Yusuf, J. (2025). Tarihin Ganuwar Wasu Al'amuran Siyasar Jam'iyyu a Cikin Rubutun Zuben Hausa Daga 1950-2023 (Ph.D. Thesis) Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo, Sokoto.
TARIHIN GINUWAR WASU AL’AMURAN SIYASAR JAM’IYYU A CIKIN RUBUTUN ZUBEN HAUSA DAGA 1950-2023
Na
Jibril Yusuf
Email: yusuf.jibril@kasu.edu.ng
Phone: +2347030399995
*** ***
BABI NA HUƊU
SIYASA A RUBUTACCEN ADABIN HAUSA
4.0 Shimfiɗa
A wannan babin an kawo
bayanai da suka shafi siyasa da ma’anonin da masana da manazarta suka ba ta, sannan aka dubi wasu na’u’o’inta
a taƙaice. Haka kuma an kawo bayanai kan waɗansu daga
cikin dalilan da ake ganin sun haifar da ƙamfar rubutaccen adabin siyasa waɗanda
wannan bincike ya mayar da hankali a kansu. Daga nan an kawo bayanai kan
irin dangantakar da take tsakanin siyasar addini da siyasar jam’iyya, wanda shi
ne ya ba da damar gane irin yadda addini da aƙidu suka yi tasiri a fagen siyasar jam’iyyu a Arewacin Nijeriya.
Haka kuma an kawo bayani kan matsayin mata a cikin siyasa da yadda ake takura wa
abokan hamayya da kuma amfani da yarfe a cikin siyasar jam’iyyu.
4.1 Ma’anar Siyasa
A ma’ana ta lugga an bayyana
kalmar siyasa da mabambantan ma’anoni kamar haka: Ƙamusun Dar-Elmashreƙ
a cikin Idris, (2016:49) an bayyana kalmar
da cewa, Balarabiyar kalma ce wadda asalinta daga kalmar “saasa” ne, amma saboda
ƙa’idar tasarifi na nahawun Larabci sai kalmar ta koma “siyaasa”, wadda take nufin
juyawa a kan wani lamari ko kuma yarda da wani ko jiɓintar al’amarin al’umma tare
da saninsu ko ba tare da saninsu ba.
Ƙamusun Ingilishi na Merriam-Webster
(2024) ya bayyana siyasa da cewa:
“the art or science concerned with guiding or influencing governmental
policy or the art or science concerned with winning and holding control over
a government, especially, competition between competing interest groups or individuals for power
and leadership (as in a government).”
Fassara;
“hanya ko fasaha ce ko kimiyya
da ta shafi karkato ra’ayin al’umma domin samun shugabanci da juya akalar gwamnati;
hanya ce ta fafutukar neman samun ƙarfin faɗa a ji, wadda kan gudana tsakanin ɓangarori
biyu, domin samun shugabanci.”
A cikin Ƙamusun CNHN, (2006:397) an
kawo ma’anoni huɗu da suke bayyana siyasa kamar haka:
-Tafiyar da al’amuran jama’a
ta hanyar neman ra’ayinsu da shawarwari da su.
-Rangwame, musamman a ciniki.
-Dabara ko wayo.
-Iya hulɗa da jama’a.
Ƙamusun nan na Ingilishi mai
suna Oxford Advanced Learner Dictionary ya bayyana siyasa da cewa:
“the activities involved in getting and using power in public life, and being
able to influence decisions that affect a country or a society.”
Fassarar Marubuci:
“harkoki ne da suka shafi
neman samun ƙarfin iko a cikin al’umma da kuma samun tasiri wajen yanke shawara wadda ta shafi
ƙasa ko al’umma.”
Shi
kuwa Ƙamusun Almunjid
Wasiɗ a cikin Idris, (2016:47) ya bai wa siyasa ma’anoni
guda biyu. Ma’ana ta farko ya bayyana siyasa da cewa ingantar da al’umma da shiryar
da su zuwa ga tafarkin tsira. Ma’ana ta biyu kuwa cewa ya yi, siyasa na nufin gudanar
da fannin mulki da ayyukan ƙasa a cikin ƙasar ko a wajenta, inda ta haka ne ake
samun siyasar cikin gida da ta ƙasashen waje.
Ta fuskar ma’ana ta ilimi kuwa,
masana da dama sun bayyana fahimtarsu dangane da ma’anar siyasa, inda suka dubi
kalmar ta fuskoki mabambanta. Daga cikin su akwai:
A
ra’ayin Mashi, (1986:16) ya bayyana siyasa ne ta fuskoki uku: Hanya ta farko ya
bayyana ta da ma’anar salo. Sauran hanyoyin kuwa wato ta biyu da ta uku, ya bayyana
siyasa da cewa sulhu ko sauƙi. Waɗannan ma’anoni da ya bai wa siyasa ba za su rasa
nasaba da yadda siyasa ta kasance hanyar lallashi ko lallaɓa mutane domin neman
goyon bayansu ba. Haka kuma ya kalli siyasa a matsayin yaudara ko ƙarya, saboda
yadda ‘yan siyasa kan tsara wani lamari na yaudara domin neman biyan buƙata. Don
haka ne ma wasu suke yi wa siyasa kallon cin amana da ƙarya da yaudara da butulci,
har ya sa ma ake ganin duk wanda bai cika waɗannan abubuwa ba, to bai ma cika ɗan
siyasa ba.
Mashi, (1986:17) ya ci gaba da cewa za a iya kallon
siyasa a matsayi guda biyu, wato za a iya samun siyasar jam’iyyu da kuma siyasar
duniya baki ɗaya. Siyasar jam’iyyu ta shafi wata ƙungiya ta siyasa wadda take neman mulkin al’umma.
Ita kuwa siyasar duniya ta shafi ra’ayoyin al’umma waɗanda kan kasance ba ƙasa ɗaya
ko al’umma guda ya shafa ba. Misali; bambancin launin fata da fafutukar neman ‘yanci
da siyasar addini da sauransu.
A ra’ayin Funtua, (2003:19-20)
ya nuna siyasa da cewa, ararriyar kalma ce ta Larabci wadda take nufin sauƙi ko
rangwame ko jin ƙai. A da, da zarar an ce wa mutum ɗan siyasa to ana nufin mutum
mai jin ƙai, kuma mai rangawame, wato dai mutum mai jin tausayin al’umma. Ya ƙara
da cewa, za a iya bayyana siyasa a matsayin hanyar sanin tafiyar da jama’a ce, kuma
nasiha ce, kuma gargaɗi ce. Wannan ne ma ya sa masana adabin Larabci suke cewa siyasa na nufin
tafiyar da mulki cikin adalci. Ya kuma bayyana cewa a wurin Balarabe inda wannan
kalma ta samo asali, idan aka ce mutum ɗan siyasa ne, to ana nufin mai tafiyar da
mulkin jama’a, mai hikima, sannan wanda yakan zauna ya yi shawara da jama’a bisa
lura. Duk wanda ya kasance da waɗannan abubuwa to ya zama ɗan siyasa ke nan.
Shi
kuwa Idris, (2016:49) ya bayyana siyasa da cewa hanya ce ta tafiyar da mulkin jama’a
a zamanance ko a gargajiyance, ko kuma dabara ce ta jawo hankalin mutane ta hanyar
karkata ta inda suka sa gaba a kowane fage. Misali idan ɗan siyasa ya lura da abin
da mutane suka fi so,
to shi ma sai ya karkata ta can ko da kuwa da gaske har cikin zuciyarsa
ba yana nufin hakan ne ba. Idris, (2016:49) ya ƙara da cewa, idan aka yi la’akari
da waɗannan halaye na ‘yan siyasa za a iya cewa, duk wanda ya iya shan kan mutane,
da lallaɓa su da iya jan ra’ayinsu ko da kuwa ta hanyar yaudara ce za a iya cewa
ya iya siyasa.
A
taƙaice dai, idan aka dubi waɗannan ma’anoni da aka bai wa siyasa za a ga cewa yawanci
ma’anonin sun yi tarayya wajen amfani da waɗansu muhimman lamura, kamar su; tausasawa
da jin ƙai da jan hankali da rangwame da mulki da ƙarya da yaudara da wayo da sauransu.
Ke
nan, a fahimtar wannan bincike, siyasa tana nufin neman ra’ayin jama’a ta hanyar
amfani da lafuzza masu daɗi da suka ƙunshi tausasawa da nuna jin ƙai da rangwame
da ƙarya, domin samun biyan wata buƙata wadda takan iya kasancewa na neman shugabancin
al’umma ko cimma wani buri na rayuwa.
Kodayake,
a yau al’umma sun fi kallon siyasa a matsayin wayo ko zance mai daɗi ko lallashi
ko ƙarya ko danne haƙƙi ko yaudara. Funtua, (2003:18). Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da irin salon
da shugabanni suka ɗauka wajen gudanar da shugabancin al’umma a yau ba.
4.2 Samuwar Siyasar Zamani ga Hausawa
Kalmar zamani suna namiji tilo,
jam’inta shi ne zamunna ko zamanai. Kalmar tana nufin yayi ko lokaci; a ma’ana ta
biyu kuma an bayyana kalmar da cewa, lokacin da ake ciki ko mai ci (CNHN, 2006:
489). Dangane da wannan aiki kuwa kalmar zamani tana nufin lokacin da al’ummar ƙasar
Hausa suka samu cuɗanya da baƙin al’umma wanda ake danganta wannan cuɗanyar da samuwar
rubutu wanda ya haifar samuwar ilimin addinin Musulunci da kuma hanyar rubutun zamani.
Idan aka dubi zamani ta wannan
fuskar za a iya cewa zamani shi ne, duk wata rayuwa da aka yi ta bayan rayuwar gargajiya
kafin cuɗanyar Hausawa da baƙi. Ke nan, idan aka yi batun siyasar zamani kuma za
a iya bayyana shi da cewa, siyasar da ta samu bayan zuwan baƙi ƙasar Hausa, wanda
ta yi nuni da hanyoyin gudanar da shugabanci da jagorancin al’umma bisa wani daidaitaccen
tsarin addini ko kuma tsarin Turawa.
4.2.1 Siyasar Addini
Idan aka yi batun siyasar addini
a ƙasar Hausa kai tsaye siyasar Musulunci ce za ta fara zuwa a rai. Wannan ba zai
rasa nasaba da yadda addinin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa kuma ya sauya rayuwar
Hausawa ta fuskoki da dama ba. Siyasar Musulunci ta samu ne bayan cuɗanyar da aka
samu tsakanin Hausawa da Larabawa a wuraren ƙarni na goma sha biyar. Yahaya, (1988:10)
da Idris (2016:37) sun bayyana cewa, Larabawa sun zo sun tarar da Hausawa da tsarin
siyasarsu ta gargajiya sai dai bayan Hausawan sun karɓi Musulunci sai suka koma
bin tsarin na Musulunci wajen gudanar da mulki da shugabanci. An faɗa cewa, wani malami mai suna Abdulkarim Almagili ya taso daga ƙasar Maroko, ya
iso ƙasar Katsina zamanin sarkin Katsina Ibrahim Maje a ƙarni na sha biyar, wuraren
shekarar 1494. Duk da cewa ko da ya iso ya tarar da malamai da masallatai a Katsina,
amma dai kafin ya tafi sai da ya kafa makarantar koyon addinin Musulunci da ilimin
shari’a da yadda za a gudanar da ita. Daga nan sai ya zarce Kano, inda ya tarar
da Muhammadu Rumfa kan mulki. Sarki ya roƙe shi kan ya rubuta masa littafi da zai
zamo masa jagora wajen gudanar da mulki da shari’a bisa tafarkin Musulunci, sakamakon
hakan ne Almagili ya rubuta masa wani littafi mai suna Taj Al-Din Fi Ma Yajibu Alal Mulk. (Idris, 2016: 37).
Hiskett, (1975:12) yana ganin
cewa Musulunci ya shigo ƙasar Hausa ne tun a wuraren ƙarni na goma sha huɗu. Hujjarsa
ita ce, samun sunayen da suke da alaƙa da Musulunci a cikin jerin sunayen sarakunan
da suka yi mulki a yankunan ƙasar Hausa a wannan ƙarnin. Musulunci bai yi ƙarfi
sosai a wancan lokacin ba, sai bayan da aka samu zuwan wasu malamai Larabawa daga
yankin Afrika ta Arewa a ƙarni na sha shida, wuraren shekarun 1504, cikinsu ne aka
samu fitaccen malamin addinin Musluncin nan wato Muhammad Bin Abdulkarim Al-Maghili
wanda ya koyar da fannonin ilimin Musulunci da dama a garuruwan Katsina da Kano.
Musulunci
ya ci gaba da yaɗuwa a yankunan ƙasar Hausa, sai dai bayan wasu shekaru, an fara
samun sauyin halaye da ɗabi’u na al’ummar Musulmi a wancan lokaci, inda suka riƙa
cakuɗa abubuwa na addinin Musulunci da gargajiya da tsafi da sauran wasu abubuwan
da Musulunci bai yarda da su ba. Wannan ne ya sa a farkon ƙarni na sha tara aka
samu waɗanda suka gudanar da jihadin gyaran halaye, waɗanda mafi yawansu Fulani
ne ƙarƙashin jagorancin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Da farko sun fara ne da wa’azi,
daga bisani kuma waɗanda suka ƙi jin wa’azin aka yi amfani da makami domin gudanar
da jihadi, wanda zuwa shekarar 1812 duk sai da ya kasance an cinye masarautun Haɓe,
aka kuma maye gurbinsu da masarautun Musulunci waɗanda ake kira daular Usmaniyya
wadda take da cibiyarta a Sakkwato(Hiskett, 1975:13).
Bayan
jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da ɗan’uwansa Abdullahi Fodiyo, an ci gaba da gudanar
da tsarin shugabanci bisa turbar Musulunci, inda a lokacin har Abdullahi Fodiyo
ya rubuta wata waƙa mai taken “Tsarin Mulki na Musulunci” wanda a ciki ya yi bayanin
yadda tsarin mulki na Musulunci yake da yadda ya kamata shugaba da mabiyansa su
kasance, da waƙar “Murnar Cin Birnin Alƙalawa”. Shi kuma Shehu Usmanu Ɗanfodiyo
ya rubuta waƙar “Wallahi-Wallahi” waɗanda duk sun ƙunshi siyasar Musulunci ne.
Bayan
kusan ƙarni guda da kafuwar tsarin mulki na addinin Musulunci a ƙasar Hausa, sai
Turawa suka shigo da nasu tsarin mulki da addini da kasuwanci irin na ƙasashensu.
Wannan shigowar tasu ita ce ta kawo tarnaƙi ga ɗorewar tsarin mulki irin na Musulunci
a hukumance a ƙasar Hausa.
4.2.2 Siyasar Jam’iyya
Kalmar
Jam’iyya tana nufin ƙungiyar jama’a ta siyasa ko ta sana’a ko ta wasu harkoki na
rayuwa, wadda take da manufa guda, da tsarin ƙa’idoji da zaɓaɓɓun shugabanni. (CNHN,
2006: 212).
Paul
da Roxana (2020: 114) sun bayyana jam’iyya da cewa ƙungiyar siyasa, ko rukunin jama’a,
ko sauran ƙungiyoyi.
Yusuf
(2018: 26) ya bayyana ma’anar jam’iyya da cewa haɗuwar jama’a ne a matsayin ƙungiya,
ko dai ta siyasa ko ta sana’a ko ta wasu harkokin rayuwa, waɗanda suke da manufofi
da ƙa’idojin da suke tafiyar da su.
A
taƙaice za a iya ba da ma’anar jam’iyya da cewa rukunin jama’a ne da suke da manufa
iri guda waɗanda suke gudanar da harkokinsu a bisa wasu ƙa’idoji da sharuɗɗa da
suka sanya wa kansu domin tafiyar da ƙungiya domin neman shugabanci ko wasu harkoki
na rayuwa.
Ke
nan, siyasar jam’iyya tana nufin neman ra’ayin jama’a ƙarƙashin wata ƙungiya guda,
ta hanyar jan hankali da lafuzza masu daɗi, ta hanyar tausasawa da nuna tausayi
da jin ƙai, domin cimma wata biyan buƙata, musamman na neman shugabanci ko jagorancin
al’umma.
Idan
aka yi batun siyasar jam’iyya, to za a iya alaƙanta shi da cuɗanyar da aka samu
tsakanin Turawa da al’ummar ƙasar Hausa. Turawan da suka shigo ƙasar nan sun kasu
zuwa gida biyar. Rukunin farko su ne ‘yan leƙen asiri, na biyu su ne ‘yan kasuwa,
waɗanda suka shigo domin hada-hadar cinikin bayi da sauran wasu kayayyaki na ƙasar
Hausa. Na uku kuwa su ne, waɗanda suka zo da niyyar yawon buɗe ido domin fahimtar
yadda ƙasar Hausa da al’ummar Hausawa suke. Ayari na huɗu sun kasance ayarin ‘yan
Mishan ne, waɗanda suka zo da niyyar ya ɗa addinin Kirista da ilimin boko, sai kuma
rukuni na biyar, su ne ‘yan mulkin mallaka, waɗanda suka zo domin shimfiɗa sabon
salon mulki irin na ƙasar Ingila a ƙasar (Yusuf, 2012: 25) da (Bunza, 2015: 11-12)
da (Yusuf, 2018: 16).
Dudley,
(1968:77) ya ce, wuraren shekarar 1903 Turawa sun mamaye ƙasar Hausa, inda suka
musanya daular Usmaniyya ta zama ƙarƙashin ikonsu, domin shimfiɗa mulkin mallaka.
Kasancewar sun sami yankin na ƙasar Hausa yana da tsarin shugabanci na sarakuna,
sai suka yi amfani da sarakunan wajen shimfiɗa tsarin nan na mulkin ‘angulu da kan
zabo’ ta hanyar amfani da sarakuna wajen gudanar da mulkin mallaka.
Sarakunan
da suka nuna tirjiya kuwa, wasu an kashe su, wasu kuwa an cire su daga kan mulki
aka maye gurbinsu da waɗanda Turawan suke so. Misali; Sarkin Musulmi Attahiru Ahmadu na ɗaya,
wanda Turawan suka kashe, da Sarkin Haɗejia Muhammadu Mai-Shahada, wanda shi ma
kashe shi suka yi, da kuma Sarkin Kano Alu wanda aka cire shi daga kan mulki. A
Zazzau an sauke Sarki Kwasau aka naɗa Aliyu Ɗan Sidi, a Gwandu kuma aka cire Sarkin
Gwandu Muhammadu Aliyu, aka maye gurbinsa da Sarkin Kalgo Halliru (Birniwa, 1987:14)
Duk
da cewa tsarin sarautar gargajiya ya ci gaba, amma sai ya kasance duk wani umarni
ko hani yana zuwa ne daga wajen Turawan mulkin mallaka ƙarƙashin tsarin En’e-En’e.
Wannan tsarin ne ya ci gaba har zuwa lokacin da hada-hadar karɓar ‘yancin kai ya
kankama a wuraren shekarun 1959. Kafin wannan lokaci an yi ta hanƙoron karɓar mulkin
kai, amma sai ‘yan Arewa na wancan lokaci suka ga cewa, ba su da isassun masu ilimin
zamanin da za su iya tsayawa a madadinsu. Bayan shigowar Turawan mulkin mallaka
a wuraren shekarar 1903, sun kafa makarantar boko a 1905 a Sakkwato, wadda ba ta
yi nasara ba, sai aka sake buɗe wata a 1909 a Kano (Yahaya, 1988:90). Wannan
makarantar elementare ce, ba a kuma samu kafa makarantar sakandare a lardin Arewa
ba sai a shekarar 1922, inda aka kafa Kwalejin Katsina, bayan kuwa a ɗaya ɓangaren
mutanen Kudu sun yi nisa kan sha’anin ilimin boko(Dudley, 1968:72). Wannan ya sa ‘yan Arewa suke ganin
cewa za su zama saniyar ware, don za a yi siyasar wannan lokaci ba da su ba ke nan.
Haka kuma, su ‘yan kudu suna so a rungumi tsarin ‘jamhuriya’ wanda a ganin ‘yan
Arewa, kasancewarsu Musulmi ya saɓa wa koyarwar addinin Musulunci. Waɗannan dalilai
su ne suka sa ‘yan Arewa suka dage cewa maimakon tsarin jamhuriya da ‘yan Kudu suke
muradi, ya kamata a rungumi tsarin ‘Mulukiya’ ne, domin a ci gaba da tsarin mulki
ƙarƙashin sarakuna. Wannan zai ba da dama su ma a dama da su cikin harkokin mulki
maimakon su zama ‘yan kallo.
(Birniwa, 1987:17-23).
Cikin
shekarar 1934 ne ƙungiyoyin suka fara zama da gindinsu a Kudancin Nijeriya, amma
a yankin Arewa ko labarin ba a ji. Daga bisani wasu ‘yan Arewa masu kishi da son
ganin ci gaban yankin suka yunƙura, domin kakkafa irin waɗannan ƙungiyoyi.
Wannan kuwa ya faru ne kasancewa zaman da suka yi da ‘yan Kudu, sai suka koyi yadda
ake mulki irin na siyasa. Mutane irin su Malam Sa’adu Zungur wanda ya riƙe muƙamin
sakatare a jam’iyyar NCNC wadda reshe ne na siyasar Kudu a Arewa tare da goyon bayan
su Azikwe, da Malam Aminu Kano da wasu da dama sun yunƙura domin kafa irin waɗannan
ƙungiyoyi (Idris, 2016: 50-51).
Birniwa, (1987:27-28) ya bayyana
cewa tun a wuraren shekarun 1930-1940 ne aka fara jin ƙamshin samuwar ƙungiyoyin
siyasa a Arewacin Nijeriya. An samu ɓullar ƙungiyoyi da dama duk da cewa ba su fito
fili ƙarara a karon farko sun kira kansu da jam’iyyun siyasa ba, amma dai sun samar
da cibiyoyin da sukan riƙa haɗuwa lokaci-lokaci domin tattauna al’amuran siyasa.
A
ra’ayin Dudley,
(1968: 78) yana ganin cewa an fara samun ɓullar ƙungiyoyi ne a tsakankanin
shekarar 1943-1944. Ƙungiyoyin da aka samar wannan lokacin sun haɗa da; Ƙungiyar
Inganta Rayuwar Mutanen Bauchi (BGIU) wadda Sa’adu Zungur ya kafa a 1943, da Ƙungiyar
Tattaunawa ta Mutanen Bauchi (BDC) a 1944, da Ƙungiyar Zumunta ta Sakkwato (YSC)
a 1945, da Ƙungiyar Matasa ta Kano (KYA) a 1948 da Ƙungiyar Matasan Zariya (ZYA)
ita ma a 1948 da sauransu.
An
faɗa cewa, lokacin da sarkin Bauchi ya fahimci cewa wannan ƙungiyar ta Bauchi akwai
alamun siyasa a cikinta, sai ya sa aka rufe ƙungiyar tare da dakatar da duk wasu
harkokin ƙungiyar(Birniwa, 1987:28).
Kamar
yadda aka gani, kakkafuwar ƙungiyoyi ne ya haifar da samuwar jam’iyyar siyasa ta
farko wato NCNC a shekarar 1944, wadda aka samu ‘yan Arewa da suka riƙe muƙamai
a cikin wannan jam’iyyar kamar su Malam Sa’adu Zungur da Sa’ad Abubakar Zukogi da
Habib Raji Abdallah da sauransu, domin a faɗaɗa jam’iyyar ta zama ta ƙasa baki ɗaya,
ba ta ‘yan Kudu kaɗai ba. Wannan ya ba wa ‘yan Arewa damar koyon yadda ake siyasa
daga Kudu, ta yadda suka zo suka kafa ƙungiyoyin da suka zama silar kafuwar jam’iyyun
siyasa a Arewa.
Daga
cikin misalan waɗannan ƙungiyoyi da aka kakkafa a Arewa, akwai Ƙungiyar Inganta
Rayuwar Mutanen Bauchi (BGIU) da Ƙungiyar Tattaunawa ta Mutanen Bauchi (BDC) da
Ƙungiyar Zumunta ta Sakkwato (SYC) da Ƙungiyar Matasa ta Kano (KYC) da Ƙungiyar
Abokai ta Kano (FAK) akwai Ƙungiyar Malamai ta Arewa (NTA) da Ƙungiyar Matasan Zariya
(ZYA). Waɗannan ƙungiyoyi da ma wasu duk an kafa su ne a
tsakankanin 1943 ne zuwa 1948, waɗanda su ne ake ganin suka narke suka zama jam’iyyar
NPC a shekarar 1951, daga baya kuma wasu suka ɓalle suka kafa jam’iyyar NEPU. (Dudley,
1968: 78-79) da (Idris, 2016:51).
Daga
bisani, Ƙungiyar Matasan Zariya (ZYA) ta kira sauran ƙungiyoyi domin tattauna yadda
za su haɗa kai su samar da wata ƙungiya wadda za ta haɗe lardin Arewa baki ɗaya,
amma wannan yunƙuri bai ci nasara ba, kasancewar wani kwaskwarima da Sir John MacPherson
ya yi alƙawarin yi wa kundin tsarin mulki, wanda daga baya ya ba da umarnin faɗaɗa
harkar ƙungiyoyi. Wannan dama ce ta sa a watan Satumbar 1948 aka kira taro domin
tattauna irin sauye-sauyen da aka samu a cikin tsarin siyasar Nijeriya. Wannan taron
shi ne ya haifar da kafa ƙungiyar siyasa mai suna Jam’iyyar Mutanen Arewa(JMA) a
watan Oktoba 1948, wadda daga bisani Malam Sa’adu Zungur ya raɗa mata suna cikin
harshen Ingilishi ya kira ta da “Northern People Congress”(NPC) (Dudley, 1968: 80-81)
da (Yakubu, 1999:75).
Dangane
da kafuwar jam’iyyar NPC kuwa, Dudley, (1968) da Birniwa, (1987) da Yakubu, (1999)
da Idris (2016) duk sun yi bayani tare da kawo manufofin jam’iyyar da dalilan kafa
ta.
An
ƙaddamar da jam’iyyar NPC ranar 1 ga watan Oktoba, 1951, bisa ra’ayin sarakuna da
shugabannin jam’iyyar a bisa manufofi da dama. NPC jam’iyya ce da ta samo asali
daga ƙungiyoyi daban-daban na Arewa(Idris, 2016: 51).
Jam’iyyar
ta samo tsittsigenta ne daga Jam’iyyar Mutanen Arewa (JMA) wadda ƙungiya ce daga
cikin ƙungiyoyin da aka kafa, domin ci gaban yankin na Arewa. Ƙungiya ce da ta sadaukar
da kanta wajen yaƙi da jahilci da lalaci da zalunci, waɗanda su ne manufofin da
aka kafa jam’iyyar NPC a kansu tun a farko(Malumfashi, 2013:12). Daga cikin magoya
bayan jam’iyyar waɗanda aka kafa jam’iyyar da su akwai; Sa’adu Zungur da Aminu Kano
da Abubakar Tafawa Ɓalewa da Aliyu Makaman Bida. Daga bisani wasu da yawa sun bar
jam’iyyar domin ta kauce wa manufofin da aka kafa ta a kansu(Birniwa, 1987: 28).
Bayan
kafuwar jam’iyyar, sai ya kasance babbar manufarta ita ce yaƙi da jahilci da lalaci
da zalunci da yin gyaran fuska ga hukumar En’e, don ta dace da zamani. Wannan ne
ya sa daga farko Arewa ta kasance mai jam’iyya ɗaya, saboda ganin cewa NPC jam’iyyar
neman sauyi da fafutukar samun ‘yanci ce, wannan ne ya sa aka hana jami’an gwamnati
na wancan lokaci shiga cikinta(Yakubu, 1999: 76). Jam’iyyar ta dawo daga rakiyar
manufofinta ne bayan ta lura cewa, ba ta samu goyon bayan sarakuna da muƙarrabansu
da samari da ma’aikata ba, sai suka yi watsi da manufofinsu na farko, domin su samu
jama’ar da za su cika jam’iyyar, wanda hakan zai ba su damar lashe zaɓe. Wannan
sauyin manufofi da jam’iyyar ta yi ya jawo mata karɓuwa da kwarjini a wajen sarakuna
da ma’aikatan En’e har ma da manyan masu faɗa a ji na Arewa. Hakan ya jawo mata
gagarumar nasarar da ta yi a zaɓuɓɓukan da aka gudanar a Arewa, har ma da matakin
gwamnatin tarayya, in ban da a watan Satumba na shekarar 1951 inda jam’iyyar NEPU
ta yi nasarar lashe kujeru 12 cikin 26(Dudley, 1968: 80) da (Idris, 2016: 52).
Wani
dalili kuma da ake ganin ya ƙara wa jam’iyyar NPC farin jini a wancan lokaci shi
ne, kasancewar Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato a cikin jam’iyyar, wanda kasancewarsa
jinin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya sa talakawa har ma da masu dukiya suka rungumi jam’iyyar.
Daga
bayanan da aka kawo, an fahimci cewa, jam’iyyar NPC ce ta kafa gwamnati a Arewa
har ma da ƙasa baki ɗaya, sakamakon rinjayen da alƙaluman zaɓe suka nuna cewa jam’iyyar
ce ta sami kaso mafi tsoka na ƙuri’un da aka kaɗa.
Baya
ga jam’iyyar NPC, jam’iyyar NEPU ita ce jam’iyyar hamayya mafi girma a Arewa da
ma ƙasa baki ɗaya a wancan lokaci. Wannan jam’iyya ta samo asali ne daga ƙungiyar
NEPA wadda tun farko ita aka fara kafawa tun a wuraren shekarar 1947. Daga bisani,
sai ‘ya’yan ƙungiyar a Kano suka kafa ƙungiyar Taron Masu Zumunta (TMZ) da Ƙungiyar
Matasan Kano (KYC) waɗanda su ne suka haɗe daga baya suka kafa jam’iyyar NEPU, bayan
an hana JMA bayyana kanta a matsayin jam’iyyar siyasa(Dudley, 1968: 80).
Masana da
manazarta siyasa irin su Dudley, (1968) da Dambazau, (1981) da Birniwa, (1987) da
Yakubu, (1999) da Malumfashi, (2009) da Idris, (2016), sun tofa albarkacin bakinsu
dangane da kafuwa da manufofi da shugabanni da magoya bayan jam’iyyar NEPU, da ma
duk wani abu da ya shafi jam’iyyar.
An
bayyana cewa an kafa jam’iyyar NEPU ranar 8 ga watan 8 da misalin ƙarfe 8 da mutane
8 a shekarar 1950, wato shekara guda kafin ayyana NPC a matsayin jam’iyyar siyasa,
bayan wani taro da wasu mutane 8 da suka haɗa da; Bello Ijumu da Abba Maikwaru da
Mudi Sipikin da Magaji Ɗambatta da Baballiya Manaja da Musa Kaula da Abdulƙadir
Ɗanjaji da kuma Garba Bida suka yi(Dambazau, 1981: 14). Wannan bayani ya fito a
cikin jaridar Sodangi ta ranar 2 ga Maris, 1960 kamar haka:
“ Mutum takwas ne suka
kafa NEPU ran takwas ga watan takwas bayan ta yi ɗimbin shekaru sai ga shi da lokacin
zaɓen majalisar Najeriya ya zo ta sami wakilai takwas da ƙyar.”
(“Mutum 84 Sun Fita Daga NEPU”, 1960).
Wannan
ya nuna cewa haƙiƙanin ranar da aka kafa jam’iyyar hamayya mafi girma ta farko a
Arewacin Nijeriya ita ce ranar takwas ga watan takwas kamar yadda tarihi ya nuna.
An tabbatar cewa mutane takwas ne suka zauna suka kafa ta kamar yadda aka zayyano
sunayensu a sama.
Tun farko sun kafa jam’iyyar ce da manufar haɗa
kan ‘yan ƙasa, ba tare da nuna bambancin addini ko ƙabila ko harshe ba, sannan a
wayar wa talakawa kai kan sha’anin mulki da tabbatar da an mayar da mulkin jama’a
ga hannunsu da kuma fafutukar neman ‘yancin kai daga Turawa. A wani wurin daban
ma an ƙara samun bayani makamancin wannan dangane da kafuwar jam’iyyar NEPU kamar
haka:
“Don na sani an kafa NEPU
ran 8/8/1950 watau yau shekara tara da wata biyar, in an bi shekarar Turawa yau
shekara goma ke nan ”
(Yakasai,
1960).
Ke
nan idan aka dubi hujjojin biyu sun nuna kafuwar jam’iyyar a wannan rana da aka
ayyana, har ma da lissafin adadin shekarun da jam’iyyar ta yi da kafuwa a wancan
lokacin, wato shekaru kimanin goma ke nan daga shekar 1950-1959.
Idris,
(2016:53) yana ganin cewa jam’iyyar NEPU ta samo asali ne daga ƙungiyoyi biyu masu
kama da juna. Ƙungiya ta farko ita ce, masu ra’ayin neman sauyi da suka baro jam’iyyar
NPC, bayan an ƙaddamar da jam’iyyar a 1950, sai kuma uwar ƙungiya, wato NEPA wadda
tun da farko aka kafa a shekarar 1947 da niyyar haɗa kan jama’ar Arewa da wayar
musu da kai kan sha’anin siyasa, domin ita da ma NEPA ba ta ƙaunar tsarin mulkin
mallaka da kuma sarakunan da suka ɗaure musu gindi. Shi ya sa NEPU ta ɗora daga
inda NEPA ta tsaya, wato ƙoƙarin ciyar da tattalin arziƙi gaba, sannan ta ci gaba
da faɗa da zaluncin Turawa da danniyar sarakuna, domin fitar da talaka daga ƙangin
bauta. NEPU jam’iyya ce ta talakawa, shugabanninta da magoya bayanta ba su wuce
malaman makaranta ba, sai ‘yan garuwa da manoma da masaƙa da majema da maɗinka da
masassaƙa da masu faskare da sauransu(Birniwa, 1987: 29-32).
Kasancewar
NEPU ba ta neman fada a wajen Turawa da sarakuna kamar jam’iyyar NPC, wannan ya
sa ta zama jam’iyyar hamayya. Hakan kuma ya jawo rashin jituwa tsakanin NEPU da
hukuma, wanda ya sa gwamnatin mulkin mallaka ta shirya tare da tsara yadda za a
yi NPC ta gaje ta ba NEPU ba.
Baya
ga siyasar jamhuriya ta ɗaya da jam’iyyun da suka yi rawar gani a cikinta, an samu
waɗansu jumhuriyoyi daban-daban, waɗanda su ma an kafa jam’iyyu kuma an gudanar
da zaɓuka a cikinsu.
A
jamhuriya ta biyu, a tsakanin shekarar 1978-1983, an samu kakkafa jam’iyyu bayan
gwamnatin Obasanjo ta cire takunkumin siyasa tare da kafa hukumar zaɓe ta ƙasa.
Ƙungiyoyi da dama, sun nemi a yi musu rajista, amma daga cikinsu biyar ne kawai
suka sami nasarar zama jam’iyyu, bayan an yi musu rajista. Jam’iyyun su ne; NPN
da UPN da NPP da PRP da GNPP. Bayan an gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, hukumar zaɓe
ta tabbatar da jam’iyyar NPN a matsayin wadda ta lashe zaɓe, inda Alhaji Shehu Shagari
ya zama shugaban ƙasa. An kuma gudanar da zaɓen jihohi, wasu daga cikin sauran jam’iyyun
sun samu nasarar lashe kujerun gwamnoni a wasu jihohi (Funtua, 2003: 37).
Sojoji
sun kawo ƙarshen gudanar da mulkin farar hula ta jamhuriya ta biyu ne a shekarar
1984, inda suka ci gaba da jan ragamar mulkin ƙasar har na wani lokaci. An gudanar
da wata gwamnatin gamin gambiza, wato ita ba soja zalla ba, ba kuma farar hula ba
a yunƙurin sake komawa ga tafarkin dimokuraɗiyya da gwamnatin soja ta janar Ibrahim
Badamasi Babangida ta yi.
An
yi ƙoƙarin kafa jamhuriya ta uku, domin a wuraren shekarar 1987 an fara ganin alamun
hakan, sannan kuma har an kafa ƙungiyoyin siyasa, kuma sun miƙa wa hukumar zaɓe,
domin buƙatar a yi musu rajista. Bayan hukumar zaɓe ta miƙa wa gwamnati shawararta,
sai gwamnati ta soke su duka, sannan ta ƙirƙiro jam’iyyu guda biyu, NRC da SDP,
waɗanda a ƙarƙashinsu ne aka gudanar da zaɓen 12 ga watan Yuni, 1993, wanda kuma
daga baya gwamnati ta soke. A dalilin wannan soke zaɓe, rikici ya ɓarke a cikin ƙasa, wanda
ya kawo ƙarshen gwamnatin Janar Babangida ranar 27 ga watan Agusta, 1993(Funtua, 2003: 40-41). An miƙa
gwamnatin a hannun Cif Shonekan a matsayin riƙon ƙwarya ya ci gaba da jagorancinta.
Wannan gwamnatin ba ta yi dogon zango ba, domin kuwa sojoji sun sake yin juyin mulki
a shekarar 1993. Hakan ya mai da janar Abacha ya zama shugaban ƙasa, inda suka soke
duk wani tsari na miƙa mulki, wanda ya kawo ƙarshen jam’iyyun NRC da SDP. Daga baya
sai gwamnati ta ci gaba da gudanar da wannan tsarin mai kama da angulu da kan zabo,
wato soja-soja, farar hula, inda har aka kafa jam’iyyun siyasa daban-daban waɗanda
suka haɗa da; UNCP da DPN da GDM da NCPA da CNC(Funtua, 2003: 40-41). Wannan yunƙuri
bai yi nasara ba, sakamakon rasuwar shugaba Abacha a shekarar 1998, inda janar Abdulsalam
Abubakar bayan zamansa shugaban ƙasa ya rusa waɗannan jam’iyyun da ma tsarin baki
ɗaya tare da shimfiɗa wani sabo a shekarar 1999(Ɗan’illela, 2010: 23).
Ɗan’illela,
(2010: 23) ya ci gaba da cewa, sabuwar gwamnatin Abdulsalami ta yi alƙawarin miƙa
mulki ga hannun farar hula a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 1999, wanda shi
ne ya share hanya zuwa jamhuriya ta huɗu. A wannan yunƙuri, an yi wa jam’iyyu rajista,
wato jam’iyyun PDP da APP da AD da APGA da kuma PAP. Waɗannan jam’iyyu sun samar
da ‘yan takara wanda a ƙarshe ɗan takarar jam’iyyar PDP Cif Olusegun Obasanjo ne
ya yi nasarar zama shugaban ƙasa a zaɓen da aka gudanar a watan Janairun 1999(Funtua,
2003: 41).
A
cikin tarihin siyasar ƙasar nan, jamhuriya ta huɗu wato wadda muke ciki yanzu, ita
ce ma fi tsawo idan an kwatanta ta da sauran jumhuriyoyin da aka yi a baya. A cikin
wannan zamanin siyasa da ake ne aka samu zangunan siyasa har guda shida, yanzu haka
ana cikin zango na bakwai. Zango na farko na jamhuriya ta huɗu ya faro ne daga watan
Mayu 1999 zuwa farkon shekarar 2003, zango na biyu kuwa ya fara daga watan Mayu
2003 zuwa farkon shekarar 2007, sai zango na uku wanda ya fara daga watan Mayu na
shekarar 2007 zuwa farkon shekarar 2011, sai zango na huɗu ya fara daga 2011 zuwa
shekarar 2015 (Idris, 2016:58). Akwai kuma zango na biyar wanda ya fara daga 2015
zuwa 2019, sai zango na shida daga 2019 zuwa 2023. A yanzu muna zango na bakwai
ne wanda ya fara daga 2023. A zango na farko an kafa jam’iyyu biyar ne kacal, su
ne; PDP da APP da AD da APGA da PAP waɗanda su ne suka yi zamani har zuwa zango
na biyu, amma a zango na biyu an yi wa jam’iyyar APP gyaran fuska inda ta koma ANPP.
A zango na huɗu kuma an samu ƙaruwar jam’iyyun siyasa, sai dai waɗanda suka yi tashe
a yankin Arewa su ne: PDP da ANPP da AC da DPP, sannan kuma a nan Arewa an samu
ƙarin jam’iyyar CPC, an kuma yi wa jam’iyyar AC kwaskwarima ta koma ACN. Daga zango
na huɗu zuwa farkon zango na biyar, an samu jam’iyyun siyasa da aka yi wa rajista
kimanin guda hamsin a wannan ƙasa.
Haka
kuma, a zango na biyar na jamhuriya ta huɗu, an samu wani irin sauyin da a tarihin
siyasar Nijeriya ba a taɓa samun irinsa ba, wato inda aka samu jam’iyyar hamayya
ta yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa. Wannan ko ya faru ne sakamakon haɗewar da wasu
jam’iyyu guda huɗu suka yi. Jam’iyyun su ne; ANPP da ACN da CPC da wani ɓangare
na magoya bayan jam’iyyar APGA, suka zama jam’iyya guda wadda aka raɗa wa suna APC,
wadda a lokacin ta zamo jam’iyyar hamayya mafi girma a Nijeriya, kuma ita ce ta
lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a shekarar 2015.
Bugu
da ƙari, A zango na shida an samu jam’iyyun siyasa kusan 60[1] waɗanda aka tsaya
takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashinsu, kodayake kaɗan ne daga cikinsu aka ji amonsu.
A wannan zango da ake ciki wato zango na bakwai kuwa, an samu raguwar jam’iyyu ne
sakamakon soke rajistar wasu da hukumar zaɓe ta yi, saboda rashin cika wasu ƙa’idoji,
inda jam’iyyun suka zama guda goma sha takwas[2]. Waɗanda suka yi
fice daga cikin jam’iyyun su ne, PDP da APC da LP da NNPP inda daga cikinsu bayan
an gudanar da zaɓe, ɗan takarar jam’iyyar APC Bola Ahmad Tinubu ya yi nasara.
4.3 Ma’ana da Samuwar
Rubutaccen
Adabin Hausa
Kalmar
adabi daɗaɗɗiyar kalma ce a cikin harshen Hausa. Bisa asali, an aro ta ne daga harshen
larabci wadda take nufin halin ɗa’a ko fasaha ko ƙwarewa. Dangane da ma’anarta a
Hausance, Ɗangambo (1984:1) ya bayyana cewa, kalmar adabi tana nufin madubin ko
hoton rayuwa na al’umma. Rubutu kuwa shi ne zanen magana a kan takarda ko allo ko
wani bagire (CNHN 2006: 374). Ke nan idan aka dubi ma’anonin kalmomin guda biyu,
za a iya cewa rubutaccen adabi shi ne hoton al’amuran da suka shafi rayuwar al’umma
wanda aka samar a rubuce.
Ta
fuskar samuwar rubutaccen adabi kuwa, za a iya cewa ya samu ne bayan da ɗan’adam
ya samu fasahar rubutu a doron ƙasa, maimakon ya ci gaba da aiwatar da adabinsa
a gargajiyance wato ta fatar baki, sai ya koma yana zana shi kan abin da yake rubutu
kansa.
Dangane
da al’ummar Hausawa ma ba ta sake zane ba, domin bayan samuwar hanyar rubutu, sai adibai suka fara
amfani da wannan hanyar wajen isar da saƙo a rubuce. Ingantacciyar hanyar rubutu
ta farko da aka samu ita ce Ajami, wanda ya samu bayan cuɗanyar Hausawa da Larabawa
abin da ya haifar da shigowar addinin Musulunci a cikin ƙasar Hausa. Hausawa sun
riƙa sarrafa baƙaƙen Larabci wajen rubuta Hausa da su. A wannan yanayi, malamai sun yi amfani
da hanyar Ajami wajen samar da ayyukan adabi daban-daban. Ɓangaren da ya yi fice
wanda malamai suka yi ayyuka a cikinsa shi ne waƙa. Daga bisani bayan zuwan Turawa
waɗanda suka zo da rubutun boko, an samu ‘yan ƙasa waɗanda suka koya, suka kuma
riƙa samar da ayyukan adabi a cikin rubutun boko. An samu ayyukan adabi da dama
waɗanda aka samar daga cikin dukkan rassan adabi guda uku, wato waƙa da zube da
kuma wasan kwaikwayo.
4.4 Ma’ana da Samuwar Rubutaccen Adabin Siyasa
Kamar yadda aka bayyana ma’anar
rubutaccen adabi a baya, ke nan za a iya cewa rubutaccen adabin siyasa wani nau’in
adabi ne wanda yake ƙunshe da al’amuran siyasa a cikinsa, wanda ya shafi tafiyar
da al’amuran jama’a da shugabanci da dai sauransu.
Tun fil azal, Hausawa suna
da irin nau’in siyasar da suke gudanarwa, wadda ta shafi mulkin gargajiya, wanda
aka kira shi na Musulunci bayan jihadin Shehu Ɗanfodiyo. Tun kafin zuwan Musulunci
Hausawa suna gudanar da shugabancinsu a tsarin gargajiya. A wancan lokacin ba a
samu wasu ayyuka da suke nuna samuwar adabin siyasa ba, sai bayan zuwan Shehu Ɗanfodiyo,
inda aka samu ayyukan malaman jihadi waɗanda mafi yawan su waƙoƙi ne, kuma su ne
suka fara fitowa da ruhin siyasar Musulunci a cikin rubutaccen adabi. Alal misali, Hiskett, (1975:13) ya bayyana irin yadda tasirin cuɗanyar da aka samu
da baƙin al’ummu ya haifar da samuwar hanyar rubutu, wanda ake ganin ya taimaka
ƙwarai wajen samuwar rubutaccen adabi, ciki kuwa har da adabin Hausa. An nuna bayan
samuwar tsarin rubutun Larabci da na Ajami ne aka fara samun rubutattun waƙoƙi,
tun kafin jihadi da kuma bayan jihadi, inda tun a wannan lokacin ake ganin an fara
samun waƙoƙi masu ɗauke da ruhin siyasa. Haka kuma an samu wasiƙu da sarakuna suka
riƙa aike wa junansu wanɗanda suke ƙunshe da abubuwan da suka shafi mulki da siyasa
da al’amuran jagorancin al’ummominsu. Ke nan an samu ɓullar rubutaccen adabin siyasa
ne bayan zuwan Musulunci, musamman kuma bayan jihadin Shehu Ɗanfodiyo.
4.4.1 Rubutattun Waƙoƙin Siyasa
Rubutattun
waƙoƙin siyasa na Hausa su ne suka share wa sauran ɓangarorin rubutaccen adabin
siyasa hanya, domin su aka fara samu a farko kafin sauran ɓangarorin da suka shafi
zube da wasan kwaikwayo. Wannan ba zai rasa nasaba da yadda waƙa ta kasance hanyar
koyo da koyar da ilimin addini a zamanin masu jihadi ba. Kasancewar waƙa ta fi saurin
isar da saƙo ga al’umma, wannan ya sa bayan zuwan Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, ƙanensa
Abdullahi Fodiyo ya rubuta wata waƙa mai suna “Tsarin Mulki na Musulunci” wanda
a ciki ya yi bayanin yadda tsarin mulki na Musulunci yake da yadda ya kamata shugaba
da mabiyansa su kasance, akwai waƙar “Murnar Cin Birnin Alƙalawa” wadda ita ma tana
magana ne a kan tsarin shugabanci a Musulunci. Shi ma Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya
rubuta waƙar “Wallahi-Wallahi” in ya yi bayani kan irin haƙƙoƙin shugaba da irin
narkon azaba da zai haɗu da shi idan bai yi wa mabiyansa adalci ba. Waɗannan waƙoƙin
sun kasance suna kira ne ga yin ɗa’a ga Allah da manzonsa da kuma shugabannin Musulmi
na wancan lokaci, wato sarakuna, domin ci gaban tsarin mulkin da Shehu ya shimfiɗa
bayan jihadi da kuma wayar wa al’umma kai kan abin da ya shafi addini(Hiskett, 1975:12).
Bayan
samuwar rubutun boko, an ci gaba da samun waƙoƙi masu ɗauke da wannan ruhi na siyasa,
duk da cewa lokacin ba a fara batun siyasar jam’iyyu ba, amma kuma siyasar neman
‘yancin kai da ta tsarin mulki da tsarin shugabancin sarakuna, da tsarin mulkin
Turawa su ne cike a cikin waƙoƙin(Hiskett, 1975:13).
Bayan zuwan Turawan mulkin
mallaka a ƙarni na ashirin sun rusa tsarin mulkin daular Usmaniyya wadda take na
Musulunci ne, sannan an samu sabon tsarin siyasa wanda Turawan suka zo da shi, inda
daga ciki aka samu siyasar jam’iyyu da aka kakkafa domin gudanar da zaɓuɓɓuka ƙarƙashinsu.
An samu marubuta da dama waɗanda suka rubuta waƙoƙi domin faɗakarwa ga jama’a, game
da muhimmancin shiga harkokin siyasa da jam’iyyar da ta dace.
Tun kafin samuwar jam’iyyun
siyasa, an kakkafa ƙungiyoyin wayar da kai kan abin da ya shafi siyasa da mulkin
Turawa. Daga baya sai ƙungiyoyin suka rikiɗe suka zama jam’iyyun siyasa(Dudley,
1968: 77-78).
‘Yan kishin ƙasa waɗanda suka
samu ilimin zamani su ne suka yi hoɓɓasa wajen ganin an samu ‘yancin kai. Bayan samuwar hakan
kuma su ne suka zama jagororin siyasar jam’iyyun da aka kafa. Bugu da ƙari kuma,
wasu daga cikinsu ne suka rubuta waƙoƙin siyasa tun a karon farko. Misali; Malam Sa’adu
Zungur ya rubuta waƙoƙi ciki akwai, “Arewa Jamhuriya ko Mulukiya” wadda ba waƙar
siyasar jam’iyya ba ce. Daga bisani, sai ya rubuta Waƙar “Jihadin Neman Sawaba”
wadda waƙar siyasar jam’iyya ce, a matsayinsa na ɗan jam’iyyar NEPU wanda yake yin
suka ga ‘yan jam’iyyar NPC mai mulki. Shi ma Mudi Sipikin ya rubuta waƙar “Arewa
jamhuriya Kawai” wadda ba ta shafi wata jam’iyya ba, amma daga bisani bayan kafa
jam’iyyu, ya rubuta waƙoƙin siyasar jam’iyyu musamman ma na jam’iyyar NPC. Mawaƙa
irin su Gambo Hawaja Jos da Aƙilu Aliyu da Lawal Maiturare da Yusuf Kantu da sauransu
duk sun rubuta waƙoƙin siyasa a wannan lokaci, waɗanda kusan za a iya cewa, su ne
mabuɗin samuwar waƙoƙin siyasar jam’iyya a Arewacin Nijeriya(Ɗangulbi, 2003: 54).
4.4.2 Rubutaccen Zube na Siyasa
Rubutaccen zube na siyasa wani
nau’in adabi ne wanda aka shirya shi cikin wani tsari da ba na waƙa ba, ba kuma
wasan kwaikwayo ba, wanda yake ɗauke da ruhin siyasar da ta shafi tafiyar da al’amuran
al’umma da jagoranci a gargajiyance ko kuma a zamanance. Galibi irin wannan rubutun
yakan zo kara zube ba tare da wata ƙa’ida ba illa ta ƙa’idojin rubutu.
Samuwar jaridu
a ƙasar Hausa sun taimaka ƙwarai wajen ci gaban siyasa musamman ma siyasar jam’iyya.
Jaridar Hausa ta farko da aka fara samu a ƙasar Hausa ita ce jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo a shekarar 1939, wadda
aka samar da ita domin farfagandar yaƙin duniya na biyu(Yahaya, 1988:142). A wani binciken kuma ana
ganin cewa, jaridar Hausa
ta farko ita ce Jaridar Nijeriya Ta Arewa
wadda aka samar a shekarar 1932 (Bunza da Mallam, 2018:293). Duk da cewa an yi amfani
da harsuna uku a cikin jaridar wato Hausa da Ingilishi da kuma Larabci, amma dai
samun wani ɓangare na Hausa a cikinta ya sa ta zama ta farko da aka fara buga labarai
da Hausa.
Tun daga shekarar 1954 kuma Gwamnatin Arewa
ta samar da jaridu na Larduna. Zuwa shekarar 1956 kusan kowane Lardi yana da tasa jaridar. A Lardin Kano, inda nan
ne hedikwatar ko mazaunin NEPU, jaridar Sodangi
da Daily Mail su ne tambarin NPC wajen farfagandar siyasa. Ta amfani da waɗannan jaridu hukumar
mulkin mallaka da jam’iyyar NPC suka shiga yaɗa zantukan hamayya game
da NEPU da magoya bayanta,
sannan
kuma hukuma ta tabbatar ba a ba ‘yan hamayya damar amfani da jaridun ba, balle a ji ta bakinsu. Duk wani aikin ci gaba ko wani abu da hukuma
ta san zai sa NEPU ta sami tagomashi ko goyon baya, to ba a sa shi a cikin jaridun
Sodangi da Daily Mail. Waɗannan jaridun sun kasance mallakin gwamnati ce, don haka
an yi amfani da su wajen yaɗa manufofin gwamnati da kuma yaƙar ‘yan hamayya.
Daga baya jam’iyyar hamayya ta NEPU ta ƙulla ƙawance
da NCNC. Wannan ƙawance
da aka ƙulla shi ne ya sama
masu
wata kafa da
suka riƙa
mayar da
martani game da farfagandar hukuma da jam’iyyar NPC. Wannan ne ya sa aka samar da jaridar Daily Comet da kuma jaridar
Northern Star ta jam’iyyar AG a Kano,
aka keɓe
wani ɓangaren jaridun domin ɗimbin masu karantun
Hausa, domin sun riga sun san cewa farfaganda ta fi armashi a cikin harshen da mutane
ke fahimta (Malumfashi,
2013:12). Samuwar waɗannan jaridun ya tayar wa da magoya bayan jam’iyyar NPC hankali,
wannan ya sa suka yi ta kiraye-kiraye a kan a tsawatar wa ‘yan hamayya kan abin da suka kira cin mutunci da zage-zage da suke yi
a cikin jaridun Daily Comet da Nothern Star. Ga misali:
“ makon da ya wuce an yi masmitin a ƙofar Mata. An yi maganar
zage-zage da wasu marasa albarka suke farfaɗa a cikin ‘Nothern Star’ kullum. Mutane
da yawa sun goyi bayan munin abin da ake rubutawa. Ba shakka ba za mu yadda ba,
don yawan zagin shugabannin ya yi yawa. Har yanzu ba a yi komai a kai ba. tun da
wuri ya kamata shugabannin NPC su tashi tsaye a kan wannan mummunan aiki. Tun ice
na ɗanye ake tanƙwasa shi, in ya bushe sai an sha wuya. Mace da namiji kowa yana
ganin irin cin mutuncin da Northern Star take yi wa shugabanni kullum, don kuwa
ba ita ce kaɗai jarida a Nijeriya ba.”
(“Baƙin Ciki Ya yi Yawa”, 1960).
Lallai wanzami ba ya son jarfa! Duk da yadda
jaridun Sodangi da Daily Mail suka samu ɗaurin gindin gwamnati,
suka riƙa yi wa ‘yan hamayya yarfe da zambo da farfaganda
lokacin ba su da bakin da za su rama, ko kuma ba su da muryar da za su mayar da
martani a ji su, hakan bai zama laifi ba sai da ‘yan hamayya suka samu dama suka mayar da martani sannan
cibi ya zama ƙari.
Baya ga nuna jin zafi da gwamnati da magoya
bayanta suka yi a cikin jaridar Sodangi, sun
kuma buƙaci a riƙa hukunta duk wanda ya yi zagi ko yarfe ko a kira shi a titsiye
shi sai ya faɗi ko da wa yake yi, kamar yadda jaridar take cewa:
“Mu abin da muka ga ya
fi a kan irin wannan sheɗana a taƙaice shi, hukuma ko gwamnati ta sa a kawo mai
irin wannan cin mutunci gaban komati a titsiye shi cikin lumana a tambaye shi cewa,
‘wa kake nufi da mai abu kazako mai yin abu kaza’. In ya ce wane nake nufi to, a
ce ka rantse da Alƙur’ani? In ya ce ‘i’ to sai a je ya yi wanka a gani a kuma ga
rantsuwarsa. In ya yi haka ya kuɓuta. In kuwa ya yi shiru ya yi iƙirari ke nan sai
a hukunta shi a bisa yadda shari’a ta ce.”
(“Zage-Zage”, 1960).
A
nan idan aka duba, za a ga cewa irin abin nan ne da masu hikimar suke cewa; Baƙar
magana ba zagi ba ce, amma ta ɗara zagi ciwo. Duk da cewa gwamnati da mahukunta
da ‘yan jam’iyyar NPC mai mulki sun yi ta amfani da jaridar gwamnati wajen yaɗa
farfaganda da yarfen siyasa ga ‘yan hamayya
a tashin farko, wato kafin ‘yan hamayya su samu kafar da za su
riƙa mayar da martani, amma da ya kasance an samu hanyar da ‘yan hamayyar za su yi magana muryarsu ta yi nisa kuma
ta kai ga inda ake buƙata, sai abin ya riƙa yi wa masu mulki da ‘yan jam’iyya mai
mulki ciwo, har suka fara neman hanyoyin dakushe muryoyin abokan hamayya. Suka riƙa
kiraye-kiraye cewa a kashe jaridun yan hamayya
ma baki ɗaya, domin a cewarsu zagin manya suke yi. An sani cewa kusan duk ‘yan siyasar
da suke cikin jam’iyyar NPC mai mulki sarakuna ne da malamai da attajirai, wannan
ya sa magoya bayan NPC suke ganin cewa jaridun suna zagin manyan ƙasa don haka bai
kamata a bar su su ci gaba ba. Dubi abin da suka ce:
“Wannan jarida ana raina
jama’a kuma ana wulaƙanta manyan malamai da shugabanni ƙiri-ƙiri Na tabbata duk
wanda ba ya ƙaunar a raina na gaba ba zai so jaridun nan biyu ba: Nothern Star da
Comet.”
(Kano, 1960).
An sani cewa, yawanci ‘yan siyasa kan yi
amfani da gugar zana ne wajen sukan abokan hamayyarsu, wanda hakan ba zai hana a
fahimci ko da wa suke yi kai tsaye ba, amma dai ba za a iya kama su da laifin cin
mutuncin wani ko wata ba don ba su ambaci suna ba. Duk da haka jam’iyya mai mulki
abin yana mata ciwo, shi ya sa ma ta fara neman hanyar da za a riƙa kama duk wanda
ya yi wa masu mulki shaguɓe a tursasa su sai sun faɗi ko da wa suke yi. Daga ƙarshe
jaridar Sodangi kasancewar ta ta gwamnati
roƙo ta yi da cewa:
“Muna roƙon Gwamnatin
jiha ta yi tunani matsananci ta duba maganar shawarar nan ta a ruguza Northern Star
da Daily Comet. Abin da gwamnati ta ga ya fi shi za ta yi a kansu.”
(“Kashe Wasu Jaridu”, 1960)
Kasancewar jaridun guda biyu dukkansu na
‘yan hamayya ne, kuma ba su barin jam’iyya mai mulki
da magoya bayanta su sha ruwa, wannan ya sa suka fara neman hanyar da za a kashe
bakin tsanya, wato a dakushe muryar jam’iyyar NEPU wadda ta kasance ƙawar NCNC ce
da kuma Jam’iyyar AG. Hakan bai samu ba kasancewar dukkan jam’iyyun sun zame wa
jam’iyyar NPC ƙadangaren bakin tulu.
Tun a wuraren shekarar
1933-1938 aka samu littattafan zube na ƙagaggun labarai na Hausa na farko. A cikin
wasu littattafan an samu waɗanda suke ɗauke da ɓurɓushin siyasa, duk da cewa dai
ba shi ne babban saƙon da littattafan suke ɗauke da shi ba, amma dai an samu abin
da za a faɗa, kuma a danganta shi da siyasa a cikin su. Alal Misali, littafin Ruwan Bagaja na Abubakar Imam ya hasko yadda
siyasar gargajiya ta tsarin sarauta da shugabancin al’umma take. Shi kuma littafin
Ganɗoki na Bello Kagara ya fito da irin
yadda siyasar Turawan mulkin mallaka ta gudana, wadda ta shafi yaƙe-yaƙen da Turawa
suka yi da sarakunan ƙasar Hausa wanda bayan cinye ƙasar Hausar ne suka kafa tsarin
mulki irin nasu. Akwai littafin Magana Jari
ce na Abubakar Imam a shekarar 1938, wanda a cikin labaru da dama na cikin littafin
an nuna tasirin siyasar gargajiya da mulki da ƙarfin iko irin na sarakuna, da kuma
yadda ake girmama su.
Da tafiya ta yi nisa,
lokacin da aka fara hada-hadar karɓar mulkin kai, nan ma an samu tasirin siyasa
ƙwarai cikin rubuce-rubucen adabin wannan lokacin, domin kuwa ɓullar jam’iyyun siyasa
ya ƙara wa abin armashi, kasancewar kusan dukkan ayyukan adabi na wannan lokacin
suna ɗauke da wannan ruhin. Bayan samun yancin kan Nijeriya a shekarar 1960 da kafa
jumhuriyoyin siyasa tun daga jamhuriya ta ɗaya har zuwa ta huɗu, an ci gaba da samun
littattafan zube na ƙagaggun labarai waɗanda suka fito da tasirin siyasar jam’iyyu
a cikinsu. Alal Misali, Littafin Tura Ta Kai
Bango na Sulaiman Ibrahim Katsina da Tsuntsu
Mai Wayo na Bala Anas Babinlata da Kan
Mage Ya Waye na Ibrahim Isa Jiƙamshi da Kowa
Ya Bi na Abdurrashid Sani Isa da Dambarwar
Siyasa na Aminiya-Trust da dai sauransu.
4.4.3 Rubutaccen Wasan Kwaikwayo Na Siyasa
Rubutaccen
wasan kwaikwayo nau’in adabi ne da yake zuwa a cikin wani tsari na daban a rubuce
cikin littafi, don samun abin karantawa a makarantu wajen koyar da ɗalibai ko a
karanta don nishaɗi. (Umar, 2022: 70). Ta la’akari da wannan ma’anar za a iya cewa
duk wasan kwaikwayon da ya ɗauki wannan sigar da aka kawo a sama kuma ya ƙunshi
jigon siyasa a cikinsa shi ake kira rubutaccen wasan kwaikwayo na siyasa.
Rubutaccen
wasan kwaikwayo gaba ɗayansa ya kasance baƙo idan aka kwatanta shi da sauran rassan
adabi na rubutacciyar waƙa ko zube (Galadanci da wasu 1992:19; Malumfashi, 1984:
3). Rubutun Ajami shi ne ya fara zuwa ƙasar Hausa a ƙarni na 15, sannan sai rubutun
boko ya biyo bayansa a ƙarni na 19. A ɓangare guda kuma rubutun Ajami ya zo ne tare
da addinin Musulunci wanda bai ba wasa matsayi ba (Malumfashi, 1984: 19; ‘Yar’aduwa
2007: 35; Yusuf 2008: 88). A ɗaya ɓangaren kuwa rubutun boko ya zo ne tare da addinin
kiristanci, musamman a kudanci da tsakiyar Nijeriya, wanda bai yi nasarar kawo wannan
addini ba a ƙasar Hausa in ban da ilimin boko (Umar, 2022:70).
Tun
a farkon ƙarni na 20 aka fara samun rubutattun wasannin kwaikwayo, sai dai ba a
samu wasanni masu ɗauke da ruhin siyasar jam’iyyu kai tsaye ba sai a littafin Kukan Kurciya na Mahmud Barau Bambale wanda
aka buga a shekarar 1993. Kodayake, kafin wannan lokaci an samu wasu wasanni da
Malam Aminu Kano ya rubuta waɗanda ba a buga su ba, da suka shafi gwagwarmayar kawo
sauyi ne da ‘yanta al’umma bisa aƙidar kawo daidaiton ajin matsayi na al’umma da
siyasa da kuma gurguzu wato rayuwar bai-ɗaya(Umar, 2022:78). Daga cikin wasannin
da ya rubuta akwai: Kai Wane Ne A Kasuwar
Kano? , Da Gudumar Dukan En’en Kano
da Ƙarya Fure Take Ba Ta ‘Ya’ya da Alhaji Kar Ka Ɓata Hajjinka A Banza da sauransu[3]. Duka waɗannan wasanni
ya riƙa rubuta su yana sanya ɗalibansa suna aiwatarwa domin wayar wa da al’umma
kai a kan aƙidun gwagwarmaya da fafutukar ƙwatar wa talaka ‘yanci daga mulkin danniya
da zaluncin da sarakunan Arewa da Turawan mulkin mallaka suke yi masu. (Paden, 1968:276)
da (Umar,2022:79). Malam Aminu Kano ya miƙa waɗannan
wasannin ga jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo
domin a buga su, amma kasancewar wasannin sun yi kakkausar suka ga manufofin gwamnati
da sarakunan Arewa sai suka ƙi karɓa balle su wallafa. Daga baya-bayan nan aka samu
littafin rubutaccen wasan kwaikwayo na siyasa mai suna Tutar Babu wanda Kabir Yusuf Anka ya rubuta a shekarar 2019.
Daga
bayanan da aka kawo an fahimci cewa, wannan ɓangare na rubutaccen wasan kwaikwayo
na siyasa bai samu tagomashi ba, musamman idan aka yi la’akari da sauran ɓangarorin
rubutattun waƙoƙin siyasa da na zube.
4.5 Dalilan Da Suka Haifar Da Ƙamfar Wasu Ɓangarori Na Rubutaccen Adabin Siyasa.
Ayyukan adabi da suka shafi
siyasa, musamman siyasar jam’iyyu, wani ɓangare ne mai muhimmanci a cikin aikin
adabi, kasancewar siyasa ta zama tamkar jinin jikin ‘yan’adam, domin rayuwa ba ta
yiwuwa sai da ita, kuma ana gudanar da ita ko cikin sani ko kuma cikin rashin sani.
Wannan ne ma ya sa al’amuran siyasa suke bayyana a cikin kowace gaɓa ta rayuwa.
Ke nan, ba za a yi mamaki ba idan aka gan ta ta bayyana tamkar rana lokacin Azahar
a cikin ayyukan adabin al’ummar wannan zamanin. Duk da cewa siyasa ta riga ta yi
ƙarfi a cikin wasu ɓangarori na adabi, duk da haka akwai ɓangarorin da aka samu
ƙamfar rubutattun ayyukan adabin siyasa. Wannan kuwa ba zai rasa nasaba da wasu
dalilai da wannan bincike ya gano ba, waɗanda ake ganin su ne suka hana wannan nau’in
adabi bunƙasa. Daga cikin dalilan akwai:
4.5.1 Tasirin Ilimin Addinin Musulunci
Addinin Musulunci addini ne
wanda al’ummar Hausawa suka karɓa, kuma suka yi imani da shi bayan samun cuɗanyarsu
da Larabawa wanda ta hanyarsa ne aka samu hanyar rubutu na farko, wato Ajami. Addinin
Musulunci ya yi tasiri ƙwarai wajen bunƙasar wasu ɓangarori na rubutaccen adabi,
kuma ya taimaka wajen samun naƙasu ga wasu ɓangarorin. Alal misali, rubutacciyar
waƙa ta girmi rubutaccen zube da wasan kwaikwayo, kuma ta fi karɓuwa a wajen al’umma
a kan sauran takwarorinta. Wannan ba zai rasa nasaba da yadda malamai suka riƙa
amfani da ita wajen yaɗa addini a lokacin jihadi ba. Waƙa ta samu karɓuwa a zukatan
al’umma ta yadda kusan duk saƙon addini da ake son isarwa a lokacin jihadi akan
yi amfani da ita, domin ta fi saurin shiga zuciya da ƙwaƙwalwa fiye sauran rassan
adabi (Adamu, 2015:128).
Tun kafin zuwan Turawa ƙasar
Hausa, an samu waƙoƙi masu ɗauke da ruhin siyasa wanda malaman jihadi suka rubuta.
Wannan ya ƙara wa marubuta waƙoƙi ƙwarin gwiwa wajen samar da wasu waƙoƙin siyasa
bayan zuwan Turawa da samuwar siyasar jam’iyyu, hakan ya sa rubutattun waƙoƙin
siyasa suka yawaita, kuma aka samu bunƙasarsu fiye da sauran rassan adabi.
Ta fuskar rubutaccen zube,
za a fahimci cewa, duk da akwai nau’o’in rubutaccen zube da addini bai ƙyamace su
ba kamar saƙo a rubuce wanda ya shafi wasiƙa da akan aike wa sarakuna da masu mulki
da makamantansu, da jawabi a rubuce da wa’azi wanda ya ƙunshi huɗubobi na malamai
da dai sauransu. Abin da ya shafi rubutattun labaran ƙirƙira kuwa wannan bai samu
tagomashi ba a karon farko. Kasancewar duk marubutan da suka samu ilimi a farko
malamai ne masana ilimin addinin Musulunci, wannan ya sa suka kalli rubutun adabi
na ƙagawa a matsayin ƙarya, ƙarya kuma babban laifi ne a cikin addinin Musulunci.
Hakan ya sa wannan ɓangaren bai samu tagomashi sosai ba da farko. Daga bisani bayan
zuwan Turawa sai aka fara samun irin wannan nau’in na rubutaccen adabi, sai dai
ba a samu ,masu ɗauke da ruhin siyasa ba kamar yadda waƙoƙi suka samu karɓuwa sai
daga baya. Kusan dai za a iya cewa shi ma wannan ɓngaren bai samu ayyukan siyasa
sosai ba, saboda ƙyamar da addini yake da shi dangane ɗabi’ar ƙarya.
Idan kuwa aka dubi fannin wasan
kwaikwayo za a ga cewa, malamai na addinin Musulunci a ƙasar Hausa suna da fahimtar
cewa, addini baki ɗayansa bai zo da wasa ba. Don haka tun daga nan aka yi wa rubutaccen
wasan kwaikwayo raunin da ya hana shi warkewa balle, ya tashi ya yi rawar gaban
hantsi. Wannan shi ne babban dalilin da ya sa wannan ɓangare na rubutaccen adabin
siyasa bai samu karɓuwa ba, kuma ya kasance shi ne mafi ƙamfa cikin ayyukan adabin
siyasa a rubuce.
4.5.2 Mulkin Soja
Idan aka yi batun rubutattun
ayyukan adabi musamman na siyasa za a tarar cewa, mafi yawa waɗanda aka samar cikin
waƙoƙi da zube da wasan kwaikwayo duk zamanin mulkin farar hula aka samar da su.
Wannan ba zai rasa nasaba da cewa soja suna da dokokinsu waɗanda suka sha bamban
da na farar hula. Idan ana batun siyasa to tunani yakan karkata a kan mulkin farar
hula ne ba soja ba, shi kuwa adabin al’umma yana nuna rayuwarsu ne, don haka in
za a yi batun siyasa sai dai a yi ta a mulkin farar hula.
Idan aka duba za a ga cewa
an samu wasu shekaru masu yawa da sojoji suka ɗauka suna mulki wanda za a iya cewa
sun kawo wa rubutattun ayyukan adabin siyasa tarnaƙi. Wannan ne ya sa rubutattun
waƙoƙin siyasa suka samu daga wuraren 1950 lokacin da aka fara siyasar jam’iyyu
har zuwa 1966 lokacin da sojoji suka yi juyin mulki na farko wanda ya kawo ƙarshen
jamhuriya ta ɗaya.
Haka kuma an ci gaba da samun
rubutattun ayyukan adabin siyasa a tsakankanin shekarun 1979-83, wato zamanin jamhuriya
ta biyu. Haka ma a rusasshiyar jamhuriya ta uku a shekarar 1993 lokacin da soja
suka shelanta miƙa mulki ga farar hula shi ma an samu rubutattun ayyukan adabi na
siyasa kama daga waƙoƙi da zuwa wasan kwaikwayo. A jamhuriya ta huɗu wadda ta fara
daga 1999 zuwa yau an samu rubutattun ayyukan adabi da dama, kuma a kullum waƙa
ita ce take ɗaukar kaso mafi tsoka a cikin rassan adabin na Hausa.
Lura da wannan bayanin za a
ga cewa, tun daga juyin mulki na farko a shekarar 1966 zuwa farkon jamhuriya ta
huɗu wadda muke ciki a yanzu, an samu sojoji sun shafe shekaru ashirin da takwas
suna mulki. Ga jerin shugabannin mulkin soja da tsawon lokacin da suka ɗauka suna
mulki kamar haka:
1- Manjo Janar Aguyi
Ironsi (1966)
2- Janar Yakubu Gowon
(1966 zuwa 1975)
3- Janar Murtala Ramat
Mohammed (1975 zuwa 1976)
4- Manjo Janar Olusegun
Obasanjo (1976 zuwa 1979)
5- Manjo Janar Muhammadu
Buhari (1983 zuwa 1985)
6- Janar Ibrahim Badamasi
Babangida (1985 zuwa 1993)
7- Janar Sani Abacha (1993
zuwa 1998)
8- Janar Abdulsalami
Abubakar (1998 zuwa 1999)
Waɗannan su ne jerin sunayen
shugabannin da suka mulki Nijeriya a ƙarƙashin mulkin soja. Kuma daga na farko zuwa
ƙarshe idan aka lissafa za a ga cewa sun shafe kimanin shekaru 28 suna mulki idan
aka lissafa tsawon lokacin da kowannen su ya shafe a kan mulki. Wannan kaɗai ya
isa ya kawo wa rubutattun ayyukan adabin siyasa tsaiko, ya kuma haifar da ƙamfarsu.
4.5.3 Ɓullowar Finafinan Ƙasashen Waje
Kalmar fim tilo ce, jam’in
kalmar shi ne finafinai. Fim na nufin haɗuwar ayyuka da maganganun mutane daban-daban
da amfani da wasu abubuwa marasa rai ta hanyar kwaikwayo ko ƙagawa da suka yi a
cikin hoton da ake kallo ta hanyar amfani da na’urorin ɗaukar hoto da nuna shi ga
jama’a, wanda yake ɗauke da wani saƙo ko saƙonni zuwa ga al’umma da aka yi abin
dominsu(Usman da Bunza, 2021).
Finafinan ƙasashen waje sun
samu ne tun kafin samun ‘yancin kai. An samar da gidajen silima a ƙasar Hausa waɗanda
Turawa suka riƙa amfani da su wajen yaɗa farfaganda da sunan ilimantarwa don su
ci gaba da shimfiɗa mulkin mallaka a ƙasar Hausa (Na’Allah, 2004: 54). Na’Allah(2004:55)
ya ci gaba da cewa, a farko Turawa sun riƙa amfani da silimar tafi-da-gidanka(mobile
cinema) zuwa lungu da saƙo na ƙasar Hausa domin yaɗa farfagandarsu. Sun riƙa bi
makarantu domin nuna finafinai ko wasannin kwaikwayo waɗanda marubuta irinsu Shakespeare
suka rubuta, waɗanda littattafansu sun yi fice a tsakanin ɗaliban adabi.
Daga bisani an samu Turawan
mulkin mallaka sun samar da gidajen silima a kusan dukkan manyan garuruwan ƙasar
Hausa kamar Sakkwato da Kano da Kaduna da sauransu. Baya ga finafinan Turawa na
yaɗa farfaganda, sai kuma aka samu finafinan Indiya da na Sin waɗanda ake nunawa
a irin waɗannan gidajen na silima a kowace rana. An samu yaɗuwar waɗannan finafinan
ne ta hannun ‘yan kasuwar ƙasashen Lebanon waɗanda su ne suka mallaki kusan dukkan
gidajen silima da suke a yankin Arewacin Nijeriya a shekarun 1950. Finafinan Indiya
su ne suka mamaye kusan dukkan gidajen silimar da ake da su a ƙasar Hausa tun daga
wancan lokaci har zuwa shekarun 1990. Haka kuma su ne aka riƙa nunawa kowane dare
a gidajen talabijin, sau shida a cikin kowane mako a duk faɗin Arewacin Nijeriya.
(Ahmad, 2004: 154).
Waɗannan gidajen kallo sun
ɗauke wa matasa hankali ta yadda suka juyar da tunaninsu ga kallon al’adun Turawa
da na Indiyawa da na al’ummar ƙasar Sin. Kai hatta waƙoƙin da ake sanyawa a gidajen
radiyo da talabijin sai ya kasance waƙoƙin Indiya sun kwashi kaso mafi tsoka, duk
da cewa ba a fahimtar me suke faɗa a cikin waƙoƙin nasu maimakon waƙoƙin Hausa da
aka sani. Wannan ya sanya tunanin rubuta adabin Hausa na siyasa bai shiga zuciyar
matasa ba, abin da ya taimaka ƙwarai wajen dakushe samuwar rubutaccen adabin siyasa
a ƙasar Hausa.
4.5.4 Tasirin Soyayya
Soyayya na nufin nuna ƙauna
daga ɓangarori biyu na masu ƙaunar juna musamman mace da namiji (CNHN, 2006: 398).
Bayan samuwar shirin bayar da ilimi bai ɗaya na gwamnatin tarayya (UPE) a shekarar
1976, an samu waɗanda suka samu ilimin zamani da dama musamman mata, waɗannan suka
duƙufa wajen rubuce-rubucen littattafai na ƙagaggun labarai musamman na soyayya
(Ahmad, 2004:155 da Malumfashi, 2018:409). Ke nan, samuwar ƙagaggun labaran soyayya
ba zai rasa nasaba da samuwar ilimi da kuma cuɗanyar da aka samu tsakanin maza da
mata a makarantun boko ba a lokacin. Ga kuma tasirin kallon finafinan Indiya waɗanda
yawancinsu na soyayya ne. Kasancewar ‘yammata da samari sun haɗu wuri guda a makaranta
sai aka riƙa samun shaƙuwa ta soyayya a tsakaninsu, wannan ya sa suka riƙa rubuta
irin abin da suke ji na shauƙin soyayya a matsayin labarai.
Bugu da ƙari, samuwar na’urorin
ɗab’i da kamfanonin ɗab’in ya taimaka wajen yaɗuwar litttafan soyayya, saɓanin a
baya da kowane rubutu sai hukumar NNPC ta tace shi ta kuma aminta da shi kafin ta
buga shi.
Kamar yadda finafinan Indiya
yawanci ake gina su kan soyayya, sai ya zama waɗannan littattafan ma akan gina su
kan soyayya da auren dole da matsalolin gida da dai sauransu.
Rubuce-rubuce na soyayya sun
yi tashe ƙwarai a wuraren shekarun 1990, tun daga kan littattafai da wasiƙu tsakanin
matasa, musamman ‘yammata da samari.
Duk da cewa an samu zamunnan
siyasa mabambanta tun daga 1950 zuwa 1990, za a iya cewa marubuta zube ba su bayar
da ƙarfi wajen rubuce-rubuce a kan siyasar ba, maimakon hakan, sun fi karkata ne
kan rubuce-rubuce na soyayya, domin ita ce take tashe tsakanin matasa a wancan lokacin.
Wannan ya haifar da naƙasu ga lamarin rubutaccen adabi Hausa na siyasa.
4.5.5 Ƙarancin Ilimin Siyasa Ga Matasa
Ilimi shi ne ƙashin bayan ci
gaban kowace al’umma, kuma da shi ne ake iya sarrafa tunani domin samun kyautatuwar
al’umma. Dukkan abin da za a gudanar matuƙar aka sanya ilimi a cikinsa to za a ga
daidai, kuma za a samu nasarar wannan abin.
Ƙarancin ilimi yana daga cikin
manyan dalilan da suka haifar da ƙamfar ayyukan rubutaccen zube na siyasa, wannan
kuwa ba zai rasa nasaba da ƙyamar da aka nuna wa ilimin zamani tun a farko ba, wanda
shi ma ya taimaka wajen samun ƙarancin ayyukan adabi rubutattu, ya kuma sanya rubutaccen
adabi na siyasa bai samu tagomashi ba.
Rashin sanin ina siyasar ta
dosa da rashin shigar matasa domin a dama da su a cikin harkokin siyasa ya ƙara
taimakawa wajen ƙamfar rubutaccen adabin siyasa, domin sai ka san abu kafin ka iya
yin rubutu a kansa. Alal Misali, kusan duk ayyukan adabin siyasar da aka samu za
a tarar masu ido a kan siyasar suka rubuta su; ko dai ya kasance a cikin jaridu
ko jawabai ko wasiƙu ko ƙagaggun labarai ko ma cikin wasanni kwaikwayo ko waƙoƙi.
Idan aka ɗauki jaridu, za a tarar cewa dukkan rahotannin da aka kawo a ciki ko wasiƙun
da aka buga a cikinsu ‘yan siyasa ne suka rubuto su, wasu ma ’yan jam’iyya ne suke
kare jam’iyyunsu. A cikin ƙagaggun labarai kuwa idan aka dubi kamar littafin Tura Ta Kai Bango, 1983 an bayyana cewa marubucin
har takara ya yi a jamhuriya ta biyu, amma bai yi nasara ba. Su kuwa marubutan wasannin
kwaikwayon Kukan Kurciya, 1993 da Tutar Babu, 2019 sun samu ilimin siyasar
ne, domin sun gani kuma a zamaninsu aka yi, duk da cewa ba takara suka yi ba, amma
dai sun samu ilimi kan abubuwan da suka faru. Wannan ne ya ba su damar sanya alƙaminsu
suka rubuta wasannin daidai da abin da suka ji ko suka gani ko kuma ya faru da su.
Don haka rashin sanin abin da ya faru a baya da wanda yake faruwa shi ma ya haifar
da ƙamfar rubutaccen adabin siyasa.
4.6 Dangantakar Siyasar Addini da Siyasar Jam’iyya
Kamar
yadda aka bayyana a baya, siyasar addini ita ce aka fara samu a ƙasar Hausa kafin
wani nau’in siyasa na daban ya samu. Haka kuma, siyasar addini ta samu bayan zuwan
addinin Musulunci, sai dai ba ta samu tagomashi a rubuce ba har sai bayan jihadin
gyaran halaye da aka gudanar a ƙasar Hausa ƙarƙashin jagorancin Shehu Usmanu Danfodiyo,
lokacin da aka samu bunƙasar rubutaccen adabin Hausa daga almajiran Shehu.
Siyasar
da aka gudanar lokacin jihadi siyasar Musulunci ne wanda yake tafe da ƙa’idoji da
koyarwar addinin Musulunci, kuma an ci gaba da tafiyar da shi har bayan Zuwan Turawa.
Za a iya cewa akwai wata dangantaka da za a iya gani tsakanin tsarin siyasun guda
biyu, duk da cewa zaman ‘yan marina suka yi wa juna, wato kowa da inda ya fuskanta.
Dagantaka
ta farko da za a iya gano a zahiri ita ce, kasancewar ‘yan siyasar farko irin su
Malam Sa’adu Zungur sun jiyo ƙamshin ƙarshen ƙarni na sha tara, wannan ya sa siyasar
su ta yi tsafta cikin riƙo da gaskiya da riƙon amana tamkar dai yadda aka gudanar
da tsarin kafin zuwan Turawa.
Haka
kuma kasancewar ilimin Larabci shi ne aka fara samu wanda shi ne ya haifar da hanyar
rubutun Ajami, wannan ya sa ko da su Malam Sa’adu Zungur da Mudi Sipikin da irin
su Malam Gambo Hawaja Jos da Malam Aminu Kano suka zo, sai ya kasance sun samar
da ayyukan adabin siyasa cikin Ajami maimakon cikin boko wanda daga baya suka koya.
Alal misali waƙoƙin siyasa da Malam Sa’adu Zungur ya rubuta kamar su “Jihadin Neman
Sawaba” da “Arewa Jamhuriya ko Mulukiya” duk da Ajami ya rubuta su, daga baya aka
juya su cikin haruffan boko. Hatta a baya bayan nan an samu marubuta adabin siyasa
irin su Malam Garba Gashuwa da suka riƙa yin rubutun waƙoƙi cikin Ajami. Alal Misali,
waƙar “ Munafurci Karen Ruwa Jam’iyyar A.P.P” da waƙar “’Yan Tagwayen Jam’iyyu SDP
da NRC”, duk waƙoƙi ne da aka rubuta su cikin Ajami.
Dukkan
abubuwan da aka riƙa amfani da su wajen jawo hankalin al’umma ko dai lokacin yaƙin
neman zaɓe ko kuma wurin gudanar da mulki kamar su adalci da tsoron Allah da haƙuri
da juriya da yi wa shugabanni biyayya da dai sauransu, abubuwa ne masu alaƙa da
addini waɗanda sun samo asali ne tun daga zamanin jihadi, wato zamanin siyasar Musulunci.
Bayan
zuwan Turawa, kafin kakkafa jam’iyyun siyasa tsarin da al’ummar ƙasar Hausa suka
so a ɗore da shi wajen gudanar shugabanci shi ne tsarin da Musulunci ya tsara, wato
ta hanyar ayyana shugaban da ya dace ba ta hanyar kaɗa ƙuri’a ba, wanda kuma zai
ci gaba da jagorancin al’umma har mutuwarsa ko kuma lokacin da aka fahimci ya yi
raunin da ba zai iya jagorancin ba sai a sake ayyana wani. Wannan yana da dangantaka
da siyasar Musulunci wanda bai zo da zaɓe ko kaɗa ƙuri’a ko neman shugabanci ba.
Bayan
Turawa sun fito da ‘yan boko, sun fito da tsarin kakkafa ƙungiyoyi waɗanda daga
baya suka rikiɗe, suka zama jam’iyyun siyasa, sai ya kasance an riƙa amfani da aƙidun
addini wajen gudanar da siyasa, ta yadda ya kasance an samu ɗariƙun Ƙadiriyya da
Tijjaniyya sun kasance kamar ma su ne jam’iyyun siyasar ba waɗanda aka kafa kuma
aka sani ba. Alal misali, ‘yan Ƙadiriyya an san jam’iyyar da suke, haka ma ‘yan
Tijjaniyya an san tasu jam’iyyar. Kasancewar kowace ɗariƙa da Shehunnai da waliyyan
da suka yarda da su, kuma suke masu biyayya, wannan ya sa ɗan wata ɗariƙa ba zai
yarda ya bi wata ɗariƙa ba (Paden, 1968:312-313).
Bugu
da ƙari, kasancewar a ƙasar Hausa an amince cewa Shehu Usmanu babban malami ne kuma
waliyyi, wannan ya sa duk wanda ya danganta kansa da shi ake yi masa kallon na kirki.
Wannan dalilin ne ya sa wasu daga cikin ‘yan siyasar farko suka riƙa danganta kansu
da shi domin jawo hankalin mabiya da kuma samun ƙarin mabiya a siyasance. Wani ɓangaren
kuma wasu ‘yan siyasar sun riƙa danganta kansu da wasu manyan malamai na wasu ɗariƙu
domin samun nasara.
Baya
ga amfani da rigar addini, irin wannan tsarin ya ci gaba har zuwa yau, inda ‘yan
siyasa kan yi la’akari da wasu mutane masu mutunci a idon al’umma ko waɗanda ake
girmamawa, sai su riƙa danganta kansu da su a siyasance, ko da kuwa wannan mutumin
ba ɗan siyasa ne ba.
Idan
aka dubi waɗannan abubuwa da aka kawo za a fahimci cewa, siyasar adddini da siyasar
jam’iyya suna da dangantaka tun da farko, kuma idan aka dubi siyasar addini za a
iya ganin tasirinta a cikin siyasar jam’iyya, musamman idan aka yi la’akari da wasu
abubuwa na addini da suka shigo cikin siyasar jam’iyya, da kuma waɗanda aka ɗauko
su aka alaƙanta siyasun biyu da su.
4.6.1 Muhimmancin Ilimi A Cikin Siyasar Jam’iyyu
Kasancewar mafi yawan al’ummar
da suke ƙasar Hausa Musulmi ne, wannan ya sa kusan dukkan al’amuransu na rayuwa
sukan yi ƙoƙarin ɗora shi yadda zai dace da koyarwar addininsu. Kowane abu da ake
gudanarwa a ƙasar Hausa akan ba shi gurbi domin ya samu gindin zama ko da ta hanyar
yi masa kwaskwarima ne. Kasancewar tsarin siyasa musamman ta dimokuraɗiyya wadda
ta ba da damar zaɓen shugaba ta hanyar gudanar yaƙin neman shugabanci da kuma zaɓe
ta hanyar kaɗa ƙuri’a ta saɓa wa koyarwar addinin Musulunci, wannan ya sa da Hausawa
suka shiga sai suka yi ƙoƙarin yi wa tsarin kwaskwarima. Wato dai irin abin da masu
hikimar magana kan ce: ‘Da baƙi ƙirin, gara baƙi-baƙi.’
Idan aka dubi ‘yan siyasar
farko-farko za a ga cewa yawancinsu suna da ilimin addini. Alal Misali, mutane irin
su Malam Sa’adu Zungur da Malam Aminu Kano da Mudi Sipikin duk sun samu ilimin addini
daidai gwargwado, wasu daga cikinsu ma sun haddace Alƙu’ani mai girma tun suna da
ƙarancin shekaru. Wannan ya sa suke ƙarfafa cewa duk wanda zai jagoranci al’umma
to wajibi ne ya zama ya fahimci ilimin addini, domin shi ne zai yi masa jagora a
cikin sha’anin shugabanci ko jagorancin al’umma. Dubi abin da Malam Aminu Kano ya
faɗa a cikin wani jawabi nasa:
“ Shin kun ma
san ma’anar kalmar Sarki? Sarki fa ba yana nufin mai rawani ne kaɗai ba. A’a, yana
nufin shugaban muminai ne. Wannan yana nufin kowane sarki a ƙasarsa shi ne limami.
Shin kun taɓa tunanin dalilin da ya sa Shehu ya bai wa Sulaimanu da Yakubu da Ummarun
Dallaji tuta su je su shugabanci Kano da Bauchi da Katsina? To ya ba su ne don su
je su zama shugabannin addini (saboda iliminsu), kuma hakan aka yi. Babu wanda zai
ce shi liman ne kuma ya kasance ba shi da ilimin addini. Don haka a Musulunce jahili
ba zai yi shugabanci ba Saboda haka shugabanni na ƙwarai suna da ilimin addini wanda
ke yi masu jagora wajen sauke nauyin da addinin ya ɗora masu
(Paden, 1968:281).
A nan Malam Aminu Kano yana
nuna muhimmancin nagartar shugaba ne ta fuskar ilimi. Bayaninsa ya nuna cewa, kowane
shugaba wajibi ya kasance mai ilimin addini, wannan zai taimaka masa wajen kasancewa
mai tsoron Allah wajen gudanar da al’amuran shugabancin da aka ɗora masa. Ya ba
da misali da sarakuna shugabannin al’umma waɗanda Shehu Usmanu Danfodiyo ya ba su
tutoci zuwa yankunan ƙasar Hausa, inda ya nuna cewa kowanne daga ciki almajirin
Shehu ne, kuma babban malami ne masani, wanda zai kasance a cikin al’ummarsa shugaba,
jagora, malami, alƙali kuma limamin gari. Ilimi kodayaushe yana yi wa mai shi jagora
ne zuwa ga aikata daidai, da kuma yin hani da horo a duk inda suka kamata. Ta fuskar
gadon sarauta da zaɓen ‘ya’yan sarakuna a cikin tsarin siyasa kuwa, Malam Aminu
Kano ya nuna muhimmancin ilimi ga duk wanda za a naɗa sarki ko kuma a zaɓe shi wani
muƙamin siyasa, inda a cikin jawabin nasa ya ci gaba da cewa:
Idan ya kasance ɗan sarki ba shi da ilimin Muhammadiyya
to ya ja baya. In kuma akwai wanda a cikinmu zai iya kafa hujjar inda Allah ya faɗa
ko Manzonsa ya faɗa a cikin hadisi inda ya halatta jahili ya jagoranci al’ummar
Musulmi to muna sauraronsa
(Paden, 1968:282-283).
A nan yana magana ne kan tsarin
gado na sarauta, inda yake nuna cewa babu wannan tsarin a Musulunci. In kuwa har
ya kasance wani ɗa zai gaji mahaifinsa, to wajibi ne ya kasance ya yi karatu, kuma
yana da ilimi kafin a ba shi. In kuwa ba shi da shi to sai dai a zaɓo wani a damƙa
masa ragamar shugabancin ko da kuwa ba shi da gadonta. A tsarin siyasar jamhuriya
ta farko, mafi yawa daga cikin masu riƙe da muƙaman siyasa musamman na jam’iyyar
NPC, daga sarakuna sai ‘ya’yansu(Dudley, 1968:73). Wannan ya sa ‘yan hamayya
suka riƙa sukar su ta wannan fuska, inda suke ganin cewa a tsarin gargajiya ma addini
shi ne ya kamata ya zama jagora ga shugabanni, don haka a tsarin siyasar jam’iyya
ma wajibi ne duk shugaban da za a naɗa ko a zaɓa ya kasance mai ilimi. Ke nan ilimi
shi ne abu mafi muhimmanci wajen zaɓen shugaban da zai jagoranci al’umma.
Malam Sa’adu Zungur ya kawo
irin wannan hujjar inda yake cewa, ilimin addini shi ne ginshiƙin shugabancin al’umma,
inda a cikin waƙar Arewa Jamhuriya ko Mulukiya ya nuna cewa, maimakon a rushe tsarin
tafiyar da mulki ƙarƙashin sarakuna ya kamata a yi wa tsarin gyaran fuska ne.
Irin wannan na muhimmancin
ilimi a cikin siyasa ya ci gaba da bayyana a cikin ayyukan rubutaccen zube kamar
yadda ya fito a cikin littafin Tura Ta Kai
Bango, inda aka nuna cewa babu ma waɗanda ya kamata su shiga siyasa kamar malamai,
domin kuwa su ne suke iya tantance fari da baƙi, kuma suna iya nusar da al’umma
inda ya kamata ta dosa. Dubi abin da marubucin yake cewa:
“Na ga kana hanyar makaranta. Ina malamai ina shiga
siyasa?”
“Malamai kuwa ai su ya kamata su yi siyasa. Suna da
ilimi, don haka suna iya nuna wa mutanen kirki. Ai zuwana kamar da ƙasa.”
(Katsina, 1983: 3)
Muhimmancin ilimi ga al’umma
tamkar makaho ne da ɗan jagora, ma’ana, duk wanda ya samu ilimi ba za a same shi
yana tafiya ido rufe ba. Don haka waɗanda suka samu ilimi suna zama tamkar fitila
ga al’umma waɗanda suke haska masu hanya don kada su faɗa inda bai kamata su afka
ba. Shi ilimi fitila ne mai haske. Kamar dai yadda fitila kan haske ɗaki ko wani
wuri mai duhu haka ma ilimi musamman na addini yakan haske duniya, ya daidaita al’amura
wanda ya shafi jagorancin al’umma. A cikin ilimin addini ne ake samun tsoron Allah
da adalci da sauran kyawawan ɗabi’u. Wannan ne ma ya sa ko a cikin siyasar aka bai
wa ilimin addini muhimmanci domin samun kyakkyawan shugabanci. Ashe ke nan babu
waɗanda suka dace su jagoranci al’umma kamar masu ilimin cikinta.
Duk da muhimmancin da
ilimin addini yake da shi a cikin tsarin shugabanci, daga baya an yi wa wannan tsarin
siyasa ta Arewacin Nijeriya riƙon sakainar kashi, ta yadda aka sanya a cikin kundin
tsarin mulkin ƙasa cewa, babu wanda zai iya tsayawa takara a mataki kaza a zaɓe
shi komai ilmin addininsa har sai ya mallaki shaidar kammala karatun boko a ƙalla
na firamare, ya danganta da matakin da mutum zai yi takara a cikinsa. Wannan ya
sa darajar ilimin addini a cikin siyasa ta fara komawa baya ana bai wa ilimin zamani
muhimmanci. Dubi abin da marubucin littafin Da
Bazarku yake cewa:
“ Mene ne dalilin da ya sa cikin kundin
tsarin mulkin ƙasar nan za a sharɗanta cewa sai wanda ya yi karatun boko mai mataki
kaza ne kawai kawai zai tsaya takara iri kaza, ko da kuwa shi hafizin Alƙur’ani
mai girma ne kuma ya iya rubutu da karatu da larabci. Sannan kuma shi ne ya fi kowa
cancanta saboda amanarsa, mutuncinsa, jama’arsa, gaskiyarsa da dai sauransu. Idan
dai har bai yi bokon ba to ala tilas sai dai a ɗauki shin-mai-ruwa-uku a ɗora a
kan wannan matsayin.”
(Surajo,2006:97)
A nan marubucin yana nuna
takaicinsa ne kan yadda aka wofintar da ilimin addini a cikin siyasa, inda ake ganin
in dai ba ka yi ilimin boko ba, to komai tumbatsar ka a cikin ilimin addini matuƙar
ba ka da takardar shaida to ba za a amince da kai a zaɓe ka ba. Marubucin ya nunar
da cewa akwai waɗanda malamai ne na addini mahaddata Alƙur’ani mai girma, kuma an
yarda da mutunci da gaskiya da riƙon amanarsu a cikin al’umma, amma saboda ba su
da ilimin boko sai a ɗauki muƙamin siyasa a bai wa waɗanda ba su cancanta ba maimakon
su.
Ire-iren waɗannan misalai
sun yi ta bayyana a cikin tarihin siyasar Nijeriya musamman a ƙasar Hausa, wanda
a zamanin da ake ciki yanzu ma kusan ba a bai wa ilimin addinin muhimmanci kwata-kwata
in dai a kan abin da ya shafi zaɓen ‘yan takara ne ko kuma naɗin muƙamai. Ko da
kuwa muƙamin kwamishinan addinin Musulunci ko mai ba da
shawara kan addinin Musulunci sai wanda yake da takardar kammala karatun zamani
za a ba shi[4].
4.6.2 Aƙidu Da Matsayinsu A Fagen Siyasar Jam’iyyu
Tun farkon siyasar Jam’iyyu a ƙasar Hausa an yi
ta samun sa-toka-sa-katsi tsakanin manyan aƙidun Musulunci na wannan yanki na ƙasar
Hausa. Ɓullowar jam’iyyun ya zo da wani sabon abu a cikin siyasar wannan yanki duk
da cewa da ma akwai bambance-bambance na fahimta a tsakanin ɗariƙar Tijjaniyya da
kuma ta Ƙadiriyya musamman ta fuskar waliyyansu.
Haka ma a cikin ɗariƙar
ta Tijjaniyya akwai bambancin fahimta tsakanin ‘yan sadalu wato mabiya Shehu Umaru
Futi da kuma ‘yan ƙabalu mabiya Shehu Ibrahim Inyasss. Waɗannan bambance-bambance
sun yaɗu ƙwarai a ƙasar Hausa. Alal Misali, a lardin Zazzau inda wuraren shekarar
1950 Sarkin Zazzau Jafaru wanda Batijjane ne, ɗan ‘Sadalu’, ya yi adawa ƙwarai da
‘yan ‘ƙabalu’ mabiya Ibrahim Inyasss, har ya kai ga bayar da umarnin cewa duk wani
ɗan ƙabalu ba zai yi limancin Juma’a ba(Paden, 1973: 122). Waɗannan bambance-bambance
a cikin aƙidu sun taka muhimmiyar rawa a cikin siyasar jam’iyyu a ƙasar Hausa.
Kasancewar a kowane lardi
na ƙasar Hausa akwai ɗariƙar da ta fi samun karɓuwa da yawan mabiya, wannan ya taimaka
wa shugabannin siyasar wannan lokacin yin amfani da ɗariƙunsu wajen neman goyon
bayan jama’a da kuma ƙarfafa hamayya tsakaninsu da wasu jam’iyyu. Alal misali, lardin
Sakkwato inda nan ne cibiyar daular Usmaniyya, ɗariƙar Ƙadiriyya ce ta fi ƙarfi,
saɓanin lardin Kano da mafiya yawansu mabiya ɗariƙar Tijjaniyya ne. Wannan dalilin
ya sanya ko da aka samu ɓullar siyasar jam’iyyu, sai ya kasance mafi yawa na magoya
bayan manyan jam’iyyu biyu na Arewacin Nijeriya, wato NEPU da NPC, suka kasance
‘yan Tijjaniyya ne da Ƙadiriyya, wato Tijjaniyya a Kano, Ƙadiriyya kuma a Sakkwato.
Da irin wannan tsarin aka faro siyasar jam’iyyu a Arewacin Nijeriya[5].
An riƙa samun rikice-rikice
tsakanin mabiya ɗariƙun biyu inda a wasu lokuta har akan samu hasarar rayuka da
dukiya. Alal misali, an bayyana cewa akwai lokacin da sarkin Musulmi ya ba da umarni
aka rushe masallatan ‘yan Tijjaniyya da dama a lardin Sakkwato, wanda hakan ya jawo
masa zage-zage daga mabiya Tijjaniyya a cikin waƙoƙinsu, saboda nuna hamayya da
yake da su. An kuma samu rikici tsakanin ‘yan Ƙadiriyya da Tijjaniyya a lardin na
Sakkwato, kasancewar Sarkin Musulmi shi ne yake da alhakin naɗa limamai, sai ya
riƙa naɗa ‘yan Ƙadiriyya a limanci. Wannan ya sa aka riƙa samun ta-da-ƙayar baya
daga mabiya Tijjaniyya na Zamfara, wanda a wuraren shekarun 1950 rikici ya ɓarke
a aƙidun biyu, har ya haifar da kisan wani limamin Ƙadiriyya a Zamfara (Scott, 1952:
2).
Irin wannan ya bayyana
a cikin jaridar Daily Mail, inda aka bayyana irin wannan rikici tsakanin aƙidu
kamar haka:
“Mutane
huɗu sun rasa rayukansu wasu da dama kuma sun samu raunuka sakamakon hatsaniyar
da aka samu a Sakkwato makon da ya gabata. Rikicin da ya ɓarke tsakanin mabiya ɗariƙu,
wanda ya fi tsanani shi ne wanda aka samu Issa da Zurmi da ke lardin Sakkwato. Wannan
rikici ya ɓarke ne tsakanin mabiya Tijjaniyya da na ƙadiriyya. Rikicin farko ya
tashi ne a Gidan Maizare wanda aka rasa rayukan mutum huɗu rikicin ya ɓarke ne sakamakon
‘yan Tijjaniyya da suka hana ‘yan Ƙadiriyya gudanar da sallar la’asar a garin Jangero
An kama mutane da dama da suke da hannu cikin rikicin.”
(“Mutane Huɗu sun Rasa
Rayukansu”, 1956)
Idan aka dubi irin waɗannan
rikice-rikice za a ga cewa suna da alaƙa da siyasa ƙwarai da gaske duba da yadda
aƙidu a addini suka yi tasiri ƙwarai a cikin siyasar jam’iyyu a farko. Rikicin siyasa
tsakanin jam’iyyu ba sabon abu ba ne a wancan lokacin, sannan kuma jam’iyyun siyasa
a ƙasar Hausa a wancan lokacin an danganta su da wasu aƙidun addini wanda kusan
duk wanda yake cikin jam’iyya kaza an san ɗan wace aƙida ce. Kasancewar Sakkwato
nan ne tushen Ƙadiriyya a ƙasar Hausa, wannan ya sa duk limamin da sarkin Musulmin
zai naɗa a ƙasar Sakkwato zai naɗa ɗan Ƙadiriyya ne wadda ake dangantawa da jam’iyyar
NPC a wancan lokaci. Su kuwa ‘yan hamayya na jam’iyyar NEPU waɗanda
yawancinsu ko ma baki ɗayansu ‘yan Tijjaniyya ne sai suke ganin ba a yi masu adalci
ba, domin akwai saɓanin fahimtar addini a tsakanin. Wannan abin da ya faru ya sanya
jam’iyyar hamayya ta NEPU a wancan lokacin ta shirya wata
muhawara wadda za ta gudana a birnin Landan, domin tattauna batun ‘yancin gudanar
da addini a Arewacin Nijeriya. Kuma don nuna goyon baya ga waɗanda aka kama aka
tsare sakamakon wannan rikici, matasan NEPU da dama sun tafi Sakkwato a matsayin
mabiyan Tijjaniyya domin nuna fushinsu kan tsare matasan Tijjaniyya a can.
Wasu suna ganin cewa ainihi
idan aka yi maganar aƙida to ana nufin Musulunci ne baki ɗaya, duk kuwa wanda ba
shi da aƙida to ba Musulmi ba ne. Idan aka ɗauki wannan fahimtar, za a ga cewa a
cikin siyasar jam’iyyu musamman siyasar jamhuriya ta farko kowace jam’iyya tana
iƙirarin ita ce jam’iyyar Musulunci, duk wadda ba ita ba ta kafirai ce. A kan wannan
aƙidar aka gina siyasar ƙasar Hausa a wancan lokaci. Dubi wannan misalin:
“ ya jawo hankalin duk mai hankali na Arewa
da Najeriya su rungumi NPC hannu bibbiyu don ita ce zata tabbatar mana addininmu
na Musulunci ta kuma ƙyale masu bin wata hanya su ta bin abarsu da kuma ƙarfafa
sarakunanmu na addini ”
(“A. G. Na Maganin Mutuwa
A Arewa”, 1959).
Idan aka dubi wannan misalin
za a ga cewa, kira ake yi ga jama’a a kan su rungumi jam’iyyar NPC don ita ce za
ta tabbatar da addinin Musulunci, saɓanin sauran jam’iyyu da ba za su kula da addinin
ba. Haka kuma idan aka lura a cikin misalin ana nuna cewa za a bar duk wani mai
aƙida ya yi aƙidarsa ba tare da an hana shi ba, sannan kuma za a ƙarfafa sarakunan
gargajiya waɗanda ya kira su da sarakunan addini don dai nuna cewa aƙida da siyasa
fa ba a raba su.
An sake samun wani rikicin
tsakanin ‘yan Tijjaniyya da ‘yan Ƙadiriyya a lardin Sakkwato wanda aka bayyana cewa
har ‘yan doka goma sha ɗaya aka kashe yayin kwantar da tarzoma. Dubi labarin da
jaridar Daily Express ta buga ranar 2
ga Afrilu 1965:
“ the disturbance broke out in Yeldu District
between Tijaniyya and Kadiriyya suppoters in Toranke, Jankuka, and Jaja, a group
of villages 60 miles North-East of Argungu.”
Fassarar marubuci:
“ hatsaniya ta ɓarke a ƙasar Yeldu tsakanin
magoya bayan Tijjaniyya da na Ƙadiriyya a Toranke da Jankuka da Jaja, wasu rukunin
ƙauyuka kimanin mil 60 Arewa Maso Gabas da Argungu.”
(Paden,1973: 122).
A cikin wannan rikicin da aka samu tsakanin mabiya
aƙidun biyu, shi ma yana da alaƙa da siyasa ƙwarai da gaske domin kuwa jaridar Morning Post ta ruwaito cewa:
“The Sultan of Sakkwato later denied that
the riot was between Qadiriyya and Tijaniya, throughout the country and more especially
in big towns, live amicably without interference in each other’s religious belief.
He referred to the rioters as ‘Yan Wazifa’ who are going beyond their bounds to
them even prayer five time a day was forbidden.”
Fassara:
Idan aka dubi misalin
da yake sama za a ga cewa siyasa ce a ciki domin kuwa wanda ya yi maganar Baƙadire
ne duk da cewa kai tsaye ba a ayyana shi a matsayin ɗan Jam’iyyar siyasa ba, amma
dai yana goyon bayan gwamnati mai mulki na lokacin wadda ta jam’iyyar NPC ce. Kalmar
”Yan wazifa” kuma tana nufin ‘yan Tijjaniyya, kalma ce ta wulaƙanci da ake faɗa
wa ‘yan ƙabalu na wasu ƙauyuka a wajen lardin Kano, kamar yadda Paden (1973: 199)
ya bayyana. ‘Yan Wazifa su ma ‘yan Tijjaniyya ne, bambancinsu shi ne, su waɗanda
aka kira ‘Yan Wazifa su ne ‘Yan Faila, masu tafiya suna zikiri, mabiya Shehu Ibrahim
Inyass. Su kuma ɗayan ɓangaren ‘yan Tijjaniyyar da ba su ba, su ne mabiya ɗariƙar
Shehu Umaru Futy. A nan ya nuna cewa ‘yan Tijjaniyya ne (NEPU) suka tayar da rikici
ba ‘yan Ƙadiriyya (NPC) ba.
Irin wannan dangantaka
tsakanin aƙidun Musulunci da siyasa ya ci gaba da bayyana a cikin rubutaccen zube,
inda aka riƙa nuna muhimmancin aƙida a cikin siyasa, wanda hakan yake sa dagantaka
ta yi daɗi idan ‘yan siyasa biyu suka zama mabiya aƙida guda, ko kuma a samu akasin
haka idan ya kasance an samu bambancin aƙidar addini. Wani lokaci akan samu ‘yan
siyasa biyu a jam’iyya guda masu mabambantan aƙidun addini, sai dai abu kaɗan zai
iya gittawa da ya shafi aƙidar ya ɓata alaƙa a tsaninsu, kasancewar aƙida a addini
abu ne da aka ɗauke shi da muhimmancin gaske, domin ya shafi imanin mutum ne baki
ɗaya. Dangantakar Sardauna da Sarkin Kano ta yi tsami wanda har ya kai ga an cire
shi daga sarauta domin bambancin aƙida, kasancewar Sarkin Kano mabiyin ɗariƙar Tijjaniyya
ne kuma makusancin Shehu Ibrahim Inyasss, wannan ya haifar da rashin fahimta tsakaninsa
da Firimiyan Jihar Arewa wanda ya kai ga cire sarki Muhammadu Sanusi daga sarauta
duk kuwa da kusancin da suke da shi. Dubi abin da awolowo ya faɗa a cikin wani rahoto:
“ kafin a sanya dokar ta-ɓaci a jihar Yamma
an sanar da ni cewa dangantaka ta yi tsami tsakanin Sarkin Kano wanda yake ɗan Tijjaniyya
ne da kuma Sardaunan Sakkwato wanda ba ɗan wannan aƙidar ba ne.”
(Paden, 1973 : 311)
Wannan yana nuna irin
yadda aƙidu suke da muhimmanci musamman a siyasar jamhuriya ta farko. Daga abin
da aka gani cikin misalan da suke sama za a fahimci cewa, abin da ya haifar da tsamin
dangantakar ba wai bambancin jam’iyya ba ne, domin jam’iyya guda suke wato NPC,
amma aƙidun da suke a cikin addinin Musulunci daban-daban ne, wato Sardauna ɗan
Ƙadiriyya ne, shi kuwa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ɗan Tijjaniyya. An bayyana cewa,
ziyarar da Shehu Ibrahim Inyasss ya kawo Nijeriya a shekarar 1962 zuwa Kano da kuma
ziyarar Sardauna zuwa Kano a rana guda su ne suka rura wutar rikicin da haifar da
tsamin dangantakar da ta yi sanadiyyar cire sarkin daga kujerarsa. An nuna cewa,
maimakon Sarkin Kano ya je ya taro Sardauna (Baƙadire) sai ya tafi wurin Shaihinsa
Ibrahim Inyasss(Batijjane)[6]. Idan aka dubi waɗannan
bayanan za a yarda cewa lallai aƙidar addini ta taka muhimmiyar rawa a cikin siyasar
Nijeriya.
Mabiya aƙidun addini sun
ci gaba da bayyana matasayarsu a cikin tarihin siyasar jam’iyyu, inda wasu sukan
fito da sunan wata aƙida su nuna ɗan takarar da suke goya wa baya, ko kuma su yi
kira da a goya wa wannan ɗan takarar baya. A wasu lokutan wasu ba su amfani da sunan
jam’iyyar da suke goya wa baya, sai dai su dubi ɗan takara da suka natsu da shi,
sai su yi kira da a goya masa baya. Irin haka ya faru a jamhuriyar da ake ciki wato
jamhuriya ta huɗu, inda malamai daga mabambantan aƙidu suka yi kira ga mabiyansu
kan wanda ya kamata su zaɓa. Alal misali, ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Iƙamatis Sunnah wadda aka fi sani da Izala
ta goya wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari baya a lokacin zaɓen 2019, kamar
yadda ya bayyana a cikin jaridar Daily Nigerian:
“Fitacciyar ƙungiyar Addinin Musulunci ta
Nijeriya wadda ke da rassa a ƙasashen Nijar da Kamaru ta yi kira ga mabiyanta da
su zaɓi shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a zaɓen da shugaban ƙasa da za a yi nan gaba
a wata mai kamawa.”
(Jafar, 2019).
Idan aka dubi wannan misali
za a ga cewa wannan umarni ne na daga ƙungiyar masu aƙidar Izala zuwa ga mabiyanta
a kan su zaɓi wani ɗan takara na wata jam’iyyar siyasa. Duk da cewa ba lallai ne
kowane mabiyin aƙidar ya karɓi wannan kira ya kuma zaɓi ɗan takarar da suka ayyana
ba, amma dai za a samu wasu kaso da za su bi wanda shugabancin aƙidarsu ta addini
ta ayyana masu, kuma wannan yana nuni ne ga irin tasirin da aƙidun addini suke da
shi a cikin siyasar jam’iyyu. Har ila yau, akan samu inda mabiya wasu aƙidun da
suke da saɓanin fahimta da Izala su ma su ce ba za a zaɓi ɗan takarar da suka ayyana
ba, domin nuna ɗan takarar da ƙungiyar ta yi ya nuna cewa yana tare da wannan aƙidar
ke nan. Don haka su kuma ba za su zaɓe shi ba. Ga misali:
“Shahararren malamin addinin Musulunci
kuma shugaba Darikatul Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yi kira ga mutanen
yankin Bogoro/Dass/da Tafawa Balewa a jihar Bauchi da su zabi kakakin majalisan
wakilai, Yakubu Dogara. Ya bayyana hakan ne yayin da kakakin ya kaiwa babban malamin
ziyara gidansa inda yayi kira ga jama'a kada su zabi malaman da suke amfani da addini
wajen raba kan al'umma. Ya ce Yakubu Dogara bai nuna bangarancin addini, yana son
zaman lafiya, kuma ya cancanci ya wakilci jama'a domin cigaba da ayyukan kwarai
da yakeyi.”
(Mudathir, 2019).
Duk da cewa a cikin wannan
misalin malamin bai kama sunan wata aƙida kai tsaye ba, amma ya yi ishara da cewa
kada a zaɓi malaman da suke amfani da addini wajen raba kan al’umma, wanda wannan
fitacciyar shaida ce da wasu aƙidun Musulunci suke yi wa masu aƙidar Izala. Bugu
da ƙari, kasancewar Yakubu Dogara Kirista ne, shi kuwa abokin takararsa a lokacin,
Sheikh Ɗalhatu Abubakar Hakimi, malami ne mabiyin aƙidar Izala, kuma shaihin na
ɗariƙar Tijjaniyya ya goyi bayan a zaɓi Kiristan maimakon Musulmi ɗan Izala, har
ma ya yi kira ga mabiyansa. Wannan ya sa ake ganin cewa bambancin aƙidarsa ta Tijjaniyya
da Izala ce ta haifar da hakan. Ke nan, wannan ma wani tasiri ne na aƙidun addini
a cikin siyasa da za a iya gani a fili, wanda kuma za a iya alaƙanta shi da irin
rashin jituwar da aka yi ta samu tun farkon samuwar siyasar jam’iyyu a ƙasar Hausa
a wuraren shekarun 1950.
Idan aka dubi dukkan bayanan
da aka kawo a sama za a fahimci cewa, tun farkon siyasar jam’iyyu a ƙasar Hausa
aƙidun addini sun riƙa taka muhimmiyar rawa a cikinta. Haka kuma tasirin waɗannan
aƙidun a cikin siyasar ya taimaka wajen ɗorewar siyasa a cikin tsawon zamani, domin
ya samar da wani salon hamayyar siyasa mai ɗauke da
ruhin addini. Haka kuma siyasa ba ta kasancewa sai da hamayya, domin shi ne sinadarinta.
4.6.3 Danganta ‘Yan Siyasa Da Masu Mulki Da
Manyan Madogaran Addinin Musulunci
A cikin tarihin siyasar
jam’iyyu a ƙasar Hausa masu mulki da ‘yan siyasa sun riƙa danganta kansu da manyan
turaku na addinin Musulunci wajen cim ma manufofinsu na siyasa. Kamar yadda aka
sani ne, babu wani mutum a cikin al’umma wanda zai so a danganta shi da wani abu
na banza ko kuma mutanen banza, kowa yana so a yabe shi, kuma a danganta shi da
abin ƙwarai ko mutanen kirki. Wannan ya sa ‘yan siyasa a kodayaushe sukan riƙa danganta
kansu, ko neman kusanci da wasu abubuwa masu ƙima da daraja a idon mutane, da kuma
danganta kansu da mutanen da suke ganin masu ƙima ne a idon al’umma.
Alƙur’ani shi ne babban
littafin da kowane Musulmi yake taƙama da shi, littafi ne mai daraja da ƙima a idon
kowanne Musulmi, domin shi ne litafin shari’ar Musulunci da Allah ya saukar wa Annabi
Muhammadu (S.A.W) zuwa ga mutane. Kowane Musulmi yana girmama Alƙu’ani kuma yana
tattalinsa, ba ya kuma ƙaunar ganin ko yaya an wulaƙanta shi, domin wulaƙanta shi
wulaƙanta addinin Musulunci ne. Wannan ya sa idan aka ce Alƙur’ani shi ne babban
madogaran addinin Musulunci to ba a yi kuskure ba. Baya ga Alƙur’ani wanda yake
maganar Allah ne kai tsaye, babu wani kuma wani abu da Musulmi suke girmamawa kamar
maganganu da ayyukan Annabi (S.A.W.) waɗanda aka tattara su cikin hadisansa. Waɗannan
su ne manyan madogaran kowane Musulmi wajen gudananar da addini, kuma duk yadda
aka wulaƙanta su dole zuciyar kowane Musulmi ta sosu.
A zamanin siyasar jamhuriya
ta ɗaya, an samu lokacin da shugaban jam’iyyar AG wato Awolowo ya gudanar da yaƙin
neman zaɓe inda ya riƙa watso takardu da suka shafi manufofin siyasarsa. Magoya
bayan wasu jam’iyyu a Arewa sun soki wannan tsari nasa, inda suka ce a cikin wannan
takardar da ake watsowa daga jirgin sama akwai ayoyin Alƙur’ani da hadisai a ciki.
Dubi abin da jaridar Sodangi ta buga:
“Mun sami wani labari daga Alhaji Salihu
Durumin Iya cewa yana so mutane su gane kuskuren shugaban jam’iyyar AG Awolowo da
yake watso wasu takardu daga jirgin samansa cikin takardun da yake watsowa akwai
masu ayoyin alƙur’ani da kuma hadisai wannan wulaƙanta ayoyin Alƙur’ani da hadisai
ne wannan ta’adda da awolowo ya yi ta ɓata wa Musulmi rai ƙwarai da gaske don haka
ba Awolowo ba ko Dujal ne muka ga yana wulaƙanta addini sai mun nuna masa kuskurensa
muna roƙon kada kowa ya ya yarda ya zaɓi AG jam’iyyar Awolowo”
(“Kuskuren Awolowo”, 1959).
A cikin jaridar an nuna
cewa, Awolowo ya tafka babban kuskure, ta hanyar watso takardun da suke ɗauke da
ayoyin Alƙur’ani da hadisai. ‘Yan hamayya sun ce wannan cin mutuncin
addinin Musulunci ne, kasancewar mafi yawan al’ummar yankin Arewa Musulmai ne, wannan
ya sa suka nuna fushinsu ƙwarai da gaske. A cikin jaridar sun bayyana cewa ba awolowo
ba, ko Dujal ne ya tafka irin wannan ɗanyen aikin sai sun nuna masa kuskurensa,
kuma suka yi kira da cewa kada jama’a su kuskura su zaɓi jam’iyyar AG ta Awolowo.
Idan aka duba za a ga
cewa, an danganta wasu manyan madogaran addinin Musulunci ne da siyasa. Da ma jam’iyyun
siyasar Arewa suna kallon jam’iyyar AG a matsayin ‘yar hana ruwa gudu ce, domin
tana ta ƙoƙarin kiran mutane su bi jam’iyyarta wanda hakan zai raunata sauran jam’iyyun
Arewa ta hanyar rage masu magoya baya. Samun wannan kuskuren na Awolowo tamkar sara
ne a kan gaɓa, domin sun siyasantar da abin, suka kuma nuna cewa ya ci mutuncin
addini kasancewarsa ba Musulmi ba don haka kada a zaɓi jam’iyyarsa.
Haka kuma, irin mutanen
da za a iya kiransu da madogaran addini da ‘yan siyasa sukan danganta kansu da su
sukan kasance ba ‘yan siyasa ba ne, suna dai da alaƙa ta kusa da al’umma ta fuskar
zamantakewa ko aƙida ko kuma ma addinin Musulunci baki ɗayansa. Wasu sukan kasance
malaman addini ne waɗanda ake ganin girmansu da ƙimarsu da kuma darajarsu, a wasu
lokutan ma wasu akan ɗauke su a matsayin waliyyai ne, domin mabiyansu suna ganin
cewa sun kai wannan matsayin duba da irin ɗimbin iliminsu, da tawali’unsu da gudun
duniya da tsantsainin da suke da shi, wannan ya sa ake ganin suna da kusanci da
Allah, wanda ya sa ake ganin girma da ƙimarsu a cikin al’umma. A wasu lokutan ma
akan samu waɗanda kan danganta kansu da tsatson Annabawa. Irin waɗannan mutane kowa
zai so a ce yana da kusanci da su, kasancewar su bayin Allah ne mutanen kirki. Irin
wannan ya fito a cikin tarihin siyasar ƙasar Hausa, domin kuwa Paden, (1973: 310)
ya bayyana cewa:
“A lokacin zaɓen 1961 ‘yan siyasa da dama
sun riƙa ƙoƙarin yin amfani da biyayyar da mabiya wasu aƙidu na addini suke wa shugabanninsu
domin samun goyon baya. Irin wannan yanayi ya ƙaru a cikin shekarun 1961 zuwa 1964.”
Masanin ya nuna, ‘yan
siyasa sun yi amfani da biyayyar da mabiya wasu aƙidu ko ɗariƙu suke yi wa malamai
ko shugabanninsu wajen neman goyon bayan al’umma, musamman daga shekarun 1960 zuwa
1964 kamar yadda ya bayyana. Ba daga nan kawai abin ya tsaya ba, an ci gaba da amfani
da irin wannan hanyar a cikin siyasar ƙasar Hausa, inda irin wannan ya fito a cikin
ayyukan rubutaccen zube na Hausa.
Tarihi ya nuna cewa, manya
kuma fitattun ‘yan siyasa a jamhuriya ta farko sun bi irin waɗannan hanyoyin domin
samun goyon bayan al’umma domin samun nasara a zaɓuɓɓuka. Ba samun nasarar ko rashinta
ne abin da wannan batu ya karkata a kai ba, an dubi irin yadda akan ƙulla alaƙar
ce domin duniya ta gani, kuma domin masoya ko mabiyan waɗannan muhimman mutane su
yarda, su kuma aminta da wanda suka gani tare da mutumin da suke girmamawa. Alal
misali, a jamhuriya ta farko an samu wani rahoto da jaridar Daily Comet ta ruwaito a kan ziyarar da shugaban
NEPU Malam Aminu Kano da wasu manyan ‘yan jam’iyyar suka kai wa Shaihin Malamin
nan kuma jagorar ɗariƙar Tijjaniyya na Afirka, Shehu Ibrahim Inyasss kamar haka:
“Babban shugaba kuma jagoran NEPU, Alhaji
Aminu Kano ya bar Ikko a jirgin sama zuwa Senegal domin ziyara ta kwanaki bakwai
ga babban Malamin addinin Musuluncin nan Shaikh Ibrahim Niass a Kaulaha. A cikin
tawagar akwai muhimman mutane biyar da suka masa rakiya, waɗanda suka hada da: Babban
sakataren NEPU, Abubakar Zukogi, uban jam’iyyar NEPU na kasa kuma wakili a majalisar
wakilai ta Arewa, Alhaji Salihu Nakande, da mataimakin ma’ajin jam’iyya na kasa
Alhaji Ahmadu Trader, da kuma Alhaji Sharif Ali fitaccen malami mai wa’azi a lardin
Sakkwato. A ziyarar da za su je Kaulaha, Malam Aminu da ‘yan rakiyarsa za su gana
da Shaikh Ibrahim Kaulaha tare da gudanar da wasu ayyukan ibada tare da shi.”
(“Aminu Kano da Tawagarsa”, 1964).
Duk da cewa Malam Aminu
Kano mabiyin ɗariƙar Tijjaniyya ne, amma idan aka duba za a ga akwai siyasa cikin
ziyarar, domin kuwa ko daga abokan rakiyar tasa wato shugabannin jam’iyyar NEPU
za a fahimci haka. Haka kuma, ko daga yadda aka buga labarin aka kuma watsa shi,
an yi ne don mabiya Shehu su san cewa manyan jagororin NEPU fa sun ziyarce shi,
ko ba komai za su ƙara samun gamsuwa da sallamawa ga jam’iyyar da shugabanninta
suka ziyarci shaihinsu. Ziyarar za ta ƙara wa jam’iyyar NEPU farin jini a wajen
mabiya ɗariƙar Tijjaniyya, sannan za ta ƙara mata yawan magoya baya. Ke nan, idan
aka duba a nan an yi amfani da darajar Shehu Ibrahim Inyasss wajen ƙara wa jam’iyyar
NEPU da shugabanninta da kuma ‘yan takararta magoya baya.
Ba jam’iyyar NEPU kaɗai
ce ta yi amfani da wannan salon ba, wasu jam’iyyu ma sun yi amfani da shi da manufar
samun goyon bayan jama’a domin samun nasarar jam’iyyarsu a wurin zaɓe. Wani ƙarin
misali shi ne, yadda jam’iyyar AG ta yi amfani da wasu ‘ya’yanta domin kai wa Shehu
Ibrahim Inyasss ziyara domin samun tubarraki. Ga misalin:
“A ƙoƙarin Obafemi Awolowo na jam’iyyar
AG da Ibrahim Imam na samun goyon bayan Ibrahim Niass a zaɓen 1961, an tattauna
batun a cikin shari’ar Awolowo a 1962 A shaidar da Ibrahim Imam ya bayar ya ce,
‘ na ziyarci Senegal har sau biyu na ziyarci Shehu Ibrahim Inyass a Kaulaha a 1956,
sannan kuma lokacin da ni da wasu muka raka ka wata ziyara a Ghana a 1961 mun haɗu
da shi (Ibrahim Inyass) a can ni ne na yi maku tafinta tsakaninka da Shehu don ina
jin Larabci shi ne shugaban ɗariƙar Tijjaniyya. Na faɗa maka cewa yana da mabiya
sosai a ɓangarori da dama na Afirka ciki har da Nijeriya inda yake da mabiya da
dama a duk faɗin ƙasar. Kuma yana da ɗimbin mabiya a yankin Arewa domin a nan ne
Musulmi suke da yawa fiye da ko ina ban taɓa tattaunawa da kai cewa idan muka samu
Shehu ya umarci mabiyansa suka goya mana baya jam’iyyarmu za ta yi ƙarfi a Arewa
ba. abin da kawai muka tattauna shi ne buƙatar addu’ar Shehu Inyass addu’ar da Shehu
zai yi mana ta neman nasarar jam’iyyar AG ce da kuma kai kanka ”
(Paden, 1973: 310)
Idan aka dubi waɗannan
bayanai za a ga cewa sun ƙunshi neman kusanci da wani muhimmin mutum ne mai daraja
domin samun nasara a siyasance. A cikin bayanin an nuna cewa, ‘yan siyasar guda
biyu suna so su yi amfani da darajar Shehu Ibrahim ne su samu jama’ar da za su goya
wa jam’iyyarsu ta AG baya a lokacin zaɓe wanda hakan zai iya sa su samu nasara.
Idan aka dubi bayanan
da Ibrahim Imam ya yi wa shugaban AG wato Awolowo, ya nuna masa cewa Shaihin malamin
yana da ɗimbin mabiya a duk faɗin Afirka ciki kuwa har da Nijeriya. Ya nuna masa
muhimmancin yankin da shi Ibrahim Imam ɗin ya fito wato yankin Arewa, inda ya nuna
masa cewa mafi yawan ‘yan Arewa Musulmi ne mabiya ɗariƙar Tijjaniyya, wanda idan
suka samu sanya bakin shaihin za su samu ƙarin magoya baya sosai daga yankin. Ko
ma dai shaihin bai sa baki a cikin lamarin siyasar kai tsaye ba, an nuna cewa ana
buƙatar ya yi wa jam’iyyar AG addu’a da kuma ɗan takararta wato Awolowo domin samun
rinjaye a zaɓen da suke tunkara a wancan lokacin. Shi kansa wannan neman sa albarkar
daga wurin muhimman mutane ko Shehunnai, wani salo ne da za a iya nuna wa magoya
baya cewa ai Shehu ya sanya wa jam’iyya kaza albarka don haka ita ya kamata a zaɓa.
A jamhuriya ta biyu ma
an samu irin wannan fasalin na danganta ‘yan siyasa da manyan madogaran addini domin
samun goyon bayan al’umma. An samu daga Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo cewa, jam’iyyar PRP ta Malam Aminu Kano ta riƙa
amfani da hoton Shehu Ibrahim Kaulaha domin neman magoya baya. Ga abin da ta ce:
An yi kira ga Hukumar Zaɓe ta ƙasa da ta
duba yadda jam’iyyar PRP take yin amfani da hoton Shehu Ibrahim Kaulaha wanda aka
rubuta harufan PRP a ciki, saboda neman magoya baya Alhaji Musan Sati ya ce, dokar
tsarin mulki ta ƙasar nan ta haramta yin amfani da addini a cikin harkokin siyasa,
amma kuma ga shi PRP tana cusa addini don neman magoya baya.”
(“Jam’iyyar PRP Na Ci
Da Addini”, 1979).
Idan aka dubi wannan batu
da yake sama za a ga cewa, a kakar zaɓe na jamhuriya ta biyu, wato shekarar 1979,
an yi amfani da darajar shugabannin addini wajen nemen magoya baya a jam’iyyun siyasa.
A cikin wannan misalin an nuna cewa jam’iyyar PRP ta yi amfani da hoton Shehu Ibrahim
Inyass domin jawo hankalin al’umma su goyi bayan jam’iyyar. Jam’iyyar sun yi amfani
da hoton shaihin malamin mai ɗauke da haruffan PRP a ciki, kasancewarsa babban jigo
ne a cikin ɗariƙar Tijjaniyya, wannan zai sa duk wani Batijjane ya ji ya gamsu da
tafiyar da aka sanya Shehu Ibrahim Inyass a cikinta. A cikin misalin an bayyana
cewa, tsarin mulkin mulkin Nijeriya ya haramta amfani da addini a cikin siyasa.
Don haka ake kira ga hukumar zaɓe da ta hukunta jam’iyyar don ta karya doka.
Irin wannan salo ya ci
gaba da gudana a cikin tarihin siyasar Arewacin Nijeriya, inda da zaran an kaɗa
gangar siyasa ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban sukan riƙa kai ziyara da sunan
neman albarka ga manyan malamai. Irin waɗannan ziyarce-ziyarce da neman sanya albarka
akan yi su ta hanyar bin wasu malaman har gidajensu ko wuraren ibada, kamar masallatan
Juma’a ko makarantu ko kuma majalisun da suke bayar da karatu. Yawancin ‘yan siyasa
sukan yi wannan ne domin samar da wata alaƙa da za a nuna wa duniya cewa suna tare
da irin waɗannan fitattun malaman. Wannan zai sa su samu goyon bayan mabiyan malamin
ko wani kaso daga cikinsu. Ga misali:
“A daya daga cikin hotunan ziyarar tasa
wanda tuni suka karade shafukan sadarwa, an gano Tinubu durkushe a gaban jigon na
darikar Tijjaniyya yayin da shi kuma ya dafa kansa sannan ya saka masa albarka tare
da yi masa tofin addu’o’i.”
(Musa, 2022)
Sanin irin darajar
babban Shaihin da kuma yawan mabiyansa a matsayinsa na babban jigo a ɗariƙar Tijjaniyya
kamar yadda jaridar ta ruwaito shi ne dalilin da ya sa ɗan siyasar ya ziyarce shi.
Kamar yadda jaridar ta nuna cewa shi ne babban jigo a wannan ɗariƙa yana da ɗimbin
mabiya waɗanda ake sa rai su goyi bayan ɗan takaran kasancewar sun gan shi tare
da shaihinsu. Ke nan har a yau irin wannan siyasar ta neman tabarruki daga manyan
madogaran addini tana tasiri a cikin siyasa.
A wani misalin
na daban kan yadda ‘yan siyasa sukan riƙa danganta kansu da manyan shugabannin addini,
Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ruwaito
cewa, ɗan takarar shugabancin Nijeriya na Jam’iyyar PDP ya kai wa Shehu Ɗahiru Bauchi
ziyara. Dubi abin da jaridar ta ruwaito:
“Dan takaran
shugaban kasa karkashin tutar jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar (Wazirin Adamawa),
ya kai wa fitaccen malamin addinin Islaman nan dake Bauchi Sheikh Dahiru Usman Bauchi
ziyara a gidan sa dake Bauchi. Atiku Abubakar
ya ziyarci jihar Bauchi a ranar Laraba shi da wanda yake masa takaran mataimaki,
gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa.”
(Isah, 2022)
Duk da cewa jaridar ba ta bayyana dalilin kai ziyarar
ba, amma dai za a iya fahimtar cewa duk abu ɗaya ake yi wa kai da kawo, wato goyon
bayan mabiya wanda ake fakewa da cewa neman albarka aka je. Duk da cewa an san malamai
mutane ne masu tsoron Allah da kuma kusanci da shi, wannan ya sa ake sa rai addu’arsu
ta kasance ta fi saurin karɓuwa fiye da waɗanda ba su ba, amma dai ko da neman addu’ar
‘yan siyasa suke zuwa suna kuma la’akari da yawan mabiya, domin kuwa wannan ya samo
asali cikin tarihin siyasar ƙasar Hausa. Akan riƙa neman kusanci da wani don a ribaci
yawan mabiyansa da kuma yadda yake da ƙarfin faɗa a ji.
Irin wannan rige-rigen
samun karɓuwa ga mabiya ya sa kowane ɗan siyasa a yau, idan bai je wurin manyan
malamai da Shehunnai sun sa masa albarka duniya ta gani ba sai a ga kamar ba ya
tare da wannan malamin. Shi kansa ɗan takaran ba zai samu natsuwa ba in bai je ɗin
ba, domin zai ga cewa zai rasa goyon bayan mabiyan wannan babban malami addinin.
Watakila wannan
dalilin ne ya sa shi ma ɗantakarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar LP a zaɓen shekarar
2023 ya garzaya shi ma kamar yadda jaridar Legit
Hausa ta ruwaito kamar haka:
“Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na
jam'iyyar Labour na kara tsawon kafa da hannu wajen tallata kansa a fadin kasar
nan gabanin zaben 2023 Obi da abokin gaminsa, Dr Yusuf Datti Baba-Ahmed sun kai
wata ziyara a jihar Bauchi, inda suka gana da babban malamin addini na Afrika, Sheikh
Dahiru Usman Bauchi.”
(Ibrahim, 2022).
A nan shi ma Peter
Obi ne da mataimakinsa suka kai ziyara kamar yadda takwarorinsu na sauran jam’iyyu
suka kai wa Shaihin. Irin wannan ziyarce-ziyarcen ‘yan siyasa sun mayar da su kamar
dole a cikin al’amuran siyasa, domin kuwa a yayin ziyarar in ba a roƙi mabiya su
zaɓa kai tsaye ba za a roƙi Shehu ya yi addu’a don neman goyon bayan al’ummar ƙasa
da kuma samun nasara.
4.6.4 Amfani Da Daraja Ko Matsayi Wajen Tallata Ɗan Takara
Amfani da daraja ko matsayin
wasu mutane wajen tallata ɗan takara abu ne wanda ya samo asali a cikin tarihin
siyasar jam’iyyu a ƙasar Hausa. ‘Yan siyasa kan yi ƙoƙarin nuna wa al’umma darajarsu
ko matsayinsu a cikin al’umma. Sukan yi amfani da alaƙa ta jini ko kusanci da take
tsakaninsu da wani mutum ko wasu mutane masu daraja a wajensu domin samun goyon
baya daga gare su. Sanannen abu ne
a ƙasar Hausa ana girmama nasaba da kuma tsatson da mutum ya fito
daga cikinsa. Wannan ya haifar da bambanci tsakanin ɗan wane da kuma ɗan ba kowa
ba. Irin wannan bambancin da aka samu shi ne kuma ya samar da waɗanda ake kira masu
shi da marasa shi, ko masu mulki da talakawa da sauransu.
Tun kafuwar siyasar jam’iyyu
a ƙasar Hausa a wuraren shekarun 1950 an riƙa samun irin wannan siyasar, wato ta
amfani da darajar ko matsayin wajen tallata ɗan takara, kuma wannan tsarin fito
da dangantakar ta yi tasiri ƙwarai ga ‘yan takara da dama, kasancewar da dama cikin
‘yan siyasar da suka fara shugabanci a farkon siyasar jam’iyyu a ƙasar Hausa sarakuna
ne da ‘ya’yan sarakuna. Wannan ya sa dangantakarsu da matsayin da suke kai na sarauta
sun taka muhimmiyar rawa wajen tallata su ga al’umma. Alal misali, Sarkin Kano Muhammadu
Sanusi da Sarkin Zazzau Jafaru da Sardauna Sakkwato dukkansu ‘ya’yan gidan sarauta
ne, kuma manya daga cikin ‘yan siyasar farko-farko waɗanda suka riƙe manyan muƙaman
siyasa a ƙasa, kuma dukkansu da ma wasu ‘ya’yan sarakunan Arewacin Nijeriya da dama
sun ci alfarmar gidajen da suka fito wajen samun muƙaman siyasa.
Irin wannan alfarma ta
ci gaba da gudana a fagen siyasar jam’iyyu a ƙasar Hausa, wanda har aka kai ga ana
tallata ‘yan takarar siyasa da su. Paden (1973: 312) ya bayyana cewa:
“ A lokacin yaƙin neman zaɓen shekarar 1964
an ga tasirin daular Usmaniyya a Kano, inda aka sanya addini ya shiga harkokin siyasa
fiye da yadda aka saba a baya. Ya kasance hotunan da jam’iyyar NPC ta yi amfani
da su domin yaƙin neman zaɓe suna ɗauke da hoton Sardauna ne haɗe da nasabarsa da
aka jero wanda aka nuna ya samu asali ne tun daga Annabi Muhammadu (S.A.W) Su ma
NEPU sai suka ɗauki wannan salon a cikin birnin Kano, inda manyan hotunan yaƙin
neman zaɓensu suke ɗauke da hoton Malam Aminu Kano tare da Shehu Ibrahim Inyasss
a Kaulaha.”
A nan idan aka duba za
a ga cewa masanin ya yi bayani ne kan yadda ‘yan siyasa suka fara amfani da matsayinsu
ko darajarsu a wurin al’umma wurin tallar siyasarsu da ‘yan takararsu. Alal misali,
jam’iyyar NPC ta yi amfani da nasabar Sardauna ta wurin kakansa Shehu Usmanu aka
ƙulla nasabar har zuwa ga Annabi Muhammadu (S.A.W) domin nuna cancantar jam’iyyarsu,
domin duk wanda ta tabbata ya fito daga wannan tsatson to lallai ya fito daga tsatso
mafi girman daraja. Don haka suna nuna idan aka zaɓi
jam’iyyar NPC an zaɓi jam’iyyar mutanen kirki. Ta wata fuskar za a
ga cewa, ai ko ba a danganta shi zuwa ga tsatson gidan Annabta ba, kakansa Shehu
Usmanu shi ma hujja ne na kyakkyawar tsatso. Ke nan, in ma don Shehu za a yi zaɓe
to jam’iyyar NPC ta kai, domin dai jam’iyyar jikokin
waliyyai ce.
Tarihi ya nuna cewa, a
ɓangaren ‘yan hamayya ma an samu irin wannan. An faɗa cewa ana
tsaka da yaƙin neman zaɓe, shugaban NEPU Malam Aminu Kano ya kira Sardauna a wayar
tarho ya ba da shawara kan raba addini da siyasa, inda a ganinsa yake ganin
bai dace ba[7]. Da suka lura da irin
salon da aka shigo da shi, sai su ma suka ce in kiɗa ya sauya to dole rawa ma ta
sauya. Nan da nan su ma sai suka ɗauki wannan salon ta hanyar haɗa hoton Malam Aminu
Kano da na Shehu Ibrahim Inyasss, inda aka riƙa tallar jam’iyyar NEPU da hoton Malam
Aminu haɗe da Shehu. Su ma a ɓangarensu suna ganin wannan zai taimaka wa mabiyan
Shehu su rungumi ɗan takarar da jam’iyyar take tallatawa, kuma su zaɓe shi.
Duk da wannan salon tallatar
‘yan takara da martabar gida da kuma matsayi, sai da ‘yan hamayya suka kushe wannan tsari
da jam’iyyar NPC ta zo da shi, inda suka riƙa kushe nasabar abokan hamayya da kuma
matsayin da al’umma suke ganin su da shi, kuma suka riƙa cewa, ai Sardauna ma ba
jikan Shehu ne ba kamar yadda ake yaɗawa. Dubi wannan misalin:
“Aminu ya ce wai Sardauna ba jikan Shehu
ne ba, kuma wai Sardauna Jahili ne cikin Musulunci. Mu kam mun amince Sardauna jikan
Shehu ne kuma ba jahili ne ciki cikin Musulunci ba.”
(Salihu, 1959).
A nan idan aka duba za
a ga cewa wani daga cikin magoya bayan NPC ne yake ƙalubalantar shugaban NEPU kan
zargin da ya yi kan nasabar shugaban NPC, inda ya ce ai ƙarya ake wa mabiya da dangantakar
jini, wai shi ba ma jinin Shehu Usmanu ne ba, domin Shehu babban malamin Musulunci
ne, shi kuwa Sardauna ba shi da wannan ilimin, inda ya kira shi jahili a cikin Musulunci
kamar dai yadda aka gani a cikin misalin da yake sama.
‘Yan hamayya na jam’iyyar NEPU sun kuma ci gaba da kushe ‘yan jam’iyyar
NPC mai mulki cewa suna ta ƙoƙarin danganta kansu da Shehu wanda hakan ba shi da
wani amfani ga talakawa, inda suka nuna cewa ai ko ma dai shi jikan Shehu ne, ba
Shehun ne za a zaɓa ba. Don haka in don Shaihu za su yi zaɓe in ji Malam Aminu Kano
to Shehu ya mutu. Dubi abin da yake cewa:
“Aminu
Kano ya zargi Sardauna da ƙumbiya-ƙumbiya cewa wai shi jinin Shehu ne, ga shi kuwa
Shehun ya mutu. Wai don haka in ji Aminu Kano bai ga ta yadda za a yi mutane su
zaɓi jinin mutumin da ya mutu ba, idan dai ba jihala mutanen suka sa a ransu ba.
(Salihu, 1959).
A nan idan aka duba za
a ga cewa, ƙoƙarin da jam’iyyar NPC take yi ne na tallata ‘yan takararta da alfarmar
Shehu Usmanu, musamman ma Sardauna, shi ne ‘yan hamayya suka ƙoƙarin dakushe
hasken wannan dangantakar tun da sun ba da shawarar cewa a cire wannan tsarin na
haɗa addini da siyasa, amma ba su yi nasara ba.
A wani misalin na daban
da ya fito a cikin jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo
ta ranar 20 ga Nuwamba, 1959, an nuna yadda wakilin da jam’iyyar NPC ta tura domin
yaƙin neman zaɓe a Sakkwato daga lardin Kano, ya nuna irin dangantakar da take tsakanin
Shehu Usmanu Ɗanfodiyu da ‘yan NPC waɗanda ya ce ‘yan NEPU suna zaginsu. Dubi abin
da jaridar ta ruwaito:
“Malam Sabo ya ci gaba da cewa, ga shi jam’iyyar
NEPU tana ta yaba wa da aikin Shehu Usman Ɗan Fodiyo sosai, amma kuma ga shi tana
ta zagin jikokinsa. Idan dai da jam’iyyar NEPU tana son Shehu Usman Ɗan Fodiyo sosai
da kuwa ba ta riƙa tozarta jikokinsa. Domin fa Hausawa sun ce maso uwa ya so ɗanta.
Malam Sabo Bakin Zuwo ya ce kure ne mutum ya so Annabi amma ya riƙa zagin jikokinsa.”
(“Sabo Bakin Zuwo Ya Yi
Nasarar Yaƙin Zaɓe”, 1959).
A nan Malam Sabo Bakin
Zuwo yana ƙoƙarin nunawa dangantakar shugabannin NPC ne da Shaihu Usmanu Ɗafodiyo.
Inda ya nuna cewa, ko don alfarmar Shaihun bai kamata ‘yan NEPU su riƙa zagin jikokinsa
ba, wato su Ahmadu Bello Sardauna. Haka kuma, dangantakar Shaihu Usmanu ta jini
ce har zuwa ga Manzon Allah (S.A.W). Don haka duk masoyin Manzon to ya zama wajibi
ya so duk wani wanda ya dangance shi. Bai kamata mutum ya riƙa iƙirarin cewa yana
son Annabi ba bayan kuwa yana tozarta jikokinsa. Don haka ya zama dole in dai mutun
yana ƙaunar Annabi to ya so Shaihu Usmanu. Wanda kuwa yake son Shaihu Usmanu to
dole ya so Sardaunan Sakkwato, kasancewarsa jikan Shaihu Usmanu.
Irin wannan ya ci gaba da fitowa a cikin ayyukan
zube na Hausa inda aka riƙa amfani da matsayi ko dangantaka wajen tallata ‘yan takara,
ko kuma a yi amfani da wannan a matsayin hanyar da ake bi domin nuna cancantar ‘yan
takara. A jamhuriya ta huɗu da ake ciki yawancin ‘yan takara ba cancantarsu ce take
sa a tsayar da su a ƙarƙashin tutar wata jam’iyya ba. Akan yi amfani da matsayinsu,
ko dai ya zama matsayinsu a jam’iyyance ko kuma matsayin abin arziƙinsu wato abin
hannunsu. Sau da dama akan samu ɗan takara ya cancanta, amma saboda ba shi da abin
hannu ko kuma ba wani matsayi mai girma yake da shi a cikin al’umma ba, sai a ce
ai bai cancanta. Misali, irin wannan ya fito a cikin Littafin Tura Ta Kai Bango, inda Shugaban jam’iyyar
Riƙau Alhaji Harambe yake jawabi a wajen yaƙin neman zaɓe. Dubi abin da yake cewa:
“ lallai kar ku sake ɗan da bai gaji arziƙi
ba ya jawo maku bala’i. In kuwa kun sake za ku yi da na sani wata jam’iyya ce wadda
ko sunanta ba zan faɗa ba cikin sharrukanta da ta tanada sun haɗa da lalata darajar
sarakunanku. Su sa talaka ya raina mutane masu martaba ”
(Katsina, 1983: 8).
Wannan misali ya fito
da hoton tallata ɗan takara ne ta hanyar amfani da matsayi ko daraja, domin an nuna
cewa talaka bai isa ya yi shugabanci ba, domin wanda bai gaji arziƙi ba ana nufin
talaka ne, kuma zaɓensa tamkar jawo wa kai bala’i ne. An ci gaba da nuna cewa jam’iyyar
da ba tasu ba tana da sharri sosai, domin za ta lalata darajar sarakuna domin su
ne masu matsayi da daraja a cikin al’umma, sannan kuma wannan jam’iyyar za ta sa
talaka ya raina mutane masu martaba. Idan aka duba za a ga, shi talaka dai a nan
ba shi da wata daraja da martaba, wannan ya sa suke ganin cewa masu hannu da shuni,
waɗanda suka gaji arziƙi da masu mulki ko sarakuna ko kuma jininsu su ne waɗanda
ya kamata su ci gaba da zama a sama, shi kuma talaka ya ci gaba da biyayya.
A wani misalin na daban
an nuna cewa, jagororin jam’iyyar hamayya da mabiyansu talakawa
ne waɗanda ba su da wata daraja ko matsayi a cikin al’umma. Don haka ba su cancanci
a zaɓe su ba. Dubi wannan misalin:
“Ni ai da ma na san wannan yaron bai gaji
arziƙi ba. Ubansa fa Na-Torami har ya mutu itace yake sarowa yana sayarwa ”
“Yo shi Garban fa? Ubansa ba mahauci ba
ne karen
lahira?”
(Katsina, 1983: 21-22).
A nan shugabannin jam’iyyar
Riƙau ne suke kushe jagororin jam’iyyar Sauyi, inda suke nuna cewa ai dukkansu ba
‘ya’yan kowa ne ba. Kamar yadda suke nuna cewa ai shi jagoran jam’iyyar ma wato
Hassan, ubansa itace yake zuwa daji ya saro ya sayar. Shi kuwa abokinsa Garba ubansa
mahauci ne, ba wani ƙima ko matsayi suke da shi da har suka cancanci a bi jam’iyyarsu
ko a zaɓe su a wani matsayi ba. Irin wannan shi ne abin ya riƙa faru a jamhuriya
ta farko ma, domin yawanci ‘yan jam’iyyar hamayya talakawa ne da msu ƙananan
sana’o’i kamar maɗinka da majema da masassaƙa da sauransu. Ita kuwa jam’iyya mai
mulki sarakuna ne da attajirai a cikinta.
Ke nan idan aka duba,
irin wannan salon na amfani da dangantaka yana da asali a cikin siyasar jam’iyyu
a ƙasar Hausa, domin kuwa shi ne ya riƙa bayyana a cikin ayyukan adabin Hausa musamman
na zube kamar yadda aka ba da misalai da su.
4.7 Tallata ‘Yan Siyasa Da Ɗaukaka Ko Martabar
Shugabannin Siyasa
Kamar yadda aka yi bayani
a sama cewa ‘yan siyasa suna amfani da matsayi ko darajar wani mutum wajen tallata
kansu ko kuma magoya bayansu su riƙa tallata su a wurin al’umma. Waɗannan masu matsayin
kan kasance ko dai ta fuskar addini ne ko nasaba ko kuma matsayinsu a siyasance.
Tarihi ya nuna cewa, bayan
wucewar jamhuriya ta ɗaya da aka riƙa amfani da darajar manyan waliyyai da Shehunnai,
an ci gaba da amfani da ƙima da matsayin manyan shugabannin siyasa waɗanda suka
shuɗe, ana amfani da abubuwan alherin da suka aiwatar ana tallata ‘yan takara da
sunansu. Alal misali, an sha jin ana kiran ‘yan siyasa da magajin Sardauna ko magajin
Malam Aminu Kano, wannan kuwa ba zai rasa nasaba da irin siyasar da suka gudanar
da kuma ayyukan alherin da suka dasa waɗanda har yanzu ana cin gajiyarsu ba.
Irin waɗannan abubuwan
alheri da manyan ‘yan siyasan suka gabatar lokacin rayuwarsu ya sa ake ganin cewa
duk wanda ya ce zai bi turbarsu, ko kuma turbarsu ma yake bi, to ana sa rai zai
gaji irin kyawawan manufofinsu ne wajen shimfiɗa nasa jagorancin idan ya yi nasara.
Alal misali, a jamhuriya ta biyu, Malam Abubakar Rimi da Malam Balarabe Musa sun
samu nasarar zama gwamnonin jihohin Kano da Kaduna ne a jam’iyyar PRP wadda Malam
Aminu Kano ne jagoranta. Haka kuma Alhaji Shehu Shagari ya yi nasarar lashe kujerar
shugabancin Nijeriya a Jamhuriya ta biyu, a ƙarƙashin tutar Jam’iyyar NPN, wadda
ake yi wa kallon gyauron NPC ta su Ahmadu Bello Sardauna, kamar yadda ake yi wa
PRP kallon gyauron NEPU ce ta su Malam Aminu Kano.
Tarihi ya ci gaba da maimaita
kansa, inda a jamhuriya ta huɗu ma an lura cewa ‘yan siyasa suna amfani da wannan
alfarma ta shugabannin siyasa wajen tallata kansu ko kuma ‘yan takararsu. Misali,
Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso yana alaƙanta tsarin siyasarsa da ta Malam Aminu Kano,
inda yake nuna cewa, turbarsa suke bi wato da shi suke koyi. Tun daga yanayin sanya
tufafinsa da kuma aƙidar ‘yanta talakawa. Da wannan ya riƙa amfani har zuwa lokacin
da ya kafa tasa ɗariƙar siyasar wadda aka kira ta Kwankwasiyya, inda shi ma a yanzu
wasu ‘yan siyasar suke raɓuwa da sunansa don cim ma burinsu a siyasance.
Wani babban misali da
za a iya gani a zahiri dangane da yadda ‘yan siyasa sukan riƙa danganta kansu da
wasu manyan ‘yan siyasa su shiga rigarsu don su samu alfarmarsu shi ne, yadda ‘yan
siyasa suka riƙa danganta kansu da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari tun daga
shekarar 2007 domin samun nasara a zaɓe. Dubi wannan misali:
“ a yau a Nijeriya, ambaton sunan Buhari
ya zama tamkar ambaton wani aikakken umurni ne, ba a ja da shi, ba a muzanta shi
kuma ba a aibanta shi. Hasali ma yawa-yawan wasu ‘yan takara da hotunan Janar Buhari
suke kamfe. Sai ka ga irin waɗannan ‘yan takara sun buga posta (poster) ɗauke da
hotunansu da Buhari, don amincewa da Buhari, don cin albarkacinsa ko tubarrakinsa
ko kuma don shuga inuwarsa, abubuwan da gaskiyarsa(shi Buharin) suka jawo masa.”
(Ibrahim, 2007).
Idan aka dubi wannan bayani
da jaridar Aminiya ta kawo za a fahimci
yadda aka riƙa tallata ‘yan siyasa da martabar shugabannin siyasa. Janar Buhari
ya zama wani tauraro a fagen siyasar zamaninsa, wanda kowane ɗan takara yake so
ya danganta kansa da shi domin ya ci albarkacinsa. Wannan ba zai rasa nasaba da
yadda farin jinin Buharin ya ratsa lungu da saƙo na ƙasar Hausa ba. Ya kasance sunan
shi ne shi ne ake ji a ko ina. Ba a ja da duk wani abu da aka danganta shi da shi,
ba a musu da duk wani abu da aka ce daga wurinsa aka ji, ba a kuma kushe shi ko
aibanta shi a bainar jama’a. Wannan ya sa ‘yan takara da dama suka suka riƙa haɗa
hotunansu da na Buharin domin nuna cewa sun amince da tsarinsa kuma suna tare da
shi, suna goyon bayansa. Sukan yi hakan ne domin cin albarkacinsa da samun shuga
inuwarsa don su samu karɓuwa ga jama’a. Jama’a a wancan lokacin sun yi imani cewa
janar Buhari mai gaskiya ne, kuma duk waɗanda suke tare da shi su ma haka ake sa
rai su zama. Wannan ya sa suka samu farin jini sosai a dalilinsa.
Baya ga ‘yan jam’iyyar
Janar Buhari ta ANPP a wancan lokacin da tarihi ya nuna cewa sun shiga inuwarsa
domin samun karɓuwa, an ci gaba da amfani da irin wannan salon har zuwa kakar zaɓen
shekarar 2015. ‘Yan takara na jam’iyyu daban-daban baya ga jam’iyyar APC wadda Janar
Buhari yake ciki, sun riƙa amfani da hotunansa, inda sukan haɗa da nasu duk da cewa
ba jam’iyya guda suke ba, domin samun tubarrakinsa. Wannan ne ma ya sa jam’iyyar
APC a wancan lokacin suka tsawatar wa ‘yan jam’iyyar hamayya cewa su daina amfani
da farin jinin ɗan takarar jam’iyyarsu domin neman jama’a. Dubi abin da jaridar
Aminiya ta ruwaito:
“Jam’iyyar APC a Jihar Katsina ta gargadi masu takara da suka fito daga wasu
jam’iyyu su daina hada hotunansu da na dan takararta na Shugaban kasa Janar Muhammadu
Buhari. Shugaban jam’iyyar, Dokta Mustafa Inuwa ne ya yi wannan gargadi a waurin
taron masu ruwa da tsaki da jam’iyyar ta yi a otel na Liyafa a ranar Litinin inda
ya ja hankalin ’yan takarar wasu jam’iyyu da ke lika hotunansu da na Buhari su daina
yin haka nan take ko su fuskanci matakin shari’a.”
(Mustapha, 2015)
Kasancewar wannan ɗan siyasa mai matuƙar farin jini a zamaninsa,
wanda har aka bayyana cewa shi ne ɗan siyasa mafi farin a kaf faɗin Nijeriya, kamar
yadda Jaridar Blueprint Hausa ta ranar
26 ga Afrilu ta ruwaito. A zamaninsa an kai ga ba ma ‘yan jam’iyyarsa kaɗai suke
haɗa hotonsa da nasa ba, har ‘yan jam’iyyun hamayya sun lura da irin farin jininsa a lokacin, sai suka riƙa haɗa
hotunansu da nasa duk da cewa su suna neman takara a wata jam’iyyar ce daban ba
jam’iyyarsa ta APC ba. Irin wannan ɗaukaka ta Buhari ta sa ‘yan siyasa a kowane
lungu da saƙo sun riƙa tallata kansu da farin jinin Buhari. A wasu wuraren ma har
magoya bayansu sukan yi masu laƙabi da ‘Buharin wuri kaza’. Alal Misali, ana kiran
wani ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Lere a jihar Kaduna da suna
‘Buharin Lere’ wanda ire-irensa suna da dama. Irin wannan tallata ‘yan siyasa da
farin jini Buhari da wasu ‘yan siyasa musamman na wasu jam’iyyun da ba nasa ba suka
riƙa yi ya kai ga har jam’iyyar APC ta yi barazanar kai ƙarar dukkan masu tallata
kansu da farin jinin Buharin kotu idan ba su bari ba, kamar dai yadda aka gani a
cikin misalin da yake sama.
Bayan kammala zaɓuɓɓukan shekarar 2015, an bayyana cewa Muhammadu
Buhari shi ne ɗan siyasar da mutane suka riƙa mutuwa don murnar samun nasararsa
a zaɓen da aka gudanar. A wannan lokacin sauran ‘yan takara da ba a kai ga yin zaɓen
su ba, kamar gwamnoni da ‘yan majalisar jihohi, sai suka ci gaba da haɗa hotunansu
da na Shugaba Buharin. Ya kai ga ko takarar kansila mutum ya fito sai ya haɗa hotonsa
da na Buhari don ya samu farin jininsa. Dubi wannan misalin da yake ƙasa:
“Wannan bawan Allah
shi ne wanda ya fi kowa farin jini a tarihin ƙasarmu Nijeriya. Ɗaruruwan mutane sun rasa ransu saboda murnar zaɓen da ya ci a
shekarar 2015. An yi lokacin da ko takarar kansila mutum ya tsaya sai ya haɗa hotonsa
da na Buhari don ya ɗosani farin jini. ‘Yan siyasa bila’adadin sun ci zaɓe a sanadiyyar ɗaga hannunsu da Buhari
ya yi, tun kafin ya ci nasa zaɓen a shekarun baya tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011
Allah kaɗai ya san adadin mutanen da shugaba Buhari ya ɗaga wa hannu suka kai labari.”
(Giwa, 2023).
A cikin wannan misalin, an nuna yadda
‘yan siyasa suka riƙa danganta kansu da martabar shugabannin siyasa, domin samun
karɓuwa a wurin al’umma tun daga shekarar 2003 lokacin da Buhari ya fara fitowa
takarar shugabancin Nijeriya zuwa saukarsa a 2023. Allah ne kaɗai ya san adadin
mutanen da suka ci zaɓe da alfarmarsa, domin tun ma kafin shi ya ci nasa zaɓen,
wato daga 2003 zuwa 2011, mutanen da ya ɗaga masu hannu ko ya yi umarni da a zaɓe
su kuma aka zaɓe a jam’iyyun APP da ANPP da CPC kuma suka yi nasara Allah ne kaɗai
ya san adadinsu. Ba ma shi Buharin kansa ba, tsintsar farin jininsa ya sa a shekarar
2015 kaso mafi tsoka na waɗanda suka fito takara a jam’iyyarsa ta APC sun lashe
zaɓe ba tare wata wahala ba, sai don albarkacin sun fito a jam’iyyar Buhari.
Inda wannan martaba tasa ta fito fili
shi ne, inda shugabannin jam’iyyar APC suka riƙa gargaɗin ‘ya’yan jam’iyyar lokacin
da zaɓen shekarar 2023 ya gabato, wato lokacin da wa’adin mulkin Buhari ya zo ƙarshe.
A lokacin sun riƙa faɗa wa ‘yan jam’iyyar tasu cewa dole fa kowa ya shiga taitayinsa,
ya koma mazaɓarsa ya nemi jama’a domin wannan karon Buhari ba ya cikin jerin ‘yan
takara. Dubi wannan misalin da yake ƙasa:
“John Udoedeghe ya ce zuwa babban zaben 2023, lokacin
da mutane za su shige inuwar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya wuce. A 2023 ne shugaba
Buhari zai kammala wa’adinsa na shekaru takwas. Ana tunanin cewa APC ta na samun
damar lashe zaɓuɓɓuka a matakai da dama saboda sunansa. Sanatan na jihar Edo ya
gargadi magoya bayan jam’iyyar da cewa, a zaben 2023, shugaba Muhammadu Buhari ba
zai fito a cikin masu takara ba.”
(Malumfashi, 2023).
A wannan misalin
an nuna cewa, duk masu shantakewa su fake da sunan Buhari su lashe zaɓe yanzu dai
lokaci ya wuce, don haka kowa ya koma mazaɓarsa ya san na yi. Kamar yadda aka gani
ciki misalin, jam’iyyar APC tana lashe zaɓuɓɓuka a matakai da dama ne saboda sunan
Buhari, kuma ga shi ya kammala wa’adinsa ba zai sake yin wani takara ba.
Idan aka dubi waɗannan
misalai da aka kawo za a fahimci cewa, amfani da matsayi ko martaba na shugabannin
addini ko na siyasa abu ne wanda za a iya cewa ya samo asali tun daga lokacin da
aka fara siyasar jam’iyyu a ƙasar Hausa, kuma irin wannan salon kaska
raɓi mai jini ya ci gaba da tafiya har zuwa wannan zamanin siyasar da muke ciki
wato jamhuri huɗu, inda ake amfani da daraja ko matsayi ko kuma sunan wasu mutane
da ma na wasu ‘yan siyasar domin samun cim ma nasara a siyasance.
4.8 Matsayin Mata A Cikin Siyasar Jam’iyyu
A ƙasar Hausa mata suna
da matsayi na musamman wanda addini da al’ada suka ba su. Mafi akasarin mata a ƙasar
Hausa a ƙarƙashin iyaye ko mazajensu suke rayuwa. Duk wata ɗawainiya tasu takan
fara ne daga kan iyaye, bayan sun yi aure kuma sai nauyinsu ya koma kan mazajensu.
Kasancewar mafi yawan al’ummar ƙasar Hausa Musulmi ne, waɗanda kuma suke da al’adu
da ɗabi’u waɗanda ba su yi takin saƙa da addininsu ba, musamman bayan jihadin Shehu
Usmanu Ɗanfodiyo, wannan ya sa ake ganin akwai wasu abubuwa da suka keɓanta da maza
kaɗai, wasu kuma mata.
Dangane da abin da ya
shafi siyasa musamman ta jam’iyya da ake magana a Arewacin Nijeriya kuwa, tun da
farko mata ba su samu wani matsayi a cikinta ba. Duk al’amuran siyasa a farko maza
ne suke gudanar da ita, kuma babu inda aka sanya mata a cikin kowane sha’ani. Manyan
‘yan Siyasar Jamhuriya ta farko irin su Malam Sa’adu Zungur da Malam Aminu Kano
su ne suka yi ta faɗi-tashin ganin an sanya mata a cikin siyasa, a cewarsu su ma
mata ya kamata a ba su haƙƙinsu. Wannan ya sa suka yi ta ƙalubalantar tsarin masarautun
gargajiya, wanda a cewarsu su ne suka hana mata rawar gaba hantsi a cikin al’amuran
siyasa ta hanyar rufe su a cikin gida ba tare da ba su ‘yancin shiga al’amuran al’umma
a dama da su ba.
Paden, (1973:290-291)
da Yakubu (1999:B.Sh) sun bayyana irin wannan tsari na danniya a cikin ayyukansu,
inda suka nuna cewa Malam Sa’adu Zungur ne ya yi ta gwagwarmaya kan lallai sai an
bai wa mata ‘yancin samun ilimi mai zurfi da kuma damar shiga siyasa.
Abubuwan da aka fi mayar
da hankali a kansu a wuraren shekarun 1950 su ne ƙalubalantar tsarin masarautu kan
batun bai wa mata dama su shiga cikin siyasa da batun iko da kuma faɗa aji. Wannan
shi ne batun da Malam Aminu Kano ya bai wa ƙarfi lokacin da ya tafi tsangayar Ilimi
a London kamar yadda ya bayyana a cikin rubuce-rubucensa.
Wanda ya fi shahara kan
batun matsayin mata a cikin al’umma shi ne Isa Wali wanda ya yi rubutun da ya ta
da ƙura a cikin jaridar Nigerian Citizen.
A cikin rubutunsa ya bayyana yadda Musulunci ya bai wa mata ‘yanci, da kuma irin
gudummawar da mata za su iya bayarwa a cikin al’umma, kamar yadda yake cewa:
“As for public life, there is nothing in
Islam which preventsa woman from following an pursuit she desire. There is no distinct
prohibition agaist her taking part in public leadership – as Aisha the prophet’s
widow and her leading women colleagues (the “Mother of Believers”) har demonstrated
Moslem history, in fact, is full of the account of Moslem women in many countries
who had been glorious rulers, counsellors, jurist and great public servants. They
commanded armies, and, when necessity arose, fought as soldiers as they did in early
Islam – before the end of tenth century.”
Fassarar marubuci:
“A cikin zamantakewa ta yau da kullum babu
inda Musulunci ya hana mata bin tsarin rayuwa daidai da su kuma yadda suke buƙata.
Babu inda aka haramta wa mace shiga harkar shugabancin al’umma kamar yadda Aisha
(Uwar Muminai) matar Manzon Allah ta nuna a cikin jagoranci da ta yi wa mata Tarihin
Musulunci a cike yake da bayanan mata daga ƙasashe daban-daban, waɗanda suka zama
shugabanni da masu faɗa a ji da masu ilimi da kuma manya hadiman al’umma.wasu ma
sun jagoranci rundunoni idan ma buƙata ta taso sukan shiga a fafata da su a matsayin
sojoji kamar dai yadda suka a farkon Musulunci kafin ƙarshen ƙarni na goma.”
(“The True Position of
Women in Islam”, 1958)
A nan ya bayyana irin
yadda addini ya bai wa mata ‘yanci ne na shiga al’amuran yau da kullum waɗanda suka
haɗa har da siyasa da shugabanci wanda masarautun ƙasar Hausa suka hana mata wannan
‘yancin. Shi kuma ya nuna cewa akwai mashahuran mata da aka yi su a tarihi tun daga
kan Uwar Muninai Nana A’isha, da ma wasu mata da aka yi su a cikin tarihi waɗanda
sun bayar da gudummawa a cikin harkar shugabanci wanɗanda kuma tarihi ya ambaci
sunayensu kuma ba zai taɓa mantawa da su ba.
Ba ma shugabanci ko jagorancin
a addini ba, a jamhuriya ta farko hatta shugabancin mata na jam’iyyar NPC a jamhuriya
ta farko tarihi ya nuna cewa namiji aka baiwa, don dai kada a bai wa mace ya zama
kamar an ‘yanta su, sai aka bai wa namiji wanda shi ne zai riƙa tattaunawa da su,
kuma ya kai rahoto ga uwar jam’iyya. Irin wannan bayani ya fito a cikin wata wasiƙa,
inda aka yi ƙorafin cewa hakan da aka yi bai dace ba. Ga abin da wasiƙar take cewa:
“Idan
Edita ya yarda ina son ɗan fili a cikin jaridarka mai ƙaunar dangi don in nuna wani
kuskure da aka yi na nada namiji shugaban matana NPC na Kano. A haƙiƙar gaskiya
wannan ba dacewa ne kawai bai yi ba har ma da shirme na tabbata dukkan matan NPC
ba za su goyi bayan a ce duk cikinsu a rasa shugabar mata mace ba, sai kurum a ce
ga wani mutum shi ne shugabanku kullum zai riƙa kiranku kwamiti.”
(Yakasai, 1960).
Daga jin abin da wannan
wasiƙar ta ƙunsa za a fahimci matsayin mata a siyasar ƙasar Hausa a farko, domin
bayanin ya nuna yadda kwata-kwata ba a bai wa mata wani matsayi a cikin siyasar
jam’iyyu a Arewacin Nijeriya ba. Yawanci ana faɗin cewa ciwon mace na ‘ya mace ne.
Ta yaya za a bai wa namiji jagorancin mata ba tare da tunanin cewa akwai abin da
ba za su iya tattaunawa da namiji ba sai ‘yar’uwarsu mace? Wannan ya nuna cewa ita
kanta muryar matan ba son jin ta ake yi ba, shi ya sa aka sanya wanda ba za su iya
kokawa har a ji amon muryar tasu ba a matsayin shugabansu, wato namiji, domin akwai
wasu abubuwan da idan suka kai kuka wurinsa shi kuma ya ga cewa har da shi abin
zai shafa, ba zai kai koken nasu ba.
Da yawa mata sun yi ta
kokawa kan rashin ilimi da ba a ba su damar yi ba, ko kuma ba su samun yin mai zurfi,
wannan kuwa ba zai rasa nasaba da irin yadda aka hana matan motsin ƙarfi ba. Da
gangan aka yi hakan domin dai duk wanda ya yi ilimi to yakan iya bambance abin da
ya dace da shi da wanda bai dace da shi ba, sannan kuma yakan san haƙƙoƙinsa. Idan
kuwa aka bari matan suka samu ilimi da kansu ma za su nemi a ba su wasu haƙƙoƙi
nasu da aka hana su. Shi kansa ilimi a farko ba a bai wa mata dama ba, akan bar
su kaɗai su san abin da ya kamata su sani na ibada ne, wasu ma ko na gudanar da
ibadar ba su samu gatan yi ba.
Ilimin boko kuwa wanda
a lokacin mazan ma ba sun gama yarda da shi ba ne balle a sanya mace. Wannan ya
sa duk waɗanda suka yi karatu mai zurfi a farko maza ne, kuma da yawansu ‘ya’yan
gidan sarauta ne, kuma ‘yan jam’iyyar NPC. An kuma sani cewa a gidajen sarauta a
ƙasar Hausa mata ba a ba su wata dama ba, an dai bar su a cikin gida ne kawai a
matsayin masu yi wa sarakuna hidima, ba su da wani aiki sai dai a biya buƙata da
su,
su kuma yi sauran hidimomi. Su kuwa talakawa na jam’iyyar NEPU suna
ganin hakan bai dace ba, shi ya sa ma suke ta fafutukar sai an bar mata sun samu
ilimi don su ma a dama da su.
Daga baya,
mata waɗanda suka ɗan fara samun ilimin zamani sun yi ta kiraye-kiraye ga mata ‘yan
uwansu a cikin jaridu cewa, su tashi su nemi ilimi don su ma a dama da su, don sun
fahimci cewa gwamnati a wancan lokacin ba ta son su san halin da ake ciki, shi ya
sa ba ta ba su damar neman ilimi ba. Dubi wannan misalin:
“ saboda haka nake ganin cewa babban abinda
ya kamata mu mata na jihar Arewa mu yi shine mu zage mu ba kanmu ilimi ta kowane
fanni, kada mu tsaya muyi jiran malalciyar gwamnatin NPC mata ba abin da ba za mu
iya ba matukar an koya mana. Babu ko wanda ya danne mu wajen ci gabanmu har matan
jihohin gabas da yamma suka wuce mu irin NPC wadda Sardauna yake ja.”
(“Mata ‘Yan Uwana Mu Nemi Ilimi”, 1961).
Wannan bayanin ya nuna
cewa, gwamnatin NPC ba ta bai wa mata ‘yanci ba ta kowace
fuska. Idan aka yi la’akari da abubuwan da suke cikin wannan misalin za a ga cewa
wasu matan sun fara fahimtar cewa suna da amfani a cikin al’umma. Sun fara fahimtar
cewa in suka samu ilimi za su iya yin wasu abubuwa kamar yadda maza suke yi, ciki
har da shiga harkokin siyasa da shugabanci a dama da su. A cikin misalin kuma in
aka duba za a ga cewa an ɗora alhakin rashin ilimin nasu a kan gazawar gwamnatin
NPC wanda su kansu ‘yan hamayya suke ta fafutukar sai
an bai wa matan dama.
Tarihi ya nuna cewa, hatta
jefa ƙuri’a tsarin sarakunan ƙasar Hausa bai ba wa mata damar yi ba. Maza ne kaɗai
suke jefa ƙuri’a a lokacin zaɓuɓɓukan da aka yi a jamhuriya ta farko, duk kuwa da
irin kiraye-kiraye da su Malam Sa’adu Zungur suka yi ta yi. Ba a samu wannan damar
ba sai a jamhuriya ta biyu a wuraren 1979 lokacin da aka bai wa mata damar jefa
ƙuri’a, kamar yadda Yakubu(1999: B.Sh) ya bayyana:
“A baya masarautu sun hana mata ‘yancinsu
na yin zaɓe da sauran haƙƙoƙi da wasu damammakinsu na rayuwa da wasu al’amuran yau
da kullum. Wannan yana cikin irin fafutukar da Sa’adu Zungur ya yi ta yi domin gina
sabuwar Nijeriya.”
(Yakubu, 1999: B.Sh)
A Jamhuriya ta biyu, Jaridar
Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ranar 9 ga Yuli,
1979 ta buga hoton wasu mata a Sakkwato, a jere bisa layin jefa ƙuri’a a zaɓen da
aka gudanar a wannan shekarar. Wannan ya nuna cewa mata ba su samu ‘yancin yin zaɓe
ba sai a Jamhuriya ta biyu kamar yadda Malam Aminu Kano ya faɗa a cikin wani jawabinsa
bayan zaɓen da aka gudanar a jamhuriya ta biyu. Dubi abin da ya ce:
“ mun fuskanci kamu da tsarewa da duka da
nau’o’in azaba da muka bayar da shawarwari a ƙyale mata su yi zaɓe, sai da aka ce
a tuntuɓi imaninmu a matsayin Musulmi aka zarge mu da’ kauce hanya’. Amma ku duba
yadda duk aka fahimci abubuwa, hakan ba nasarar PRP ba ce?”
(Jega da wasu, 2002:38).
Wannan ci gaba ce aka
samu a ciki tsarin siyasar jam’iyyu, musamman idan aka kwatanta da yadda aka fito
a jamhuriya ta ɗaya. Kafin samun wannan cigaban, Malam Aminu Kano ya ce ‘yan jam’iyyar
NEPU sun fuskanci nau’o’in azaba da suka shafi kamu da ɗauri da duka duk don sun
bayar da shawarar a bar mata su yi zaɓe, har sai da ta kai ga ana ganin ma sun kafirce
wa addini inda aka ce a binciki imaninsu, sai dai a ƙarshe ya nuna cewa an samu
nasara, tun da an bai wa mata ‘yancin yin zaɓen.
A ci gaba da fito da matsayin
mata a cikin siyasar jam’iyyu a cikin tarihi, Malam Aminu Kano a jawabinsa na kafa
jam’iyyar PRP a jamhuriya ta biyu, ya bayyana cewa sun daɗe suna gwagwarmayar samo
wa mata ‘yanci tun a zamanin NEPU, kuma za su ci gaba har sai an kai ga nasara.
Dubi abin da yake cewa:
“A ci gaba da gwagwarmayar da muke game
da mata kuwa, a wannan jam’iyyar za mu ci gaba da wannan ƙoƙari har sai mun ci nasara.
Idan za ku iya tunawa, a shekarun baya mun yi gwagwarmaya domin samo wa mata ‘yanci
don su shiga harkokin ƙasa, wannan gwagwarmaya ta fara haifar da nasara. Ba za mu
gajiya ba har sai mun ci nasara baki ɗaya.”
(Jega da wasu, 2002:18).
A cikin bayanin nasa,
ya nuna cewa gwagwarmayar nema wa mata ‘yanci da jam’iyyarsa take fafutuka ya haɗa
har da ba su dama su shiga cikin harkokin ƙasa, wanda ya shafi mulki da shugabanci
da aikin gwamnati, inda ya nuna cewa, wannan fafutukar tasu ta fara samun nasara.
A ƙarshe an bai wa matan dama ciki har da na jefa ƙuri’a da shiga harkokin siyasa
kamar yadda aka bayyana a sama.
Daga cikin mata da suka
shahara a fagen siyasa tun daga jamhuriya ta ɗaya har zuwa jamhuriya ta biyu akwai
Hajiya Gambo Sawaba. Tana cikin ajin farko a ɓangaren mata da suka shiga siyasar
jam’iyya. Ta taka rawar gani, musamman wajen fafutukar ƙwato haƙƙin mata ta fuskar
damar samun ilimi da jefa ƙuri’a da kuma shiga zaɓuɓɓuka. Duk da cewa ba ta samu
damar yin ilimin boko ko wani ilimi mai zurfi ba, amma dai gudummawar da ta bayar
a fagen siyasar jam’iyyu a ƙasar Hausa abu ne da tarihi ba zai manta da ita ba.
Ita ce mace ta farko da fara zama shugabar mata ta ƙasa ta jamiyyar NEPU.
An zaɓi Gambo sawaba da
wasu sauran mata 18 na jam’iyyar NEPU a kan muƙamai daban-daban da suka shafi mata
a shekarar 1958[8]. Wannan ya nuna
cewa jam’iyyar NEPU ce ta fara bai wa mata damar shiga harkokin siyasa a aikace
kamar yadda jam’iyyar take ta kiraye-kiraye.
Wani cigaba da aka samu
kan abin da ya shafi shigar mata cikin al’amuran siyasar jam’iyyu shi ne, yadda
matan suka riƙa kakkafa ƙungiyoyi na siyasa, kuma suka ci gaba da fafutukar neman
a ba su dama musamman a jamhuriya ta biyu, inda suka samu damar yin zaɓe da shiga
al’amuran da suka shafi jam’iyyun siyasa. Dubi jawabin sakatariyar ƙungiyar matan
PRP ta ƙasa inda ta ce:
“Ba ƙaramar nasara ba ce don an kafa wannan
ƙungiya ta matan Ceton Al’umma, wanda a cikinta muna da damar tatttauna abubuwan
da ya kamata a cikin jam’iyyar Shekaru da dama da suka wuce, ayyukan ci gaban ƙasa
da gudanarwa duk yana danƙe a hannun maza, tun ma ba a nan jihohin Arewa ba. Yau
a ƙarƙashin Jam’iyyar Ceton Al’umma, mun sami dama kuma mun ɗaura niyyar kawar da
wannan tsari ”
(“Sakatariyar Jam’iyyar
PRP”, 1979).
Ba zaɓe ne kaɗai mata
suka samu damar yi a jamhuriya ta uku ba, har da shiga harkokin siyasa a dama su.
Kamar yadda wannan misalin da yake sama ya nuna, mata sun kakkafa ƙungiyoyi na siyasa
ƙarƙashin jam’iyyu, inda matan jam’iyyar PRP ma suka kafa tasu. Wannan ƙungiyar
kamar yadda sakatariyarta ta bayyana za ta ba su damar tattauna al’amuran siyasa
da suka shafi jam’iyyarsu ta PRP. Sun nuna cewa, dukkan wani abu da ake gudanarwa
maza ne suke riƙe da shi musamman a Jihohin Arewa. Sun lashi takobin kawar da wannan
tsarin na danniyar maza kamar yadda suka ce, tun da sun samu damar shiga cikin siyasar
su ma a dama da su.
Wannan ya nuna cewa, mata
suna da ƙishirwar son shiga cikin siyasa da gudanar da al’amuran jama’a tun daga
jamhuriya ta farko inda fafutukar ta soma, wanda sai a yanzu ne suka samu cikakkiyar
dama. Sakatariyar ta ci gaba da nuna cewa, a cikin tarihin ginuwar siyasar a ƙasar
Hausa, akwai mashahuran mata da suka ba da gagarumar gudummawa. Dubi abin da ta
ce:
A cikin tarihin Nijeriya, ba za mu manta
da muhimman abubuwan da manyan mata kamar Sarauniya Amina ta Zariya wadda ta yaƙi
ƙasashe, kamar Nana Asma’u Ɗanfodiyo wadda ta yi iyakacin ƙoƙari cikin al’amuran
siyasa. Waɗannan mata sun yi iya ƙoƙari wajen ayyukan ci gaban ƙasa, kuma sun kafa
mana tushe don matan da za su taso, amma saboda irin mulki na son danniyar hana
mata ci gaba, mazanmu suka kashe ƙoƙarin da mata suke yi. Yau a cikin ƙungiyar nan
ta matan Jam’iyyar Ceton Al’umma, mun dawo da mu tabbatar da wannan cin nasara.”
(“Sakatariyar Jam’iyyar
PRP”, 1979).
A nan ta nuna cewa mashahuran
mata irin su Sarauniyar Zazzau Amina, da Nana Asma’u ‘yar Shaihu Usmanu Ɗanfodiyo
sun ba da gagarumar gudummawa wajen ginuwar siyasa da sha’anin mulki a ƙasar Hausa.
Sun yi ƙoƙari wajen ayyukan ci gaban ƙasa kamar yaɗa ilimi da sauran muhimman al’amura,
wanda ya zama madubi ga mata masu tasowa. Duk da haka maza sun hana mata bayar da
irin tasu gudummawar, saboda son danne haƙƙi wanda ya hana a ga ƙoƙarinsu. Sun bayyana
cewa, a cikin ƙoƙarin wannan ƙungiya tasu, za su tabbatar sun farfaɗo da irin wannan
tsari na magabata, kuma su tabbatar an yi nasara.
A siyasar jam’iyyu kusan tun da aka bai wa mata
damar shiga da jefa ƙuri’a, duk abin da ya shafe su a cikin siyasar su matan ne
suke gudanarwa. Alal misali, akan naɗa mata su shugabanci mata, lokacin yaƙin neman
zaɓe ko tallata jam’iyya, duba da yanayin tsarin ƙasar Hausa, matan su ne suke shiga
gida-gida wajen mata domin tallar jam’iyya da kuma neman ƙuri’arsu. Wannan ya bayyana
a ciki littafin Tura Ta Kai Bango kamar
haka:
“Haka
kuma a sami mace ko kuma matan da za su jawo mata cikin jam’iyyar.”
(Katsina, 1983: 18).
Mata ne akan sanya musamman
lokacin tallata jam’iyyu ko ‘yan takara su riƙa bi gida-gida don jawo ra’ayin mata
a cikin siyasa, kamar yadda aka gani a cikin wannan misalin da yake sama, inda ‘yan
jam’iyyar Sauyi suke shawarar sanya matan da za su bi mata har gidajensu domin jawo
ra’ayinsu ga jam’iyyarsu. Irin wannan ya ci gaba har zuwa yau, inda akan riƙa amfani
da mata ‘yan jam’iyya domin karkato hankalin mata zuwa ga jam’iyya ko ɗan takarar
da ake buƙatar tallata masu.
Irin fafutukar da mata suka riƙa yi wajen ganin
an ba su damar shiga cikin siyasa domin su ma a dama da su ya ci gaba da bayyana
a cikin rubutaccen zube na Hausa. A cikin littafin Mace Mutum an fito da irin wannan fasalin, inda aka riƙa nuna
cewa an hana mata damar shiga siyasa, don haka ya zama dole su tashi tsaye domin
kada a ci gaba da barin su a baya, kasancewar su su ma suna da haƙƙi. Dubi abin
da marubuciyar take cewa:
Aikin da zan ƙara shi ne zage damtse don
nemo wa mata gurbinsu a siyasa Ba shugaban ƙasa ko matar shugaba ko na’ibi muke
nema ko shugabar majalisa ba. Don ba albashi muke nema ko suna ba, muna neman kujerun
duk abin da mata suka fi naƙasa ne a kansa. Kujerar kwamishina ko ministan ilimi
dole mu nema ba za mu guji gwamnati ba don mu ma mutane ne.
(Majid, 2006: 415)
A nan ɗaya daga cikin
‘yan ƙungiyar ‘Ya’yan Godiya ne, wato Habiba, wadda ta samu ilimi fannin siyasa
take bayanin yadda za su gudanar da fafutukar nema wa mata ‘yancin shiga siyasa
domin su ma a dama da su. Ta nuna cewa za ta yin amfani da ƙwarewarta wajen nema
wa mata gurbi a cikin siyasa, domin a tafi tare da su. A cikin misalin da yake sama,
ta nuna cewa, ba burinsu ne su shiga siyasa domin neman kuɗi ko suna ba, sai dai
domin share wa mata hawaye kan matsalolin da suka fi addabar su, kamar rashin ilimi.
Wannan ne ya sa ta ce ya zama wajibi su miƙe su nemi kujerar kwamishina ko ma na
ministan ilimi. Wannan ya nuna cewa, a baya ba a bai wa mata damar riƙe manyan muƙaman
gwamnati ba, hakan ya sa suka tashi domin fafutukar neman sanya su cikin gwamnati
domin su ma suna da irin gudummawar da za su bayar.
Tarihi ya nuna cewa, bayan
bai wa mata damar jefa ƙuri’a da kuma damawa da su a cikin al’amuran siyasa a jamhuriya
ta biyu, bincike ya nuna tun daga wancan lokaci zuwa jamhuriya ta huɗu, mata su
ne suka fi jefa ƙuri’a da kashi sittin cikin ɗari, kamar yadda jaridar Leadership Hausa ta nuna:
“Kaso 60 na waɗanda suke kada ƙuri’a mata
ne don haka yan da kyau mata su gane cewar juya akalar zaɓe na hannun mata. Saboda
dayawan masu kada ƙuri’ar matan ne, amma da zarar an ci zaɓe da wuya ka ji wani
abu da ya shafi rayuwar mata a matsayin ƙudurin da za a gabatar a majalisun ƙasar
nan.”
(Usman, 2023).
A nan an nuna cewa mata
su ne suka ɗauki kaso mafi tsoka na masu kada ƙuri’a a yau, domin sun ɗauki kaso
sittin ciki ɗari na masu zaɓe. Wannan ya nuna cewa, mata suna da rawar da za su
taka a cikin siyasa. Haka kuma duk da yawan kason da suka na masu zaɓe, matan ba
su cika fitowa takarar siyasa ba idan aka kwatanta su da maza. In ma sun fito ba
su cika yin nasara ba. Wannan ba zai rasa nasaba da koyarwar addinin Musulunci ba,
wanda shi ne addini mafi rinjaye ga al’ummar ƙasar Hausa.
A yau matsayin mata a
cikin siyasa a ƙasar Hausa ya wuce su tsaya ga jefa ƙuri’a ko ƙungiyoyin mata kaɗai,
inda har ya kai mata sukan shiga takara don a zaɓe su, kuma sukan yi takara da maza
a wasu matakai, ko kuma a ba su wasu muƙamai a siyasance waɗanda a da maza ake bai
wa su. Alal misali, an samu mata da dama da suka zama kwamishinoni a wasu yankunan
Arewacin Nijeriya, inda suka riƙe ire-iren waɗannan muƙaman a ma’aikatu da dama.
An hasko irin wannan bayani a cikin littafin Mace Mutum kamar haka:
“A taƙaice na yanke shawarar yin takara
tare da na’iba mace wadda za ku ba ni daga cikin ku. Sa’annan akwai kujerar ministoci
guda huɗu da na ware domin bai wa mata ganin cewa a wannan sashi ne suka fi samun
tawaya. Waɗannan kujeru su ne, ministar mata, ministar kiwon lafiya, ministar ilimi
da ministar al’adu in kun yarda da wannan tsari sai mu yi a rubuce, mu haɗa ƙarfi
mu nemi ƙuri’a, mu yi yaƙin neman zaɓe tare.”
(Majid, 2006: 505).
A cikin wannan misalin
da yake sama, shugaban ƙasa ne yake tattaunawa da ‘yan ƙungiyar ‘Ya’yan Godiya ƙarƙashin
jagorancin Habiba wadda ta kasance ‘yar siyasa a cikinsu, inda ya bayyana masu cewa
ya yanke shawarar ɗaukar wadda za ta zama mataimakiyarsa a takarar shugaban ƙasa
da zai sake tsayawa daga cikin mata ‘ya’yan wannan ƙungiyar. Baya ga kujerar mataimakiyar
shugaban ƙasa kuma zai ba su muƙamin ministoci guda huɗu waɗanda suka haɗa da na
ilimi da lafiya da al’adu da kuma harkokin mata, waɗanda a cewarsa mata sun fi buƙatarsu
ne domin suna da tawaya a waɗannan ɓangarorin. Kamar yadda misalin ya nuna, duk
da cewa an ba su gurbin mataimakiyar shugaban ƙasa da kuma ministoci, sai kuma ana
ka nuna wa matan cewa za su fito a yi fafutukar neman ƙuri’a tare da su.
A baya bayan nan, an samu
mataimakiyar gwamna a jihar Kaduna wadda suka tsaya takara kuma suka yi nasara.
Haka kuma a Arewacin Nijeriya (Jihar Adamawa) mace ta yi takarar gwamnar jihar a
jam’iyyar APC, kuma an kai-ruwa-rana da ita duk da ba ta yi nasara ba. An naɗa mata
ministoci da dama daga ƙasar Hausa, waɗanda bayan samun ilimi mai zurfi suka shiga
siyasa don a dama da su kamar yadda aka yi ta fafutuka a baya.
4.9 Takura Wa Abokan Hamayya Hamayya a cikin siyasa
tamkar gishiri ne a cikin miya, wanda muhimmancinsa akan ce in babu shi babu miya,
wato miyar ba za ta yi daɗi ba. Siyasa musamman ta jam’iyya ba ta yiwuwa sai da
hamayya tsakanin jam’iyyu. Kowace jam’iyya tana
ƙoƙarin ganin ta yi nasara a kan abokiyar hamayyarta, idan kuma ta samu nasarar
ɗarewa kan madafun iko to za ta yi duk yadda za ta yi domin ganin ta ɗore a kan
mulki, kuma jam’iyyar hamayya ba ta samu dama ba.
Kamar yadda tarihi ya
nuna, tun daga farkon kafa siyasar jam’iyyu a ƙasar Hausa, an samu jam’iyyun da
aka kafa waɗanda suka yi hamayya da juna, wanda a ƙarshe wadda ta yi nasara wato
NPC ta ɗare mulki, NEPU kuwa ta zama jam’iyyar hamayya wadda a kullum take ganin
masu mulki ba su iya ba, ko kuma suna yin wasu abubuwa ba bisa tsari ko ƙa’ida ba.
Irin wannan kuwa yakan zama al’ada ce ga kowane abokin hamayya domin ya nuna fagen gazawar
abokin hamayyarsa. Jam’iyyun biyu sun ci gaba da nuna
tsananin hamayya ga juna, inda ‘yan hamayya
kan riƙa sukar gwamnati da masu riƙe da madafun iko ta kowace fuska. Ita kuwa gwamnati
a nata ɓangaren sai ta riƙa amfani da ƙarfin mulki wajen yaƙar ‘yan hamayya
ta hanyar ɗauri da tara da dai sauransu.
‘Yan NPC sun sha yin iƙirarin
cewa sarki da alƙali duk nasu ne, don haka duk wanda ya faɗa masu magana marar daɗi
za a miƙa wa alƙali ya yi masa hukunci, wanda ba su wuce duka ko ɗauri ko kuma tara
ba. Wannan kuwa ya bayyana a cikin wasu rahotanni da suka fito a cikin jaridun Arewacin
Nijeriya waɗanda suka riƙa bayyana yadda shari’o’in kotunan lardi suke gudana, musamman
tsakanin mabiya jam’iyyar hamayya da ta masu masu mulki.
A cikin wasu jaridun tun daga kanun labarai za a nuna irin mutanen da aka yi wa
shari’a ko aka yanke wa hukunci. Dubi wannan misalin:
“Umaru Aska wanda ya yi jifa a Ofishin Alƙali
ya samu ɗaurin wata ashirin da ɗaya. Wanda ya haddasa abin kuma har ya tuɓe zai
bugi dogarin alƙali ya samu ɗaurin wata goma sha takwas.
Malam Abdu Tela kuma shugaban wannan taro
ya sami wata takwas a gidan yari. Bayan waɗannan kuma an sami mutane takwas masu
ɗaurin wata tara tara. Mutane ashirin da ɗaya kuma duk an ɗaure su wata bakwai bakwai.”
(“Shari’ar ‘yan NEPU a
Katsina”, 1957).
A wannan rahoton na jaridar
Gaskiya Ta Fi Kwabo, tun daga kanun labarin
wato “Shari’ar ‘yan NEPU a Katsina” za a fahimci inda aka dosa, wato ba laifin ko
masu laifin ake kallo ba, jam’iyyar siyasar da suke ra’ayi ake duba. In kuwa haka
ne ashe da wuya komai gaskiya ɗan hamayya a iya yi masa adalci.
Haka kuma, idan aka dubi yadda ake yanke masu watanni masu yawa a kan laifin da
bai taka kara ba balle ya karya, za a fahimci irin halin da ‘yan hamayya
suka shiga a wannan lokaci.
Hujjoji na tarihi sun
nuna cewa, an samu lokacin da hatta alamar jam’iyyar hamayya ta NEPU idan aka ga wani
da ita to kashinsa ya bushe, domin tana iya ja masa ɗauri a gidan kaso. A cikin
wata wasiƙa da babban Sakarataren NEPU Malam B. M. Dzukogi ya aike wa Razdan na
Katsina, ya yi ƙorafi tare da nuna ɓacin rai kan yadda ake takura wa ‘yan NEPU a
Katsina, inda ya nuna cewa an ɗaure ‘yan jam’iyyar da dama don kawai sun sanya alamar
NEPU a gidajensu. Dubi abin da aka tsakuro daga cikin wasiƙar:
“I am directed to protest to you against
the recent order of the Katsina N. A. banning the display of this Party’s symbol
in Katsina Division. This party Understands that already many of it’s members and
supporters in Katsina have been convicted only for posting of our symbols in front
of their houses. I am to point that our part’s symbol, a five pointed sta, has already
been registered officially with the Federal Electoral Commission and we take a serious
view of any attempt by which ever quarter to refuse the displaying of this symbol
there is no reason why you should back the Katsina Native Authority to make an order
banning the display of opposition party’s symbols during an election of great importance
to the whole nation.”
Fassara:
“An umarce ni da in rubuta wannan takarda
domin nuna ɓacin rai kan umarnin da hukumar En’e ta bayar na hana amfani da tutar
jam’iyyarmu a yankin Katsina. Jam’iyyarmu ta fahimci cewa, akwai ‘ya’yanta da magoya
bayanta da dama da aka ɗaure saboda kawai sun sanya tutar jam’iyyarmu a ƙofar gidajensu.
Ina ƙara jaddada cewa, jam’iyyarmu mai alamar tauraro an riga an yi mata rajista
da hukumar zaɓe ta ƙasa, don haka babu wani dalili da zai hana mu bayyana alamominta
babu wani dalilin da zai sa ka goyi bayan Hukumar En’e ta Katsina domin sanya dokar
hana bayyana alamar jam’iyyar hamayya a irin wannan lokaci
na zaɓen da yake da matuƙar muhimmanci ga ƙasa baki ɗaya.”
(Abba, 2000:95-96).
Idan aka duba nan za a
ga cewa, ‘ya’yan jam’iyyar NEPU a Katsina sun riƙa kafa tutocin jam’iyyarsu a ƙofar
gidansu domin nuna cewa su magoya bayan jam’iyyar ne, amma sai aka riƙa amfani da
ƙarfin iko wajen hana su kafawa ta hanyar tsorata su da kamu da ɗauri a gidan kurkuku,
domin dai a hana jam’iyyar tasu yin tasiri.
Kasancewar gwamnati ita
take da iko a kan kotun alƙali da na sarki, wannan ya sa da zaran ‘yan hamayya
sun yi laifi ko yaya sai a yanke masu tara mai girma ko kuma ɗauri a gidan kurkuku,
wani lokacin ma akan haɗa masu da duka na nau’o’in azaba iri-iri har ma da kisa.
Irin wannan ya fito a cikin wani jawabi da Malam Aminu Kano ya gabatar, inda yake
cewa:
“Mun fara a matsayin samari matasa tsayayyu
wajen yaƙi da zaluncin sarakunan Arewa sai muka tsaya wajen yaƙi da su, an ɗaure
mu an doke mu an hana m,u abubuwa da dama yana da kyau mu san cewa duk wata hanyar
tsanani da azaba da kashe waɗansu daga cikinmu ba zai wadatar ba, da yawa mutanenmu
sun rasu irin su Aminu Sudawa da Ɗalha Ɗanƙasa da sauransu, ba za mu taɓa tsorata
ba ”
(Jega da wasu, 2002: 59-60)
A nan idan aka duba za
a ga cewa tun farkon fara siyasar jam’iyyu ba a bar ‘yan hamayya sun sha ruwa ba, domin
kuwa daga wannan misalin da yake sama za a fahimci irin halin matsi da ƙuncin da
aka jefa ‘yan hamayyar wancan lokacin wanda hakan bai sa sun karaya
sun ja da baya ba. An nuna cewa an riƙa dukan ‘yan hamayya da gana masu azaba da
ɗauri, inda har abin kan kai ga rasa rai. Duk wannan ‘yan hamayya sukan
ɗora laifin a kan masu mulki ne, domin su ne suke da wuƙa da nama, kuma ba su son
suka da ‘yan hamayya suke yi masu.
A wasu wuraren kuma akan
samu inda a kan ɗai laifin da bai taka kara ya karya ba sai a kama abokan hamayya
a ci su tara. Don kawai wani abu ya haɗa su da ɗan jam’iyya mai mulki, sai a bai
wa abokin rigimar tasa ɗan jam’iyyar hamayya rashin gaskiya har a ci tararsa, kamar
yadda ya zo a wannan misalin da yake ƙasa:
“Mun
samu labarin wai wani ɗan NEPU mai suna Ya’u mutumin Sumaila ta Kano, an yi masa
tara fam 20 saboda ƙin halartar kotu. Daman dai an samu Ya’u Sumaila ne da laifin
cin mutuncin wani ɗan NPC mai suna Ɗanladi na Alhaji Inuwa. Har wa yau kuma an sami
Ya’u da laifin yin wasu abubuwa da za su haddasa fitina.”
(“An Yi Wa Ɗan NEPU Tarar
€20”, 1960).
A nan kamar yadda jaridar
ta ruwaito, an yanke wa ɗan NEPU tarar fam 20 ne don ya ci mutunci wani ɗan NPC,
kuma an kira shi kotu ya ƙi zuwa, sannan aka ce wai kotu ta same shi da laifin ƙoƙarin
haddasa fitina. Ire-iren waɗannan abubuwan na tarihi da suka shafi takurawa da ƙuntata
wa ‘yan hamayya sun yi ta bayyana a cikin rubutaccen zube
tun daga farkon siyasar jam’iyyu. Ba ma wai sai an taɓa ɗan jam’iyya mai mulki ne
kaɗai irin waɗannan abubuwa na ƙuntatawa kan taso ba, akan iya amfani da kowane
irin dalili ko ma babu gaira babu dalili matuƙar dai mutum ya kasance ɗan hamayyar
gwamnati ne. Alal misali, a wata wasiƙa da aka aika wa jaridar Sodangi an nuna cewa ko maras lafiya ne ɗan
jam’iyyar hamayya ba a ba shi kulawa a asibiti don kasancewarsa
ɗan hamayya kamar yadda wannan misalin ya nuna:
“ ana nuna bambancin siyasa a asibiti, wato
dai idan ɗan NEPU ya ji rauni ko ya kai mai ciwo sai Alhaji Rabi’u ya ƙi karɓa don
shi mai shawara da kansa an yi masa haka.”
(“Majalisar Birnin Kano”,
1960).
A cikin wannan misalin
an nuna cewa, asibitin gwamnati ne, su kuwa ma’aikatan gwamnati ce ta ɗauke su,
kuma da umarninta suke aiki. Wannan ya sa ko dai ya kasance an bai wa ma’aikacin
lafiyar umarnin cewa kada ya duba ‘yan hamayya, ko kuma shi ma da kansa
ɗan hamayyar ne wannan ya sa ba zai duba su ba domin
zafin hamayya. Marubucin wasiƙar ya ce idan ɗan NEPU ya samu rauni ko ba shi da
lafiya ba a duba shi, domin shi hakan ya faru da shi a karan kansa. Idan aka duba,
za a ga cewa, dangane da halin da ‘yan hamayya suka shiga, musamman
a jamhuriya ta farko hali ne na takura, ko dai ka bi jam’iyya mai mulki, ko kuma
ko yaya wata matsala ta haɗa ka da masu riƙe da madafun iko kashin ka ya bushe.
Ta wata fuskar kuma ‘yan
jam’iyya mai mulki ta NPC suna ganin cewa, duk kumfar bakin da NEPU take yi cewa
ana takura wa magoya bayanta da azabtar da su, su ne suke ja wa kansu, don haka
ma suka ce ai ba ɗaure su ake yi ba, su ne suke ɗaure kansu, kamar yadda aka samu
daga jaridar Sodangi cewa:
“ sau da yawa nakan ji ana faɗi a rediyo
ko kuma nakan karanta a jaridu cewa mutanen NEPU suna ta yin surutai barkatai wai
hukuma na yawan ɗaure su kuma tana yawan wulakanta su. Bisa gaskiya mutanen NEPU
su ne suke ɗaure kansu suke kuma wulaƙanta kansu da kansu. Gama a Najeriya ba jam’iyyar
da ke keta doka kamar jam’iyyar NEPU.
(“NEPU Ke Daure Kan Ta”,
1960).
A wannan misalin ‘yan
NPC suna ganin cewa babu wata jam’iyyar da take keta doka kamar NEPU, duk kuwa wanda
ya keta doka to ya kamata doka ta yi aiki a kansa. Akwai tsare tsaren gwamnati da
dama da NEPU ba ta amince da su ba. Alal misali, biyan haraji da noman gandu da
sauran wasu nauye-nauye da jam’iyyar NPC take da alhakinsu, abubuwa ne da jam’iyyar
hamayya take yaƙi da su ƙwarai. A ganin su bai
kamata talaka ya biya haraji a ƙasarsa ba, kuma in har za a nome wa sarki gonarsa,
to ya kamata ya ɗauki ‘yan ƙwadago ne su yi masa ya biya su ba wai a sa mutum ya
yi na dole kuma babu ko sisi da za a biya shi ba, hasali ma, sai dai bayan talakawa
sun gama nome gandun sarki su je fada su yi gaisuwa su yi godiya su koma gidajensu.
Duk waɗannan NEPU tana yaƙi da su. Wannan ya sa ake ganin cewa sun raina hukuma,
don haka idan suka shiga hannu ba za su ji daɗi ba.
Tarihi ya nuna cewa, lokacin
da Turawan mulkin mallaka suka shigo ƙasar Hausa sun bai wa sarakunan ƙasar ƙarfi
sosai ta hanyar haɗa kai da su wajen danne talaka, kamar yadda Malam Aminu Kano
ya bayyana a cikin jawabinsa:
“ a lokacin da Turawan mulki suka zo sun
ɗaga darajar sarakuna a kan ta kowa suka yi amfani da su wajen rashin gaskiya ”
(Jega da wasu, 2002: 59-60)
Ke nan, Turawa sun yi
amfani da sarakuna wajen cimma burinsu a ƙasar Hausa, ta hanyar amfani da ƙarfin
faɗa-aji da sarkuna suke da shi da kuma ƙarfin iko suka shimfiɗa ikonsu yadda suka
so. Kasancewar jam’iyyar NPC ita ce take mulki, su kuma Turawa su ne a sama wajen
bayar da umarni, sannan kuma duk sarakuna suna karɓar umarni ne daga Turawa, sannan
kuma sarakunan su ne ‘ya’yan jam’iyyar ta NPC, wannan ya sa suke da ƙarfin iko a
gargajiyance da kuma a siyasance. Da wannan dalilin ne ya sa sarakuna ba su bar
‘yan hamayya sun shaƙata ba, musamman idan aka samu
shari’a ta haɗa su da mai goyon bayan jam’iyya mai mulki. A cikin wanna misalin
da yake biye za a ga irin wannan yanayin ya fito a cikinsa. Ga misalin:
“Kuma sai ga shi sarakunan NPC sun fito
sosai suna nuna ƙiyayyar su ga jam’iyyar hamayya sun dage suna yi wa NPC aiki sosai
ta wajen daure abokan hamayya da danne su wajen sharia da nuna bambanchi da laftawa
talaka harajin da ya fi karfinsa da dai dukkan abubuwan da bai kyautu wanda yake
sarki ba ya yi.”
(Kano, 1961).
A shekarar 1961, jaridar
Daily Comet ta buga wannan wasiƙar da
aka tsakuro a sama, inda a ciki aka bayyana cewa sarakuna sun nuna ƙarara cewa jam’iyyar
NPC mai mulki suke yi, babu ruwansu da jam’iyyar NEPU. A ganin abokan hamayya
ai sarakunan ma aiki suke wa jam’iyya mai mulki ta hanyar ɗaure abokan hamayya
da danne masu haƙoƙƙinsu a wajen shari’a ta hanyar nuna bambanci tsakanin ɗan jam’iyyarsu
da wanda ba ɗan jam’iyyarsu ba, maimakon su yi shari’a bisa adalci ba tare da nuna
sani ko sabo ba.
Har ila yau, a cikin wasiƙar
tasa ya nuna cewa, sarakunan suna sanya wa talaka haraji mai yawa da ya fi ƙarfinsa,
wanda yake ganin hakan bai dace ba. A cewarsa a matsayinsu na sarakuna iyayen al’umma,
ya kamata su kasance suna tare da kowane ɓangare ba tare da nuna bambanci ba. Wannan
bambancin da suke nunawa ne ma ya sa ya kira su da sarakunan NPC, maimakon sarakunan
gargajiya.
A wata tattaunawa da aka
yi da fitacciyar ‘yar siyasa Hajiya Maryam Inuwa wadda aka fi sani da Asabe Reza
ta bayyana yadda aka riƙa gallaza masu don kawai suna goyon bayan jam’iyyar hamayya.
Ta bayyana yadda aka yi ta ɗaure ta a gidan yari don kasancewarta ‘yar Jam’iyyar
NEPU, da irin yadda aka riƙa azabtar da su. Dubi abin da jaridar Aminya ta ruwaito:
“Wallahi duk kurkukun da ke kewaye da garuruwan
nan namu babu wanda ba a taɓa kai ni ba. Daga caji ofis a kai ka kurkuku, daga kurkuku
a kai ka basikel wanda ake kwana a tsaye Ba mu da wata dama a lokacin NEPU sai shan
duka da ɗaukar kashi a ka ”
(Ayuba, 2010).
A cikin bayaninta kan
irin ƙalubalen da ta fuskanta kasancewarta ‘yar jam‘iyyar hamayya ta NEPU, ta bayyana cewa
duk kurkukun da ke kewaye da su babu wanda ba a kulle ta a ciki ba. wani lokaci
ba a ma batun zuwa kotu, daga an kama ɗan hamayya an kai shi ofishin ‘yansanda
sai a wuce kurkuku a ɗaure. A kurkukun ma har akan kai su ɗakin da ake cewa ‘basikel’,
wanda ba zama balle kwanciya, a tsaye mutum zai kasance duk daɗewar da zai yi a
cikin wannan ɗakin. Duk wannan azabar don sun kasance ‘yan hamayya
ne.
Baya ga ɗauri a gidan
kurkuku, akan lakaɗa wa ɗan hamayya duka a wancan lokacin
kan abin da bai kai ya kawo ba. Kamar yadda wannan ‘yar siyasa ta faɗa kamar haka:
“Akwai wani mutum maɗinki da aka samu labarin
ɗinkin rigunan da ya yi wa Malam Aminu Kano, sai da aka je har zauren gidansa aka
kama shi, aka yi ta duka kamar za a kashe tun daga garin Ringim za a ɗauro mutum,
a yi masa ƙuƙumi, sannan a kawo shi gidan kurkukun Kano a ɗaure. Za ki ga mutum
bai aikata wani laifi ba, don kawai ya faɗi kalmar sawaba, sai a ɗaure shi a jikin
doki, ɗan doka da ke kan dokin ya riƙa jan sa da igiya mun sha tafiyar ƙafa ga duka.
A yanzu haka jikina duk yanka ne na wajen damben rigima da gwagwarmaya. Kai har
yanzu akwai tabo a kaina ”
(Ayuba, 2010).
Idan aka dubi wannan misalin
za a ga cewa, a cikin tsawon tarihin siyasar jam’iyyu, ‘yan hamayya
sun sha tsanani a wajen masu mulki musamman a jamhuriya ta farko, wanda ya shafi
kowane irin nau’i na azaba da ɗauri da duka kamar yadda Asabe Reza ta ambata cikin
bayananta. A wancan lokacin babu wata alaƙa da za ta haɗa ka da wani abu da ya shafi
NEPU in dai kana so ka zauna lafiya. Ko da sana’a kake yi ba za ka yi wa ɗan NEPU
ba, sai dai in ra’ayinta kake yi. Kamar dai yadda ta ce tela ya yi wa Malam Aminu
Kano ɗinki, hakan ya sa aka zo har gida aka yi masa duka kamar za a kashe shi. A
wancan lokacin, ambaton kalmar sawaba kaɗai ya isa ya sa a maka tsattsauran hukunci.
Daga bayanan da aka gani
za a lura cewa, ba maza ne kaɗai suka fuskanci irin wannan takurawa daga jam’iyya
mai mulki ba, mata ma sun ɗanɗana. Su ma sun yi gwagwarmaya a nasu ɓangaren wajen
ganin sun samu dama a siyasance da kuma wasu fannoni na zamantakewar rayuwa ta yau
da kullum.
Irin wannan takura da
ake yi wa ‘yan hamayya ta ci gaba har zuwa jamhuriya ta biyu.
An samu wasu misalai irin waɗannan da suke nuna cin zarafin ‘yan hamayya
da kuma take masu haƙƙi wanda jam’iyyar hamayya ta PRP ta koka kan yadda ake kama
‘ya’yanta ana tsarewa ba tare da wata ƙwaƙƙwarar hujja ba.
“
NPN yanzu ta ƙyanƙyashe sabuwar maƙarƙashiya, mun fahimci cewa sun rubuta wasiƙa
zuwa Legas suna zargin magoya bayanmu da abubuwa na ƙarya, har waɗansu daga cikin
mutanenmu irin su Yusuf Kududdufawa an kama su daga umarnin gwamnatin jiha, saboda
wannan dalili na rubuta wasiƙa zuwa ga shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo domin a sako
mana mutanenmu, Muhammadu Abubakar Rimi da Isa Ibrahim ne suka kai wasiƙar.”
(Jega da wasu, 2002:29-30).
Malam Aminu Kano ya bayyana
cewa, jam’iyyarsu ta PRP ta gano wata maƙarƙashiya da jam’iyyar NPN take shirya
masu, wanda ake kama ‘ya’yanta bisa zarge-zarge marasa tushe ana ɗaurewa tun ma
kafin a kai ga gudanar da zaɓe, domin a karya lagonsu. Wannan ya sa Malam Aminu
ya rubuta wa shugaban ƙasa wasiƙa don ya sanar da shi kokensu.
Ire-iren waɗannan abubuwan
da suka shafi takura wa abokan hamayya ya zama ruwan dare a cikin al’amuran siyasar
Arewacin Nijeriya, kuma yawanci ‘yan siyasar da suke da ɗaurin gindin gwamnati ne
suke samun wannan damar domin su hana abokan hamayyarsu rawar gaban hantsi. An samu
tabbacin irin wannan salon siyasar a cikin tarihin ginuwar siyasar jam’iyyu a ƙasar
Hausa, ashe ba abin mamaki ba ne idan aka samu marubutan ƙagaggun labarun Hausa
sun tsara labarin da ya fito da irin wannan fasalin. Alal misali, an nuna yadda
aka riƙa kama magoya bayan jam’iyyar Sauyi ana ɗaure su ba tare da wani ƙwaƙƙwaran
laifi ba, kamar yadda ya bayyana a cikin littafin Tura Ta Kai Bango kamar haka:
“ ba wannan kawai ke damun su Ta-gyare da
Hassan ba, sai magoya bayansu da ake ta kamawa ana jefawa kurkuku a bisa raunannun
dalilai, shi kansa Hassan an taɓa kulle shi kwana biyu a Kabobi da sunan cewa ya
yi lacca ba tare da izini ba. Jiya kuma aka sallamo Garba bayan wata uku a kurkuku
da zargin cewa ya ingiza wasu mutane sun tayar da hankali shi da abokanensa a nan
Ƙoramu.”
(Katsina, 1983: 70).
Idan aka dubi wannan misali
za a ga cewa, tamkar hoto ne na siyasar jamhuriya ta farko da ta biyu, domin kuwa
kamar yadda aka riƙa kama mutane ana ɗaure su a kurkuku bisa dalilan da ba su kai
na ɗauri ba, haka ma aka nuna yadda su Hassan da Ta-gyare suka riƙa nuna damuwarsu
kan hakan. A ganinsu an takura masu ne don kawai suna hamayya da jam’iyyar Riƙau.
An bayyana cewa shi kansa Hassan a matsayinsa na shugaban jam’iyyar Sauyi na yankinsu
an taɓa kama shi an kulle da sunan ya yi lacca ba tare izinin hukuma ba, sai abokinsa
Garba shi ma an ɗaure shi wata uku bisa laifin tunzura wasu mutane a lokacin da
ya yi wani jawabi shi da abokansa. Irin wannan idan aka duba hotunan abubuwan da
suka riƙa faruwa ne a cikin tarihin ginuwar siyasar Arewacin Nijeriya.
Bugu da ƙari a wani misalin
an nuna yadda ake ƙulla wa ‘yan hamayya sharri da cewa sun raina hukuma ko sun raina
sarakuna, sai a kai su kotu a yanke masu tsattsauran hukunci, kuma babu wanda zai
ce an yi ba daidai ba, sai dai su ‘yan hamayyar su nemi hanyar da za su fitar da
fushinsu ga al’umma domin a san halin da ake ciki. Dubi abin da marubucin littafin
Tura Ta Kai Bango yake
cewa:
“ wani mutum da ake kira Buwai da ya yi
wa su Alhaji galari, nan da nan aka ƙulla masa sharrin cewa wai ya zazzagi maigari.
Da haka alƙali ya ɗaure shi wata biyu. Ga shi kuwa da mata da ‘ya’ya shida.”
(Katsina, 1983: 51).
Kasancewar su Alhaji Kaukai
‘yan jam’iyyar Riƙau, wani abu ya haɗa su Buwai ɗan jam’iyyar Sauyi har suka yi
tankiya, sai suka ƙulla masa cewa ya zagi maigari. Bai zagi maigari ba, ƙage suka
masa Haka kuma alƙali bai yi la’akari da cewa yana da iyali da ‘ya’ya shida ba,
ko kuma tunanin wa zai kula da su ba, ya yanke masa hukuncin ɗaurin wata biyu a
gidan yari.
Irin wannan ya biyo tsawon
tarihi har zuwa siyasar jamhuriya ta huɗu. A jamhuriya ta huɗu abin ya sauya fasali,
domin bayan an yi amfani da wannan salon na takura wa abokan hamayya, ta hanyar
kamu da ɗauri da dai sauran abubuwa, sai kuma aka yi amfani da Hukumar Yaƙi da Cin
Hanci da Zambar Kuɗaɗe (EFCC) don ta zama wata hukuma da ake firgita ‘yan hamayya
ko kuma duk wani wanda yake takun saƙa da jam’iyya mai mulki. Akan tura ma’aikatan
hukumar da sunan binciken almundahanar kuɗi don a kama mutum a ɗaure ko kuma a hana
shi yin wani amfani mai ƙwari musamman idan kakar zaɓe ya zo. Domin tabbatar da wannan batu, dubi abin da aka tsakuro
daga jaridar Aminiya:
“Tuni
dai wasu suka masu fashin baƙi suka fara hasashen cewa, Gwamnan ya canja sheƙar
zuwa jam’iyyar PDP ne saboda ya sami mafaka daga tuhumar da hukumar nan mai yaƙi
da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC).
(“Na Bar ANPP Ne Saboda”,
2007).
Gwamna Adamu Aleiro na
jihar Kebbi ɗan jam’iyyar hamayya ta ANPP ne wanda hukumar hukumar yaƙi da masu
yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa wato EFCC ta tuhume shi da almundahana a gab da
ƙarshen wa’adin mulkin shugaba Obasanjo a shekarar 2007. Kasancewarsa ɗan jam’iyyar
hamayya, kuma hukumar ta tuhume shi ne lokacin da aka fara shirin babban zaɓen ƙasa.
Ana ganin cewa hukumar ta yi haka ne domin ta tsorata a mastayin ɗan jam’iyyar hamayya.
Kwatsam, sai aka ji ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP mai mulki. Wannan ya sa aka
fara tunanin ya yi hakan ne domin guje wa binciken da hukumar za ta yi masa, inda
ya shiga ƙarƙashin inuwar jam’iyya mai mulki domin samun mafaka. A wancan lokacin
an yi zargin cewa, gwamnati tana amfani da hukumar a matsayin karen farauta, domin
takura wa ‘yan hamayya.
Wata hujja da ta nuna
cewa masu hamayya da gwamnati ne ake takura wa ta hanyar amfani da hukumar EFCC
ita ce, batun da shugaban majalisar dattawa ya yi na cewa ya kamata fadar shugaban
ƙasa ta tsame hannunta daga al’a muran hukumar. Domin kuwa tsoma bakinta zai iya
gurgunta dimokuraɗiyyar ƙasar. Ga abin da ya ce:
“Shugaban majalisar dattawa ya yi Allah
wadai da yunƙurin da fadar shugaban ƙasa ke yi na dakushe ‘yancin da hukumar EFCC
ke da shi, domin kuwa a tsarin dimokuraɗiyya irin wannan hukumar dole ne ta zama
mai cin gashin kanta ba ta zama a ƙarƙashin fadar shugaban ƙasa ba dokar da ta kafa
hukumar EFCC ba ta amince wa hukumar ta miƙa sunayen mutanen da take zargi ga fadar
shugaban ƙasa ba, sai dai ta gabatar da su gaban kotu domin a hukunta su Matuƙar
yaƙin da ake yi da cin hanci da rashawa zai karkata ne ga waɗansu ‘yan siyasa da
ake zargi da cin hanci ba duka waɗanda ake zargi ba, ‘yan Nijeriya za su ci gaba
da nuna shakku a kan adalcin EFCC ɗin.”
(“An Baddala Sunayen da
EFCC ta Fitar”, 2007).
Gwamnatin Obasanjo ta
yi amfani da wannan hukuma ƙwarai da gaske domin samun goyon baya ko ta halin ƙaƙa
daga ‘yan jam’iyyarsa da kuma ‘yan hamayya. Domin kuwa a wannan lokacin duk wanda
ya nuna ba ya tare da gwamnati ko kuma yana hamayya da ita sai a tura irin waɗannan
hukumomi su bincike shi. Kamar yadda wannan misalin da yake sama ya nuna, Hukumar
EFCC ta fitar da sunanyen waɗanda take zargi da cin hanci, maimakon a miƙa su kotu
ta hukunta su, sai aka kai sunayen fadar shugaban ƙasa. Shugaban majalisar dattawa
ya nuna cewa hakan ba daidai ba ne, domin ya saɓa wa dokar da kafa hukumar. Ya bayyana
cewa in dai ba a daina zaɓen ‘yan siyasar da za a tuhuma a bar wasu ba, bayan kuwa
dukkansu ana zargin su, to hakan zai iya ci gaba da karya guiwar ‘yan hamayya a
kan adalcin hukumar. Wannan tsoma bakin da fadar shugaban ƙasa ta yi a kan aikin
hukumar ya sa da dama cikin masu hamayya da gwamnati suka yi biyayya ba don suna
so ba, wasu kuma suka ja bakinsu suka yi shiru, musamman waɗanda suke riƙe da muƙamai
ko kuma suka taɓa riƙewa a baya, domin gudun kada allura ta tono garma.
An ci gaba da bin irin
wannan hanya ta takura wa abokan hamayya har zuwa shekarar 2010, lokacin ana gab
da kakar zaɓe na shekarar 2011. An riƙa amfani da hukumar EFCC wajen tuhumar duk
wani da aka san mai faɗa a ji ne a siyasance, wanda kuma zai iya kawo wa jam’iyya
mai mulki ta PDP matsala a siyasance. A lokacin da aka fara tunanin haɗewar jam’iyyu
a shekarar 2010 don su ƙalubalanci jam’iyyar PDP a zaɓen 2011 ma an samu irin wannan
fasali na takura wa abokan hamayya. Dubi wannan misalin:
Kamun da aka yi wa Bafarawa, bayan shekaru
biyu da saukarsa daga kujerar mulki da kuma shari’ar da ta biyo baya a babbar kotun
jihar Sakkwato, musamman a daidai lokacin da ya fito fili ya funjima on gama kan
jam’iyyun hamayya wuri ɗaya, al’amari ne da masu kula da al’amuran yau da kullum
ke gani a wani abu na taɓarɓarewa ga Hukumar ta EFCC, ta yadda ta zama karen farautar
Jam’iyyar PDP wajen wulaƙanta da kuma ɓata sunan mutanen da gwamnati ke ganin su
a matsayin ‘yan hamayya.”
(“Hukumar
EFCC Da Tsoffin Gwamnoni”, 2010).
A cikin wannan misalin, an alaƙanta kamun
da hukumar EFCC ta yi wa tsohon gwamnan jihar Sakkwato a shekarar 2010 a matsayin
hamayyar siyasa. An nuna cewa, ba a kama shi ba sai bayan da shekara biyu da sauka
daga kujerar gwamnan jihar, kuma sai da ya fito fili ya nuna aniyarsa ta haɗe kan
jam’iyyun hamayya domin su tunkari jam’iyya mai mulki a zaɓen shekarar 2011. Daga
nan sai aka ji hukumar EFCC ta kama shi tare da tuhumarsa kan almundahana. Wannan
dalilin ya sa al’umma sun ci gaba da yi wa hukumar kallon wadda ake amfani da ita
wajen takura wa ‘yan hamayya da ɓata masu suna a siyasance.
Tarihi ya nuna cewa, a
lokacin da rikice-rikice suka dabaibaye jam’iyyar PDP, wasu suka riƙa ficewa daga
cikinta suna komawa jam’iyyun hamayya. Wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar PDP ɗin da
ba su fita ba, amma suka riƙa nuna kurakuran jam’iyyar, sai aka yi masu barazana
da hukumar ta EFCC idan ba su kame bakinsu ba. jaridar Aminiya ta kawo wannan bayanin kamar haka:
“Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamiɗo
ya ce sabon yankan rake a siyasa za a firgita ba irinsu da suka goge a fagen siyasa
ba, inda ya ce babu wanda zai yi musu barazana da EFCC don su daina faɗin gaskiya.”
(Majeri, 2013).
A nan gwamnan ya nuna
yadda aka riƙa masu barazana ne da hukumar ta EFCC don suna faɗin gaskiya a kan
jam’iyyarsu ta PDP. Ya ce su ba ‘yan koyo ne a siyasa ba, ƙwararru ne kuma gogaggun
da barazana ko tsoratarwa ba za ta yi tasiri a kansu ba. Don haka ba za su daina
faɗin gaskiya dangane da jam’iyyar ba. Idan aka duba za a ga cewa, a jamhuriya ta
huɗu ba ma ‘yan hamayya kaɗai ba, duk wanda ba zai yi wa gwanati biyayya ido rufe
ba, ma’ana ba tare da yana ganin kuskuren yana nunawa don a gyara ba, to gwamnatin
za ta sa ƙafar wando ɗaya da shi. Za ta yi amfani da hukumar EFCC don a dankwafe
shi, ko kuma a hana shi motshi baki ɗaya a siyasance.
Irin wannan ya ci gaba
har zuwa lokacin da jam’iyyar hamayya ta APC ta karɓi ragamar shugabancin ƙasar,
shugaba Buhari ya yi ƙoƙarin yaƙi da rashawa kamar yadda gwamnatin nasa ta ayyana.
Kamar dai yadda siyasar ta gada, yawanci irin wannan yaƙin kan ƙare ne a kan ‘yan
hamayya, domin su ne za su zama waɗanda za a riƙa farauta da takura da kuma firgitarwa.
Wannan ya sa ma duk wanda yake so ya tsira daga irin wannan matsin na gwamnati,
sai ya koma jam’iyyar gwamnati a tafi tare da shi.
4.10
Yarfe Ga Abokan Hamayyar Siyasa
Ƙage da Ƙazafi kalmomi ne da
suke da makusantan ma’anoni da juna ko ma a ce ma’anarsu guda, sai dai kowacce da
asalinta, kuma ana iya amfani da wata a maimakon wata. Kalmar Ƙage Bahaushiyar kalma
ce, tana ajin suna ne mai ɗauke da jinsin namiji. Tana nufin a ce mutum ya yi abin
da bai ji ba, bai gani ba ko kuma a ƙulla masa sharri (CNHN, 2006: 273). Ƙazafi
kuwa kalma ce da take da asali daga Larabci wato ‘Ƙazaf’, wadda Hausawa suka ara
suka yi mata ƙarin -i a ƙarshenta ta koma ƙazafi. Ma’anar kalmar a Hausa da Larabci
duk abu guda take nufi. Kalmar Ƙazafi suna ne mai ɗauke da jinsin namiji, kalmar
tana nufin laƙa wa mutum laifi ko yi masa sharri (CNHN, 2006: 279).
Kalmar Yarfe Bahaushiyar kalma ce, tushen kalmar
shi ne [yarf-], da aka yi mata ɗafin
[-a] a ƙarshenta sai ta koma [yárfà] wadda take kalmar aikatau ce mai
ɗauke da karin sautin sama-ƙasa, daga gare ta ne aka samo kalmar [yarfe] bayan an shafe wasalin ƙarshe [-a] aka yi wa tushen kalmar ɗafin [-e] a ƙarshenta, sai ta koma [yárfé] wanda ya sa karin sautinta ya sauya
zuwa sama-sama maimakon sama-ƙasa a kalmar ‘yarfa’, sai kuma sauyawar karin sautin
ya haifar da sauyawar ajin nahawun kalmar daga aikatau zuwa suna[9].
Ƙamusun CNHN (2006: 479-480)
ya bai wa kalmar yarfe ma’anoni guda biyar kamar haka:
i- Maka ko daka
ii- watsa
iii- ƙaga
iv- aika da, musamman
na zagi
v- amfani da hannu don
share wani abu.
Daga cikin waɗannan ma’anonin,
ma’ana ta biyu da ta uku ne suke da alaƙa kai tsaye da wannan aikin, domin a ƙarƙashin
ma’ana ta biyu an ba da misali da ‘na watsa
masa taɓo’ kuma duk abin da aka watsa masa taɓo to an ɓata wannan abin, domin
zai nuna alamomi a wurare da dama a jikinsa. Ita ma ma’ana ta uku daga cikin ma’anonin
an ba da misali ƙarƙashinta kamar haka: ‘Sun ƙaga masa laifi’. Ke nan kalmar yarfe tana nufin ƙaga wa wani mutum
wani laifi kamar yadda aka bayyana ta a sama. Idan aka ƙaga wa wani mutum wani laifi
wanda bai ji ba, bai gani ba yakan zubar masa da ƙima ko ya rage masa ƙima a idon
mutane. Idan magoya bayansa ne sai a samu wasu su dawo daga rakiyarsa.
Don haka, kalmar tana
nufin a sanya wani baƙon abu a jikin wani ta yadda zai iya yin ɗigo-ɗigo a jikinsa
har ya fito a gani. Alal misali, kamar a samu farar tufa a yarfa mata manja ko wani
baƙin mai wanɗa zai zama an ɓata wannan tufar. Manufar yarfe a siyasance ita ce
ɓatawa, kamar yadda aka yarfa wa wannan farar tufar wasu launuka don a ɓata ta.
Kalmomi biyu na farko
wato ‘ƙage’ da ‘ƙazafi’ dukkansu kalmomi ne da ake amfani da ma’anarsu a cikin harkokin
yau da kullum, kuma in aka yi amfani da su suna iya dacewa da ko wa aka jefa da
su. Akan iya cewa an yi wa wane ƙage, ko an yi wa wane ƙazafi, amma kalmar yarfe
ta kasance kalma ce da ta keɓanci siyasa. A siyasance ba a cewa an yi wa mutum ƙage
ko ƙazafi, sai dai a ce an yi masa yarfe[10]. Ke nan, daga bayanan
da suka gabata za a fa himci cewa, kowane yarfe, ƙage ko ƙazafi ne, amma ba kowane
ƙazafi ko ƙage ne yarfe ba.
Yarfe wani yanayi ne da
abokan hulɗar siyasa sukan ɗauko wani abu su ɗora wa wani wanda bai ji ba bai gani
ba don kawai a ɓata shi a siyasance.
Yarfe zai iya kasancewa
a tsakanin ‘yan jam’iyya guda masu hamayya da juna, waɗanda sukan ƙirƙiri wani abu
su jingina shi ga wani abokin hulɗar siyasarsu na jam’iyya guda don su musguna masa.
Akan kuma samu yanayin da jam’iyya guda ake, amma ana ƙarƙashin wani uban gida na
siyasa, sai a yi wa juna yarfe don neman samun gindin zama a wajen iyayen gidan
nasu. A wani gefen kuma yakan iya zama ba jam’iyya guda ‘yan siyasar suke ba, sai
a ƙirƙiri wani abu a jefa wa abokin hamayya don mutane su dawo daga rakiyarsa, don
neman samun nasara a kan jam’iyyar da ake hamayya da ita[11]. Alal misali an ga yadda
aka riƙa yamaɗiɗi da wani batu da ake cewa wai ‘ɗan takarar shugabancin Nijeriya
a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ce, Allah ba ya karɓar addu’ar talakawa’,
amma kuma duk wanda aka tambaye shi yaushe ya faɗa? A ina ya faɗa? Babu wanda zai
iya kawo hujjar muryarsa, ko hoto mai motsi, ko kuma a rubuce, sai dai a ce kawai
haka aka ce. Wa ya ce? Shi ma a nan sai kuma a fara ‘yan kame-kame. Ma’ana dai yarfe
ne aka yi masa wanda kuma ya yi tasiri ƙwarai a zukatan al’ummar ƙasa. Akwai ire-iren
waɗannan misalai da dama da aka riƙa samu a cikin siyasar jam’iyya, sai dai waɗanda
wannan bincike ya taƙaita a kansu su ne waɗanda aka samu a cikin rubutaccen zube
kaɗai ban da na baka.
A taƙaice, kalmar Yarfe
bisa fahimtar wannan aikin tana nufin faɗin wani abu da bai tabbata ba, tare da
danganta shi da abokan hamayyar siyasa ko jam’iyyar siyasa ko ɗan siyasa, wanda
zai sa jama’a su ga baƙinsu.
Jam’iyyun siyasa sun shahara
ƙwarai wajen yi wa juna yarfe, kasancewar kowacce tana so ta ɗaukaka a kan abokiyar
hamayyarta, wannan ya sa abokan hamayyar siyasa sukan riƙa ƙaga aibu ga ‘yan’uwansu
suna faɗa wa jama’a don su guje su, ko da kuwa daga baya za a fahimci cewa wannan
abin da aka danganta jam’iyyar ko ɗan siyasar da shi ba gaskiya ba ne.
A lokacin da aka fara
siyasar jam’iyyu a ƙasar Hausa, jam’iyyu biyu ne aka kafa a ƙasar Hausa kuma suka
yi tashe, sannan kuma dukkansu sun yi gwagwarmayar neman mulki, inda ɗaya ta yi
nasara, ɗaya kuma ta zama jam’iyyar hamayya. Al’adar siyasa ce dole in za a tallata
jam’iyya ko ɗan takara, bayan an yi amfani da yabon abin da ake tallatawa, wajen
faɗin ingancinsa, sai kuma a kushe abokin haɗinsa ko abokin hamayyarsa domin a sake
fito da hasken abin da ake tallatawa ya fito fili, al’umma su karɓe shi, su kuma
guji wanda ba shi ba. A wurin wannan kushen ne ake samun yarfe
ga jam’iyyun siyasa.
Tun daga jamhuriya ta
farko an riƙa samun irin waɗannan bayanai a cikin rubutaccen zuben Hausa, inda jam’iyyu
biyu masu hamayya suka yi ta yi wa juna yarfe a tsakaninsu. A wasu lokutan ma ba
tsakanin jam’iyyun kaɗai yake tsayawa ba, har ma da ‘yan jam’iyya, inda akan kama
suna, wani lokaci kuma sai dai a yi ishara. Jam’iyyar NEPU da Jam’iyyar NPC sun
yi suna wajen irin wannan siyasar, wadda za a iya cewa daga gare su ne tsarin siyasar
jam’iyya ya ginu a ƙasar Hausa. Irin waɗannan misalai na yarfe sun fito a cikin
rubutaccen zube na Hausa, waɗanda suka yi nuni da irin wainar da aka toya a fagen
siyasar Jam’iyyu a wancan lokacin. Daga bisani, an ci gaba da samun yarfe a cikin
rubutattun ayyukan zuben Hausa waɗanda suka ci gaba da fito da hoton yadda siyasar
jam’iyyu ta gudana har zuwa yau.
Dangane da wannan bincike
an raba yarfen siyasa zuwa gida uku, sannan an ɗauki kowanne an yi
bayaninsa tare da misalan da suka dace kamar haka:
4.10.1 Yarfe Na Addini
A fahimtar wannan aiki,
addini hanyar rayuwa ce ta ɗan Adam, wadda ake bi ta hanyar yarda da saudaukar da
kai da kuma bauta domin samun biyan buƙata ko kariya ko kuma tsira a gaban Ubangiji.
A siyasance addini yana
taka muhimmiyar rawa wajen neman shugabanci da kuma tafiyar da shi, kasancewar shi
ne hanyar rayuwar da ‘yan Adam suke bi kuma suka amince da shi. Ita kuwa siyasa
ta kasance ginshiƙi a rayuwar ɗan adam wadda yake gudanar da ita da saninsa ko ba
da saninsa ba. Wannan ya sa ‘yan siyasa suka riƙa amfani da addini wajen cimma burikansu
na siyasa ta fuskoki da dama.
Yarfen siyasa yana daga
cikin abubuwan da aka riƙa amfani da addini wajen gudanar da shi, inda aka riƙa
amfani da wasu abubuwa na addini domin daƙile tafiyar abokan hamayya. Kasancewar
addini yana da tasiri ƙwarai a wajen masu shi ko mabiyansa akan samu wasu ‘yan siyasa
su yi amfani da shi wajen shafa wa abokan hamayya wani mummunan abu wanda zai sa
a ga baƙinsu, a ƙyamace su.
Tarihi ya nuna cewa ‘yan
siyasa sun riƙa yi wa abokan hamayyarsu yarfe ta hanyar amafani da addini kamar
yadda Paden (1973: 122) ya kawo bayanai a kan irin rikice-rikicen
da aka riƙa samu a tsakanin mabiya aƙidun Tijjaniyya da Ƙadiriyya har suka riƙa
yi wa juna yarfe kamar haka:
The
Sultan of Sakkwato later denied that the riot was between Qadiriyya and Tijaniya,
throughout the country and more especially in big towns, live amicably without interference
in each other’s religious belief. He referred to the rioters as ‘Yan Wazifa’ who
are going beyond their bounds to them even prayer five time a day was forbidden.
Fassarar marubuci:
Sarkin Musulmi ya ƙaryata batun rikicin
da ya faru tsakanin Tijjaniyya da Ƙadiriyya, waɗanda suke zaune lafiya a duk faɗin
ƙasar musamman ma a manyan garuruwa, inda ya bayyana cewa waɗansu masu neman wuce
gona da iri ne; masu cewa sallah biyar a wuni haramun ne, waɗanda ake kira ‘yan
wazifa suka tayar da rikicin.
Tarihi ya nuna ce, a farkon
kafuwar siyasar jam’iyyu, aƙidun Addinin Musulunci sun taka muhimmayar rawa a a
cikin siyasar ƙasar Hausa, duk kuwa da cewa shaihunnan waɗannan ɗariƙu ba ‘yan siyasa
ne ba, kuma ba su da alaƙa da ita, amma an yi amfani da darajarsu da na aƙidunsu
a cikin siyasar wancan lokacin, inda suka kasance tamkar ma su ne jam’iyyun a karon
farko. Idan aka yi la’akari da magoya bayan kowace jam’iyya za a ga cewa akasarinsu
mabiya aƙida guda ne, duk da cewa akan samu wasu ‘yan kaɗan da suke da bambancin
aƙidar. Alal misali, Jam’iyyar NPC ta su Ahmadu Bello Sardauna kaso mafi tsoka na
mabiyanta ‘yan Ƙadiriyya ne, haka ma dukkan manyan masarautun ƙasar Hausa ɗariƙar
Ƙadiriyya suke bi in ban da fadar Kano a wancan lokacin zamanin Sarki Abdullahi
Bayero wanda shi mabiyin ɗariƙar Tijjaniyya ne[12]. Ita kuwa jam’iyyar NEPU
ta su Malam Aminu Kano mafi yawa na mabiyanta a wancan lokacin ‘yan Tijjaniyya ne.
Wannan dalilin ne ya sa ko da aka riƙa samun rikice-rikice tsakanin aƙidun biyu
sai aka riƙa danganta shi da siyasa.[13] Dangantakar siyasar da
take tsakanin aƙidun biyu ya sanya suka riƙa yi wa juna yarfen siyasa a tsakaninsu.
Idan aka dubi bayanin
da yake sama za a fahimci cewa, kasancewar Sarkin Musulmi Baƙadire kuma a wancan
lokacin dukkan sarakuna suna goyon bayan jam’iyyar NPC ne, wannan ya sa ya yi wa
‘yan NEPU waɗanda suke ‘yan Tijjaniyya ne galibinsu yarfe da cewa sun ce sallah
biyar a wuni haramun ne kamar yadda misalin ya nuna. Duk da cewa a cikin bayaninsa
bai fito ƙarara ya ce ‘yan Tijjaniyya ba, amma ya yi amfani da kalmar “Yan Wazifa”
wadda kalma ce ta ƙasƙanci da ake faɗa wa ‘yan Tijjaniyya a wajen Lardin Kano.[14] Idan aka duba za a ga
cewa wannan yarfe ne na addini domin kuwa ‘yan Tijjaniyya ba su haramta sallah ba,
sai dai kawai za a ga hakan a matsayin wanin salo ne na rage wa aƙidar da ma mabiyanta
magoya baya waɗanda suka kasance ‘yan NEPU a wancan lokacin domin raunana siyasarta.
Irin wannan ya ci gaba
da bayyana a cikin ayyukan rubutaccen Hausa na zube, inda ‘yan siyasa suka riƙa
yi wa abokan hamayyarsu yarfe don mabiya su ji cewa jam’iyyar da suke bi ba ta cancanci
su bi ta ba. Galibi a siyasa irin waɗannan abubuwa da akan yi yarfe da su ƙaga su
ake yi ba tare an ji ko an gani ba, abin nufi babu tabbas a faruwarsu. Alal misali,
jamiyyar NPC ta ce jam’iyyar NEPU jam’iyyar kafirai ce, don ɗabi’unsu irin na Kirista
ne. Dubi abin da suka ce:
tsakanin
‘yan NPC da na NEPU waɗanne ne ɗabi’arsu irin ta Kirista ce? Har wasu daga cikinsu
sukan ce ba sa bin addinin Musulunci?
(Nadabo, 1960).
Duk da cewa tambaya ce
aka yi, amma dai ta sigar yarfe ce aka yi ta domin dai amsar a ƙarshe za ta faɗa
kan NEPU ne, domin kuwa ‘yan NPC ne suke tambayar, kuma a jaridar gwamnati wadda
ba a sanya bayanan ‘yan hamayya a cikinta, balle kuma abin da ya shafi yarfe. Idan
aka duba a cikin wannan misali za a ga cewa an yi wa ‘yan hamayya ne yarfe cewa
ɗabi’unsu irin na Kiristoci ne, wanda an san dai cewa kaso mafi tsoka na al’ummar
ƙasar Hausa Musulmi ne, kuma addinin Kirista yana takin saƙa ne da na Musulunci.
Wannan ya sa ‘yan jam’iyyar NPC suke ganin idan suka jefi NEPU da mummunar kalma
irin wannan zai haifar masu da koma-baya. Haka kuma ba wai ɗabi’unsu ne kaɗai irin
nan Kirista ba, domin ana iya samun wani Musulmi mai yin wasu ɗabi’u irin na Kirista,
sai suka ƙara masu da cewa ai wasu ma daga cikin ‘yan hamayya sukan ce su ba Musulmi
ba ne, wato dai sun ma yi ridda, sun bar addinin Musulunci ke nan. Idan aka duba
za a ga cewa wannan ba ƙaramar magana ba ce, domin kuwa jifar ‘yan jam’iyya da kafirci
ba ƙaramin illata jam’iyyar zai yi ba don al’ummar ƙasar Hausa akasarinta Musulmi
ne.
Kasancewar al’ummar Hausawa
suna girmama shugabanninsu matuƙa, wannan bai sa sun girmama wani sha’ani na siyasa
fiye da addini ba. Tarihi ya nuna cewa abokan hamayyar siyasa, musamman na jam’iyyar
hamayya ta NEPU suka riƙa amfani da wannan wajen yi wa magoya bayan NPC yarfe ta
hanyar nuna cewa ai sun fi girmama Sardauna da shugabanninsu na siyasa fiye da Ubangiji.
Sun nuna cewa yadda suke tsoron Sardauna ba su jin tsoron Allah haka. Dubi dai abin
da suka ce a cikin jaridar Daily Comet:
Kai wawa, jahili, daƙiƙi, sususu, bari in gaya maka
duk cikin Shari’ar Islama ba inda aka ce a nuna bambanci, ba inda aka ce a bada
kuɗi don neman galaba, ba inda aka ce a girmama Sardauna a wulaƙanta gyartai. In
kuwa akwai, ka gaya mani ayar da ta ce a yi kukan masallaci na ƙarya don jin daɗin
Sardauna da jam’iyyarsa
(“Addinin Musulunci a Mazahabar Maliki”, 1960).
Idan aka dubi wannan misalin da yake sama
za a fahimci cewa, mayar da martani ne aka yi ga kalaman abokin hamayya. A cikin
wannan martanin an yi wa shugabannin jam’iyyar NPC yarfe ta hanyar ƙaga masu wasu
batutuwa munana da kuma danganta su da su ba tare da ƙwaƙƙwarar hujja ba. A cikin
misalin an nuna cewa ‘yan NPC suna aikata wasu abubuwa na addini ne domin ganin
idon Sardauna ko don su faranta masa. Misali, ɗaukaka Sardauna saboda samun duniya
da wulaƙanta talaka. Haka kuma an nuna cewa suna yin kuka a masallaci ne ba don
tsoron Allah da ya cika zuciyarsu ba, sai don Sardauna da jam’iyyarsa su ji daɗi.
Kamar yadda ‘yan NPC suka riƙa nuna cewa,
jam’iyyar NEPU jam’iyya ce ta kafirai maƙiya addini, su ma NEPU sun yi amfani da
wannan yarfen ta hanyar nuna cewa shiga jam’iyyar NPC ko AG tamkar shiga kafirci
ne, kamar dai yadda wannan misalin ya nuna:
domin
ni har abada ba zani shiga AG ko NPC ko wata jam’iyya ba illa NEPU wadda na dade
kuma nake ciki a yanzu. Domin shiga NPC ko AG shiga uku ne, saboda haka Allah ya
tsari Musulmi da shiga waɗannan jam’iyyu
(Alasan, 1961).
Wannan misalin ya nuna
cewa duk jam’iyyar da ba NEPU ba to shigar ta tamkar shiga uku ne. Idan aka ce mutum
ya shiga uku kuwa ana nufin ya shiga masifa da bala’i ke nan. Babu kuwa wata masifar
da ta kai kafirci, wannan ya sa a cikin misalin da yake sama aka ƙarasa da addu’ar
neman tsarin duk wani Musulmi da shiga Jam’iyyar NPC da AG, wato duk Musulmi bai
kamata ya shiga jam’iyyun ba, to wanda ya shiga fa? Ke nan, ba Musulmi ne shi ba.
A siyasance, idan aka
lura cewa mutum yana da muhimmanci a cikin tafiyar wata jam’iyya to za a yi duk
yadda za a yi domin karkato hankalinsa don ya bi wata jam’iyyar da ba ita ba, kuma
kowace jam’iyya za ta so ya kasance a cikinta domin irin amfanin da zai jawo mata.
Idan aka bi duk hanyar da za a bi domin raba shi da jam’iyyar da yake ba a yi nasara
ba, sai kuma a nemi hanyar da za a ɓata shi don dai a yi irin abin nan da ake cewa
a fasa kowa ya rasa, wato a bi shi da yarfe don a karya lagon siyasarsa. Irin wannan
ne ya faru da Hassan a cikin littafin Tura
Ta Kai Bango, inda abokan hamayya na jam’iyyar hamayya suka yi masa yarfe cewa
ya shiga jam’iyyar kafirai. Dubi misalin da yake a ƙasa:
Eh to lafiya, amma ba lau ba. Hassan ne
na ga yana neman ya shiga hanya ta Allah wadai, wadda sharrinta ba shi kaɗai zai
shafa ba, har da danginsa da mutanen gari. A taƙaice dai yana neman kawo jam’iyyar
siyasa ce ta kahurai a nan garin.’
‘Kahurai ɗan nan?’
‘Kahurai Inna! Mu kuma muna ganin yadda
mai gidan nan ya nuna masa hanyar makaranta bai kamata ba a ce karatun da ya yi
ya zo ya tafi a banza ke nan.
(Katsina, 1983: 43-44)
A wannan misalin idan
aka duba za a ga cewa, magoya bayan jam’iyyar Riƙau ne suka tafi suka samu mahaifiyar
Hassan suka ce ai jam’iyyar da su Hassan ɗin suke son kawowa garinsu jam’iyya ce
ta kafirai, kuma yana neman shiga. Wannan ya sa hankalin mahaifiyarsa ya tashi don
ta ji zancen cewa ɗanta zai shiga mummunar hanyar da ba shi kaɗai sharrinta zai
shafa ba har da danginsa da sauran mutanen gari. Domin Hassan ɗan gidan
malamai ne, kuma ya samu tarbiyya irin ta malanta bai kamata a ji shi ya shiga irin
wannan hanya ba. Idan aka duba za a ga cewa yarfe ne aka yi wa Hassan na addini,
inda aka danganta jam’iyyarsa da ta kafirai don kawai a ɓata shi a wajen mahaifiyarsa
don ta hana shi bin jam’iyyarsa ta Sauyi.
Idan aka dubi waɗannan bayanan da misalan
da aka kawo za a fahimci cewa, ‘yan siyasa suna amfani da addini wajen yi wa abokan
hamayya yarfe domin nuna wa al’umma cewa ba su cancanci a bi su ba.
4.10.2
Yarfe Na Ƙima/Halaye
Ƙima yana nufin hali na
ban girma (CNHN, 2006:244). A siyasa ana la’akari da halaye da ɗabi’un ‘yan siyasa
wanda dole ne a zahiri su kasance na ƙwarai domin magoya bayansu samu dalili da
ƙwarin guiwar goya masu baya da kuma tallata su domin zaɓensu. Samun ‘yan siyasa
da wasu munanan ɗabi’u ko wasu miyagun halaye ko tarihin wani abin kunya yakan sa
a yi wa jam’iyyarsu suka da mummunar shaida ta hanyar danganta su da wannan halin
wanda zai iya raunana farin jinin jam’iyyar ga magoya bayanta.
A cikin tarihin siyasar
Jam’iyyu an sha zargin ‘yan NEPU da tsaurin ido ga mahukunta, kasancewar sun yi
imani cewa mahukunta suna danne masu haƙƙoƙinsu. Wannan ya sa duk yadda suka juya
ko suka furta wani abu ‘yan NPC sukan ɗauke shi a matsayin tsageranci ne maimakon
neman haƙƙi. A wata wasiƙa da aka samu a jaridar Sodangi an nuna yadda ‘yan jam’iyyar NPC suke jingina wa ‘yan NEPU rashin
tarbiyya, inda har a cikin wasiƙar ya kira ‘yan NEPU da cewa sun raina iyayensu.
Dubi wannan misalin:
Ina so Edita ka ban ɗan fili don in bayyana
rashin tarbiyyar NEPU. Abin mamaki, don wanda ya ce mahaifinsa ma ba kowa ba ne,
ina ga wani? Kwanan baya ne can, ranar da suka yi lacca a Tudun Wada, sun taso suna
komowa gida suna ta ƙetare babban titi babu tunanin komai, sai ga wata mota ta ɓillo
daga Airport. A nan suka dinga yi wa mai motar tsawa tun yana nesa, wai ya tsaya
sai Firimiya ya wuce wato Malam Aminu Kano bayan wucewar wannan direba sai wasu
jakan ‘yan NEPU suka bi shi da zagi. Wannan kuwa rashin tarbiyya a fili ke nan.
(“Lallai
Babu Tarbiyya”, 1957).
A cikin wannan misalin,
an nuna yarfe ne inda aka bayyana cewa ‘yan NEPU ba su da tarbiyya. An sani cewa
tarbiyya muhimmin abu ne a rayuwar Hausawa, kuma duk wanda ya rasa ta ana yi masa
masa kallon mutumin banza maras ƙima da daraja a idon mutane. Haka kuma duk wanda
ya rasa tarbiyya ana kallon sa a matsayin wanda ba ya ganin mutuncin kowa. Wannan
ya sa a cikin misalin bayan marasa tarbiyya da aka kira su, sai kuma aka ce sun
raina iyayensu, in kuwa hakan ta kasance to ke nan babu wani mai sauran mutunci
a idonsu. Da wannan ‘yan NPC suka riƙa nuna wa al’umma cewa magoya bayan NEPU tsageru
ne marasa kunya da mutunci, don haka kada a bi su ko kuma a goya masu baya.
Da aka ci gaba da tafiya
lamarin yarfe ma ya ci gaba, domin a wuraren shekarar 1959 an samu wani bayani da
ya nuna ‘yan siyasa sun ci gaba da yi wa abokan hamayyarsu yarfe, don nuna cewa
ba su da halin kirki, ko kuma ba za a samu wani abin kirki da al’umma za ta amfana
ba in aka zaɓe su. Alal misali, a cikin jaridar Sodangi an ga inda aka yi wa jam’iyyar NEPU yarfe da cewa cuta take
yaɗa wa magoya bayanta kamar haka:
amma
NEPU ta zama tunku da ƙararrawa mai jawowa dangi cuta koyaushe, ita ko kujera ɗaya
ba za ta samu ba, sai ta koma Kudu wajen Enugu ko ta lasa a can.
(“A.G.
Na Maganin Mutuwa a Arewa”, 1959).
A nan ɗaya daga cikin
magoya bayan NPC ne yake nuna cewa Jam’iyyar NEPU babu alheri tattare da ita, inda
ya kwatanta jam’iyya da wani dabba mai suna tunku, wanda ya ce ba ya kawo wa ‘yan’uwansa
alheri, kullum sai sharri. Don haka magoya bayan jam’iyyar ba za su samu wani alfanu
daga gare ta ba sai dai cutuwa da za su yi. Ya nuna cewa ba za ta samu ko kujera
ɗaya ba a Arewa idan aka yi zaɓe, sai dai ta koma Kudu ko za ta samu a can. Idan
aka dubi yadda ya nuna cewa Jam’iyyar NEPU tana yaɗa wa ‘ya’yanta cuta za a fahimci
cewa lallai yarfe ne ya yi wa jam’iyyar ta hanyar amfani da wani hali mummuna na
yaɗa cuta, don dusashe haskenta ga mogoya bayanta. Duk da cewa babu wanda aka ji
cewa jam’iyyar ta sa masa wata cuta ko kuma ta jawo masa wani sharri, illa dai ya
ƙaga zancen ne don ya sanya wa jama’a shakku a kanta.
Yana daga cikin yarfen
da aka samu a cikin tarihi tun a jamhuriya ta farko, jingina wa mutum wani mummunan
aiki wanda bai aikata ba, ko kuma ya aikata sai a yi ƙoƙarin danganta mummunar aikinsa
ga wasu don a nuna cewa duk haka suke ko kuma halinsu guda. Wannan ya yi daidai
da wani misali da aka samu a cikin jaridar Sodangi
wanda aka yanke wa wani ɓarawon agwagi shekara ɗaya a gidan yari. Dubi misalin:
Mai shari’a ya sami Gambo da laifin satar
agwagi bayan an tambaye shi (Gambo) ya tabbatarwa da shari’a sai mai shari’a ya
yanke masa hukunci da shekara ɗaya. Har wa yau dai ashe a jikin rigar mutumin nan
a gaba da baya duk tauraro ne a jikinta To wannan abin kunya ko lallai ya kai a
ce da mai shari’a an ji kunya ko ba ita a ce dai mai riga da tauraro ya sato agwagi
(Mohamed, 1960).
An tuhumi wani mai suna
Gambo da satar agwagi, kuma an same shi da laifi. A matsayinsa na wanda aka samu
da laifin sata, sai kawai aka yanke masa hukunci daidai da laifin da ya aikata.
Bayan haka sai aka lura cewa, a jikin rigar ɓarawon akwai hoton tauraro wanda yake
alama ce ta jam’iyyar NEPU, sai aka nuna cewa ai ɓarawon nan ɗan NEPU ne, don haka
sai ‘yan NPC suka ce ‘yan NEPU su faɗa wa mai shari’a sun ji kunya. In kuwa ba su
da kunya to su faɗi cewa an kama mai riga da alamar tauraro ya saci agwagi. Wannan
shi ma zai iya kasancewa yarfe ne kawai irin na siyasa, domin kuwa da ganin tauraro
a jikin rigar ɓarawo ba zai tabbatar cewa shi ɗan NEPU ne ba, don yana iya kasancewa
ma rigar sato ta ya yi a wani wuri ya sanya ta ba tare da la’akari da alamar da
take jikinta ko na wace jam’iyya ce ba. Don an kama wani ɗan jam’iyya da laifi ba
shi yake nuna cewa duk ‘yan jam’iyyar ne suka yi laifin ba, hasali ma su laifin
bai shafe su ba.
Wani misalin yarfe na
halaye shi ne, yadda za ka ga wata jam’iyya tana faɗin miyagun maganganu a kan wata,
inda za ta riƙa danganta ta da munanan halaye kamar su hassada da ƙarya da cin amana
da dai sauransu. A wannan misalin da yake ƙasa an samu irin wannan:
Ofishin
ba da labarai na jam’iyyar NEPU ya Zargi Jam’iyyar NPC a kan sunan nan da ta yi
na irin halin nan nata na hassada a kan maganar da awolowo ya yi cewa babu irin
mulkin da ya fi dacewa da Nigeria illa na jamhuriya.
(Bai
Kyautu NPC Ta Soki Maganar Da Awolowo Yayi Ba, 1961).
A cikin wannan Misalin
NEPU ta siffanta jam’iyyar NPC da ɗabi’ar hassada, inda ta nuna cewa da ma halin
jam’iyyar ne, domin a ganin NEPU shawarar da Awolowo ya bayar kan tsarin mulkin
da ya kamata a bi shi ne daidai, kawai dai hassada ce ta sanya NPC sukar wannan
batu. Idan aka duba za a ga cewa, hassada mummunan abu ne, kuma babu wanda zai so
a danganta shi da shi, su kuwa a wurin ‘yan siyasa abu ne da suke amfani da shi
don hana abokin hamayya motsi. Ya zama wani hali na ‘yan siyasa wanda da zarar an
ga kuskuren ɗan siyasa aka nemi yi masa gyara sai a ce hassada ake yi masa. Wannan
ya sa abokan hamayya da zarar sun yi magana sai a ce hassada ce suke yi wa jam’iyya
ko ɗan siyasa ba da zuciya ɗaya suke yi ba.
Jam’iyyar NEPU ta kamanta
jamiyyar NPC da jam’iyyar gumaka, inda ta yi kira da kada a zaɓe ta. Kalmar gunki
dai an san wani abu ne da aka sassaƙa ko a ƙera ko a gina wanda yake da sifar mutum
ko wani abu mai rai, wanda ba ya iya amfanar da kansa komai, kuma ba ya iya kare
kansa daga cutarwa ko ya kare wani. Gunki ba ya magana ba ya motsi balle ya iya
aiwatar da wani abu. Ga misalin kamar haka:
ina
jan hankalin mutane masu zaben NPC da su manta da ita domin jam’iyyar gumaka ce
(Gasakas,1961).
A nan ‘yan
jam’iyyar hamayya ne suke yi wa masu mulki yarfe da cewa jam’iyyarsu ta gumaka ce.
A nan ɗayan uku ne, ko dai jam’iyyar ba ta iya tsinana wa al’umma komai kamar yadda
gunki ba ya iya amfanar kansa balle waninsa, ko kuma manyan jam’iyyar NPC ne aka
danganta su da gumaka domin ana yi masu biyayya tamkar yadda ake bauta wa gumaka,
ko kuma su ‘yan jam’iyyar baki ɗaya daga shugabannin har mabiyan bautar gunki suke
yi ba Allah suke bauta wa ba. Tun daga taken wasiƙar da jaridar ta buga za a fahimci
cewa, mai wasiƙar yana nufin duk wanda ya bi jam’iyyar NPC ya ɓata kamar dai yadda
mai bautar gumaka yake ɓatacce kamar yadda Musulunci ya nuna.
Daga cikin yarfe na ƙima
wani lokaci akan danganta shi da wani makusancin ɗan jam’iyya, wanda ake ganin zai
iya shafar su har ya yi tasiri a cikin siyasarsu. Alal misali, wani ɗan siyasa wanda
yake tsohon shugaban ƙaramar hukuma ne, a lokacin da yake neman kujerar ƙaramar
hukuma an yi masa yarfe da cewa mahifinsa ɓarawon keke ne lokacin yana matashi,
don haka ba za a zaɓi wanda yake da gadon sata ba, bayan kuwa hakan bai taɓa faruwa
ba.[15] Irin wannan yarfen ya
yi kama da wanda aka nuna a cikin littafin Tura
Ta kai Bango kamar haka:
Ni ai da ma na san wannan
yaron bai gaji arziƙi ba. Ubansa fa Na-Torami har ya mutu itace yake sarowa yana
sayarwa. Kwana bakwai ma kafin ya mutu, sai da na sa shi ya kawo min kai uku har
gida Wani ya ce, Yo shi kansa Garban fa? Ubansa ba mahauci ba ne, karen lahira?
(Katsina, 1983: 21-22)
A cikin wannan misalin ana an yi wa ‘yan jam’iyyar
Sauyi ne yarfe cewa talakawa ne ‘ya’yan matsiyata ba su da komai, duk da cewa suna
da jama’a kuma sun zamar wa jam’iyyar Riƙau ƙadangaren bakin tulu. An nuna cewa
ai Hassan mahaifinsa sana’ar saro itace yake zuwa ya yi, ya zo gari ya sayar. Shi
kuwa Garba an ce wai mahaifinsa mahauci ne karen lahira. Irin waɗannan abubuwan
akan samu duk yarfe ne don jama’a su ɗauka cewa ai ba wata ƙima suke da ita a cikin
al’umma ba. Bayan kuwa babu ruwan shugabancin siyasa da arziƙinsu matuƙar dai sun
cancanta, amma sai a yi amfani da ƙimarsu a yi masu yarfe da shi.
A wasu lokuta akan nemi
abin da za a shafa wa ɗan siyasa domin ya zubar masa da mutunci a idon a jama’a,
inda za ka ji an zargi wani ɗan takara da yi wa wata cikin shege, ko wani makamanci
haka, a yaɗa don a sanya masa baƙin jini a cikin al’umma. A tarihin siyasar jam’iyyu
an samu irin wannan yarfen wanda jaridar Gaskiya
Ta fi Kwabo ta ruwaito, inda aka yi wa mataimakin shugaban ƙasa a jamhuriya
ta biyu yarfe da cewa, ya yi lalata da wata mata har ta samu juna biyu. Ga misalin:
Wata mujallar kasar nan mai suna The Week
ta taɓa buga wani labari, inda ta nuna cewa, wata matar aure ta shaida wa kotu cewa
Alex Ekwueme ne ya yi mata ciki har Allah ya sa ta sami ƙaruwa Amma shi Ekwueme
ya ce abin da Adeline ta fada karya ne kuma bata suna ne.
(“Ekwueme zai ba mu kunya”,
1999).
Alex Ekwueme shi ne mataimakin
shugaban ƙasa a jamhuriya ta biya, kuma shi ne aka yi wa wannan yarfen a lokacin
ana shirye-shiryen sake zaɓen su a karo na biyu a shekarar 1983. Wata matar aure
ce mai suna Adeline ta yi iƙirarin cewa shi ne ya yi mata cikin shege har ta haifi
‘ya’ya biyu, inda shi kuma ya ƙaryata. Ya nuna cewa abin da ta faɗa ba shi da tushe,
hasali ma yarfe ne kawai aka masa domin a ɓata masa suna.
Samun tababa a cikin nasabar
mutum babban abu ne da kan sa mutum ya rasa ƙimarsa a idon mutane, wannan ya sa
‘yan siyasa kan riƙa yin yarfe a duk lokacin da aka samu wata ƙofa wadda ta ba su
damar hakan. A baya an yi ta yaɗa maganganu na yarfe da suke nuna cewa wani mataimakin
shugaban ƙasar Nijeriya tsintacce ko kuma ba a san iyayensa ba. ‘Yan hamayya sun
yi ta amfani da wannan domin dasusashe haskensa. Irin wannan ya fito a ciki littafin
Kowa Ya Bi inda aka nuna cewa gwamnan
jihar bai san iyayensa ba. Ga misalin:
to
amma yadda za ku san batun ƙaryar shekarun da takardun da ma uwa uba rashin tabbacin
iyayen gwamna don kowa ya san a gidan marayu ya girma. Sannan har yanzu gwamna ya
kasa fitowa ƙarara ya ƙaryata zarge-zargen a idanun duniya. Sai kame-kame yake yi
idan an tambaye shi. An ma taɓa tambayar mai ba shi shawara
a kan batun shari’a sai ya ce wai a je gidan marayu za a ga tarihinsa a rubuce.
To ya ‘yan’uwa mu da Allah (SWT) ya ba mu wannan babban gari mai tarihi ga manyan
bayin Allah da waliyyai wai mun ba wa jikan Musailamatul-Kazzabi yana mulkarmu ku
san ba zai yiwu ba.
(Gwammaja, 2007: 30)
Kamar yadda aka riƙa yada
cewa wancan mataimakin shugaban ƙasar ba shi da iyaye, haka wannan misalin ya nuna
cewa gwamnan bai san iyayen sa ba a gidan marayu ya tashi, kuma ‘yan hamayya ne
suka sanya shi gaba suna yi masa yarfe da wannan. Ba sabon abu ba ne a siyasar Nijeriya
a zargi mutum da rashin takardun karatu, wanda a lokuta mafi yawa akan samu yarfe
ne kawai domin idan aka bincika akan tarar sun yi har ma da shaida. Akan yi wa mutum
yarfe da cewa ba shi da iyaye ne don a rage ƙimarsa a idon duniya musamman idan
an rasa da me za a ɓata sunansa da shi.
Irin wannan ya sake bayyana
a cikin littafin Dambarwar Siyasa, inda
aka so yarfa wa Farfesa don a ɓata masa suna da cewa ya yi wa wata yarinya fyaɗe
kamar haka:
Ganin cewa haƙarsu ba ta cim ma ruwa ba
sai suka ƙudurci ko ta wane fanni sai sun dakushe farin jinin Farfesa tare da zubar
masa da mutunci a idon jama’a. Ranar wata Lahadi tarkonsu ya kama kurciya, domin
a ranar ne suka samu nasarar shigar da wata yarinya ‘ya shekara goma sha biyu cikin
gidan gonar Farfesan, a daidai lokacin da ya je duba wani aiki da aka gudanar. Bayan
‘yan iskan sun yi mata rubdugun fyaɗe, sai suka lallaɓa suka sulale ba tare da wani
ya gan su ba, tare da yada ta a bakin hanyar shiga da fita ta gidan gonar. Tun daga
nesa Farfesan ya hango ta a yashe, cikin hanzari ya yunƙura da niyyar kai mata agaji,
tabbacin da ya samu tana da sauran numfashi a jikinta ya sa ya yunƙura tare da cicciɓar
ta da niyyar sa ta a mota ya kai ta asibiti, a daidai wannan lokacin ‘yan sanda
suna zuwa. Abin ka da ture, take suka zargi Farfesa da aikata wannan aika-aika.
(Aminiya-Trust, 2020:
41).
A cikin wannan misalin
za a fahimci cewa yarfe ne aka shirya wa Farfesa a matsayinsa na mutum mai gaskiya
da riƙon amana da kuma mutunci a cikin al’umma wanda gaskiya da mutunci suka sanya
jama’a suke ƙaunarsa, kuma suka tsayar da shi takarar gwamna a wata jam’iyya, inda
‘yan hamayya suka lashi takobin ko ta halin ƙaƙa sai sun tabbatar bai kai labari
ba. Bayan tsallake dukkan makirce-makircen da aka riƙa ƙulla masa ne aka yi tunanin
a shirya masa yarfen da zai taɓa mutuncinsa ya sa al’umma su dawo daga rakiyarsa.
Idan aka duba za a ga cewa, fyaɗe mummunan abu ne a cikin al’umma, wannan ya sa
aka danganta ɗan takarar da shi ta hanyar jefar da yarinyar a bakin gidan gonarsa,
kuma aka jira sai da ya zo inda take aka ce ana zargin shi ya yi mata.
Yarfen siyasa ya ci gaba
da bayyana a cikin tahin siyasar jam’iyyu, domin bayan faɗuwar jam’iyyar PDP a babban
zaɓen ƙasa a shekarar 2015, shugaba Muhammadu Buhari ne ya zama shugaban ƙasar Nijeriya
a jam’iyyar APC. Bayan rantsar da shi ya yi fama da rashin lafiya, inda ya tafi
jinya ƙasar Birtaniya. Bayan dawowarsa don ci gaba da gudanar da harkar mulki, sai
aka yi ta raɗe-raɗin cewa ai ainihin Buhari ya mutu, an sauya shi ne da wani mai
kama da shi mai suna Jibril daga Sudan. Wannan zance ya yi tashe a cikin al’umma
kasancewar tun da ya dawo sai karsashinsa ya sauya ya ragu tamkar ba Buharin da
aka zaɓa ba. Wannan ya sa wasu al’ummomi daga wasu ɓangarorin ƙasar suka riƙa kiransa
da Jibril na Sudan. Shugaba Buharin ya nuna cewa shi ne da kansa ba a sauya shi
da na bogi ba. Dubi wannan misalin:
A jiya Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
ya bayyana cewa shi ba na bogi ba ne, ya bayyana hakan ne a ganawar da ya yi da
al’ummar Najeriya mazauna kasar Poland a birnin Krakow a ziyarar da ya kai kasar
domin halartar taron sauyin yanayi na Majalisar dinkin duniya. A yayin ganawar,
wani dan Najeriya ne ya yi masa tambaya a kan cewa shin da gaske ne cewa shi ne
Buhari da aka sani ko kuma wani ne ke kwaikwayon sa da ake kira Jibril daga Sudan.
Shugaban ya yi Allah wadai masu yada wannan
jita-jitar tare da cewa, ba su san ya kamata ba
(Adamu, 2018).
Shugaba Buhari ya fito
ne ya tabbatar wa duniya cewa yarfen da ake yi masa cewa shi ba na bogi ne ba, shi
ne dai gangariyarsa, ba wani ne yake kwaikwayonsa ba, kuma ya nuna rashin jin daɗinsa
da wannan labarin da ake ta yaɗawa. Irin wannan yarfe ne na ƙima domin ana nuna
cewa ba shi da nagarta kamar yadda aka san shi a farko kama mulkinsa a matsayin
zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.
A jamhuriya ta huɗu an
samu wata hanya ta yarfe wadda za a samu wani ɗan bangar siyasa a biya shi, sai
a kitsa masa abin da ake so ya fito ya faɗa a wata kafar watsa labarai, kuma in
ma wani abu ya biyo baya iyayen gidansa na siyasa su ne za su tsaya masa don fitar
da shi. Irin waɗannan mutane da akan ɗauka haya a siyasance ana kiran su da ‘sojojin
baka’. Aikin irin waɗannan sojojin bakan shi ne su fito su ƙalubalanci ‘yan hamayya
ta hanyar yarfe ko kuma su kare iyayen gidansu ta hanyar yi wa abokan hamayya yarfe.
Irin wannan misalin na sojan baka ya bayyana a cikin littafin Da Bazarku inda aka bai wa wani sojan baka
mai suna Auwalu wasu bayanai na yarfe a rubuce wanda aka yi wa Farfesa Auta. Ga
misalin:
Wai yaro ƙarami kamar Auwalu wanda mahaifinsa
ma almajirinka ne wai shi ne yau zai shiga gidan rediyo yana faɗar wai Farfesa ma
da ake kiranka na je-ka-na-yi-ka ne… kuma wai kai ɗin nan Bafillatani ne, don haka
idan aka yi kyakkyawan bincike wai kai ba ma mutumin ƙasar nan ba ne Farfesa Auta
ya yi murmushi ya ce, na saurari duk abin da yaron nan ya faɗa, amma kai da ji ka
san rubuta masa aka yi ya haddace domin haka ka rabu da su ko ba-daɗe ko ba-jima
gaskiya dai ɗaya ce tal kuma siyasa ba da gaba muke yin ta ba.
(Surajo, 2006: 95).
A cikin misalin an nuna
cewa Auwalu ya shiga gidan rediyo ya yi wa Farfesa Auta yarfe ta hanyar taɓa ƙimarsa
da cewa wai shi ɗin Farfesan bogi ne, kuma wai in ma aka tsananta bincike a tarar
cewa shi ba ɗan ƙasa ba ne don kawai shi Bafulatani ne. Don a nuna cewa sojan baka
ne shi ɗaukar hayansa aka yi, sai Farfesa Auta ya ce, ai ko da jin yadda yake magana
za a fahimci duk bayanan da yake faɗa rubuta masa aka yi ya haddace su, kuma in
aka yi haƙuri gaskiya za ta bayyana.
Idan aka dubi dukkan bayanan
da aka kawo a wannan ɓangaren za a fahimci cewa, wani nau’in yarfe ne da ake amfani
da ƙima ko halaye wajen yin sa. Akan yi amfani da irin wannan yarfen ne don taɓa
ƙimar wani ɗan siyasa ko jam’iyyarsa ko kuma nuna wani mummunan hali tare da danganta
shi da shi.
4.10.3 Yarfe Na Tafiyar Da Shugabanci
Tafiyar da shugabanci
wani nauyi ne na al’umma wanda akan ɗora wa shugabanni domin gudanar da al’amuran
al’umma yadda ya dace bisa tsarin doka. Tsarin shugabanci na siyasa ya tanadi wasu
tsare-tsare na dokoki waɗanda ake amfani da su wajen warwarewa da kuma daidaita
abubuwan da suka shafi gudanar da al’amuran jama’a, ba tare da sanya son zuciya
ko kuma bai wa wani ɓangare fifiko a kan wani ba. Bin ire-iren waɗannan dokoki sau
da ƙafa galibi shi ne yake haifar da daidaito da adalci da kuma zaman lafiya. Sau
da dama duk wanda ya bijirewa irin wannan tsarin doka akan kalle shi a matsayin
mara gaskiya.
Duk da cewa bin waɗannan
dokokin tsarin mulki shi ne daidai kuma abin da ya dace, amma wasu kan yi amfani
da wannan don ganin wallen masu so su ɗabbaƙa su, har ma a wasu lokuta a zarge su
da rashin yin abin da ya dace tun da ba su bar kowa ya yi yadda ya ga dama ba. A
cikin siyasa akan yi wa ɗan siyasar da ya nuna cewa in ya hau mulki zai riƙe gaskiya
da adalci ba tare da nuna sani ko sabo ba yarfe da cewa zai wulaƙanta manya ko zai
ci mutuncin wasu. Alal misali, a lokacin da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
yake gudanar da yaƙin neman zaɓe ya yi ta bayyana cewa zai hana cin hanci da rashawa
da almundahana da dukiyar ƙasa, kuma duk wanda ya saci dukiyar ƙasa za a ƙwato,
sai aka riƙa yi masa yarfe cewa yana da niyyar cin mutuncin manya ne. Wannan ya
sa abokan hamayya suka dage don ganin bai kai labari ba. Irin wannan misali ne na
yarfe na tafiyar da shugabanci, domin ana nuna cewa ga hanyar da zai bi ne wajen
tafiyar da jama’a idan ya samu ya ɗare karagar mulki. Irin wannan misalin ya bayyana
a cikin littafin Da Bazarku. Ga misalin:
a cikin wannan jaridar tabbas na karanta wata hira
da aka yi da Farfesa Auta a kan gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar nan …Ya dai so
ya yi taɓargaza ne, tun da cewa ya yi shi fa har yanzu bai iya faiyace takamaiman
aikin da sarakuna suke yi ma talakawansu. Saboda haka wai shi yana ganin ya kamata
a faiyace wannan lamari a cikin sabon kundin da ake shirin tsarawa Lauya ya ce,
‘to a nemo mana ita daga nan zuwa jibi ko gata, mu kuwa za mu yi farfaganda mu birkita
abin da ya faɗa a ciki, shafa masa kashin kaji a idanun talakawa da sarakuna. Kai
kuwa tauraruwarka ta haskaka hasken da ba wanda ya isa ya dusashe ta.
(Surajo, 2006: 50-51).
A cikin wannan misalin an
nuna yadda ɗan takarar shugabancin ƙasa Farfesa Auta ya yi hira da ‘yan jarida ne
kan batun yi wa kundin tsarin mulki gyaran fuska, inda ya nuna cewa ya kamata a
fayyace aikin sarakuna a cikin kundin tsarin mulki. Wannan ya sa aka shirya nemo
jaridar a birkita zancen a shigar da abin da za a yi masa yarfe da shi don a shafa
masa kashin kaji. Idan aka duba wannan yarfe ne na tafiyar da shugabanci, domin
ya nuna idan ya samu dama zai yi gyara ga kundin tsarin mulki ta hanyar bayyana
irin aikin da ya kamata sarakuna su riƙa yi wa talakawa, amma sai aka nuna za a
shafa masa kashin kaji da wannan don al’umma su dawo daga rakiyarsa, kuma tauraron
abokin takararsa ya haskaka.
A jamhuriya ta huɗu zamanin mulkin Muhammadu
Buhari an yi amfani da wani nau’in yarfe da ya dusashe hasken ‘yan siyasa da dama.
A lokacin mulkin na Buhari musamman daga 2015 zuwa 2019, an ɗauka cewa duk wanda
ba ya tare da shi to kamar mutum ne da bai yi imani ba, domin ana ganin kauce wa
tsarin tafiyar Buhariyya kamar kafirci ne a siyasance. Wannan yana daga cikin dalilan
da suka sanya da yawan ‘yan siyasa suka bi ɗariƙar Buhariyya ba don suna so ba,
sai don su tsira da imaninsu a siyasance a fuskar mabiyansu. In ba haka ba za a
bi su da yarfe cewa suna hamayya da Buhari ko tafarkinsa. Dubi wani misali mai kama
da wannan a ƙasa:
Saboda mutane sun dauki Shugaba
Muhammadu Buhari tamkar mahadi da saba masa tamkar saba wa Allah ne, sai wasu ’yan
siyasa suke amfani da wannan dama wajen bata abokan siyasarsu don su lalata su.
Duk wanda yake son lalata maka siyasa sai ya ce kana fada da Buhari.
(Mustapha,
2015).
Akwai waɗanda
aka gurgunta tafiyar siyasarsu sanadin yarfen da aka yi masu da cewa suna faɗa da
Buhari, domin a lokacin mutane suna yi wa Shugaba Buharin kallon wani waliyyi a
siyasance wanda saɓa masa tamkar saɓa wa Allah ne, shi ya sa idan ana so a ɓata
siyasar wani sai a yi masa yarfe da cewa yana yi wa Buhari zagon ƙasa ko yana faɗa
da shi. Irin wannan ya karya alkadarin ‘yan siyasa da dama a zamaninsa.
Wani lokaci idan ana so a
yi wa ɗan siyasa yarfe sai a yi masa riga-malam-masallaci ta hanyar aikata wani
abu don nuna cewa shi ya kasa, ko kuma a yi kira gare shi ko jam’iyyarsa kan aikata
wani abin da ya dace ba don ana son a aikata ɗin ba, sai don al’umma su yarda cewa
jam’iyyar hamayya ba ta kan tsarin da ya dace ko ba ta bin doka da oda. Alal misali,
jaridar Leadership Hausa ta buga wani
labari wanda ta ce jam’iyyar hamayya ta PDP ta yi kira ga gwamnan jihar Kebbi da
ya miƙa ragamar mulki a hannun mataimakinsa bayan bayyana cewa gwamnan yana shirin
tafiya aikin Hajji. Ga misalin:
Mataimakin
gwamnan jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida, ya nesanta kansa da sanarwar da
jam’iyyar hamayya ta PDP ta fitar na neman a miƙa ragamar mulkin jihar biyo bayan
gwamnan jihar na shirin tafiya aikin Hajji 2024.
Tun da farko dai jam’iyyar
PDP ce ta fitar da sanarwa a ranar Laraba 5 ga watan Yuni a Birnin Kebbi inda ta
buƙaci Gwamnan Jihar da ya miƙa ragamar mulki ga mataimakinsa tun da yana shirin
tafiya Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana.
(Birnin-Kebbi, 2023).
Idan aka duba za a ga cewa a doka idan
gwamna zai yi tafiya irin wannan zai bar ragamar tafiyar da al’umma a hannun mataimakinsa
ne, amma sai aka jiyo jam’iyyar hamayya tana yin kira ga gwamnan jihar da ya yi
hakan. Wannan idan aka kula za a ga cewa yarfe ne na tafiyar da shugabanci, domin
yana nuna cewa kamar gwamnan ba ya bin tsarin doka na tafiyar da mulkin jihar ne,
kuma wannan zai iya yin tasiri ga al’umma wajen ganin wallen gwamnan. Hakan ne ya
sa mataimakin gwamnan jihar ya fito ya mayar masu da martani cewa, ko da yaushe
gwamnan jihar yana miƙa mulki ga mataimakin nasa ko da tafiyar yini ɗaya ya yi na
barin ya jihar. Dubi abin da ya ce:
A cewar Sanata Umar, “Mun yi mamakin
da’awar da ƴan hamayya ke yi na cewa a miƙa min ragamar mulki, domin ko da rana
ɗaya Gwamna Nasir bai taɓa hanani yin aiki ba.
(Birnin-Kebbi, 2023).
Idan aka duba za a fahimci cewa wannan
yarfe ne aka yi wa jam’iyya mai mulki ta hanyar nuna cewa ba su iya tafiyar da shugabanci
ba, ko kuma ba su bin doka a tsarin shugabancinsu.
Idan aka dubi waɗannan
bayanai da suka shafi yarfen siyasa, za a fahimci inda aka fito a tarihin ginuwar
siyasar jam’iyyu a ƙasar Hausa, wanda wannan shi ne ya share hanya zuwa sauran jamhuriyoyin
da aka samu bayan ta farko. Irin waɗannan sun ci gaba da faruwa a cikin siyasar
ƙasar Hausa, kuma an ci gaba da amfani da su a matsayin hanyoyin samun magoya baya
da kore wa abokan hamayyar siyasa mabiya.
4.11 Naɗewa
A wannan babi an kawo bayanai
kan abin ya shafi ginuwar siyasar jam’iyyu tun daga samuwar ta, da kuma irin yadda
jam’iyyun suka riƙa gwagwarmaya don neman mabiya ta kowane hali. Tun da farko an
kawo ma’anar siyasa da nau’o’inta, sannan an kawo ma’anar adabin siyasa da kuma
bayani kan wasu dalilan da ake ganin sun taimaka wajen haifar da ƙamfar ayyukan
adabin siyasa. Daga nan kuma sai aka ci gaba da nazarin ginuwar siyasar ƙasar Hausa,
inda kawo bayanai kan yadda aƙidu suka taka rawa wajen ginuwar siyasa a ƙasar Hausa,
inda aka nuna irin gudummawar da ɗariƙun Tijjaniyya da Ƙadiriyya suka bayar wajen
ci gaban siyasa da kuma ƙoƙarin neman mabiya. A cikin wannan babin an kawo yadda
‘yan siyasa suka riƙa amfani da matsayi da dangantakarsu da manyan Shehunnan ɗariƙu
da sauran aƙidu da kuma manyan ‘yan siyasa wajen samun karɓuwa a siyasance. Daga
nan kuma an dubi matsayin mata a siyasar ƙasar Hausa da irin gwagwarmayar da aka
yi wajen ba su ‘yancin neman ilimi da shiga siyasa a dama da su. A ƙarshe, babin
ya dubi yadda ‘yan hamayya suka riƙa shan matsi daga masu mulki da irin kai-ruwa-ranar
da aka riƙa yi tsakaninsu, wanda ya haifar da siyasar yarfe a tarihin ginuwar siyasar
ƙasar Hausa.
[1] Dubi
https://www.inecnigeria.org/wp-content//uploads/2019/02/ANNEURE-1.pdf
[2] Dubi https://govote.ng/political-parties/
[3] Waɗannan
wasannin duk ba a wallafa su ba kamar yadda Umar, A. U. (2022: 78-79) ya
bayyana.
[4] Tattaunawa da Dr.Kabir Sufi Sa’id, masanin harkokin siyasa kuma mai
sharhi a kan al’amuran yau da kullum, sannan Malami a kwalejin CAS da ke Kano,
ranar 27 ga watan Janairu, 2024 da misalin ƙarfe 5:20 na yamma, ta wayar tarho.
[5] Hira da Farfesa Atiku Ahmad Dunfawa a ofishinsa da ke sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya, jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato. Ranar 15/7/24 da misalin
ƙarfe 2:15.
[6] Dubi lamba ta 4
A duba Paden, J. (1973) Religion and
Political Culture in Kano. Shafi na 69 da shafi na 182.
[7] Dubi Paden (1973) Religion and Politcal Culture in Kano, shafi na 312.
[8] Dubi Alƙasum Abba (2000) The Politics of Principles in Nigeria: The
Example of NEPU. Shafi na 73.
[9] Hira da Dr. Isah Abdullahi Muhammad malami a sashen Koyar da Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato. Ranar 15/7/2024 a ofishinsa.
[10] Hira da Dr. Rabiu Bashir, ɗan siyasa kuma malami a ofishinsa da ke
sashen Koyar da Harsunan Nijejiya da
Kimiyyar Harshe, jami’ar Jihar Kaduna, ranar 16 ga watan Mayu, 2024.
[11] Dubi lamba ta 10.
[12] Dubi lamba ta 5
[13] Dubi Paden, J. (1973:122) Religion
And Political Culture in Kano.
Dubi Scott, P. H. G. (1952:2) A survey of Islam in Northern Nigeria.
[14] Dubi lamba ta 8
[15] Hira da Uwargidan Alhaji Ibrahim Lazuru, tsohon shugaban ƙaramar
hukumar Lere, jihar Kaduna a gidansa da ke Sabon Kawo Kaduna. Ranar 22 ga
Maris, 2021.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.