DAGA
CIKIN ƘA'IDOJIN FAHIMTAR ALƘUR'ANI
Hanyar koyon Tafsirin Alkur'ani
Duk wanda zai bi wata hanya, ko ya aikata wani aiki kuma ya zo masa ta hanyarsa da za ta kai gare shi, kuma ya zo masa ta kofarsa, to alal hakika babu makawa zai ci nasara, zai isa zuwa ga manufa da muradinsa, kamar yadda Allah ya ce: {Ku zo ma gidaje ta kofofinsu} [Baqara: 189].
Haka kuma duk lokacin da abu ya zama mai girma, to
nemansa ta hanyar da ta dace abu ne mai muhimmanci, kuma cikakken bincike a kan
mikakkiyar hanya mai sadarwa gare shi ya zama dole. Lallai babu shakka Tafsirin
Alkur'ani yana cikin abubuwa mafi girma da muhimmanci, kai, shi ne ma asali da
tushensu.
Ka sani, lallai wannan Alkur'ani mai girma, Allah
ya saukar da shi a matsayin shiriya ga mutane da abu mai dora su kan hanya,
kuma a kowane lokaci da zamani da wuri yana shiryarwa zuwa ga al'amura mafiya
shiriya mafiya daidaito da dacewa. Allah ya ce: {Lallai wannan Alkur'ani yana
shiryarwa ga hanya mafi daidaito} [Isra'i: 9].
Saboda haka, wajibi ne a kan mutane su koyi sanin
ma'anonin Maganar Allah kamar yadda Sahabbai ® suka koya daga Annabi (saw),
saboda sun kasance, idan suka karanta Ayoyi goma (10) ko kasa da haka ko sama,
ba sa wuce su har sai sun san abin da suke nuni gare shi na imani da ilimi da
aiki, kuma sun yi aiki da shi, kuma suna saukar da su a kan abubuwa da suke
faruwa na halin yau da kullum, suna yin imani da abin da suka kunsa na Aqidu da
labarai, suna mika wuya suna aiki da abin da ke cikinsu na umurni da hani, suna
dabbak'a su a kan dukkan abin da suka gani na ababen da suke faruwa da su ko
wasunsu, kuma suna hisabi ma kawunansu; shin sun tsayu sun ba da hakkinsu ko
kuma ba su ba da hakkinsu da abin da ake bukata ba?
Suna tambayan kawunansu, ta yaya za su tabbatu a
kan abubuwa masu amfani, su yi kokarin toshe gi'bin da aka samu daga wurinsu?
Ta yaya za su rabu da abubuwa masu cutarwa?
Sai suka wayi gari masu shiryuwa da ilimominsa,
suna siffantuwa da halayensa da ladubansa, kuma sun san cewa; Alkur'anin magana
ce zuwa gare su daga masanin gaibi da abin da yake zahiri, kuma sun san ana
bukatar su san ma'anoninsa, su yi aiki da abin da yake hukuntawa.
Duk wanda ya bi wannar hanya da Sahabbai suka bi,
ya yi kokari wajen tadabburin Maganar Allah, babbar kofa a Ilimin Tafsiri za ta
budu masa, hanyar saninsa ga abubuwa za ta karfafa, basirarsa za ta haskaka,
kuma zai wadatu da wannar hanya daga k'ak'ale-k'ak'alen wasu masu tafsirin, da
wasu bincike da ba muhallinsu ba ne, musamman in yana da kaso mai tsoka a
fannin harshen Larabci, kuma yana da damuwa da bangaren tarihin rayuwar Annabi
(saw) da halayensa tare da majibintansa da abokan gabansa, lallai wannan babban
abin taimako ne a wannan fanni na fahimtar Tafsirin Alkur'ani.
Duk lokacin da bawa ya san cewa; lallai Alkur'ani
akwai bayanin komai a cikinsa, kuma ya san cewa; ya lamunce mana dukkan
maslahohin rayuwa, kuma shi mai bayaninsu ne, mai kwadaitarwa a kansu, kuma mai
tsawatarwa daga dukkan abubuwa masu cutarwa, kuma ya sanya wannar ka'ida a
gaban idonsa, kuma ya yi amfani da ita a kowane abu mai faruwa, ko wanda ya
faru a baya ko wanda zai faru a gaba, to lallai girman wannar ka'ida da yawan
amfaninta da fa'idojinta zai bayyana gare shi.
Wannan shi yake nuna mana cewa; duk wanda yake so
ya fahimci Alkur'ani mai girma, ingantacciyar fahimta to ya koma ga fahimtar
Sahabban Annabi (saw) da tafsirinsu, da kuma na mabiyansu da kyautatawa cikin
Tabi'ai da mabiyansu, saboda su suka fi kowa fahimtar Alkur'ani, kuma suka fi
aiki da shi.
Dr Aliyu Muh'd Sani (H)
17 May, 2018
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.