Ticker

6/recent/ticker-posts

Sheikh Nasirudden Albaniy Ya Tona Asiri

A bayaninsa game da Manhajin Kungiyar Ikhwan Babban Malamin Hadisin ya ce:

إن منهج الإخوان كتل ثم ثقف ثم لا شيء، ما فيه إلا التكتل الأعمى لا ثقافة ولا شيء بدليل، و كاد يمضي قرن من الزمان على الإخوان المسلمين في مختلف البلدان وهم على النظام العسكري مكان راوح لما لأن منهجهم هكذا يوحي إليهم، فهم لا يتقدمون لا علما لا عقيدة لا سلوكا، كما هم تماما لا يمكن أن تجد أخا من الإخوان المسلمين ينهج منهج السنة ظاهرا على الأقل ظاهرا، تجد أحدهم يتشبه بحسن البنا يأخذ من لحيته ويجعلها كما يقول بعض الفقهاء الحنفية في كتب الأحناف، كما يفعل الأعاجم أو المغاربة، فهم يهتمون بالاقتداء بحسن البنا ولا في بالهم الاقتداء بسيد الأنبياء عليه الصلاة والسلام

سلسلة الهدى والنور للعلامة الألباني الشريط رقم: 600b

"Lallai Manhajin Ikhwan shi ne a tara mutane (kungiya) sa'annan a wayar da su (game da harkar siyasa), daga wannan kuma shi kenan. Babu komai a cikin Manhajin face kungiyartar da mutane suna biyayya ido rufe, babu wayewar babu yin abu bisa dalili.

Yanzu kusan karni guda (shekara 100) da kafa kungiyar Ikhwan a kasashe daban daban, amma suna nan a kan tsari irin na soja (obey before complain), saboda haka Manhajin nasu yake nuna musu. Ba sa cigaba, sawa'un a ilimi ne ko a Aqeeda ko a kyawawan dabi'u, kamar yadda suke ne, ba za ka samu Dan Ikhwan yana bin Manhajin Sunna a bayyane ba, alal akalli a bayyane, kawai sai dai ka samu kowane daya daga cikinsu yana koyi da Hasanul Banna, yana aske gemunsa, yana rage shi kamar yadda wasu Malaman Hanafiyya a cikin littatafansu suke fadi, kamar yadda ajamawa suke yi, ko mutane Magrib. Duka damuwarsu ita ce koyi da Hasanul Banna ba ruwansu da koyi da shugaban Annabawa (as)".

Shaikh yana bayani ne a kan yadda Kungiyar Ikhwan ta zama ba ruwanta da damuwa da Sunna, balle kira gare ta, balle kuma yakar Bidi'a da raddi ga 'Yan Bidi'ar. Wannan ya sa ba ruwansu da kira ga Tauhidi da Sunna da yakar Shirka da Bidi'o'i, kawai damuwarsu ita ce kafa Gomnati don su yi mulki.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments