Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mace Ta Tada Ikama A Sallah

HUKUNCIN MACE TA TADA IQAMA A SALLAH

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin Mace Ce za ta Tada Iqama Idan Za su yi Sallah Da Mijinta, Ko Mijin ne?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

An tambayi Lajnatul da'imah Shin an shar'antawa mace tada iqama idan za ta limanci 'yan'uwanta mata Sallah? Sai Suka Amsa: ba a shar'antawa mace tada iqamar sallah ba, ita kaɗai zatai sallah ko za ta limanci matane, hakama ba a shar'anta musu kiran Sallah ba. fatawa lajnatul da'imah (6/84).

An tambayi shaik Bn baaz rahimahullah Shin ya halatta ga mace tai kiran Sallah ko tada iqama inzatai Sallah ko ba a halatta mata ba? Ya Amsa: ba a shar'antawa mace tai kiran sallah ko ta tayar da iqama ba a cikin sallar ta, wannan ga maza kaɗai ne, amma mata ba a shar'anta musu ba, zasuyi Sallah babu kiran Sallah ko Iqama. Maj-mu'u fatawa (10/356).

Saboda haka ba mace ce za ta tayar da Iqamar Sallah ba idan zasuyi sallah da mijinta, mijinne zai tayar da iqamar sallah, saboda su mata ba a shar'anta musu yin kiran Sallah ko iqama ba idan zasuyi Sallah.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments