Kowa ya san cewa; Addinin Muslunci ya ginu ne a kan imani da Allah da imani da Manzonsa Muhammad (saw).
Imani da Annabi (saw) kuwa ya kunshi gaskata shi cikin Manzancinsa, da gaskata shi cikin duk abin da ya ba da labari, saboda ba bisa son ransa yake magana ba, duk abin da ya fada gaskiya ne da wahayi daga Allah. Allah ya ce
{وَمَا يَنْطِقُ عَنِ الْهَوَى (3) إِنْ هُوَ إِلَّا وَحْيٌ يُوحَى
(4)} [النجم: 3، 4]
Don haka
kamar yadda gaskata shi ya kunshi bangarori biyu, haka karyata shi ma ya kunshi
bangarori biyu
1- Karyata Annabi da yake kore imani da shi, wato
karyata Manzancinsa. Lallai wannan kafirci ne mai warware Musluncin mutum.
Allah ya ce
{وَإِنْ تُكَذِّبُوا فَقَدْ كَذَّبَ أُمَمٌ مِنْ قَبْلِكُمْ وَمَا عَلَى
الرَّسُولِ إِلَّا الْبَلَاغُ الْمُبِينُ } [العنكبوت: 18]
Kuma ya ce
{إِنْ كُلٌّ إِلَّا كَذَّبَ الرُّسُلَ فَحَقَّ عِقَابِ } [ص: 14]
2- Karyata shi a abin da ya ba da labari a
Hadisansa, imma karyatawa kai tsaye, ko ta hanyar canza magana da yin
Tawilinta. Wannan kuma yana tauye cikan imani da Annabi (saw). Sahabban Annabi
(saw) sun kasance suna gaskata shi a kan dukkan abin da ya ba su labari.
Allah ya ce:
{وَلَمَّا رَأَى الْمُؤْمِنُونَ الْأَحْزَابَ قَالُوا هَذَا مَا وَعَدَنَا
اللَّهُ وَرَسُولُهُ وَصَدَقَ اللَّهُ وَرَسُولُهُ وَمَا زَادَهُمْ إِلَّا إِيمَانًا
وَتَسْلِيمًا } [الأحزاب: 22]
Wannan ya sa Alkali Iyadh ya ce
أنا نعلم من دين الصحابة وعادتهم مبادرتهم إلى تصديق جميع أحواله
وللثقة بجميع أخباره في أي باب كانت وعن أي شئ وقعت وأنه لم يكن لهم توقف ولا تردد
في شئ منها ولا استثبات عن حاله عند ذلك هل وقع فيها سهو أم لا؟
الشفا بتعريف حقوق المصطفى (2/ 135)
"Mun san cewa; Addini ne a wajen Sahabbai
kuma al'adarsu ce, suna gaggawan gaskata dukkan halayen Annabi (saw), suna
aminta da dukkan labarun da yake ba su a kowane babi ya kasance, kuma ko da a
kan komai labarin ya faru, kuma Sahabbai ba sa dakatawa ga karban labari daga
wajensa, ko su yi shakkan karban wani abu daga labarin, ko su tsaya binciken
neman tabbatar da halin da yake ciki a lokacin da ya ba da labarin, suna
tambayan cewa: mantawa ya yi ne ko a'a?".
Haka halin Sahabbai yake. Wannan ya sa a muka yi
imanin cewa: Duk Sahabban da suka san Annabi (saw) ya ce: Iyayensa suna wuta,
to dukkansu sun gaskata shi, babu mai shakka a kan haka. Shi ya sa har yau ba a
samu wanda ya fadi wani abu a kai ba. Saboda sun ji, sun gaskata, sun mika
wuya, shi kenan magana ta kare.
Haka sauran Salaf suke a dukkan abin da ya ba da
labari a kai. Tabi'i Imamu Zuhriy Malamin Imamu Malik ya ce
«من الله عز وجل العلم، وعلى الرسول البلاغ، وعلينا التسليم»
السنة لأبي بكر بن الخلال (3/ 579)
"Allah ne mai ilimi da ya san komai, Manzo
kuma aikinsa isarwa ne, mu kuma gaskatawa da yarda da mika wuya shi ne
wajibinmu".
Saboda haka, hakikanin imani da Annabi (saw) shi
ne gaskata shi a dukkan abin da ya tabbata ya ba da labari.
Alkali Iyadh ya ce
والإيمان به صلى الله عليه وسلم هو تصديق نبوته ورسالة الله
له وتصديقه في جميع ما جاء به وما قاله
الشفا بتعريف حقوق المصطفى (2/ 3)
"Imani da Annabi (saw) shi ne gaskata
Annabtarsa da Manzancinsa, DA GASKATA SHI a dukkan abin da ya zo da shi, DA
DUKKAN ABIN DA YA FADA".
Saboda haka kawai imani da Annabi (saw) ake so mu
yi da gaskata shi a dukkan labari da ya tabbata daga gare shi, sai mu ja
bakinmu mu yi shiru kamar yadda Sahabbai da Tabi'ai suka yi. Amma in muka ce:
za mu yi Tawili da canza ma'anar Hadisi, to alal hakika mun kama hanya
karkatacciya.
Dr.
Aliyu Muh'd Sani (H)
12
June, 2017
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.