Ticker

6/recent/ticker-posts

Sauye-Sauyen Zamani a Wasu Sarautun Sana’o’in Gargajiya Da Ayyukansu a Garin Kano (Kashi Na Biyu)

Article Citation: Suleiman, M. (2025). Sauye-sauyen zamani a wasu sarautun sana’o’in gargajiya da ayyukansu a garin Kano [Master’s dissertation]. Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.

SAUYE-SAUYEN ZAMANI A WASU SARAUTUN SANA’O’IN GARGAJIYA DA AYYUKANSU A GARIN KANO

Na

SULEIMAN Musa
Email: musasuleiman424@gmail.com  
Phone: 08061256096

Sauye-Sauyen Zamani a Wasu Sarautun Sana’o’in Gargajiya Da Ayyukansu a Garin Kano

BABI NA ƊAYA

GABATARWA

1.0 Shimfiɗa

Masana tarihi da manazarta al’adun Hausawa sun taka muhimmiyar rawa wajen bin salsalar tarihin samuwar sarautun ƙasar Hausa[1]. Wannan ya faro ne tun daga kan tsarin rayuwar Hausawa ta dauri, wadda ta ƙunshi maigida da uwar gida da iyalinsa.[2] Haka kuma, abin ya tafi har aka kai ga gidan gandu; da tafiya ta yi tafiya sai aka samu tunga; da zamantakewa ta yi nisa, sai aka samu unguwanni da ƙauyuka da gundumomi da kuma masarautu. Hakan shi ya jawo aka samu Maiunguwa da Dagaci da Hakimi da kuma Sarki. Sakamakon haka shugabancin sarauta a ƙasar Hausa ya zama tamkar ɓawon albasa.[3] Don haka tsarin ya kasance Sarki shi ne yake kula da al’ummar wannan ƙasa baki ɗaya. Sannan kuma, daga gare shi ne sauran Hakimai da Dagatai suke karɓar umarni.[4]

Akan samu sarautun sana’o’in gargajiya a ƙarƙashin kowane babban Sarki na ƙasar Hausa. Masu riƙe da waɗannan sarautu su ne jagorori masu kula da rukunin wasu mutane masu gudanar da waɗannan ire-iren sana’o’i na gargajiya. Kowace sana’a tana da Sarki da yake jagorantar masu wannan sana’a, don ya yi musu sulhu da sasanci a tsakaninsu, da kuma tafiyar da wannan sana’ar bisa ingataccen tsari. Ire-iren waɗannan sarautu na masu sana’o’in gargajiya sun haɗa da Sarkin noma da Sarkin maƙera da Sarkin gini da Sarkin rini da Sarkin ɗori ga maɗora da Sarkin aska ga wanzamai da San ƙira ko Sarkin roƙo ga maroƙa da Sarkin fawa ga mahauta da sauransu da dama. Ita kuwa sana’a tafarki ne na dogaro da kai, ko kuma tafarki ne na tsayawa da ƙafafu domin biya wa kai buƙatu da suka shafi ci da sha da sutura da muhalli (Durumin Iya, 2006:IX).

Tun ran gini ran zane, al’ummar Hausawa tun can asali al’umma ce wadda ta dogara da kanta wajen samar da hanyoyin tattalin arzikinta. Ba a san Hausawa da kasala ko ragwanci ba, domin tun asali sukan tashi tsaye, tsayin-daka da yin sana’o’i daban-daban don wadatar da kansu daga buƙatunsu na yau da kullum. Ta haka ne ya zama a kowanne gidan Hausawa za a tarar yana da sana’o’in da yake aiwatarwa.

Buƙatar ɗan’adam ta son abinci da sutura da muhalli ne ya haifar da sana’o’i irin su noma da farauta da saƙa da gini da sauransu (Yahya da wasu, 1992:48).

Kasancewar sana’a tafarkin rayuwa ce da mutum kan riƙe ya riƙa aiwatarwa da zummar samun abin da zai biya buƙatunsa na yau-da-kullum. Haƙiƙa sanaoin Hausawa na gargajiya su ne mafi girman tafarkin da Hausawa suke bi domin samar da biyan buƙata. Domin kuwa ta hanyar sanaa ne suke sarrafa albarkatun ƙasa da sauran niimomin da Allah ya yi musu domin su mallaki abubuwan buƙata na rayuwarsu ta yau da kullum.

1.1 Dalilan Bincike

Ga al’adar nazari, akan samu wani abu da ya ja hankalin mai bincike ya gudanar da aiki a kan wani abu da ake laluben sanin yadda yake. A sakamakon haka, Hausawa suke cewa “Dalili mai sa a yi tsintuwar jigida a cikin gafaka”. Dalilin da ya sanya aka gudanar da wannan bincike shi ne: Duba yanayi da makomar sarautun sana’o’in gargajiya da sauye-sauyen da ake samu a cikinsu, tare da taskace al’adun da suke tattare da su. Wannan shi ne ya haifar da Sha’awar gudanar da binciken.

1.2 Manufofin Bincike

Babu wani bincike na ilimi da za a gudanar ba tare da wata manufa da yake son cimma ba. Daga cikin manufofin da aka gina wannan bincike akwai:

1.      Fito da yanayin da sarautun sana’o’in gargajiya suke ciki a yanzu.

2.      Gano ayyukan sarautun sana’o’in gargajiya da sauye-sauyen da aka samu a yanzu.

3.      Lalubo muƙamai da al’adun da ke tattare da sarautun sana’o’in gargajiya.

4.      Binciko matsayi da dangantakar sarautun sana’o’in gargajiya.

1.3 Tambayoyin Bincike

Domin daidaita akalar bincike, akwai manyan tambayoyi guda huɗu da wannan bincike ya duƙufa wajen samar da amsoshinsu. Samuwar amsoshin nasu shi ya kai ga cin nasarar manufofin wannan bincike. Bisa ga haka, an tsara waɗannan tambayoyi kamar yadda ake gani:

1.      Wane yanayi sarautun sana’o’in gargajiya suke ciki a yanzu?

2.      Waɗanne ayyuka ne sarautu sana’o’i suke yi, kuma waɗanne sauye sauye aka samu a yanzu?

3.      Waɗanne muƙamai ne da aladu suke tattare da sarautun sanaoin gargajiya?

4.      Wane matsayi da dangantaka sarautun sana’o’in gargajiya suke da shi?

1.4 Farfajiyar Bincike

Saboda gudun kauce wa kwasar karan mahaukaciya, an yi wa aikin kadada, inda aka taƙaita shi ga wasu sarautun sanaoin gargajiya a ƙwaryar birnin Kano. Hakan ya sa ake kauce wa kitso da kwarkwata. An ɗauki sarautun sana’o’in gargajiya waɗanda Sarkin Kano ne ya naɗa su, kuma suke wakiltar Sarki a wajen gudanar da waɗannan sana’o’i nasu. Sarautun sana’o’in da wannan bincike ya mai da hankali a kan sun haɗa da:

1.      Sarautar Sarkin Ɗori

2.      Sarautar Sarkin Fawa

3.      Sarautar Sarkin Gini

4.      Sarautar Sarkin Ƙira

1.5 Muhimmancin Bincike

Kamar kowane nagartaccen bincike, wannan bincike yana da muhimmanci mutuƙa, musamman a harkokin da suka shafi siyasar al’adun sana’o’in Hausawa na gargajiya. Wasu daga cikin muhimmancinsa sun haɗa da:

1.      Binciken zai taimaka wajen fito da tunanin Hausawa a kan waɗannan sarautu na sana’o’in gargajiya da yadda ake kallonsu a jiya da yau.

2.      Wannan aiki zai haskaka wa al’umma matsayi da kuma ayyukan sarautu sana’o’i a a jiya da yau.

3.      Gudanar da wannan bincike tamkar wata kafa ce da za ta zaburar da masu sha’awar nazari a wannan fage na sarautun sana’o’in gargajiya ta yadda za su iya hango wani giɓi da ba a cike shi ba, domin su yi ƙoƙarin cike shi, ko dai ta fuskar tarihin sana’o’in ko kuma al’adunsu.

4.      Aikin da aka gudanar zai zama wata gagarumar gudummawa da fagen nazarin al’adun Hausawa ya bayar wajen lalubo zamantakewar waɗannan sarautu na sana’o’in gargajiya wadda aka taskace.

5.      Binciken zai kasance tamkar wani kundi ne da aka taskace al’adun wasu sarautun sana’o’in gargajiya na jiya da kuma na yau. Wannan ya faru ne sakamakon neman hanyar tseratar da al’adun daga barazanar zamani da take kai wa al’adun Hausawa farmaki.

1.6 Waiwayen Tubalan Kalmomin Matashiya

Hausawa kan ce “Waiwaye adon tafiya”. A wannan bagire, an yi ƙoƙarin ganin an waiwayi maanonin tubalan kalmomin matashiyar wannan bincike. Yin hakan ya taimaka wajen ƙara ba da haske a kan wannan bincike.

1.6.1 Sauyi

Bargery (1934) ya fassara kalmar sauyi da “Exchanging”. Ma’ana sauyawa.[5]. Shi kuwa Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero (2006:394) ya bayyana ma’anar sauyi da cewa “Canji ko juyi”. Shi kuma Ƙamusun Hausa (2020:214) ya bayyana maanar sauye-sauye da cewa Changes” ma’ana sauyawa.[6]

Ta la’akari da waɗannan ma’anoni da suka gabata, wannan bincike na ganin sauyi a matsayin shugowar wani sabon abu cikin wanda aka saba da su yau da kullum, ko dai a sakamakon zamantakewa da baƙin alummu, ko tasirin zamani ko kuma addinin Musulunci.

1.6.2 Sarauta

Bargery (1934:905) ya bayyana sarauta da cewa: “Kalmar sarauta na nufi (noun) Any official position; the domain of any ruler.” Ma’ana duk wani matsayi da ya keɓanta da wani basarake.[7] Shi kuwa Gusau (1988:24) yana da tunanin sarauta ta jiɓinci: “Shugabantar wata jama’a ko ƙungiyar mutane don kiyaye addininsu da tafiyar da harkokin siyasarsu da kuma samar musu da hanyoyin jindaɗin rayuwa masu kyau da kyautata hanyoyin tattalin arziƙinsu da duk wasu ayyukan yau da gobe.”[8] Haka shi ma Gaya (1998:10) yana da ra’ayin sarauta tana nufin: “Gudanar da mulki ga talakawa ba tare da nuna bambanci ba, da kare ‘yancincinsu da walwala. Kodayake Gulbi (2000), ya ɗauki kalmar sarauta a sababbiyar hanya ce da Hausawa da ma waɗanda ba Hausawa ba suka gada tun kaka da kakanni ta hanyar yin amfani da wakilta wani mutum daga cikinsu domin ya jagorance su tare da ƙoƙarin ƙwato haƙƙin wani bisa ga wani idan buƙatar hakan ta taso.”Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero (2006:391) ya bayyana ma’anar Sarauta da cewa: “Suna ne na jinsi mace dake ɗaukar sarautu a matsayin jam’i mai nufin Shugabanci musamman irin na gargajiya.” Shi ma Muhammad (2020:10) ya bayyana sarauta da cewa “Mulki ko shugabanci ko jagoranci, bisa wani tsari da mutane suka amince wa.”

Bisa la’akari da bayanan da suka gabata, wannan bincike yana da ra’ayin cewa: Sarauta na nufin jagorantar al’umma ta hanyar kare lafiyarsu da dukiyarsu da ba su tsaro da kula da tattalin arziƙinsu da zamantakewarsu da sasanci da hukunci da kare haƙƙin alumma da sauran abubuwan da suka shafi alamuran rayuwarsu na yau da kullin.

1.6.2.1 Sarauta A Ƙasar Hausa

Idan aka ce asalin sarauta ana nufin bin diddigin tarihi samuwar sarauta a ƙasar Hausa tun a dauri. Sarautar gargajiya a ƙasar Hausa ta daɗe matuƙa ta yadda har wasu suke kwatanta daɗewarta da tsayin rayuwar Hausawa. Asalin sarauta yana farawa ne daga gida, wato matsayin mai gida a cikin iyalansa. Irin wannan gida da ake magana yakan zamo babba, wato gidan Gandu, inda za a samu maigida da ‘ya’yansa da jikoki da agololi da ‘ya’yan jikoki kai har ma da tattaɓa kunne da sauran dangi da barori da suke zaune a wannan gida (Saleh, 2006:32).

A irin wannan gida akan zaɓi Dattijo wanda ya fi kowa yawan shekaru a matsayin mai gida, wanda nauyin duk wanda yake a gidan ya rataya a wuyansa, tun daga kan cin su da shan su da kula da lafiyarsu da sauransu. A bisa al’ada, duk lokacin da maigida ya rasu, sai babban ɗansa ko ƙaninsa ya karɓi ragamar jagorancin gidan (Bello, 1991:3).

Yayin da waɗannan gidaje ɗaiɗaiku suke ƙara yawa, yakan zama dole mazauna wurin su zaɓi wani dattijo wanda ya fi kowa yawan shekaru, domin ya zama shugaba wato mai Unguwa. Akasari akan zaɓi wanda ya ƙware a kan sanaar da mutanen suka gada kuma suke gudanarwa. Misali: Noma ko Ƙira ko Saƙa ko Sassaƙa ko Wanzanci da sauransu. A lokacin da tafiya ta yi tafiya, mutane da suke zaune a wannan wuri, wato unguwa, sukan warwatsu zuwa wurare daban-daban, saboda matsalolin rayuwa da suka shafe su. Misali: mai gida yakan rarraba ‘ya’yansa, domin kula da wasu ayyuka kamar gona da garka da makamantansu. Wani lokaci akan sami babbar sana’a daga wannan Unguwa zuwa waccan. Ma’ana kusan kowace unguwa tana da irin sana’arta da kuma shugabanta (Bello, 1991:4).

Wannan warwatsuwa da aka yi takan sanya mutane su ƙara ƙaruwa a sassa daban-daban na unguwanni. Wannan yakan ƙara bunƙasa gari. Sai a zaɓi mutum daga cikin waɗannan rukunin unguwanni ko ƙauyuka a matsayin shugaba, wato Dagaci, wanda alhakinsa ne ya kula da wannan ƙauye ko rukunin unguwanni. Sanadiyyar ƙaurar mutane daga wasu wurare zuwa wannan ƙauye a ƙoƙarinsu na neman wajen zama ko farauta ko don tsaro, yakan sa waɗannan ƙauyuka su ƙaru ta fuskar jamaa da yawan gidaje da kuma filayen noma. Yayin da alumma suka yawaita, sai a sami gari babba, wanda yakan tilasta a zaɓi wanda zai shugabanci waɗannan ƙauyuka ko gari wato hakimi.

Idan aka sami yawaitar garuruwan hakimai, nan ma sai a zaɓi shugaba guda ɗaya wanda zai kula da sha’anin mulkin waɗannan garuruwa a matsayin Sarki. Yahaya (1979:93). A wannan lokaci akan zaɓi shugaba ne dangane da shahararsa a sana’ar da wannan al’ummar ko jaruntaka ko kwarewarsa ta fuskar tsafi.[9] Yahaya da wasu (1992). Sun bayyana hanyoyi uku da ake la’akari da su wajen zaɓen shugaba. Hanyoyin kuwa sun haɗa da: Shugabancin da yake farawa daga gida, wato inda ake zaɓen mai yawan shekaru a matsayin maigida, wanda jagorancin al’amuran iyalin wannan gida suke wuyansa a matsayinsa na maigida.

Haka kuma, akan zaɓi shugaba ta fuskar jaruntaka, musamman kasancewar wancan zamanin lokaci ne na yawaitar yaƙe-yaƙe. Wannan yanayi na rashin zaman lafiya da tsaro, shi ya sa jama’a sukan zaɓi jarumi wanda zai tsaya a matsayin shugabansu, don ya taimaka musu wajen kare su daga hare-haren abokan gaba.

Har ila yau, ana la’akari da addini wajen zaɓen shugaba, amma kafin zuwan addinin Musulunci akan sami mutane da suka yi fice da kuma kula da wuraren tsafe-tsafe, ma’ana waɗanda suka ƙware ta fuskar tsafi. Wasu na ganin sarauta a ƙasar Hausa ta faro ne ta wannan hanya ta bautar iskoki, waɗanda suke da tasiri har yanzu a zukatan Hausawa.

1.6.3 Sana’a

Masana da manazarta sun bayar da irin tasu gudummawa wajen bayyana ma’anar sana’a. Ga abin da wasu daga cikinsu suke cewa: Musa, (1991) ya bayyana sana’a da cewa “Wata hanya ce da ɗan’Adam kan bi ta hanyar yin amfani da hikimomin da Allah ya hore masa don samun abubuwan gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum”. Shi kuwa Sani, (1995) ya bayyana sana’a da cewa, hanya ta amfani da azanci da hikima a sarrafa albarkatun da ni’imomin da ɗan’Adam ya mallaka don buƙatun yau da kullum. Don haka, sanaa aba ce wadda mutum ya jiɓinci yi da nufi samun abin masarufi don gudanar da harkokin rayuwa. Muhammad da Ibrahim, (2004) suna ganin sana’a a matsayin hanya ce ta sarrafa albarkatun ƙasa da sauran niimomin da Allah ya yi wa ɗan’Adam kamar amfanin gona da dabbobi da tsirrai da kuma wasu albarkatu waɗanda suke ƙarƙashin ƙasa, ya Allah dutse ko kuma ruwa domin samun abin masarufi. Sai dai Muhammad, (2019) na ganin sana’a hanyoyi ne da ake gudanar da saye da sayarwa da harkokin yau da kullum, ko sarrafa wani abu zuwa wani nau’in daban. Duk da haka, kowa ce sana’a tana irin yadda ake gudanar da ita, da masu yin ta, da wurin gudanar da ita, da abubuwan da ake gudanar da ita.

Bisa ga wannan ma’anoni da masana suka bayar a kan sana’a, wannan aikin yna ganin sana’a da cewa “Hanya ce da al’umma suke amfani da ita wajen sarrafa wasu albarkatu domin saye da sayarwa ga mabuƙata tare da samun abin rufin asiri na yau da gobe.

1.6.3.1 Asalin Sana’o’in Hausawa na Gargajiya

Abu mai wuya ne a ce ga takamaimai lokacin da sana’a ta samu ko kuma asalinta ga al’ummar Hausawa. Sanin asalin sana’o’i’n Hausawa na gargajiya abu ne da ake ta hasashe kawai a kansa. Hasashen ya nuna cewa sana’a ta samu a lokacin da al’ummar Hausawa suke da buƙatuwar wasu muhimman abubuwa na rayuwa, kamar abinci da sutura da muhalli. Waɗannan buƙatu su ne suka assasa samuwar sanaoin Hausawa na gargajiya.

A lokacin da Hausawa suka gane dabarar noma, wanda ake wa kirari da “Na duke tsohon ciniki kowa ya zo duniya kai ya tarar”. A wannan lokacin ba su da kayan aiki, da hannu ake yin noma. Da aka fara ci gaba, sai suka gane dabarar feƙe ɓangarorin duwatsu, a yi wa wasu faɗi wasu kuma a yi musu tsini domin su huta yin amfani da hannunsu. Da tafiya ta yi tafiya, suka gane dabarar sarrafa ƙarafa domin yin fartanya ta aikin noma. Har sannu a hankali suka fara gyara kayan aikin nomansu daidai da zamaninsu. Wannan gyare-gyare da suke yi, shi ne ya sa wasu daga cikin Hausawa suka zama gwanaye wajen ƙera abubuwan amfani na yau da gobe. Ganin yadda suka kware a wajen ƙere-ƙere ya sa suka dai na fita farauta a lokacin rani suke tsaya suke yin ƙira. Ƙira ta zame musu wata sabuwar sana’a bayan noma. Rimmer da Wasu (1948:42). Waɗansu suka koyi saƙa, waɗansu kuma suka koyi kwaɓa yumɓu suna gina tukwane waɗansu kuma sassaƙa.

A hasashen Auta (1983) yana ganin cewa, buƙatuwar ɗan’Adam na abinci su ne suka haifar masa da sana’o’i kamar noma da farauta da dai sauransu. Haka kuma, buƙatun ɗan’Adam na sutura da su ne sanadiyar samun sana’ar jima da rini da saƙa da ɗinki da sauransu. Har ila yau, buƙatar ɗan’Adam na tsaron lafiya su ne suka haifar da sana’ar bori da tsibbu da ‘yar maiganye. Kasancewar ɗan’Adam mai son hutu ne da nishaɗi ya sa aka samu sana’ar kiɗa da waƙa. Sannan akwai kuma batun motsa jiki da suka haifar masa da sanaar dambe da kokawa da shaɗi da dai sauransu. Wannan a taƙaice kenan dangane da asalin sanaoin Hausawa na gargajiya.

1.6.4 Gargajiya

Masana da manazarta sun yi ƙoƙari wajen bayyana maanar kalmar gargajiya daidai ƙoƙarinsu. Saboda haka, an dubi abin da wasu daga cikinsu suke cewa dangane da wannan kalma ta gargajiya.

Bunza (2006:xxvii) ya bayyana cewa an samo kalmar gargajiya daga kalmar gado ne, daga nan ta koma zuwa gadajje da gargajiya. Ya ƙara da cewa, kalmar gargajiya ta yi ƙaurin suna musamman idan aka ce gargajiyar Bahaushe da ke takin-saƙa da kyawawan a ƙidojin Musulunci. Nason addini Musulunci a zukatan Hausawa ya jawo wa kalmar gargajiya cikas da a yi amfani da ita ta wakilci nazarin al’ada na gaba ɗaya.[10]

Bisa ga haka, wannan bincike na iya kallon gargajiya da cewa duk wata al’ada da Hausawa suke aiwatarwa wadda suka gada tun daga kaka da kakanni. Sannan suka tashi a cikin kuma har tsawon rayuwarsu suna gudanar da wannan abu da suka gada da kakaninsu, ba tare da shigar zamani ko wata baƙuwar alada ta wayewa ba.

1.6.5 Waiwayen Tarihin Birnin Kano a Taƙaice

Tarihin birnin Kano ba ɓoyayye ba ne a ƙasar Hausa. Wannan ya samo asali ne tun daga fice da birnin ya yi ta fuskar kasuwanci a ƙasar Hausa, da ma nahiyar Afrika baki ɗaya. Akwai rubuce-rubuce da dama da aka gudanar a mataki daban-daban na ilimi a kan wannan ƙasaitaccen birni. Daga cikinsu akwai: Palmer (1908) da Dokaji (1958) da Bahago (1998) da Waya (2000) da Ibrahim (2001) da Gwangwazo (2004) da Gwangwazo (2005) da Almajir (2009) da Bilhassan (2018) da Dan-iya (2020).

A bisa wannan, kawo tarihin birnin Kano tiryan-tiryan zai zama maimaici ne kawai a kan abin da aka riga aka kundace a rubuce-rubucen da suka gabaci wannan. A sakamakon haka, wannan binciken ya mayar da hankali a kan waɗansu muhimman al’amura game da wannan ƙasaitaccen birni.

Kano tana ɗaya daga yankin tsakiya na arewacin ƙasar Hausa. Daga gabas ta yi iyaka da ƙasashen Barno da Bauchi, daga yamma ta yi iyaka da Katsina, daga kudu ta yi iyaka da Zariya, daga arewa kuwa ta yi iyaka da Jamhuriyar Nijar Dokaji (1958:1). Kano gari ne na Hausawa, kuma cibiyar ilimi da siyasa da sanaa da kasuwanci ta ƙasar Hausa. Don haka ne garin ya zamo alƙarya tun da ita ce tsakiyar Sudan duka. Wannan ya yi daidai da wasu baitukan Aminu Ladan Abubakar (Alan Waƙa). A cikin waƙar Tumbin Giwa baiti na biyu (2) da na uku (3), inda yake cewa:

Kano garin saye da sayarwa tun zamanin zuwan Larabawa,

Tun zamanin su Shehu Maghili an san mu kan siye da sayarwa,

Waɗanda suka kawo saƙon Manzon mu adali ɗan baiwa,

Jalla uwar jahohin Hausa mai tambari da tumbin giwa.

 

Jahohi anai musu take mu namu tambarin kasuwa,

Kasuwa a kai miki dole ko an ƙi ko ana so baiwa,

Mahadi ta al’ummomi kowane ɗan jaha ya zowa,

Uwa ma ba ɗiya mama ƙasurgumin gari son kowa.

 

Ba a iya nan ya tsaya ba a cikin baiti na biyar (5) na wannan waƙa, ya ƙara da cewa:

 

A ɓangaren sana’ar hannu mun markaɗe jahohin kowa,

Na tuno ranar baje koli ranar da na gano turawa,

Sun zo suna ta yin ta’ajibi an kai su sun gano dukawa,

Balle a kai su fannin ƙira ko nahiyar ta majemawa.

 

Gusau (1988:54) ya bayyana cewa, farfajiyar Kano tana daga cikin wurare masu yalwa mutuƙa da albarkar ƙasa, don haka, noma ya zama babbar sanaa a wannan wuri. Sannan ana samun ƙarfen tama da ake haƙo shi daga bakin dutsen Dala da sauran duwatsu da suke zagaye da wannan wuri, da ake amfani da shi wajen ƙere-ƙere. Wannan yanayin wurin ya sa mutane daga wurare daban-daban sun yi wo ƙaura zuwa birnin Kano. Don haka, wasu suka ci gaba da zuwa wurin suna zama a gindin sauran tsaunuka da suke kewaye da wurin, kamar dutsen Magwan da Fanisau da Gwauron Dutse da sauransu.

Dangane da asalin sunan wanann kuwa, Almajir (2009:25) ya rawaito cewa “Sunan shugaban Abagayawa da suka fara zuwa suka zauna a waurin shi ne Kano. An ce daga sunansa ne wannan farfajiya ta samo na ta sunan, wato Kano. Abagayawa sun zauna lokaci mai tsawo a Kano. Sannan kuma suna samun ruwan shan su ne daga kogin Jakara da ya ratsa birnin Kano. Shugaba na biyu a jerin shugabannin Abagayawa wanda ya fi duk sauran shahara shi ne, Barbushe. Bayan barin mulkinsa ne sai matsaloli suka taso waɗanda suka jefa Kano da mazaunanta cikin ruɗani da rashin kwanciyar hankali. Wannan ne ya sa wasu mutanen Kano suka dinga zuwa Daura. Wannan ta sa Sarkin Daura Bawo ya aiko ɗaya daga cikin ‘ya’yan sarautar Daura mai suna Bagauda domin ya je ya tabbatar da zaman lafiya a Kano.

Almajir (2009:26) ya sake rawaitowa cewa: Ƙwalli (1996:278-279) ya bayyana yadda Jihar Kano ta samu kafuwa kamar haka:

“Yunƙurin samar da jihar Kano kuwa ya samo asali ne tun lokacin Sarki Sunusi murabus (1963-1964). Ganin haka ‘yan Kano da dama suka fita daga jam’iyyar NPC da NEPU, suka kafa Kano People’s Party, wadda daga baya ta juya ta zama Kano State Movement. Wato ƙungiya mai neman kafuwar Jihar Kano. Shugabannin ƙungiyar sun haɗa da Alhaji Ahmad Tireda da Alhaji Tanko Yakasai da Malam Aminu Kano da sauransu. Haka abin ya ci gaba har zuwa ranar 24/05/1967 aka samar da Jihar Kano.”

Haka kuma, Almajir (2009:26-27) ya bayyana cewa: Adamu (1999:116) ya faɗi yadda aka fara faɗaɗa ƙasar Kano kamar haka: Tsara birnin Kano da faɗaɗa shi ya fara ne tun zamanin Sarkin Kano Muhammadu Rumfa (1463-1499). Shi ne ya gina gidan Sarki a wurin da yake a yanzu, kuma ya daddatsa birni ya zuwa unguwanni guda goma. Waɗannan unguwanni sun haɗa da; Makama da Sheshe da Yakasai da Ƙoƙi da Daurawa da Kududdufawa da kuma wasu uku da tarihi bai tabbatar da su ba. Sannan ƙauyuka da suke gefen garin Kano da ke ƙarƙashin kulawar Sarki su ne Waika da Ɗorayi da Jaen da Salanta da da kuma Gwagwarwa.

Adamu (1999:20-25) ya bayyana cewa mazauna garin Kano kaso biyu ne. Al’ummar Maɗatai,[11] waɗanda Yamalawa ne masu noman rani. Babu tabbacin lokacin da suka zo Kano, amma bayanai sun tabbatar da cewa rushewar wata madatsar ruwa da suke zaune a kusa da shi ne ya sa suka warwatsu a duniya. Zaman su a Gaya da farko ya sa sun koya wa al’umma noman rani. Kasancewar ana ta samun kwararowar al’umma, sai wasu maharba suka zo, suka zauna tare da waɗannan Yamalawa. Shugabanninsu sune; Gwale da Sheshe da Yakasai da Guguwa. Kowane daga cikinsu ya shaci fili domin yin noma. Waɗannan wurare kuma daga baya sun zama unguwanni da suka haɗa da unguwar Gwale da unguwar Yakasai da unguwar Sheshe a cikin birnin Kano da kuma Ɗanguguwa a cikin Dawakin-Tofa.

Wannan shi ne ya jawo mutanen Kano a wannan lokaci suka daina yin farauta, suka koma noma. A irin wannan noma suna yin kayan abinci sosai, kuma wannan lokaci ya yi dai-dai da ɓarkewar yunwa a yammacin Afrika. A wannan lokaci a Kano ne kawai ake samun isasshen abinci. Don haka, sai mutane daga ɓangarori daban-daban suka yi ta zuwa birnin Kano. Wannan dalilin ya sa wannan birni ya tumbatsa har ya kere sa’a ta fuskar kasuwanci da yawan al’umma da sauransu da dama.

1.7 Naɗewa

Wannan babi a taƙaice, ya tattauna a kan shimfiɗa da dalilin bincike da manufofin bincike da kuma maƙasudan bincike. An kawo tambayoyin bincike da farfajiyar bincike da kuma muhimmancin bincike. Sannan babin ya yi ƙoƙarin waiwayen tubalan kalmomin matashiyar wannan bincike, inda ya waiwayi kalmar falsafa da sarauta da asalin sarauta a ƙasar Hausa. Haka kuma, ya waiwayi maanar sanaa da asalin sanaoin Hausawa na gargajiya da kuma maanar kalmar gargajiya. Daga ƙarshe babin ya waiwayi tarihin birnin Kano sai kuma naɗewa.



 1Wasu daga cikinsu sun haɗa da: Palmer, H. R. (1908). The Kano Chronicle”. The Journal of the Royal Anthropologica Institute of Great Britain and Ireland, vol. 38, pp. 58-98. da Muhammad, M.(2020). Bahaushiyar Al’ada. Kano: Bayero University Press.

[2] Bunza, A. M. (2023). “Sarauta a Tsarin Ikon Ƙasar Hausa (Yadda Take da Yadda Ake Samar da Ita)”. Maƙalar da Aka Gabatar a Taron naɗin Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo a Matsayin Sarkin Malaman Hausa na Afrika, a Fadar Sarkin Hausawan Afrika Dr. Abdulƙadir Koguna Da ke Unguwar Yola a Cikin Birnin Kano, ranar Asabar 3/06/2023.

[3] Alhassan da Wasu (1988:67). Zaman Hausawa. Bugu na Biyu. Lagos: Islamic Publications Bureau.

[4] Tattaunawar da aka yi da Ɗanrimin Kano, Alhaji Sarki Waziri a ofishinsa dake Hedikwatar masarautar Kano (Kano Emirate Council), ranar Talata 5/4/ 2022 da misalin ƙarfe 3:20 na yamma.

[5] Daidai da ɗure na biyar (5).

[6] Fassarar mai bincike

[7] Fassarar mai bincike.

[8] Gusau, S. M.(1988). Waƙoƙin Makaɗan Fada: Sigoginsu da Yanayinsu, Musamman A Ƙasar Sakkwato. Kundin Digiri na Uku (PhD), Sashe Koyar da Harsunan Nijeriya. Kano: Jami’ar Bayero.

[9] Tsafi da bautar iskoki tana da muhimmanci game da samuwar sarauta a ƙasar Hausa. A sanadiyyar hakan, aka sami wasu manyan garuruwan ƙasar Hausa da suka faro sarauta ta irin wannan tsari. Misali: Wurare irin su dutsen Dala wanda yake da Tsumburbura a ƙasar Kano. Kuma Barbushe shi ne shugaban wannan tsafi. A dutsen Kufaina wanda mutanen Zariya suke bautar dodannin da ake kira Madaru da Kufe. Haka abin yake a wurin Maguzawan Kaina-fara, wato Arnan Birchi, suna bautar Ɗantalle a cikin dutsen Birchi a Kurfi ta ƙasar Katsina.

[10] Bunza, A.M (2006). Gadon Feɗe Al’ada. Jerin Littattafan Cibiyar Nazarin Al’adun Hausawa. Lagos: Tiwal Nigerian Limited.

[11] Wannan al’umma ta Maɗatai su suka kafa wasu garuruwa a gefen garin Kano. Kamar su; Lambu da Kanwa da Kwankwaso da Kura da Tamburawa da Yankatsari da Mariri da kuma Gunduwawa.

Post a Comment

0 Comments