Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Mutum Zai Iya Yi Wa Kansa Karin Karatu

SHIN MUTUM ZAI IYA YI WA KANSA ƘARIN KARATU?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Malam Dan Allah inada tambaya Amma dai Dan Allah kada a gaji dani kada tambayoyina su fara yawa. Malam na kasance a lokacin da na taso ina yarinta karatun da nayi na islamiya ba wani sosai bane saboda na sanya wasa a lamarin Amma kuma gaskiya ko malamanmu sun sani a lokacin ina da saurin ɗaukar karatun cikin kaina sai dai kuma yanzu ina son karatun gashi kuma a inda Nike kasuwanci wlh babu islamiyya kwata kwata Amma ina ta qoqarin yiwa kaina qari da sauraron karatun sudais da na sauran maluma to sune dayake na iya tada baqi sai in ɗauko Alkur'ani ina yiwa kaina qari shin malam tambayana anan yana da kyau mutum ya dinga yiwa kansa qari?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatulLahi wa barakatuhu.

A'a yadda kakeyi ɗin babu laifi saboda larurar da kake ciki. Maimakon zama haka baka yin komai, yana da kyau ka rika karanta Alqur'anin kamar yadda na baka shawara achan baya.

Amma kasan shi ilimi nakaltarsa akeyi daga bakunan Malamai, babu damar mutum ya ɗauki littafi ya karanta da kansa ba tare da samun jagoranci daga wani Malami masanin wannan fannin ba, to hakanan shima karatun Alqur'ani fanni ne na musamman wanda yana da Maliman dake karantar dashi bisa Qa'idodin yadda ake karantashi bisa duk riwayar da mutum ya zaba. Amma in dai ɗauka zakayi da kanka ka karantashi ba tare da naqaltarsa daga bakin wani malami masani akan fannin ba, to za'a samu ta'adi da ɓarna acikin karatun naka kuwa.

Matsalar zata zamto mai sauki gareka idan ya zamto daman ka riga ka koyi ilimin tajweedi kuma ka kware, kasan nau'in maddodi da Qalqala da hukunce-hukuncen harrufa da siffofinsu da makharij da sauransu.

Shawarar da zan baka ita ce idan kasan kana da ilimin tajweedi, kaci gaba da yin yadda kakeyi ɗin nan amma tare da bin shawarwarin wani Malami masanin abin, koda ta hanyar yin waya dashi ne, kana tambayarsa abinda baka fahimta ba. Idan kuma babu ilimin wannan fannin tare dakai, zaifi kyau ka hakura kaci gaba da maimaita wuraren da ka karanta agaban Malamai, ka jira duk sanda ka dawo gida Arewa ka koma wajen malamanka kaci gaba da dora karatun.

Allah shi Qara maka kokari da jajircewa, ya sanyamu dukkanmu cikin ceton Alqur'ani mai girma.

WALLAHU A'ALAM.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments