Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Azumin Tasu'a Da Ashura A Ranar Da Aka Hana Azumi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum warahmatullah Malan. An yini Lafiya ya koqari Dakuma karatu Allah ya taimaka Kuma Muna godiya Sosai. na ce Malan Dan Allah a daure aqara mana karatu Dakuma dogon bayani kan azumin tasu'ah Dakuma ashura Dan wasu Suna Ganin Kamar ranar da zai fada ranar yin azumin tasu'ah Dakuma ashura Kamar Wai ba ranakun da'ake son yin azumin ba ne to shi ne nake so Malan yaqara wayar mana dakai.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis salaam wa rahmatullahi wa Barkatuhu, Ameen Ya Yayyu Ya Qayyum 🤲🏽.

Toh 'Yar uwa ai hadisi ya zo daga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam cewa, "Kada ku yi azumi ranar asabar sai abin da aka farlanta muku Shi". (Abu-dawud hadisi mai lamba ta :2423).

Sai dai malamai sun yi saɓani akan ingancin wannan hadisin, akwai malaman da suka tafi akan cewa hadisin karya ne, Abu-dawud ya hakaito hakan daga Imamu Malik.

Akwai waɗanda suka inganta shi, akwai kuma malaman da suka ce hadisin akwai kuskure a ciki, saboda ya Saɓawa hadisin da ya fi shi inganci, inda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yake cewa; "kada ɗayan ku ya azumci ranar juma'a, sai in ya azumci yinin da yake gabanin ta, ko kuma wanda yake bayan ta". (Bukhari a hadisi mai lamba ta 1884,). wannan hadisin yana nuna halaccin azumtar asabar ga wanda ya azumci juma'a.

Akwai malaman da suka tafi akan cewa wannan hadisin an goge shi da wasu hadisan, saboda yadda aka rawaito cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yana azumtar mafi yawan kwanaki a cikin watan Sha'aban, wannan sai ya nuna cewa dole asabar ma za ta fado a cikin azumin sa, ga shi kuma Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Ya halatta yin irin azumin Annabi Dawud, wanda za ka yi azumi yau ka sha gobe, ke nan babu yadda za a yi mutum yayi azumin Annabi Dawud ba tare da Asabar ko Juma'a ta fado a cikin Azumin sa ba.

Zancen miliyoyin malamai shi ne ya halatta ayi azumi ranar asabar ga wanda yayi Azumi ranar juma'a. Don neman karin bayani duba: Tahzibu sunani Abidawud 1\469

Sa'annan Azumin indai sun fado a ranar Juma'a ko Ranar za a yi su wadda su waɗannan Azumin hanin da ake Faɗi akan sa babu shi dole ne idan Azumi ya Fado a ranar Juma'a, ko Asabar ko Lahadi toh mutum zai yi Azumin sa, kamar misalin Azumin Arfa.

Azumin Arfa sai ya Faɗo a ranar asabar ne, ko Juma'a ko Lahadi duk za a yi domin babu wannan hanin a kansa, Ku Dena Amfani da maganar jahilai cewa wai bai halatta ayi ba, Karfi da yaji a Haramta Muku samun wnnan ladan ku, Akan Cewa Wai ba a yin Azumi ranar Ranar asabar ko Azumin Ranar Juma'a. Shakka babu Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya hana Musulmai yin Azumi a ranar Juma'a kaɗai da asabar, _Ma'ana ki ware ranar Juma'a ko asabar kaɗai, ki ce a wannan ranar ne zakiyi Azumin ki ko Azumin Ramako ko wani Azumin da kike so ki samu Ladan ki, ko Kuma ki ce sai Ranar lahadi kaɗai, duk Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya Hana yin Azumi a Irin Waɗannan ranakun. Toh amma Wannan Azumin da Za a Yi a Ranar Juma'a da asabar Bai shafi hanin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yake nufi ba, domin Azumi ne na Nafila Kuma Azumi ne wadda yake da sababi irin wancan ba ne.

Sabida haka Azumin ARFA, Azumin ASHURA da TASU'A, duk Wannan idan sun Faɗo a irin waɗannan ranar Za a iya yin Azumin nan babu Wannan hanin. Sabida haka a ji tsoron Allah a bar mutane su yi Ƙayan su idan ke ba zakiyi ba toh kada ki cewa wasu kada su yi. Idan Kai ba zakayi ba toh Bai kamata ka Haramtawa Bayin Allah yin Azumin su ba. Idan har Nafila na Zama Mai sababi ce, toh ana iya yin sa ko da a lokacin Hani ne domin Halin Bai shafe shi ba, balle ma ai wannan Azumin ya zo daidai da abun da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce Idan za a yi asabar toh dole ne a fara shi daga Juma'a. Kuma ai wannan Azumin ya fara daga Juma'a ne zuwa Asabar kin ga ke nan daidai ne, ko kuma idan ba ki samu yin Juma'a ba toh sai kiyi Asabar naki da Lahadi duk ya halatta.

Cewa akayi, ayi Azumin ranar Tasu'a Da Ashura ne, ai bawai kaine ka kayyade wannan ranar cewa dole zakayi Azumin a wannan ranar ba, Allah da iKon sa ne ya sa Azumin zai faɗa a ranar Juma'a da asabar, ke nan babu wani hani a kansa, sai dai idan kaine za ka Hana kanka. (Bukhari 1985, MUSLIM 1144). Malamai Sun yi magana akan ba za a yi Azumi a ranar Juma'a ko asabar kaɗai ba, (Tirmizy 744 da abu-dawud 2421, Bnu majah 1726). duk Suna magana Akan ba a yin Azumin ranar asabar ko Juma'a kaɗai sai wadda Allah ya farhanta muku shi.

Sabida Haka wannan Azumin Mai sababi ne Bai dace ace ana ta yada abun da Bai dace ba ko ba a San hukuncin abun ba, a Hana mutane yin Aikin Ladan su, kowa sai ya amsa tambaya a ranar Alkiyama. Allah ya tsare. ana ta yadawa status ne a ko Ina a social media ai Bai halatta ayi Azumin ba tunda ranar Juma'a da asabar ba, waye gaya ma? a Rika fahimtar Hadisan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam dakyau don Allah. Allah ya shirya.

Sa'annan ko ana bin ki Bashin Azumin watan Ramadan kina iya yin wannan Azumin Tasu'a Da Ashura ɗin ki daga baya kiyi niyyar Rama Azumin Farillah naki shike nan, sa'annan ko kin makara kina iya wucewa da wannan Azumin matukar za ki iya, sai dai Sharadin ya kasance cewa tun daga lokacin da kika farka har zuwa safiya ba ki ci komai ba, toh sai ki wuce da Azumin ki, idan kuma kin ci wani abun toh shike nan ba za kiyi Azumin wannan Yinin ba, shi Azumin Nafila ko mutum bai kwana da Niyya ba zai iya kulla niyyar sa da Safe indai bai ci komai ba, domin haka inda Hadisan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam suka nuna Hakan cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yana zuwa gidan sa ya ce akwai Karin Kumallo? Idan an ce eh! Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya karɓa Abincin ya ci, idan an ce babu sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce toh ya wuce da Azumi, sabida haka za ki iya yin haka kema indai za ki iya yin sa.

Baya ga Hakan idan ba ki samu damar yin Azumin Tasu'a ba toh sai kiyi na Ashura sai ki haɗa shi da ranar Lahadi, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya Sanya yin Azumin Tasu'a ne a dalilin cewa a Saɓawa Yahudawa da Nasara, sabida haka idan ba ki samu yin na ranar Juma'a ba toh sai kiyi Asabar da kuma Lahadi yayi. Allah ya amsa mana ya bamu Ladan sa Ameen Ya Yayyu Ya Qayyum 🤲🏽.

Wallahu A'alamu.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments