Ticker

6/recent/ticker-posts

Sun Yi Aure Ba Ta San Ba Shi Da Lafiya Ba

TAMBAYA (10)

Aslm Allah ya qarama malammamu lpy Ameen tambayata ita ce nayi aure yanxu cikin shekara ta biyu ce muke ashe shi mijin nawa bayada lapiyar gaba kuma bai fadi ba yaboye muna har akayi aure mlm koya kwanta dani banjin komae mlm yanxu takae da inya kwanta dani ina sabama Allah ina abinda Allah bayaso 😭😭 to yanxu nabar barin ya kwana dani tunda sai yayi ne ya motsamin da shaawa kuma baya iya biyamin ita   har nabiyewa son zuciya ina sabama Allah 😔mlm inada laifi nan? Dan Allah mlm kaban shawara😔

AMSA:

Indai ta fannin neman magani ne wannan ai ba wata matsala ce babba ba, kisa a ranki ai gashinanma har ya warke (idan har ya tashi da gaske ya nemi magani) saboda hadisin Ma'aiki SAW wanda ya ce wanda aka karbo daga Abu Hurairah (RA), ya ce: Annnabi (SAW) ya ce: "Babu wata cuta da Allah SWT ya halitta face ya halicci maganinta" (Bukhari 7563 da Muslim 2220)

Na biyu, kinyi wasu laifuka guda biyu na farkonsu shi ne biyawa kanki buqata da kikeyi da hujjar fakewa da cewar ai wanda zai biya miki buqatar bashida lafiya wanda malamai suke kiran wannan biyawa kai buqata da suna "Istimna'i" (wato wasa da al'aura har sai mutum ya biyawa kansa buqata) wanda a likitance hakan yanada illa sosai ga lafiyar mutum. An samu banbancin ra'ayin malamai akan "Istimna'i" wanda mazhabin Hanafiyya da wani sashe na Hanabila sun ta fi ne akan cewa asali dai yin Istimna'i haramunne, to amma yana iya zama halal tare da wasu Sharudda, sukace nafarko ya kasance Mutum bashi da aure, nabiyu ya kasance in baiyi hakanba to ba makawa dole sai yaje yayi Zina, na uku kada yayi nufin jindadi kawai, saidai yayi nufin yana sone yakarya karfin-Sha'awarne, kokuma ya kasance idan Mutum baiyiba hakan na iya haifar masa da wata cuta ajikinsa, sukace idan akwai irin waɗannan Sharudda to ya halatta Mutum yayi Istimna'i, saboda ka'idar nan ta Usul da take cewa:

        (إرتكاب أخف الضررين)

Mafi rinjaye kamar bangaren Malikiyya sun ta fi akan cewar haramunne

Saboda fadin Allah SWT a cikin Suratul Muminun ayata 5:

ُوالَّذِينَينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ..........

​​MA'ANA:​​ ​​(Muminai) sune waɗanda suke kiyãye farjinsu (bãsayin zina kuma bãsa yarda kowa yaga tsiraicinsu)…………har zuwa ƙarshen ãyõyin:

Sai kuma laifi na biyu mai girma da kikai shi ne qauracewa shimfidar mijinki wanda hadisi ya tabbata cewar mala'iku zasu kwana suna tsinewa duk matar da mijinta ya nemeta kuma ta bijire masa (zasuyita tsine mata har sai mijinnan ya haqura), sannan kuma Annabi SAW ya ce idan miji ya nemi matarsa ko da akan abin hawane to ta gaggauta biya masa buqatarsa

Wadannan sabon da kike yiwa Allah SWT ya kamata ki gaggauta yin taubatun nasuha ma'ana ki qudirci niyyar bazaki sake ba

Kada ki manta don kin yarda da kalmar shahada ba hakan yana nufin Allah bazai jarabceki a rayuwa ba domin kuwa wadanda akafi jarabta a cikin mutane sune Annabawa sai na kasa da su. Allah SWT ya ce:

( أَمْ حَسِبْتُمْ أَن تَدْخُلُوا الْجَنَّةَ وَلَمَّا يَأْتِكُم مَّثَلُ الَّذِينَ خَلَوْا مِن قَبْلِكُم ۖ مَّسَّتْهُمُ الْبَأْسَاءُ وَالضَّرَّاءُ وَزُلْزِلُوا حَتَّىٰ يَقُولَ الرَّسُولُ وَالَّذِينَ آمَنُوا مَعَهُ مَتَىٰ نَصْرُ اللَّهِ ۗ أَلَا إِنَّ نَصْرَ اللَّهِ قَرِيبٌ )

البقرة (214) Al-Baqara

Ko kuna zaton ku shiga Aljanna kuma tun misãlin waɗanda suka shige daga gabãninku bai zo muku ba? Wahalõli da cũta sun shãfe su, kuma aka tsõratar da su har manzonsu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi su ce: "Yaushe taimakon Allah zai zo?" To! Lalle ne, taimakon Allah yana kusa!

Mafita: Ki shawarci mijinnaki yaje Islamic chemist wadanda suke bada sahihin maganin irin cutar da take damunsa, in sha Allahu zai warke. Domin kuwa daman kowa da irin halittar karfin sha'awarsa kuma mata sunfi maza karfin sha'awa. Don haka kiyi masa uzuri tare da shawartarsa ya nemo magani

Na biyu, idan bai dauki shawararki ba to sai ki je ki sami waliyyanki ki sanardasu ga halin da ake ciki. Kada kiji nauyi ko kunya domin kuwa a wannan yanayin babu wani batun kunya saboda magana ake ta magani da kuma neman hanyar ceto ki daga halaka

Na uku, ki ci gaba da yi masa biyayya har bayan anyi masa maganin ki tuno cewar zaman ibada (bautar Allah kikazoyi) bawai iya zaman biyan buqatarki kikazo kiyi ba. Amman duk yanda za'ayi kada ki kashe aurenki saboda matsalar da za'a iya maganinta, shaidan ne yake kokarin ya rinjayeki domin kuwa kashe aure shi ne babban abinda yafi so idan kin dauke laifin shirka, kuma kashe auren zai zame miki danasani la'akarida in kika ji labarin matsalar wasu ma'auratan to zakice ashe nawa nafila ne akan na wasu. A karshe muna miki fatan haqurin zaman ibada da kuma fatan samun lafiyar mijinki

Wabi hazal qadari kifaya. Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa:

✍️Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments