Yusuf, J. (2025). Tarihin Ganuwar Wasu Al'amuran Siyasar Jam'iyyu a Cikin Rubutun Zuben Hausa Daga 1950-2023 (Ph.D. Thesis) Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo, Sokoto.
TARIHIN GINUWAR WASU AL’AMURAN SIYASAR JAM’IYYU A CIKIN RUBUTUN ZUBEN HAUSA DAGA 1950-2023
Na
Jibril Yusuf
Email: yusuf.jibril@kasu.edu.ng
Phone: +2347030399995
*** ***
BABI NA BIYU
BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA
2.0 Shimfiɗa
Wannan ɓangaren ya ƙunshi bitar
ayyukan da suka gabata ne masu dangantaka da wannan bincike. An yi bitar ne domin
a fahimci ina aka faro daga cikin ayyukan masana da manazarta, wanda shi ne ya ba
da damar sanin inda aka fito da inda ake domin sanin inda aka dosa a cikin binciken
da aka gudanar.
2.1 Kundayen Bincike
An yi bitar kundayen
digiri na uku da na biyu da kuma na ɗaya. Ire-iren waɗannan
kundayen digiri suna da muhimmanci ga irin wannan bincike. Ganin irin wannan muhimmancin
ne ya sa aka yi bitar wasu daga cikinsu domin samun ƙarin haske ga wannan bincike.
2.1.1 Kundayen Digiri Na
Uku
An gabatar da bitar kundayen
digiri na uku da suke da alaƙa da wannan bincike kamar haka:
Olafioye
(1974) ya yi nazarin jigon siyasa ne a rubutattun waƙoƙin siyasa na yankin Afirka.
Tun da farko an kawo bayani kan al’adun Afirka da abubuwan da suka ƙunsa a taƙaice.
Daga nan, sai aka tsunduma cikin aikin inda aka riƙa kawo baitocin da ke ɗauke da
jigon siyasa ana yin bayanin abubuwan da suka ƙunsa. Haka kuma an kawo bayanin salo
a cikin rubutattun waƙoƙin siyasa waɗanda aka nuna cewa su ne ke fito da jigon fili
domin a gan shi. Aikin Olafioye yana da dangantaka da wannan, saboda dukkansu sha’anin
siyasa ne suka duba. Bambancinsu shi ne, aikinsa ya shafi waƙoƙin siyasa ne, shi
kuma wannan ya shafi rubutaccen zuben Hausa ne kaɗai.
Birniwa, (1987) ya yi nazarin waƙoƙin siyasa na jumhuriya ta farko da na jumhuriya ta biyu,
inda ya nazarci waƙoƙin da aka gina kan jam’iyyun NPC/NPN da kuma NEPU/PRP. Binciken
ya yi ƙoƙarin gano asalin siyasa a ƙasar Hausa. Haka kuma, ya dubi waɗannan jam’iyyu
masu hamayya da juna ta fuskar waƙoƙin da aka yi musu a jumhuriya ta ɗaya da ta
biyu. Birniwa ya yi ƙoƙarin fito da jigogi da salailan waɗansu daga cikin waƙoƙin.
Wannan aiki ya taimaka ƙwarai da gaske, domin kuwa binciken da aka sanya gaba yana
da alaƙa da kundin, kasancewar a kan rubutaccen zube ne da ya shafi siyasa aka gudanar
da shi. Sun bambanta kasancewar kundin Birniwa an gudanar da shi ne a kan nazarin
riƙau da sauyi a cikin waƙoƙin siyasar jumhuriya ta farko da kuma jumhuriya ta biyu.
Shi kuwa wannan bincike da aka gudanar alƙiblarsa ita ce duba ginuwar siyasa ne
a cikin rubutaccen zuben Hausa.
Sani
(1988) ya kawo bayanai a kan yadda siyasa takan zama wata hanya ta samar da sababbin
kalmomi a cikin harshen Hausa. A cikin aikin nasa ya dubi dangantakar harshen Hausa
ne da siyasa, inda ya kawo bayanai da suka shafi ire-iren-kalmomi da aka samar daga
cikin zuɓe na siyasa da kuma waƙoƙin siyasa, da kalmomin da aka samu a kakar zaɓe
da kuma waɗanda ba lokacin zaɓe ba, sannan ya dubi kalmomin da suka samu a lokacin
kamfe da kuma waɗanda aka samar da su a zaurukan majalisun ƙasa. Ya yi nazarin nasa
ne ta fuskar duban irin salailan da ake amfani da su wajen isar da saƙonnin siyasa.
Dangantakar binciken nasa da wannan shi ne dukkansu sun shafi siyasar jam’iyya ne,
sai da sun bambanta kasancewar nasa ya karkata a kan nazarin harshen siyasa ne,
wannan kuwa ya shafi binciken tarihin ginuwar siyasar Arewacin Nijeriya ne a cikin
rubutaccen zuben Hausa.
Shi
kuwa Sa’id (2002) ya yi bayani ne kan rubutattun waƙoƙin Hausa, inda ya fara da
ɗaurayar waƙoƙin ƙarni na sha tara, da na ƙarni na ashirin, har ma ya kawo tarihin
samuwarsu da kuma gudummawar Ajami da Boko wajen rubuta waƙoƙin. Aikin ya yi bayanin
jigogin waƙoƙin da aka rubuta a jihohin Sakkwato da Kabi da Zamfara waɗanda suka
haɗa da: addini da tarihi da mulki da siyasa da ilimi da sauransu. Wannan kundi
ya taimaka wa wannan aikin da aka gudanar, domin ya taɓo wani ɓangare da wannan
aikin ya kalla wato siyasa da kuma mulki. Bambancin aikinsa da wannan shi ne, aikin
nasa ya dubi rubutattun waƙoƙi ne na ƙarni na sha tara da na ashirin, a wannan kuwa,
an yi ƙoƙarin fito da ginuwar siyasar jam’iyya da cigaban jama’a ne a ƙasar Hausa
daga cikin rubutaccen zuben Hausa.
Idris
(2016) ya yi nazari ne a kan wani fage da ba a saba jin ɗuriyarsa a fagen nazari
ba. Shi ya karkata akalarsa ya yi nazarin yadda mawaƙa ke amfani da salon bijirewa
wajen nuna ƙin wani abu ko juya masa baya. Ya yi bayanin bijirewa a waƙoƙin siyasa
na farko inda ya kamo aikin daga shekarar 1903 zuwa 1991, ya riƙa kafa hujja da
waƙoƙin da aka samar bayan jihadi har zuwa jumhuriya ta uku. Sannan kuma sai ya
yi nazarin bijirewa a waƙoƙin dimokuraɗiyya daga 1991 zuwa 2015, ya kuma riƙa kafa
hujjoji daga waƙoƙin siyasa. Wannan aikin ya taimaka wa wannan binciken, domin ya
shafi bayanai masu muhimmanci game da tarihin samuwar siyasar zamani da dimokuraɗiyya
da kafuwar jam’iyyu da sauransu. Abin da ya bambanta wannan aiki da wanda aka gudanar
shi ne, shi ya yi nazarin bijirewa ne a cikin waƙoƙin siyasa, a wannan binciken
kuwa an fito da ginuwar siyasar jam’iyya da cigaban al’umma ne a cikin rubutaccen
zuben Hausa.
Gandu
(2016) ya yi nazari ne a kan harshen siyasa, inda ya nazarci jigo da salo a cikinsu.
Aikin nasa ya dubi wasu salailai da yadda ake amfani da su a siyasar demokuraɗiyya
a jamhuriya ta huɗu a Arewacin Nijeriya. Ya yi wannan nazari nasa ne ta hanyar kafa
hujoji daga jawaban siyasa da allunan tallar ‘yan siyasa da saƙonnin da suke jikin
hotunan tallar ‘yan siyasa da kuma muryar tallar ‘yan siyasa a kafafen watsa labarai.
Dangantakar aikinsa da wannan binciken shi ne, aikin nasa ya shafi siyasar jam’iyyu
ne a jamhuriya ta huɗu, daga shekarar 1998 zuwa 2010, kuma ya kafa hujjoji daga
jawaban siyasa da sauran wasu al’amura da suka shafi siyasar jam’iyya, kamar yadda
wannan binciken shi ma aka kafa hujjoji daga jawaban siyasa. Bambancin aikinsa da
wannan shi ne, aikinsa ya karkata ne a kan harshen siyasa, kuma abubuwan da aka
kafa hujja da su na baka ne ba rubutattu ba. Wannan bincike kuwa ya shafi tarihin
ginuwar siyasa ne a cikin rubutattaccen zuben Hausa.
Muhammad
(2017) ya kawo bayani ne kan siyasar cikin gida a cikin jam’iyyar PDP, inda ya kawo
bayani kan abin da ya shafi zaɓen fid da gwani na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar
a jihar Kaduna daga shekarar 1999 zuwa 2015. A cikin aikin nasa ya kawo abubuwan
da suka haifar da matsalolin da jam’iyyar ta yi fama da su a wurin gudanar da zaɓuɓɓukan
fid da ɗan takara a matakin gwamna. A ciki an kawo matsaloli kamar su amfani da
kuɗi da ƙabilanci da ɓangaranci da siyasar ubangida da ƙarfin mulki da dai sauransu.
Dangantakar wannan aiki da wanda aka gudanar shi ne, ya haska wa wannan binciken
irin fasalolin da siyasa take ƙunshe da su wanda binciken zai kalla kamar su, amfani
da kuɗi a cikin siyasa da siyasar uban gida da dai sauran su, kamar yadda aka kawo
a cikin aikin. Bambancin aikin da wanda aka gudanar shi ne, shi ya shafi bayani
ne kan siyasar cikin gida na wata jam’iyya da irin matsalolin da akan fuskanta musamman
lokacin gudanar da zaɓen fid da gwani na ɗan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, wannan
aiki kuwa ya shafi nazarin wasu ɓangarori ne a cikin tarihin siyasa daga ciki rubutaccen
zuben Hausa na siyasa.
Adamu
(2019) ya nazarin kwatanci ne tsakanin waƙoƙin siyasar jumhuriya ta uku da na jumhuriya
ta huɗu a Nijeriya. A cikin aikin nasa ya kawo bayanai kan siyasa, sannan ya kawo ire-iren siyasa ya yi bayaninsu. Haka kuma ya kawo bayani kan kafuwar jumhuriya a Nijeriya tun daga ta ɗaya zuwa ta huɗu, sannan daga bisani ya tsunduma cikin nazarin inda ya
kwatanta waƙoƙin jamhuriyoyin guda biyu ta fuskar jigo da tsari da kuma salo. Dangantakar
aikinsa da wannan binciken ita ce, dukkansu sun shafi siyasar jam’iyya ne, sai dai
inda suka bambanta shi ne, nasa ya shafi nazarin kwatanci ne a yayin da wannan binciken
ya dubi ginuwar siyasar jam’iyya da cigaban al’umma a cikin rubutaccen zuben Hausa.
Aikin
Adamu (2021) an yi nazarin dabarun jawo hankali ne a waƙoƙin siyasa na jihohin Kano
da Katsina da Zamfara, a cikin aikin an kawo wasu salailai ne da mawaƙa suke amfani
da su a cikin waƙoƙinsu domin jawo hankalin masu sauraren su. A cikin aikin an kawo
bayanai da dama da suka shafi siyasa da waƙoƙin siyasa. Bambancin aikin da wannan
shi ne, yayin da wannan aiki ya shafi nazarin salo a waƙoƙin siyasa, wanda aka gudanar
kuma ya ƙunshi fito da wasu gaɓoɓin tarihin siyasar jam’iyya a cikin rubutaccen
zuben Hausa.
2.1.2 Kundayen Digiri Na Biyu
Baya ga kundayen digiri na uku, akwai kuma kundayen
digiri na biyu waɗanda aka yi bitar su domin fito da dangantaka da kuma bambancinsu
da wannan bincike. Ga su kamar haka:
Omar
(1984) wannan aikin ya shafi salo da sigogin waƙoƙin Malam Mu’azu Haɗeja ne. A cikin
aikin an nuna cewa wasu daga cikin waƙoƙin musamman waɗanda da suka shafi siyasa
da mawaƙin ya rubuta sun ɓace. Duk da haka dai, waɗanda aka samu a cikin binciken sun taimaka ƙwarai wajen
aiwatar da wannan binciken da aka sanya a gaba. Dangantakar aikinsa da wannan shi
ne, kundin ya shafi rubutattun waƙoƙi ne kuma cikinsu har da na siyasa waɗanda suka
ƙara haske ga wannan binciken da aka gudanar, sai dai a wannan ba nazarin waƙoƙi
ne aka yi ba, an yi laluben tarihin ginuwar siyasar jam’iyyu ne a cikin rubutaccen zuben Hausa.
Mashi
(1986) ya yi aiki a kan waƙoƙin baka na siyasa, inda ya kawo dalilansu da sababinsu
ga rayuwar Hausawa, inda a cikin aikin ya yi bayani kan hikimomin da ke ƙunshe cikin
waƙoƙin baka na siyasa. Tun a farko ya kawo ma’anar waƙa da ma’anar siyasa ta fuskoki
da dama yadda za a sami damar fahimtar dalilin waƙoƙin da aka rera wa siyasar. Haka
kuma ya kawo waƙoƙin siyasar gargajiya da misalai daga waƙoƙin da aka yi wa masu
mulki da ma shi kansa mulkin. Mashi ya kawo tarihin siyasa a ƙasar Hausa, da bayanin
yadda aka kafa jam’iyyun siyasa da irin manufofinsu. Duk da cewa wannan aikin an
gudanar da shi ne a kan ginuwar siyasa cikin tarihi da kuma dangantakarsu da cigaban
ƙasa, amma kuma kundin Mashi ya taimaka ƙwarai duk da kasancewarsa an gudanar da
shi kan waƙoƙin baka, domin dai tubalin da aka aza binciken a kai (siyasa) ya danganta
aikinsa da wannan.
Ɗiso
(1997) ya gudanar da nasa aikin ne domin binciko irin tasirin da zambo da yabo suke
da shi a cikin rubutattun waƙoƙin siyasar jam’iyya. Ya kawo tarihin siyasa da ire-irenta,
da kuma tarihin gwagwarmayar siyasar jam’iyyar da aka yi a Nijeriya tun daga zamanin
mulkin mallaka. Haka kuma ya kawo bayani kan siyasar jam’iyya, inda ya kawo tarihinta
da tsokaci kan wasu abubuwa da rubutattun waƙoƙin siyasar jam’iyya suka ƙunsa. Bugu
da ƙari, an kawo bayanai kan zambo da yabo a cikin waƙoƙin Hausa na jam’iyyun siyasa.
Wannan kundi yana da dangantaka da wannan binciken, domin kuwa kamar yadda ya shafi
waƙoƙin siyasar jam’iyya, sannan kuma ya taɓo wani ɓangare wannan aikin ya ƙunsa,
wato dangantaka tsakanin masu mulki da ‘yan hamayya, inda a nan ne ake samun zambo
da kuma yadda mabiya wata jam’iyya sukan riƙa yabonta da tallarta. Bambancinsu shi
ne, shi a wannan daga cikin rubutaccen zube ne aka fito da wasu abubuwa da suka
shafi ginuwar siyasar jam’iyya a Arewacin Nijeriya, a yayin da aikin Ɗiso ya ta’allaƙa
a kan tasirin yabo da zambo a cikin waƙoƙin siyasar jam’iyya.
Funtua (2003) ya kawo tarihin
samuwar siyasa a Nijeriya da kuma mawaƙan siyasa na baka da kuma marubuta waƙoƙin
siyasa. Haka kuma ya kawo jigogin waƙoƙin siyasa daban-daban daga mawaƙa mabambanta.
Wannan aiki ya taimaka gaya wajen gudanar da wannan binciken. Bambancinsu shi ne,
wannan ya shafi nazarin guniwar siyasar jam’iyya ne daga cikin rubutaccen zube na
Hausa. Shi kuwa nasa aikin ya dubi sigogin waƙoƙin siyasar jamhuriya ta uku ne kawai.
Aikin
Ɗangulbi (2003) ya yi bayanin gudummuwar marubuta waƙoƙin siyasa ga kafa dimokuraɗiyya
a jumhuriya ta huɗu ne. A cikin aikin an kawo tarihin kafuwar siyasa a Nijeriya,
yadda waƙoƙin siyasa suka samu da kuma irin saƙonnin da suke ɗauke da su. Haka kuma
an yi sharhi kan wasu waƙoƙin jam’iyyun PDP da ANPP ta hanyar fito da zubi da tsari
da kuma salon sarrafa harshe a cikin waƙoƙin. Wannan kundin ya taimaka wajen samun
nasarar wannan binciken, domin shi ma ya dubi ginuwar siyasa ne a cikin tarihi daga
rubutaccen zube na Hausa.
Imam
(2007) ya yi nazari ne kan yadda kyakkyawan shugabanci yake haifar da cigaban ƙasa,
inda ya ɗauki zamanin mulkin Janar Buhari na soja daga shekarar 1983 zuwa 1985 ya
yi nazari a kansa. Aikin nasa ya dubi wasu abubuwa muhimmai waɗanda kan sa a samu
kyakkyawan shugabanci. Abubuwan sun haɗa da gaskiya da riƙon amana da adalci da
sauransu. Ya nuna cewa samun waɗannan abubuwan a cikin shugabanci ne yake kawo ci
gaban ƙasa. Aikin ya yi waiwayen tsarin shugabanci tun daga samun ‘yancin kai har
zuwa zamanin mulkin Janar Buhari ƙarƙashin mulkin soja. Alaƙar aikinsa da wannan
shi ne, ya taɓo waɗansu abubuwa wanɗanda samun su ne yake haifar da kyakkyawar shugabanci
wanda shi ne yake haifar da cigaban ƙasa. Haka kuma, a cikin wannan binciken an
kawo irin fasalin da suka fito a cikin rubutaccen zuben Hausa.
Ɗan’illela
(2010) ya yi bincike a kan rubutattun waƙoƙin siyasa na jihohin Sakkwato da Kebbi
da kuma Zamfara. Tun da farko ya fara da kawo tarihin jihohin ne, sannan ya kawo
tarihin samuwar siyasar jam’iyyu inda ya ratsa zangunan siyasa tun daga jumhuriya
ta ɗaya har zuwa ta huɗu, ya kuma kawo bayanai a kan bunƙasar siyasar jam’iyyu a
waɗannan jihohi. Daga ƙarshe ya kawo waƙoƙin jam’iyyu guda biyar, wato: APP/ANPP
da PDP da DPP da AC da kuma PRP. Sannan ya yi sharhin wasu daga cikinsu ta la’akari
da zubi da tsari da jigo da kuma salonsu. Kundin yana da alaƙa da wannan binciken,
musamman kasancewarsa kan rubutattun waƙoƙin siyasa, kuma wannan binciken ma ya
shafi siyasar Arewacin Nijeriya ne, wanda aka yi nazarin ginuwarta daga cikin rubutaccen
zuben Hausa. Bambancinsu shi ne wannan ya shafi ginuwar siyasa ne a cikin tarihi
daga rubutaccen zuben Hausa, shi kuwa nasa nazarin waƙoƙin ne aka yi.
Abdullahi
(2011) a aikinsa ya yi nazarin yadda ‘yan siyasa suke amfani da ‘yan bangar siyasa
wajen haifar da rikice-rikice bayan zaɓe, inda ya yi wa aikin nasa kadada da masarautar
Zuru da ke jihar Kebbi ta hanyar kafa hujja da zaɓuɓɓukan da aka yi a shekarun 2007
da kuma 2011. Nazarin nasa ya fito da yadda akan sami ɓarkewar rigingimu lokacin
zaɓe da kuma bayan sanar da zaɓe, da kuma abubuwan da ke haifar da su. Haka kuma
a cikin aikin ya kawo bayanai kan zaɓuɓɓukan da aka gudanar a matakin ƙasa tun daga
shekarar 1959 har zuwa 2003. Daga bisani ya yi nazarin yadda waɗannan rikice-rikice
suke faruwa da yadda ‘yan siyasar ke ɗaukar nauyin ‘yan bangar siyasa wajen aikata
ayyukan ta’addanci. Alaƙar wannan aiki da wannan binciken ba a ɓoye take ba, kasancewar
kusan babu wani zaɓe da aka gudanar wanda babu irin waɗannan ayyukan ta’addanci
na ‘yan bangar siyasa, kuma wannan binciken ya ɗan taɓo wani abu da ya shafi bangar
siyasa. Bambancin da za a iya gani tsakanin aikinsa da wannan shi ne, a wannan binciken
an fito da bangar siyasar ne a matsayin wani abu da ya riƙa faruwa cikin tarihin
siyasar jam’iyya a Arewacin Nijeriya, inda za a kafa hujja da rubutaccen zuben Hausa.
Abdullahi (2011) a cikin aikinsa ya yi nazarin
wasu waƙoƙin hamayyar siyasa ne na Haruna Aliyu Ningi, inda a cikin nazarin ya dubi
salo da jigo da zubi da tsarin waƙoƙin. Wannan aiki nasa yana da alaƙa da wanda
za a gudanar kasancewar ya shafi waƙoƙin siyasar jam’iyya waɗanda suke nuna hamayyar
siyasa. Bambancin aikinsa da wannan shi ne, shi ya ɗauki wasu daga cikin waƙoƙin
mawaƙi guda ne ya yi nazarinsu, saɓanin wannan aiki da aka gudanar da ya shafi rubutaccen
zuben Hausa, domin fito da ginuwar siyasar jam’iyya da cigaban al’umma a Arewacin
Nijeriya.
Adamu
(2012) ya yi nazarin salo da sarrafa harshe ne a waƙoƙin siyasa, inda aikin ya fi
mayar da hankali kan waƙoƙin jam’iyyun ANPP da PDP a jihohin Kano da Jigawa. Aikin
ya dubi irin salailan da mawaƙan suke amfani da su ne wajen isar da saƙonsu ga al’umma.
Dangantakar wannan aiki da wanda za a gudanar shi ne, ya shafi siyasa ne a Arewacin
Nijeriya kamar yadda wannan da aka yi ma ya shafi siyasar Arewacin Nijeriya. Bambancin
aikinsa da wannan aikin shi ne, nasa ya shafi nazarin salon sarrafa harshe ne a
waƙoƙin siyasa, wannan kuwa ya shafi nazarin ginuwar siyasa da cigaban al’umma ne
a cikin tarihi daga rubutaccen zuben Hausa.
Sani
(2012) a nasa binciken ya yi ƙoƙarin yin nazarin waƙoƙin siyasa ne da Malam Hassan
Nakutama ya rubuta, inda tun a farko ya kawo tarihin mawaƙin. Sannan ya yi nazarin
salo da jigo a waƙoƙin nasa. Wannan aikin ya taimaka wa aikin da aka sanya a gaba
ganin cewa dukkansu sun shafi bincike ne a kan adabin siyasa. Bambancin shi ne, a wannan
binciken an yi ƙoƙarin fito da wasu gaɓoɓin tarihi ne a siyasar jam’iyya daga cikin rubutaccen zuben Hausa.
Yahaya
(2012) a nasa kundin ya yi bincike ne kan waƙoƙin da aka yi wa baƙin abubuwa da
suka zo ƙasar Hausa waɗanda a da can ba a san da su ba kamar siyasar jam’iyyu. A
cikin aikin nasa ya kawo bayani kan siyasar jam’iyyu da waƙoƙin da aka yi wa jam’iyyu.
Aikin nasa ya taimaka wa wannan kasancewar ya kawo bayanai da misalai daga waƙoƙin
siyasa, sannan ya kawo tarihin siyasar zamani da kafuwar jam’iyyu a taƙaice, wanda
kuma shi kansa wannan bincike da aka gudanar ya ginu ne kan siyasa da cigaban al’umma,
inda aka dubi tarihi da ginuwar siyasar jam’iyya da kuma cigaban da aka samu a ƙasar
Hausa, wanda aka fito da shi daga cikin rubutaccen zuben Hausa. Abin da ya bambanta
wannan binciken da nasa shi ne, shi ya yi nazarin waƙoƙi ne da aka yi wa baƙin abubuwa
irin su siyasar jam’iyya da karen mota da sauransu. A wannan aiki kuwa an fito da
ginuwar siyasa da cigaban al’umma ne a ƙasar Hausa daga cikin rubutaccen zuben Hausa.
Adamu
(2014) a bincikensa ya yi nazari ne kan salon tallata ‘yan takara a jumhuriya ta
huɗu. A cikin aikin ya kawo bayani kan siyasa da waƙoƙin siyasa. Haka kuma ya kawo
taƙaitaccen tarihin samuwar siyasa a Nijeriya inda a nan ne ya kawo bayanai kan
zamunnan siyasa tun daga na ɗaya har zuwa na huɗu. Haka kuma ya kawo sharhin wasu
waƙoƙin siyasar jumhuriya ta huɗu, daga bisani kuma ya yi nazarin salo da tsarin
waƙoƙin. Dangantakar aikinsa da wannan shi ne, kasancewar ya shafi siyasa ne, kuma
wanda aka gudanar ma ya shafi siyasa ne. Kuma aikin ya kawo bayanai kan ginuwar
siyasa wanda ya haska wa wannan bincike hanya ƙwarai. Bambancin aikinsa da wannan
shi ne, nasa ya shafi nazarin waƙoƙin ne, wannan kuwa ya kalli ginuwar siyasar jam’iyyu
a cikin rubutaccen zuben Hausa.
Sani
(2018) ya yi nazari ne kan wasu daga cikin waƙoƙin Dauda Kahutu Rarara, inda a cikin
aikin ya yi ƙoƙarin fito da salailan da mawaƙin kan yi amfani da su a cikin waƙoƙinsa.
A cikin aikin nasa ya fito da nau’o’in salo da wasu dabaru musamman na kwatance
da maganganun azanci waɗanda mawaƙin ke amfani da su a cikin waƙoƙinsa. Dangantakar
wannan aiki nasa da wannan shi ne, kasancewar mawaƙin da aka yi wannan bincike kan
waƙoƙinsa mawaƙin siyasa ne, kuma waƙoƙin da aka ba da misalai da su a cikin aikin
waƙoƙin siyasa ne. Wannan aikin kuwa ya shafi fito da wasu batutuwa na tarihin siyasar
jam’iyyu ne a cikin rubutaccen zuben Hausa ne. Bambancin su shi ne, shi ya kalli
nazarin salo ne a cikin waƙoƙin siyasa, shi kuwa wannan ya kalli ginuwar siyasar
jam’iyya a cikin rubutaccen zube na Hausa ne.
Yusuf
(2018) ya yi ƙoƙarin fito da tarihin jam’iyyar PDP ne a cikin waƙoƙin siyasa, inda
ya dubi jam’iyar PDP tun daga kafuwarta har zuwa faɗuwarta a zaɓen shekarar 2015.
A cikin aikin nasa ya riƙa kawo bayanai da suka shafi tarihin jam’iyyar inda ya
riƙa kafa hujjoji daga baitocin wasu waƙoƙin siyasa, tun daga farkon aikin nasa
har zuwa ƙarshe. Alaƙar wannan aiki da wanda za a gudanar ta kusa ce, domin kuwa
aikin ya shafi tarihin jam’iyyar siyasa ce a cikin adabin Hausa, kamar yadda a wannan
ma aikin ya shafi tarihin ginuwar siyasar jam’iyya ne a cikin rubutaccen zube na
Hausa. Inda suka bambanta shi ne, a wannan an dubi tarihin siyasar jam’iyyar ce
baki ɗayanta a cikin rubutaccen zuben Hausa.
Lawal (2018) a nasa binciken ya dubi yadda al’amuran tarihi ne suke ƙunshe
cikin wasu zaɓaɓɓun wasannin kwaikwayon Prietze wato Turbar Ƙudus da Turbar Tarabulus
da Tarihin Rabe. Binciken ya yi waiwaye
zuwa ga tarihin hulɗar kasuwanci a tsakanin Hausawa da Larabawa da tarihin Masallacin
Qudus da kuma tarihin rayuwar Rabeh (Fadl Allah). An yi wannan nazarin ne domin
fito da tarihin da ke cikin wasannin wanda ya faru a zahiri ta hanyar amfani da
ra’in tarihanci. Dangantakar wannan aikin nasa da wannan shi ne, aikinsa ya shafi
binciken tarihi a cikin wasannin kwaikwayon Hausa ne bisa ra’in tarihanci, kamar
yadda wannan aikin shi ma aka gudanar da binciken tarihin siyasar jam’iyyu Arewacin
Nijeriya bisa ra’in tarihanci. Inda suka bambanta shi ne, shi wannan binciken ya
shafi binciken tarihi da ginuwar siyasa ne daga cikin rubutattun ayyukan adabin
Hausa na zube.
Aikin
Imam (2019) ya shafi nazarin rayuwar Malam Gambo Hawaja Jos ne da waƙoƙinsa, inda
a cikin aikin nasa ya kawo tarihin mawaƙin a matsayin fitacce kuma shahararren mawaƙin
siyasa a jamhuriya ta ɗaya. Ya yi nazarinsa ne ta hanyar duba zubi da tsari da salo
da kuma jigon waƙoƙinsa. Dangantakar aikinsa da wannan shi ne, ya shafi siyasar
jam’iyyu ne, kuma shi ma wannan aiki a kan siyasar jam’iyyu aka gudanar da shi.
Bambancin aikinsa da wannan shi ne, ya karkata a kan rayuwar mawaƙi guda ne ya kuma
yi nazarin waƙoƙinsa. Wannan binciken kuwa zai leƙa rubutaccen zuben Hausa ne domin
fito da ginuwar siyasar jam’iyyu a Arewacin Nijeriya.
Saminu (2020) ya gudanar da nasa binciken ne a
kan waƙoƙin Kabiru Yahaya Kilasik inda ya yi nazarin turke da tubalan zamantakewa
a cikin waƙoƙin nasa. A cikin aikin nasa ya kawo bayanai filla-filla kan turakun
da mawaƙin yake gina waƙoƙinsa a kai a cikinsu har da turken siyasa, wanda ya yi
bayaninsa tare da kawo hujjoji daga wasu baitoci daga waƙoƙinsa. Dangantakar wannan
aiki da wanda aka gudanar shi ne, aikin ya shafi rayuwar mawaƙin siyasa ne da waƙoƙinsa
inda a ciki har an yi nazarin turken siyasa. Bambancin aikinsa da wannan shi ne,
an yi nazarin turke da tubalan zamantakewa a waƙoƙin wani mawaƙi guda, a wannan
kuma an yi nazarin ginuwar siyasar jam’iyya daga cikin rubutaccen zuben Hausa.
Bawa
(2021) ya yi nazarin yadda siyasa ta kasance tamkar jini da tsoka a rayuwar al’umma
daga cikin rubutattun labaran Hausa. Aikin nasa ya dubi yadda masu mulki suke ƙoƙarin
ɗorewa a kan mulki ta kowane hali ba tare da la’akari da halin da talakawa suke
ciki ba. A cikin aikin ya yi ƙoƙarin nazarin yadda talakawa suke ƙoƙarin ƙwato wa
kansu ‘yanci da zaluncin shugabanni. Haka kuma ya fito da muhimmancin mata a cikin
siyasa kamar yadda adibai suka nuna a cikin ayyukansu. Ya yi nazarin ne ta hanyar
fito da fasalce-fasalcen da gwagwarmayar neman ‘yanci kan ɗauka a cikin rubutattun
labaran Hausa. Dangantakar aikinsa da wannan shi ne, aikinsa ya shafi nazarin siyasa,
a cikin rubutattun ƙagaggun labaran Hausa. Bambancin aikin da wannan shi ne, wannan
ya dubi ginuwar siyasa da cigaban ƙasa ne a cikin tarihi, inda aka dubi ginuwar
siyasa da abubuwan da kan haifar da cigaban al’umma ko akasin haka a siyasance daga
cikin rubutaccen zuben Hausa.
2.1.3 Kundayen Digiri Na Ɗaya
A ɓangaren kundayen digiri
na ɗaya waɗanda suke da alaƙa da wannan bincike akwai;
Ɗiso
(1979) ya kawo tarihin mawaƙin ne a taƙaice, sannan ya kawo irin gudunmawarsa kan
adabin Hausa. Kasancewar Mudi Sipikin ya rubuta waƙoƙin siyasa a ƙarni na ashirin,
wannan ya sa ake kundi ya taimaka ƙwarai wajen fito da bayanai kan yadda aka faro
a jiya da kuma inda aka kwana yau, da kuma ƙoƙarin hasashen me gobe za ta haifar
a fagen siyasar Nijeriya. Alaƙar aikinsa da wannan shi ne, nasa ya shafi waƙoƙin
siyasa da kuma gwagwarmayar Mudi Sipikin a cikin siyasar Nijeriya, wanda ya ba da
haske ga aikin. Inda suka bambanta shi ne, nasa ya shafi waƙoƙi ne, a wannan kuwa
an lalubo ginuwar siyasa da cigaban al’umma a siyasar Arewacin Nijeriya daga cikin
rubutaccen zuben Hausa ne.
Musa
(2007) ya gudanar da bincikensa ne kan waƙoƙin Haruna Aliyu Ningi, inda ya yi nazarin
yabo da zambo a cikin waƙoƙin. A cikin aikin, bayan ya kawo tarihin mawaƙin a matsayin
mawaƙin siyasa, sai ya kawo nau’o’in waƙoƙinsa. Bayan nan sai ya tsunduma cikin
nazarin inda ya yi nazarin yabo da zambo a cikin waƙoƙin siyasa da dama da mawaƙin
ya yi. Alaƙar aikinsa da wannan shi ne, aikinsa ya shafi siyasa ne a cikin adabin
Hausa, haka ma wannan aiki ya shafi siyasa a adabin Hausa. Abin da ya raba wannan
aiki nasa da wannan shi ne, an yi nazarin ne a cikin waƙoƙin siyasa, a wannan kuwa
za a fito da tarihin ginuwar siyasa ne a cikin rubutaccen zuben Hausa.
Isah (2023) a cikin kundinsa ya yi nazari ne a cikin waƙoƙin
siyasar Nijeriya inda ya fito da
irin matsalolin da ƙasar take ciki kamar yadda mawaƙan suka kawo.
Aikin nasa ya ta’allaƙa ne kan waƙoƙi guda uku, daga mawaƙa guda uku; waƙar ”Baubawan
Burmi” ta Aminu Ala da “Mafarkin Mulkin” ta Jibril Jalatu da kuma “Mafitar Nijeriya”
ta Sulaiman Farfesan Waƙa. Dangantakar wannan aikinsa da wannan shi ne, kasancewar
duk ayyukan sun shafi siyasar jam’iyyu da wasu bayanai a kan siyasar Nijeriya wanda
wannan aikin ya amfana da su. Bambancinsu shi ne, aikinsa ya shafi waƙoƙi ne, wannan
kuwa zai kalli rubutaccen zuben Hausa ne.
A
taƙaice waɗannan kundaye da aka yi nazari su ne waɗanda aka samu kai hannu a kansu.
2.2 Maƙalu
Maƙalu
suna ɗaya daga cikin matakan kai wa ga nasarar kowane irin bincike, domin a cikinsu
akan iya yin dace da wasu bayanai da za su taimaka ga samun nasara. Ganin muhimmancin
maƙalu ya sa aka nazarci wasu daga cikinsu. A nan an fara
kawo Bugaggun maƙalu, sannan aka
kawo waɗanda ba a buga ba. An kuma kawo bitar bugaggun littattafai, daga bisani aka yi bitar waɗansu bayanai
da aka samu a kafar intanet.
2.2.1 Bugaggun Maƙalu
Bugaggun
maƙalu su ne waɗanda aka buga su a cikin mujallun ilimi. Irin waɗannan maƙalu akan
tace su ta hanyar aika wa masana domin su tabbatar da irin gudummawar da yake cikinsu
da ingancinsu kafin a kai ga buga su. An yi bitar irin waɗannan bugaggun maƙalun
daga cikin mujallun ilimi daban-daban kamar haka:
Dunfawa
(1999) a maƙalarsa ta yi tsokaci ne kan gwagwarmayar neman shugabanci tsakanin ɗariƙun
sufaye. A ciki ya kawo tarihin zuwan Ƙadiriyya da Tijjaniyya ƙasar Hausa. Daga nan
sai ya kawo manyan abubuwan da gwagwarmayar neman shugabanci tsakanin aƙidun ya
ginu a kai, wato fifikon waliyyai da ƙablu da sadalu da kuma siyasa. Ɓangare na
ukun wato siyasa shi ne abin da ya danganta wannan bincike da wannan maƙala, domin
an kawo bayanin yadda alaƙa ta yi tsami tsakanin jam’iyyar NPC wadda shugabanta
Ahmadu Bello ne jikan Shaihu Usmanu, kuma Baƙadire, da kuma jam’iyyar NEPU wadda
mafi yawan mabiyanta ‘yan Tijjaniyya ne, wadda har ta kai ga an rushe wa ‘yan Tijjaniyya
masallaci. Bambancin wannan maƙala da wannan bincike shi ne, ta kalli gwagwarmayar
neman shugabanci ne a cikin ɗariƙun sufaye, yayin da wannan binciken ya dubi tarihin
ginuwar siyasar jam’iyya ne a rubutaccen zuben Hausa.
Birniwa
(2004) a nazarinsa ya dubi yadda mawaƙan siyasa suke amfani da adon harshe wajen
isar da saƙonninsu. A cikin maƙalar ya kalli siffantawa a matsayin wani kandamemen
bagire idan aka yi batun salon sarrafa harshe a waƙa. A nazarin nasa ya kawo sauran
adon harshe kamar su: mutuntarwa da dabbantarwa da abuntarwa kuma ya danganta su
da juna ta hanyar sanya su duk ƙarƙashin siffantawa. Ya kuma kawo bayaninsu ta hanyar
kawo misalai daga waƙoƙin siyasa na jumhuriya ta ɗaya da ta biyu. Wannan takarda
ta taimaka wa wannan aikin kasancewar ta shafi siyasar jam’iyya kamar yadda wannan
bincike ya shafi siyasar jam’iyya amma a cikin rubutaccen zuben Hausa ne.
Uba
(2006) ya yi nazari ne kan irin ra’ayoyin jam’iyyun NEPU da NPC. Inda ya bayyana
jam’iyyar NPC da cewa jam’iyya ce ta danniya wadda ke ƙoƙarin ganin ta ɗore a kan
mulki ko ta halin ƙaƙa. Ya nuna su kansu talakawa suna kallon jam’iyyar a matsayin
barazana gare su domin irin fin ƙarfin da ake nuna musu kan abubuwan da suke mallakarsu
ne, amma sai a nuna musu an fi su iko da su. Ta ɗayan ɓangaren kuwa, takardar ta
bayyana jam’iyyar NEPU da cewa jam’iyya ce ta masu neman sauyi, domin tana faɗa
ne da zalunci da danniya. Takardar ta fito da irin sakamakon da kan samu da zarar
irin wannan zaluncin da danniya suka kasance, sai mutane su fara nema wa kansu mafita
ko ta halin ƙaƙa. Wannan maƙala tana da alaƙa da wannan aikin bincike da za a yi,
domin ta nuna irin salon da jam’iyyun da suka wanzu a can baya suka ɗauka. Wannan
maƙalar ta kalli irin ra’ayoyin da jam’iyyun siyasa kan ɗauka ne, wato ko dai sauyi
ko kuma riƙau. Shi kuwa wannan binciken ya shafi tarihin siyasar jam’iyya Arewacin
Nijeriya daga cikin rubutaccen zuben Hausa ne.
Egwim
(2007) a maƙalarsa ya yi nazari ne kan yadda jam’iyyar PDP take ƙoƙarin dakushe
mulkin dimokuraɗiyya da ƙoƙarin ruguza tsarin ƙasar, ta hanyar naɗin muƙamai ba
tare da la’akari da wanda al’umma suka fi so ko suka zaɓa da hannunsu ba. Ya kawo
bayanai kan yadda shugaban ƙasa na wancan lokacin ya zama tamkar kura da fatar akuya,
inda ya riƙa yanke hukunci ko naɗa muƙamai ba tare da neman shawarar manyan ‘yan
jam’iyyar ba, wanda hakan ya haifar da matsaloli ga jam’iyyar da ma ƙasa baki ɗaya.
Wannan takardar ta taimaka wa wannan aiki sosai, domin kuwa ta ƙara haske a kan
wani ɓangare na tarihin ginuwar siyasa musamman a Arewacin Nijeriya. Bambancin takardar
da binciken shi ne, a wannan aikin an fito da tarihi da ginuwar siyasar jam’iyya
ne daga cikin rubutaccen zuben Hausa.
Takardar
haɗin guiwa tsakanin Yahya da Dunfawa (2010) ta fito da saƙon waƙar “Motar Siyasa”
ne a fili ta hanyar yin sharhin feɗe biri har wutsiya. Takardar ta bayyana yadda
‘yan siyasa suke yaudarar talakawa da yi musu daɗin baki domin su sami damar ɗarewa
madafun iko, amma da zarar sun samu sun ɗare sai su watsar da talakawan, su shiga
harkar gabansu. Wato dai ya zama talakawan sun yi abin nan da ake kira sun tura
mota ta baɗe su da hayaƙi. Takardar ta fito da yadda masu mulki suke kwashe dukiyar
ƙasa su mai da ita tasu, su bar talaka cikin wahala. Kasancewar wannan waƙar tamkar
wayar da kai ce ga al’umma su tashi su kare ‘yancinsu, kada su sake sakankancewa
da yaudarar ‘yan siyasa. Dangantakar wannan maƙala da binciken da za a gudanar shi
ne, ta shafi bayani kan siyasa da tsarin mulkin danniya da handama da babakere a
cikin mulkin dimokuraɗiyya, wanda yana daga cikin abubuwan da wannan aiki ya duba.
Haka kuma maƙalar ta yi nazarin wasu daga cikin halayyar ‘yan siyasa wanɗanda aka
fito da su cikin binciken. Bambancinsu shi ne, a wannan binciken an yi nazarin ginuwar
siyasar jam’iyya ne wanda a ciki za a fito da yadda ‘yan siyasar sukan kasance kafin
da kuma bayan sun ɗare madafun iko daga cikin rubutaccen zuben Hausa.
Malumfashi
da Kuna (2014) sun dubi irin musayar yawun da aka yi ne lokacin ana gab da samun
‘yancin kai, inda a arewacin Nijeriya ‘yan siyasa suka riƙa yaƙin junansu ta hanyar
musayar kausasan kalamai ko dai a waƙe ko kuma a cikin jawabai. Takardar ta fito
da yadda Turawan mulkin mallaka tare da goyon bayan sarakunan gargajiya suka riƙa
gallaza wa talakawa. Abin da talakawan suka kira da mulkin danniya, kuma suka riƙa
faɗa da wannan salon mulkin ta hanyar faɗin albarkacin bakinsu da nufin saƙo zuwa
ga masu mulki. Haka kuma maƙalar ta kawo misalan yadda ɓangaren masu mulki da na
waɗanda ake mulka suka riƙa kai suka da tsinin alƙalami da nufin tonon silili ko
kuma mayar da martani ta hanyar waƙoƙi da kuma jawabai waɗanda aka riƙa bugawa a
jaridu domin yaɗa manufa da wayar wa al’umma kai. Wannan takarda za ta taimaka wajen
gudanar da wannan bincike, domin kuwa binciken ya kawo bayanai kan irin salon mulkin
siyasa, aka riƙa kafa hujjoji daga rubutaccen zuben Hausa.
Ɗangulbi
(2015) a maƙalarsa ya yi bayanin yadda marubuta waƙoƙin siyasa suke yin amfani da
suka da mai da martani a cikin waƙoƙinsu, da kuma dalilan da sukan sanya a yi amfani
da su. A cikin takardar ya bayyana yadda mawaƙan jam’iyyu ke yin amfani da suka
ga abokan hamayyarsu domin fito da gazawarsu ta fuskoki da dama a harkar mulki.
Bugu da ƙari, ya bayyana irin yadda suka da mai da martani suke da muhimmanci a
siyasance, har ya nuna cewa, idan babu su to gwamnati za ta zama ta danniya. Wannan
takarda tana da dangantaka da wannan bincike da aka gudanar, domin binicken zai
shafi rubutattun ayyukan adabin Hausa na zube masu ɗauke da ruhin siyasa ne. Bambancin
maƙalar da wannan bincike shi ne, maƙalar ta yi
nazarin suka ne da mayar da martani a waƙoƙin siyasa, a
wannan kuwa an yi nazarin ginuwar siyasar jam’iyya ne da a cikin rubutaccen zuben
Hausa.
Omilusi
da Ajibola (2016) sun yi nazarin tarihin jam’iyyun siyasa ne a cikin mulkin dimokuraɗiyya
a Nijeriya. Tun da farko a cikin takardar an kawo bayanai kan samuwar jam’iyyun
siyasa, inda suka ci gaba da ƙulla zaren tarihin har zuwa wannan jumhuriya da muke
ciki wato jumhuriya ta huɗu. Takardar ta kuma kawo irin rawar da jam’iyyun siyasa
suke takawa wajen ci gaban tsarin dimokuraɗiyya. Wannan takarda tana da muhimmanci
ga wannan bincike, domin ko ba komai ta taimaka da wasu bayanai da suka shafi tarihin
samuwar siyasar jam’iyyu. Bambancin takardarsu da wannan binciken shi ne, sun kalli
jam’iyyun siyasa ne cikin tarihi, amma ba a cikin rubutaccen zube ba. Saɓanin wannan
da aka dubi tarihin ginuwar siyasa a cikin rubutaccen zuben Hausa.
Maƙalar
Iliyasu da Ƙanƙara (2016) an yi nazari ne kan siyasar jam’iyya a jihar Katsina bayan
dawowa mulkin dimokuraɗiyya, inda aka kawo bayanai kan abubuwan da suka faru a fagen
siyasar jihar da kuma irin ci gaban da aka samu a cikin tarihi tun daga shekara
1999 har zuwa 2015. Maƙalar ta kawo bayani kan zaɓuɓɓukan da aka gudanar a jihar
ta Katsina tun bayan komawa mulkin demokuraɗiyya daga 1999 har zuwa lokacin da jam’iyyar
hamayya ta karɓe mulki a 2015. Alaƙar wannan takarda wannan aiki shi ne, takardar
ta kawo bayanin wani ɓangare na mulkin dimokuraɗiyya, wanda bayanan za su taimaka
wa binciken da za a gudanar. Bambancin wannan takarda da wannan binciken shi ne,
an kawo bayanan ne cikin tarihi kaɗai, a wannan binciken kuwa an lalubo ginuwar
siyasa ne a cikin rubutaccen zuben Hausa.
Brigaglia
(2017) a maƙalarsa ya yi nazarin irin yadda alaƙa ta yi tsami ne tsakanin mabiya
ɗariƙar Tijjaniyya da na Ƙadiriyya. A cikin nazarin nasa ya kawo yadda mabiya ɗariƙar
Ƙadiriyya ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi suka riƙa gallazawa wa mabiya Tijjaniyya,
har ya kai ga an rushe masu masallatai. Hakan ya haifar da samuwar wasu waƙoƙi daga
mabiya Ɗariƙar Tijjaniya, waɗanda suke ɗauke da zambo/zagi a cikinsu. Nazarin ya
yi ƙoƙarin fito da siyasar addini ne a cikin tarihi inda ya gangaro har zuwa samuwar
siyasar jamiyyu a tsakankanin shekarun 1950. Dangantakar wannan maƙala da wannan
bincike da aka gudanar shi ne, ta shafi tarihin ginuwar siyasa a Arewacin Nijeriya
wanda tushensa daga siyasar addini ne ya gangaro har zuwa siyasar jam’iyyu. Bambancinsu
shi ne, wannan aikin ya shafi ginuwar siyasar jam’iyya ne a cikin rubutaccen zube
na Hausa.
Ɗangulbi
(2021) a cikin wata maƙalarsa ya yi nazarin salo ne a cikin waƙoƙin siyasa. Marubucin
ya fito da salailan da mawaƙan siyasa sukan yi amfani da su, domin jawo hankalin
al’umma ko nusar da su kan wani abu da ya shafi siyasa. Ya yi amfani da ire-iren
salo wajen tsettefe bayanai tare da kafa hujjoji daga baitocin wasu waƙoƙin siyasar
jam’iyya. Alaƙar wannan maƙala da wannan bincike shi ne, duk sun shafi siyasar jam’iyya.
Bambancinsu kuwa shi ne, a yayin da marubucin ya karkata akalar alƙalaminsa ta fuskar
nazarin salo a cikin waƙoƙin siyasa, wannan binciken ya yi nazarin ginuwar siyasar
jam’iyyu ne a cikin rubutaccen zuben Hausa.
Maƙalar
Idris (2021) ya yi nazarin bijirewa ta hanyar amfani da adon magana a cikin waƙoƙin
siyasa na Hausa. A cikin maƙalar tasa ya yi bayani kan yadda mawaƙa suke amfani
da adon magana wajen nuna bijirewa kan wasu abubuwa da gwamnati kan zartar wanda
jama’a ba su so. Ya fito da wasu nau’o’in adon magana kamar zambo da habaici da
kushe da tonon silili da sauransu ta hanyar kafa hujja da wasu baitocin waƙoƙin
siyasa. Dangantakar wannan maƙala da wannan binciken shi ne, ta shafi wasu muhimman
bayanai a kan siyasa, haka wannan binciken shi ma ya shafi rubutaccen zube ne na
siyasa. Abin da ya bambanta su shi ne, wannan aikin ya shafi ginuwar siyasar jam’iyyu
ne a cikin tarihi daga cikin rubutaccen zuben Hausa.
2.2.2 Maƙalu Da Ba A Buga
Ba
Malumfashi
(2009) maƙalarsa ta yi nazarin irin sa-toka-sa-katsin da aka yi ta yi ne tsakanin
masu mulki da waɗanda ake mulka. Bugu da ƙari, takardar ta fito da irin tashin-tashinar
da ta yi sanadiyyar samuwar wasu ayyukan adabi da suka shafi waƙoƙi da wasiƙu da
jawabai na mayar da martani ga abokan hamayya. Tun da farko maƙalar ta hakaito yadda
tsarin mulkin Turawa da yadda suka tafiyar da salon mulkin mallaka, da kuma yadda
masu ra’ayin riƙau wato sarakuna da alƙalai da malamai suka bi ra’ayin Turawa wajen
gudanar da abin da talakawa suka kira shi da mulkin danniya da babakere. Haka kuma,
maƙalar ta kawo bayanai kan irin wasiƙu da jawabai na mayar da martani waɗanda ‘yan
jam’iyya mai mulki wato NPC da kuma ‘yan hamayya na jam’iyyar NEPU suka riƙa aika
wa juna ta cikin jaridu da kuma rubutattun waƙoƙi. Wannan maƙalar za ta taimaka
wa wannan bincike da aka sanya a gaba domin kuwa ta hasko yadda aka fara tun a farko
a fagen siyasar Nijeriya, wanda hakan ya taimaka wajen fahimtar inda aka fito da
inda ake da kuma sanin inda aka dosa a siyasance a yau. Wannan maƙalar ta yi magana
kan siyasar jumhuriya ta ɗaya ne kaɗai, kuma ta karkata ne kan irin tashin-tashinar
da aka riƙa samu tsakanin jam’iyyu biyu. A wannan aiki kuma an yi ƙoƙarin yin nazarin
ginuwar tarihin siyasar jam’iyya a Arewacin Nijeriya da irin ci gaban da aka samu
a cikin siyasar ta hanyar kafa hujjoji da rubutattun ayyukan adabin Hausa na zube.
A
nazarin Malumfashi (2013) ya yi ƙoƙarin
fito da tarihin wasu abubuwan da suka faru ne a fagen siyasar Nijeriya a cikin waƙoƙin
siyasa, inda ya kalli abin tun kafin samun ‘yancin kai har zuwa bayan samun ‘yanci,
da kakkafa jam’iyyu da irin yadda mawaƙan suka riƙa sukar juna da yi wa juna tonon
silili. Haka kuma takardar ta dubi irin yadda mawaƙan suka fito da hoton abubuwan
da suka faru a fagen siyasar Nijeriya wanda tarihi ba zai manta da su ba. Wannan
takarda ta ƙara wa wannan aiki ƙwarin gwiwa ƙwarai, ganin cewa shi ma a wannan bincike
an yi ƙoƙarin fito da ginuwar siyasa da irin cigaban da aka samu, a ciki siyasar
jam’iyya a ƙasar Hausa, daga cikin rubutattun zuben Hausa. Abin da ya bambanta wannan
takarda da wannan bincike shi ne, takardar ta kalli yadda jam’iyyun siyasa na farko
suka riƙa yi wa juna tonon silili ne, saɓanin wannan aiki da ya kalli ginuwar siyasa
da cigaban al’umma daga cikin rubutaccen zuben Hausa.
Birniwa,
(2013) a wata takarda da ya gabatar, ya yi bayani kan yadda waƙoƙi suke taimakawa
wajen haɓaka siyasa. Ya faro bayani tun daga kan waƙoƙin siyasar Musulunci wato
na zamanin jihadi, ya gangaro zuwa siyasar Afirka. Daga nan sai ya karkato zuwa
siyasar Arewacin Nijeriya. A nan ya yi bayanin zamunnan siyasa da aka samu guda
huɗu, wato jumhuriya ta ɗaya har zuwa ta huɗu. Kuma kowane zamani ya kawo misalai
daga waƙoƙin da aka samu a wannan lokacin, in ban da jumhuriya ta uku, inda ya nuna
cewa an sami waƙoƙin siyasa, amma kasancewar wannan zamanin siyasa bai yi armashi
ba, wataƙila shi ya sa waƙoƙin ba su yi tashe ba. A ƙarshen takardar ya nuna cewa
waƙoƙin siyasa tamkar gishiri ne a cikin miya, wanda masu magana suke cewa idan
babu shi babu miya. Haka ma waƙoƙin siyasa rashin su a cikin siyasar jam’iyyu ba
ƙaramar naƙasu ce ba. Takardar tana da alaƙa da binciken nan, domin ta shafi bayanai
a kan muhimmancin waƙa a siyasar jam’iyya. Bayanan sun taimaka wajen fahimtar
inda aka fito da inda aka dosa a siyasance, sanna sun ba da haske wajen sanin irin
wainar da aka toya a cikin tarihin siyasar Nijeriya.
Bambancin wannan maƙala da binciken nan shi ne ya kalli muhimmancin waƙa ne a siyasar
jam’iyya, saɓanin wannan aikin wanda ya shafi tarihin siyasar jam’iyya daga cikin
rubutaccen zuben Hausa.
Birniwa
(2015) a maƙalarsa ya yi bayani a kan irin rawar da waƙoƙin Hausa suke takawa a
cikin siyasar wannan zamani. Maƙalar ta nuna irin gudummawar da waƙoƙin siyasa suka
riƙa bayarwa a fagen siyasa, da irin musayar kalamai da suka da zambo tsakanin magoya
bayan jam’iyyu daban-daban. Tun da farko, maƙalar ta kawo bayanai kan abin da ya
shafi rawar da mawaƙa ke takawa tun daga jumhuriya ta farko, inda aka riƙa kawo
misalai daga irin waƙoƙin siyasar wancan lokaci da sauran zamunnan siyasar da aka
yi har kuma zuwa yau. Takardar ta mayar da hankali ne kan waƙar “Masu Gudu Su Gudu”
inda aka kawo sharhin waƙar tare da bayanin zubinta da tsarinta da kuma salonta.
A cikin takardar an kawo bayanan wani ɓangare mai muhimmanci na tarihin siyasar
Nijeriya, inda a karon farko jam’iyya mai mulki ta yi rashin nasara a hannun ‘yan
hamayya. Maƙalar ta kawo bayanai muhimmai waɗanda suka taimaka wa wannan aiki.
Yusuf
(2016) ya yi nazari a kan rayuwar Malam Sa’adu Zungur tun daga haihuwarsa da neman
iliminsa da ayyukansa da rubuce-rubucensa. Bayan nan ya tsunduma cikin nazari don
fito da yadda wannan gwarzo ya mayar da alƙaminsa ya zama makamin yaƙinsa a fagen
siyasa. Kasancewarsa ɗan jam’iyyar NEPU mai hamayya a wancan lokaci, ya yi ta kai
ruwa rana da waɗanda ya kira masu mulkin danniya na jam’iyyar NPC. Ya riƙa amfani
da alƙalaminsa wajen suka da sara ga abokan hamayyarsa na siyasa ta hanyar waƙoƙi
da wasiƙu da jawabai. Kasancewar wannan bincike ya gudana ne kan ginuwar siyasa
da ci gaban al’umma a Arewacin Nijeriya, wannan ya sa aka leƙa ƙunshiyar wannan
maƙala domin samun ƙarin haske kan yadda abubuwa suka kasance a wancan zamanin,
wanda shi ne zai zama kamar tubalin ginin wannan bincike. Takardar ta shafi tarihin
rayuwar ɗan siyasa ne da rubuce-rubucensa na siyasa. Bambamcin wannan maƙala da
aikin shi ne, maƙalar ta dubi tarihin ɗan siyasa ne da ayyukansa na siyasa, yayin
da wannan aiki ya dubi ginuwar siyasar Arewacin Nijeriya a cikin rubutaccen zuben
Hausa.
‘Yanɗaki
da Iliyasu (2016) a maƙalarsu sun yi nazarin tarihi da gudummawar wasu fitattun
‘yan siyasa ne ‘yan asalin ƙasar Katsina, waɗanda suka bayar da gagarumar gudunmawa
ga siyasar yankin nasu da ma ƙasa baki ɗaya. Waɗannan mashahuran mutane da takardar
ta yi nazari a kansu su ne; Musa Musawa da Wada Nas da Dakta Yusuf Bala Usman da
Samban Barkan da kuma MD Yusuf. Takardar ta kawo bayanin irin aƙidarsu ta siyasa,
da gwagwarmayar da suka yi a siyasance, wasu tun daga zamanin siyasar NEPU da NPC,
wasu kuma daga zamanin PRP da NPN, wasu ma daga ciki irin su Alhaji Musa Musawa
har Allah ya tsawaita rayuwarsu har zuwa jamhuriya ta huɗu da su. Wannan takarda
tana da alaƙa da wannan aikin, domin ta fito da irin aƙidar ‘yan siyasa musamman
wajen riƙo da jam’iyya. Bambancin wannan takarda da wannan aiki shi ne, sun yi nazarinsu
ne ta fuskar tarihi tsantsa ba a cikin rubutaccen zuben Hausa ba.
Iliyasu
(2018) a maƙalarsa ya kawo tarihin sauyin sheƙa ne da ‘yan siyasa suka riƙa yi daga
wata jam’iyya zuwa wata daga shekarar 1999 zuwa 2018. A cikin bayanansa ya kawo
dalilan da sukan sanya ‘yan siyasa ficewa daga wata jam’iyya zuwa wata, a ƙarshe
kuma ya kawo jerin sunayen ‘yan siyasar da suka sauya sheƙa daga waɗansu jam’iyyu
da kuma jam’iyyun da suka koma. Wannan takarda tana da dangantaka wannan binciken,
domin kuwa bayanin ginuwar siyasar jam’iyya da gwagwarmayar cigaban al’umma ba zai
kammalu ba, ba tare da an ambaci sauye-sauyen sheƙa da ‘yan siyasar suka riƙa yi
bisa wasu dalilai ba. Bambancin takardar da wannan binciken shi ne, wannan daga
cikin rubutaccen zuben Hausa aka fito da bayanin ginuwar siyasa da cigaban ƙasa
wanda ya ƙunshi har da batun sauyin sheƙa na ‘yan siyasa.
2.3 Bugaggun Littattafai
A
cikin aikin bincike, duba littattafan da aka wallafa mataki ne da yake taimaka wa
mai bincike wajen samun wasu bayanai da suke da kusanci, kuma masu fa’ida ga bincikensa.
Saboda haka a wannan binciken an yi bitar littattafan da hannu ya samu kaiwa gare
su domin tsintar abin da malamai suka rubuta suka bari musamman a kan siyasa.
Daga
cikin littafan da aka duba akwai: Dudley (1968) wanda a cikin littafinsa ya kawo
bayanai kan abubuwan da suka faru tun
daga farkon samuwar siyasar jam’iyyu a arewacin Nijeriya. A cikin littafin ya kawo
bayanai kan irin yadda aka kakkafa ƙungiyoyin siyasa da kuma yadda ƙungiyoyin suka
rikiɗe suka zama jam’iyyun siyasa na farko a yankin arewacin Nijeriya. Marubucin
ya kuma kawo irin rawar da jam’iyyun suka taka a zaɓuɓɓukan da aka gudanar a zamaninsu.
Haɗuwa da wannan littafi ya ba da danar sanin inda aka faro a fagen siyasar Nijeriya,
musamman ma kan abin da ya shafi kakkafa jam’iyyu da kuma irin manufofin jam’iyyun
da suka wanzu a wancan lokaci. Wanɗannan bayanai sun kasance tamkar fitila da ta
haska wa wannan bincike hanya ya kai ga nasara.
A
cikin littafin Paden (1973) an kawo bayanai ne kan yadda siyasar addini ta yi tasiri
wajen samuwa siyasar jam’iyyu bayan zuwan Turawa. Haka kuma a cikin littafin an
kawo irin tasirin da aƙidoji a cikin addinin musulunci suke da shi dangane da mulki
da siyasa a Arewacin Nijeriya. Marubucin ya kawo cikakkun bayanai a kan yadda mabiya
ɗariƙu mabambanta suka riƙa hamayya da juna, da kuma yadda suka riƙa danganta kansu
da manyan waliyyai ko shehunnai domin samun nasara a siyasance. Wannan littafi ya
ba da damar fahimtar yadda siyasar jam’iyya ta kafu tare da taimakon siyasar addini.
Wannan littafi ya taimaka wajen gane ina aka fito a siyasance, musamman siyasar
addini da kuma tushen siyasar jam’iyya a Arewacin Nijeriya. Bambancin wannan littafin
da wannan aikin shi ne, marubucin ya dubi siyasar addini ne da kuma dangantakarta
da kafuwar siyasar jam’iyya a ƙasar Hausa. Wannan bincike kuwa ya dubi ginuwar siyasa
ne cikin tarihi, inda aka kafa hujjoji daga rubutaccen zuben Hausa.
Kano
(1973) a nasa littafin ya kawo bayanai
ne kan rayuwar jajirtaccen ɗan siyasa kuma ɗan kishin ƙasa, wanda ya sadaukar da
rayuwarsa wajen faɗa da zalunci da danniya da babakeren masu mulki. A cikin littafin
ya kawo bayanai kan irin yadda ya san Malam Sa’adu Zungur a matsayin malaminsa a
makaranta, kuma malaminsa a fagen siyasa, wanda ya nuna cewa yana alfahari da shi,
domin shi ne ya koya masa siyasa cikin rashin tsoro ko shakkar wani. Malam Sa’adu
Zungur yana daga cikin ‘yan ƙasa na farko da suka kafa jam’iyyar siyasa ta farko
a Arewa. Malam Sa’adu ya kasance mutum mai sha’awar rubuce-rubuce, domin ya yi rubuce-rubuce
da dama na siyasa a jaridu daban-daban. Ya rubuta waƙoƙin siyasa fitattu waɗanda
suka ja hankalin ‘yan ƙasa dangane da tsarin mulki da siyasa da sauransu. Haɗuwa
da wannan littafi ya taimaka wa wannan bincike wajen sanin inda aka faro a fagen
siyasa, da irin ɗauki-ba-daɗin da aka yi wajen yaƙi da danniya a wancan lokaci da
kuma lura da yadda salon danniyar ya ci gaba har zuwa wannan lokaci.
Littafin Abdulƙadir (1974) littafi
ne da ya shafi rayuwar Malam Sa’adu Zungur da bayanin wasu daga cikin waƙoƙinsa.
Marubucin ya kasa littafin zuwa babi-babi har biyar, inda a farko ya kawo tarihin
rayuwa da gwagwarmayar Malam Sa’adu Zungur tun daga haihuwarsa da neman iliminsa
da gwagarmayar rayuwarsa da ayyukansa har zuwa mutuwarsa. Daga babi na biyu zuwa
na biyar ya kawo waƙa guda a kowane babi tare da yin sharhinta domin fito da kayan
cikinta. Wannan littafi ya samar da bayanan da suka taimaka wajen samun nasarar
wannan binciken, kasancewar Malam Sa’adu Zungur fitaccen ɗan siyasa, kuma wanda
ya yi gwagwarmayar neman ‘yanci, ya ƙyamaci mulkin danniya, sannan ginshiƙi wajen
kafa siyasar jam’iyyu a Nijeriya.
Dambazau
(1981) kuwa a tasa hoɓɓasar ya kawo bayanai
ne kan abin da ya shafi kafuwar waɗannan manyan jam’iyyun hamayya a Arewacin Nijeriya,
wato jam’iyyun NEPU da PRP. A cikin littafin ya kawo bayanan abubuwan da suka faru
da jam’iyyun biyu tun daga kafuwarsu. Kasancewar marubucin wannan littafi ɗaya ne
daga cikin waɗanda suka kafa waɗannan jam’iyyu guda biyu, wannan ya sa ya iya rubuta
kusan komai dangane da abubuwan da suka wakana a wancan zamanin na abin da ya shafi
rikita-rikitar siyasa musamman na jam’iyyun guda biyu. Marubucin ya raba littafin
nasa zuwa manyan sassa guda biyu; sashe na farko ya kawo bayanai kan yadda aka kafa
jam’iyyar NEPU da tsare-tsarenta, da shugabanninta da rigingimun da suka yi ta faruwa
tsakaninta da wasu mutane da kuma abokan hamayya, da kuma wasu abubuwa da suka shafi
gudanar da jam’iyyar. A sashe na biyu kuwa sai ya kawo bayanai kan jam’iyyar PRP
da kafuwarta da mambobinta da rigingimun da suka faru a cikinta da duk wani abu
da ya shafi jam’iyyar har zuwa shekarar 1981. Wannan littafi yana da dangantaka
da wannan binciken, kasancewar ya taɓo wani ɓangare na bayanin kafuwar jam’iyyun
siyasa, musamman jam’iyyun hamayya na wancan lokaci, da duk abin da ya shafe su.
Wannan littafin ya taimaka wajen hasko inda aka fito a cikin tarihin siyasar jam’iyyu,
wanda kuma zai haska wa wannan bincike wajen lalubo yadda siyasa ta ginu daga cikin
rubutattun ayyukan zuben Hausa.
Ɗan’Asabe da Aliyu da Mohammed (1995) a cikin littafinsu
na haɗin guiwa sun kawo tarihi da gwagwarmayar rayuwar fitaccen ɗan siyasa Malam
Muhammadu Ɗanjani Haɗeja. A cikin littafin sun bayyana irin gwagwarmaya da faɗi
tashin da ya yi a matsayinsa na ɗan jam;iyyarsa NEPU, wanda bayan shuɗewar jamhuriya
ta farko ya ci gaba da siyasa a jam’iyyar PRP daga baya kuma ya shiga jam’iyyar
NPP. A cikin littafin sun kawo wasu jawaban siyasa da ya gabatar a lokacin rayuwarsa.
Dangantakar littafin da wannan aiki shi ne, an kawo jawaban siyasa waɗanda binciken
ya amfana da su wajen kafa hujjo da ma wasu bayanai da aka samu a cikin littafin.
Bambancin littafin da wannan aikin shi ne, tarihin gwagwarmayar ɗan siyasa guda
aka kawo a cikinsa, inda a wannan binciken aka dubi tarihin ginuwar siyasar jam’iyya
daga cikin rubutaccen zuben Hausa.
Yakubu
(1999) a littafinsa ya kawo cikakken bayani
kan rayuwar Malam Sa’adu Zungur, tun daga haihuwarsa da ayyukansa da rubuce-rubucensa
da gwagwarmayarsa a fagen siyasa har zuwa mutuwarsa. Ya kawo bayanai da suka shafi
siyasar Turawan mulkin mallaka irin gwagwarmayar da aka yi lokacin kakkafa jam’iyyun
siyasa na farko. Ya kuma kawo bayanai kan irin zafin hamayyar siyasar da ta wanzu
a wancan lokacin, da irin yadda ‘yan jam’iyya mai mulki wato NPC suka riƙa cin karensu
ba babbaka a fagen siyasa tare da haɗin kan Turawa. A ɗayan ɓangaren kuma ya kawo
yadda ‘yan hamayya na jam’iyyar NEPU suka riƙa nuna hamayyar su ga gwamnatin da
suka kira ‘yan danniya. Marubucin ya fito da rayuwar Malam Sa’adu Zungur a matsayin
fitaccen ɗan kishin ƙasa wanda ya kasance cikin ‘yan hamayya har zuwa ƙarshen rayuwarsa.
Haɗuwa da wannan littafi ya taimaka wajen samun nasarar binciken.
Littafin Abba (2000) ya kawo cikakken bayani ne
kan yadda aka kafa jam’iyyar NEPU da waɗanda suka kafa ta da manufofinta da aƙidojinta.
Marubucin ya kawo dukkan wasu bayanai da suka shafi jam’iyyar NEPU, kasancewarta
jam’iyyar hamayya ta farko a Arewacin Nijeriya. Ya bayyana irin faɗi-tashi da gwagwarmayar
da ‘ya’yan jam’iyyar suka yi domin ganin ta ɗore. Bayanan da suke cikin wannan littafi
sun taimaka wa wannan aiki ƙwarai domin fahimtar irin gwagwarmayar da suka yi da
masu mulki a wancan lokaci. Samun wannan littafi ya ba da haske wajen daidaita alƙiblar
wannan aiki.
A
cikin wani littafi na Jega da wasu (2002) an kawo zaɓaɓɓun jawabai ne da wasu rubuce-rubucen
Malam Aminu Kano tun daga shekarar 1950 har zuwa 1982. A cikin littafin an kawo
tarihin rayuwar Malam Aminu Kano tun daga haihuwarsa har zuwa mutuwarsa. Daga bisani
sai aka riƙa kawo jawabansa a tarurrukan siyasa waɗanda ya gudanar da su a lokuta
mabambanta a kuma garuruwa daban. Har ila yau a cikin littafi an kawo rubuce-rubucensa
ya riƙa yi a cikin jaridu da kuma wasiƙun da ya riƙa aika wa manyan masu faɗa a
ji. Alaƙar wannan littafi da wannan binciken shi ne, an kawo matanin wasu jawaban
siyasa da dama a cikinsa waɗanda aikin ya amfana da su wajen kafa hujjoji.
Jega
da wasu (2003) a wani littafi nasu sun kawo bayanai kan rayuwar Mudi Sipikin baki
ɗaya, tun daga haihuwarsa da neman iliminsa har zuwa shigarsa al’amuran siyasa.
Haka kuma a matsayinsa na marubucin waƙoƙi sun yi ƙoƙari wajen bayyana irin gwagwarmayarsa
a wannan fage, ta hanyar kawo bayanai kan abin da ya shafi waƙoƙinsa, ciki kuwa
har da na siyasa. Daga bisani sun yi nazarin waƙoƙin nasa domin ganin irin baiwar
da Allah ya hore masa. Kasancewar Mudi Sipikin ɗaya daga waɗanda aka yi gwagwarmaya
da shi a fagen siyasar Nijeriya, sannan kuma marubucin waƙoƙin siyasa, ya sa haɗuwa
da wannan littafi ya taimaka ƙwarai wajen samun nasarar wannan aiki.
Anwar
(2007) ya ware kashi guda na littafinsa inda ya kawo matanin wasu waƙoƙin siyasa
waɗanda suka shafi gwagwarmaya tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulka. Kasancewar
marubucin ya shiga cikin harkokin siyasar jumhuriya ta biyu, wannan ya sa ya rubuta
waƙoƙi da dama waɗanda suka shafi rayuwar siyasa na wancan lokacin. A kashi na huɗu
na littafin nasa ya kawo waƙoƙin siyasa guda ashirin waɗanda ya rubuta a jumhuriya
ta biyu. Samun wasu bayanai daga cikin wannan littafi ya taimaka ƙwarai wajen daidaituwar
wannan bincike da aka gudanar.
2.4 Bayanan Intanet
Kafar Intanet kafa
ce mai muhimmanci wadda ta ƙunshi abubuwa da dama waɗanda suka haɗa har da bayanai
na ilimi da ayyukan bincike. A yayin gudanar da wannan bincike an ci karo da waɗansu
maƙalu a shafukan intanet waɗanda aka yi bitar su kamar haka:
Bello
da Bappi (2015) wanda suka dubi yadda al’amuran maguɗin zaɓe suka wakana daga 1999
zuwa 2015. Sun kawo wasu abubuwa da ake ganin sun taimaka wajen aiwatar da maguɗi
a wannan lokacin kamar amfani da ‘yan bangar siyasa wajen tayar da yamutsi domin
yin maguɗi. Dangantakar wannan maƙala da wannan aiki shi ne, ta taɓo wani ɓangare
daga cikin batutuwan da aka tattauna a cikin wannan aikin wato maguɗin zaɓe, sai
dai sun bambanta kasancewar hujjojin da aka bayar a cikin maƙalar ba daga cikin
rubutaccen zube aka kawo su ba. Shi kuwa wannan aikin ya ƙunshi tarihin ginuwar
siyasar ƙasar Hausa ne daga cikin rubutaccen zuben Hausa.
Ibrahim
da Abubakar (2015) sun gudanar da nazarinsu ne kan irin rikice-rikicen cikin gida
da akan samu a cikin jam’iyyun siyasa, wanda kan samo asali daga rashin fahimtar
juna tsakanin magoya bayan jam’iyya guda. Nazarin nasu ya dubi yadda jam’iyyar PDP
ne ta yi ta fama da rikice-rikice a lokuta mabambanta, wanda hakan ya riƙa kawo
wa jam’iyyar ci baya. Sun bayyana yadda sakamakon waɗannan rashin fahimta da aka
riƙa samu ya haifar da ficewar wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar da dama zuwa
jamiyyar hamayya, wanda hakan ya taimaka wajen rashin nasarar da jam’iyyar ta yi
a zaɓen ƙasa na shekarar 2015. Wannan nazari ya taimaka wa wannan bincike, domin
ya taɓo wani ɓangare da wannan binciken zai kalla, wato sauya sheƙar da ‘yan siyasa
kan yi daga wata jam’iyya zuwa wata. Bambancin wannan takarda da binciken shi ne,
a nan an yi nazarin ginuwar siyasa ne a cikin tarihi daga cikin rubutaccen zuben
Hausa.
Gudummawar
Odundayo (2016) ta shafi tarihin rikice-rikicen cikin gida ne da aka yi ta fama
da su a cikin jam’iyyar PDP. Tun da farko ya fara da kawo tarihin rikicin cikin
gida na jam’iyyun siyasa wanda ya riƙa kawo tarnaƙi ga ci gaban jam’iyyun. A nazarin
nasa ya kawo bayanai kan abin da ya shafi rikicin jam’iyyu tun kafin samun ‘yancin
kai, inda ya gangaro har zuwa jumhuriya ta huɗu. Ya kawo dalilai da yake ganin su
ne suka haifar da rikice-rikice a cikin jam’iyyar PDP wanda ya haifar da sauya sheƙar
da wasu manyan ‘ya’yanta suka yi zuwa jam’iyyun hamayya. Haka kuma nazarin ya kawo
wasu dalilai da yake ganin sun taka muhimmiyar rawa wajen rashin nasarar da jam’iyyar
ta yi a babban zaɓen ƙasa bayan ta kwashe shekaru goma sha shida tana mulki. Wannan
nazarin ya taimaka wa wannan bincike, domin kuwa ya ba da haske a kan abin da ya
shafi rikicin cikin gida na jam’iyyun siyasa da kuma sauyin sheƙa ga ‘yan siyasa.
Abin da ya bambanta wannan nazari da wannan binciken shi ne, wannan binciken ya
fito tarihin ginuwar siyasa ne daga cikin rubutaccen zube na Hausa, saɓanin nasa
da aka gudanar da shi ta fuskar tarihi tsantsa ba daga rubutaccen zube ba.
Takardar
Micheal da Ogunrotimi da Roland (2023) ta kawo bayanai kan ginuwar maguɗin zaɓe
a cikin tarihi. Takardar ta kawo bayanai kan zaɓuɓɓukan da aka gudanar a shekarar
1959 da 1964 da 1965 da kuma 1983. Duk da cewa ita ma wannan takardar an kawo tarihin
maguɗin zaɓe ne wanda shi ya danganta ta da wannan aiki, amma abin da ya bambanta
ta da wannan aikin shi ne, ba a cikin rubutaccen zuben Hausa aka kafa hujjojin da
aka yi amfani da su ba.
Waɗannan
ayyuka su ne aka yi bitar su domin ganin inda aka tsaya da kuma inda ya kamata a
ɗora. Ayyukan sun kasance tsani ne da aka taka wajen hango inda ya kamata a dosa
kan wannan bincike.
2.5 Hujjar Ci Gaba Da
Bincike
Bisa
ga abin da aka gani cikin bitar ayyukan da suka gabata, masana da manazarta sun
baje kolin ilimi wajen yin nazarce-nazarce da bincike-bincike kan abin da ya shafi
siyasa da nazarin ayyukan adabin siyasa rubutattu da na baka da sauransu. Da yake
da na gaba ake gane zurfin ruwa, wannan waiwayen ya ba da damar gano cewa, tun daga
matakin digiri na ɗaya har zuwa na uku, babu wani aiki da hannu ya kai kansa, wanda
aka gudanar da ya shafi nazarin ginuwar siyasar jam’iyya a cikin tarihi daga 1950
zuwa 2023 a cikin rubutaccen zuben Hausa.
Ke
nan, ana ganin cewa wannan ya isa ya zama hujjar da aka dogara da ita wajen gudanar
da wannan binciken, don ganin irin rawar da rubutaccen zuben Hausa yake takawa wajen
adana tarihin al’amuran siyasar jam’iyyu a Nijeriya.
2.6 Naɗewa
A
cikin wannan babin an kawo bayanai da suka shafi bitar ayyukan magabata. A ciki
an yi bitar kundayen digiri tun daga na ɗaya da na biyu da kuma na uku. Daga nan
sai aka kawo bitar maƙalu, waɗanda suka haɗa da bugaggu da waɗanda ba a buga, sannan
aka kawo bitar bugaggun litattafai. An kuma yi bitar waɗansu bayanai da aka samu
daga intanet. Bayan kammala bitar ne aka kawo hujjar ci gaba da bincike, daga nan
aka naɗe babin.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.