DAGA CIKIN ƘA'IDOJIN FAHIMTAR ALƘUR'ANI – KASHI NA 2
Idan Aya ko Sura ta sauka saboda wani sababi, to
ba ta kebanta da sababin kawai ba, a'a, ta game sauran yanayi.
Lallai wannar ka'ida ce mai matukar amfani. Idan bawa ya kiyaye wannar ka'ida zai samu alheri da ilimi mai yawa, kamar yadda in ya yi watsi da ita, ya kawar da kansa daga gare ta zai rasa ilimi mai yawa, kuma zai afka cikin kuskure mai girma.
Wannar
ka'ida masu tahqiqi cikin Malaman Usulul Fiqhi da wasunsu sun yi ittifaqi a
kanta. Don haka duk lokacin da ka ba ta hakkinta, ka san abin da masu tafsiri
suka fada na sabuban saukar Ayoyi to za ka san cewa; kawai tamkar misalai ne
don bayanin ma'anonin lafuzan Ayoyin, ba –wai- ma'anonin Ayoyin sun takaita a
kan sabuban saukan nasu ne ba.
Idan Malaman Tafsiri suka ce: Aya ta sauka a kan
kaza da kaza…, abin nufi shi ne: wannan sababin yana cikin ma'anar Ayar, yana
cikin abin da Ayar take nufi. Saboda Alkur'ani – kamar yadda ya gabata – ya
sauka ne don shiriyar al'umma, tun daga farkonta har karshenta, a duk inda
take, a duk yanayi da halin da take ciki.
Allah ya umurce mu da tunani da sanya lura
(tadabburi) ga littafinsa, don haka idan muka lura da lafuza na gamayya, muka
fahimci cewa; ma'anar lafuzan sun kunshi abubuwa da yawa, to saboda me za mu
fitar da wani abu daga cikin ma'anonin, tare da cewa; ma'ana irinta ko
makamancinta za ta shiga cikin ma'anar lafazin?
Saboda haka ne Abdullahi bn Mas'ud ® ya ce:
"Idan ka ji an ce: {Ya ku wadanda suka yi imani}, to ka kashe kunnenka,
don imma alheri za a umece ka da aikatawa ko kuma za a hane ka ne a kan aikata
sharri".
Don haka duk lokacin da ka zo kan bayanin Siffofin
Allah da Sunayensa da abin da ya cancanta na kamala, da abin da ya tsarkaka
daga gare shi na tawaya, to ka tabbatar masa da cikakkiyar ma'anar da Allah ya
tabbatar ma kansa, kuma ka tsarkake shi daga dukkan abin da ya tsarkake kansa
daga gare shi. Haka nan idan ka iso kan labari a kan Manzanninsa da
Littatafansa da Ranar Karshe, da ma dukkan abubuwa da suka wuce ko masu zuwa
nan gaba, to ka tabbatar a yanke babu shakka cewa; duka gaskiya ne a bisa hakikanin
yadda yake. Kai, ka dauka a yanke cewa; gaskiya ne mai kololuwar daraja cikin
gaskiyar magana da zance.
Haka kuma idan Allah ya yi umurni da abu to ka ka
duba ma'anarsa da dukkan abin da zai shiga cikin ma'anar, da abin da ba zai
shiga cikinsa ba, kuma ka san cewa; lallai wannan umurni an fiskantar da shi ne
ga dukkan al'umma gaba dayanta, haka a hani ma.
Wannan ya sa sanin iyakokin ma'anonin abin da
Allah ya saukar wa Manzonsa shi ne tushen dukkan alheri da rabauta, jahiltarsa
kuma shi ne tushen dukkan sharri da hasara.
Don haka lallai kula da wannar ka'ida da yin aiki
da ita babban abin taimako ne wajen sanin iyakokin ma'anonin abin da Allah ya
saukar wa Manzonsa.
Lallai Alkur'ani ya hada manyan ma'anoni kuma mafi
fa'ida da gaskiya cikin kyawawa lafuza bayyanannu, kamar yadda Allah ya ce: {Ba
za su zo maka da wani misali ba face mun zo maka da gaskiya da kuma bayani mafi
kyau} [Al-Furqan: 33].
Saboda haka, amfani da wannar ka'ida wajen
Tafsirin Alkur'ani shi zai bude ma bawa kofofin ilimin Alkur'ani da sanin
ma'anoninsa.
Dr Aliyu Muh'd Sani (H)
18 May, 2018
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.