Ticker

6/recent/ticker-posts

Sauye-Sauyen Zamani a Wasu Sarautun Sana’o’in Gargajiya Da Ayyukansu a Garin Kano (Kashi Na Uku)

Article Citation: Suleiman, M. (2025). Sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano [Master’s dissertation]. Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

SAUYE-SAUYEN ZAMANI A WASU SARAUTUN SANA’O’IN GARGAJIYA DA AYYUKANSU A GARIN KANO

Na

SULEIMAN Musa
Email: musasuleiman424@gmail.com  
Phone: 08061256096

Sauye-Sauyen Zamani a Wasu Sarautun Sana’o’in Gargajiya Da Ayyukansu a Garin Kano

BABI NA BIYU

BITAR AYYUKAN DA SUKA GABATA

2. 0 Shimfiɗa

Wannan babi mai take bitar ayyukan da suka gabata, babi ne da aka yi bitar ayyuka masu alaƙa da wannan bincike. Wannan ne ya sanya babin ya fi mayar da hankali a kan bitar ayyukan da suka shafi sarauta da sana’o’in Hausawa na gargajiya, da aka samo a kudayen digiri na uku da na biyu da na farko da bugaggun littattafai da maƙalu a cikin mujallu da maƙalu kuma takardun ilimi. Daga ƙarshe, babin ya yi bayani a kan hujjar ci gaba da wannan bincike, sannan aka rufe babin da naɗewa.

2.1 Rukunin Kundayen Bincike

A wannan sashe an yi nazarin kundayen bincike na matakin digiri na uku da na biyu da na farko, waɗannan suke da makusanciyar dangantaka ko ta nesa a matsayin fitilar da ta haska wannan bincike. Waɗannan kundaye da aka yi bita sun haɗa da:

2.1.1 Kundayen Digiri na Uku.

Usman, (1980) binciken ya yi bayani mai faɗi a kan mulki kafin ya tafi kai tsaye ga sauye-sauyen mulki a masarautar Katsina. Sannan ya yi bayani a kan asalin kalmar Katsina da kuma yadda garin Katsina ya kafu. Haka kuma, wannan binciken ya yi bayanin sauye-sauyen mulki tsakanin Dallazawa da Sulluɓawa, tare da yadda Sarakunan suka gudanar da nasu mulki. Akwai dangantaka tsakanin aikin Usman da wannan aikin da aka gudanar ta fuskar Sarauta da sauye-sauye da aka samu. Sai dai Usman ba kan masarautar Kano ya yi aikinsa ba, ya yi binciken shi ne a kan masarautar Katsina. Shi kuwa wannan aiki an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyuakansu a garin Kano.

Sallau, (2009) aikin ya yi bayani a kan tattalin arziƙin ƙasar Hausa ta ɓangarorin sana’o’i daban-daban, ya kawo tattalin arziƙin da aka gada iyaye da kakanni da suka shafi sanaoin gargajiya. Haka kuma, ya kawo yadda aka samu wasu baƙin sanaoi a sakamakon cuɗaya da baƙin alummu a ƙasar Hausa. Wannan aikin na Sallau yana da alaƙa da wannan bincike da aka gudanar ta fuskar sana’o’in gargarji. Haka kuma, sun bambanta ta fuskar baƙin sanaoin da aka samu a sakamakon cuɗanya da baƙin alummu a ƙasar Hausa. Shi Sallau ya yi aikinsa a kan sanaar wanzanci da sauye-sauyen zamani. Wannan nazari kuwa an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Gaya, (2012) kundin ya yi wadataccen bayani a kan sarautun gargajiya da muhimmancinsu. Ya yi bayani a kan ƙasar Hausa da muƙaman sarauta da ayyukansu. Ya kuma zaƙulo aladun sarauta na gargajiya. Binciken ya kawo yanayin sarautun gargajiya kafin mulkin mallaka, da kuma jirwayen siyasa a aladun sarauta. Ko shakka babu, wannan aikin Gaya yana da alaƙa da wannan binciken da aka gudanar ta fuskar Sarauta da ayyukan Sarauta. Haka kuma, sun bambanta ta tsarin siyasa da aka tsarmo a cikin aikinsa. Domin kuwa, shi Gaya ya yi aikinsa kan tasirin siyasa a Sarautun gargajiya, musamman a masarautar Sakkwato da Katsina da Kano da Daura daga 1960 zuwa 2019. Shi kuwa wannan aiki an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Fadama, (2014) binciken ya yi bayani a kan yadda ake gudanar da sana’ar kamun kifi da kuma yadda zamain ya yi tasiri a kan wannan sana’a ta kamun kifi a dalilin zuwan Turawa. Ya kawo kayan kamun kifi na zamani da ake amfani da su wajen kamun kifi. Wannan aikin suna da alaƙa da wannan nazari ta fuskar sanaoin gargajiya da kuma tasirin zamani. Haka kuma sun bambanta da wannan aiki ta sanaar kamun sarkanci da ya fi karkata a kai. Domin shi ya gudanar da aikinsa mai taken sarkanci a lardin Sakkwato. Wannan aikin kuwa an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Lawal, (2019) aikin ya kawo bayanin ma’anar falsafa da falsafa a wajen Hausawa. Aikin ya kawo cikakken bayani a kan saye a al’adun Hausawa da tsarin zamantakewar Hausawa. Sannan binciken ya yi bayani a kan yanayin saye a fada, inda ya taɓo saye a fadar Kano da Katsina da Haɗeja da Sakkwato da Maraɗi da Zazzau da kuma Daura. Bugu da ƙari, binciken ya kawo saye a wasu sanaoin Hausawa Hausawa na gargajiya, inda ya taɓo sana’ar noma da wanzanci da ɗori da fawa da farauta da su da maita. Wannan aikin yana da alaƙa da wannan bincike ta fuskar fada da sanaoin Hausawa na gargajiya. Sannan binciken sun bambanta ta saye a tunanin Bahaushe da ya fi maida hankali a kansa. Kasancewar binciken ya yi bayani ne a kan nazarin saye a tunanin Bahaushe jiya da yau. Shi kuwa wannan aiki an gudanar da shi a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

2.1.2 Kundayen Digiri Na Biyu

A ɓangaren kundayen digiri na biyu kuwa, an samu ayyukan manazarta da dama da suka gudanar a wannan fanni. Bisa ga haka, aka yi duba zuwa gare su kamar yadda masu iya magana ke cewa “ Waiwaye adon tafiya”. Daga cikin ayyukan akwai:

Maradun, (1992) kundin ya yi bayani a kan tsarin sarauta tsakanin al’ummar Hausawa da kafuwar daulolin ƙasar Hausa. Binciken ya ƙara kallon muƙaman sarakunan gargajiya a ƙasar Hausa tare da tasirin da muƙaman suke da shi a sarautun gargajiya. Ya kuma yi bayani mai gamsarwa kan sarauta a yankin Sakkwato da sarakunan majalisar Sarki da yadda suke gudanar da ayyukansu. Haka kuma, aikin ya zaƙulo irin canje-canjen da aka samu a Majalisar Sarkin Musulmi. Wannan aiki na Maradun yana da dangantaka da wannan bincike, domin kuwa duk suna magana a kan masarauta da kuma sarauta da kuma sauye-sauyen da ake samu. Sai dai kuma sun yi hannun-riga ne ta fuskar bambancin masarautun da aka gudanar da binciken a kansu. Maradun ya gudanar da nasa aikin a kan muƙaman sarautun gargajiya a fadar Sakkwato, yayin da Shi kuwa wannan aiki an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Dawaki, (1994) bincike ya yi cikakken bayani a kan tarihin Ɗorayi da dangantakarta da birnin Kano ta fuskar tattalin arziƙi. Binciken ya kawo bayani kan sarautar Kano da tarihin Sarkin Kano Abdullahi Bayero da yadda aka samar da gandun sarki na Ɗorayi. Ya kawo irin matsallolin da aka fuskanta na Turawan mulkin mallaka a Ɗorayi. Haka kuma, ya kawo yadda aka riƙa yin haramtaccen cinikin bayi da matsalolin da ya haifar a Ɗorayi. Wannan aikin na Dawaki yana da dangantaka da wannan binciken saboda sarauta da tattalin arziƙi a aikinsa. Haka kuma, sun bambanta ta cinikin Bayi da harkar kasuwanci tsakanin Kano da Ɗorayi. Shi Dawaki ya yi aikinsa kan Ɗorayi da tarihin tattali arziƙi da sauye-sauye a ƙarni na 19 da na 20 a masarautar Kano. Shi kuwa wannan aiki an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Gaya, (1998) binciken ya yi gamsasshen bayani kan yanayi da sigar sarautun gargajiya, da tsarin sarautun gargajiya, da ayyukan Sarki, da muƙarrabansa, da ayyukan masu unguwanni. Binciken ya kawo tasirin mulkin soja a kan sarautar gargajiya da matsayin sarautun gargajiya a halin yanzu. Ko shakka babu, wannan aikin yana da alaƙa da binciken, kasancewar duk a kan masarauta ɗaya aka gudanar da su da kuma tasirin zamani. Haka kuma, sun bambata da wannan bincike kasancewar shi Bello tsarin mulkin gargajiya ya kalla a aikinsa. Ya yi aikin ne a kan tsari mulkin gargajiya jiya da yau musamman a Kano. Shi kuwa wannan aiki an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Saleh, (2006) aikin ya yi ƙoƙarin bayani a kan sarauta kafin ya kalli tsarin sarauta a masarautar Kano. Ya yi bayani a kan Sarautar Shamaki da Ɗanrimi da ayyukansu a masarautar Kano. Haka kuma, bincike ya kawo ma’anar Bawa tare da jero Sarautun Bayi a wannan masarauta. Binciken yi bayani a kan asalin samuwar Sarautar Shamaki da Ɗanrimi tare da jero ƙananan Sarautun da suke ƙarƙashin kulawar waɗannan sarautu. Binciken ya gano cewa Sarautar Shamaki da Ɗanrimi suna da mutuƙar muhimmanci a masarautar Kano. Alaƙar aikin na Sale da wannan bincike da ake gudanarwa ita ce Sarauta, duk da cewa a masarauta ɗaya aka gudanar da binciken. Duk da haka bai hana ayyukan su bambanta ta fuskar sarautun da ake binciken a kansu ba. Don shi Sale ya yi aikinsa a kan Sarautar Shamaki da Ɗanrimi a fadar Kano. Wannan binciken kuwa an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Abubakar, (2008) kundin ya yi bayani a kan matsayin sarautar Sallama da Sarkin Hatsi a fadar Kano. Haka kuma, aikin ya kawo ma’anar sarauta da asalin sarauta da nau’o’inta. Binciken ya kawo ma’anar Sallama da Sarkin Hatsi da asalin sarautarsu da ayyukansu da kuma sarautun da suke a ƙarƙashinsu. Wannan aikin na Abubakar yana da dangantaka da wannan nazari da za a gudanar ta fuskar Sarauta da kuma masarautar Kano. Sannan sun bambanta da wannan bincike ta nauin sarautun da kuma ayyukansu, kasancewar shi Abubakar ya gudanar da aikinsa a kan sarautar Sallama da Sarkin Hatsi a fadar Kano. Wannan bincike kuwa wannan aiki an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Isma’il, (2011) binciken ya yi bayani a kan asalin sarauta da ma’anar sarauta nau’o’in sarauta gabanin ya kawo ma’anar zube da nau’o’insa a nazarin ƙagaggun labarai. Binciken ya kawo maanar fada da ire-iren tasirin sarautun a cikin littafin Magana Jari Ce, da yawan labaran da suka ƙunshi sarautun gargajiya da ba su shafi aikinsa ba. Sannan kuma, ya kawo dangantakar sarautun gargajiya na cikin littafin Magana Jari Ce ta 1-3 da rayuwar zahiri da kuma bambancin wasu sarautu da suka fito a cikin Magana Jari Ce 1-3. Bincike ya zaƙulo tasirin da sarautun za su yi a zuciyar mai karatu. Tabbas, wannan aiki na Isma’il yana da alaƙa da wannan nazari ta fuskar Sarauta. Haka kuma, sun bambanta ta kalon da ya yi wa sarauta a ƙagaggun labarai. Domin Ismail ya yi aikinsa kan tasirin sarautun gargajiya a cikin littafin Magana Jari Ce 1-3. Shi kuwa wannan aiki an yi shi ne a kan da sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Aliyu, (2017) aikin ya yi gamsasshen bayani kan matsayin Sarki, da hakimai, da matsayin Sarkin a fadar Katsina. Binciken ya kawo matsayin Sarki a jiya da yau da ayyukan Sarki a jiya da ayyukan Sarki a yau. Haka kuma, ya kawo ire-iren Hakimai a fadar Katsina da matsayinsu da kuma ayyukansu. Wannan binciken yana da alaƙa da wannan aiki da za a yi ta fuskar ire-iren Hakimai da kuma sarauta. Haka kuma, sun bambanta ta masarautar da aka gudanar da aikin. Saboda shi Aliyu ya yi aikinsa ne a kan nazarin matsayi da dangantaka tsakanin Sarki da Hakimai a fadar Katsina. Shi kuwa wannan aiki an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Abdullahi, (2021) kundin ya kawo ma’anar sana’ar noma da kiwo da fawa da wanzanci da kitso da kuma bayar da magungunan gargajiya. Sannan ya yi bayanin kayan kayan da aike gudanar da sana’o’in da kuma yadda ake sarrafa su. Haka kuma, ya yi bayani a kan al’adun masu bayar da maganin gargajiya da suka haɗa da siddabaru da surkulle. Wannan aikin na Abdullahi yana da alaƙa da wannan bincike ta fuskar sanaoin gargajiya. Haka kuma, sun bambanta da wannan aiki ta kallon sanaoin a cikin finafinan Hausa da ya yi. Sai shi wannan aikin an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Danjuma, (2021) kundin ya yi bayani a kan yanayin al’adun sarauta na masarautar Kano da Dass. Aikin ya kawo al’adun da suka shafi Sarki da zaman fada da zaman gadon sarauta da hakiman cikin gidan sarki da al’adar yin iso wajen sarki. Haka kuma, binciken ya kawo al’adun da suka shafi barori da al’adar kiran jikoki da ‘ya’ya. Wannan bincike na Ɗanjuma yana da alaƙa da wannan bincike ta fuskar sarauta da masarauta. Sannan sun bambanta da wannan aikin ta yanayin aladun masarautar Dass, kasancewar shi ya yi aikin ne a kan kwatanta wasu al’adun sarauta a tsarin zamantakewa na fadar Kano da ta Dass. Shi kuwa wannan aiki an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Hamji, (2023) ya yi bayanai a kan samuwar wasu muƙaman sarauta a masarautar Kano. Ya kawo dangantakar da ke tsakanin Hausaw da Fulanin Gombe da samuwar hagalaje a masarautar Gombe. Haka kuma, ya kawo muƙaman sarautun aro a masarautar Kano da Gombe. Aikin nasa ya kalato ayyukan wasu shugabanin sarautun gargajiya. Har ila yau, bincike na shi ya yi bayani a kan muƙaman masu riƙe da sarautu, da suka haɗa da masu zaɓen sarki da ‘yan majalisar sarki a masarautun Kano da gombe. Sannan ya yi bayani a kan sarautun bayi da na barori da n sauran jama’a da sarautun karramawa da sarautun sana’o’i da na wasu ƙabilu. Bugu da ƙari, ya kawo dangantaka a wasu sarautun Kano da Gombe da kuma matsayin sarautun jiya da yau. Wannan bincike yana da alaƙa da wannan aikin ta fuskar sarauta da masarautar Kano da kuma sarautun sanaoin gargajiya da ya yi bayani a cikin aiki. Sannan sun yi hannun riga da wannan bincike ta wasu muƙamai da ya yi bayani a kan su na masarautar Gombe. Domin shi ya gudanar da aikin a akan dangantakar a tsakanin wasu muƙaman masarautar Kano da Gombe. Shi kuwa wannan bincike an gudanar da shi ne a akan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Albarkawa, (2023) ya yi bayani a kan tarihin Zazzau da masarautar Zazzau. Haka kuma ya kawo sauye-sauyen al’adu da aka samu a masarautar Zazzau, daga cikin sauyin da akan samu akwai takon giwa da babbar ƙofa da turakar sarki da ofis da asibiti. Haka ya kara kawo wasu da suka haɗa da wurin adan akayan tarihi da sarautun aro da tufafi. Wannan aiki na da dangantaka da wannan aiki ta fuskar sarauta da sauyi. Haka kuma sun bambanta da wannan bincike ta masarautar Zazzau da ya gudanar da aikinsa a kanata. Domin shi ya yi aikinsa akan sauye-sauyen wasu al’adu a fadar Zazzau. Shi kuwa wannan aikin an gudanar da shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

2.1.3 Kundayen Digirin Farko

A wannan ɓangaren an duba ayyukan kundayen digiri na farko, domin a share fage da shi a wannan bincike. Duk da cewa ba bincike ne mai zurfi ba, amma hannun mai bincike ya kai ga taɓo wasu ayyuka da aka yi waɗanda suke da alaƙa da wannan bincike. Wannan ne ya sa aka kasa jurewa sai da aka ɗauko su domin a yi bitarsu, kamar yadda aka gani a ƙasa.

Zhenghong (1985) binciken ya yi bayani a kan asalin Hausawa da bayanin tsarin mulki gargajiya kafin Sarauniya Daurama a ƙasar Hausa. Bincike ya kawo tsarin mulkin gargajiya a zamanin Sarakunan Haɓe da kuma zamanin sarakunan Fulani a masarautar Kano. Sannan ya ci gaba da bayanin a kan tsarin mulkin gargajiya kafin zuwan Turawa da bayan zuwan su ƙasar Hausa da kuma bayan samun yancin kai. Wannan bincike na Zhenghong yana da dangantaka da wannan aikin da za a gudanar ta fuskar Sarauta da ya yi aikinsa a kanta. Haka kuma, sun bambanta da wannan aikin ta tsarin mulki kafin zuwan sarauniya Daurama da Turawan mulkin mallaka. Kasancewar shi Zhengong ya yi bincikensa kan tsarin mulkin gargajiya a ƙasar Hausa, Shi kuwa wannan aiki an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Musa, (1991) aikin ya yi bayani a kan tarihin asalin Hausawa da samuwar sana’o’i da rabe-rabensu ta ɓangaren maza da mata da kuma na haɗa ka. Haka kuma, ya kawo dangantakar sana’o’in da muhimmancinsu. Haka kuma, aikin ya taɓo ɓangaren sarauta da gudummawar da sana’o’in gargajiya ga tsarin mulkin ƙasar Hausa. Sannan aikin ya kawo bayani a kan ginuwar tattalin arziƙi da sanaoin gargajiya da matsayin sanaoin gargajiya a lokacin zuwan Turawa ƙasar Hausa. Bincike ya kawo yadda sanaoin suka riƙa faɗuwa da bunƙasa a dalilin zuwan Turawa. Bugu da ƙari aikin ya kalato baƙin aladu da aka samu a sakomakon cuɗanya da Turawa kamar samuwar kuɗi da ilimin boko da kuma hanyoyin da za a bi wajen farfaɗo da sana’o’in Hausawa na gargajiya. Aikin yana da alaƙa da wannan bincike ta sarauta da sanaoin Hausawa na gargajiya. Haka kuma, sun bambanta da wannan aikin ta tarihin ƙasar Hausa da ya kawo a cikin aikinsa. Domin ya yi bincikensa a kan tasirin zuwan turawa a kan sanaoin Hausawa na gargajiya. Shi kuwa wannan aikin an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Suleiman, (1993) bincike ya yi bayani a kan sana’o’in gargajiya da yadda ake aiwatar da su a gargajiyance. Haka kuma, aikin ya kawo yadda ake aiwatar da sana’o’in ta hanyar amfani da baƙin kayan aikin. Kundin ya nazarci sanaar kiwo da farauta da kuma noma da dai sauransu. Aikin nasa ya ƙyalloro sanaoin da suka samu a zamanance da kuma illolin da suka samu. Aikin yana da alaƙa da wannan aiki da za a gudanar da fuskar sanaar gargajiya. Haka kuma, kuma sun bambanta da wannan aikin ta faɗaɗuwar sana’o’in gargajiya a zamanance. Shi kuwa wannan aikin an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Aliyu, (2004) aikin yi bayanin sarauta da asalin sarauta da ire-iren sarauta da sauye-sauyen zamani a sarautar gargajiya. Sannan kundin ya kawo tarihin sarautar ƙasar Tsafe da asalin sarautar garin Tsafe da jerin sarautar sarakunan masarautar Tsafe. Haka kuma, binciken ya kawo matsayin sarautar Tsafe a yau da taƙaitaccen tarihin sarkin tsafe na yanzu. Babu shakka, aikin Aliyu yana da alaƙa da wannan binciken ta fuskar sarauta da sauye-sauyen zamani. Haka kuma, sun bambanta ta yanayi da tsarin sarautun masarautar Tsafe. Domin Aliyu ya yi aikinsa kan yanayi da tsarin sarautun gargajiya a ƙasar Tsafe. Wannan aiki kuwa an gudanar da shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Ƙaraye, (2008) kundin yi bayani a kan asalin sana’a da ma’anarta da kuma ire-iren sana’a a birnin Kano da kewaye. Haka kuma ya kawo ma’anar hula da yadda ake gudanar da sana’ar ɗinkin hula da kuma kayan da ake amfani da su wajen sana’ar ɗinkin hula. Sannan kuma ya kawo matsayi da muhimmancin hula ga Bahaushe. Aikin yana da dangantaka da wannan nazari da za a gudanar ta sana’a. Haka kuma, sun bambanta da shi ta sana’ar ɗinkin hula da ya karkata a kansa. Kasancewar shi Ƙaraye ya yi aikinsa a kan sanaar ɗinkin hula a birnin Kano da kewaye. Shi kuwa wannan nazari an gudanar da shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Salisu, (2011) binciken ya yi gamsasshen bayani a kan sarakunan ruwa na Argungu gabanin ya kawo asalin da tarihin sarautar Makwashe a ƙasar Argungu. Haka kuma, binciken ya kawo matsayin sarautar Makwashe ga aladun kamun kifi a garin Argungu. Wannan aiki na Salisu yana da alaƙa da bincike da ake so a yi, domin duk sun yi bayani kan sarauta da kuma sanaar kamun kifi. Sannan wannan aikin ya bambanta da bincike ta yanayin ayyukan sarautun da ake binciken a kansu. Aikin ya gudanan da aikinsa a kan sarautar Makwashe a garin Argungu, yayin da wannan bincike da aka gudanar da shi a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya ayyukansu a garin Kano.

2.2 Maƙalu a Cikin Mujallu

A wannan ɓagiren, an bibiyi mujallu waɗanda manazarta suka yi aiki da suke da alaƙa ta kusa ko ta nesa da wannan bincike da aka gudanar, domin yin bitarsu don a ga rawar da manazarta suka taka a wannan fage. Hausawa na cewa, “ Da na gaba ake gane zurfin ruwa”. Waɗannan mujallu sun haɗa da:

Palmer, (1908) binciken ya yi gamsasshen bayani a kan ƙasar Hausa da yadda mulkin Fulani ya wanzu a ƙarƙashin jagorancin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Ya kawo yadda addinin Musulunci ya zo ƙasar Kano a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa, da zuwan Kalinwama Kano da daular Barno. Aikin ya kawo tarihin Kano a zamanin Barbushe da Tsumburbura da kuma itaciyar tsafin da ake bautawa wato Shamus. Maƙalar ta kawo tarihin Sarakunan Kano tun daga zamanin Bagauda ɗan Bawo har zuwa Sarkin Kano Muhammadu Bello ɗan Sarkin Kano Ibrahim Dabo. Haka kuma, ya kawo tarihin yadda masarautar Kano ta fara naɗa hakimanta da masu naɗa Sarkin da sarautun ‘ya’yan Sarki da na Bayin Sarki tun daga zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa har zuwa Sarkin Kano Muhammadu Bello da Sarkin Kano Ibrahim Dabo. Ko shakka babu, wannan maƙala ta Palmer tana da alaƙa da wannan bincike ta fuskar sarauta. Haka kuma, sun bambanta da wannan aikin ta tarihin Zamfara da Gobir da Nupe da zuwan musulunci ƙasar Kano da tarihin Bayajidda. Domin Palmer ya yi aikinsa kan Jerin tarihin Sarakunan Kano (Kano Chronicle). Shi kuwa wannan binciken aka gudanar da shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Ɗantiye, (1989) binciken ya yi ƙoƙarin yin bayani a kan yadda Hakimai ke karɓar haraji da jangali a Masarautar Kano, da yadda tsarin saratun masarautar Kano yake, da yadda Dagatai ke karɓar haraji da tsarin jakada wato jeka fada a zamanin Sarkin Kano Aliyu Yaji Ɗantsamiya. Sannan bincike ya zaƙulo yadda aka fara tsarma Bayi a cikin tsarin sarauta a masarautar Kano, da lokacin da aka naɗa sarautun Bayi na Ɗanrimi da Sallama da Shamakin farko, a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa. Haka kuma, binciken ya fito da ayyakun jakada a masarautar Kano da yadda huɗɗarsa take kasancewa tsakaninsa da hakimai da kuma dagatai a yayin karɓar haraji da jangali. Ko shakka babu wannan aikin na Ɗantiye yana da danganta da binciken da za a gudanar. Dalili kuwa shi ne ya gudanar da aikin nasa a kan sarauta. Duk da ba za a rasa jini mahauta ba, an ɗan samu bambanci da binciken da za a gudanar ta fuskar haraji da jangali da binciken Ɗantiye ya fi ƙarfafawa. Ɗantiye ya yi aikinsa a kan karɓar haraji daga dagatai da hakimai a masarautar Kano. Shi kuwa wannan aikin ya fi karkata ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Ƙani, (1999) aikin ya yi bayani mai gamsarwa a kan matsayin Kano a ƙasar Hausa da addinin Musulinci a ƙasar Kano. Sannan ya taɓo al’adun Sarauta da tarihim masarautar Kano musamman zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa da zuwan Al-Maghili Kano. Binciken na Kani ya hango irin gudummawar da Malaman addini suka bayar a masarautar Kano da yadda Malaman suka ƙulla dangantaka da Sarakunan Kano. Babu shakka, wannan aiki na Ƙani yana da alaƙa da wannan nazari da za a gudanar ta fuskar sarauta. Haka kuma, sun bambanta ta tarihin zuwan malamai Kano da kuma gudummarsu ga yaɗa addini a ƙasar Kano. Ƙani ya yi aikinsa kan gurbin Kano a tarihin Bilad al Sudan. Shi kuwa wannan aikin an gudanar da shi ne kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Daura, (2012) binciken ya kawo bayani a kan kafuwar garin Daura da al’adun Hausawa da sarautar gargajiya a ƙasar Hausa. Haka kuma, binciken ya kawo nauikan sarautun Daura da muhimmancin sarautar gargajiya ga jamaa. Ko shakka babu, wannan aiki na Daura yana dangantaka da binciken da za a gudanar, domin dukkansu kan sarautar gargarjiya suke bayani. Haka kuma, sun yi hannun-riga ta fuskar masarautun da aka ɗora binciken a kansu. Kasancewar aikin Daura an ɗora shi a kan masarautar Daura, yayin da wannan binciken an ɗora shi a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Uba, (2021) aikin ya yi bayani yadda ake bukukuwan sarauta musamman a Kano da Katsina. Binciken ya kawo yadda ake naɗin sarauta da bayar da sandar sarauta. Sannan mai binciken ya yi bayani dangane da Hawan sallah a Kano da Katsina. Tabbas wannan aiki yana da alaƙa da wannan bincike. Domin manazarci ya yi aikin ne kacokan a kan sarauta. Sannan kuma, aikin nasa ya bambanta da bincike da za a gudanar, kasancewar a aikin ya haɗe masarautu biyu ne wato masarauta Kano da kuma Katsina. Uba ya yi bincikensa kan yadda ake gudanar da bukukuwan sarauta a yankin Kano da Katsina. Shi kuma wannan aikin za a aiwatar da shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya a garin Kano.

2.3 Maƙalu A Tarukan Ƙara wa Juna Ilimi

A wannan fasali, an kawo maƙalun da aka yi bita waɗanda suke da makusanciyar dangantaka ko ta nesa, waɗanda suka yi daidai da wannan binciken da aka gudanar. Daga cikin maƙalun da aka yi bita akwai:

Bunza, (2016) binciken ya yi bayani a kan sarauta da tsaro da gargajiya gabanin ya kawo gudummawar sarautun tsaro. A binciken nasa ya yi bayani kan sarautun tsaro a cikin fada tare da ayyukan da suke gudanarwa a fada. Haka kuma, aikin ya kawo masu riƙe muƙaman tsaron ƙasa na gargajiya a fadojin ƙasar Hausa. binciken ya kalato wasu sarautun sanaoin gargajiya tare da matsalolin da tsaro yake fuskanta a gargajiyance. Aikin Bunza yana da dangantaka da wannan bincike, domin kuwa duk yana magana ne a kan sarauta da kuma muƙaman sarauta. Sannan kuma, sun yi hannun-riga da wannan binciken kasancewar Bunza ya fi karkata aikinsa kan sarautun tsaro. Saboda, Bunza ya yi aikin nasa kan gudummawar sarautun tsaro a arewacin Nijeriya. Shi kuwa wannan bincike an gadanar da shi ne kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Bunza, (2023) aikin ya yi bayani a kan sarauta da iko da mulki da kafa harsashin sarauta a ƙasar Hausa. binciken ya kawo bayanin tushen sarautar gari da ta sanaoi da gunduma da kuma ƙasa, tare da yadda aka kafa gari da kuma shimfiɗa sarauta a wasu garuruwan ƙasar Hausa. Haka kuma, ya yi kawo bayani a kan sarakunan masarautu da na ƙasa da na fada. Binciken na Bunza ya ƙyallo manyan sarautun na yayan Sarki da na tsaro da na fada da na alfarma da na karaga da na aro da na bayi kuma na makwabta. Ko shakka babu, wannan aikin yana da alaƙa da wannan bincike ta fuskar sarauta da sarautun sanaoi. Sai dai sun bambanta da wannan bincike ta tarihin ƙasar Hausa da kuma yadda ake zama Sarki, domin kuwa Bunza ya yi bincikensa a kan sarauta a tsarin ikon ƙasar Hausa (Yadda take da yadda ake samar da ita). Shi kuwa wannan nazari an gudanar da shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

2.4 Bugaggun Littattafai

A nan an yi bitar littattafai waɗanda suka taɓo wani abu da ke da kusanci da wannan binciken da aka gudanar. Daga cikin litattafan akwai:

Rimmer, da Wasu (1975) sun yi bayani a kan yadda al’amuran duniya ke ci gaba da kuma yadda mutane suke ƙoƙarin daidai zamansu da sauyawar zamani a ɓangaren sana’o’i. Littafin ya yi bayanin asalin sana’o’in Hausawa tare da bayyana yadda ake gudanar da su a Nijeriya da kuma ƙasashen Turai. A cikin littafin sun kawo bayanin sanaoi da suka haɗa da noma da ƙira da su da jima da kuma sassaƙa. Haka kuma, aikin ya waiwayi hanyoyin sifiri da suka haɗa da mota da jirgin ruwa da dabbobi da jirgin sama. Wannan aiki yana da dangantaka da wannan bincike da aka gudanar ta la’akari da sana’o’in gargajiya da sauye-sauyen zamani. Haka kuma, sun bambanta da wannan bincike ta yadda ake aiwatar da sana’o’in a ƙasashen Turai da kuma hanyoyin sifiri. Su sun gudanar da aikinsu mai taken zaman mutum da sanaarsa. Shi kuwa wannan bincike an gudanar da shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Madabo, (1979) ya yi bayani kan sana’o’in Hausawa da kuma al’adun masu yin sana’ar. Haka kuma, ya yi bayanin wasu sana’o’in Hausawa na gargajiya da na zamani da ake gudanarwa a kasuwar Kurmi . Aikin na Madabo yana da alaƙa da wannan aikin ta fusakar sanaoin Hausawa na gargajiya. Haka kuma, sun banbanta da wannan aiki ta sanaoin zamani da ya kawo a cikin littafinsa. Domin kuwa shi ya yi aikinsa a kan ciniki da sanaoi a ƙasar Hausa. Shi kuwa wannan bincike an gudanar da shi a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Liman, (1985) ya yi bayani daidai gwargwado a kan wasu sana’o’in Hausawa na gargajiya da suka haɗa da noma da ƙira da saƙa da makamantansu. Aikin nasa yana da alaƙa da wannan bincike da za a yi ta fuskar sanaoin Hausawa na gargajiya. Inda suka bambanta da wannan aikin shi ne bai yi magana a kan sarakunan sanaoin ba. Shi kuwa wannan bincike an gudanar da shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Alhassan, da Wasu (1988) sun yi bayani a kan al’adun Hausawa na gargajiya da kuma ƙasar Hausa da yanayinta. Haka kuma, sun yi bayani aure da haihuwa da mutuwa da tarbiyya a aladar Bahaushe. Sannan sun bayani game da sana’o’in Hausawa na gargajiya da kuma sauye-sauyen zamani a kan al’adun Hausawa. Sun ƙara kawo sabbin sanaoin kamar aikin direba da yan kamasho da lebura da masinja da sauransu. Wannan aikin yana da dangantaka da wannan bincike ta sanaoin Hausawa na gargajiya da tasirin zamani. Haka kuma sun bambanta da wannan aikin ta sabbin sanaoi da suka kawo a cikin littafinsu. Sai dai shi wannan aikin ya fi mai da hankali ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Rose, (1994) ta yi bayanin tarihin Sarkin Kano Ado Bayero tare da zayyano ƙyawawan halayensa. Sannan kuma, ta kawo aladun da suka shafi masarautar tun daga zamanin sarakunan Haɓe zuwa na Fulani. Haka kuma, binciken ya yi bayani kan daular Fulani wato tun daga zamanin Sarkin Kano Suleimanu zuwa kan Sarkin Kano Ado Bayero. Sannan ta kawo irin gudummawar da suka bayar wajen bunƙasa masarautar Kano musamman ta fuskar tattalin arziƙi da aladunta. Bugu da ƙari, ta yi bayanin yadda aka zaɓi Sarkin Kano Ado Bayero a matsiyin Sarki, da kuma bayanin muƙaman Hakimai na masarautar Kano, tun daga Hakimai da Dagatai zuwa kan masu Unguwanni da ayyukansu. Ko shakka babu, wannan aiki na Rose na da alaƙa da wannan aiki ta fuskar sarauta da tattalin arziƙi. Sannan kuma, sum bambanta da wannan aikin ta fuskar tarihin sarakunan da ta kawo a cikin aikinta. Domin bincike ta yi shi ne a kan tarihin Sarkin Kano Ado Bayero da masarautar Kano. Wannan aikin kuwa an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano..

Rufa’i, (1995) ya yi bayanin tarihin Kano da abubuwan da suka shafi sha’anin mulki da tattalin arziƙi da kuma zamantakewa. Haka kuma, ya kawo bayanin kan fadar Kano da tsarinta, tun daga lokaci da aka kafa ta, da kuma irin ci gaban da aka samu a zamanin sarakunan da suka gabata. Sannan kuma, ya yi bayani a kan unguwanni da suke cikin gidan sarki da kuma sarautun cikin gida na maza da mata. Aikin ya kawo muhimman aladun da suka shafi zamantakewa a gidan sarki. Haka kuma, ya kawo wasu daga cikin sarautun bayi maza da mata a taƙaice. Wannan aiki na Rufa’i yana da alaƙa da wannan aikin ta fuskar sarauta da tattalin arziƙi. Sannan sun bambanta da wannan bincike ta kawo tsarin masarauta da zamantakewa da kuma Sarautun Bayi da ya yi bayani a taƙaice. Rufai ya yi aikinsa kan gidan Rumfa da masarautar Kano. Shi kuwa wannan aikin an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Waya, (2000) ta yi bayani a kan wanzuwar mutane da kafuwar mazaunai a Kano. Sannan ya yi bayani mai gamsarwa kan masarautu da tsarinsu a Kano. Marubuciyar ta kawo tarihin sarakunan da wasu sarautu a fadar Kano. Binciken Waya yana da dangantaka ta kusa da wannan aikin da zan gudanar, domin kuwa shi ma aikin ya yi bayani ne akan sarauta. Haka kuma, sun bambanta ta fuskar tsarin sarautun da ta yi bayaninsu, duk da cewa jero su kawai ta yi ba tare da bayaninsu ba. Waya ya gudanar aikinsa inda ta kalli masarautar Kano jiya da yau. Shi kuwa wannan aikin an gudanar da shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Ibrahim, (2001) ya yi bayani kan tarihin Sarkin Kano Ado Bayero da wanzuwar mulkin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa. Ya kawo bayanin kan naɗa wasu sabbin hakiman tare da tabbatar da su a matsayin cikakkun hakimai a masarautar Kano. Aikin ya kawo bayani kan yadda aka karrama Adamu Gaya da dambarwar da ta faru tsakani Aminu Babba Ɗanagundi da masarautar Kano. Haka kuma ya kawo matsayin sarakuna a zamanin mulkin Shugaban ƙasa Janar Sani Abacha, da kuma yadda aka dakatar da Sultan Ibrahim Dasuƙi. Ko shakka babu, wannan aikin na Ibrahim yana da alaƙa da ta kusa da wannan bincike da za a gudanar domin kuwa ya yi bayani a kan masarautar Kano da naɗa wasu sarautun hakimai da sauye-sauye da aka samu. Sannan sun bambanta da wannan aikin ta wanzuwar mulkin Soja. Ibrahim ya gudanar da aikinsa mai taken Mai zamani: Ado Bayero da Sauye-sauyen da aka samu a masarautar Kano. Wannan bincike kuwa an gudanar da shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Hussaini, (2008) ya yi bayani a kan tarihin Sarkin Kano Ado Bayero da tarihin rayuwar masu riƙe da sarautun masarautar Kano, tun daga lokacin da aka naɗa Sarkin Kano Ado Bayero a shekarar 1963 har zuwa 2008. Haka kuma, Hussaini ya kawo jerin sunayen masu riƙe da sarautun tun daga 1963 har zuwa 2008, tun daga kan waɗanda suka riƙe sarautun suka sauka, wasu kuma aka ɗaga darajar sarautarsu zuwa wata sarauta. Aikin ya jero adadin sarautun masarautar Kano a zamanin mulkin Sarkin Kano Ado Bayero. Wannan aikin na Hussain yana da alaƙa da wannan aikin ta fuskar sarauta. Haka kuma, sun bambanta da wannan binciken ta tarihin masu riƙe da wannan sarautu. Domin shi Hussain ya yi aikinsa kan gwarzayen masarautar Kano daga 1963 zuwa 2008. Shi kuwa wannan aiki an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Gwangwazo, (2010) ya yi bayani kan haihuwar sarkin Kano Muhammadu Rumfa har zuwa aurensa. Binciken ya fito da bayanin kan naɗin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa. Gwangwazo ya ƙara bayani kan bunƙasar Kano da shahararta a zamanin Muhammadu Rumfa. Haka mawallafin ya zayyana tarihin wasu unguwanni a da kuma asalinsu. Haka kuma, ya kawo bayani a kan yadda Sarkin gini ya gina gidan sarautar kano na yanzu wanda ake kira da gidan rumfa. Wannan aiki na Gwangwazo yana da dangantaka da binciken nan, domin shi ma ya yi bayanin sarkin gini. Haka kuma, sun sha bamaban da wannan bincike, domin Gwangwazo ya fi mai da hankali kan tarihin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa da Unguwannin Kano. Shi kuma wannan aikin da an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Ɗan’iya, (2020) ya yi bayani kan huɗɗar kasuwanci da ta wanzu tsakanin Larabawa da Hausawa da kafuwar masarautar Kano. Sannan, ya taɓo kaɗan daga cikin tarihin Shehu Usman Ɗanfodiyo da koyarwarsa da dangantakarsa da masarautar Gobir. Haka kuma, ya kawo bayani kan zuwan Katambale da Clapperton Sakkwato. Bugu da ƙari, ya yi bayani kan jahadin Kano da wanzuwar mulkin Sulluɓawa a Kano da mulkin sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo da irin gudummawar da ya bayar wajen ci gaban masarautar Kano. Binciken nasa ya taɓo kaɗan daga cikin bayanin kan masarautar Ringim. Daga ƙarshe kuma, ya kawo dangantakar da ke tsakanin masarautar Rano da Gaya da Ƙaraye da Bichi da Dutse da masarautar Kano. Ko shakka babu, wannan aikin na Ɗaniya ya yi kama da binciken da za a gudanar ta fuskar sarauta da kasuwanci. Haka kuma, sun bambanta da wannan binciken ta tarihin Shehu Usmanu Ɗanfodiya da dangantakarsa da masarautar Gobir da zuwan Katambale da Clapperton Sakkwato. Ɗaniya ya yi aikinsa mai taken Dabon Kano (The Dabo of Kano). Shi kuwa wannan binciken an gudanar da shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Muhammad, (2019) ya yi bayani sosai a kan sana’o’in Hausawa na gargajiya tare da faɗaɗa ma’anar sana’a da kuma kallon sana’a a mizanin al’ada. Haka kuma, ya kawo dabaru da Hausawa suke amfani da su wajen tsumi da tanadi. Wannan aikin na Muhammad yana da alaƙa da wannann bincike, domin kuwa ya taɓo abin da ya shafi sana’o’in Hausawa na gargajiya. Haka kuma, sun bambanta da wannan aikin ta ta dabarun tsumi da tanadin Hausawa. Domin shi ya yi aikinsa mai taken sana’a sa’a. Shi kuwa wannan aikin an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano.

Muhammad, (2020) ya yi bayani a kan al’ada da asalin Hausawa da tsarin ƙasar Hausa da ma’anar sarauta a ƙasar Hausawa da kuma tsarin sarauta. Haka kuma, ya yi bayani kan matsalar sarauta, da bunƙasarta a ƙasar Hausa, da matakan rayuwar Hausawa, da yadda ta kasance kafin zuwan addinin musulinci. Ya taɓo abin da ya shafi ɗabi’u na yau da kullun da ɗabi’u na mu’amulla da ɗabi’un da Hausawa suka ƙyama. Mawallafin ya kalli abin da ya shafi sanaoin Hausawa na gargajiya da tsami da tanadi da kuma muhallin Bahaushe. Wannan aikin na Muhammad yana da alaƙa da aikin da za a gudanar, domin kuwa ya yi bayani kan abin da ya shafi sarauta da sanaoin Hausawa na gargajiya. Haka kuma, sun bambanta ta wani ɓangare domin Muhammad ba a sarauta ya tsaya ba. Ya taɓo al’adun Hausawa da suka shafi ɗabi’un da suke ƙyama a cikin aikinsa. Aikin nasa ya yi shi ne a kan Bahaushiyar Alada. Wannan bincike kuwa ya fi mai da hankali ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya a garin Kano.

2.5 Hujjar Cigaba da Bincike

Masu iya magana kan ce “Sassabe mafarin aiki”. Ko shakka babu, haka abin yake a fagen nazari. Idan aka ɗauki littattafai, da kundaye, da maƙalu a cikin mujallu, da maƙalun da aka ambata a bitar ayyukan da suka gabata aka yi musu duba na basira, an ga cewa sun yi takin saƙa da wannan bincike da aka gudanar. Gwargwadon ayyukan da aka samu damar kaiwa gare su, ba a samu wani aiki da ya yi daidai da wannan bincike da an gudanar ba. Mafi yawanci ayyukan da hannu ya samu damar kai wa gare su, sun fi karkata a kan sana’oin Hausawa na gargajiya. Wannan bincike kuwa an yi shi ne a kan sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano. Wannan dalilin ya sa aka kafa hujja da bayanin da aka samu daga bitar, domin tabbatar da akwai hujja ta cigaba da bincike bisa wannan take.

2.6 Naɗewa

A wannan babin, an yi bayanin shimfiɗa da rukunin kundayen bincike da aka yi bitar su, musamma masu alaƙa da wannan aiki. Waɗannan kundaye sun haɗa da na matakin digiri na Uku da na biyu da kuma na farko. Sannan babin ya kawo bayanin bitar da aka yi a kan maƙalu a cikin mujallu da maƙalu a tarukan ilimi da kuma bugaggun littattafai. Daga ƙarshe, babin ya yi bayani a kan hujjar cigaba da bincike da kuma rufe babin da naɗewa. 

Post a Comment

0 Comments