Ticker

6/recent/ticker-posts

Falalar Zuwa Masallacin Juma‘A Da Wuri

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum malam Ina fatan kana lafiya. Malam Ina da tambaya, idan mutum ya samu sallahr juma'a Amma bai samu Khuduba ba (ya zo an tada ikama) mene ne hukuncinsa? Inason ayi mana bayani akan falalar zuwa masallacin juma‘a da wuri

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Da yawa mukan shagalta da wasu al‘amura na rayuwar duniya har mu kwashe lokaci mai tsawo ba tare da mun damu ba, amma cikakkun awowi biyu (2hrs) ba zamu iyayi a wurin bautar Allah cikin nishad‘i ba. A ranar Juma‘a ana son zuwa Masallaci da wuri domin samun babbar rabo!

An karɓo Hadithi daga: Abu Hurairah (RA) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: ((Duk wanda yayi wanka, sannan ya tafi Masallacin Juma‘a (da wuri), yayi Sallah (ta nafila) gwargwadon abinda ya samu, sannan ya saurara, har Liman ya fito domin yin Khudubah, ya saurari Khudubah aka yi Sallah tare da shi: to, an gafarta masa abinda ke tsakanin Juma‘ar da kuma wata Juma‘a mai zuwa, tare kuma da bashi falala ta kwanaki uku)) [MUSLIM]

Zuwa Masallacin Juma'a da Wuri Yanada Tarin Lada Mai Yawa. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yana Cewa: (Wanda Yayi Wanka a Ranar Juma'a, Sannan ya Tafi Zuwa Masallaci a Farkon Lokaci, Yanada Lada kamar Yayi Sadaka da Rakumi. Idan Yaje a Sa'a ta Biyu kamar yàyi Sadaka ne da Saniya. Idan Yaje a Sa'a ta Uku kamar Yayi Sadaka ne da Rago. Idan Yaje a Sa'a ta Huɗu kamar Yayi Sadakane da Kaza. Idan Yaje a Sa'a ta Biyar kamar yayi Sadakane da Dabino. Idan Liman Yazo Ya Hau kan Mimbari Sai Mala'ikun su Rufe Takardunsu su tsaya Suna Sauraran Khuduba).

Wanda ya tafi a kasa zuwa Sallar Juma'a Yana Samun Ladar Azumin Shekara Guda da tsayuwar dare na Shekara Guda ga Kowane taku. Daga Ausi bn Ausi (ra) Daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce: (Dukkan Wanda Yayi Wanka a Ranar Juma'a (Wankan Juma'a) Yayi Sammako Yaje da Wuri, ya Zauna ya Saurari khuduba yayi shiru beyi Magana ba, Ya kasance yana da Lada ga Kowane Taku da Yayi Zuwa Masallaci, Yanada Ladar Azumin Shekara Guda da tsayuwar dare na Shekara Guda).

Saboda haka ‘Yan‘uwa mu dinga zuwa Masallaci da wuri. Allah ya bamu ikon gyarawa.

WALLAHU A'ALAMU

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments