for National Development a cikin GNOSI:
Interdiciplinary Journal of Human Theory and Praxis vol. 1(1).
[10] Ɗan jam’iyyar NEPU ne na
farko-farko, sannan kuma a jamhuriya ta biyu
yana cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar PRP tare da Malam Aminu Kano; da
aka zo jamhuriya ta huɗu kuma ya shiga jam’iyyar PDP.
[11] Dubi lamba ta 21
[12] Abdulƙadir Koguna, shugaban jam’iyyar NPC na lardin Kano a jamhuriya
ta ɗaya.
[13] Tattaunawa da Malam Abdul’aziz Lawal a gidansa da yake Ƙofar Marusa Layout, Katsina, ranar 03/12/2022 da misalin ƙarfe 5:47 na yamma.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.