Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin 'Yan Kala-Kato Muminai Ne?

SHIN 'YAN ƘALA-ƘATO MUMINAI NE?

Allah ya ce:

{وَأَطِيعُوا اللَّهَ وَرَسُولَهُ إِنْ كُنْتُمْ مُؤْمِنِينَ } [الأنفال: 1]

Bisa zahirin wannar Ayar, tana nuni ga abubuwa masu yawa. Daga ciki

1- Sharadi ne wajen zaman mutum Mumini sai ya yi da'a wa Allah da Manzonsa.

2- Kuma a zahirin Ayar, da'a wa Manzon Allah ba shi ne da'a wa Allah kadai ba, a'a, kari ne a kan da'a wa Allah.

3- Babu sabani cewa; da'a wa Allah shi ne bin Alkur'ani da aiki da shi.

To, abin tambaya a nan shi ne

1) Shin da'a wa Manzon Allah shi ne bin Hadisai da aiki da su, ko kuma a'a?

2) Idan da'a wa Manzon Allah ba shi ne bin Hadisai da aiki da su ba, to menene da'a wa Manzon Allah?

3) Idan kuma da'a wa Manzon Allah shi ne bin Hadisai da aiki da su, to su 'Yan Kala-kato, wadanda suka kafirce wa Hadisai ba su kasance Muminai ba kenan?

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

[10:50 pm, 06/05/2025] Umar Aliyu Misau: HANYAR SANIN GASKIYA DA BATA

(1) ILIMI SHI NE ABIN DA YA GINU A KAN DALILI.

(2) ILIMI MAI AMFANI SHI NE WANDA AKA SAME SHI TA HANYAR ANNABI (SAW).

(3) DUK ABIN DA BA SHI DA DALILI SUNANSA BATACCE.

(4) SHIRIYA ITA CE BIN ABIN DA ALLAH YA AIKO MANZONSA DA SHI.

(5) ABIN DA ALLAH YA SAUKAR DA SHI A CIKIN LITTAFINSA, YA AIKO MANZONSA DA SHI, DA SHI NE AKE SAMUN SHIRIYA DA ILIMI DA IMANI.

(6) DUK WATA MAGANA TA WANI DAGA CIKIN MUTANE ANA AUNATA NE DA ABIN DA MANZON ALLAH (SAW) YA ZO DA SHI, IN TA DACE DA SHI TA ZAMA GASKIYA, IN KUMA TA SABA MASA TO TA ZAMA BATACCIYA.

(7) IN KUMA BA KA SAN CEWA: MAGANAR TA DACE KO TA SABA WA ABIN DA ANNABI (SAW) YA ZO DA SHI BA, TO KA JA KA YI SHIRU A KAN MAGANAR, SABODA BA A MAGANA SAI DA ILIMI.

(8) ZA A IYA SAMUN ILIMI TA HANYAR WANI WANDA BA ANNABI (SAW) BA, AMMA FA BA A LAMARIN ADDINI BA, SAI DA A LAMURAN DUNIYA, KAMAR YADDA A YAU MUKE KOYON ILMOMIN LIKITANCI DA KERE - KERE DAGA WAJEN KAFIRAI. AMMA ADDINI KAM, DOLE SAI TA HANYAR MANZON ALLAH (SAW) KAWAI.

(9) MANZON ALLAH (SAW) YA FI KOWA SANIN GASKIYA, KUMA YA FI KOWA SON SANAR DA MUTANE GASKIYA DA BAYANINTA, KUMA YA FI KOWA IKON SANAR DA GASKIYAN DA YIN BAYANINTA.

Shaikhul Islami Ibnu Taimiyya (r) ya ce

إن العلم ما قام عليه الدليل والنافع منه ما جاء به الرسول فالشأن في أن نقول علما وهو النقل المصدق والبحث المحقق فإن ما سوى ذلك - وإن زخرف مثله بعض الناس - خزف مزوق وإلا فباطل مطلق

مجموع الفتاوى (6/ 388)

Kuma ya ce

جماع "الفرقان" بين الحق والباطل والهدى والضلال والرشاد والغي وطريق السعادة والنجاة وطريق الشقاوة والهلاك: أن يجعل ما بعث الله به رسله وأنزل به كتبه هو الحق الذي يجب اتباعه وبه يحصل الفرقان والهدى والعلم والإيمان فيصدق بأنه حق وصدق وما سواه من كلام سائر الناس يعرض عليه فإن وافقه فهو حق وإن خالفه فهو باطل وإن لم يعلم هل وافقه أو خالفه لكون ذلك الكلام مجملا لا يعرف مراد صاحبه أو قد عرف مراده ولكن لم يعرف هل جاء الرسول بتصديقه أو تكذيبه فإنه يمسك فلا يتكلم إلا بعلم. والعلم ما قام عليه الدليل والنافع منه ما جاء به الرسول. وقد يكون علم من غير الرسول؛ لكن في أمور " دنيوية " مثل الطب والحساب والفلاحة والتجارة. وأما الأمور " الإلهية والمعارف الدينية " فهذه العلم فيها مأخذه عن الرسول فالرسول أعلم الخلق بها وأرغبهم في تعريف الخلق بها وأقدرهم على بيانها وتعريفها فهو فوق كل أحد في العلم والقدرة والإرادة وهذه الثلاثة بها يتم المقصود ومن سوى الرسول إما أن يكون في علمه بها نقص أو فساد وإما أن لا يكون له إرادة فيما علمه من ذلك فلم يبينه إما لرغبة وإما لرهبة وإما لغرض آخر وإما أن يكون بيانه ناقصا ليس بيانه البيان عما عرفه الجنان.

مجموع الفتاوى (13/ 135 - 136)

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

06 May, 2015

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments