Article Citation: Suleiman, M. (2025). Sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano [Master’s dissertation]. Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
SAUYE-SAUYEN ZAMANI A WASU SARAUTUN SANA’O’IN GARGAJIYA DA AYYUKANSU A GARIN KANO
Na
SULEIMAN Musa
Email: musasuleiman424@gmail.com
Phone: 08061256096
5.0 Shimfiɗa
Wannan babi shi ne na ƙarshe a wannan bincike, a nan ne aka taƙaita bayanin wannan bincike gaba ɗaya. Sannan aka
shimfiɗa shawarwari da ake ganin idan aka bi su a fagen nazari, to lallai nan ba
da jimawa ba za a fitar da jaki daga duma. Haka kuma, an kawo sakamakon wannan
bincike da manazarta daga ƙarshe.
5.1 Taƙaitawa
Wannan kundi yana ɗauke da manyan
babuka guda biyar. Babi na ɗaya shi ne gabatarwa, wanda a nan ne
aka shimfiɗa tsarin wannan bincike. Sannan an kawo dalilan bincike da manufofin
bincike da maƙasudan bincike da tambayoyin bincike da
farfajiyar bincike da muhimmancin bincike. Haka kuma, an yi waiwayen tubalan
kalmomin matashiyar wannan bincike, inda aka waiwayi kalmomi irin su sarauta,
da asalin sarauta, da sana’a, da asalin sana’o’in Hausawa na gargajiya, da
ma’anar kalmar gargajiya, da kuma waiwayen tarihin masarautar Kano.
Babi na biyu, shi ne inda aka yi bitar
ayyukan da suka gabata, wato aka yi bitar kundayen digiri na uku da na biyu da
kuma na farko. Sannan an yi bitar maƙalu cikin mujallu
da maƙalu a tarukan ilimi da bugaggun
littattafai, daga ƙarshen babin kuma aka kawo hujjar ci
gaba da wannan bincike.
Babi na uku kuwa, shi ne aka yi wa take
da hanyoyin gudanar da bincike, inda aka yi ziyara da tattauna da waɗanda suke da
masaniya a kan wannan bincike. Haka kuma, an tuntuɓi masana da
manazarta don samun ƙarin haske a kan wannan bincike. Sannan
an nazarci rubuce-rubuce masana da suka shafi wannan aiki. Haka kuma, an
tuntubi kafafen yaɗa labarai da jaridu da kafafen sadarwa
na intanet. Haka kuma, an kawo hanyoyin tantance bayanan bincike da kuma ra’in
bincike.
Babi na huɗu, an yi bayani a
kan sarautun sana’o’in Hausawa na gargajiya, inda aka dubi sarautar Sarkin ɗori, da Sarkin
fawa, da Sarkin gini, da kuma Sarkin ƙira. Baya ga haka,
an yi bayani a kan asalin sarautun sana’o’in gargajiya da sarautun a jiya da
kuma a yau. Haka kuma, an yi bayani a kan taƙaitaccen tarihin sarakunan da ke riƙe da waɗannan sarautu na
sana’o’in gargajiya a garin Kano. An yi bayanin a kan haƙiƙanin sarautun da ayyukansu da ƙananan sarakunan waɗannan sana’o’i. Sannan, an yi bayani a
kan ayyukan sarakunan sarautun da sauye-sauyen da ke tattare da al’adun
sarautun sana’o’in Hausawa na gargajiya. Bugu da ƙari, an yi bayanin matsayi da dangantakar sarautun sana’o’in Hausawa na
gargajiya.
Babi na biyar kuwa, bayan taƙaitaccen bayani a kan binciken, an fitar da sakamakon da aka samu bayan an kammala binciken. Haka kuma, a ƙarshen aikin, an bayar da shawarwarin da za su inganta waɗannan sarautun. Wasu shawarwarin, an bayar da su ga masu riƙe da waɗannan sarautun, wasu kuma, an bayar da su ga hukumomi da jami’o’i da sauran makarantu da cibiyoyin ake gudanar da bincike na ilimi.
5.2 Shawarwari
Wannan kundi ya kawo wasu shawarwari da
yake ganin idan aka bi su, za su taimaka wajen kawo ci gaba da haɓaka sarautun
sana’o’in gargajiya a garin Kano. Daga cikin waɗannan shawarwari
akwai:
1.
Akwai buƙatar inganta sarautun sana’o’in gargajiya a Masarautar Kano,
kasancewar sarautu ne na gado, da suke da ƙima a idanun al’umma. Yin hakan zai ƙara ɗaga darajar
sana’o’in da kawo ci gaba ga masu gudanar da waɗannan sana’o’i na
gargajiya a garin Kano.
2.
Ba da sarautun sana’o’in gargajiya ga
nagartattun mutane waɗanda suka cancanta zai ƙara kankaro martabar sarautar gargajiya a idanun al’umma, musamman a ce sarautun an ba da su ga masu sha’awar sarauta. Hakan zai taimaka wajen yaɗuwa da kuma tsare ƙyawawan al’adun masarautar Kano.
3.
Al’ummar garin Kano suna mutuƙar ganin ƙimar sarautar
gargajiya. Wannan dalilin ne ya sanya mutanen karkara da na alƙarya suke mutuƙar biyayya ga masu
sarautun gargajiya. Don haka, yana da mutuƙar kyau masu riƙe da irin waɗannan sarautu na
sana’o’in gargajiya su ci gaba da nuna halaye na gari waɗanda al’umma za su
yi koyi da su.
4.
Yana da mutuƙar ƙyau masarautar Kano ta ci gaba da
jajircewa wajen sanin halaye da kyawawan ɗabi’u waɗanda za a naɗa a waɗannan sarautu na
sana’o’in gargajiya. Yin hakan zai ƙara kare daraja da
martabar masarautar Kano a idanun al’umma da duniya baki ɗaya.
5.
Akwai bukatar jami’o’i da manyan
makarantu da cibiyoyin gudanar da bincike na ilimi, su ci gaba da yin nazarin
al’adun ire-iren waɗannan sarautun gargajiya domin fito da
alfanun da ke cikinsu, domin taskace su. Dalilin kuwa, a kullum ana samun
sauye-sauyen waɗansu ala’du, wasu kuma suna salwacewa.
5.3 Sakamakon Bincike
Wannan bincike da
aka gabatar, ya samar da sakamako da ake ganin samuwar sa shi zai tabbatar da
kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Daga cikin sakamakon da
wannan bincike ya samo, sun haɗa da:
1.
Kundin ya fito da yanayin da wasu
sarautun sana’o’in gargajiya suke ciki a yanzu, inda ya kawo yanayin sarautun
sana’o’in gargajiya da suka haɗa da: Sarautar Sarkin ƙira da sarautar Sarkin ɗori da sarautar
Sarkin gini da kuma ta Sarkin fawa.
2.
Binciken ya gano ayyukan sarautun
sana’o’in gargajiya da sauye-sauyen da aka samu a yanzu, inda aka kawo wasu
abubuwan da suka samu a sakamakon tasirin zamani da addini Musulunci a cikin
tsarin waɗannan sarautu na sana’o’in gargajiya a garin Kano.
3.
Aikin ya lalubo muƙamai da al’adun da ke tattare da sarautun
sana’o’in gargajiya, inda aka fito da hakimai da sarautun yanki da suke taimaka
wa waɗannan sarakuna wajen gudanar da ayyukansu.
4.
Kundin ya binciko matsayi da
dangantakar sarautun sana’o’in gargajiya musamman a garin Kano.
Abdulƙadir, Ɗ. (1979). Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Da da Na Yanzu. London: Great Britain by Bulter &
Tanner Limited.
Abdullahi, M.
(2021). Gudummawar Finafinan Hausa Wajen Raya Sana’o’in Gargajiya Hausawa.
Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Abubakar, A. S. (2008). Sarautar
Sallama da ta Sarkin Hatsi a Fadar Kano. Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Adamu, D. (2019).
The Role Of Colonial Administration in the Depositiion of Traditional Rulers in Katsina Emirate 1903-1960. M. A Dessertation.
Department Of History. Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo
University.
Adamu, M. T
(1997). Asalin Hausawa da Harshensu.
Kano: Ɗansarkin Kura Publishers Limited.
Ado, A. (2017). Ra’o’in Bincike Kan Al’adu Hausawa.
Katsina: Kanki Media Enterprises.
Albarkawa, S. Y.
(2023). Sauye-Sauyen Wasu Al’adu A Fadar Zazzau. Kundin Digiri na Biyu, Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe. Kaduna: Jami’ar Jihar Kaduna.
Alhassan, H. da
Wasu. (1988). Zaman Hausawa. (Bugu na
Biyu). Lagos: Islamic Publition Bureau.
Aliyu, B. (2004). Tsafe Garin ‘Yandoto: Yanayi da Tsarin
Sarautun Gargajiya a Ƙasar Tsafe. Kundin Digiri na Biyu,
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Aliyu, L. (2017).
Nazarin A Kan Matsayi da Dangantaka Tsakanin Sarki da Hakimai a Fadar Katsina.
Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Almajir, T. S.
(2009). Tasirin Zamani a Kan Rayuwar Hausawa Matasan Kano. Kundin Digiri Na
Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jam’ar Bayero.
Amin, M. L.
(2004). Falsafar Bahaushe A Kan Rayuwar Ɗan’adam. A cikin
Mujallar Algaita, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Argungu, A. I.
(2017). Sarauta a Daular Kabi Jiya da
Yau. Sokoto: University Press Limited Usmanu Danfodiyo University.
Auta, A. L.
(1986). Gudummawar Mawaƙan Hausa Dangane da Adana Tarihi.
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Bahago, A. A
(1998). Kano ta Dabo Tumbin Giwa: Tarihin
Unguwanni Kano da Mazaunanta da Ganuwa da Ƙofofin Gari. Kano: Munawwar Books Foundation. (MBF).
Bargery, G. P.
(1934). A Hausa-English Dictionary and
English-Hausa Vocabulary. Zaria: Ahmadu Bello University Press.
Bello, A. M.
(1991). Tasirin Zuwan Turawa Kan Sarautun Gargajiya Na Ƙasar Hausa. Kundin Digiri na Biyu, Sahen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano:
Jami’ar Bayero.
Bunza, A. M.
(2006). Gadon Feɗe Al’ada. Jerin Littattafan Cibiyar Nazarin Al’adun Hausa. Lagos: Tiwal Nigerian Limited.
Bunza, A. M.
(2009). Narambaɗa. Lagos: IBRASH Islamic Publication Centre Limited.
Bunza, A. M.
(2013). Makamin Dimokraɗiyya A Falsafar Al’ada. Takardar da aka
gabatar a matsayin jagora ga takardun Al’ada a taron ƙara wa juna sani na ƙasa na farko a kan
Harshe da Adabi da Al’adun Hausawa, a
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Bunza, A. M.
(2022). Tatsaka Mai Wuyar Sani (Lalurar Makafta a Al’adance, da Addinance, da
Zamanance). Maƙalar da Aka Gabatar a Taron Ƙungiyar Makafi Ranar 08 ga Oktoba, 2022 a Jahar Kebbi.
Bunza, A. M.
(2023). Sarauta a Tsarin Ikon Ƙasar Hausa (Yadda
Take da Yadda Ake Samar da Ita). Maƙalar da Aka
Gabatar a Taron Naɗin Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo a Matsayin Sarkin Malaman Hausa
na Afrika, a Fadar Sarkin Hausawan Afrika Dr. Abdulƙadir Koguna Da ke Unguwar Yola a Cikin Birnin Kano..
Bunza, D. B.
(2016). Gudummawar Sarautun Tsaro a Arewacin Nijeriya. Takardar da Aka Gabatar
a Taron Ƙara wa Juna Ilimi na Ƙasa a Tsangayar Fasaha da Addinin Musulinci. Sakkwato:
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Chen, X. da Wasu (2010).
Perceived Social Change and Childrearing Attittudes In China. Eur Psychol, 15:260-270 http://dx.doi.org/10.1027/1016-9040/a000060.
CSNL (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya.
Kano: Jami’ar Bayero.
Ɗan’alhaji, A. (2016). Shin Ko Akwai
Wata Aba Ita Falsafa a Adabin Hausa? Cikin
Kadaura Journal of Hausa Multidisplinary Vol1, No 2, Department of Nigerian
Languages and Linguistics. Kaduna: Test and Print Ventures.
Ɗan-Iya, I. A. (2020). The Dabo Of Kano. Kano: MJB Printers.
Ɗanjuma, S. A. (2021). Kwatanta Wasu
Al’adun Sarauta a Tsarin Zamantakewa Na Fadar Kano Da Dass. Kundin Digiri na Biyu, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Kano:
Jami’ar Bayero.
Ɗantiye. N. I. (1989). Taxation And
Hakimi’s Envoys: The Status of Ribats of Rano, Ƙaraye, Ɓaɓura, Gwarzo, and Their Residents Rulers
Within the Administration System of Kano Emirate. (Editor). Barkinɗo, B. K. In Kano
and Some of Her Neighbours. Pp
79-103. Department of History. Kano: Bayero university.
Daura, R. J.
(2012). Sarautun Ƙasar Daura Da Muhimmancinsu ga Al’umma. In
Amfani, A. H. et,al. (Editors.), Champion of Hausa Cikin Hausa: A Festschrift In Honour Of Ɗalhatu Muhammad. Pp
468-472. Department Of African Languages And
Culture. Zaria: Ahmadu Bello University Press.
Dawaki, I. A.
(1994). Ɗorayi: A History of Economic and Social
Trasformation In the 19th and 20th Centuaries Kano Emirate. M. A. Dessertation, Department Of History: Sokoto: Usmanu
Danfodiyo University.
Dobie, A. B.
(2002). Theory Into Practice: An
Introduction To Literary Critism. Internartional Students Edition. Second
Edition. USA: Wadswarth Cengage Learning.
Dokaji, A. A
(1958). Kano ta Dabo Ci gari. Zaria:
Northern Nigerian Publishing Company limited.
Durumin Iya, M. A.
(2006). Tasirin Kimiyya da Ƙere-Ƙeren Zamani a Kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya. Kano: Print Services.
Fadama, M. (2014).
Sarkanci a Lardin Sakkwato. Kundin Digiri na Uku, Sashen Nazarin Harsunan
Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Farouk, A. U.
(2O21). Nazarin Sana’ar Rinin Fata A Unguwar Daurawa Da ke Ƙaramar Hukumar Dala a Birnin Kano. Kundin Digiri na Biyu,
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Garba, C. Y.
(1991). Sana’o’in Gargajiya a Ƙasar Hausa.
Ibadan: Spectrum Books Limited.
Gaya, A. M.
(1998). Tsarin Milkin Gargajiya Jiya Da Yau Musamman A Kano. Kundin Digiri na
Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Gaya, A. M.
(2012). Tasirin Siyasa A Masarautun Gargajiya, Musamman A Sakkwato Da Katsina
Da Kano Da Daura Daga 1960 Zuwa 2019. Kundin Digiri Na Uku, Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Gulbi, A. S.
(2000). Sarautun Gargajiya a Ƙasar Gummi Jiya da
Yau. Kundin digiri na ɗaya, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya.
Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Gusau, S. M.
(1988). Makaɗan Fada Sigoginsu da Yanaye-Yanayensu Musamman a Ƙasar Sakkwato. Kundin Digiri na Uku, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya.
Kano: Jami’ar Bayero.
Gusau, S. M.
(2002). Salihu Jankiɗi Sarkin Taushi. Kaduna: Baraka Press and Publishers Limited.
Gwangwazo, M. A.
(2001). Tarihin Sarakunan Kano 1805-2003.
Kano: Truimph Publication Company.
Gwangwazo, M. A.
(2004). Tarihin Sarkin Kano Kafin Jihadi
Littafi na 1 da 2. Kano: Truimph Publishing Company.
Gwangwazo, M. A.
(2010). Tarihin Sarkin Kano Muhammadu
Rumfa: Zuri’ar Sarkin Kanawa Gidan Makaman Kano Rumfa. Kano: Ja’afaru’s
Press.
Hamji, M. (2023).
Dangantaka a Tsakani Wasu Muƙaman Masarautar
Kano da Gombe. Kundin Digiri na Biyu, sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano:
Jami’ar Bayero.
Hussaini, I.
(2008). Gwarzayen Masarautar Kano A
Shekaru 45 (1963-2008) Na Ado Bayero A Milkin Kano. Kano: Talles Consulting
Company Limited.
Ibrahim, O. F.
(2001). Prince of the Time: Ado Bayero
and Transformation of Emiral Authority in Kano. Canada: Africa World Press.
Isma’il, H. A.
(2011). Tasirin Sarautun Gargajiya A Cikin Littafin Magana Jari Ce 1-3. Kundin
Digiri na Biyu, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Ƙani, A. M. (1999). The Place of Kano In
The Intellectual History of Bilad Sudan. In Degel.
Faculty of Arts And Islamic Studies. Pp 50-58. Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.
Ƙaraye, N. D. (2008). Sana’ar Ɗinkin Hula a Birnin Kano da Kewaye. Kundin Digiri na
Farko, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Kwalli, K. M.
(1996). Kano Jalla Babbar Hausa. Babu
Sunan Maɗaba’a.
Lawal, N. (2019).
Nazarin Saye a Tunanin Bahaushe Jiya da Yau. Kundin Digiri na Uku, Sasahen
Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Liman, A. (1985). Mu Fara Karatu. Zaria: Longman Nigerian
Limited.
Longman, (2003). Longman Active Study Dictionary for
Egyptian Secondary Schools. New Edition. England: International Students
Edition, Person Education, Edinburgh Gate.
Madabo, M. H.
(1976). Ciniki da Sana’o’i a Ƙasar Hausa. Lagos: Thomas Nelson Nigerian Limited.
Maradun, M. S.
(1992). Sarautar Gargajiya a Ƙasar Hausa:
Nazarin Muƙaman Sarautar Gargajiya A Sakkwato.
Kundin Digiri na Biyu, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Muhammad, B. A.
(1991). Tasirin Zuwan Turawa Kan Sarautun Gargajiya Na Ƙasar Hausa: Tsokaci Kan Sarautar Kano. Kundin Digiri na biyu, Sashen Koyar
da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Muhammad, B. A.
(2009). Hausawa da Al’adunsu. Kano:
Absar Comprint.
Muhammad, M. S.
(2019). Sana’a Sa’a.Kaduna:
Gado-da-masu Communication.
Muhammad, M. S.
(2020). Bahaushiyar Al’ada. Kano:
Bayero University Press.
Musa, A. (1991).
Tasirin Zuwan Turawa a Kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya. Kundin Digiri na
Farko, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Musah, M. T.
(2021). Tasirin al’adun Sarautar Hausawa Na Gargajiya A Kan Wasu Na Ƙabilun Ƙasar Zazzau.
Kundin Digiri na Biyu, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Na’iya, M. R.
(1983). Tsarin Gine-Ginen Hausawa na Gargajiya. Kundin Digiri na Farko, Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Newman, P. da Ma
Newman, R. (2020). Hausa Dictionary English-Hausa/Hausa-English. Kano: Bayero
University Press.
Palmer, H. R.
(1908). The Kano Chronicle. The Journal of the
Royal Anthropological Institute of Great Britain and Ireland, vol. 38, pp.
58-98.
Rambo, R. A.
(2018). Nazarin Ayyukan Sana’ar Sassaƙa da Fasahohinsu a
Rayuwar Hausawa. Kundin Digiri na Uku, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya.
Katsina: Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua.
Rimmer, da Wasu
(1975). Zaman Mutum da Sana’arsa. Zaria:
Northern Nigerian Publishing Company Limited.
Rose, A. O. (1994).
Alhaji Ado Bayero On The Royal Court Of Kano.
Kano: Ugosons Press Limited.
Rufa’i. A. R.
(1995).Gidan Rumfa: The Kano Palace.
Kano: Truimph Publishing Company.
Saleh, G. (2006).
Shamaki da Ɗanrimi a Masarautar Kano. Kundin Digiri
na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Salisu, I. (2011).
Sarautar Makwashe Da Tasirinta A Garin Argungun. Kundin Digiri Na Farko, Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya. Sakkwto: Usmanu Ɗanfodiyo University.
Sallau, B. A.
(2009). Sana’ar Wanzanci da Sauye-Sauyen Zamani. Kundin Digiri na Uku, Sashen
Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Sallau, B. A.
(2013). Wanzanci da Sauye-Sauyen Zamani.
Zaria: Ahmadu Bello University Press.
Sani, H. T.
(1995). Tsarin Shugabanci da Ɗaukar Nauyin Al’ummar Hausawa. Kundin Digiri na Farko, Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Shu’aibu, H.
(2002). Dangantakar Da Ke Tsakanin Sana’o’in Hausawa Na Gargajiya. Kundin
Digiri na Farko, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Smith, S. S.
(2004). The New International Webster’s
Comprehensive Dictionary of English Language. New Delhi: Trident Press.
Soba, A. S.
(2017). Tanadin Tsaron Gargajiya a Ƙasar Zazzau:
Waiwayen Cikin Zamunan Sarakunan Habe 1435-1804. Kundin Digiri na Uku, Sashen
Nazarin Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Suleiman, A. M.
(1993). Faɗaɗuwar Sana’o’in Gargajiya a Zamance. Kundin Digiri na Farko, Sashen Koyar da
Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Tukur, A. (1999). Kowace Ƙwarya da Abokin Burminta. Babu Sunan Maɗaba’a.
Uba, A. (2021).
Yadda Ake Gudanar da Bukukuwan Sarauta A Yankin Kano Da Katsina. In Yakasai,
A.S. Et,Al. (Eds), A Great Scholar And
Linguist: A Festschrift In Honour Of Professor Ibrahim Ahmad Mukoshy. Pp 714-724. Kaduna: Amal Printing And Publishing Nigerian Limited.
Umar, M. B. (1987). Dangantakar
Adabin Baka da Al’adun Gargajiya. Kano: Truimph Publishing Company Limited.
Usman, Y. B.
(1980). The Transformation of Katsina. Kundin Digiri na Uku. Zaria: Jami’ar
Ahmadu Bello.
Waya, Z. I.
(2000). Kano da Masarautarta Jiya Da Yau.
Zariya: Gaskiya Corperation Limited.
Weinstock, M
(2015). Changing Epistimologies Under Conditions of Social Change In Two Arab
Communities In Israel. Int J Psychol.
http://dx.doi.org/10.1002/ijop.12130.
Weinstock, M. da
Wasu (2014). Societal Change and Value In Arab Communities In Israel:
Intergenerational and Rural-urban Comparisons. J Cross-Cult Psychol. http://dx.doi.org/10.1177/00220221/1455/792.
Yahaya, I. Y. da
Wasu (1992). Darussan Hausa Don Manyan
Makarantun Sakandire. Zaria: University Press.
Yahya, A. B.
(1979). Jigon Nazarin Waƙa. Kaduna: Fisbas Media Services.
Yakubu, A. M.
(2006). Emirs And Politician: Reform, and
Recrimination in Northern Nigeria 1950-1966. Kaduna: Baraka Press and
Publishers Limited.
Yakubu, S. da
Gafai, B. M. (2018). Tsatsube-Tsatsuben Mahauta Wajen Kare Martabar Sana’ar
Fawa. Cikin Kadaura Journal of Hausa
Multidisplinary Vol1, No 4 Studies, Department
of Nigerian Languages and Linguistics.Kaduna: Test and Print Ventures.
Zhenghong, M. (1985).Tsarin Mulkin Gargajiya a Ƙasar Hausa. Kundin Digiri na Ɗaya, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.
Rataye Na Ɗaya
Mutanen Da Aka Tattauna Da Su
I. Tattaunawar da aka yi da Ɗanrimin Kano, Alhaji Sarki Waziri a
ofishinsa da ke Hedikwatar masarautar Kano (Kano Emirate Council), ranar Talata
5/4/ 2022 da misalin ƙarfe
3:20 na yamma.
II. Tattaunawa da Sallaman Kano Alhaji Daud\a
a gidan da ke Ƙofar Ƙwaru cikin gidan Mai martaba Sarkin Kano
Alhaji Aminu Ado Bayero, ranar Laraba 06/4/2022 da ƙarfe 8:00 na dare.
III. Tattaunawa da Nafi’u Uba Muhammada
(Babban ɗan
Sarkin Ɗorin Kano) a gidan Sarkin Ɗorin Kano da ke unguwar Ƙofar Na’isa a cikin birnin Kano. Ranar Juma’a 18/08/2023, da misalin ƙarfe 3:30 na yamma.
IV. Tattauwanawa da Sarkin Ɗorin Kano Alhaji Uba Yusuf Muhammad
ranar Asabar 05/07/ 2023. da misalin karfe 3:30 na yamma a gidansa da ke Ƙofar Na’isa a cikin Birnin Kano.
V. Tattaunawa da Dr. Datti Sani likitan
dabbobi a ranar Laraba 6/9/2023 a ofishi likitan dabbobi na Abbatuwa da ke
cikin birnin Kano.
VI. Tattaunawa da Shamakin fawan Kano Malam
Abubakar Hamisu a gidansu da ke Unguwar Arzai a cikin birnin Kano, a ranar
juma’a 11/08/2023 da misalin ƙarfe
3:30 na rana.
VII. Tattaunawa da Sarkin
fawan Kano Alhaji Isiyaku Alin Muli a ofishinsa da ke Abbatuwa a Unguwar Ƙofar Mazugal da ke cikin birnin Kano,
ranar Laraba 6/9/2023 da misalin ƙarfe
11:00 na safe.
VIII. Tattaunawa ta 2 da
Sarkin Ginin Kano Abdulƙadir
Muhammad a gidansa da ke unguwar Yakasai a cikin birnin Kano, Ranar Talata
5/9/2023 da misalin ƙarfe
goma na safe.
IX. Tattaunawa da Lawan Gwadabe Sarkin Gini a
gidan Sarkin gini Kano da ke unguwar Yakasai a cikin birnin Kano, Ranar Talata
5/9/2023 da misalin ƙarfe
goma na safe.
X. Tattaunawa da Balarabe Hassan Ka iya gini. Ɗaya daga cikin magina da ke zaune a
unguwar Kofar mazugal. Ranar Laraba 20/09/2023 da misalin ƙarfe 3:00 na rana.
XI. Tattaunawa da Yusuf Usman ɗaya
daga cikin ‘ya’yan Sarkin Maƙeran
Kano a ranar 16/08/2023. A lokon maƙera
da ke unguwar Galdanci a cikin birnin Kano, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma.
XII. Tattaunawa da Sarkin Maƙeran Kano Alhaji Usman Muhammad a gidansa da ke unguwar Galadanci a cikin birnin Kano. Ranar 16/08/2023 da misalin ƙarfe 3:30 na yamma.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.