A wajen Sufaye da zaran ka ambaci Annabi (saw) ka kore masa wani hakkin Allah, ka ce: ba za a bauta wa Annabi (saw) ba, ba za a roke shi biyan bukata ba, ba za a nemi taimakonsa ba, ba za a nemi agajinsa ba.. duka wannan a wajensu RASHIN LADABI ne.
Al-Bakriy, Sufin da ya kafirta Ibnu Taimiyya ya ce
"ومن خص الرسول أو الملائكة بنفي خاص، يفهم منه طرح رتبتهم وعدم
صلاحيتهم للأسباب فقد نقصهم بعبارته؛ وإن نوى معاني التوحيد".
الاستغاثة في الرد على البكري (ص: 230)
"Duk wanda ya kebance Manzon Allah ko
Mala'iku ya kore musu "Istighatsa" a kebance, za a fahimta daga gare
shi cewa; ya zubar da martabarsu, da nuna rashin dacewarsu ga zamowa sabuban
alheri, don haka ya soke su, ya nakasa su da lafazinsa, ko da kuwa ma'anar
Tauhidi ya nufa".
Shi ya sa a gaba ya ce
"وأما قول هذا المبتدع لا يستغات بالرسول فإنه كفر".
الاستغاثة في الرد على البكري (ص: 335)
"Amma fadin wannan dan bidi'ar (yana nufin
Ibnu Taimiyya) cewa: ba a neman agaji da Manzon Allah to lallai KAFIRCI
ne".
Ma'ana; fadin Ibnu Taimiyya cewa; "ba za a
nemi agajin Annabi (saw) ba" nakasa Annabi (saw) ne da sukarsa,
"su'ul adabi" ne gare shi, kuma hakan kafirci ne.
Sufaye da wasu Ahlus Sunna sun yi Ittifaqi a kan
cewa; Dr. Idris Abdul'azeez ya yi "su'ul adabi", wato rashin ladabi
wa Annabi (saw). Sai dai sun banbanta ne wajen yanke masa hukunci
Su Ahlus Sunnan suna ganin Dr. Idris Abdul'azeez
dole a yi masa Nasiha, ya gyara Uslubi.
Su kuma Sufaye suka ce: A'a, ai tun da dai ya
tabbata ya yi magana ta rashin ladabi wa Annabi (saw) to JININSA YA HALASTA,
sawa'un ya tuba ko bai tuba ba, kuma ko da don kare Tauhidi ya fadi abin da ya
fada, bisa kyakkyawar niyya.
To wannan shi ya banbanta wadannan Ahlus Sunna da
kuma Sufayen.
Daga cikin shubuhohinsu su ne
Ai ya ambaci Annabi (saw) bayan ya ambaci wadanda
yake yi musu batanci.
Alhali ya ambaci Annabi (saw) ne don ya nuna cewa;
Sufaye suna neman taimako wajen yaye bala'i a wajen Shehunansu, wadanda suke
dauka a matsayin Waliyyai, to sai ya nuna cewa: a wannan babi hatta Annabi
(saw) ba a neman taimakonsa, saboda hakkin Allah ne shi kadai.
Don haka a nan ba an hada Annabi (saw) da Shehunan
ne a matsayinsu a wajensa ba, a'a, ya daidaita su ne a wajen kore musu hakkin
Allah. Ma'ana; hatta Annabi (saw) wannan ba hakkinsa ba ne.
Kuma ambaton Annabi (saw) bayansu ba zai zama
"su'ul adabi" gare shi ba, saboda kamar yadda Allah ya zargi
Kiristoci ne, inda ya jera Annabi Isa (as) tare da Malaman Coci da Fada-fadansu
wadanda suka rike su Alloli. Allah ya ce
{اتَّخَذُوا أَحْبَارَهُمْ وَرُهْبَانَهُمْ أَرْبَابًا مِنْ دُونِ اللَّهِ
وَالْمَسِيحَ ابْنَ مَرْيَمَ وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا إِلَهًا وَاحِدًا
لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ سُبْحَانَهُ عَمَّا يُشْرِكُونَ (31)} [التوبة: 31]
A cikin wannar Ayar, sai Allah ya ambaci Annabi
Isa (as) bayan ambaton Shehunan Kiristoci da Waliyyansu, wadanda aka mayar da
su tamkar Allah. Kuma babu wanda zai ga rashin Uslubi cikin haka, balle
"su'ul adabi".
Wasu kuma suka ce: ai ya ce wa Annabi:
"KO"…
Alhali Kalmar ko a nan ma'anarta ita ce:
"HATTA" (حتى), wacce take nuni ga kaiwa
kololuwa. Ma'ana; in dai a maganar hakkin Allah ne, na neman taimako, hatta
wanda ya fi dukkan halittu daraja, wato Annabi (saw), shi ma ba za a nemi
taimako a wajensa ba, a abin da hakkin Allah ne.
Saboda haka ni har yanzu ban ga wannan rashin
uslubi ko "su'ul adabi" da ake zargi a cikin maganar Malam Idris ba.
Kuma wannan shi yake nuna mana cewa; dole ne fa a
tsaya a tantance "Su'ul adabi" din nan, don kar 'yan bidi'a su cigaba
da zaluntar wadanda suke sukar Akidunsu, suke nuna bacinsu.
Daga karshe, kamar yadda yake wajibi ne mu girmama
Annabi (saw) mu yi masa ladabi, to wajabcin girmama Allah da yi masa ladabi da
kiyaye hakkinsa na Tauhidi, da nisantar yi masa shirka SHI YA FI GIRMA. Kuma
wannan shi ne abin da aka rasa daga Sufaye, musamman a raddin da suke yi wa
Malam Idris a wannan dambarwa. Mun ga misalai da dama na rashin ladabi ma Allah
daga wajensu, amma ba mu ga an tayar da hankali a kansu ba.
Dr
Aliyu Muh'd Sani (H)
1
May, 2023
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.