Ticker

6/recent/ticker-posts

Salatul Ga'ib: Tsakanin Sunna Da Bidi'a

Daga cikin manyan ta'adi da aka yi wa Ilimin Shari'a a wannan zamani, da sunan "Bin Sunna", akwai mayar da saɓani tsakanin Mazhabobin Fiƙhu a matsayin saɓani tsakanin Sunna da Bidi'a. Alhali saɓani a mas'alolin Fiƙhu saɓani ne tsakanin ra'ayi mai rinjaye da maras rinjaye, da ra'ayi sahihi da ra'ayi mai rauni, ko ɓatacce. Saboda asali duka Mazhabobin Fiƙhu ba su fita a shiriyar Annabi (saw) ba, balle a siffanta su da Bidi'a.

Haka kuma dalilan Fiƙhu suna da yawa, ba su taƙaita a kan Nassin Alƙur'ani da Hadisi ba. A'a, daga cikin dalilan Fiƙhu akwai Zahirin Alƙur'ani da Hadisi, da "umumi", da "muɗlaƙi", da Ijma'i, da Ƙiyasi, da Ƙaulin Sahabi, da Aikin mutanen Madina, da "Sadduz zari'a",,, da sauransu...

Saboda haka dalilin Fiƙhu bai taƙaita a kan Nassin Aya ko Nassin Hadisi kaɗai ba.

Bayan haka Malamai suna lura da dalalar Ayoyi da Hadisan.

A Hadisai, dalalar maganar Annabi (saw) daban take da dalalar aikinsa (saw),

haka dalalar "Taƙriri" ta sha banban da dalalar magana da aikinsa (saw).

Haka dalalar umurni da hani, akan samu abin da zai canza su daga asalin dalalar tasu. Shi ya sa sai Malamai sun tattara dukkan dalilan mas'ala, sun kalle su a gamayyarsu, sai su fitar da hukunci.

To rashin sanin irin waɗannan, ko rashin ɗaukarsu da muhimmanci shi ya sa waɗanda suka naɗa kawunansu a matsayin Malamai suke raba mas'alolin tsakanin Sunna da Bidi'a. Wanda ya zo a Hadisin da ya sani ya ce: Sunna. Wanda kuma ya saɓa masa ya ce Bidi'a, saboda ya zo a dalilin da bai sani ba. Kuma ba tare da fahimtar Hadisin da ya riƙen ba.

To ka ga ashe jahilci ita ce matsalar mai bin irin wannan salo.

To irin haka ne yake sa ka ji wani ya fito yana cewa: Yin "Salatul Ga'ib" wa mutumin da ya mutu a garin da Musulmai za su yi masa Sallah Bidi'a ne.

To ta yaya ya zama Bidi'a, alhali Malaman Fiƙhu sun fahimci yin hakan ta hanyar wasu dalilai daga cikin dalilan Shari'a da ake lura da su?!

Yin "Salatul Ga'ib" ma wanda za a yi masa Sallah a garin da ya mutu shi ne fahimtar Malamai A'imma, irin su: Imamu al-Shafi'iy, da Imamu Ahmad, da Ibnu Hazm, da Jumhurin Salaf.

Ka ga dai waɗannan duka Malamai ne masu bin Hadisi, kuma da Hadisai suka kafa hujja a kan fahimtarsu, kamar Hadisan da Annabi (saw) ya yi Sallah ma wasu mutane suna cikin ƙabarburansu, alhali an yi musu Sallah. Shi ya sa Imamu al-Shafi'iy ya ce

"ورويتم عن النبي صلى الله عليه وسلم: أنه صلى على قبر، والميت في القبر غائب، وإنما الصلاة دعاء للميت، وهو إذا كان بيننا ملففا يصلى عليه فإنما ندعو له بالصلاة بوجه علمناه، فكيف لا ندعوا له غائبا وفي القبر بذلك الوجه؟".

معرفة السنن والآثار (5/ 315)

Ka ga sai Imamu al-Shafi'iy ya yi bayanin cewa: shi ma wanda yake cikin ƙabari, bayan an yi masa Sallah "ga'ib" ne, wato wanda ba ya nan ne, amma Annabi (saw) ya yi masa Sallah, bayan an masa Sallah.

Amma a hakan wani da ko sunan dalibi na gaske bai cancanci a kira shi ba, zai zo yana siffanta hakan da Bidi'a?!

Don haka Malamai suna da hanyoyi masu yawa na fahimtar hukunce - hukuncen mas'alolin Fiƙhu daga Ayoyi da Hadisai, ba -wai - bisa zallan ra'ayi suke magana ba.

Ala ayyi halin, mas'alolin Fiƙhu ba a babin Sunna da Bidi'a suke ba, suna babin dadai ne ko ba dadai ba. Ko mai ranjaye da maras rinjaye.

Mas'alolin Aƙida ne suke babin Sunna da Bidi'a, saboda su babin labarai ne, waɗanda ake so ka gaskata, idan ka saɓa to kamar ka ƙaryata ne. Bidi'a kuwa ita ce saɓa Alƙur'ani da Sunna da Ijma'i.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments