Ticker

6/recent/ticker-posts

Banbancin Sufaye a Yakin Iran da Izra'ila

BANBANCIN SUFAYE A YAƘIN IRAN DA IZRA'ILA

Duk da munin Aƙidun Sufaye, amma ban san suna da tarihin ta'addanci a kan al'ummar Muaulmi ba.

A wannan zamani, za a iya cewa: ƙasar Moroco ita ce ƙasar da ta yi fice wajen tsayawa a matsayin gomnati mai bin tafarkin Sufanci, amma ban san tana da manufa ta mamaya, ko manufa ta zubar da jini da ta'addanci a kan sashen al'ummar Musulmi ba, ko abokan saɓaninsu.

Wannan ya sa idan Izra'ila za ta yaƙi Moroco, ko wata ƙasa da za a iya cewa ta Sufaye ce, to za mu goyi bayanta, saboda ba mu san Sufaye da zalunci da ta'addanci, da mungun nufi a kan al'ummar Musulmi ba.

Saɓanin Rafidha ƴan Shi'a masu mummunan shiri na mamayar ƙasashen Musulmai, tun daga ƙasashen Larabawa, har ƙasashen Afirka, da manufar ɗaukar fansar jinin Sayyidina Hussain (ra) a kan Nawasib, wato Ahlus Sunna (Sunny), waɗanda suke ɗauka a matsayin maƙiya Ahlul Baiti, jikanun Yazidu, mashaya jinin Hussaini (rs). A kullum suna shelanta sai sun ɗau fansa.

Wannan ya sa Gomnatin Rafidha ƴan Shi'a ta "Wilayatul Faƙeeh" (ولاية الفقيه), mai mulki a Iran, take da mungun nufi a kan Ahlus Sunna da ma'anarsa ta babban zaure (Sunny). Wato waɗanda suke kira "Nasibawa". Suka yi wani tsari (Plan) na shekara hamsin (الخطة الخمسينية), don mamaye ƙasashen Musulmi, har Makka da Madina, da gasa musu aya a hanu. Sun yi aiki da wannan tsari a ƙasashen Larabawa; gabashin Saudiyya, Bahrain, Kuwait, da kuma Yamen, Iraq da Syria da Labanon da sauransu. Hatta ƙasashen Afirka ba su tsira daga tsarin ba, ta hanyar abin da suka kira da cigaban mamayar Iran "تصدير الثورة" (Export of revolution). Tare da ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ta'addanci masu zubar da jinane, da ɓarna a bayan ƙasa.

A taƙaice, duk wanda ya san shirin Iran, da mugun nufinta a kan al'ummar Musulmi, ya san cewa; idan sharrin Iran bai fi sharrin Izra'ila ba, to za su yi kunnen doki. Ka tambayi tarihi a kusan nan, ka ji irin ta'addancin da Iran ta yi a Iraq, Syria, da Yamen, dss, da muzgunawar da take yi wa Ahlus Sunna ƴan ƙasar ta Iran. Wanda hatta Masallaci ba su da ikon mallaka.

A taƙaice, wannan faɗa da ake yi na Iran da Izra'ila, sauran Musulmai ba ruwansu da shi. Saboda ba faɗa ba ne na Addini. Azzalumai ne biyu suke faɗa da juna, saboda maslahohinsu na mamayar ƙasashen Musulmai.

Don haka idan Izra'ila ta ba da kashi wa Iran, sai mu taya ƴan Syria da Iraq dss murna. Haka idan Iran ta lallasa Izra'ila, sai mu yi murna, mu taya Falasɗinawa murna.

Sabda haka Rafidha azzalumai ne masu mungun nufi a kan Musulmai, kamar yadda Yahudawa ma haka, saɓanin Sufaye, su ba mu sansu da haka ba.

Ya Allah ka sa su ruguza junansu, ka dirkake su gaba ɗaya.

~ Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments