HUKUNCIN RUFE ƘAFAFU A CIKIN SALLAR MACE
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu. Ina wuni Malam fatan ka wuni lafiy. Ya hakuri da mu. Allah ya saka da alhairi. Allah ya qara illimi mai amfani da albarka. Mene ne Hukuncin rufe kafa yayin Sallah. Na ji wasu sun ce idan ba a rufe ba. To wai Sallah ba ta Inganta ba.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salám,
malamai sun yi saɓani game da
hukuncin rufe qafafun mace mai sallah, ta inda mafi yawan malaman Musulunci
suke da fahimtar suturta qafafu ga mace mai sallah wajibi ne, saboda mace gaba ɗayanta al'aura ce in banda fuska da tafukan hannu. Wannan
ita ce fahimtar maz'habar Malikiyya da Shafi'iyya da Hanabila. Amma su
Hanafiyya suna da fahimtar cewa rufe qafafu ga mace a lokacin sallah ba wajibi
ba ne saboda a wurinsu qafafu ba al'aura ba ce. Duba Almausu'atul Fiqhiyya
(7/85).
Saboda haka ne mafi yawa
daga cikin malamai suka ce idan mace ta yi sallah alhali qafafunta a buɗe sai ta sake yin wata sallar matuqar lokacinta bai wuce
ba, amma sallolin da lokacinsu ya wuce ba za ta rama su ba saboda uzurin rashin
sani.
Abin da ya fi dacewa shi
ne mace ta fita daga cikin saɓanin malamai ta
riqa rufe qafafunta a duk sallar da za ta yi, sallolin da ta yi a baya kuma ba
sai ta rama su ba saboda a lokacin ba ta sani ba.
Allah S.W.T ne mafi
sani.
Jamilu Ibrahim Sarki,
Zaria.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.