Ticker

6/recent/ticker-posts

Sun Yi Imani Amma Su Mushrikai Ne

Akwai mutane da yawa suna Sallah, suna Azumi, har suna zuwa Hajji, suna amsa sunan Musulmai, amma abin takaici, suna shirka ma Allah. Suna kiran wanin Allah, suna neman taimako a wajensa, suna rokonsa biyan bukata. Kamar wanda zai kira Annabi, ko Waliyyi ko wani salihin bawa, yana neman taimakonsu, ko yana rokonsu biyan bukata, ko neman ceto a wajen Allah. Idan an yi musu inkari sai su ce Tawassuli suke yi, saboda mutanen da suke kira suna da kusaci a wajen Allah, suna da alfarma a wajensa. Kamar yadda Allah ya bayyana mana yadda suke a fadinsa

{والذين اتخذوا من دونه أولياء ما نعبدهم إلا ليقربونا إلى الله زلفى} [الزمر: ٣].

{Wadanda suka riki Majibinta koma bayan Allah (sukan ce): ba ma ba bauta musu sai don su kusantar da mu zuwa ga Allah mu samu kusaci}.

Wannan shi ne shubuhar mushrikai a kowane zamani, sun riki wasu koma bayan Allah ne don su yi musu iso wajen neman biyan bukata a wajen Allah.

Irin wadannan su ne wadanda sun yi imani da Allah, amma kuma suna shirka ma Allah. Kamar yadda Allah ya ce

{وما يؤمن أكثرهم بالله إلا وهم مشركون} [يوسف: ١٠٦].

{Mafi yawansu ba sa imani da Allah face su Mushrikai ne}.

Sai Allah ya tabbatar musu da imani, kuma ya tabbatar musu da shirka. Duka a lokaci guda; suna imani, kuma suna shirka. Shi ya sa Magabata suka fassara da cewa: imaninsu shi ne suna cewa; Allah ne ya yi halitta, amma kuma suna shirka ma Allah a cikin ibada.

To irin wannan imani ba shi da amfani. Ba zai amfani bawa ba a wajen Allah. Don kawai ya yarda Allah shi ne Mahalicci, shi ya halicci sama, shi ya halicci kasa, shi ya halicci dukkan halittu, amma yana rokon Inyas biyan bukata, yana rokon Tijjani yaye bala'i, yana neman taimako a wajen Annabi (saw) yana rokonsa ceto, to ko shakka babu ya zama mushriki, imaninsa da Allah ba zai amfane shi. Ba zai tsira a wajen Allah ba, a wuta zai dawwama.

Allah ya mana tsari da tabewa.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
11 June, 2023

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments