Ticker

6/recent/ticker-posts

Haɗin Kan Musulmi a Wajen Aikin Hajji

HADIN KAN MUSULMI A WAJEN AIKIN HAJJI

Kusan duk shekara ana samun karin kusantar juna tsakanin Malamai Ahlus Sunna da Malaman bidia a wajen Aikin Hajji, la'alla da nufin neman hadin kan al'ummar Musulmi.

To, lallai Hadin kan Musulmai lamari ne mai girma, mai muhimmanci. Abu ne da Allah ya wajabta shi, kuma ya fadi yadda ake yinsa.

To a yau gama garin mutane, da 'yan siyasa, da shugabannin gomnati, da 'yan boko jahilai suna so Musulmai su hada kai. To amma su irin wadannan mutane da yake mafi yawansu sun jahilci iyakokin abin da Allah ya saukar wa Annabinsa (saw), irin hadin kan da suke so a yi ba irinsa Allah ya ce a yi ba. Kuma ba irinsa ne hadin kai mai haifar da d'a mai ido ba.

Asali hadin kan da Allah ya yi umurni da shi, shi ne haduwa a kan riko da igiyar Allah, bin Alkur'ani da Sunna, haduwa a kan Musluncin da Sahabbai da Tabi'ai suka rayu a kai. Idan kowa ya bar bidi'arsa, dan Darika ya bar Sufancinsa, dan Shi'a ya bar Rafidhancinsa, dan Kala-kato ya bar Qur'aniyancinsa, ya zo aka hadu a kan Alkur'ani da Sunnar Annabi (saw), bisa tafarkin Musulman farko to shi ne an yi hadin kai na gaskiya, za a dena fada da juna. A nan ne za a samu hadin kan Musulmi mai dorewa.

Amma saboda jahilci ko maslaha sai wadancan mutane suke zaton za a iya hadin kai ba tare da kowa ya bar bidi'arsa ba. To alal hakika wannan ba zai samu ba, sai dai idan wanda yake kan tafarkin Sunna ya fifita maslahar samun abin duniya, na dukiya da daukaka, ya koma girmama Malaman bidi'a, yana kambama su. Duk don a nuna neman hadin kai, da nuna sassaucin ra'ayi, da nuna cewa Ahlus Sunna ba sa yin abin da ake zarginsu da shi na kafirta 'yan Darika da bin tsattsauran ra'ayi, da makamancin haka.

Lallai yanzu muna zamani ne na fitina, an kakaba mana talauci, da yawa cikin masu wa'azi suna ra'buwa da 'yan siyasa, don samun abin duniya, da daukaka da shahara. Don haka malami ya tsare Addininsa a wannan yanayi yana da wahala, kuma kokarin hakan yana cikin Jihadi. Don kawai biyan muradun gomnati da bukatun 'yan siyasa kada ka yi sakaci da Manhajinka na tafarkin Sunna.

Allah ya kare mana Addininmu, ya ba mu wadatar zuci, ya tabbatar da mu a kan tafarkin gaskiya.

Dr. Aliyu Muh'd Sani
18 June, 2024

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments