Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarihin Ginuwar Wasu Al’amuran Siyasar Jam’iyyu a Cikin Rubutun Zuben Hausa Daga 1950-2023 (Babi Na Shida)

Yusuf, J. (2025). Tarihin Ganuwar Wasu Al'amuran Siyasar Jam'iyyu a Cikin Rubutun Zuben Hausa Daga 1950-2023 (Ph.D. Thesis) Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo, Sokoto.

Tarihin Ginuwar Wasu Al’amuran Siyasar Jam’iyyu a Cikin Rubutun Zuben Hausa Daga 1950-2023

TARIHIN GINUWAR WASU AL’AMURAN SIYASAR JAM’IYYU A CIKIN RUBUTUN ZUBEN HAUSA DAGA 1950-2023

Na

Jibril Yusuf
Email: yusuf.jibril@kasu.edu.ng
Phone: +2347030399995

*** ***

BABI NA SHIDA

KAMMALAWA

6.0 Shimfiɗa

Wannan babin shi ne na ƙarshe, a cikinsa an taƙaita bayanan abin da ya gudana a cikin binciken baki ɗayansa. An ɗauki kowane babi aka taƙaita abin da ya ƙunsa, wato daga babi na ɗaya har zuwa babi na shida. Bayan taƙaitawa, an kuma kawo sakamakon bincike. Sakamakon bincike da aka kawo shi ne gudummawar da wannan bincike ya bayar ga duniyar ilimi da bincike. Haka kuma a cikin wannan babin an kawo shawarwarin da binciken ya bayar ga masana da manazarta da kuma ɗaliban tarihin adabin Hausa musamman ma adabin siyasa. Daga ƙarshe sai aka naɗe babin. An kawo manazarta, wato jerin gwanon wuraren da aka samu bayanan da aka yi amfani da su a cikin binciken.

6.1 Taƙaitawa

Wannan bincike mai taken “Tarihin Ginuwar Wasu Al’amuran Siyasar Jam’iyyu A Cikin Rubutun Zuben Hausa Daga 1950-2023” bincike ne da aka aiwatar da nufin a bibiyi tarihin ginuwar siyasa a Arewacin Nijeriya a cikin rubutaccen zube na Hausa, waɗanda suka haɗa da jaridu da wasiƙu da jawaban siyasa da ƙagaggun labarai. Domin samun nasarar binciken, an kasa binciken zuwa babi-babi har shida. Babi na farko an yi masa take da gabatarwa. A cikin babin ne aka yi wa aikin shimfiɗa, inda aka kawo bayanan da suka yi wa mai son karanta wannan bincike jagora. A cikin gabatarwar an nuna cewa bincike ne na tarihi wanda aka gudanar da shi ƙarƙashin rubutaccen zuben Hausa. An amince cewa dukkan abubuwan da aka kafa hujjoji da su a cikin binciken suna ƙarƙarshin rubutaccen zube ne, wato jaridu, da wasiƙu da jawaban siyasa da aka samu a rubuce, da kuma ƙagaggun labarai. Shi kuwa rubutaccen zube wani ɓangare ne na rubutaccen adabin Hausa.

An ci gaba da kawo bayanai a kan kayan cikin gabatarwa, inda aka kawo dalilin bincike, wato dalilin da ya sanya mai baincike yin tunanin gudanar da bincike kan ginuwar siyasa a cikin rubutaccen zube na Hausa. Daga nan sai aka kawo manufar bincike, wanda ya ƙushi manufofin da binciken ya yi ƙuduri domin cim masu. An kawo bayanai a kan muhimmancin bincike, wato irin amfanin da binciken yake da shi ga duniyar ilimi da bincike. Bugu da ƙari an kuma kawo farfajiyar bincike, wato inda kadadar binciken ya shafa ba tare da tsallakawa wani ɓangaren da ba shi ba. A ƙarshen wannan babin an kawo tambayoyin bincike, waɗanda su kuma sun shafi abubuwan da bincike ya yi tambaya a kansu ne, waɗanda kuma binciken ya amsa su a yayin gudanarwa, wanda samun amsoshinsu ne ma ya bayar da sakamakon bincike a ƙarshen aikin.

A babi na biyu an kawo bitar ayyukan da suka gabata, inda aka kawo ayyukan da suke da alaƙa da wannan aiki waɗanda suka shafi siyasa. An fara da bitar kundayen digiri na uku, daga nan sai aka biyo bayansu da na digiri na biyu, sai kuma na digiri na ɗaya. An yi bitar mujallu da maƙalu waɗanda aka buga da waɗanda ba a buga ba, sannan kuma an yi bitar bugaggun littattafai. Yadda aka tsara bitar shi ne, duk bayanin da ya zo hannun mai bincike an taƙaita bayaninsa ne, aka kuma kawo dangantaka da take tsakaninsa da aikin da aka gudanar da kuma inda suka bambanta. Wannan ne ya ba da damar fahimtar giɓin da binciken ya gano, wanda shi ne ya ba da damar gudanar da shi.

A babi na uku, an tattauna hanyoyin da aka yi amfani da su ne wajen samun bayanan da suka gina wannan binciken. An kawo manyan hanyoyi da suka haɗa da tattaunawa da masana da ‘yan siyasa domin samun muhimman bayanai a kan wasu al’amura da suka shafi siyasa. Sauran hanyoyin da aka yi amfani da su sun haɗa da karance-karance na litattafan ƙagaggun labarai da jaridu da litattafan da aka taskace jawaban ‘yan siyasa da wasiƙu na siyasa musamman a cikin jaridu. Haka kuma an yi amfani da na’urorin zamani kamar wayar hannu domin yin hira da kuma naɗar murya. An yi amfani da na’urar kwamfiyuta domin shiga intanet don lalubo bayanan da hannu ba zai iya kaiwa gare su ba. Bugu da ƙari, a ƙarshen babi na uku, an kawo bayani a kan ra’in Tarihanci da aka ɗora a kan binciken domin samun kyakkyawar sakamako a ƙarshe.

A babi na huɗu an tattauna batutuwan da suka shafi mafarin siyasar jam’iyya a cikin tarihin siyasar jam’iyyu. An tattauna dalilan da suka haifar da ƙamfar adabin siyasa, wanda hakan ya sa ba a samu ƙagaggun labarai na siyasa a farkon siyasar jam’iyyu ba sai daga baya. An kuma kawo batutuwan da suka shafi samuwar adabin siyasa da batun samuwar jam’iyyu da tallata su a cikin tarihi. A cikin babin an kawo yadda aƙidun addini suka ba da gudummawa wajen ginuwar siyasar jam’iyyu. Haka kuma an kawo bayani a kan yadda aka riƙa amfani da manyan jagororin addinin Musulunci wajen tallata siyasar jam’iyyu da kuma amfani da matsayin shugabannin siyasa wajen tallata ‘yan siyasa. Har ila yau a cikin babi na huɗu ne aka tattauna matsayin mata a cikin tarihin siyasar jam’iyyu, da yadda jam’iyya mai mulki ta riƙa takura wa abokan hamayya. Daga ƙarshen babin ne binciken ya dubi yadda aka riƙa amfani da yarfe a cikin tarihin siyasar jam’iyyu.

A babi na biyar, an tattauna manufar siyasar jam’iyyu, wanda tsarin siyasar jam’iyyu a Arewacin Nijeriya ta ginu a kansu. Da waɗannan manufofi ne kowace jam’iyyar siyasa take neman ra’ayin jama’a da su. Baya ga nan, an kuma tattauna irin gwagwarmayar da aka riƙa yi cikin tarihi domin samar da cigaba ga al’umma a siyasance. A nan ne aka tattauna abubuwan da suka ƙunshi kakkafa jam’iyyun siyasa da tallata su da tallar ‘yan takara da kuma yaƙin neman zaɓe, wanda aka bi zaren tarihi da ganin yadda suka riƙa bayyana a cikin ayyukan zube na Hausa. Bugu da ƙari, an ci gaba da tattauna abubuwan da akan riƙa amfani da su wajen gwagwarmayar samar da cigaban al’umma a cikin siyasa kamar su, rarrashin jama’a da sauya sheƙa da haɗakar jam’iyyu da ma tsare ƙuri’a da sanya ido domin a tabbatar an samu nasara. Waɗannan duk wannan babin ya tattauna su a matsayin hanyoyin samar da ci gaba ne a siyasance, domin sai da su siyasa take gudana har a iya samar wa da al’umma cigaba mai ma’ana.

A hannu guda kuma, an tattauna waɗansu abubuwa waɗanda suka zama matsala ga siyasar jam’iyyu, waɗanda suke haifar da cikas ga samun cigaban al’umma a siyasance. An bi zaren tarihin siyasar jam’iyyu inda aka riƙa ganin waɗannan al’amura sun bayyana a wasu wurare cikin rubutaccen zuben Hausa. Wannan ya nuna samuwarsu a cikin tarihi. A ƙarshen babin ne aka tattauna irin dangantakar da take tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulka. A nan ne binciken ya tattauna yadda talakawa suke kallon ‘yan siyasa da kuma yadda ‘yan siyasa suke kallon talakawa.

Daga nan kuma sai babi na shida, wanda yake ɗauke da jawabin kammalawa. A cikinsa an taƙaita duk bayanan da aka samar a cikin biciken. An kawo bayanin sakamakon bincike, wato abin da binciken ya gano bayan an kammala. An kawo shawarwari da binciken ya ba masana da manazarta da ɗalibai da ‘yan siyasa da masu mulki da ma al’umma baki ɗaya kan yadda za a inganta wannan fagen nazari na tarihin ginuwar siyasa a cikin rubutaccen zuben Hausa.

6.2 Sakamakon Bincike

Kowane bincike na ilimi da aka gudanar ana sa rai a samu sakamako daga ƙarshe. Da wannan sakamakon ne za a iya gane cewa an fito da wani sabon abu daga cikin wannan binciken wanda manazarta da masu bincike ba su lura da shi ba. Daga cikin abubuwan da bincike ya gano sun haɗa da:

i- An gano cewa, rubutaccen zuben Hausa irin su jaridu da wasiƙu da jawaban siyasa suna da tasiri a cikin tafiyar da harkokin siyasa, da bunƙasa demokuraɗiyya musamman idan aka yi la’akari da yadda suka zama hanyoyin da ‘yan siyasa suke amfani da su wajen isar da saƙonnin siyasa mabambanta ga abokan hamayya da ma sauran al’umma.

ii- Binciken ya gane waɗansu abubuwa waɗanda suka haddasa ƙarancin ayyukan rubutaccen zuben Hausa na siyasa, inda aka yi bayaninsu a matsayin dalilan da ake ganin su ne suka sanya rubutaccen zuɓe na siyasa bai yawaita ba idan aka kwatanta shi da wasu ɓangarori na adabi.

iii- Binciken ya kuma gano cewa, al’amuran siyasa da dama da suke faruwa a yau, sun samo asali ne tun daga farkon siyasar jam’iyyu, kuma suka ci gaba da wanzuwa har zuwa yau kamar yadda aka gani a cikin binciken. Kasancewar an ratsa wasu zamunnan siyasa daban-daban, ya sa wasu al’amuran suka riƙa sauya fasali, wato yadda suka gudana a farko, ya sha bamban da yadda ake gudanar da su a yau.

iv- Binciken ya gano waɗansu abubuwa da suka shafi manufofin siyasar jam’iyyu a cikin rubutaccen zuben Hausa, waɗanda ‘yan siyasa suke amfani da su a matsayin hanyoyin samar da ci gaba al’umma da kuma waɗansu abubuwa da suka riƙa kawo cikas wajen samar da ci gaba a cikin tarihin siyasar jam’iyyu.

v- Haka kuma binciken ya gano irin alaƙar da take tsakanin masu mulki da ‘yan siyasa da kuma talakawa, inda ya gano irin kallon da masu mulki da ‘yan siyasa suke yi wa talaka da kuma yadda shi ma talakan yake kallon masu mulki.

vi- Haka kuma, an gano cewa binciken shi ne na farko da ya fito da tarihin ginuwar wasu al’amuran siyasar jam’iyyu daga cikin ayyukan zuben Hausa. An fahimci hakan ne ta hanyar bitar ayyukan da suka gabata wanda hakan ya nuna cewa ba a yi wani aiki da ya fito da tarihin ginuwar siyasa a cikin rubutaccen zube ba. Ke nan, za a iya cewa binciken ya yi nasarar cike wani giɓi, ya kuma buɗe sabon fagen nazarin tarihin ginuwar siyasar jam’iyyu a cikin rubutaccen adabin Hausa.

6.3 Shawarwari

Dangane da wannan bincike, akwai shawarwari da aka ga ya kamata a bayar ga masana da manazarta da ɗaliban adabin Hausa. Kasancewar adabi rumbu ne na tattara tunanin jama’a, da kuma kasancewarsa hoton rayuwar al’umma. Wannan ya sa ya ƙunshi duk wani abu da ya shafi rayuwar al’umma a cikin kowace gaɓa ta rayuwa da aka samu. Idan haka ne, ashe adabi ƙunshe yake da tarihin abubuwa da dama na rayuwa ba siyasar jam’iyyu kaɗai ba. Ya kamata a mayar da hankali sosai wajen nazarin tarihin waɗannan abubuwan a cikin adabin zuben Hausa baki ɗaya, ba rubutacce kaɗai ba.

Wannan bincike ya karkata kaɗai a kan tarihin ginuwar siyasar jam’iyyu ne a cikin rubutaccen zube na Hausa. Ya kamata masana da manazarta da ɗalibai su karkata bakin alƙalaminsu zuwa sauran al’amuran siyasar da ba su shafi siyasar jam’iyya ba, kasancewar siyasar tana da nau’o’i daban-daban, domin ganin irin wainar da ake toyawa a cikin sauran nau’o’in siyasar a cikin rubutaccen zuben Hausa.

6.4 Naɗewa

Kamar yadda aka gani a cikin babin, tun da farko an kawo shimfiɗar babin, sannan aka kawo taƙaitawa kan abubuwan da aka tattauna a cikin aikin tun daga babi na ɗaya har zuwa babi na shida. Daga nan an kawo sakamakon bincike, wato abin da binciken ya gano. An kuma kawo shawarwari ga masana da manazarta da ɗalibai domin faɗaɗa bincike a kan tarihin siyasa a cikin rubutaccen adabin Hausa.

Post a Comment

0 Comments