Ticker

6/recent/ticker-posts

Yawaitar Faduwar Gaba Sanadiyyar Istimna'i

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum ina fatan malam nacikin koshin lfy mlm matsalan dake damuna achan da ina yin istimna,i amma yanzu cikin ikon Allah nadaina saboda ina biye da shafin zauren fiqhu a facebook. mlm don Allah ina son ataimakamani saboda  kusan kullum inafamada mafarkin inasaduwa da mace amma  yanzu nadaina sai dai yanzu ina fama da bugawar kirji faduwan gaba mlm don Allah ina neman taimako albarkancin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam. kahuta lfy daga Ibrahim sokoto

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.

Istimna'i wanda a turance ake kiransa 'Masturbation' wani abu ne da wasu samari har 'yan mata ke yi ta hanyat taɓa al'aurorinsu domin biya wa kansu bukata.

Yana haifar da matsaloli da yawa ga lafiyar mutum har addininsa ma. Daga cikin matsalolin akwai samun shafar aljanu ta sanadiyyar wannan dalilin. Sai kuma raunin idanu, raunin al'aura, rikicewar tunani, dakushewar kwakwalwa (wato toshewar basira) faduwar gaba Da sauransu.

Kamar yadda kayi bayani, gaskiya duk waɗannan abubuwan da kakeji suna daga illolin da istimna'in yake haifarwa. Don haka shawarar da zan baka anan ita ce ka yawaita tuba da kuma gyara ayyukanka na addini, sannan ka yawaita zikirin Allah da karatun Alqur'ani da nafilfili.

Ka kiyayi leka shafukan yanar gizo wadanda ke ɗauke da hotuna ko labarai na batsa. Ka kiyayi duk abinda zai janyo maka motsawar sha'awar aikata zina. In kana da halin yin aure ma ya kamata kayi domin tsare mutuncinka.

Matayen Aljanu sukan shiga jikin namiji saurayi alokacin da ya keɓance kansa yana aikata istimna'i ko a toilet ko dakinsa. Shi yasa mafiya yawan masu aikatawa zaka samu suna da shafar aljanu ajikinsu. Haka ma mace budurwa idan ta keɓance kanta tana aikata wani abu irin wannan, to yakan kasance mazajen aljanu su shiga jikinta.

Don haka Ka rika tofa waɗannan ayoyi da surori acikin ruwa kana sha kana shafe jikinka dashi kullim kafin ka kwanta barci :

1. Fariha 7.

2. Ayatul Kursiyyi 41.

3. Suratu Yaseen 1.

4. Suratul ikhlas 11.

5. Suratul falaq 11.

6. Suratun Nas 11.

In shaAllahu zaka samu lafiya. Idan kuma ka gwada waɗannan amma abun bai ta fi gaba daya ba, ka tuntubi ZAUREN FIQHU ta kan wannan lambar kamar haka :07064213990.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments