Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarihin Ginuwar Wasu Al’amuran Siyasar Jam’iyyu a Cikin Rubutun Zuben Hausa Daga 1950-2023 (Babi Na Uku)

Yusuf, J. (2025). Tarihin Ganuwar Wasu Al'amuran Siyasar Jam'iyyu a Cikin Rubutun Zuben Hausa Daga 1950-2023 (Ph.D. Thesis) Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo, Sokoto.

Tarihin Ginuwar Wasu Al’amuran Siyasar Jam’iyyu a Cikin Rubutun Zuben Hausa Daga 1950-2023

TARIHIN GINUWAR WASU AL’AMURAN SIYASAR JAM’IYYU A CIKIN RUBUTUN ZUBEN HAUSA DAGA 1950-2023

Na

Jibril Yusuf
Email: yusuf.jibril@kasu.edu.ng
Phone: +2347030399995

*** ***

BABI NA UKU

HANYOYI DA DABARUN GUDANAR DA BINCIKE

3.0 Shimfiɗa

A nan an kawo bayanai ne kan nau’in binciken da aka gudanar da kuma dabarun da aka bi wajen tattara bayanan da aka yi amfani da su, wajen gudanar da wannan binciken tun daga farko har ƙarshensa.

3.1 Hanyoyin Tattara Bayanai

Akwai hanyoyi ingantattu da aka bi domin tattara bayanan da wannan bincike ya dogara a kansu. Da farko an yi amfani da rubutattun ayyukan adabi da suka shafi rubutaccen zube, waɗanda aka samu, aka karanta su domin fito da hujjojin kamawa daga cikinsu, wurin fito da bayanai a kan ginuwar siyasar jam’iyyu a Arewacin Nijeriya.

3.2 Manyan Hanyoyin Tattara Bayanai

A nan an kawo manyan hanyoyin da aka yi amfani da su ne domin samun bayanan da aka yi amfani da su yayin gudanar da wannan binciken. Waɗannan hanyoyin su ne manya, domin a kansu binciken ya dogara.

3.2.1 Bibiyar Tarihi da Karance-Karance Kan Abubuwan da suka Shafi Zube.

Babbar hanyar da aka bi wajen tattaro bayanai domin gudanar da wannan aiki ita ce bibiyar tarihi cikin abin da ya shafi zube. Wannan ya haɗa da karance-karance da suka ƙunshi bayanan jam’iyyun siyasa a jaridu da mujallu da wasiƙu da jawaban siyasa da ƙagaggun labarai da sauran rubuce-rubuce na zube da suka shafi siyasa.

3.2.2 Hira Da Masana Da ‘Yan Siyasa

Hanya ta biyu da ta shafi wannan aiki ita ce yin hira da masana da manazarta da ‘yan siyasa da ‘yan mazan jiya waɗanda suka ga jiya da yau, domin samun ƙarin haske a kan yadda siyasa ta kasance a zamunnan baya da kuma irin sauye-sauyen da aka samu zuwa yau. Wannan ya ba da damar yin fashin baƙin hujjojin da binciken ya amfana da su domin guje wa yin kitso da ƙwarƙwata.

3.2.3 Tattaunawa da Marubuta Ayyukan Adabi

Kasancewar binciken ya gudana ne a kan ginuwar siyasar jam’iyyu a cikin tarihi daga cikin rubutaccen zuben Hausa, wannan ya sa aka fi mayar da hankali kan rubutattun bayanai da aka samu domin kafa hujja da su. Da yake ayyukan adabi suna cikin kaso na rubutaccen zube, don haka aka tuntuɓi wasu marubutan adabi domin samun ƙarin haske.

3.3 Ƙananan Hanyoyin Tattara Bayanai

Waɗannan su ma hanyoyi ne da aka yi amfani da su wajen gudanar da binciken, kuma sun taimaka wajen samun waɗansu bayanai da kuma adana su.

3.3.1 Ziyara Zuwa Ɗakunan Ajiyar Littattafai Domin Nazari

Bayan an ɗaura ɗamarar gudanar da wannan bincike, an ziyarci wasu muhimman wurare domin tattaro bayanai da suka taimaka tare da haska wa binciken hanya, domin kaiwa ga nasara. Daga cikinsu akwai tsangayoyin ilimi da ɗakunan karatu na jami’o’i kamar su: Jami’ar Bayero, Kano da Jami’ar Ahmadu Bello da take Zaria da Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da take Katsina. Haka kuma, an ziyarci ɗakunan karatu na Jami’ar Jihar Kaduna da kuma nan gida Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato da sauran cibiyoyin bincike irin su, Arewa House, Kaduna da Mambayya House, Kano da Gidan Tarihi na Waziri Junaidu, Sakkwato, domin samun ingantattun bayanai.

3.3.2 Amfani da Na’urorin Zamani

An samu waɗansu bayanai waɗanda hannu ba zai iya kaiwa kansu ba dangane da abin da ya shafi ginuwar siyasa, musamman siyasar jam’iyya a ƙasar Hausa. A nan an yi amfani da intanet domin samo bayanan. An kuma tattauna da wasu mutane ta wayar tarho domin samun ƙarin bayanai. Haka kuma, an yi amfani da kafofin sa da zumunta na intanet (Watsap da fesbuk da imel da dai sauransu) domin tattaunawa don samo bayanan da ba za a iya samun su a rubuce ba, ko kuma hannu ba zai iya samun damar kaiwa gare su ba.

3.4 Ra’in Bincike   

An ɗora wannan bincike a kan Ra’in Tarihanci (Historicism Theory), wanda masanin falsafa Karl Wilhelm Fredrich Schlegel (1772-1829) ya samar.

Masana da manazarta irin su, Blackburn (1994) da Barry (1995) da Habib (2008) da kuma Lawal (2018) sun ba da ma’anar tarihanci daidai fahimtarsu kamar haka:

A fahimtar Blackburn (1994: 167) ya bayyana ma’anar tarihanci da cewa, hanya ce ta fahimtar abubuwan zahiri na zamantakewa ta yadda za a iya bin diddigin faruwarsu da haɓakarsu, domin ba a iya gane abubuwan zahiri na rayuwa, kamar dimokuraɗiyya ko sassaucin ra’ayi ta la’akari da yadda suke a yanzu, ba tare da kallon tarihinsu ba. Masanin ya nuna cewa sanin tarihin abubuwan da suka faru a cikin al’umma musamman abin da ya shafi salon shugabanci kamar na dimokuraɗiyya ko wasu ra’ayoyi na rayuwa, ba a iya fahimtarsu ta hanyar duban halin da ake ciki a yanzu, dole sai an koma ga tarihi.

Shi kuwa Barry (1995: 170) a tasa fahimtar ya bayyana tarihanci da cewa, wata hanya ce ta ƙulla alaƙa tsakanin matanin adabi da wanda ba na matani ba, sau da yawa masu ɗauke da lokacin tarihi iri ɗaya. Ya nuna cewa, a cikin nazarin adabi ta fuskar tarihanci akan ƙulla alaƙa ne tsakanin matanin adabi wato rubutaccen adabi da wanda ba rubutacce ba. A nan idan aka lura za a ga cewa ta hanyar tarihanci ne ake tabbatar da wani abu da ya faru a cikin tarihi da zamanin da ya faru ta hanyar amfani da matanin adabi.

Habib (2008: 147) a tasa ma’anar ya bayar da wasu siffofi ne da za a iya tantance tarihanci da su, inda ya nuna cewa, dole ne a karanci adabi ta muhallin al’adarsa, da sauran muhallan tattaunawa waɗanda suka kama tun daga siyasa da addini da ƙawa ko kwalliya, da kuma tattalin arziƙi. A nan masanin yana nufin idan har za a yi nazarin adabi ta mahangar tarihanci to wajibi ne a dubi wasu mihimman abubuwa waɗanda akan tattauna a kansu kamar siyasa da addini da tattalin arziƙi da sauransu.

A wata ma’ana da Lawal (2018: 34) ya kawo, ya ce, tarihanci yana nufin duba yadda al’amuran tarihi suke a cikin matanin adabi ta hanyar la’akari da rubutaccen tarihi domin samun tabbas.

Ke nan, idan aka dubi waɗannan ma’anonin da aka kawo sama za a iya cewa tarihanci ba wani abu ba ne illa, nazarin wasu al’amuran da suka shafi rayuwa waɗanda suka danganci al’ada da addini da siyasa da tattalin arziƙi da sauran gwagwarmayar rayuwa a cikin matanin adabi ko ba na matani ba ta hanyar duba zuwa ga ingantaccen tarihi.

An fara amfani da ra’in tarihanci ne tun a ƙarni na 18. Ra’in yana bayani ne a kan yadda tarihi yake bayyana hanyoyi da tsarin rayuwar al’umma. Haka kuma, yana bayyana yadda wasu al’amurra suka faru a cikin wani zamani, da irin ci gaban da aka samu cikin al’adu na can dauri da kuma bayanin wurin zaman wata al’umma.

George Hegel (1770- 1831) yana ganin cewa tabbatuwar ‘yancin ɗan Adam shi ne maƙasudin adana tarihi, wanda kuma hakan kan samu ne kaɗai ta hanyar samar da tabbatacciyar ƙasa. A ganin wannan masani, sanin abin da ya faru a baya shi ne yake ba da damar rayuwa cikin ‘yanci da fita daga ƙangin bauta, domin yakan ba da damar fahimtar inda aka fito don a ƙara ɗaura ɗamara zuwa inda aka dosa.

Ƙarƙashin wannan ra’in an sake samun wani sabon tunani a wuraren shekarun 1980 da aka kira shi da suna “Sabon Tarihanci” wanda wani Ba’amirke matarki mai suna Stephen Greenblatt ya samar a shekara ta 1980. Greenblatt ya samar da Sabon Ra’in Tarihanci ne a sakamakon wasu nazarce-nazarce da ya gudanar, sai aka buƙaci ya tattara ayyukan ya nazarce su ta fuskar wani ra’i na musamman, sai ya samar da wannan ra’i da ya kira Sabon Tarihanci “New Historicism” a shekarar 1980 (Lawal ,2018:35).

Nazari ta mahangar ra’in tarihanci, shi ne dubi zuwa ga al’amura na tarihi a cikin adabi ta hanyar danganta wannan adabin zuwa ga tarihi na haƙiƙa daga masana tarihi, kuma wannan tarihin ya kasance tabbatace ta sigar rubutu.

Greenblatt (1980:47) ya tabbatar cewa, tarihanci yana ɗauke da manyan ginshiƙai ko tubala guda biyu da ake dubawa a wajen tarken adabi. Ga su kamar haka:

i. Matsayin Tarihi a Cikin Matani(Historisity of a Text)

ii. Sahihancin Tarihi a Rubutaccen Labari(Textuality of history)  

Ke nan, a duk lokacin da ake tarken adabi ta mahangar tarihanci, sai an dubi yadda adabin yake ɗauke da zantuttuka na tarihi a cikinsa, wato yadda aka gina zantuttukan tarihi da nuna su a bisa tarihin na gaskiya. Na biyun kuwa, shi ne a nazarci yadda labarai ko bayanai da aka rubuta suke ɗauke da tarihin da su marubutan suka sarrafa da irin sahihancin wannan tarihin daga tunanin marubutan, wato ya kasance tabbatacce ne ta sigar bayar da labari. A ƙarƙashin waɗannan manyan tubala guda biyu ne ake tarken adabi ta mahangar ra’in tarihanci kamar yadda Greenblatt (1980:47) ya bayyana.

Idan aka dubi ra’in da kyau za a fahimci cewa, da farko an kira shi tarihanci ne kawai, sai bayan tatttara ayyukan da Greenblatt ya yi ne ya sake nazarinsu bisa ra’in na tarihanci sai ya kira su “Sabon Tarihanci”.

Dangane da bambanci tsakanin Tarihanci da Sabon Tarihanci kuwa, Habib (2008: 147) ya ce, mafi yawan abubuwan da suka gabata a ƙarƙashin jagorancin “Sabon Tarihanci” ba wani sabon abu ba ne, sai dai za a iya cewa yana wakiltar salon nazari da bunƙasar tarihanci na gargajiya da ya gabata ne. Idan aka lura za a fahimci cewa, Sabon Tarihanci ba wani sabon abu ne na daban ba, sai dai za a iya cewa Sabon Tarihanci ci gaban Tsohon Tarihanci ne kawai, domin duk manufarsu ɗaya ce a fagen nazari.

Mabiya wannan mazahaba sun haɗa da: Louiz Montrose da Michael de Montaigne da G. B. Vico da George Hegel.

Wasu daga cikin nazarce-nazarce na adabin Hausa da aka gudanar ta mahangar ra’in tarihanci sun haɗa da: Usman (2016) da Bunza (2018) da Yusuf (2018) da Lawal (2018) da Bunza (2018) da kuma Ali (2020).

Wannan ne ya sa aka ga dacewar zaɓen wannan ra’in aka kuma ɗora shi a kan aikin, kasancewar yana bayani kan abin da ya shafi tarihi a cikin adabi, kamar yadda aikin ya dubi tarihin ginuwar siyasar jam’iyya a Arewacin Nijeriya, wanda aka fito da shi daga cikin rubutaccen zube na Hausa.

3.5 Naɗewa

A cikin wannan babi, an tattauna hanyoyin gudanar da bincike ne, wato dabarun da aka yi amfani da su wajen tattaro bayanan da aka yi amfani da su domin tabbatar da kammaluwar binciken. Tun da farko an yi shimfiɗar inda babin ya dosa. Daga ƙarshe an kawo bayanin a kan ra’in da aka ɗora a kan binciken, sannan aka kawo naɗewa.

Post a Comment

0 Comments