Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Iya Tashin Abokina Daga Bacci Saboda Ya Yi Sallah?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaykum wa rahamatullahi wa barakatuhu. Da fatan mallam da duka jama'ar wannan fili na cikin ƙoshin lafiya. Tambaya ta, mallam, ita ce, mutum ne ya ke bacci, ya na cikin baccin nan har lokacin sallah ya yi, shin za'a tashe shi ne daga baccin ya yi sallah? Ko kuwa barin shi za'a yi har sai lokacin da ya tashi da kan shi, sannan ya yi ramuwar sallah?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Za'a tashe shi mana, in har ba lalura ce da shi ba, da zai cutu in ya farka, saboda a taimaka masa wajan aikata Alkairi, da yin sallah a lokacinta.

Allah ya umarci Muminai da taimakekeniya wajan biyayya ga Allah a aya ta (2) a suratul Ma'idah:

وَتَعَاوَنُوا۟ عَلَى ٱلۡبِرِّ وَٱلتَّقۡوَىٰۖ وَلَا تَعَاوَنُوا۟ عَلَى ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَ ٰنِۚ

Kuma ku taimaki juna a kan alkhairi da ƙarin taƙawa, kuma kar ku taimaki juna a kan zunubi da ƙetare haddi. (Surah Al-Maaidah: 2).

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam a cikin hadisin Abu-dawud ya yi adduar Rahma ga mutumin da ya ta shi da daddare don ya yi sallah ya ta shi matarsa, in ba ta tashi ba ya yayyafa mata ruwa.

In har bai samu wanda zai tashe shi ba, ya yi sallah bayan lokacinta ya wuce, to Allah ya ɗauke Alkalami akansa kamar yadda ya zo a hadisi tabbatacce.

Allah ne mafi sani.

Amsawa🏻

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments