Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanyar Koyon Ilimin Fikihu

HANYAR KOYON ILIMIN FIƘHU

Daga cikin ababen mamakin malumtar zamani, -wai- dangantuwa ga Mazhaba aibi ne. Alhali babu wani Malami da yake da kyakkyawan ambato a cikin al'umma face akwai Mazhabar da ake danganta shi gare ta.

Idan kana karanta littatafan da suke hakaito maganganun Malamai a kan mas'alolin Addini, za ka ga bayan Mazhabobi huɗu mafiya shahara, za ka samu suna ambaton Mazhabar Zahiriyya da Mazhabar Ahlul Hadith. Abin da zai nuna maka cewa; dukkan Malaman Muslunci ba su fita daga Mazhaba ba.

Abin da ya janyo wannan mummunan tunani shi ne; wasu masu shiga harkar ilmi, sun ɗauka Mazhaba ita ce bin ra'ayi da jefar da Nassi. Ko shi ne taƙlidancin malami da saɓa wa Annabi (saw), a mas'alolin Fiƙhu. Alhali abin ba haka ba ne. Bin Mazhaba shi ne aiki da ƙa'idoji da "Usul" na wani Imami daga cikin Imaman Shiriya a wannar al'umma, irin su Imamu Malik d.s, wajen fahimtar Nassoshin Shari'a, da fitar da hukunci daga cikinsu.

Abin nufi, fahimtar mas'alolin Shari'a bisa ƙa'idojin wata Mazhaba, da gina Ijtihadi a kansu abu ne sananne a wajen Malaman al'umma, Mujtahidai masu fatawa.

Kasancewar bin Mazhabobi tafarkin Malamai ne, shi ya sa yana daga cikin abin da aka soki Imam Muhammad bn Abdilwahhab - don a yi ɓatanci wa da'awarsa - wai ya saɓa wa Mazhabobin Fiƙhu. Wanda hakan ya sa ya yi ta bayani don nuna saɓanin haka. Saboda shi Mazhabar Hanabila yake bi.

Haka in ka dawo cikin almajiransa da 'ya'yansa da zurriyarsa, za ka samu duka suna bin Mazhaba. Wannan ya sa har yau, a ƙasar Saudiyya, tsarin karatun Fiƙhu da Alƙalanci ya ginu ne a kan Fiƙhun Mazhabar Hanabila.

Haka Malamanmu a can suka yi ta yi mana wasiyya da cewa; idan za mu karanci Fiƙhu, hanyar Malamai ita ce; koyon Fiƙhun bisa Mazhaba guda ɗaya cikin Mazhabobin nan huɗu.

A takaice, hanyar da Malamai suke bi wajen neman ilimin Fiqhu shi ne koyon Fiƙhu bisa ɗaya daga cikin Mazhabobi yardaddu.

Da wannan za ka fahimci cewa; bin Mazhaba ko rashin bin Mazhaba ba shi da alaƙa da Aƙida ko Salafiyya ko Da'awar Tauhidi da Sunna. Shi ya sa ƙasar Saudiyya mai bin Aƙidar Salafiyya, a Fiƙhu Hanbaliyya suke bi.

Masu bin Aƙidar Salafiyya a ƙasashen Larabawan Afirka (المغرب العربي), a Fiƙhu Malikiyya suke bi. Dss..

Don haka duk wanda ka gani yana sukar bin Mazhaba to ka sani ya jahilci Manhajin Malamai Limaman Shiriya a cikin al'umma.

Kuma sai ka same shi da bin ra'ayoyin da magabata sun ƙaurace musu, sun yi watsi da su, ra'ayoyi shazzai, da ƙirƙiran ra'ayoyi masu rushe ƙa'idojin Shari'a, bayan magabata sun gama saɓani a kan mas'alar, kamar ƙirƙiran ra'ayi na uku, bayan magabata sun yi saɓani zuwa ƙauli biyu, wanda hakan ɓata ne, da fita daga Ijma'in al'umma.

Don haka nake yi wa ɗalibai wasiyya, da su koma su koyi ilimin Fiƙhu ta hanyar da Malamai suke koyonsa, wannan shi zai ba su daman yin kyakkyawar fahimta ga mas'alolin Addini, su dena faɗawa cikin ruɗani, a munasabobi, da faɗawa cikin munanan ra'ayoyin da Malamai suka ƙaurace musu, kamar ra'ayin "Ba Juma'a, Ba Azahar", idan Eidi ya haɗu da Juma'a.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments