NA TUBA DAGA LEKEN TSIRAICIN MUTANE
𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum wa rahmatullah. Malam na ga tambayar daka amsa game da masu leken tsaraicin mutane, Kuma naga amsar daka bayar. Harga Allah Nima nayi irin wannan abun Abaya wlh abun ya dameni har yanzu Malam na kasa sakewa, na tuba Amma har yanzu inata tsorata mallam mene ne mafita, saboda mutanen dana zalunta ta wannan hanyar?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Mafita ita ce ka yawaita nadama tare da neman
gafarar dukkan zunubanka (Istighfari), Kaji tsoron Allah ka kyautata ayyukanka
na gaba, sannan ka yawaita ayyukan alkhairi musamman ayyukan jin-kai da
taimakon al'ummah domin neman kusanci zuwa ga Allah.
Sannan kaje ka nemi yafewar wadanda ka yiwa wannan
laifin idan hakan bazai janyo tashin hankali ba, Koda ba tare da bayyanar musu
da irin laifin da ka zaluncesu dashi ba.
Idan kuma hakan ba zata yiwu ba, ka yawaita yi musu addu'ar neman gafara
misali acikin addu'o'inka ka rika cewa "YA ALLAH KA GAFARTA WA DUK MUTANEN
DA NA ZALUNCESU CIKIN KUSKURE KO RASHIN SANI KODA GANGANCI, KA YAFE MUN SUMA KA
YAFE MUSU LAIFUKANSU. KA SANYA ZALUNTARSU DA NAYI TA ZAMA KAFFARA AGARESU DA
LADA DA DAUKAKAR DARAJA".
Allah mai yawan falala ne kuma mai jin kai ga
bayinsa. In dai ka tuba tare da kyakyawar manufa kuma ka gyara ayyukanka, to
tabbas Allah zai yafe maka kuma zai kankare maka zunubanka. Domin Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce "ALLAH YANA KARƁAR TUBAN BAWANSA MUTUKAR DAI BAI KAI GARGARA BA
(WATO MUTUKAR DAI BAI KAI LOKACIN DAF DA FITAR RANSA BA).
Allah shi yafe mana baki daya.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.