Yusuf, J. (2025). Tarihin Ganuwar Wasu Al'amuran Siyasar Jam'iyyu a Cikin Rubutun Zuben Hausa Daga 1950-2023 (Ph.D. Thesis) Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo, Sokoto.
TARIHIN GINUWAR WASU AL’AMURAN SIYASAR JAM’IYYU A CIKIN RUBUTUN ZUBEN HAUSA DAGA 1950-2023
Na
Jibril Yusuf
Email: yusuf.jibril@kasu.edu.ng
Phone: +2347030399995
*** ***
BABI
NA ƊAYA
GABATARWA
1.0 Shimfiɗa
Nazari a kan ayyukan adabi da suka haɗa da rubutattun
waƙoƙi da rubutattun wasannin kwaikwayo da kuma rubutattun labaran zube ba sabon
abu ne a fagen nazarin Hausa ba, musamman idan aka yi la’akari da irin gudummawar da masana da manazarta suka
bayar wajen fito da muhimman abubuwan da suka ƙunsa.
Masana da manazarta sun yi nazarce-nazarce ne ta la’akari da yadda adibai suka baje
kolin basirarsu kan al’amuran siyasa a cikin ayyukansu na adabi. Yawancin nazarce-nazarce
da ayyukan da aka gudanar sun shafi nazarin zubi da tsari da salo da kuma jigo ne;
sai aikin Idris (2016) ya yi nazarin bijirewa a waƙoƙin siyasa da Yusuf (2018) wanda
ya yi nazarin tarihin Jam’iyyar PDP a cikin rubutattun waƙoƙin siyasa.
Duk da irin yadda manazartan suka bayar da gagarumar
gudummawa kuma suka cancanci yabo, amma kasancewar ilimi kogi ne, wannan ya sa ba
a sami wani aiki na nazarin ilimi da aka gudanar da ya yi nazarin ginuwar siyasar
jam’iyya daga cikin rubutaccen zube ba.
Siyasa wani ɓangare ne na rayuwar al’umma, wadda ba
makawa dole Hausawa su tsinci kansu a ciki, da saninsu ko ba da saninsu ba. Kasancewar adabi hoto ne da ke nuna rayuwar al’umma,
wannan ya sa a kowace gaɓa ko yanki na rayuwa da aka riska ba a taɓa rasa ɓurɓushin
siyasa a cikin adabin al’ummar wannan lokaci. Shi kuwa Zube ɓangare
ne na adabi da ake iya samu a adabin baka ko rubutacce. Ɗangambo (1984: 9) ya bayyana
cewa, ‘’Zube shi ne duk wani rubutu ko wata wallafa da ba waƙa ba ce, kuma ba wasan
kwaikwayo ba ne.” Ya ƙara da cewa, “Zube ya ƙunshi ƙagaggun labarai da rubuce-rubucen
tarihi da na siyasa da sauransu’’. Wannan ne ya sa aka samu rubutaccen zube mai
ɗauke da ruhin siyasa a cikin ayyukan adabin Hausa. Ke nan, dangantakar
siyasa da zube tamkar ta jini da tsoka ce.
Sunan wannan bincike shi ne, ‘Tarihin
Ginuwar Wasu Al’amuran Siyasar Jam’iyyu A Cikin Rubutun Zuben
Hausa Daga 1950-2023’.
Binciken ya fito da abubuwan da suka shafi siffofin siyasar jam’iyyu ne; lokacin ana gab
da samun ‘yancin kai kafin ma a kai ga kakkafa jam’iyyu har zuwa kafuwarsu da bunƙasarsu
da kuma yadda aka gudanar da zaɓuɓɓuka a ƙarƙashinsu. Haka kuma bayan kafa jam’iyyu
da gudanar da zaɓe, jam’iyyar hamayya ta wancan lokacin ta zargi jam’iyya mai mulki
da rashin adalci da danne haƙƙin talaka da kuma yin rub da ciki a kan dukiyar talakawa.
Irin wannan fasali ya ci gaba da fitowa a rubutaccen adabin Hausa na zube har zuwa
yau, inda marubutan kan nuna irin yadda masu mulki suke yin wadaƙa da dukiyar ƙasa.
Aikin ya yi ƙoƙarin lalubo wasu muhimman abubuwa da suka faru a cikin siyasar Arewacin
Nijeriya tun daga farko har zuwa yau, inda aka riƙa kafa hujjoji na wani abu da
aka ci karo da shi daga wasu sassan rubutaccen zube da suka haɗa da jaridu da wasiƙu
da jawaban siyasa da kuma ƙagaggun labaran Hausa domin ganin irin yadda almuran
siyasa suka riƙa gudana a tsakanin shekarun 1950 zuwa 2023.
A cikin wannan babin za a kawo
bayanai kan muhimman abubuwan da aka ɗora binciken a kansu waɗanda su ne suka zama
tubalin ginin binciken tun daga farkonsa har ƙarshensa. A cikin wannan babin an
kawo dalilin da ya haifar da tunanin yin binciken, sai aka kawo manufa da muradun
bincike da kuma muhimmancin da binciken yake da shi ga fagen ilimi da ma al’umma
baki ɗaya. Daga sai aka kawo farfajiyar bincike wato inda binciken ya tsaya. An
kuma kawo tambayoyin bincike waɗanda su ne binciken ya amsa kafin daga ƙarshe aka
naɗe babin.
1.1 Dalilin Bincike
Babban
dalilin gudanar da wannan bincike shi ne, ganin yadda aka ratsa wasu zamunna na
mulkin dimokuraɗiyya, kuma an samu rubutattun ayyukan adabi musamman rubutaccen
zube, wanda ya fito da hotunan yadda rayuwar siyasar lokutan ta riƙa gudana har
zuwa shekarar 2023. Wannan ya sa aka ga dacewar a shiga cikin rumbun ayyukan adabin
Hausa, domin lalubo wasu gaɓoɓin tarihin siyasar jam’iyyu a Arewacin Nijeriya daga
cikin rubutaccen zube, da kuma irin fasalin da aka riƙa samu a cikinsa na cigaban
al’umma da kuma ɗorewar siyasar. Haka kuma, sha’awar da ake da ita na karance-karance
na rubutaccen zube da bibiyar al’amuran siyasa, shi ma ya ƙara wa wannan bincike
ƙwarin guiwar gudanar da shi.
1.2 Manufar Bincike
Manufar
wannan aiki bincike ita ce yin nazarin ginuwar siyasar jam’iyyu a cikin tarihi daga
cikin rubutaccen zuben Hausa. Muradun wannan bincike sun haɗa da:
i.
Ƙoƙarin zaƙulo wasu ayyukan rubutaccen zube da suka shafi siyasa domin ganin
yadda adibai suka fito da wasu batutuwan siyasa a cikin tarihin siyasar
Nijeriya.
ii.
Gano irin gudunmawar da wasu marubuta zube suke bayarwa wajen ci gaba da
bunƙasar dimokuraɗiyya, da kuma irin gudummawar da adibai suke bayarwa wajen
adana tarihi a cikin ayyukansu.
iii.
A yi ƙoƙarin fito da irin abubuwan da sukan zama silar samun cigaba a siyasance
daga cikin rubutaccen zuben Hausa.
iv.
A yi ƙoƙarin lalubo wasu abubuwa da suka riƙa zama tarnaki wajen samun cigaban
al’umma a cikin a cikin tsawon tarihi daga cikin rubutaccen zuben Hausa.
v.
Fito da irin dangantakar da take tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulka ta
hanyar nazarin irin kallon da kowane ɓangare yake yi wa juna.
vi.
Fito da fasalolin da suka riƙa bayyana a cikin siyasar Nijeriya, kamar yadda
suka fito cikin wasu rubutattun ayyukan adabin Hausa na zube.
1.3 Muhimmancin Bincike
Wannan bincike ya kasance wata
madogara ga
masu sha’awar nazarin tarihin al’amuran siyasa a cikin zuben Hausa, domin kuwa alƙiblar
da binciken ya kalla, wato fagen nazarin tarihi a cikin rubutaccen zube bai shahara
sosai ba a fagen nazari.
Binciken yana da muhimmanci
domin ya haska wa manazarta wurin fito da tarihin faruwar wasu abubuwa a siyasar
Nijeriya daga cikin rubutaccen zube na Hausa.
Haka kuma, wannan binciken
ya fito da manufofin siyasar jam’iyyu a fili ta yadda
za a fahimce su, saboda yadda wasu marubuta zube suka taskace su.
Haka kuma, ta hanyar binciken
an fahimci yadda ake gwagwarmaya wajen samun cigaban al’umma da kuma abubuwan da
kan kawo tarnaƙi ga samun cigaba a siyasance.
Bugu da ƙari, binciken ya taimaka
wajen fito da irin dangantakar da take tsakanin masu mulki da wanɗanda ake mulka,
da kuma irin kallon da kowane ɓangare yake yi wa juna kamar yadda ya fito cikin
ayyukan zube na Hausa.
1.4 Farfajiyar Bincike
Aikin
bincike da nazari a Hausa yana kasancewa ne a ɗaya daga cikin ɓangarori uku na nazarin
Hausa. Yana iya kasancewa cikin ɓangaren al’ada ko adabi ko kuma harshe. Wannan
aiki mai suna ‘Tarihin Ginuwar Wasu Al’amuran Siyasar Jam’iyyu A Cikin
Rubutun Zuben
Hausa Daga 1950-2023’ ya kasance ne a ɓangaren adabi. A nan ma binciken ya kasance ne a cikin
kason rubutaccen zube.
1.5 Tambayoyin Bincike
Yawancin
ayyukan bincike da nazarce-nazarce kan samo asali ne sakamakon tuzgowar wasu tambayoyi
da mutum yakan yi wa kansa ko wani ya yi masa ko kuma shi ya tambayi wani ko wasu.
Neman amsar waɗannan tambayoyi a wasu lokuta yakan haifar da musayar ra’ayi, ko
kuma ya haifar da ruɗanin tunani ga wanda ya yi wa kansa da kansa tambaya. Dangane
da wannan bincike da aka gudanar shi ma dai ba ta sake zani ba, domin kuwa akwai
tambayoyi da dama waɗanda suka bijiro, waɗanda binciken ya amsa su. Tambayoyin sun
haɗa da:
i. Wace irin rawa zube yake takawa ga cigaban
al’amuran siyasa?
ii. Waɗanne dalilai ne suka haifar da ƙamfar wasu
ayyuka na rubutaccen zuben Hausa na siyasa?
iii. Ko za a iya ganin manufofin siyasar jam’iyyu a
cikin rubutattun ayyukan zuben Hausa?
iv. Ta yaya rubutaccen zuben Hausa ya haska abubuwan
da suke zama sila ga samun cigaban al’umma a cikin siyasar jam’iyyu?
v. Waɗanne abubuwa ne marubuta zube suka danganta ga
kawo cikas ga amfana da manufofin siyasar jam’iyyu?
vi. Me za a iya gani a cikin rubutaccen zube dangane
da kallon-kallo tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulka?
Waɗannan
tambayoyi ne wannan bincike ya amsa daga bayanan da ya ƙunsa a cikinsa.
1.6 Naɗewa
Wannan babin shi ne mabuɗin
aikin. A ciki an yi shimfiɗar inda aikin ya dosa. Daga nan aka kawo dalili da manufa
da kuma muhimmancin bincike. Bayan nan kuma sai aka kawo bayani kan farfajiyar
da binciken ya tsaya.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.