Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Iya Jinkirta Isha'i Zuwa Lokacin Bacci?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, Malam Ina jinkirta sallah ISHA Sai nazo bacci, shin hakan ya dace?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam, bai halatta ga musulmi ba ya ji kıran sallah, ya ki tashi ya tafi masallaci, in ba da wani uzuri ba, Allah yana cewa a cikin suratun Nisa'i aya ta: 103:

إِنَّ الصَّلَاةَ كَانَتْ عَلَى الْمُؤْمِنِينَ كِتَابًا مَّوْقُوتًا 

"Tabbas Sallah wajibi ce akan muminai a çıkın lokuta kayyadaddu".

Jinkirta sallah dağa lokacin ta yana çıkın tozartata, Allah ya yi alkawarin saka wadanda suke tozarta sallah a wani kwari a cikin wuta, kamar yadda aya ta: 169 a suratul A'araf ta tabbatar da hakan.

Tozarta Sallah alama ce ta tozarta ragowar ayyukan alkairi, saboda ita ce ginshikin Addini, duk Wanda ya kiyaye Allah zai kiyaye shi, wanda ya kiyaye Allah zai same shi a gaban sa.

Allah ne mafi Sani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments