Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Azumi Don Neman Biyan Wata Bukata

๐“๐€๐Œ๐๐€๐˜๐€

Assalamu alaikum Malam Shin zan iya ษ—aukan azumi na kwana uku Domin fatan Allah ya karษ“i addu'a na ya biya min wasu bukatuna?.

๐€๐Œ๐’๐€❗️

Wa alaikis salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.

Eh kwarai kuwa ya halatta Musulmi ya ษ—auki wata nau'in ibada wacce ake neman kusanci ga Allah da ita, ya yita musamman domin neman biyan wata bukatarsa awajen Allah Subhanahu wa Ta'ala.

Misali kamar sallolin nafila, azumin nafila, karanta wasu surori na Alqur'ani, taimakon marayu, ciyarwa, tona rijiyoyi, Gina makarantu ko asibitoci ko masallatai, da sauransu. Duk wanda mutum yayi tare da kyakkyawar niyyah Allah zai karษ“a masa ya biya masa bukatarsa. Idan kuma wata musiba ce yake neman yayewarta awajen Allah, zai samu abinda ya nufa.

Hujjah kamar yadda yazo cikin hadisin Sahihu Muslim : "Ku riskar da bakin cikinku da damuwarku ta hanyar yin sadakoki. Allah zai yaye muku chutarku kuma ya taimakeku akan makiyanku".

Amma dai abinda akafi so ga Mumini shi ne yayi ayyukan ibadarsa domin neman yardar Allah kaษ—ai ba tare da neman wata amfanuwa irin ta duniya ba. Idan kuma Allah ya dubeshi da rahamarsa ya biya masa wata bukatar duniya to shikenan. Amma dai ba ita kaษ—ai aka nufa ba.

Dagewa da nau'o'in ibadu musamman domin neman yardar Allah da kusanci gareshi, sunnah ce ta salihan bayin Allah daga magabata. Musamman idan muka kalli rayuwar mutanen kirki irin su : Fudhayl bn 'Iyadh, Imam Hasanul Basariy, Rabi'atul Adawiyyah, Nafisatul Hashimiyyah, Hasanatul Abidah da sauransu.

Waษ—annan duk Salihan bayin Allah ne da suka rayu cikin rashin wadatar abun duniya amma suna yin ibadah dare da rana tare da yin azumin nafilah kullum don neman yardar Allah kaษ—ai ba tare da neman wata bukata ta duniya ba.

Idan muka duba cikin Alqur'ani zamu ga yadda Allah yake bada labarin Annabawansa irin su Annabi Zakariyya wanda yakan tashi yayi sallolin dare ko azumi kuma harma yayi addu'ar neman haihuwa, kuma Allah ya biya masa bukatarsa.

Ibnu Jareer Attabariy (rahimahulLah) acikin tafsirinsa (juzu'i na 12 shafi na 347) ya ce : "Wanda duk ya aikata wani aikin alkhairi don neman amfanuwar duniya kaษ—ai, kamar azumi ko sallah ko tsaiwar dare, to Allah ya ce zai biya masa bukatar tasa ta duniya ษ—in, amma aranar lahira aikin nasa zai lalace ba zai samu komai awajen Allah ba.".

A takaice dai Malamai sun raba abun kashi-kashi kamar haka :

1. Idan mutum ya nufi lahira kaษ—ai, Allah zai karษ“a ya tabbatar masa da ladansa. Koda wasu bukatunsa sun samu tabbatuwa anan duniya, wannan ba zai rage masa ladansa awajen Allah ba.

2. Idan mutum ya raba niyyarsa biyu, yana son bukatar duniya, kuma yana neman lada awajen Allah, to Malamai sun yi saษ“ani. Amma dai ra'ayi mafi karfi shi ne, Allah zai kyaleshi da aikinsa ne. "Domin Allah ba ya karษ“ar wani aiki sai wanda akayi dominsa kaษ—ai" - inji Shugaba Sallallahu Alaihi Wasallam.

3. Idan kuma zallar bukatar duniyar ce kaษ—ai agabansa, to Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce : "Wanda hijirarsa ta zamto domin duniya ne ko wata mace da yake so zai aura, to ladan hijirarsa yana cikin abinda yayi hijirar dominsa.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

๏บณُ๏บ’๏บคَ๏บŽ๏ปงَ๏ปšَ ๏บ๏ปŸ๏ป َّ๏ปฌُ๏ปขَّ ๏ปญَ๏บ‘ِ๏บคَ๏ปคْ๏บชِ๏ป™َ ๏บƒ๏บทْ๏ปฌَ๏บชُ ๏บƒ๏ปฅ ๏ปŸَ๏บŽ ๏บ‡ِ๏ปŸَ๏ปชَ ๏บ‡ِ๏ปปَّ ๏บƒ๏ปงْ๏บ–َ ๏บƒ๏บณْ๏บ˜َ๏ปْ๏ป”ِ๏บฎُ๏ป™َ ๏ปญ๏บƒَ๏บ—ُ๏ปฎ๏บُ ๏บ‡ِ๏ปŸَ๏ปดْ๏ปš

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

๐–๐‡๐€๐“๐’๐€๐๐๐Ÿ‘‡

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

๐…๐€๐‚๐„๐๐Ž๐Ž๐Š๐Ÿ‘‡

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ษ—aya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan ฦ˜ur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waษ—anda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ฦ™arin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments