Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Kasuwanci Da Kudin Zina

HUKUNCIN KASUWANCI DA KUƊIN ZINA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam dafatan kana lfy Allah ya ba ku ladan aikinku na alhairi. Malam tambayata shi ne wata yayata ce abaya tana zina har tasayi Kayan sawa tasayawa iyayenta kuma suna ibada dakayan kai harda itakanta tana sallah dashi to yanzu ta tuba tabar yin zina kuma batada sana'ar yi indai tana zaune za ta Iya koma aikin zina don tasamu kuɗin Sabulu da sauran bukatunta da yaranta marayu guda uku shi ne ta tambayi wani malamin shin kudinta da tara nazina yakai dubu 40 shi ne takeso tahada dawani kuɗin taja jari don rufin asirinsu sai ya ce ya hallata data gayamin na ce bari nayi bincike cikin lamarin daga gurin malaman sunnah.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumusalam warahmatallahi wabarakatuh.

Ya halatta tayi Kasuwancinta da wannan kuɗin, tinda har ta tuba. Allah ya ce

فَمَن جَاءَهُ مَوْعِظَةٌ مِّن رَّبِّهِ فَانتَهَىٰ فَلَهُ مَا سَلَفَ وَأَمْرُهُ إِلَى اللَّهِ وَمَنْ عَادَ فَأُولَٰئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ

Wanda wa'azi daga Ubangijinsa, ya je masa, sa'an nan ya hanu, to yana da abin da ya shige, kuma al'amarinsa (ana wakkala shi) zuwa ga Allah. Kuma wanda ya kõma, to, waɗannan sũ ne abõkan Wuta, sũ a cikinta madawwama ne. (Suratul Baqara Aya ta 275).

Sabida haka babu lefi tayi kasuwanci da kuɗinta.

Allah shi ne masani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments