Ticker

6/recent/ticker-posts

Kyautata Mu'amala Da Mutane

Idan kana so ka rabauta a mu'amalarka da mutane, to ka mu'amalance su saboda Allah ta hanyoyi kamar haka

1- Duk wata Ibada ta kyautatawa ga mutane - kamar sadaka ko ihsani da yi musu alheri - ka yi ta don neman yardar Allah, kar ka yi don su mutanen, don su yaba maka, ko don tsoron kar su zarge ka.

2- Ka ji tsoron Allah game da mutane, amma kar ka ji tsoronsu a hanyar Allah.

3- Ka kyautata musu don neman lada da yardar Allah, ba don su mutanen su saka maka ba.

4- Ka kame hanunka da harshenka daga cutar da su da zaluntarsu saboda tsoron Allah ba don tsoronsu ba.

Imam Ibnu Rajab ya ce

((والإحسان الواجب في معاملة الخلق ومعاشرتهم: القيام بما أوجب الله من حقوق ذلك كله، والإحسان الواجب في ولاية الخلق وسياستهم، القيام بواجبات الولاية كلها)).

جامع العلوم والحكم ت ماهر الفحل (1/ 428)

((Kyatatawa na wajabi wajen mu'amalantar mutane da zamantakewa da su shi ne ka yi abin da Allah ya wajabta maka game da su, na ba su hakkokinsu gaba daya. Kyautatawa na wajibi wajen mulkan mutane da jagorantarsu a siyasa shi ne tsayuwa wajen sauke abubuwan da Allah ya wajabta a kan shugaba na hakkokin talakawa)).

Annabi (saw) ya ce

«أكمل المؤمنين إيمانا أحسنهم خلقا»

سنن أبي داود ت الأرنؤوط (7/ 70)، سنن الترمذي ت شاكر (3/ 458)

((Wanda ya fi cikan Imani cikin Muminai shi ne wanda ya fi su kyawawan halaye)).

Dr. Aliyu Muh'd Sani

11 June, 2022

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments