Tambaya:
"Assalamu
alaikum. Don Allah dan uwa me zaka karar dani dangane da matsalar cika
ciki?".
Amsa:
Lallai abin da
ya tabbata a Sunnar Manzon Allah (saw) shi ne yin Azumi a ranar "Tasu'a da
Ashura". Wato ranar 9 da 10 ga watan Muharram, watan da muke ciki. Gobe
Juma'a 9 ga wata, Asabat kuma 10. Don haka yana daga cikin Sunna yin Azumi a
cikin wadannan ranaku guda biyu.
Manzon Allah
(saw) bayan ya yi hijira zuwa Madina ya yi Azumin Ashura, kuma ya yi umurni da
yinsa, kuma ya yi bayanin falalarsa.
Kuma saboda
saba ma Yahudawa, sai Annabi (saw) ya yi azamar yin Azumin Tasu'a, saboda su ma
Yahudawan suna yin na Ashuran, saboda a ranar ce Allah ya tsiratar da Annabi
Musa (as) daga Fir'auna da mutanensa. To amma kafin shekara ta zagayo Annabi
(saw) ya yi Tasu'an sai ya koma ga Ubangijinsa. Don haka za a yi Azumin Tasu'an
don a saba wa Yahudawa, don su ma sun kasance suna yin Azumin na Ashura.
Saboda sabawa
Yahudawa da Nasara da Mushrikai yana daga cikin Manufofin Shari'a.
To amma 'yan
bidi'a sun saba wa Sunna a game da ranar Ashura kamar haka:
1- 'Yan Shi'a
sun riki ranar Ashura a matsayin ranar nuna bakin ciki da kuka da zaman makoki
da sauran abubuwan da suke yi. Suna yin haka ne saboda a Ranar aka kashe jikan
Annabi (saw) Hussaini (ra).
To amma wannan
ba ya daga cikin Addini, saboda babu wanda ya ce ayi haka. Kuma babu wanda ya
yi daga cikin Sahabbai.
Kuma an kashe
wadanda suka fishi falala a wajensu, kamar babansa Aliyu (ra) da Dan uwansa
Hassan (ra) - wanda suke ganin kashe shi aka yi - amma ba su riki ranakun da
aka kashesu a matsayin ranakun bakin ciki ba, har suke yin irin abin da suke yi
a ranar Ashura saboda kashe Hussain (ra).
2- Nasibawa
makiya Ahlul Baiti: su ma wadannan 'yan bidi'a ne, wadanda suke kin Aliyu (ra)
da 'ya'yansa a matsayin kishiyantar 'Yan Shi'a. Su kuma sun riki wannar rana a
matsayin rana ta farin ciki da murna na kashe Hussaini (ra) jikan Manzon Allah
(saw). Wannan ya sa suke yin liyafa, da bikikuwa da yalwata abinci a wannan
rana. Duka don nuna murnan kashe Jikan Annabi (saw) Hussaini (ra), saboda
kiyayya da suke yi masa.
To wannan
babban laifi ne, saboda son Sahabbai, - musamman iyalan gidan Annabi (saw) -
yana daga cikin Imani. Aliyu (ra) da 'ya'yansa Hassan da Hussaini (ra) da
matarsa Fatima 'Yar Manzon Allah (ra) duka Sahabbai ne, kuma Ahlul Baiti ne.
Wajibi ne a sosu, saboda su Sahabbai ne, kuma su Dangin Annabi (saw) ne. Kinsu
yana daga cikin Munafurci.
Don haka
wadannan babban laifi suke yi.
'Yan Shi'a da
wadannan Nasibawa duka kowane bangare ya kirkiri Hadisan karya don tabbatar da
abin da yake yi na bidi'a a cikin wannar rana, alhali Hadisai ne na karya, ba
su da wata kima a Addini.
To su 'yan
Shi'a suna nan har yanzu akwaisu a wannan zamani, suna aikata bidi'o'insu a
wannar rana ta Ashura. Amma su Nasibawa babu su, sun kare tun tuni, kamar yadda
Malamai suka tabbatar. Amma kuma bidi'o'in da suke yi a ranar Ashura na cika -
ciki da yalwata abinci sun saura a cikin gama - garin al'ummar Musulmai, ana
aiki da wannar bidi'a ta cika - ciki a matsayin Eidi, har ake kiransa da
"Sallar Kaji", saboda jahilci, da kuma yadda jahilai suke yada
wadancan hadisan karya da aka kirkira a game da cika - ciki. Amma ba mutane
suna yin cika - cika ba ne saboda kin Ahlul Baiti, kamar yadda su wadancan 'yan
bidi'a Nasibawa suke yi, suna yi ne a bisa zaton cewa; Hadisan karya da aka
kirkira tabbatattu ne daga Annabi (saw).
Allah ya sa mu
dace gaba daya, ya yi mana afuwa da mu da iyayenmu a kan kuskuren da suka yi ta
yi a baya na aiki da bidi'ar cika - ciki.
Allahu A'alam.
Dr. Aliyu
Muh'd Sani (H)
30 September, 2017

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.