𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum mallam don Allah ya halasta a sha jinin dabba domin magani? an ce in saman ma yarana kunkuru in dafa musu kuma in basu jinin da maltina su sha. Na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salam, ƴar'uwa malaman Musulunci sun haɗu a kan cewe haramun ne a sha jini ko a yi wani amfani da
shi, saboda jinin da ya zuba daga jikin mutum ko dabba najasa ce. Allah Ta'ala
ya haramta jini a Alqur'ani Mai girma a inda yake cewa:
حُرِّمَتْ عَلَيْكُمُ الْمَيْتَةُ وَالدَّمُ وَلَحْمُ الْخِنزِيرِ
وَمَا أُهِلَّ لِغَيْرِ اللَّهِ بِهِ وَالْمُنْخَنِقَةُ وَالْمَوْقُوذَةُ وَالْمُتَرَدِّيَةُ
وَالنَّطِيحَةُ وَمَا أَكَلَ السَّبُعُ إِلَّا مَا ذَكَّيْتُمْ وَمَا ذُبِحَ عَلَى
النُّصُبِ
An haramta muku mũshe da jini da nãman alade da
abin da aka ambaci sũnan wanin Allah a gare shi, da mãƙararriya da jefaffiya da mai gangarõwa da sõkakkiya, da abin
da mãsu dãgi suka ci, fãce abin da kuka yanka, da abin da aka yanka a kan gunki
(shĩ ma an haramta). ( Suratul Má'ida aya ta: 3).
A wata ayar kuma Allah ya ce:
قُل لَّا أَجِدُ فِي مَا أُوحِيَ إِلَيَّ مُحَرَّمًا عَلَىٰ
طَاعِمٍ يَطْعَمُهُ إِلَّا أَن يَكُونَ مَيْتَةً أَوْ دَمًا مَّسْفُوحًا أَوْ لَحْمَ
خِنزِيرٍ فَإِنَّهُ رِجْسٌ أَوْ فِسْقًا أُهِلَّ لِغَيْرِ اللَّهِ بِهِ فَمَنِ اضْطُرَّ
غَيْرَ بَاغٍ وَلَا عَادٍ فَإِنَّ رَبَّكَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ
Ka ce: ''Bã ni sãmu, a cikin abin da aka yõ wahayi
zuwa gare Ni, abin haramtãwa a kan wani mai ci wanda yake cin sa fãce idan ya
kasance mũshe kõ kuwa jini abin zubarwa kõ kuwa nãman alade, to lalle ne shi ƙazanta ne, kõ kuwa fãsiƙanci wanda aka kurũrũta, dõmin wanin Allah da shi.'' Sa'an nan wanda larũra ta kãmã shi, bã mai fita jama'a
ba, kuma bã mai ta'addi ba, to, lalle Ubangijinka Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. (Suratul An'am aya ta: 145).
Malaman tafsiri sun ce jinin da ke kwarara shi ne
wanda yake zuba daga jikin dabbar da aka yanka ko ta sanadiyyar jin ciwo, ko
saboda wata lallura daga jikin mutum ko dabba. Sai hakan ya cire hanta da saifa
daga cikin jinin da aka haramta, saboda ba a raba hanta da jini, kuma su jinin
da ke tare da su ba mai kwarara ba ne, shi kuma Allah ya bayyana cewa jini mai
kwarara ya haramta a waccan ayar ta suratul An'am.
Imamul Qurɗubiy a cikin
littafin Tafseerinsa ya ce: "Malamai sun yi ittifaqi cewa lallai jini
najasa ce kuma haramun ne, ba a cin sa, kuma ba a amfani da shi". Dubi
Aljámi'u Li'ahkamil Qur'an (2/221).
Imam Annawawiy ma ya ce: "Dalilan da ke nuna
zaman jini najasa bayyanannu ne, ban san wani da ya saɓa daga cikin musulmai ba, sai dai abin da mai littafin
Alhaawiy ya hakaito daga wani mai Ilmul Kalam da ya ce jini na da tsarki, sai
dai ba a lura da ƴan Ilmul Kalam a cikin abin da aka yi ijmá'i, da saɓawarsu a kan
Maz'habi ingantacce wanda mafi yawan malaman Usulu suke a kai, daga ƴan maz'habarmu da
wasunsu, musamman a mas'aloli na Fiq'hu". Almajmú'u Sharhul Muhazzhab (2/557).
Saboda haka ƴar uwa jinin da ya zuba a jikin dabba ko mutum najasa ce, kuma haramun ne a
ci ko a sha, ko a yi wani amfani da shi bisa ijma'in malaman Musulunci. Kenan
sai ki nemo wata hanyar maganin halastacciya da ba wannan ba.
Allah S.W.T ne mafi sani.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.